irin nata shiri da ta zo da shi, haΖoranta a fili kamar an mata albishir da gidan aljanna
A'isha ta ce" Aunty , me hadinki da wani cen shashasha kuma ana maki magana ta namiji har namiji Yayanmu a yau Adu'armu ta karbu burinmu ya cika?"
A harzuke , jin maganar rainin dai A'isha zata ci gaba da mata ta dafa ta mike lokaci daya zannin da ta daura saman doguwar rigar barcinta irin mai santsin nan har kasa wace ta kasa cenzawa tunda ta yi wanka sai zani kawai ta dora Mata a samanta ta zurma hijab take jiran zuwan TAUFEEK ko ya fita ya gano mata me ya samu Salis ya kwonce ta kuma ki bi ta kansa ta cire hijabin dan jin wani zafi ya fara ratsa mata jiki da fata ta bude yan yatsunta ta nufi fuskar A'isha zuciya daya muradi daya shine ta saukewa A'isha gigitacen marin da zai sa ta gane me take fada ko zata saita harshenta ta mata magana da Yaren da ta iya ba sakaran Yare ba, sai dai gannin haka da gudu Aishar ta yi bayan Hajia da ta shigo fuskar nan kamar gonar auduga tana salalami da fadin" Aunty dukana zaki yi?"
KHausar rai bace ta ce" Idan ban dauke ki da mari ba ki ce min shashasha, sa'arki ce Ni wai? Ni zaki rainawa wayo ne?"
HAJIA da ta ta yi dibi dibi sakamakon cakumeta da A'isha ta yi dan neman agaji ta yi raf da hannun A'isha ta ce" Ke tsaya ta mareke, in dai rainawa matar MAGIDANCI wayo zaki yi tsaf zan daureki mu zane banza, aikin banza ya zaki saka ta kunce zani tana tiitirniya ki tara mata gajiya? Ke dauko zanninki daura Ni ga galan din cen maza kafin nan zuwa dare shanye min shi tass, yanzun wancen gidan zan je in ga ubanda ya Hanna mattar mai kwanoni zuwa daurin auren MAGANIN gida magajin dukiya alwalin Gawa, dan daura kar a shigo a tsaya kallo wannan sababi hakka Masha Allah "
KHausar ta yi kasakai tana kallon HAJIA, bayanan hajiar na son rikitar da tunaninta fiye da na su Rukaya
A hankali Rukaya ta zagaya ta ja mayafinta ta nufi dakin mamansu a lokacin da Khausar ta matso daf da HAJIA ta ce" HAJIA, wai an daura auren ne? Da Salisss ko?"
HAJIA dake rike da hannun A'isha taf ta sakarwa KHausar harara da jin haushi ta ce" Uban wanene SALIHU kuma ke Khausara? Ki fa kiyayeni yaya ina baki kina roko?, Maganar Magidanci zaki hada da wani shashasha?, Ke amshi nan, nace amshi uwaki, to wa bilahilazi sai in zaneki tas bayan Mamuda ya rike min ke, to ke matar MAGIDANCI kike ba SALIHU ba!"
HAJIA bata san cewa ita ke dauke da kalaman fadi, KHausar ke dauke da abin aikatawa
A birkice KHausar ta zaro ido, lokaci daya jikinta ya dauki rawa
Ζasa ta silale daidai shigowar Mama dakin da salama a bakinta
KHausar na hada zufa kamar da wasa lokaci daya ta yi wani wiki wiki da ita ta dubi mama muryarta cen ciki ta ce" Mama, kin ji abinda HAJIA ke fada da Yaren nan kuwa? Yanzu fisabililahi wannan maganar a tsakani mutun da ita ce? Innalilahi ina Ni ina TAUFEEK zasu ringa min wani magana daban? TAUFEEK ai haramunane dan uwana ne fa"
HAJIA ta zarro ido lokaci daya ta rike baki ta ce" To fa, yau ga zamanin yan iska!"
"Mama ina Ni ina Besty? Aure? Aure dai aure? Shi auren nan dai aure? Haba Mama fisabililahi idan Salisss dinma ya fasa sai kawai a ba TAUFEEK? Na nawa nema taufeek din ina maganar aure Ni da shi? Aure mama aure? Innalilahi ai ba maganar soyayya bale zaman aure tsakanina da shi ko?"
