yana ɓata fuska kamar zai yi kuka, sai taganta kamar shine a gaban ta.
"Ammina dan Allah fa nace" Umaimah ta katse mata tunani, Khadijah tayi ƙwafa tace "muje badan halin kiba kuma na fasa siyan tablet ɗin."
Har office ɗin Principal Umaimah ta raka ta, bayan sun gaisa.
Principal ta kalli Khadijah tace "jiya sun zo da Uncle ɗin ta, nace tazo da babba kamar babanta haka ba Uncles ɗin taba ko Aunty."
Khadijah tayi murmushi dan ta gane abinda Principal ɗin take nufi, wato ance tazo da babba sai kuma ta kawo Auntyn ta. Khadijah cikin nutsuwa tace
"sorry Mah I'm not her Aunty, I'm her biological mother." Principle ta sake gyara zaman eyesglass ɗin idon ta tace "if i understand you very well, you mean Fatima Tahir Al-arabey is your daughter right?" Khadija ta ɗaga mata kai alamar tabbatar wa.
"Wow!"
Saida Khadijah ta kashe cases ɗin Umaimah sannan ta fito ta tafi.
*****
Yau Friday wanda yayi daidai da satin Tahir biyu ke nan da zuwa Nigeria, still yau ma a Masallacin Da'awa yayi Sallar jumma'a, amma yau ma haka ya gama dube duben sa baiga kowa daya danganci Khadijah ba.
Jikinsa a sanyaye ya kira Bolt (mai motar haya irin wanda ake kiransu ta Application) yace ya kaishi Bank, gobe zai koma Lebanon yanason ya gyara bankin sa na Nigeria, kasan cewar ya kwana biyu bai yi amfani da shi ba, ga kuma manya kuɗaɗe aciki sai suka rufe bankin, dole sai yaje bankin yayi wasu cike cike kafin a buɗe masa bankin.
Directly mai motar ya kaisa GT Bank dake kan MM way. Yana shiga cikin bankin ya samu customers care yayi musu bayanin abinda ya kawo sa, a daidai lokacin ne kuma Aliyu ke sakko wa daga sama, kamar wanda aka cewa ya juya, ida nunshi suka sauka akan Tahir dake zaune yana cike Form, Aliyu ya sake buɗe idanunshi da kyau yaga tabbas fa Tahir ne yake gani a Nigeria, a Nigeria ɗin ma a cikin bankin su. Da sauri ya juya ya koma sama ya shige office ɗin shi ya rufe.
Ƙarfe 4 da 30 Aliyu ya shigo cikin gidan direct falon Umma ya nufa. Umma na ganinsa tace "a'a Babangida yanzu ka dawo ke nan?.
"Umma barka da diga. Aliyu ya gaida Umma fuskar nan a tsume, yace "Umma yaran nan sun gama exams ko?"
"Eh su Amira sun gama nasu tin jiya yau kuma suka yi hutu, Hakimi ne dai bai gama ba."
"Na siya musu ticket gobe za su tafi Lagos, already na yiwa Daddy magana." Umma tace "Babangida ka shigo a tsume kana magana bana gane wa, su waye zasu Lagos ɗin gobe shine ban gane ba?"
"Umma su Amira ne za su." Umma ta riƙe baki tace "amma Babangida wacce irin tafiya ce haka babu shiri? Kuma su kaɗai ne zasu yi tafiyar daga nan har Lagos?"
Aliyu yace "Umma ki kwantar da hankalin ki, basu kaɗai zasu tafi ba, na yiwa Ibrahim magana shi zai kai su goben saiya juyo. Aliyu na gama faɗar haka ya fita daga falon yabar Umma da mitar wannan wacce irin tafiya ce rana tsaka babu shiri.
💫 UMAYMAH 💫
✍️A&A PEN
Follow our Whatsapp group via this link https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3
https://wa.me/+2348039352724
VOLUME ONE
EPISODE 2️⃣8️⃣
Wanne irin lagos kuma ana zaune ƙalau, ya ƙi tsayawa yayi min bayani kamar uban mutane, to babu inda zasu, Umma keta mita tin bayan fitar Uncle Aliyu.
wayarta tayi ringing, tana dubawa taga Baba ne, Umma ta ɗaga wayar da sallama.
