Share this page
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels 💫 UMAYMAH 💫 ✍️A&A PEN Follow our Whatsapp group via this link https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3 https://wa.me/+2348039352724 VOLUME ONE EPISODE 0️⃣1️⃣ Yana tsaye a bakin ƙofar yayi Knocking har wajan sau uku kafin cikin husky voice yace "Khadijah buɗe ƙofar nan kar ranki ya baci" yayi maganar cikin harshen larabci. can na hangota a ƙarshen gadon a cure tana motsi, ashe da mutum a ɗakin. "Khadijah" ya ɗaga muryar, a fusace wannan karon ya kira sunan ta, sai kuma yaja tsaki yana barin ƙofar ɗakin yace "ki fito ki same ni a falo yanzun nan kar ki ɓata min lokaci. A hankali ta yaye bargon data rufa dashi ta fito, kana ganin ta zaka gane a tsotse take, tayi duhu, ga wani kashin wuya tsab wasu kwandaloli za su ɓata (su samu wajan zama) a wuyan ta, idanuwan ta sun wani jeme (sun koɗe) sun ƙankance sun yi ja, da alama dai tasha kuka, koma nace kukan ma ta ke yi, bakin ta a bushe kamar wacce ta fito daga rana, fatar jikin ta ta ɗashe tayi wani irin fari kamar mai ƙaramin Yaron ciki, kanta babu ɗankwali kalaba ce a kanta ta tsofa sosai ta zubo har kafaɗun ta, laushin gashin saiya ƙara fito da tsufan kalbar, riga da wando ne a jikin ta pink color da fararen flowers a jiki, ƙafafun ta sun yi sirara a cikin wandon. Ta mike da ƙyar ta buɗe wardrobe ta ɗauki hula ta saka, tana tafe tana bin bango, ta buɗe kofar kenan ta kara jiyo muryar shi yana cewa "wallahil azeem na taso yau sai jikin ki ya faɗa miki" Da ƙyar ta ƙaraso jikinta har rawa yake ta fito palour, yana zaune akan one sitter hankalinsa kwance kamar ba shine yayi mata ihun ba, yana riƙe da remote a hannusa yana canja channel, da ƙyar ta ƙaraso ta durƙusa a gaban shi, sai da ya kai kamar minti biyar tana tsugunne bai ce mata komai ba kafin ya bude bakin shi yayi mata magana cikin isa "Dago kan ki magana zamu yi" kana jin hausar tasa kasan ba cikakken bahaushe ba ne. "Khadijah"! Ya kira sunan ta, ta ɗago kai ta kalle shi cike da kokonto dan suna ne da ba zata iya tuna randa ya kirata da shi ba, amma yau Khadijah gatsal tunanin tane ya katse jin yana cewa "yau ce ranar ki ta ƙarshe a gidan nan" da hanzari ta dago kanta ta zuba masa ido, nan da nan hawaye suka wanke mata fuska, karon farko ta buɗe bakin ta tayi magana muryarta na karkarwa saboda kuka tace "Habibi me nayi maka? Na tambaye ka laifina har bansan adadi ba, amma sai kace ba komai. Dan Allah dan son ka da Manzon Allah kayi hakuri kayi min bayanin abinda nayi maka, nayi maka alkawarin zan gyara kuskure na Habibi, so yana zama ƙiyayya ne dama? Kai kadai na ke so a rayuwata, kai ka nuna min so, ba zan iya rayuwa babu kai ba Habibi dan Allah kaji tausayi na" ta ƙarasa maganar tana shesshekar kuka, yadda take rusa kukan tana roƙon sa yayi hakuri saida zuciyarsa ta motsa, yaso yaji wani abu a ransa mai kama da tausayinta, tsayawa yayi yana saurarenta kamar ba zai yi magana ba sai kuma yace "Khadijah khuruj min hayati (get out of my life). Cikin kuka ta