Share this page
kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuΙ“i wannan number 97 82 44 94 *SECRET DE LA FEMME DU MANGA* Gidan Kamshi, Sirrin Manyan MataπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒ Hankali tashe ta yaye labulen dake kare mai saka kaya ta fito tana fadin" A'isha wannan rigar fa? Ji fa yadda ta min daga nan?" Ta fadi nan din tana nuna wajen cinyoyinta irin yadda rigar ta dameta ta fitar da yannayin kirar jikinta Ido da baki da hanci Usaina ta saki tana mamakin Kausar, kai subahanalah, da haka yannayin jikinta yake take fama da zumbulelen hijab kamar zata kifa? Haka yannayinta yake yanzunma ta zo da wata riga ne bubu zumbuleliya wace bata kama ko'ina na jikinta ba sai yawo take a ciki ashe ashe abinda ke kasa kennan? Su sunna yiwa Aisha kallon masha Allah mai manyan mazauna ashe ga wace tace kau bani waje, eh lalle Kausar tanada tumbi wanda da ace bayanta ba pankameme bane haka da tsaf zai iya zamewa matsala a kwaliyarta, sai dai yanzun haka kadan ne ake ganninsa sakamakon yannayin halitar da Allah ya yi mata, sosai suka taimaka suka rufe mata yannayin tumbinta saima su da suke bugon idannuwa Nan fa aka shiga rikici, domin firr ta ja ta tsaya kan ba zata saka rigar nan ba, sai dai bata sani ba tsiya ce kannen nata suka shirya mata domin kaf kayan lesh din shine dama dama wanda ya dan rufe mata sutura Tamkar zata yi kuka haka take sake maimaicin ba inda zata iya fita a haka, ba zata iya ba Gannin rikicin na gaske ne Usaina ta je ta dauko wata alkyabarta baka mai shara shara, shara shara ne da ita sosai alkyabar dan yan mata ke yawan sakata sai yan gayun matan aure , itama irin shigarta kennan , Alkhyabar ba wani abu da take boyewa sai dai ta dan kare dai , sunna ne domin gwarama mayafi da ita , nan ta dawo tana budewa ta ce" Aunty, kin ga wannan alkyabar sabuwa ce sau daya tak na sakata in har zaki iya sakawa mu gama daurin ki saka ki ga zata rufe fa" Kausar dake zaune ta harde hannu ta gama kutuntumawa Aisha da rukaya ashar sai huci take kan bafa zasu fitar da ita tsirara ba jiki a sanyaye ta ce" Usaina ni da a je a daukon sabon hijabina na sallah da muka yi sai na rufa, yaya zna rabaki da kayanki kumaa bayan wannan nauyi da muka dora maki?" Usainar ta ce" Lah, aunty walahi ba wani maganar nauyi, kuma ba maganar aro tsakaninmu, kin ganta in dai zaki saka din ni zan ji dadi, yanzu yaushe aka koma aka dauko maki hijab aka dawo inace yanzu Mama ta gama fadan baku karaso ba?" Shiru ta yi, du nauyi ya damu zuciyarta, haka aka daura mata daurin da ya idasa fitar da sirrin kwaliyar sannan ta saka alkyabar wace ita da kanta sai ta tsaya gaban madubin a hankali tana shafa yan kannanun walwalin gaban alkyabar farare karkar ba masu yawa ba tana gannin yadda alkyabar ta hau yannayin dinkin har kasa da irin yadda kwaliyar ta hau kalar fatarta tamkar ba ita ba A hankali ta daga idannuwanta ta kalli kannenta da suka sakata a tsakiya sunna kallon madubin su dukansu Wani ni'imtacen murmushi ne ya kwace mata a fuskarta a hankali ta ce" tabarikalah masha Allah" Aisha ta saki murmushin itama a hankali ta ce" Tsarki ya tabaka ga ubangijin da ya halici samai da kasai da dukan halitun ciki, Aunty kwaliya tana maki kyau sosai haka dama?" Rukaya ta yi murmushi itama a hankali ta ce" Tamkar ba aunty ba, kalli yadda ta yi? Inama Elhaji ya ga kwaliyar nan na tabata yau zai ce a daura aurenku" Da yar dariya ta mintsini