"wa alaikumussalam wa rahmatullah Umman khadija kuna lafiya? Baba ya faɗa daga ɗaya bangaren.
"lafiya ƙalau Baban Khadijah, ni kaɗai dai yanzu nake ta mita." Baba yace "keda waye?
"ni da Babangida mana, haka kawai rana tsaka ya tashi tafiya gobe goben nan wai su Umaimah su tafi Lagos, haka ake tafiya babu shiri, babu sanarwa, sai yayi tayin abu babu shawara kamar shi ya haifi mutane."
Baba yayi murmushi har tana iya juyo sautin sa sannan yace
"Ayi masa haƙuri Siyama, ɗazu ya kira ni yace zai siya musu ticket zasu hutu Lagos, menene abun damuwa, yau su ka fara zuwa hutu Lagos? Umma ta katse Baba da cewa
"Ba haka ba ne, ya zai zartar da hukunci kamar shi ne uban mutane. ina zaune cikin gidan nan ban sani ba sai yanzu?za su yi tafiya ai sai ya fada da wuri ko?.
"Toh yayi kuskure ayi mishi afuwa, zan mishi magana, mun dauki gyaran." Baba ya faɗa.
Umma tayi ajiyar zuciya tace "shikenan"
"Yawwa Siyama ta, ko dai akwai wani abu bayan wannan? Baba ya tambaya. Umma tace "rigimar Umaimah ce abin ji, dan jiya ta yi min maganar zata din ga bin Amminta shago, tana so ta fara koyon dinki, na kuma amsa mata.
Baba yayi dariya "eh ke ma ki na da hanzarin ki, Umaimah yar kasuwa, kuma hakan yana da kyau su yi engaging kan su da skills, yanzu ka gama karatu babu aiki. Gwamnati ba ta da vacancy na ɗaukan ma'aikata, amma da skills ɗin sai kiga koya ya rike kan shi, kar ki damu da Umaimah. Ni na kira na ji muryar Giwa ta kin tsare ni da maganar yan hutu. ko dai har kin fara missing kishiyar ne? Umma tayi murmushi "Umaimah ke nan."
Umaimah da ƴan Friday partyn tane suke ta iface iface, Umaimah ta riƙe tray babba ta ɗora plates akai tana rabawa yara abinci, Amira nabinta a baya tana raba musu bobo, Mama Rabi kuma daga gefe tana bawa wasu a baki kar su bata kayansu.
Umaimah tace "toh maza ku ƙarasa cin abincin, waye be samu ba? Ikram tace "Ni Aunty Umaimah."
Amira tace "ke dai acici ce, wannan na gaban ki wa ya ci? Ikram ta fara raba idon rashin gaskiya, "kyale Amira zo ki karɓa, ina zuwa ta fita. Umaimah ta faɗa tana miƙa mata wani,
Wani yaro ne ya hau kan table ya Dirgo, da ke akwai tables da kujeran roba a garden ɗin, sauran yaran ma suka fara hawa, sun mayar da abin wasa, Amira na ta tsawatar musu, amma ina wasan su kawai sukeyi. "kai wlh na gaji, Baba Rabi lokaci ma ya kusa ko? Amira ta faɗa tana kallon Baba Rabi.
"eh yayi, amma bari uwarɗakina (Umaimah) ta zo ta sallame su da kanta." Amira tace "to kuwa ni zan shiga gida nagaji ku ƙarasa, don Umma ta ce na taya ta ne, amma wlh duk jumaa da ciwon kai na ke kwanciya saboda hayaniyar su. Baba rabi ta murmusa tace "ina ruwan uwarɗakina, ita ta saba da kwarabniyar yara. subnallahi Baba Rabi ta miƙe da sauri. Isi ce da Ikram aka kaure da faɗa. "ya ya, me ya faru? Baba Rabi ta tambaye su.