tari numfashin sa da cewa "Anta li wa ana laka (you are for me and i am for you). Kanta ta kife akan cinyarta ta saki kuka mai cin rai, tin daga ƙasan zuciyar ta take jin wani irin ciwo yana taso mata. "Ƙararati laa yumkin taghiruhaa (my decisions cannot be changed)." Cikin kuka tace "anaa asif arjuk a tini farsah thaniyah (I'm sorry please give me a second chance)." "na kiraki na baki takardar ki ne, ban kira ki dan ina son kallon fuskar ki ba, har yanzu you are a young girl find someone I'm no more interested, kamar kullum na faɗa miki ba ki yi min komai ba, Na gaji da zama ke ne kawai, nima zan auri wadda ta dace da ni." Shi kansan yasan hundred percent abinda yake faɗa ba shine a ƙasan zuciyar saba, to amma furta kalaman ga Khadijah kamar wani umarni ne dake riƙe da ransa wanda sam ba zai iya ƙinfaɗar suba. Da sauri ta dago kai ta kallesa, jajayen idanuwanta da suka kumbura ta zuba masa ta ƙara maimaita "wata kuma" Ina Alkawarin mu? habibi pls na roƙe ka ka yi haƙuri mu rayu da juna, Habibi dan Allah ka janye zancen sarkin nan, zan cigaba da zama dakai koda ba zaka bani abinci ba kamar yarda muke a yanzu, auren mu just six month na koma gida, na zama karamar bazawara kenan? Saboda kai ban cigaba da karatu ba, Babana baya son auren mu ka sani, ka manta yadda Hakimi ya shiga maganar auren nan? iyayena suna son nayi karatu. Ka san 'yan boko ne, gaba ɗaya dangin mu babu wanda ya taɓa yin aure a kananan shekaru sai ni. Da sauri ya katse ta da cewa "Ban manta ba Khadijah, ina zan manta yadda iyayenki suka amince da kyarata, da yadda suka rinƙa ce min baƙon haure, duk da mahaifi na ya dade a Kano kafin ya koma ƙasar mu gaba ɗaya, amma haka iyayen ki suka ce mana baƙin haure, yanzu sai ki koma gida ki auri ɗan 'uwan ki Bahaushe" ya daga kiran daya shigo wayar shi "eh ina gida ki ƙaraso." Shiru falon ya ɗauka sai Tv da ke aiki kamar mintuna sha biyar aka yi sallama wata Matashiyar budurwace ta shigo zata bawa Khadijah shekaru ɗaya zuwa biyu, riga da skirt ne a jikin ta na atampa matsattsu ta yafa siririn mayafi a wuya da takalmi mai tudu baki da bakar jaka, bata da tsaho, tana da dan haske amma daga gani ana shiga kanti sosai tana bleaching, dan fuskarta ta yi wani dabbara dabbara da pink, kamar tana da dan budewar ido, idanuwanta kanana ne hancin ta gajere bata da diri ko kadan daga saman ta kirjinta a cike yake sosai har yayi mata yawa. Khadijah na ganinta ta miƙe da sauri cike da ƙarfin hali tace "yauwa Zaliha zo ki roƙarmi Habibi yayi hakuri dan Allah" ta rike mata hannun. tace "Dan Allah Zaliha idan aka ce miki Habibi zai rabu dani za ki yarda?" Zaliha ta kalli hannunta da Khadijah ta rike ta zame hannunta tana mata wani irin yi mata kallon kyama ta wuce ta, kai tsaye ta tafi kusa da shi ta zauna kamar zata shige jikin shi. "Kin ƙaraso, kin bar ni ina ta jira? amma mun kusa kai wa ƙarshe" Da mugun mamaki khadija ta juya tana kallon su su biyun, me ke nan, me suke nufi? ta tambayi kanta, Zaliha fah ƙawarta take gani a kusa da mijinta a zaune? me hakan