Share this page
ban san yanzun a kan wani mataki za'a yishi da Ni ba, kar aje Ni din ta kaina ake bi ana cimma mutanena...." Daga haka ta sake mika hannu ta ja mayafinta, wannan karro tun kafin ta ja mayafin ya sauka daga hannunsa , ta janye a hankali ta dora shi a gefen kafadarta sannan ta juya wajen motar nan ta dauki jakarta ta rataya ta kama hanyar tafiya tana share idannuwanta har gabanta na mata ruwa ruwa kamar wace ta sha wani abu A tsaye yake, yana binta da kallo har ta bacewa ganninsa gaba daya A hankali ya dan ja numfashi a kirjinsa ya sake rintse idannuwansa ya bude ya kuma bin hanyar da ta bi da kallo A cen kasan zuciyarsa kokarinsa ya ba kansa tabacin cewa ranta ne ya baci iya bacewa shi yasa har ta yanke wannan hukuncin, ya san yadda zai bi ya bata hakuri ta sauko Dan murmushi ya yi a hankali yana juyawa dan ba sauka ya yi ba su doctors ya takawa sai ya ganta tsaye , a sanyaye ainun ya dan sake sakin murmushi, yana so lalle sai ya kori wani gefe na zuciyarsa dake fada masa kamar ba wasa take yi ta hanyar tabbatarwa ransa cewa to ai kadan daga aikinta, in dai Khausar ce idan ranta ya baci tsaf take wanke shi abinta, bata ko duban girmansa abinta, uhum abin haushi wai mayafin da ya mata magana kansa karshema a kafada ta yafa Bama rufashi ta yi ba, ai zai ga in zata iya tafiya har gida da shi a gefen kafada Yana shiga office dinsa ya ciro wayarsa ya zauna a hankali ya shiga kiran numbarta Kira na farko ya shiga, ama na biyu sai kiran ke dawo masa Ido ya dan zarro dan hakan na nufin ta saka shi a Black list kennan A hankali ya ajiye wayar yana furta " Uhum Allah shi kyauta ya shirye ki" Daga haka ya ci gaba da yan aikace aikacensa, duda hankalin nasa a rabe yanzu, ama haka ya ringa aikin dan dole ne ya gama abinda ke gabansa a yau Khausar bata isa gida ba sai kusan magariba Koda ta je ta tarda Mama bata nan ama ta Bara mata ky a makota, dan haka ta amso ta zo gida ta cenza kayanta sannan ta shiga kimtsa gidan ranta a matukar bace Tana gamawa ta dora masu yar makaroni ta koma ta zauna ita kadai tana cije lebe da kuma tarin jin haushin da ya daskare mata a cen kasan zuciyarta Yanzu ita? Kennan waye ya dauketa da mahinmanci ne a duniya bayan iyayenta? Bata taba tunanin zata iya riskar wannan gagarumar surprise daga mutun mafi kusanci da duniyarta ba irin TAUFEEK Ita fa babu wani uzuri da zai gabatar mata ko za'a fada mata ta saurara ko ta gane A zamantakewarsu ya dace ace ya fi kowa Sannin wacece ita, idan tace wacece ita tana nufin koda aikin sirri yake yi a yadda ya gama karantarta in ba dan yana anfani da ita dan cinma aikin nasa bane da ya sanar mata sirrin dake boye a tsakaninsu Ita me ta boye masa ne? Irin yadda take yiwa umarninsa biyayya kuwa tana tunanin su Aba kadai suke gaban furucinsa Wata kwafa ta yi tana amsa salamar su Salma yarinyar dake bayan layinsu ta mike daga zaunen da take a zuciyarta tana ayana' hijab ko?, Zan saka ama na rantse maka ba dai irin wancen ba, kai ba zan kuma maka biyayya ba, ba Ni ba kai! Zan kiyaye adinina ama bi izinillah nima zan dauki wasu shawarwari da ake bani a matsayina na budurwa kuma musulma dan gyaran kaina ba dan batawa ba na kasance kamar kowa!, Wani sa'in harma da gudun kar kace yace nake bulumtun nan! A yanzu ka jima baka ce ba, koda yake Bama sai na kuma haduwa da kai ba bale har ka