HAJIA kam ta gaza rike salamamen rashin mutuncin nan ta gyara zaman sabon hijabinta ta riko hannun Mama dake tsaye itama baki bude tana kallon yadda KHausar ke bayani baki bude dan kuwa sai malolowa take yi kamar mai fama da zazafan ciwon ciki ta mirgina nan hannunta a mike tana bayani hawaye wani na korar wani ga kan nan ta kunce shi baima samu gyaran saloon din ba nunawa kawai take tana hawaye ta ce" Kin ga, bari in tare bakin cen dan ba'a rasa yan munafurcin da basa son tarayar nan ba, ita kuma wannan y'a ki san ta inda zaki biyo da ita dan wa bilahilazi a kan auren nan sai in batawa kowa, rainin hankali za'a min? Me take nufi da yaushe aka haifi Magidanci? Allah kawo ki dakinsa sai mu sake zaunawa, dama da wahala dan fari ka ganshi rass da wayo abinsa, ke dai Allah shirya kuma in bata shanye tsumin nan ba na dawo nice nan zan mata wankan rubutu in sauke mata aljannun kanta!"
Cabdijan, watau yar kukutar Aba fa so take ta kankaro mana rikici na kasa da kasa, baki san ainahin waye shi ba yarinya mu karki janyo mana, Meyema to in ba neman rigima ba, bakin cikin cinya sa zaki mana kau? Ta Allah ba taki ba wai SALIHU πππ
.ππππβ€βπ©Ήβ€βπ©Ήππππ
*DA CIWO A ZUCIYATA*
ππππβ€βπ©Ήβ€βπ©Ήππππ
_MALLAKIN_
*SAJIDA NIJAR*
*FREE BOOK NE* 4οΈβ£0οΈβ£
*GARABASA, GARABASA, PROMOTION, PROMOTION DIN LITATAFAN MARUBUCIYAR A KAN FARASHI MAI SAUKI 1K, YAN NIJAR KUWA 1000 FRANCS CEFA*
1: Duk karyar kada
2: Yar mahaukaciya
3: Neman na kaina
4: Bani da zabi
5: Bak'a ce
6: Kutkale
7: Makauniya ce
8: Mage
9: Duk nisan jifa
10: Idan ka raina inda kake
11: Dutse
12: Alkalamin kadarata
13: Bani da zabi
14: Dakika Biyar
15:Wata kokowar
16: Aure yakin mata
17: Ni zan ladabi
18: Daga tafia daukar soja
*Dukansu a kan farashi mai sauki, zaka saka dubu guda ne domin promotion ne nake yi, ka tuntubeni kan layina kamar haka +227 93 81 16 18, Sajida Nijar*
Now
*Da CIWO A ZUCIYATA*
*Tallah, tallah, tallah*
*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*
_Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_
Farar Humura
Bakar Humura
Humura special,
humura de bain
Humura epicΓ©
Lait de nuit
Parfums dΓ©sodorisant
Parfums rideau et dras
Lait de nuit
Alkam
Kulakcam
*WaΙannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa*
Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes
*Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:*
mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata
Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwaraiππ
Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuΙi wannan number 97 82 44 94
*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*
Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mataπππππ
HAJIA ke cikin fada, bata ankara ba Mama ta kaiwa bakin KHausar bugu tana hade girar sama da ta kasa
"Lah ha ila ha ilalahu Muhammadu rasululahi sallalahu alaihi wa Salam, ke me ta maki?" HAJIA ta fada tana tarewa dan Mama abin haushi ya bata yadda KHausar ko kara babu take abu kamar wace ta. Samu tabin hankali, yanzu ta budi baki ita KHausar ta ringa rufi irin wannan? Lalle dan Adam, nan KHausar ke fadin ko waye aka bata tana so, itama burinta ace an mata aure, shine dan wulakanci Allah ya amshi adu'arta yau din itama ta samu yanci irin na mata ama take wani abu kamar an ce an hadata aure da makiyinta?
HAJIA rai bace ta ce" Kul , banda duka, daga fadin nusar da ita da baki da wayo?"