yake nufi? dama Zaliha ta san zancen sakin ke nan, to amma ta yaya? Habibi ya dade yana mata barazanar saki, toh barazana mana zata ce, kwata-kwata auren nasu wata shida, wata uku ne kawai tayi su a kwanciyar hankali. Muryar Zaliha ta katse mata tunani da cewa "Malama ba mu da lokacin zaman jiran ki." Zaliha ta mike ta ƙaraso har inda Khadijah ta ke, ta kalle ta ta yi wani murmushin mugunta tace "Khadija kenan 'yargata kuma 'yar so hmmm! ki na mamakin na san maganar saki ko? ta ƙara faɗaɗa murmushinta "Dama tun farko ta dalili na kika hadu da shi Khadija da alama kamar kin manta hakan ko?" Khadija ta kalle ta baki buɗe kamar mutum mutumi (robot) da mamaki sosai a fuskar ta "rufe baki baiwar Allah" sai da Zaliha ta faɗi haka sannan ta san bakin ta a bude yake tsabar mamaki. Zaliha ta juya wajan sa cikin gadara tace "Ka rubuta mata takardar sakin ne? Jikin sa na rawa yace "yanxu zan rubuta mata" ya miƙe ya shiga ɗakin shi. Khadijah ta bi bayan shi da kallo, sai kuma ta fara tari kamar wadda aka shaƙe. Zaliha nayi mata dariyar mugunta tace "Ay baƙin ciki yanzu za ki fara gani Khadijah, komai ke Allah zai bawa kin fini kyau, kin fini ilimi, kin fini gata, iyayen ki masu rufin asiri, kin auri miji na gani na fada, sutura sai kin cire ki bani kwance (kyauta). A makaranta ke ce mai farin jinin Malamai da ɗalibai, kowa inya buɗe baki sai dai yace Khadija, Abinci ma Ummanki ke bamu, wallahi Khadija kullum zuciya ta tafasa takeyi da waɗannan ni'imomin da Allah yayi miki, duk lokacin da kike walwala kunci na ke yi." Wani zazzaɓi ne ya rufe Khadija, lokaci guda miyau (saliva) ɗin baki ta ya ƙafe da ƙyar ta kalli Zaliha tace "ashe ba da zuciya ɗaya kike zaune da ni ba? ashe alkhairi yana zama sharri, kar ki yi min haka Zaliha kinsan ina san Habibi, karki cutar da zuciya ta da babu komai acikin ta sai alkhairi, soyayya da kyautatawa, ban san kiyayya ba Zaliha, ke da Munnirah ɗaya ku ke a waje na, bani da Aminai sama da ku." Zaliha ta ɗaga mata hannu "Ke dan Allah tsaya kar ki ɓata min rai, wannan munafukar wadda ta tsaya min a wuya, ba dan ita ba da tuni ma ba a zo nan ba, da tuni na shafe babinki Khadija, akwai yar iska irin Munnirah Algunguma na dade ina neman dama akan ki shegiyar ta kafa ta tsare kamar uwar ki, duk abinda tace miki shi kike yi, sai yanzu Allah ya kawo silar da ta tafi ta bar ki, Khadijah nafa san duk shawarwarin dana ke baki ita ce take ɓata min aiki, haka kuke wani cewa juna my sis, itama tace miki my sis, kun ware ni a gefe ga matsiyaciya ko? ko kin taɓa kirana da wani suna bayan Zaliha? Munnirah ta sha daƙile ni tsinanniya sai ga shi ta kira ni tana kuka Mamanta bata da lafiya zata yi tafiya, to bari na faɗa miki ba ƙaramin daɗin labarin tafiyar tata naji ba, dan nasan yanzu ne zan iya yin maganin ki cikin sauƙi, Allah yasa daga can uwar ta mutu, Annamimiyah" A wannan lokacin Khadija komai kwance mata yayi, sai ta buɗe ido ta rufe, daga kwancen da take cike da fata tace "Allah yasa duka wannan mafarki nake yi" "buɗe idon ki da kyau ba