"bobo na ta ɗauka min." "yi haƙuri ungo wani. "ni wlh nawa nake so." Ana haka Umaimah ta dawo, ta ga duk sun hargitse sai hawa table ake ana dirgowa, ta tsaya tana kallon su tana murmushi cikin jin daɗi tace
"if you are happy and you know clap your hands." sai duka suka ɗauki tafi, ji kake raf! raf! raf!!!
"if you are happy and you say hurray.
"hurray" suka faɗa da karfi.
"if you happy and you know and you really want show if you are and you know"
Umma ce ta shigo wajan ta katse Umaimah da cewa
"ya isa haka magariba ta ƙarato."
"haba Siyama ana nishaɗi zaki yi min haka, wancan satin fah kinsan abun da ya faru." Umaimah ta faɗa tana ɓata fuska.
Umma tace "toh yanzu dai za'a tashi? ko kuwa?" Umaimah tace "Siyama kin isa dole a tashi. Sai kuma ta kalli yaran
"Maman babangida tace a tashi. Umma ta kama baki "Au haka kika ce? shikenan zan faɗa mishi ne."
"toh yara kowa ya sha bobo? Khalifa ya ce "a'a." Umaimah sai cewa ta yi "Allah ya tsine uwar mai ƙarya."
Umma ta harare ta "baa na son Allah ya tsine uwar me ƙaryar nan da kike fada. Amminki bata san hawa ba bata san sauka ba a dinga tsinewa uwar me ƙarya."
"Siyama uwar me ƙarya fah nace." Umma ta ce "akwai wanda ya kai ki ƙarya ne?
Ta sha kunu "toh yara sai Allah ya kaimu next week." Umma a ranta tace next week ɗin ma ba kya nan.
Baba Rabi ta miƙe ta tattare plates, Amira ta tattara musu su dankwalayen su da suka zubar. Umaimah ta rinƙa saka musu takalman su.
Da daddare bayan an gama dinner Ibrahim yana danna wayar shi ya kalli Aliyu yace "wanne time ne tafiyar? Aliyu ya ɗaga kai ya kalle shi "ka duba na tura maka a mail ɗinka, ka yi printing tickets ɗin. Umma ta sauko daga sama, Aliyu ya gyara mata kujera ta zauna "Umma a yi haƙuri na ga ranki ya baci. Umma tace "to ai kaine Babangida baka tsaya ka yi min bayani ba, kawai ka yanke hukunci kai tsaye kamar uban mu." "Ayi min hak'uri Umma."
"Assalamu alaikum." Khadijah ta fada tana shigowa cikin falon. wa alaikumussalam suka amsa. "Yaya Khadijah aiki yana riƙe ki kwanan nan." Ibrahim ya faɗa yana miƙa mata ruwa, ta karɓa ta balle murfin ta sha kusan Rabi sannan ta ajiye, tace "thank you. Umma sannu da gida."
"Yawwa Yayarsu."
Aliyu ya ce "Amma ki rin ƙa dawowa da wuri, duk inda magriba ta yi, Please make sure ta yi miki a gida." Khadijah ta kalle shi ya ɗauke kai kamar bashi yayi maganar ba. Aliyu da shi ne gaba da ita ƙa'idoji zai gindaya mata, toh amma duk inda Namiji ya ke shi ne shugaba, kuma ta na appreciating effort din shi ko a kan Umaimah, Allah ya sani ta na jin dadi, ta san ko bata nan Aliyu zai cigaba da playing fatherly role akan Umaimah, tuna hakan nasa hankalinta ya kwanta, dan Umaimah sai da jan ido. Khadijah ta ce "toh In sha Allahu za'a kiyaye Yayanmu."
Umma ta yi dariya "lalle kam sai fah Yayan naku, wannan da ƙasa kike da shi za ki sha takunkumi." Khadijah dai murmushi ta ke bata ce komai ba, Ibrahim ya ce "ni wlh sai na gani ma duk kin rame." ta ke murmushin fuskar ta ya bace, jikin Ibrahim ya yi sanyi har ya yi dana sanin yin maganar, Aliyu ya kalli Umma "yaran nan sun shirya kayan su? "Na fara faɗa musu dazu, amma bari na kira Auta ta haɗa musu. Khadijah ta kalle su "ina zasu? Ibrahim ya ce "Lagos."