Mama ta sada kanta tana ji ranta na Ιaci ta ce" HAJIA, KHausar fa wani sa'in zuma ce sai da wuta, in ba rashin hankali ba mu sa'anninta ne zata sakamu a gaba da kukan rashin godiyar Allah?, To ta kireshi shi marainin nata ta fada masa !" Daga haka Mama ta yi gaba ranta a bace
HAJIA ta sakarwa A'isha harara ta ce" to ai sai ki bita, ga dukkan alamu in aka bar maku ita tsaf zaku sa kumarinta ya rage, bita bi mamanki kar na rama a kanki"
A'isha ta yi murmushi ta juya ta fice, tana ji a ranta tunda take bata taba jin tsohuwar nan a rai ba irin na yau, lalle matar nan ALKHAIRI ce ita, kuma tana mata Adu'ar gamawa da duniya lafiya, wani gefe na cikin zuciyar Tata kuwa tarin mamakin yannayin auntyn nasu ya gama rike mata wuya, yanzu wace mace ce zata ki yayansu? Menene dalilinta na nuna kiyawarta a lamarin? Allah shi kyauta
"Kin ga, ki rufawa kanki asiri da koke koke, tunda kin ga auren nan dai an daura shi ba kuma za'a kwonce ba da izinin mai sama, kar dan zuwan da zan yi in dawo ta shigo ta dakeki a banza a wofi kin ji? Ba dai Magidancin bane bai maki ba? Ai shan koko bukatar rai ba sai kin daga hankali ba idan ya ji da shi aka daura auren ki rintse ido ki masa jan ido ki ce takardarki, da bakinki sa komai? Yanzu ki daina wani kuka dan bashi da anfani kin ji y'ar albarka?" HAJIA ta fada bayan ta rike hannun KHausar ta tausasa muryarta ainun
KHausar a hankali ta ce" HAJIA, Kennan shima bai san da wannan abin ba?"
HAJIA cikin hikima Tata ta amsata da" Eh, bai sani ba, hasalima iyayenku suka tsayar da hakan bisa rokon mahaifinsa "
KHausar cike da mamaki da wani firgicin ta ce" HAJIA aba na cen gidan ne ya nemi auren?"
HAJIA ya ce" Eh, shi da kansa mai kwanoni ba"
KHausar ta shiga gyada kai cike da kalar tausayi ta ce" Na san bai san inada saurayi ba, Ama HAJIA shima TAUFEEK din ai an cuta masa, auren dole ai akai masa shi dinma ko?"
HAJIA ta gyada kai ta ce" Wannan haka yake, Ni Bama abinda zai batan rai a zo ana fadin kuma daga aurenki an sake ki y'ar nan, ke dai yanzu ki share hawayen ki ki tausayawa kanki, komai dan a bi a hankali ne, duniyar nan akoy mai gudun bacin ranki irin Magidanci? Idan kuka zauna sai ku yanke abinda ya dace da ku ko?"
KHausar ta ringa jan hanci tana sauraron yar hayaniya bayan fitar Hajiya
Gaba daya abin yana nema ya girmami tunaninta
Ta rasa a inda zata ajiye wannan sabon abin
Abu daya ta sani shine ita da TAUFEEK *HARAMUN DIN JUNNA NE*!, idan ta tuna menene aure da tsarabe tsarabensa sai ta ji hankalinta na neman sake tashi , da sauri ta ringa kade tunanin tana jin tamkar wace ta tafka sabo tuna abinma a ranta, 'Hum, Allah ya kiyashemu abin kunyar nan ba da mu ba, bawan Allah in ya ji wannan aiki ta yiwu saima ya yi kukan takaici!' ta ayyana a zuciyyarta ta kuma dauri zaman daki ba tare da ta fito ko ta kimtsa gashin kanta ba, ita bata ga lokacin ba wani abu wai shi gashi ba a yanzun kam, ana ta Kai wa yake ta kafa?
Murmushi kawai HAJIA ke yi a ranta tana Ayana ' Tirkashi, ai Inaga Bama sai na wani boye masa ba, tunda har Allah ya yi yarinyarma ba zata amshi abin da dadin rai ba koda ta amsa din, ama ba Ni zan sanar maka ba zan bar mahaifinka ya sanar maka, abinda na sani daya ne tak a yanzu ka yi aure, a yanzu ka auri yar mutuncin da ta san darajar iyayenka, babu ruwana da kyan banza da farin fatar banza da iyayi na gayu, abinda na sani shine wannan yarinya itace daidai da kai, kuma bi izinillah itace haske a cikin hasken gidan Mai kwanoni!'