mafarki ba ne" Zaliha ta ƙaraso gaban Khadija dai dai saitin fuskar ta, ta daga hannu ta shafa fuskar tace "wannan kyakkyawar fuskar taki na riga nayi mata illah Khadijah, ba ita yake gani ba yanzu, koda yake babu amfanin yi miki wani dogon bayani, ki gafarce ni na kamu da son abinda yake mallakin ki ko?" Zaliha tayi maganar cikin izgilanci. Khadijah ta ƙura mata ido "mamaki kike yi ne? zaliha ta tambaya. dai dai lokacin kuma ya fito daga ɗaki hannunsa riƙe da farar takarda ya nufo su jikin shi a sanyaye, fuskar shi ba wani karsashi, kana ganin sa kasan yana cikin tashin hankalin dashi kansa bai san kona meye ba, amma kuma ba zai iya tsallake umarnin da zuciyar shi take basa ba. Da sauri Zaliha ta tare shi ta karɓi takardar ta buɗe ta karanta, sai ta ɗago ta kalle shi tace "Amma D ay daka cike mata ukun kawai" sai kuma tayi murmushi ta linke takardar ta nufi Khadija dake yashe akan tilas ta buɗe hannunta ta saka mata takardar tace "Allah ya raka taki gona" ta faɗa tana sakin murmushin jin daɗi. Readers hope kun dan ji dadin first Episode din nan? We want lots of comments and reactions.....! 💫 UMAYMAH 💫 ✍️A&A PEN FOLLOW OUR WHATSAPP GROUP VIA THIS LINK https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3 https://wa.me/+2348064789370 VOLUME ONE EPISODE 0️⃣2️⃣ Mutane ne ke ta kaiwa da kawowa tako ina, ana ta hada-hadar kasuwanci kamar ba dare ba, yawanci mutanen Takari ne mostly Hausawa ne, bare-bare, ƴan Niger, Yara bawa da ƴan Ghana, masu siyar da abinci da sauran kayayyaki irin su dogayen riguna, takalma, hijabai turaruka da kayan wasan yara, duba da lokaci ne na Zahama kamar yadda suke cewa, lokaci ne na Azumin watan Ramadan. Wata mace ce da zuwan ta kenan ta durƙusa tana baza kayan siyarwa ta, kayan ba wasu masu yawa ba ne kwalli, miski, carbi, turarukan miski, sai kayan wasan yara, "Magajiya yau kin makara" cewar wata mata a kusa da inda tayi shimfiɗar, wacce aka kira da Magajiya na girgiza kai tace "kedai bari Asabe jiya ba mu rintsa ba Asjar ne suka shigo Shara shittin, sun yi kame an tafi da su Talatu abun dai babu dadi, nima a banɗaki na kwana, Allah dai yayi ba a kama ni ba, yanzu gidan mu sai mu uku, Jimmai ita ta tafi gidan aiki kinsan kwana take yi acan dawowarta gidan namu ba koda yaushe ba yawanci ma sai ƙarshen wata take zuwa." "Nawa ne miski?" Wata mata ta katse musu hirar tasu da tambayar kuɗin miski. Magajiya tace "Ashara riyal (riyal goma)" matar ta ɗakko kuɗin ta miƙa mata ta karɓi miskin tayi gaba. Wajen da suka baje hajjar ta su land premier ne, yawanci duk wanda ya taɓa zuwa Umara ko aikin Hajji ya san wajen, saboda duk abincin da ka ke so namu na gida akwai sa a wajen, kama daga kan tuwon shinkafa, semo, Ɗanwake, kosai tsire da sauransu duka zaka samu a wajan, dan haka wajan ya tara mutane sosai kamar dai kana bakin asibitin jahar Kano (Kurmi). Matar na tafiya suka ci gaba da hirar su. "Wannan wahala Allah dai ya kawo mana ƙarshen ta, ni na bawa agent kuɗi zai sama min aiki a gidan Larabawa ko na samu nutsuwa na huta