Share this page
Munnirah na idar da sallah ta fara dariya, "kun damar min my sis." "abunda zaki faɗa mata ne mu ke taya ki." Hindu ta faɗa, Umaimah ce ta shigo da sallama suka Amsa "Ammi camera ta zaki bani." ta nuna mata lungun wardrobe, ta shige tana nema. Surayya ta mike "koh tafiya fah sai kin canja. ta fara tahowa daga bakin ƙofa tana cat working, magana ma gaskiya sai kin ƙara yiwa muryarki kwaskwarima duk da dai tana da zaki, ki ƙara jan aji tunda ya taɓa aure dole fah ya ga banbanci ki fah zage." Khadija idonta ya tara ruwa "gaskiya kun dami ƙawata. Anisah ta miƙe ta fara wata karairaya "kin ga irin haka, ban da garaje a yin abubuwa." dariyar Umaimah ce ta katse maganar sun manta tana ɗakin "Au kina nan? fito ki bamu waje ko na ci mutuncin ki." Aunty Amal ta faɗa, ta fito da camera a hannu tana dariya ta yi ƙasa wajen su Daddy, ta tafi da gudu sai ganinta suka yi tana haki "yaya dai Amaryar? Daddy ya faɗa, sai ƙunshe dariya ta ke yi, "hmmm Daddy kasan me? "Sai kin faɗa." "ka ga." sai kawai ta karkace ta fara catworking sai lankwasa ta ke yi. "Toh fah." Baban sama ya faɗa, "kusan wa ake koyawa tafiya? Umaimah ta faɗa, "Ammina Aunty Amal take koyawa wai sai ta dage ta wani make murya magana ma haka aka ce tayi." Baba Dr dasu Daddy dariya kawai su ke yi, Sa'ad tunda abun nan ya faru be yi dariya ba sai yau, shi kuwa Fahad ko ɗago kai be yi ba shi Allah Allah ya ke yi a sallame su wannan Noisy girl ɗin ta zo, sai da suka gama dariya tace "Daddy ku haɗu na yi muku hoton tarihi." Aliyu ya harare ta, ta nutsu ita ta manta yana wajen ma, bata kula ba, "wannan gaskiya ne gaba-daya kakannin suka haɗu ta yi ta ɗaukan su a hoto, "toh kuma ku shigo." ta kalli Sa'ad, yace "ay dole mu shigo." suka shisshiga Fahad da Aliyu ko motsi ba suyi ba sai da Baban sama yace "Dattijo, Zakin ma'aiki ku shigo mana." sannan suka Shigo, ku ce "chess." Umaimah ta faɗa tana dariya, tana gulmar Fahad a ranta dan shi wani wajen yake kallo, "Uncle Isma yayi missing ana yi babu shi." "Sa'ad karɓi ka yi mana da uwata." Baban ABU ya faɗa, ta shiga tsakiyar su aka ɗauke su, Daddy yace ɗauke mu, mu biyu." Sa'ad ya ɗauke su, yace "kai amma yayi kyau." ya nunawa Daddy daya ke camerar digital ce, kai kai wannan enlargement ɗin shi zan yi, duk mun cinye, dukkan su sai da aka yi musu da Umaimah. Khadija ce ta sauko Baba Dr yace "sai ina? "hmm dama shi ya zo, zan karɓi saƙo." ta sunkuyar da kai, Sa'ad daya ke abokin wasa ne sai cewa yayi "yanzu aka gwada mana yarda zaki yi tafiya." Khadija ta kasa motsawa kunya ta rufe ta, Baba Dr yace "to ga yar rakiya nan." ya faɗa yana dariya, har Umaimah ta taho da sauri Daddy ya ce "zo nan ay ba mu gama hoton ba." yana hararar Dr, jeki abinki ta wuce kamar kwai ya fashe mata a ciki, tana fita wasu matasan yamma ta suka Shigo suka gaishe da su Daddy, dayar tace "Fatima Mohammad mu ke nema." Baba yace "tana sama." "ba fa Fatima Tahir ba." Baba yayi murmushi yace "ita dai tana sama." har sun fara hawa steps Umaimah ta fito daga kitchen ta gan su da gudu ta yi wajen su har ta take kafar Fahad wajen sauri ya rintse ido, ita bata ma sani ba, "small clown." ya faɗa a ran shi. ***** Tahir ne yake yiwa Yaseer bayani sun yi magana da