A baban gida shagali ake yi wanda ya daure kan daidaiku daga cikin ahalin gidan, domin babu abinda ya fi basu mamaki da daure masu kai irin yadda suka ga Mama na shige da fice cikin fara'a da farin cikin da suka gaza hade mahadar abin, to su basu ga hadi ba, inma zaman bikin karar kawar danta ta yi niyar yi ta je gidan su yarinyar su yi zaman mana? Ta yi zamanta a nan harda girki da samun baki? Lalle, wani shagalin sai a gidan mai kwanoni! Gefe guda kuwa ga Hajia tana nata itama shagalin, dan kuwa ita din tuya ake ta yi ta masa ana fitarwa sadaka sosai , dan hakan ta shirya wunin yau din dama, sai da yama ta yi sosai ta kimtsa ta nufi bangaren TAUFEEK, domin ta tambayi yan matasan dake zuwa wajensa inda yake sun tabbatar mata yau din bai fito ba, sai kuma ta karra tabatarta a wajen mai gadi dan haka ta mike ta nufi bangaren nasa hankali kwonce
Kamar yadda ta saba bayan sun gaisa da Yumnah ta sanar mata ta sanar masa itace, ama bayan zamanta a kalla ta dauki minti ya fi Ashirin bai sauko ba, hakan ya sa ta rasa shin hawa zata yi ko dai zaman zata ci gaba da yi ko Allah zai sa ya sauko? Gashi Yumnahma tunda ta hau bata dawo ba shiru kake ji
Har HAJIA zata yi tafiyarta gannin shirun ya yi yawa ta tuna waye jikanta, idanma dodo yake a wani wajen banda a gareta da ahalinsa baki daya, ta tabbata in dai ya san da zuwanta ba zai dauki lokaci kalau haka bai sauko ba, dan haka ta juya jiki ba karfi ta shiga hawa tana salama dan gudun shiga hakin kowa
A kofar dakin ta dakata ta yi bugu ya fi a irga tana Salama, ama yarinyar nan da dakinta ke daf da nasa bata fito ta nuna mata ta san da mutun a wajen ba, ita kuma ta ki ta hakura dan jikinta ke bata ba lafiya ba
A bangaren Yumnah kuwa tana sauraron HAJIA, hasalima a tsaye take jikin kofarta tana murguda baki kasa kasa ta ce" Yau na ga jarabar naci, ba zan kira maki shi din ba, Ni kam Inaga bayan rabuwata da wancen a nacin saura wannan masifafiyar tsohuwar, a wuni sai ta mana shigowa uku in yana nan ta zo ta ishe shi da surutu ta tafi, ko mahaifiyarsa bata masa zuwan nan kamar yadda wannan mata ke yi, ba abinda ke bani haushi irin turare turaren shirmen da take masa, ko me take tunani?, Inma menene bata isa ta nunan son mijina ba ama sai tana abu kamar wace bata san me take yi ba, a barshi ya huta tunda bai fito ba ai damu ne baya so zan gani in har zaki shigo dakin kai tsaye ne, inama ace dakin na shige na same shi koda wani abin yake in dauki hankalinsa !"