hannun Rukaya sannan suka juyo Usaina ta ringa kashe masu hotunna sunna faman fadin ta ajiye masu zasu zo su amsa a wanke a fitar masu tunda babu mai babar waya a cikinsu Sai bayan sha biyu na rana suka fito daga gidan kwaliyar suka shiga adaidaita wace Rukaya da kyar ta samu waje dan wajen matse masu yake sai sun jijirga suk dauki hanyar gidan su TAUFEEK da akwatinsu Sunna karasawa suka tarar gidan dinke da al'uma, babu kalar da babu tun daga tsofafi har zuwa yara kannana, kai yan matan dake gidan tamkar gida mai yan mata bayan yan matan gidan basu wani girma ba, yan matan cikin gidan ne dangi ne da ango dinsu na safe, sai dai ba irin lesh din su KAUSAR ba domin wannan su Mama ne suka yi shi iri guda sai makusantanta da ta ba ita da kanta, lesh ne mai daraja da tsadar gaske hakan ya sa har suka karasa bangaren Maman akan bisu da kallo ne ga tsararen kwaliyarsu ga lesh din jikinsu sai a yi tunanin wasu makusanta ne wa Hajia watau mahaifiyar TAUFEEK din yinin biki kawai ake yi ba ji ba gani, biki irin na manya masu hannu da shunni Kokarin dukawa take yi dan gaisar da Mama da ta nufota tana murmushi hakoran makarta biyu na walwali ta saka hannayenta ta tareta tana fadin" Oyoyo yarinyata, koda yake fada ya dace na rufe ki da shi, ama ba yanzu ba sai mun salami baki zan maki tass a gidan nan, zo maza ga abincin TAUFEEK dauki yana bangaren Hajia dan Allah kai masa ki dawo ku je da yan uwanki bangaren cen na amarya ku kai na baki ance zasu iso su yi gyaran dakinta dan yau za'a kawota" Baban faranti mai dauke da kula biyu masu marfin kwalba rantsarsu ne Mama ta saka aka miko mata, a dan gagauce Maman ke bayanin dan yannayin taron kuma dama zata fita ne ta samu wanda ta yarda da shi ya kaiwa TAUFEEK abincin sai ga KAUSAR din, hakan ya sa ta juya da abincin su kuwa su A'isha suka bi bayan Maman domin ta ja su ne tana fadin" Ku zo ku kuwa yayana kafin ta dawo a shirya na bakin, ga mamanku cen a dakina da baki idan mun gama kwa gaisa" A nutse take nufar hanyar bangaren Hajiar har ta karasa ta saka kafarta a hankali ta bude tana ta Adu'ar Allah ya kaita lafia domin takalmin kansa da take kai da kyar take rike kanta a sama, ga alkyaba ga kuma kwaliyar da take jin kunya kamar me wace tana ji a jikinta da wahala ta iya wuni da wannan hodar a fuskarta da sauransu A hankali ta saka kanta falon tana yin salama Jin salama ya saka Hajia dakatawa wace ke shirin shiga kicin sai fada take yi tana yadda hannun anma rainata a kan me za'a bar mata jika da yinwa har sha biyu? Lalle zata iya sabawa uwar Ι—an nan, shine fa zata shiga ta ga abinda zata sama masa koda danwake ne kafin a jima a bashi tuwo sai ta ji salama Da farko furkar ta zubawa ido, sai kuma ta shiga binta tun daga kanta har zuwa inda ya fi tsole mata ido da sakata zarro ido kamar zasu fado kasa Da sauri ta yi ribasss ta juyo ta karasa shigowa ta zo inda TAUFEEK kw zaune da Alhhusain sunna dan zantawa ta zauna daf da shi hadi da riko hannunsa na hagu ta jimko da bakinta ta shiga nuna masa abinda take ganni yau ra'ayne da ayne Alhhusain ne ya amsa salamar a bayane sosai yana juyowa, sai kuma shima ya dan zarro ido kadan dan har ga Allah da farko bai gane fuskar ba da yannayin har sai da ta saki murmushi tana idasa shigowa gaba dayanta ta nufo falon bayan ta cire takalman ta ce" Ka ga abokin ango, menene nake gannin ka yi wani laushi ko yinwar ne kaima?" Hajia ta saki hannun TAUFEEK da ya irin