kukanma ya dauke azaba ta yi azaba kuma ga abinda mijinta yace
Mama ta ce" Elhaji a kaita asibiti mana, sannu Allah ya raba lafiya"
Daga haka maman ta juya da nufin komawa
Da mamaki ya ce" A'a, yaya zaki ce haka ki juya , wai yaya zaku tsaya wasa da haihuwa ne? Ke ku kamata a kaita asibiti" ya fada yana duban su KHausar dake tsatsaye, domin a lokacin da TAUFEEK ya maka wayar da suka yi da Mama a kas ya fice bai ce da ita ufan ba ta fito a guje ta bi bayansa tana ihun lafiya? Sai ta ga ya nufi bangaren Yumnah, da farko ta so komawa sai sai sunna tunkara ta ga an talabo Yumnar, a dole ta karasa tana aukin sannu, sai dai abinda ya fada ya saka su Dukansu rikicewa a lokacin da TAUFEEK, professeur TAUFEEK ya dubi tsabar idannuwan MACEN dake kan gwuiwa matarsa yace idan har aka fita da ita a bakin aurenta, sannan ya dubi mahaifiyarta yace da ita babu wanda ya isa ya wulakanta min uwata in ga darajarsa a duniya ko waye, sai kuma ya kalli HAJIA nawarah wace ta fara sarewa yace da ita a yau a gidan nan ko Ni ko ke, sai suka idasa sarewa duniya baki dayansu
HAJIA ce ta yi gagawar fadin" A kama wace? Sunna da damar tafiya da ita ama ka ji ai abinda mijinta yace , duk shegiyar da ta isa ta fita da ita a bakacin aurenta!"
Da mamaki Mai kwanoni ya sake yinkurawa zai yi wata maganar da tsawa da kuma rarashi da fadan a yi maza a kai baiwar Allah asibiti sai Yumnah ta yi wani irin ihu da nishi wanda ke nuni du inda kan d'a yake yana daf da zuwa duniya
A rikice suka rikice, gasu a falo su duka, Mama tuni ta komawarta dakinta ta datse da ky dan ta san mai kwanoni na iya cenza mata ra'ayi YANZUN nan, ita kuma ta yi rantsuwa babu ruwanta, abin ya isa haka, iskancin ya kai wajen da ba zata iya dauka ba kuma!
Kiri kiri TAUFEEK ya yi tsaye kikam a lokacinda KHausar ke sake sakin nishimai tare da bayanin fitowar kan Da daga jikinta
Da sauri mai kwanoni ya fice, kusan suka fita tare shi da KHausar wace ta yi bangarenta da gudu ta warto Safar hannu da kayan aikinta ta juyo da gudu gudu tana saka Safar hannun ta koma dakin hankalinta tashe , kana ganninta ka san taimako ne zata bada dan ceton rai
Wato an yi gudun Gara an fada gidan zago, sai ga KHausar din da aka so sai an haihu ta ji duke gaban Yumnah ฦafafuwan Yumnah Ware a irin mummunar warewa, jikinta bude a budewar da ko mijinta da wahala in ya taba gani a zamantakewarsu, jiki ya aune halitta ta zazago ta bude kai ya bado tana ihun azaba da ni'imar ubangiji har kai ya fito KHausar ta kama cikin kwarewa na cikakkiyar likita mai ruwa da tsaki a fannin amsar haihuwa ta juya jikin baby cikin dabara ta fitar da hannu daya sannan ta sake juyawa ta fitar da dayan kafin ta janyo babyn da ta tsalara kuka kamar a baakinta aka fara gwajin kukan, ta mike ta mikawa Aunty Akilah dake hawaye, hawayen girma irin na hukuncin ubangiji wanda ya fi kowa tsara komai, wannan shine kana naka Allah na nashi,daga wannan idan mahaifiyarsu da kanwarta suka ci gaba da wani abin to lalle zata dage da sanarwa ubangiji kan ya shirye su baki daya, a raunane ta sake kallon mijin kanwar nata wanda ya juya ya fice a lokacin da aka shiga musayar yawun ta karu, sai an yi mata ษinki, gashi ya Hanna fitar, wannan shine ga koshi ga kwanan yinwa , ga amsar haihuwa daga wajen kishiya ga kuma ษinki da kishiyar zata mata.........