Khadijah bata sake cewa komai ba ta miƙe "bari na hau sama."
"Ki je ki ɗebi abinci Baba Rabi ta kwashe na nan ta ɗauka an gama." Umma ta faɗa tana kallon Khadijah.
"tea kawai zan sha Umma, bari na watsa ruwa."
"Khadijah ki rinƙa cin abinci, ki sakawa zuciar ki salama dan Allah." Umma tayi maganar jikin ta a sanyaye. Da sauri Khadijah tace "wlh Umma ba na jin yunwa ne, Munnirah yau a shago ta yini ta taho mana da abinci.' Umma tace "shikenan."
*****
Zaune suke a kitchen Umaimah da Amira na soya gullisuwa, Baba Rabi na yanka alawar madara, Isma'il kuma ya dage yana saka Albishir a leda. sun kachame a kitchen ɗin suna ta aiki, Umaimah ta kalli Baba Rabi tace
"A'a Baba Rabi yankan 50 Naira ne fah, wannan da kike yi ai yayi girma da yawa, sai ka ce na 100 Naira." Baba Rabi tayi dariya "uwarɗakina shi yasa nace ki bar min suyar ke kiyi yankan."
"Eh gaskiya zaifi, karɓi suyar bari nayi yankan." Umma ta shigo kitchen ɗin "kina ta wahalar da kan ki ,ina zaki da su?Ke da za ki yi tafiya gobe." Umaimah ta tsaya da yanakan "Siyama wacce irin tafiya kuma dan Allah? meow meow Magen ta tayi kuka, subhanallahi Umma ce ta taka ƙafar Sasi bata sani ba.
"wannan mage da naci take duk inda kike tana nan." Umma ta faɗa tana matsawa baya.
💫 UMAYMAH 💫
✍️A&A PEN
Follow our Whatsapp group via this link https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3
https://wa.me/+2348039352724
VOLUME ONE
EPISODE 2️⃣9️⃣
Umaima wai me yaasa ba'a abun arziki da ke ne? Toh Siyama tsakani da Allah haka muka yi da ke? nace miki zani koyon ɗinki kince to, kuma yanzu ba za ki ci ka alkawari ba." Umaimah ta faɗa. Umma ta dafe kai irin na shiga ukun nan tace
"sau nawa zan faɗa miki ban san da tafiyar ba." Umaimah ta dinga birgima a kan gadon tana borin ita dai bata yarda ba. Umma tayi ƙwafa "tun ɗazu na ke fama da ke, amma kinƙi saurara ta ko? To bari ki gani." Umma ta ɗauki waya ta yi dialing number, Umaimah na ganin haka ta taso da gudu "dan Allah kar ki kira shi. Ita ta ɗauka Uncle Aliyu Umma zata kira, sai kuma ta ji muryar Baba.
"ka yi mata magana akan tafiyar nan. Umaimah ta karɓi wayar, Baba yace "uwata an ya alkawari ya ce haka kuwa gidan Daddyn kine fa?" Ta wani cuna baki kamar Baba yana ganin ta "Baba ba haka ba ne. "toh yaya ne? Sai kuma ta yi shiru. Baba yace "na miki alkawari wani hutun zaki je koyon ɗinkin shi ke nan ko?" Ba haka taso ba amma babu yadda ta iya dole ta amsa da "toh Baba zaka zo? Ina kenan? Umaimah tace "Lagos ɗin.
Baba yayi murmushi yana jinjina rigimar Umaimah, "to zan zo idan na samu lokaci, ko akwai wani abu?" Da murna tace "a'a babu komai.
"toh kar ki da mu Siyama kinji ko." Ta daga masa kai, "to bata wayar." Umaimah ta miƙawa Umma wayar tayi waje.
Umma ta shigo ɗakin su Umaimah tace "Amira kun haɗa kayan? "eh na haɗa Umma, amma na Umaimah wlh akwai masu datti." Umma ta girgiza kai, "Allah ya kyauta, kawo mu gani?" Amira ta ɗebo wa Umma kayan, ta fara buɗewa ta fitar da masu datti.