iya bani opinion dinka a kan abinda yake nawa! Domin daga yau Ni nice Ni daya ce kuma, du wani bestyma ai cuta ce, kwarai Hajia ta yi gaskiya ashe amincinmu akoy wata a kasa? Watar kuwa ba komai bace face cuta tsagwaronta!, Wasu mutanen dai sun ji kunya' Tabarma ta shinfida masu, sunna neman zaunawa sai ga Maman ta dawo a gajiya tilis, dama daga gidan rasuwa take kuma na kusa ne sosai tarema suke da Aba, Jin rasuwar da aka yi ya sakata kin fada masu abinda ta ƙunso take jira ta sanar masu, saima ta shiga hidimarsu ba tare da ta gane cewar salmar nan wajenta ta zo ba har sai da Maman ta kireta daka ta ce" Khausar, yaya zaki bar bakuwarki zaune ita daya ne haka?" Khausar da mamaki ta ce" Mama bakuwata kuma? Na zata ko aikota aka yi wajenki?" Maman ma da mamaki ta ce" Wajena kuma? To wa zai aikota Wajena?, Da aikotan ne aka yi ai da ta sanar min ko?, Na ga tare na tardo ku kuma Ni bata nuna Wajena ta zo ba ki je ki dan saurareta mana ?" Khausar ta fito zuciyarta cike da mamaki, abinda ya sa mamakin ke damunta Salmar nan dai na farko ba sa'arta bace, dan a kadan tana iya bata shekara shida ko fiye, sannan irin rikakun yan ji da kan nan ne na anguwa wa'inda ko gaisuwarka basu cika amsawa ba don mahaifinsu na mai kudin anguwa, a gaskiya a gidansu ana fadin sun cika girman kai, kuma daga mahaifiyarsu suka dauko domin kaf layin nan da bayanshi babu wanda mahaifiyarsu ke hulɗar arziki da shi, ita ta fi karfin ajinsu, mahaifinsu dai da sauki dan shi ko me ake yi a anguwa in dai ya ji ana yi da shi yana zuwa fatiha na sunna ta aure ko zana'iza Zama ta yi yanzun du a takure ba kamar dazu da take sake ba, dan dazu a tunaninta wajen mahaifiyarta Salma ta zo Salma kam ko a yanzu da Khausar ta dawo ta zauna tsaf ta kare mata kallo,.kallo irin na son Sannin shin da gaske ƴaƴanta matar nan ta masa ne har da ya nace haka da son samun kusanci irin na zuciya da zuciya da ita ko da akace likita ce ita din yake so ta zamto a cikin ahalinsu? Dan murmushi ta yi tana mikewa ta saba jakarta a kafadarta ta yan gayu tana kallon KHausar ta ce" Sister, zan juya, ki dan ban numbarki dama fira na kawo maki" Sosai Khausar ta so cewa Fira kuma? Ta me fa? Sai dai ta kasa fada saima hijab da ta saka a shigarta dakin dan bata cika son kallo irin wannan ba a rayuwa yana damunta ainun Wayarta ta dauko ba wata damuwa ta ba Salma numbar tata harma ta dan taka mata bakin kofar gida sannan ta dawo da sauri tana ta hade rai dan a dan fitar nan ta san ta sake cirarwa kanta magana, ana iya cewa bata mu'amala da mutane talaka sai masu kudi, shi yasa batama tsaya har Salma ta shiga motarta ba ta dawo da sauri A wannan daren abincin kirki kasa ci ta yi, danma juwa ta fara nusar da ita menene yinwa, da tana iya kasa cin abincin kwata kwara dan cin amanar da akai mata, wani sashe na zuciyarta kuwa kuka yake yi sosai na decision dinta, sai dai ta ja ta tsaya zata ga waye keda iko cikin ita fa shi! ____________________________________ Karfe bakwai na safe *TAUFEEK* Zaune yake saman table yana karyawa kira shigo wayarsa, kira ne mai mahimmanci dan haka ya dan mike ya shiga amsawa, Yumnah kuwa ta bishi da wani irin sansanyan kallo tana jin wani irin nutsatsen kusancin zuci da idannuwa idan tana ta kallonsa Idannuwanta ta lumshe, tana matukar jin tarin kauna da girman mijinta a zuciyarta Dawowarsa ya