*ASALAMU ALAIKUM WA RAHAMATULAH YAN UWA, SAKWANI NA SAMUNA SOSAI TA MAGANA KAN TALLAH DA NA SAKA , ANA CEWA TA YI YAWA, HAKANE KAM TALLAH NA SAKATA SOSAI MASHA ALLAH, A HAKAMA NA RUFE AMSA NE , KU YI HAKURI TALLAR NAN DA KUDI NE NAKE YINTA๐๐ฅน , ama idan da wace zata maida masu kudadensu sai na bayar da account numba a maida masu sai na daina sakawa in sha Allah, daya ta biya Ni a kudinmu na Nijar jaka arba'in, dayar kuwa ta saka dubu goma dan mutunci, na gode๐๐๐๐๐๐๐๐*
๐๐๐๐โคโ๐ฉนโคโ๐ฉน๐๐๐๐
*DA CIWO A ZUCIYATA*
๐๐๐๐โคโ๐ฉนโคโ๐ฉน๐๐๐๐
_MALLAKIN_
*SAJIDA NIJAR*
*FREE BOOK NE* 6๏ธโฃ4๏ธโฃ
*GARABASA, GARABASA, PROMOTION, PROMOTION DIN LITATAFAN MARUBUCIYAR A KAN FARASHI MAI SAUKI 1K, YAN NIJAR KUWA 1000 FRANCS CEFA*
1: Duk karyar kada
2: Yar mahaukaciya
3: Neman na kaina
4: Bani da zabi
5: Bak'a ce
6: Kutkale
7: Makauniya ce
8: Mage
9: Duk nisan jifa
10: Idan ka raina inda kake
11: Dutse
12: Alkalamin kadarata
13: Bani da zabi
14: Dakika Biyar
15:Wata kokowar
16: Aure yakin mata
17: Ni zan ladabi
18: Daga tafia daukar soja
*Dukansu a kan farashi mai sauki, zaka saka dubu guda ne domin promotion ne nake yi, ka tuntubeni kan layina kamar haka +227 93 81 16 18, Sajida Nijar*
Now
*Da CIWO A ZUCIYATA*
*Tallah, tallah, tallah*
*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*
_Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_
Farar Humura
Bakar Humura
Humura special,
humura de bain
Humura epicรฉ
Lait de nuit
Parfums dรฉsodorisant
Parfums rideau et dras
Lait de nuit
Alkam
Kulakcam
*Waษannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa*
Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes
*Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:*
mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata
Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai๐๐
Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuษi wannan number 97 82 44 94
*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*
Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata๐๐๐๐๐
Tallah 3
Hajiata, ke kin san rayuwar aure sai da anini, in babu jagab a babar eriya oga ya kama tofa yawu da neman yadda zai yi bawan Allah, idan kuma babar haja a bude ham ai ba labari oga sai dai ya shiga ya fito kamar ya shiga kofar ruwa๐, zo ki ji, a farashi mai rahusa zaki gwangwaje ki rike bakin Elhaji gudun tada yara, ama idan lamari ya yi lamari tsaf zaku karya gadoโน๏ธ๐ซฃ
๐ฅ๐ฅ๐ฅ๐ฅ๐ฅ๐ฅ๐ฅ๐ฅ๐ฅ๐ฅ๐ฅ๐ฅ๐ฅ๐ฅ
*HOHOHO WANI KAYA SAI AMALE, DON JAKI BAZAI 'DAUKA BA, INA MATA MASU BUK'ATAR 'DAGA DARAJARSU A WAJAN MAZAJENSU INA MATAN DAKE SHAN WULAK'ANCIN MIJI KO NA KISHIYA ,INA MATAN DAKESON ZAMOWA MOWA AGIDAJEN AURENSU TO ALBISHINRU MAMAN ZARAH YAR MUTAN SOKOTO TA SHIRYA TSAF DOMIN GABATAR MAKU DA ZAFAFAN KAYAN MATA MASU KYAU DA INGANCI WANDA BASUDA ALGUS ACIKI , AKWAI MAGANI DANAYI BINCIKE AKANSU DAN FARIN CIKIN MA'AURATA NAMU BA IRIN NASU BANE KAYAN MU NA DABAN NE NA ASALIN SAKKWATAWAN SHEHU MASU ABUN MAMAKI* 07034251528