da guje-gujen nan, amma har yanzu shiru kakeji abin ya ci tura" cewar Asabe, Magajiya saida ta numfasa kafin ta yi magana "Allah na tuba idan ba ƙaddara bama me zai kawo ka wannnan Rayuwa ai sai dai kazo da ziyara, ni ɗin nan da kike gani shekara tara data wuce, a shekarun baya da suka shuɗe babu abin da na sani sai dai na saka biyar na tsoma goma, ni na taɓa tunanin zan shiga wanna rayuwar ma, koda yake daɗin da naji na lokaci ne ƙanƙani komai ya canja, nan ɗin ma da taimakon wata Aminiyata tayi min hanya na zo nan da sunan neman kuɗi, ga shi nan babu abinda na tarar sai wahala baƙa ƙirin." Sunata firarsu sauran Mutane kuma suna ta sabgogin gaban su wata mata ta kurma ihun Baladiya, zo ki gaa gudu ko wacce ta tattare kayanta ta saɓa a kafaɗa ta kwasa da gudun neman tsira. Magajiya da Asabe kafin kace meye wannan suka tattare kayan su cikin hanzari suka faɗa cikin hotel din land premier, ta ƙofar baya suka fita ta main entrance ɗin Hotel ɗin, suna ta zuba sauri da kullikan kayan. Wannan ita ce rayuwar duk wasu ƴan kashi a wannan wajen, duk yadda suka kai ga harkokin kasuwancin su suna ankare da ko wanne irin motsi a shirye suke zama yadda ana ƙwala ihun Baladiya kafin kace kwabo zaka neme su ka rasa da kayan su. Duk wanda ya san ƴan kashi a Makka ya sansu da baƙin naci, Hukumomin ƙasar ta SAUDIA babu yadda ba suyi dasu akan su dena kashin kayan siyarwa a wajan ba, amma sam sunƙi ji Saboda kuɗin da suke samu a wajan, dan haka hukumomin ƙasar ta SAUDIA kusan kullum cikin kaɗa su suke babu ɗaga ƙafa, wanda ya gudu ya tsira wanda suka kama kuma duk magiyar da zakiyi bazasu sake kiba, haka zaka ga an kama mace tana kuka tana magiyar Askar ( jami'in tsaro) ya sake ta, amma ko ta kanta bazasu biba, haka zasu tafi da ita a wulaƙance, amma duk da haka wannan baya hana ƴan kashi sake fitowa harkokin su gobe. Da sauri suka shiga cikin gidan su, suna sauke kaya "har kin dawo Magajiya yau da wuri haka" Jimmai ta tambaya, da ke ita kaɗai suka tarar a gidan itan ma bata jima da zuwa ba Magajiya tace "hmm bari kedai Jummai masu kame ne suka je wajenmu shine nace Asabe ta zo nan kafin a jima ta tafi" Jummai tace "tofa Allah ya ƙara kiyaye wa tinda kun tsira" Tsakar gidan bata da wani girma be fi taci tabarma ƙarama guda ɗaya ba, sai ɗakuna biyu a jere da banɗaki daga hannun hagu, kitchen yana kallon ɗakin kwanan su, ɗakin Magajiya kaya ne jibge a daddaure himili guda a wani farin kakkauran yadi da yawanci ƴan zaman saudia suke ɗaure kaya da shi, ɗakin akwai AC, a gefe ga keken ɗinkin nan da ƙulli-ƙullin kaya kamar ƴan gudun hijirah. "Asabe bari na sama mana abincin sahur a gidan hajiya hauwa" Magajiya ta faɗa tana yunƙurawa zata tashi wayar ta ta yi ƙara, ta buɗe ta dauka tana cewa "ah ah Aminiyata, wallahi ɗazu nake maganar ki, ta ɗanyi shiru tana saurarar abinda ake cewa a wayar "toh tih yaushe? Ewa, Ewa, Ewa." ta amsa, sun yi kamar minti biyar suna wayar sannan ta katse wayar ta kalli Asabe da murmushi a fuskar ta tace "kin ji Aminiyata Suwaiba

Chapter 1 of 29