sakata sake zuba masa wani shayin sannan ta koma ta zauna tana kallon yadda yake dan sha yana duban screen din wayarsa dake ajiye a saman table din Dubanta ta kai itama, sai ta ga kamar call ne yake aikawa Har zata cire kanta sai ta sake dubawa dan haka kawai ta ji idannuwanta sun sake likuwa a saman screen din wayar Da sauri ta dauke idannuwanta ta zuba a saman fuskarsa Yannayin fuskarsa sam ba walwala a tare da ita, tana fadin tun jiya kamar hankalinsa a dan rabe , kuma yanzu sai ta ga yana kiran matar da ta yi tunanin ko ta tabata ne? Watau an yi baram baram ne? Dan kuwa an jima bata ga kiranta a wayar mijinta ba Ajiyar zuciya ta sauke mai zafi a lokacin da ya gama sha ya nuna ba zai iya karyawa da wuri ba zai dan fita, sannan ya mike yana daukan rigar dake ajiye mai ruwan ashe color ta vst ya dan rayata a hannunsa na hagu da dayan hannun nasa ya dan talafota a lokacin da ta karaso tana kokarin dane damuwarta Fuskarta ya dan zubawa ido kadan, kasa kasa ya ce" Ki yi kokarin wuni a wajen hajia yau Yumnah...." Cikinta sai da ya juya daga tsayan da take, ta zata ya manta da maganar cewa ta je 5 gaisar da Hajiar da ya mata, sai gashi abin ya ce za zani harda su ta wuni a cen?, Wuni? Ita da matar nan? Tap to ita ta wuni a yaya kennan? Ai ta tabata tana iya wuni ne cikin ukuba da tsoro, matar da kowa tsoronta yake a gidan? Bale ita da ta tsaneta ƙarara? ..... gaba daya sai ta rasa kuzari har ya fice a gidan ba tare da ta tabuka abin kirki ba Saman kujera ta zauna tana sauke numfashi bayan ta dannawa mahaifiyarta kira Kamr ko yaushe jajen Khausar ne suka yi, mahaifiyarta cike da mamaki ta ce" Wai a yanzunma da yarinyar nan ta fita a makarantar su ba zata rabu da shi ba?, Alakarsu ta fara bani tsoro Yumnah" Yumnah ta share hawayen da suka tarun mata a gurbin idannuwanta a sanyaye ta ce" Mama, sai kin ga kamar ba ita a duniyar da sai kuma ki ga tana nan daram a duniyar tasa, kin ga dai an dan jima ban ji duriyarta ba, kuma bata zo gidan ba tun wancen zuwan da wancen tsohuwar ta yayabota, sai kawai dazu na ga yana ta danna mata kira da safiyar nan, Ni kam ban san wannan wace irin maya ce ba!" Mahaifiyarta ta yi dan tsai, a dan kausashe ta ce" kema sai nake gannin harda laifinki, ta yaya zaki bari yana maki kiran wata a lokacin da kike tare da shi? Wannan fa saken ki ne ba komai ba, kuma yanzu ki zo ke hankalinki a tashe nima kina tayar min da hankali, a gaskiya wannan din saken ki ne!, ya dace ki san mace kike in ta laluma ko ta tsiya ki kwatantawa mijinki idan yana gabanki kece a gabansa ba wata banza ba koda matarsa take bata da wannan hurumin in yana gabanki naki ne ke daya!, Ama sai kina wani abu kamar wace ke jin tsoronsa, in na baki shawarwari ki nunan kin dauka ama in na tambaya sai ki nunan baki yi ba zaki yi, mazan nan na zamaninmu ma ba wani cika kiyaye hakin iyali suka yi ba bale na yanzu!, Na fada maki da kirsa zamu rabata da shi ama kuma wani abin sai mun dora doka irin tamu ta mata, ki sani mace fa sarauniya ce in ta yi wasa kuwa tana iya zama bola, kuma du namijin da yace shi karya ne babu macen da ta isa ta juya shi ko wani abin karya yake Yumnah, bai dai hadu da mai juya shin ba, kar ki yarda TAUFEEK ya fi karfinki ta yadda zaki dawo kina kuka da barin jiki idan ya yi magana Ni dai na fada maki, kuma maganar zuwa wajen kakarsa ban ce