kayanmu masu inganci ne masu ladaftar da kowane irin namiji
Kad'an daga cikin abubuwan da muke dasu
Ingantaccen maganin nono , Wanda zai gyara maki nononki donmin dawo da martaban nononki acikin kankanin lokaci komai lalacewarshi kuwa sauran bayani sai mun had'u pc +234 703 425 1528
Maganin hips (hips up) Wanda zai ciko maki da hips dinki su cika suyi bul bul ga laushi dasu k'ara suyi dass abun sha'awar kowane namiji
Maganin infection Sha yanzu magani yanzu Yana fatattakar sanyi cikin kankanin lokaci magani ne na maza da Mata insha Allah kowane irin sanyi gareki kikayi amfani dasu anwuce wajan
Ingantacce Kuma sahihin maganin k'iba Wanda Zaki ciko acik kankanin lokaci zakiyi kibar ki Yar dai dai misali ki huta Zama da Rama Baki rasa ci ba Baki rasa sha ba amma kullum Ana kallon cewa kinada matsala agidan aurenki saboda wannan ramar , Rama batayi ba Sam Yar uwa
Sabulun wanka
Kalolin sabulun tsarki
Turaren tsugunno
Turaren al'ajab
Hatsabibin turare
Da sauransu 07034251528
Kalolin gumba
Gumbar Dabino
Gumbar gero
Gumbar madara
Gumbar matsi
Gumbar ukku bala'i
Gumbar tada zaune tsaye
Gumbar sabon budurci
Gumbar sa buzu kuwa
Gumbar aya da kwakwa
Gumbar ridi
Gumbar mazari
Sarauniyar gumba 3in1
Da sauran kalolin da bansamu fadi ba,
Kalolin gari
Garin mallaka
Garin hutar da malaminki
dakan jaraba
Dakan Amare
Dakan Ni'ima
Dakan kishiya in bakiyi bani waje
Garin sa buzu kuwa
Garin buje.sharkaf
Garin Dan la'asar
Yayan hadiya mai suna dan la'asar
Original Dan goshi
Original Dan goshi (sabon salo)
Original man damo
Original man ayu
Kitsen damo
Sirrin tafin kafa
Sirrin farinjini na uwargida da amarya harma da yan mata
Kwallin idonka idona
Muna hada set na sirrin mallaka hajiya ba boka ba Mallam sai tarin sirrika kema kizama kowa agidan surenki
Akwai hadin sabon budurci ga yarinyar data rasa budurcinta ta hanyar fyade ko yaudarar d'a namiji da izinin Allah akayi maki wannan hadin to an wuce wajan sauaran bayani sai mun had'u pc
Kalolin tsumi
Tsumin mallaka
Tsumin jaraba
Tsumin madarar ni'ima
Tsumin tabaje
Tsumin Amare
Tsumin sabon budurci
Tsumin nono rakumi
Matan gaske
Ruwan jaraba,
Da sauran kalolin da ban fada ba
Kalolin matsi da basuda illa ajikin mace sai dai ma sukara maki lafiyar
Matsin Dan mannau
Matsin mallaka
Dan la'asar
Sabon budurci
Mak'alemata
Mashahurin matsi
Ukku bala'i
Matsin uban budurwa
Akwai gumba ta matsi wadda Shanta akeyi ga matan da basa son yin matsi
Muna hada set ga wadda Allah ya jaranfa da matsalar fyade har yarasa budurcinta , muna hada mata kaya ingantattun don dawo da martabar ta,
Hohohohoho in ana dara fidda uwa ake