cire kan nan ya ki kula KAUSAR ko kallonta bai yi ba shi kam wai fushi yake yi sai yanzu zata zo aurensa dan wulakanci, ta tafa hannayenta tana tare gefen kuncinta ta hade da dan kunnen zinarin dake kunnenta ta ce" Na ga annabi in na yi hali na gari, yar nan Ke ce? Dama haka kike ama kike lumbukewa a hijabi bakya ko shafa fankeke? Lah ha ila ha ilalahu muhamadu rasululahi sallalahu alaihi Wa salam ku duba ku ga halitar ALLAH a yanke masha Allah kamar kamar lah kamar mema zan ce ke ama kina kokari haka kike tafia ras irin nawa.......?" KAUSAR wani irin tsuru tsuru ta yi tana kallon Hajia, TAUFEEK ya zubawa hajia ido kafin ya juyo da dubansa dan gannin meye wai ya saka hajia magana haka?, Alhhusain kuwa sai ya mike ya amshi farantin dan yadda ta yi sai ya so bashi dariya ta yi tsuru tsuru kar ta saki abincinsu , shi da kansa mamaki ya kasa barinsa haka kuma idannuwansa sunna matukar son kare mata kallo duda ya san hakan kamar ai ba daidai bane kau? Ido ya zuba mata, fuskarta ita ta fi bashi mamaki, kwaliyar dake zane a saman fuskar nata ta fi bashi mamaki, sai dai bai san cewa abin mamakin a gaba ba sai da ya dan so gannin meye yankawar da Hajia ke fada ya dan kalli yannayin shigar jikinta a dan gurguje ba da nufin komai ba sai dan ya ga wani hijab ne ta saka wai HAJIA ke wannan surutun sai ya ga wani ikon Allahn da ya so sakashi kyatsa rantsuwar sam bamaa ita bace ta hanyar dauke kansa da sauri ya juyo barin hajia , sai dai yanna kallon Hajiar ya ga ta tsatsareshi da ido da duba wani kala daban irin marar kyau din nan kuma da ido tana aniyar neman yin tsegumi da shi bayan cin naman wani haramun ne dan haka ya kauce idannuwansa ya hade fuska sannan ya mike tsaye daga zaunen da yake ya daga kafarsa zai karasa sai ya ji hannunsa rike taf a na hajia, Dubanta ya yi sannan ya kalli hannun nasa ya ce" Sakeni mana" Sai a lokacin Hajia ta saki hannun tana sakin harare ta ringa lekawa ta ga ya karasa inda KAUSAR ke tsaye ya mata nuni da ta wuce ciki, sumui sumui ta yi cikin ta tsaya shi kuwa ya karasa ya tsaya gabanta da sauri yana hade fuska ya bude baki zai yi magana ya ga HAJIA ta masu tsuru tsuru sai zarro ido take yi hakan ya sa ya sake jin wani takaici ya lulube shi ya ce" Hajia meye wai?" Hajia ta tabe baki ta ce " Meye kuwa, miya ce, me zaka fada mata ne?" Ikon Allah....., Ya ayyana a zuciyarsa ya zamto sunna kallon kallo su ukun Yannayinta da sanyi ta ce" Ka yi hakuri besty gidan kwaliya muka tsaya shi yasa fa bamu karaso da wuri ba, ka tambayima su Aisha " Da bacin rai ya ce" Haka fa, gama katt na gani, yanzu meye anfanin haka KAUSAR? Kefa ba wata yarinya bace da zaki biyewa yara ki je ki yi wannan abin ki biyo titi, yanzu ko kunya bakya ji???" "Yo kunyar uban wa kake so ta ji ? Yau ga jaraba auren wani shegen ke kanta da za'a hannata yafe ta zaga gari? Da yafen nan take na rantse da huwa rahamanu Ι—an nan na tabata da yanzu y'ar nan ta yada na biyar ko na shida ta dauki wani cikin dan bana tunanin akoy shahashan da zai iya hakura da y'ar nan,kuma nice nan makaryaciyarka zaka ga yadda zata yi kasuwa, dama abinda ke hijabin nan kennan???" Hajia ta fada, hankali kwonce har tana dafe haba Gaba daya wata irin kunya ce ta nemi halaka KAUSAR A tsayen da take sai ta duke tana rufe fuskarta a cinyoyinta ta furta" innalilahi HAJIA, na shiga uku aa fa" TAUFEEK dake tsaye ya rasa wanene ya dace ya yiwa wa'azin jin tsoron Allah a tsakanin