ki wuni ba, ko daya ban saka ki ba, ki je ki gaisheta sama sama ki dawo dakinki ko uwarsa ban saka ki sakin jiki da ita ba bale wata kakarsa da ba sonki take yi ba ni kin ji maganata!" Daga haka ta kashe wayar tana ta bambaminta, ta bar Yumnah cikin wani dogon tunanin da sake daurar damarar yaki da duk wata halitar da zata iya zamtowa matsala a duniyarta da mijinta ko wacece! Da wuri ya iso asibitin, domin yau aikin ba iya na takarda bane na aikace ne wanda yake saka tsauri sosai a cikin lamarin A wajen ajiye motocinsa na asibitin dake gefe daban da sauran motocin manyan ma'aikatan cikin asibitin ya ajiye motarsa a hankali ya sake daukan karamar wayarsa a kasan zuciyarsa yana tunanin me kennan? Me yasa take kin daga kira harda numbar da bata sani Bama?, Bai san me yasa fushin nata ya masa katutu a cikin zuciya ba Iska ya fitar mai zafi daga bakinsa a hankali ya juya da niyar daukan bak'ar jakarsa dake ajiye dan ya fice zuwa ciki, domin tuni vigil biyu ke jira ya fito su amshi kayan hannunsa idan yana da su, ya dago dubansa a hankali dan bude motar ya fito nan ya dakata da sauri yana ruko idannuwansa ya zuba mata ido A hankali ya sake dan kifta idannuwansa yana sake dubanta dan tabbatarwa ko dai ba ita bace? , Sai dai a lokacin da ta dan dakata tana laluba yar bakar dake hannunta ta ciro karamar bak'ar wayarta ta duba kiran da shine ya yi mata shi ta katse kiran ta jefa wayar a jakar ya tabatar masa lalle wannan baiwar Allahn dake tafiya zuwa cikin asibiti da shiga irin ta riga da sket daidai da jikinta, kanta da dan karamin hijab fari kal mai dan kwaliya, sai kuma dan mayafinta siriri fari kal a gefen kadarta ta yi yafe da shi, yafe jama'a ba ta bude shi ta rufe jikinta ba, harda yar agogo siririya a hannunta baka sidik wace ta kama hannun nata ya mata wani irin sassa gwanin kyau Bai ankara da kallon da yake mata ba har sai da ta bacewa ganninsa Da mamaki ya dan dafe goshinsa a hankali ya furta" me kike nufi ne Khausar?, Baki isa ba!, Hakan ba zai taba yiwuwa ba, dan kina fushi da ni ba zaki fito a haka ba sutura ba!" 😔😕 Inaga dole sai mun hadashi da Hajia ta ce igiyar uban wa ke wuyanta? Ni dai ba luwana🤣🚶🏻‍♀️🚶🏻‍♀️🚶🏻‍♀️🚶🏻‍♀️🚶🏻‍♀️🚶🏻‍♀️ 💔💔💔💔❤‍🩹❤‍🩹💔💔💔💔 *DA CIWO A ZUCIYATA* 💔💔💔💔❤‍🩹❤‍🩹💔💔💔💔 _MALLAKIN_ *SAJIDA NIJAR* *FREE BOOK NE* 3️⃣0️⃣ *GARABASA, GARABASA, PROMOTION, PROMOTION DIN LITATAFAN MARUBUCIYAR A KAN FARASHI MAI SAUKI 1K, YAN NIJAR KUWA 1000 FRANCS CEFA* 1: Duk karyar kada 2: Yar mahaukaciya 3: Neman na kaina 4: Bani da zabi 5: Bak'a ce 6: Kutkale 7: Makauniya ce 8: Mage 9: Duk nisan jifa 10: Idan ka raina inda kake 11: Dutse 12: Alkalamin kadarata 13: Bani da zabi 14: Dakika Biyar 15:Wata kokowar 16: Aure yakin mata 17: Ni zan ladabi 18: Daga tafia daukar soja *Dukansu a kan farashi mai sauki, zaka saka dubu guda ne domin promotion ne nake yi, ka tuntubeni kan layina kamar haka +227 93 81 16 18, Sajida Nijar* Now *Da CIWO A ZUCIYATA* *Tallah, tallah, tallah* *SECRET DE LA FEMME DU MANGA* _Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_ Farar Humura Bakar Humura Humura special, humura de bain Humura epicé Lait de nuit Parfums désodorisant Parfums rideau et dras Lait de nuit Alkam Kulakcam *Waɗannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa* Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes *Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:* mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃 Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan number 97 82 44 94 *SECRET DE LA FEMME DU MANGA* Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata💃💃💃💃💃 Cike da jin haushin ta ya yi kyaftu ya zauna nan ba tare da ankara da yannayin lokaci ko yannayin da yake ciki ba, shi ba aiki ba, shi ba tafia gida ba, karshema sai ya danna buton ja dake nunin idan yar fitilarsa ta bada kar a shigo office dinsa baya bukatar gannin kowa A lokacin da Khausar ta fito sauri ta ringa yi wajen saukowa daga kasa, cikin sauri ta nufi bangaren su ta shige dakin su na mata sannan ta yi bayinsu da sauri ta shiga ta rufe kafin ta karasa ta dukar da kanta jikin abin alwallah ta ringa sakin nishi a jajere a jajere, sai kuma hawayenta suka bale tamkar an bale mata su ne Bata san dalilin da ya sa take jin dacin abin har haka a ranta ba Ko ba komai ai ya nuna mata a kan aikinsa yake, kawai abinda ya sa abin ya mata ciwo ainun tunanin an wulakantata ne, an wulakanta iliminta da hankalinta A kan abu daya ta ajiye kusancin da TAUFEEK ya kirkira tsakaninsa da ita dan ta zamto balagazar makaranta wace ta san kowa take hulda da kowa ba ruwanta da ta birgeka ko ta mata kwaskwasa dan ka sota, kana iya yin firarka a gabanta dan ba abinda ya shafeta, haka mu'amalarta da malamai du irin yadda duniya ta lalace ita dai da su ido ne domin ko kucakin malami ba birgeshi zata yi ba a yadda ta gudanar da rayuwar makarantarta A dole abin ya mata ciwo mai zafin gaske A dole abin nan ya taba mata zuciya Bata san me zata ce ba, yaya zata yi, tana matukar jin ciwo mai girma a zuciyarta na irin yadda mu'alamarsu zata ruguje tana ji tana gani Sai dai rugujewar shine alkhairi dan bata ga kuma me zasu iya cewa junna a yanzu ba, ya fi karfinta ya fi karfin ajinta shi din ba abokin yinta bane, ta kowani fani idan ta duba a yanzu sai ta ga idan har ta yarda ta sakawa ranta ci gaba da shi din kamar ta cuci kanta da kanta ne A hankali ta dafe kanta hawaye take yi sosai sannan ta dafe gaban kirjinta a sanyaye ta ce" Ama da wa zan yi fira? Wa zan SANARWA damuwata?, Wa zai rarasheni? Waye zai min fada? Wanene zai ringa sakani ko hannani bayan su Mama?, Me yasa ka saka na sakankance da kai haka? Me yasa ka shiga jikina haka?, TAUFEEK baka min adalci ba, baka min adalci ba TAUFEEK, shin yaya zan ci gaba da walwala ba farin cikinka a tare da Ni? Ya Allah ka bani mafita mai sauki a cikin lamarina.........." Surutu take yi irin na zafi da ciwo a cen kasan zuciyarta....... Ta shagala sosai yar karamar wayarta ta shiga kuka a cikin aljihun rigarta Da sauri ta lalubo tana tunanin ko dan sahunta ne da ya ga shiru bata tabo shi ba har yanzu? Numbar ta zubawa ido tana kallo, domin bakuwar lamba ce a wayar Tata A hankali ta daga tana dan gyara muryarta hadi da yin salama sannan ta yi shiru "Amincin Allah ya tabata a gareki kema Likitana....." Shiru ta yi, jin Muryar namiji ne, da kuma abinda aka fada din A hankali ta dan budi bakinta ta ce" Ban gane mai maganar ba?" Dan murmushi ya yi shima ya ce" Allah sarki dama nace akoy sanyin murya matata to be in sha Allah, jiya na turo kanwata Salma ta amsar min numbar dan na yi na yi na tareki na amsa na kula da wahala fa ki saurareni a hanya, karma aje ki ce min bakya so na na suma dan