"Allah ya shiryi Umaimah, ina sababbin kayan da Daddyn ku ya siya muku? Umma ta tambaya. Amira tace "Wanne?
"Wanda Hidaya ta ba ku a Bichi." "yana wajen Yaya Khadijah. "je ki karɓo sai a canja muku da su." gowns ne sai riga da skirt high waist ta haɗa musu har da Abayas
Umaimah keta mitar yanzu ita shi ke nan za'a ja tayi asarar Kasuwar ta. Umma tace "wacce kasuwar kike ta mita akai ne wai? naga dama shago za'a kai miki tinda kunyi hutu ko." Umaimah taba kula Umma ba ta shige ɗakin Uncle Isma, yana kwance ta shigo "Dan Allah Uncle Isma ga shi nan, na bar maka dukiya ta a hannunka, idan ya ƙare Baba Rabi ta taya ka kuyi wani, za mu yi waya dai pls." ta faɗa tana kallon shi sai kace wata babba, yace "Na ji." Toh Allah ya siyar mana. ya ce "Amin pls ki fita bacci zan yi." Umaimah tace "kai Uncle Ismah ko missing ɗina ba za ka yi ba? Bai bi takan zancen taba yace "Kwashe kayanki ki fita." Yayi maganar ransa a ɗan ɓace, ta miƙe tace "me yayi zafi?" sai da safe.
****
Tahir Jirgin safe zai hau, yana ta kokarin meeting up kar ya yi missing flight, dan yaso makara, Allah ya taimake shi safiya ce babu hold up, yana isa airport ɗin direct ya wuce ya karɓi boarding pass, ya samu waje ya zauna kafin a kira su, dan sai ya je Abuja ta can zai hau jirgin Emirate wanda zai wuce dashi Lebanon.
Suna shigowa kafin su zauna Ibrahim ya karɓo musu boarding pass, kafin su ƙaraso inda za su jira, dan jirgin su ya kusa tashi Air peace za su hau. Umaimah ta kalli Ibrahim tace fitsari ta ke ji, Ibrahim kamar ya ma ke ta ya ce da Amira ta ƙarasa wajan zaman ta jira ya raka Umaimah toilet
Amira na zama su ka hada ido da Tahir dake zaune a gefan ta, yayi mata murmushi, ta ce "good morning." yace "morning kanwata." yadda Amira ta kalle shi da mamaki abun saiya sashi murmushi, "kina mamaki nayi Hausa? Amira ta ɗaga kai, yace "matata yar kano ce."
"tana ina? Amira ta tambaya, wani abu ya yaji ya motsa mi shi, ya shafa kai, "neman ta nazo." Amira ta zare ido "neman ta kuma? ya amsa "eh."
Haka kawai Tahir ya ji jinin shi ya haɗu da yarinyar.
"toh ɓata tayi? Yayi murmushi mai ciwo, sannan yace "a'a laifi dai nayi mata, yanzu nake neman ta." Da tausaya wa Amira tace "Allah ya bayyana maka ita.
"Amin." ya faɗa, sai kuma yace "how old are you?
"I'm 13 by February will be 14." ya yi murmushi, da zaman su ya ɗore da Khadija da za su iya haifar kamar wannan. "ba ki faɗa min sunanki ba?
"Fatima, amma ana ce min Amira." Fuskarsa wa dace da fara'a yace "sunan Ummina, nice name ki ba ni digits ɗin ki zan rinƙa gaishe ki." haka kawai ya ji bakin shi ya faɗa. Amira ta buɗe baki da mamaki "ay ba ni da waya, Baba ya hana mu waya sai mun gama secondary school." Tahir ya jinjina kai, "hakan yayi kyau, ke da waye aka hana ku? Kina da sister ne? "Ni da Umaimah."
"Umaimah" ya sake maimaita sunan, ya ce "duka sunan Ummina ne." "ka ce sunanta Fatima?