Hajia da ita wannan yarinyar da ta tashi tana rufarta a kamilance ta wani saki jiki kamar ba KAUSAR ba? Kai wannan abu ya bakanta masa rai menene wannan shashancin? Rai bace ya juya, har ya nufi falon ya dawo ya nunota da yatsa ya ce" kin ga daga falon nan in kafarki ta fita waje sai na saba maki KAUSAR, ba zan kyaleki da mutuncinki ki ringa yawo haka ba, shirme kawai kin iya sakani gaba ki wankeni in na dan yi wani abin kamar wata ta Allah kece ke yawo haka, an ji kunya!" Ya idasa fada ya yi gaba Hajia dake rike da haba al'ajabi na neman sakata marmaren yan maye na iya shegen Elhaji karami ta duko ta gyara daurinta ta nuno KAUSAR da yatsa ta ce" ki ji ni da kyau , ni nan nice uwar uban elhaji karami, kin ga kuwa na ga duniya gannin idona, nice zan fada maki mai fisheki, in bamu maki aure ba kwadaki zamu yi mu cinye ne? Kin ga kwaliyarki ba rashin kunya ko rashin kamun kai a ciki, Allah na tuba yo alherin nan ai ba kowa ke samu ba, tashi maza kada su baza su ki shige jama'a babu abinda za'a yi, in banda bakin hali irin na Elhaji karami in aka hannaki kwaliyar kika rasa mijin shi zai ji dadi ne! Ana abu ba tsoron Allah sam? Tashi maza wataya bikin amini kike shagali maki gani ya mutu dan bantan uba !" To fa, Hajia kin kuwa zo da tsoron Allah anya?😁😁😁😁😁😁 Hajiar shagali πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”β€β€πŸ©Ήβ€β€πŸ©ΉπŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’” *DA CIWO A ZUCIYATA* πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”β€β€πŸ©Ήβ€β€πŸ©ΉπŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’” _MALLAKIN_ *SAJIDA NIJAR* *FREE BOOK NE* 1️⃣3️⃣ LITATAFAN MARUBUCIYAR Duk karyar kada Yar mahaukaciya Neman na kaina Bani da zabi Bak'a ce Kutkale Makauniya ce Mage Duk nisan jifa Idan ka raina inda kake Dutse Alkalamin kadarata Bani da zabi Dakika Biyar Now *Da CIWO A ZUCIYATA* *Tallah, tallah, tallah* *SECRET DE LA FEMME DU MANGA* _Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_ Farar Humura Bakar Humura Humura special, humura de bain Humura epicΓ© Lait de nuit Parfums dΓ©sodorisant Parfums rideau et dras Lait de nuit Alkam Kulakcam *WaΙ—annan kadan ne daga bangaren turaran ruwa* Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes *Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:* mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwaraiπŸ’ƒπŸ’ƒ Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuΙ“i wannan number 97 82 44 94 *SECRET DE LA FEMME DU MANGA* Gidan Kamshi, Sirrin Manyan MataπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒ Dawowarsa da hijab din hajia na sallah rike a hannunsa ya saka hajiar yin shiru da bakinta daga hudubar da take yiwa KAUSAR ta zuba ido tana kallonsa Fuska a daure ya ajiye mata hijab din gefenta, murya cen ciki ya ce" I'm hungry,,,," Daga haka ya juya ya koma wajen zamansa fuskar nan tasa zaka rantse wani mugun abu akai masa Kausar ta saka hijab din bayan ta dubi yannayin hajia , a hankali ta zame dan kwalin dake ciki ta cire sannan ta iya mikewa tana jin wani nauyi na kwaliyar a ranta ta sake dakatawa tana dyban HAJIA Hajia ta hade hannayenta wajen kirjinta kasa kasa ta ce" Je zuba masa abincin sai mu dinke a daka na gama baki shawara, kin san dama shi magidanci tuwonma sai an zuba masa, matarsa dai zata ga iya shege, jibi keya uwa mun aikata sabo irin yadda yake harararmu, je zuba masa sai mu gama maganar " Ajiyar zuciya ta sake