*Kyallen al'ajabi* babban sirrin mallaka mai abun al'ajabi mallaki naki don samun damar shiga cikin jerin mata masu fada aji a gidan mazajensu ,
KARKU manta da sunan maman zarah sokoto sayen nagari maida kudi gida
07034251528 ina maraba daku sayen daya ko sari ina Sokoto sannan ina aikawa kowane gari cikin aminci da yardar Allah
Ga Wanda suke bukatar ganin kalolin kayana to suyi sarving number na suyimun magana nayi sarving number ku zaku dinga ganin kalolin kayana a status ngd sosai 07034251528
Maman zarah mabera SOKOTO
Ba tare da KHausar ta saka komai a ranta ba, ta haษa allurar ษinkin nan ta saka wata Safar ba ta yi kyankyaminta ba, bata yi komai ba ta sake zaunawa ta mika hannu da nufin janye rufar da mahaifiyarta ta yi mata tana share mata hawaye kanta a kirjinta ta yi mata mugun rikon da tabas sai ya tambayeta domin rikon MACEN dake kan gabar haihuwa ai riko ne na neman ceton rai
Maman Yumnar ne ta iya tare hannun KHausar tana kallonta ta ce" Me zaki yi mata kuma?"
KHausar ta dubi mahaifiyar Yumnah, sosai take gannin tashin hankali da abubuwa a fuskar matar, a sanyaye da kula sosai ta ce" Mama, ta karu ne, zan dinke mata ne"
Maman Yumnah ta mayar da rufar ta rufe jikin Yumnar ta ce" Ba sai kin yi ba wannanma an gode"
KHausar ta zuba mata ido, sai kuma ta juya bata ce komai ba ta mayar da kayan aikinta ta mike ta dauka ta nufi hanyar ficewa
HAJIA dake zaune ta yi kwafa tana gyada kai ta juya da nufin bin KHausar din, sai ta ji kuryar Akilah a sanyaye ta nufota tana kallonta ta shiga miko mata jaririyar dake cikin zani sai ihu take yi ta ce" HAJIA, baki amshi y'ar taki ba, HAJIA baki yiwa yar magidancinki Adu'a da Barka da zuwa duniya ba fa?"
HAJIA ta lumshe idannuwanta, du yadda ta so kar a ga kwalarta sai da aka gani, murya a sanyaye sosai tana kallon y'ar da ta ci buri da Adu'ar Allah ya nuna mata ta zo ko ya zo duniya, sai gata ta zo din ama a cikin wannan yanayi, ga dai mafarkinta da adu'arta kan Allah ya nuna mata jinninsa, ya haihun a cikin wannan yannayi
Murmushi ta yi tana share kwalar ta dubi Akilah dake hawaye a bayyane ta ce" Allah ya maki albarka jikata, ya kuma shiryi yar uwarki da mahaifiyarta, kin ga Akilah bana gaba da kowa Ni, ama yarinyar da bata ga darajar khadija ba, ai ba zata ga tawa ni Dije kakar TAUFEEK ba, Ni kuma kin ga ba tsohuwar da za'a wulakanta bace, koda yarona da jikana basu san zafina na zan gudu na adana kaina ne a wani waje, sai gashi sunna so na, ina son yarinyar nan kamar raina, ama ba zan tabata ba sai mahaifinta ya taba ta, ki kaima su nawarar su rike mata su mata soyyayar mu gani idan har ta Allah ce zata jima!"
Daga haka HAJIA ta yi tafiyarta, ta bar Akilah kamar zata kifa, domin abin nan ita fa yana daga mata hankali fiye da tunani, shin yaya za'a yi ace haihuwar da ake yiwa rububi sunna ji sunna gani sunna neman dakilewa?