Baba Isah ashe shiyasa ba ya samun shi a waya sai ta WhatsApp su ka yi magana baya nan ya je Egypt za a yi mishi aikin mafitsara, amma yace babban dan shi Hamza ya wakilce shi, su je Bichin tare, yayi hakan ma Yasir yace "yaushe ne tafiyar? "Wednesday zamu tafi, mu huta Thursday ranar Friday zamu Bichin, tare da Dr Huzaifi tinda ya zo hutu." "masha Allah, Allah ya kaimu." ****** Gaba-dayan su a zaune su ke a falon Baba bayan sun gama dinner suna taɓa hira, saboda suna da yawa Dinning yayi musu kaɗan Umma ta shinfiɗa musu ledar cin abinci, Daddy yace wa Baba zai bar mishi kula da ginin shi daya ke jikin gidan Baba da be kammala ba, yana so idan ya dawo daga India gidan ya kammala, hakan yayi Baban sama ya faɗa, Sa'ad, Aliyu, Ibrahim Farouk da Fa'iz suna tura bulk message na friends ɗin su da ba a basu card ba, Fahad na zaune yayi zaman cin abinci ya harɗe Kafa, su Surayya, Amal, Hindu da su Munnirah daga wajen Dinning suna ta packaging souvenirs, su Mami kayan gara suke sakawa a kananan bokiti da za a bawa mutane, Khadija na gefe tana jan carbi, jikinta duk a sanyaye, Amira, Hidaya da Isma'il suna ta kallon hotonan da Umaimah ta ɗauka ɗazu. Umaimah tun dazu ta ke ƙunci tambayar duniya taki magana, har Uncle Ismah ya tambaye ta, tace babu komai. ta kalli Daddy tace "Daddy ashe ni shegiya ce? DUMMM Khadija ta ji carbin hannunta ya faɗi ƙasa, wani salati Umma da Mami suka yi, "na shiga uku ni Maryama, waya faɗa miki? Wannan wacce irin magana ce mara daɗin ji? Umma gaba-daya ta ruɗe." "Da Allah nutsu." Daddy yace da Umma, Umaimah ta ƙara maimaita maganar tana kafe Daddy da ido, "waya faɗa miki haka?" Baban sama ya tambaya, "ba ƙawayen Amira ba ne da suka zo ɗazu." salati Mami ta ke yi tana rufe baki, gaba-daya falon yayi shiru har Fahad sai da ya daga kai ya kalli Umaimah da ke hawaye, da wuya ka ga tana kuka, "zo nan Amaryata." Daddy ya miko mata hannu, Amira sai rantsuwa ta ke yi tana zare ido "wlh ni bana nan suka faɗa mata." Baba dai babu bakin magana. "Faɗa min ya aka yi? "ɗazu ƙawayen Amira sun zo naje dakin mu da su, shi ne su ka ce min na cika takama kamar gidan ubana, Abunda ni shegiya ce ba ni da uba lokacin Umma ta yi kiran Amira, na ji haushi shi na fita na bar musu ɗakin." "kina da uba kin ji kar ki damu." "toh yana ina? Ko hoton shi ba a nuna min ba."Baba yayi kass da kan shi, ya tafka kuskure yayi dana sanin kona komai daya danganci Tahir ashe irin wannan ranar zata zo? Aliyu jikin shi har rawa yake yace Amira ta taso su je gidan yan iskan ƙawayen nata ya daka mata tsawa, su Surayya kowa jiki yayai lakwas abun be yi daɗi ba "Dawo ka zauna." Baban ABU ya faɗa, bar su kawai haka za a yi ta yawo da maganar." ya kalli Umaimah yace "kina da Baba yana Lebanon, shi balarabe ne." Tayi murmushi "Dan Allah?" ya gyaɗa mata kai, "ke mai Baba biyu ma ɗaya a Lebanon, ɗaya a india, in ye yar gata, Uncle Ahmad ay kin san shi ko?" ta gyaɗa Kai, "a india ya ke?" Umaima ta tambaya, Daddy yace "eh tare zamu tafi da Ammin taki, ba sai ta manta da zancen bata da uba ba, ta kurma uban ihu, "ba wanda ya faɗa min Ammina zata tafi ta bar ni na tabbata marainiya ba uwa ba uba wayyo Allah na." duk ta rikita su da kyar Sa'ad ya ja ta waje yace ta zo