HAJIA kam jin shirun ya yi yawa ta shiga tunanin ko sauka take yi ta koma bangarenta ta yi kiran mahaifinsa ya mata kiransa ta ji yana kalau? Idan har ta ji an gama wannan ne kaΙai damuwarta dan bata son abinda take ji a ran nan nata
Sai kuma ta shiga tunanin yaushe ta koma cen?, Kai ina , a dan daburce ta juyo ta kama kofar ta bude tana Salama da karfi hadi da Hanna idannuwanta dagawa koda taka tarda wani abin to fa ya zamto idannuwanta basu gani ba
Shirun ya yi yawa, a hankali ta shiga bin dakin da kallo
A gyare yake tsaf tsaf ga kanshin turare da sanyi mai karfin tsiya a ciki har idannuwanta suka sauka kansa wajen kujerar dakin ta gaf da gado kansa a saman kujerar yana zaune a kasa jikinsa ba riga dan ya samu ya cireta da ya raarafa ya yi sallar azahar daga ita bai samu yin ta la'asar ba domin yana kwatanta mikewa sai ya ji kamar za'a maka shi a kas ga wani ciwon kai mai tsanani da bugawar zuciyar da sam bai san zasu iya riskar shi a irin wannan lokacin ba
Gaban HAJIA sai da ya fadi, ta dakata tana kiran sunansa ama ya kasa amsa mata
Da sauri ta daga kaffarta ta karasa inda yake ta shiga tabashi da ambaton sunnansa
A hankali ya iya buda idannuwansa ya sauke kwayarsu a saman fuskarta a lokacin da ta duko tana taba wuyansa ta ce" Subahanallah, Magidanci baka da lafiya ne dama ban sani ba? Ama dazun fa da na Barka kalau na tafi"
Idannuwansa ya lumshe yana sauke numfashi a hankali yana lumshe sunansa kasa kasa , muryarsa cen ciki ya ce" HAJIA......, Kin dawo?"
HAJIA ta gyada kai ta ce" Bari in kira a kaika asibiti kai fa baka iya ciwo ba, na shiga uku ka ga yadda idnanuwanka suka kade kuwa? Jiki du ya dime da zafi jijiya ta yi rado rado, kai subahanallah wannan yarinya da kake aure Ni tana da hankali kuwa? AI sai ki fada bashi da lafiya ko?"
Da kyar ya iya karasa jin maganar da HAJIA ke yi, a hankali ya dan mirgina ya dora kansa saman kaffafuwanta dan hakan yake da bukata, shi dama mutun ne da bai iya ciwo ba sam, kuma idan yana ciwo ta yannayin shanyuwarsa ake ganewa ba zai zo da kansa yace ciwo yake ba har sai ciwon ya kayar da shi tamkar ba likita ba, HAJIA kam ji ta yi hankalinta ya kara tashi, domin ko yana ciwo bai cika yin laushi da ita haka ba, abinda tana ihun a kaishi asibiti yana fadan ba inda zai je? Ama yanzu jikinsa kamar ana rura wuta?
Hankali tashe take janyo abin gadon dan hango salularsa da ta yi karamar , dan kuwa tana iya kamo lambar mai kwanoni da tasa tsaf a kanta
Tana ta rubuta numbobin muryarsa cen ciki da kyar ya iya budar bakinsa a hankali ya ce" HAJIA, KHausar.....yanzu ta daina kukan ko? An mata auren ta huta ko?"
Da sauri HAJIA ta yi cakkkkk daga abinda take yi tana kallonsa
A raunane ta ce"
Kai dai gaskiya bana so ma nace an ji kunyatu sai an saka nace, fisabililahi kar dai kace ciwon Kauna kake? To wai kai dilla mikeππππππππ
π¨π¨π¨π¨ Akoy fa rikici, watau ita Bama ta hango halal a ita da Magidanci ba, magidancinma nawa yake in ji matar jikan HAJIA!π¨π¨π¨π¨
ππππβ€βπ©Ήβ€βπ©Ήππππ
*DA CIWO A ZUCIYATA*
ππππβ€βπ©Ήβ€βπ©Ήππππ
_MALLAKIN_
*SAJIDA NIJAR*
*FREE BOOK NE* 4οΈβ£1οΈβ£
*GARABASA, GARABASA, PROMOTION, PROMOTION DIN LITATAFAN MARUBUCIYAR A KAN FARASHI MAI SAUKI 1K, YAN NIJAR KUWA 1000 FRANCS CEFA*
1: Duk karyar kada
2: Yar mahaukaciya
3: Neman na kaina
4: Bani da zabi
5: Bak'a ce
6: Kutkale
7: Makauniya ce
8: Mage
9: Duk nisan jifa
10: Idan ka raina inda kake
11: Dutse
12: Alkalamin kadarata
13: Bani da zabi
14: Dakika Biyar
15:Wata kokowar
16: Aure yakin mata
17: Ni zan ladabi
18: Daga tafia daukar soja
*Dukansu a kan farashi mai sauki, zaka saka dubu guda ne domin promotion ne nake yi, ka tuntubeni kan layina kamar haka +227 93 81 16 18, Sajida Nijar*
Now
*Da CIWO A ZUCIYATA*
*Tallah, tallah, tallah*
*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*
_Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_
Farar Humura
Bakar Humura
Humura special,
humura de bain
Humura epicΓ©
Lait de nuit
Parfums dΓ©sodorisant
Parfums rideau et dras
Lait de nuit
Alkam
Kulakcam
*WaΙannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa*
Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes
*Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:*
mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata
Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwaraiππ
Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuΙi wannan number 97 82 44 94
*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*
Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mataπππππ
A raunane Hajia ta ce" Eh an daura ama tana cen tana ihun bata so kuma, y'ar nan dai sai addu'a sosai abin nata sai addu'a dan nan, gashi aure ya dauru kuma"
Idannuwansa da sukai masa nauyi ya bude yana kallonta, ya dan dauki lokaci yana nazarin maganarta kafin ya ce" bata so? Auren da ta kawo mutumen da kanta ne bata so Hajia..........