firgici" A hankali Khausar ke dan sauke numfashinta, lokaci daya ta afka wata sabuwar duniya ta tunani da tarin mamaki Yayan Salma?, To wane? Salma dai Salma? Kai, anya kuwa? Har yake kiranta da matarsa? Ko dai ya yi batan numba ne?, Da wahala in ba batan numba ya yi ba, ya rab........., Sai dai du rikicewar ta wannan karron sai ta ki kashe kiran haka kuma ta kasa yin wata magana da zai iya jin ba dadi Ko ba komai tana kan gaba ne ta nema irin wannan A hankali ta dan sauke numfashi jin yana ta afkin fadin ta amsa shi plz A sanyaye sosai ta dan ja numfashi ta ce" Zan je gida ne na ga dan sahuna na kira" Shima a sanyayen ya ce" Ba damuwa, sai kin zo, plz ki kular min da kanki, sannan zan yi kira idan kin huta dan ina so ki amsheni, ki dubeni ki bani dama kin ji kanwata????" Murmushi ta samu kanta da saki a hankali ta furta" Na gode" Sannan ta kashe kiran tana dan samun kanta da sake sakin murmushi Yayan Salma? Yayunta maza biyu ta sani.....shin wanene a cikinsu?................haka kawai ta tsinci zuciyarta da jin nutsuwa da farin ciki harma ta wanke fuskarta ta fito ta cire rigarta ta nade ta saka a jaka sannan ta dauki kayanta da mayafin nan nata ta kade ta dora a kafadarta tana turo baki cike da jin haushin furucinsa wai wani bata yi kyau ba, kar ta yin, karma ta yin! Ai dama ba cewa ta yi ita mai kyau bace, kwaliya ne yace itama ta aura irin na yan mata!........... Haka ta yi ta fadanta a zuciyarta har ta samu ta fada adaidaitar, domin ba wani a sake take ba da mayafin nan, kawai rikici ne rigima ce, kuma tunda ta yafa shi mamama da mamaki tace a haka zata tafi ne? Tace eh, mama ta ce da ta bude shi ta dan yafa jikinta duka sai tace ai ba komai , ita dai Mama kallonta ta yi tana jira ta ga da gaske? Sai kuwa ta ga da gasken ta tafi da yafen, jirantama tane yi a gidan ta dawo su zauna dan ba dabiar kirki bane hakan sam Rai bace Taufeek ya dawo gida, domin kowa bai je nema ba dan a sama sama yake ba zai iya jure wani neman fitinan ba, direct bangarensa ya nufa yana mai kokarin kawar da dukkan wani bacin rai dake taso masa ko dan kar ya shiga hakkin abokiyar zamansa, domin ba ita ta hasala shi ba idan ya sauke mata fushinsa bai yi mata adalci ba Sai da ya yi wanka ya sauko sakamakon irin yadda ta yi ta kai kawo cewar abincinsa na jiransa Zama ya yi saman cafet a hankali ya mika hannu ya kashe tv dake yi, domin baya son hayaniya ne sam, kansa na dan masa ciwo, gaba daya ransa a dagule yake, sai dai abu daya da ya sani shine ba damuwa ya kyaleta, zumunci ne tunda ta katse babu yadda zai yi, ba zai saka mata wuka a wuyanta ba kan dole sai ta yi zumunci da shi tunda bata ra'ayi, yaya zata kasa yi masa uzuri a kan abinda yake aiki ne nasa? Idan ta ji cewa Yumnahma bata san komai game da aikinsa ba a matsayin dan kasuwa kuma matashin dan makaranta ta san shi ta ce me kennan? Ya dace ta masa uzuri, yaya take tunanin zai fito ya ringa yayata mata maganar sirrin aikin da yake da girma da daraja irin ta taimakon rayuwar dan adam?, Itama da gangan ta kasa gane cewa ya jima da samun takarda irin tata take tafe a makance, da gangan ta ki fahimta dan kawai ta daga masa hankali, kuma ta taki Sa'a ta daga masan domin ta fado a daidai lokacin da ta riga ta gama zamtowa tamkar jinnin jikinsa, yar uwarsa ta jinni, ama kuma ba komai dan uwankama

Chapter 21 of 47