"Na'am sunan ta Fatima, amma Kakata tana ce mata Umaimah, saboda sunan mahaifiyarta ne, Umaimah (small mother).
Suna ciki hirar aka yi announcing za su ta shi, ya Ciro kuɗi da yawa ya bawa Amira, ta girgiza kai alamar ba zata karɓa ba, baice mata komai ba ya ajiye mata kuɗin kusa da ita, yace "toh Ummina zan tafi Allah yayi miki albarka." Ya miƙe ya bi sahun passengers, sai bayan da ya tafi Amira ta ce wlh suna kama da Umaimah ikon Allah. Kamar jira ake ya tashi, saiga su Umaimah sun dawo.
Amira tace "Yaya Ibrahim ka gani Amira ta nuna mishi kudin? "waya baki? "Wani ne wlh me kama da Umaimah."
Da sauri Umaimah tace "dan Allah? ina ma na gan shi da an yi mana hoto." Ibrahim ya katse Umaimah da cewa
"akan me zai baki kudi?" "cewa yayi sunan Maman shi ne dani shine ya ba ni." A dai faɗi gaskiya. Umaimah ta faɗa. Ba na son wulakanci karya zan mi ki."
Ibrahim yace "shikenan kawo kuɗin." Umaimah tayi caraf tace "Uncle Ibrahim kawai mu raba, rabon mu ne ya tsaga."
Amira ta harare ta, "saiki ƙwata ai." Aka kira su suka shige.
******
Su Umaimah an kwana an hantse a gidan Daddy, Ibrahim yana kaisu yabi yo Jirgin yamma ya juyo Kano. Daddy da Mami suna zaune Umaimah ta fito bakin nan a saba. Daddy yana ganin ta yayi murmushi
"Zo nan ki faɗa min ke da waye? Wa ya taɓa min Amrya ta." daddy ya faɗa yana nuna mata kusa da shi. Umaimah tace "basu Hidaya ba ne wai yau a ƙasa zan yi shinfiɗa, ni kuma na ce wlh ba su isa ba." Daddy ya kalli Mami "kin ji yaran nan ko?" Mami ta ce "kira min su."
Umaimah ta miƙe ta tafi kiran su Amirah, ba a daɗe ba sai ga su sun dawo tare, Daddy ya kalli Hidaya "me ya sa kuka ce uwata ba za ta kwanta a kan gado ba? "wlh Daddy bata iya kwanciya ba, jiya mun sha wahala gaba ɗayan mu ta yi mana duka."
"duka kamar yaya? Daddy ya tambaya. Hidaya tace "toh Daddy haure haure da ƙafa take sai dai ka ji Kafa a ruwan cikinka." Amira ta karɓe da cewa "Daddy dama fa ko a gida da Umma su ke kwanciya, Allah bata iya kwanciya ba, duk jikin ka sai yayi tsami." Daddy yayi murmushi, idon Umaimah ya ciko da ƙwalla "wlh sharri ne Daddy." Mami ta ce "rabu da su, su ƙarata, ki je ɗakina ki yi kwanciyar ki ke kaɗai." Daddy yace "shikenan uwargida ta kawo maslaha, zo nan Amaryata kin ji." Umaimah ta matso kusa da Daddy, "rabu dasu kin ji, kiyi kwanciyar ki ke kaɗai, ki yi birgimarki san ranki." Umaimah ta yi dariya tace "dama jiya da kyar na yi bacci, duk sun dame ni da surutu.
AMERICA
Dr ya kalli Fahad bayan ya gama examine result ɗin shi, ya ce
"Mr Isma'il I changed your medication with Benzodiszepine, this drug will treat anxiety symptoms associated with OCD, and again medication is just one part of OCD treatment, A comprehensive treatment plan should include a combination of medication, and therapy, I assure you, you will get better with therapy, I'm here for you and we ll face this journey together everything will be okay." yayi rubuce rubuce ya miƙa mishi. Da ƙyar Fahad ya motsa babi kamar wanda aka yi wa dole, ya ce "Thank you Dr." ya karɓa ya miƙe ya fita daga
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 15 Chapter of 29