"Akilah, ki kirawo direba mu kaita asibiti, kin ji ta karu ai" Mamansu ta fada muryarta a sanyaye sosai, ta kasa tsayar da tunaninta matsaya daya, wai da gaske yarinyar da suka gama tsara sai dai ta ga Yumnah da yarta ce ta amshi haihuwarta?, Me mahaifiyarsa take nufi tana kallo sarakuwar a halin nakuda ama sai kace ba musulma ba ta kada kai ta tafiyarta? Maganar TAUFEEK kuwa ita ta fi komai tsaye mata a kirji
"Mama, yace idan aka fita da Ni a bakin aurena....." Yumnah ta fada muryarta a sanyaye tamkar wace take daf da summa, domin kana ganninta zaka fahimci bayan tashin hankalin rikici da firgicin haihuwa harda na furucin mijinta ke neman tabbata, du irin zumudi irin na uwa da son ganin abinda ta haifa ita kunnayenta na jiyo mata kukan yar da bata kashewa kowa ba bata birnewa kowa ba ta kasa amsarta ko ta dubeta, ji take yi kamar tana daf da barin duniyar baki daya
Bata taba tunani cewa wannan lamari zai juye mata haka ba, yau gata zaune kishiyar da take tunanin ko fatar Mamanta ba zata taba gani ba koda ta haihu ce ta amshi haihuwarta, karshe mijinta da take hangen wannan rana da tunanin irin farin cikin da zai yi na murnar gannin abinda ke cikinta ya juya ya fita bayan ya ji kukan shigowar abinda ta haifa duniya bai ko kali jaririyar ba ya yi tafiyarsa ? Innalilahi Wa inna ilaihi raj'une
"Yumnah, ki yi hakuri idan bamu je aka dinke ki ba wajen nan tsami zai yi sai kin wahala sosai koda awa daya ya dauka, an fi so da zafi zafin abin haihuwar nan a dinke , mu tafi" mahaifiyarta da ta kamata sosai ta rungumeta take takawa da ita a hankali
Murya na rawa Yumnah ta ce" Mama, TAUFEEK, TAUFEEK bai kalli babynsa ba, bai kalleta ba, Mama ban taba tunanin zai iya yin fushi irin wannan ba, Mama babu inda zan je koda kuwa rubewa zan yi, tunda ya fadi haka ba zan taka kofa ba, idan na mutu ai Shikenan, ko me na masa ai sai ya sasauta min haihuwa fa Mama wayo Allahna " ta karashe tana sake fashewa da wani kukan mai tsananin gaske
Akilah dake gaba da babyn nan ta dan dakata har suka tardota suka karasa bangaren na Yumnah sai aukin sannu suke yi mata, hankali tashe mahaifiyarta ta zauna tana cusa hannayenta bibiyu a cikin hijab dinta tana murza goshinta da gashinta tana ji kanta kamar zai buga da ciwo dan tashin hankali kaffafuwanta kuwa ji take yi du mujirya ke jansu kamar ba nasa ba
Ya Allah, wannan wace irin masifa ce, shin du tsanar ce ta haifar da haka tsakanin yarta da mijinta ko menene? Me aka yi da zafi da zai yi haka?
Akilah na shiga ruwa ta tara mai zafi sosai yadda zata iya saka babyn ta zauna ta wanketa sal , yarinyar sai tsala ihu take ta fito ta kimtsata sannan ta jona wani ruwan mai yawan gaske ta tara shi sosai yana ta tururi ta fito ta samu Yumnah kwonce saman shinfidar da Mamanta ta mata har yanzu ta ki ta cire zanin da ya yi kaca kaca da jinni , fuska daure ta ce" Tashi mu je na maki wanka"
Yumnah ta dago tana kallonta , da kyar ta budi baki a raunane ta ce" Aunty, ba zan iya wankan nan ba, dan Allah ki ba TAUFEEK hakuri"
Akilah ta daure fuska tana kallonta sosai ta ce" Idan kin kula da jikinki zaki bashi hakurin da kanki, in har ya ga zai iya yafe maki ki ci gaba da raina masa uwa tashi daya zai yafe, kin san ke kika san ciwon taki mahaifiyar shi bai sani ba!"