saukewa a hankali ta karasa inda suke zaune, Salisu na magana, Adamu na dariya yana duba abinda yake nuna masa, shi kuwa TAUFEEK din yana zaune ne yana kallon shima abinda suke yiwa dariyar wanda sam shi bai ga wani abin dariya a nan ba, wasu yan mata ne a tiktok ke tikr rawa tamkar zasu karya kaffafuwa sai kace wasu jakai, shine suka ga abin birgewa a nan Plate ta karo a kicin din HAJIA ta zo cikin nutsuwa ta zauna ta bude abincin ta shiga zubawa a zuciyarta tana ta tunanin abinda ta masa da yake jin haushinta, bata san ta inda zata kamo ba, batama san takamaiman laifinta ba, ta yiwu dan ta fito ba hijab ne, bai san itama fin karfinta su Aisha suka yi ba, da bata fito din a haka ba, lalle tana tausayawa YUMNAH, koda yake ta yiwu kuma in dai mai saukin kai da jin magana ce ba zata wahala a wajen mijin nata mai tsatsauran ra'ayi ba A hankali ta dago dubanta dan tana ji yadda abokanansa ke fira da raha,ama shi ya wani kyale su sunna ta zuba su kadai bayan gayar nan idan tana tune tasa ce Da idannuwanta ta bi inda ya zubawa ido, wato hannayenta dake rike da cokali mai dan girma tana zuba abincin, Wa'inda suke dauke da jan kunshi irin na yan mata da aka yi kata itama ta cancana abinta A hankali ta sake zuba idannuwanta a saman fuskarsa, hakan ya sa suka yi ido hudu da shi Bata saba dan sun yi ido hudu da TAUFEEK, TAUFEEK din abokinta ta fauke dubanta ba, ko yanzu da suke kallon ido cikin ido sai bata janye nata ba bale shi da take fadin kulun bashi da kunyar kallon idon mutun ya janye A saman labanta ta iya budawa kadan, kasa kasa sosai ta ce" Me yake damunka ne?, Fushin me kake yi? Wate ya bata maka rai?" Har ta ajiye maganarta yana kallon yannayin da ta yin, bai bata amsa ba ya janye dubansa a kanta ya maida wajen abokansa dake tataunawa sunna ta sako shi a ciki daga shi har ita Tana gama zubawa ta so zama, sai dai da ido TAUFEEK ya mata alamun ta tafi, hakan ya saka ta shaka, shaka irin ta jin haushi harma ta gaza hakura ta sauke masa duba mai shige da harara kasa kasa sai dai a kausashe ta ce" Malan in nice baka son gani a taron naka na yi tafiyata mana? Me na maka tunda na zo kake bina da kallo irin na tsana?, In wani ya taba ka ka huce a kansa mana sai mu dake tare da kai kuma a rana baba irin wannan? Karma ka kula nin TAUFEEK sai me?" Tana gama fada ta yi gaba da tafia irin ta sauro mai bayanar da irin tata baiwar wace ba kowa keda ita ba ama kuma idon kowa na iya ganni Wani takaicin ya sake shaka har ya saka hannunsa ya talabe habarsa dan takaici da rashin madafa Abincin sama sama ya iya cinsa dan ya riga ya gama fice masa a rai da abubuwan dake faruwa da shi a yau din Sai da suka gama suka fice da abokansa wajen da taron ya fi yawa yana ji kamar kansa zai buga dan ciwo, domin hayaniyar tana nema ne ta fi karfin kwakwaluwarsa Kusan karfe hudu na yama a dole ya mike ya shiga cikin gidansu dan irin hayaniyar dake ta tashi sama sama Ikon Allah ta tsaya yake kallo a lokacin da ya ga iyalan mai kwanoni sunna raba hali tamkar an aiko su, fada ne ko mema zai kirayi abin? Shi dai ya ga abin tamkar ba na masu hankali ba kuma kunnayensa na nema su sanar masa wace ake son takalowa Idannuwansa ne suka sauka a kan Maman su KHAUSAR dake tsaye da waren takalmi a hannunta , takalmin da ya san mamalakinsa , watau mahaifiyarsa Wanzuwarsa a wajen ya saka yawanci kame bakinsu suka yi shiru, domin TAUFEEK bako yake a inda yake so a ganshi