ta ji wata magana tana hadiyar zuciya ta bi shi, Khadijah da dama daurewa take yi kar tayi kuka, ta tashi ta hau sama da gudu. Fahad ne ya bi ta da ruwa mai sanyi a hannun shi da cup, yayi knocking ya shiga, ya tarar da ita tana rusa kuka ya zuba mata ta karɓa ta sha ya miƙa mata hanky mai kyau ya zauna kusa da ita yace "pls stop crying I'm sure everything will be fine. Its okay, it's okay, it's okay." yayi ta maimaita wa, tana ta ajiyar zuciya, sai da ta nutsu tace mishi "thank you." Fahad sai da ya tabbatar ta samu relief ya baro ɗakin. ***** Tahir ne ya ke ta azalzalar su Yaseer da Dr Huzaifa, su yi sauri kar su makara, so yake su yi sallar juma'a a Bichi, Dr Huzaifa yana ta yi masa tsiya shi dai yau zai ga wannan Khadija, Hamza ya kira wayar Tahir ya ce yana waje su fito ya taho da Ummi dayake ita a gidan Baba Isah ta sauka, su kuma sun sauka a hotel, Ummi tana gaba,Tahir, Dr Huzaifa da Yasir suna baya. Sun iso Kofar fada a ciki yake da bil Adama, Hamza yace ko sallar juma'a aka yi ne kamar an idar ma ya tambayi wani mutum yace an idar daurin aure za a yi, suka fito daga motar, Hamza yace ummi ta zauna a mota tukun, suka ji an fara siga a loudspeaker ta cika wajen "an daura auren Isma'il Ibrahim Bichi da Amaryar shi Aysha Bello akan sadaki 200k, sai Auren Ahmad Bashir Lamiɗo da Amaryar shi Khadija Muhammad Bichi akan sadaki 500k lakadan ba ajalan ba,Tahir daya dauko sallaya a mota ta faɗi daga hannun shi duk suka zuba mishi ido, Ibrahim ne cikin turmutsutsun mutane ya fito zai shigo da abokan shi kamar wanda wuta ta ja Tahir yana ganin shi ya zabura ya karasa wajen shi, "da gaske khadija aka daura wa aure? Ibrahim da mamakin ganin shi ya ke yi ya mika mishi hannu Tahir mutumin shi ne yace "eh Yaya Khadija ce wayar hannun Ibrahim ta yi ƙara ya ce "bari na shigo da baƙi na dawo" Ay nan ya sanƙame ya faɗi, hankali tashe Dr Huzaifa suka mayar da shi mota, Ummi tana ta tambayar lafiya, ba wanda yayi magana, Hamza ya figi mota don su shiga cikin gari da wuri su nemi Asibiti. An shirya khadija a green lafaya tana ta kuka, Umaimah ta rungume ta za su tafi airport, Mami keta bata haƙuri "ay muna tare baki da matsala, kin ji daughter." Munnirah tana ta goge mata hawaye da tissue, Aysha ma an kawo ta nan gidan Baba su sai gobe za su tafi ita da Fahad, Amira kuka, Umaima kuka, Munnirah ce take ce mata "ba gani ba." tana ta faman rarrashin ta, Umma ma sai kuka haka dai aka rabu ana ta koKe koke jikin Umaimah yayi zafi, zazzaɓi ya rufe ta Uncle Isma ne da Sa'ad suka kaita Asibiti da wannan damar Amarya Khadijah aka raka ta airport tare da Angonta sai Daddy da Mami, an bar Hidaya tare da Amal saboda makaranta sai dai mu ce Amare da Angwaye Allah ya bada zaman lafiya. Gammmmm! Gammmmm!!! Hellooooooo my beautiful readers nace akwai magana fa! Umaimah da Fahad na kira a VOLUME TWO in sha Allah. Ni kaina na matsu naga yadda za'a tsinke wannan fure tsakanin Umaimah da Fahad! Alhamdulillah Anan na kawo karshen VOLUME ONE sai Allah ya haɗa mu a VOLUME TWO kuma na karshe in sha Allah. Special Thanks to you A&A'S UNIVERSE, thanks for your support i really appreciate it. STORY BY A&A An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 29 of 29