Da mamaki Mamansu dake jijiga babyn take duban Akilah, dan kuwa da wahala ka ga Akilah da magana da dacima bale har haka
Ita dinma murya a sanyayen ta ce" yaya zaki ce haka? Wani ya raina masa uwa ne?, haba Akilah hankali zaki daga min bayan kina gannin abinda yake faruwa?"
Akilah ta sauke ajiyar zuciya ta kama Yumnah suka nufi bayin
Ba sasautawa ta yi mata wankan nan sannan ta tara ruwan masu dumi sosai ta danata ciki, ita kuma ta ringa ihu dan kamar zanta zai fita take ji, sosai wajen ya fara yin tsami sosai da sosai
Sai da ta riketa suka fito daga dakin suka samu Mamansu na waya da babansu tana sanar masa ai a gidama ta haihu abinda ya sa bai gansu sun dawo ba bata jin dadi ne zasu shigo komai dare in sha Allah
Bude wajen da ta tanadi su audugar mata da pant ta yi ta ciro mata komai sannan ta miko mata ta koma ta zauna nesa da su kadan tana kallon mahaifiyarta ta ce" Yaya za'a ce ba'a wulakanta mahaifiyarsa ba bayan abin a bayyane yake ba a boye ba?, na sha fada mata cewar idan ta yarda TAUFEEK ya kula da wani lamari na rashin da'a da take wanzarwa tsakaninta da mahaifiyarsa baki daya darajar da take tunanin tana da ita a duniyarsa tana iya nema ta rasa, uwa wasa ce?, ta san ciwon nata mahaifiyar ama ta kasa girmama ta mijinta? Ban taba gannin banzan tunani irin naki ba Yumnah, ban taba haduwa da mai taurin kai irinki ba, shigowata kasar nan uku bayan aurenki saboda ke, ama a banza, to zan fada maki magana daya tak, duk wani wanda zai so ki kashe aurenki ki fito ba masoyinki bane, mahaifiyarmu ba zata taba fita daga bayanmu ba, haka Allah ya haliceta idan me muka zo mata da shi tana bayanmu ne, da yawa zasu yi anfani da wannan damar su wulakantaki idan har baki san ciwon kanki ba, wace soyayya ce abokiyar ZAMANTA zata maki wace ta zarce Tata? Kina kallo basa son mijinki wace ke da zasu so ki? Na so ace kin yi wayo kin koma gefe kin kalli fadan da bai shafe ki ba wanda kika tarar ana yi a ahalin mijinki, tsakaninsu, na yi iya yina dan ki gane, ama kika kiya kika rintse ido kike daukan hudubar banza kina yabawa kanki dan a rabaki da kishiya!, su su raba kansu da ita mana? Kin kasa ganewa kansu suke nemawa mafita ta kowace fuska, ga dai haihuwar da ta dace ace zuwa yanzu kina nan tamkar sarauniya an zagayeki yan uwa da aminan arziki ana nan nan da ke, ama cikin ikon Allah halayanki sun saka sai kunshe y'a muke daga mu sai mu kamar y'ar gaba da fatiha!, a yanzu bani da abin ce maki, idan kin yi niya ki nemi mafita tun kafin jikinki ya lalace, dan nama kike kayan banza yanzu zaki rube ki fara wari a Gaza haษawa a dinke a yi biyu babu, babu kyan wannan waje ai kin san TAUFEEK ba zai zauna da ke ba koda kece autar matan duniya!" Tana gama fada da wani bacin ran ta je ta karbi babyn ta wuce ta dauki zamzam da dabino ta wuce ta sauka falon kasa da ita tana jijigata tana tauna mata dabinon da niyar ciyar da ita da shi da kuma ruwan zamzam ranta a mugun bacen da ta jima bata shiga irin halin damuwa saboda bacin rai irin haka ba
Kwarai mahaifiyarta ta fi jin Yaren Akilah fiyema da ita, a tsaye take tana rarabawa kanta tunani da neman mafita a zuciyyarta, ga kuma mijinta ya ce da ita duk mutanen gidan nan basu isa duba mata y'a ba sai itace zata zauna? Ta koyi kara mana ta juyo gida ta barta koda da Akilah ne
Neman rasa madafa ya sakata fitowa bayan ta saka hijab dinta ta shiga neman Mai kwanoni a cikin gidansa
Da kyar ta ganshi bayan an mata iso ta duka tana sake sanar masa halin da ake ciki
Sosai ya ji zuciyarsa na neman shiga wani hali, subahanallah ta sauka? Ama babu wanda ya zo ya sanar masa? Bai jima da shigowa daga wajen datawan Anguwar ba sun je neman auren jikar malam, jin shiru ya zaci ana cen ana gumurzu, bale da bai ga TAUFEEK ba ya zaci yana ciki ana taimaka mata dan ta sauka,
Wayarsa ya dauka ya shiga kiran numbar TAUFEEK din
Kira na farko ya daga yana yin salama
Murya a hade Baba ya ce" kana ina?"