........." Ya karashe yana sake rintse idannuwansa da karfi saboda sara masa da kansa ya yi
Hajia ta so cicidawa da shi ama ta gaza dan gaba daya yana son sage mata gwuiwoyinta da nauyinsa da kuma rigimarsa, da kula sosai ta ce" Eh wai bata so ina ita ina mijin , yaro ne meye meye, kai dai abu sak irin na kamun aljannu da kyar na fito dan na ji a raina kamar kana wani hali "
Shiru yanzun ya mata, shiru sosai ya mata banza, ta ci gaba da maganarta ya kyaleta
Jin ya yi shiru ya saka Hajia taba wuyansa, sosai jikinsa keda zafi haka kuma ita da ya ajiye kansa a saman kafafuwanta tana iya jin yadda zuciyarsa ke bugawa
Da kula ta ce" Bari in kira mai kwanoni mu je a kaika asibiti magidanci ka ji?"
Shiru ya mata bai ce mata eh ko a'a ba, shi kadai ya san irin nauyin da karfin da kansa ya masa, jikinsa kuwa tamkar ba nasa ba haka yake ji
Hajia ta samu da kyar ta sauke kansa ta Ιora saman filo harda rufa masa abin rufa sannan ta fita ta sauko kasa tana faman duba wayarta
Turus ta yi tana kallon Yumnah, wace ke zaune a baban falon kafa daya kan daya tana amsa waya, yannayinta na iya fasara maka halin farin cikin da take ciki,
Itama Yumnar da mamaki take kallon Hajiar, domin a tunaninta Hajiar ta jima da barin gidan ai
Bata ce mata komai ba ta yi hanyar fita sai sake riΖe hijabinta take yi, ita yanzun ai bata da lokacin uban kowa tunda magidanci ba lafia , bari dai a kaishi asibiti a dawo sai ta rikita kowa a gidan nan, ta kula yarinyar nan banda abinda ke damunta na rashin auki harda hauka take fama da shi, wannan ai ba matar auren magidanci bace, ace magidanci ba lafiya matarsa zaune tana waya? Sakarcin banza sai fama da kashi a wuya ita ga mace, shirme zata ga mata gannin idonta
Karasawa ta yi har bangaren su Mama ta hadu da yarinyar wajen kishiyar maman wace take riko wato Hamdiya
Wayar ta mika mata ba tare da ta iya amsa gaisuwarta ba ta ce" Ke Hamada dubo min lambar mai kwanoni kaina ya fashe na gaza ganewa dama Ni a duniya lambar magidanci kadai na hadace a kaina"
Cike da ladabi Hamdiya ta amsa ta fitar da numbar aban ta aika kiran sannan ta ba Hajiar
Hajia ta dakata har Aba ya daga wayar ta dan matsa tana rage murya ta ce" Kana ina ne Ni?"
Aba ya sanar mata cewa yana tare da baki ne dan bai zaci yar gayar da ya yi za'a taru haka ba
Hajia ta ce" To ko me kake yi ka bari ka zo ka kaimin magidanci asibiti, ka ganshi cen rai a hannun Allah jikinsa zafi rau, Ni abin ya bani tsoro tunda Ni din nan ya dora kansa a kafata yana min magana a sanyaye ka san kuwa ba lafiya ba dan in dai lafiyar Allah ai bama magana a hankali da Magidanci ko?"
Aba ya yi dan
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 27 Chapter of 47