bako, sanane shi a hali na dabanci da jagaliya idan halin hakan ya kama, TAUFEEK mutun ne mai hali kala uku a rayuwa, a gaban tsagera shi din baban tsagera ne, a gaban iyayensa yana da ladabi da biyaya da kishinsu, sai mace daya tak dake taka shi ta masa rashin kunya son ranta, ita kuwa baya fatan a wayi gari ta ga kalarsa da yan gari suka sani, ya fi so ya ci gaba da kasancewa mutun mai matukar laushi, sanyi, rashin sannin ciwon kai a gabanta, dan tana da daraja da mahinmancin da baya so idan ta gane waye shi ta tsorata da shi, Hular dake kansa ya cire a hankali yana sake bin yayar hajia da wani kallo mai kama da daf yake da budar bakinsa ya yi mata barin mahaukaciya komai girmanta da tsufanta kuwa, domin abu daya ne ta taka take fada daga bakinta wanda a duniyar nan baya tunani wuta ko mashi zasu hanna shi farautar mai zaginta, watau mahaifiyarsa, shi fa komai girmanka ka girmama iyayensa to fa zaka more shi fiye da tunaninka, idn kuwa ka yarda, ka kuskure, wata motsarariyar giyarka ta saka ka take masa martabar masu martaba babu abinda zai hanna shi aikata aiki irin na yaren da basu da tarbiya ta hanya watsa hannayens aa fuskarka ya ce da kai UWAKA ko kuwa ya ja baya ya shige ka kowa ya mutu a huta Da sauri hajia ta kama hannun yar uwarta tana fadin" Wai menene kuka tsaya kunna kallon mutane ba zaku iya raba fada bane jama'a? Dan Allah kowa ya kama gabansa tunda abin hakane, yaya zaku taru kunna kallon abu na faruwa ama kowa ya ja ya hade hannunsa ya nade yana kallo? Wannan ai sam bai dace ba" Da mamaki yar uwar tata ta kalleta jin furucinta, kasancewarta ita ta izata sosai kan su zo a yita ta kare kuma sai ta ji magana irin haka? Zata yi magana ta ga kula da abinda bata kula da shi ba da farko, watau TAUFEEK tsaye ya jinginu da abin labule idannuwan nan nasa sun kade sun yi jajir tamkar wanda ke shirin hadiye dan mutun yana bin kowa da kallo Bata iya yin maganar ba sai hannunta da ta warce ta shiga haurawa cike da takaici Hajiya Fatahiya ta saki yar guda tana sake yafa gyalenta ta ce" Wai rashin kunyar karya, ki ci gaba mana mu gani buge ko zobe zai ci nasara" Hajia Nawarah da abin mayarwar ama ta yi shiru ta bari zata rama ne, saima kokarin korar mutanen da aka tara na arziki ta shiga yi tana fadin tunda hakane kowa ya watse ai an ci an sha sauran sa yi A hankali ya dago daga inda ya jinginar ya nufo inda HAJIA Nawarah ke tsaye Gaban Maman KHAUSAR kuwa sai da ya kwonci kwonci ya fadi, a dan firgice ta zuba masa ido tana tunanin abin yi, domin mahaifiyarsa ne ta sakata zuwa dan kar ta bari ya aikata wani abin a wajen nan in dai ya ji hayaniyar da ake yi Har ya kusa cin mata da sauri Mama ta yi raf da hannunsa na dama tana cicira ido , muryarta a raunane ta ce" Aya D'an nan ina zaka je ne haka?" Dakatawar da ya yi, niyarsa ya warci hannunsa da karfin da zai saka wanda ya rike masa watsuwa a kasa, sai dai muryar da ya ji ya saka shi sake ambaton Allah, sannan a hankali ya juyo yana dan kakaro murmushi ya ce" Mama, hajia ce zan cewa kar ta kori kowa, a ci gaba fa biki kawai" Kai Mama ta gyada da sauri ta ce" To to to, ai ina iya fada mata ka je kawai abinka zan sanar mata in sha Allah " Hannun nasa da ta rike ya sake kallo, a hankali ya sauke yar ajiyar zuciya sannan ya yi gaba bayan ta sakar masa hannun Yana tafia Maman ta sake sauke ajiyar zuciya tana ta Adu'a a ranta sannan ta samu ta shiga bada hakurin laifin da

Chapter 9 of 47