TAUFEEK ya kalli HAJIA dake jan carbi tana gyangyadi, tunda KHausar ta ishe shi da kukan sai ya je ya duba Yumnah ya baro bangaren nata ya dawo wajen HAJIA wace ta masa damu da ฦanฦara tace ya sha ya KWONTA ya kuma cire damuwar kowace Shegiya babu wace zata dagawa jikanta hankali shi kuma ya yi kwoncen burinsa ya je ya dauketa ya kaita a masa hoton cikinta, ama ya san ba zata yarda ba, hasalima ya ga ta nufi wajen Mama ya tabbata tana cen sunna kwasa
A tausashe ya ce" Aba ina wajen HAJIA"
HAJIA ta yi firgigit ta farka daga barcin ta miko hannu tana fadin" Bani shi nan, Allah na tuba masifa muna sume ma yi muke, mai kwanoni kana ji na? Wace tsiyar kake so da jikana ne Ni? Ka fa kiyayeni an jima da shiga duniyar yancin kai tsaf nake kai karar ka a mana tsakani, yau ga neman magana , yaro sai motsewa yake saboda kun tsane shi? To Ni ina so kuma ba zan amince a lalata min kwonciyar hankalin jika na, ka fadi maganarka wa Ni in ji daidai nake da kai"
Tunda ta fara fadan Baba ya sada kansa tamkar yana gabanta, a tausashe sosai ya ce" Ki yi hakuri HAJIA, ki yi hakuri dan Allah, Allah ya huci zuciyarki, babu wanda zai masa komai, dama so nake yi mu hadu da shi a cen bangaren iyalin nasa da KHausar da kuma mamansa dan a sasanta wannan rigimar domin ban ga anfaninta ba sam"
HAJIA ta tabe baki ya ja tsaki ta ce" Dama du Kai ka bada kofa aka raina mana wayo, ka ringa kwasarmu kana kai mu gabanta kamar uwarmu ana ja mana kunnen mu ringa yi mata biyayya, 5
To kai dan huwa rahamanu yau karya kake yi, ka daukota ku zo nan da kai da kowama idan mun gusa daga nan Ni da Magidanci ba dije ba Sarkin mahalba ya saka min da ya haifeni, kuma ita khadijar yau in ta je CEN din da Ni kake magana dan Allah Habu ka saka khadija ta je bangaren yarinyar nan Allah kuwa sai na saka ka a tashin hankali, aikin banza aikin wofi ku wani sako ya da danta a gaba, kaniyar du shegen da ya fasa daga ita uwar Tata , da uban n......"
Kitttt ya datse yana sada kai sosai domin Muryar HAJIA a bayyane yake ba a boye ba, ana jin amonta sosai fa, sai ya ji kunyar zagin da sirikan nasa suka sha , dan sarai maman Yumnah ta ji
Ita din kanta ji ta yi ta fara shayin zaman nan, ama kuma da wata masifar gwara wata, da ace harda mijinta a zaman
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 45 Chapter of 47