Khadijah, da kuma faɗa mata da yayi yana sonta zai Aure ta.
Baba ya cika da mamaki dan shi dai yasan Khadijah bata kula Samari, sannan bashi da labarin Khadijah tanabin ƙawarta Zaliha Company.
Baba ya girgiza kai cike da mamaki. Directly ya yiwa Tahir bayanin Khadijah karatu takeyi dan ko secondary school bata gama ba, kuma su basa aurar da yaran su sai sunyi karatu mai tsayi. Dan haka yayi hakuri.
Ko kaɗan Tahir baiji daɗin bayanin Baba ba har fuskarsa saida ta nuna haka, dan harga Allah yake san Khadijah baya jin kuma zai iya hakura da ita.
Haka suka yi sallama da Baba ranar jikinsa duka a sanyaye ya tafi, amma a cikin ransa ya ƙudurce wa kansa dole zai dawo ba zai iya hakura da ita ba.
Baba yana shiga gida ya rufe Umma da faɗan yaushe aka fara barin Khadijah kula Samari bada sanin saba, kuma yaushe ta fara zuwa Company bashi da labari.
Umma tayi sak tana saurarar Baba dan duka cikin maganar tasa babu wacce ta san inda ta nufa. Saida Baba ya gama faɗan sa tas, sannan Umma tayi masa bayanin abunda ta sani.
Aliyu na gida lokacin yana hutu Baba ya kalle sa, yace
"Babangida maza kirawo min Yayar ku a ɗakin ta.
Khadijah na zuwa Baba ya hauta da faɗa babu sararawa dan ransa ba ƙaramin ɓaci yayi ba, a take ya hanata zuwa gidan su Zaliha, yace bai hana su ƙawancen suba, amma daga yau koda wasa karya sake ji taje gidan su Zaliha.
Aliyu najin haka yace "Alhamdulillah daman wallahi ni Baba bana so tana mu'amala da yarinyar nan, sam bata da kamun kai, ina yawan ganin ta a wajan su Mudan mai shago tanayi musu dariya yadda kasan ba mace ba, wallahi Baba haka zaka ganta a majalissar su Mudan suyi ta janta da zance tana biye musu.
Umma tayi sauri ta katse shi da cewa
"Ina ruwan ka Babangida kai fa in kaƙi mutum kuma shi ke nan an shi ga tara."
Baba yace "a'a gaskiya ce Azumi bari zanyi mata magana itama ai ƴata ce, ina amfani ace mace na sakarwa maza baki, kuma Ni nafi ganin lefin Khadijah da ba tace zata bita ba zata jata ne, kin dai ji na faɗa miki daga yau babu ke babu shi."
Jikin Khadijah a sanyaye ta tashi ta koma ɗaki, ranar ko abincin dare bata iya ciba saboda damuwa, da gaske take son Tahir.
Munnirah da taji labarin Baba ya hana Khadijah zuwa gidan su Zaliha abun ba ƙaramin daɗi yayi mata ba, Khadija har saida taji haushin ta.
Kwana biyu a tsakani saiga Tahir da Aminin Baban sa Baba Isah sunzo gidan su. Cikin ikon Allah suka iske Baba yana gida. Baba har cikin Falo ya shigo da su. Bayan sun gaisa Baba Isah ya yiwa Baba bayanin shi sunan shi Alhaji Isah kuma shi Aminin Baban Tahir ne tin yana raye.
Anan Baba Isah ya yiwa Baba bayanin abinda ke tafe dashi, na ganin Khadijah da Tahir yayi yana santa zai kuma Aure ta in sun amince masa.
Baba yayi shiru cikin tunanin yadda zaiyi ya rabu dasu Baba Isah. Dan mutumin nada nutsuwa da kamala ba yaso ace ya faɗa musu wani abu mara daɗi.
Baba ya numfasa a mutumce yace wa Baba Isah
"Alhaji kuyi hakuri magana ta gaskiya bama aurar da yaran mu sai sun gama karatu, kuma ita Khadijah kaga ko secondary bata gama ba sai wannan shekarar zata gama in sha Allahu. Dan haka ina mai godiya tare da baku hakuri akan wannan lamari.
Da sauri Tahir muryarsa kamar zaisa kuka yace wa Baba
"Nayi Alkawarin zan barta tayi karatunta har zuwa inda kuke so, nidai na roƙe ku saboda Allah ku bani Auran Khadijah, ina santa sosai zan kula da ita, sannan nayi magana da Ummina da kuma ɗan uwana duka suna santa sun kuma amince mini na aure ta, zamu kula da ita sosai dan Allah karka hanani Auran ta.
Baba yayi shiru yana kallon Tahir cike da mamakin maganganun sa, koda yake babu mamaki wannan shi ne bambanci mai girma dake tsakanin ƙabilar Mallam Bahaushe da sauran ƙabilu, inba haka ba babu yadda za'ayi ace wanda ke neman Auran ƴar ka ya zauna a gaban ka yana faɗa maka haka. Koda yake a ƙabilar Balarabe wannan ba ko mai bane.
Maganar Baba Isah ce ta dawo da Baba daga tunanin daya tafi.
"Alhaji Muhammad a duba mana saboda Allah, inada tabbaci akan ahlin Tahir mutanen kirki ne, na tabbata zasu riƙe muku ƴarku Amana. Baba Isah ya faɗa da sigar riƙo.
Gaba ɗaya sai suka saka Baba a tsakiya Baba Isah na ajiye zance Tahir zai ɗora. Baba ya rasa yadda zai yi dasu.
Daga ƙarshe dai Baba yace musu suyi hakuri su bashi lokaci zaije ya faɗa wa iyayen shi, tinda sune gaba dashi duk abin da suka ce zai sanar da su.
Tahir zai sake magana Baba Isah ya dakatar dashi, suka yiwa Baba godiya, sannan suka yi sallama da Baba bayan Baba Isah ya karɓi number wayar Baba akan saiya jisa.
Tahir sai wai waye yake a cikin Falon ko zaiga Khadijah, amma har suka tafi bai ganta ba.
*****
💫 UMAYMAH 💫
✍️A&A PEN
FOLLOW OUR WHATSAPP GROUP VIA THIS LINKhttps://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3
https://wa.me/+2348039352724
VOLUME ONE
EPISODE 3️⃣6️⃣
Baba na dawowa daga raka su Tahir ya wuce ɗaki, ya samu Umma tana gyara kayan sawar sa asif. A bakin gado ya zauna yana sauke ajiyar zuciya. Umma ta rufe sif ɗin tazo kusa dashi ta zauna.
Cikin alhini Baba ya yiwa Umma baya nin duk abinda ya faru, Umma tayi shiru tana tunani, can kuma tace
"Ikon Allah, abun har ya kai haka? Amma yanzu ya kake ganin za'ayi?"
Baba yaja ajiyar zuciya "magana ta gaskiya bana son yiwa Khadijah Aure yanzu kindai san familyn mu ba'a haka. Sannan Yaron nan ba Bahaushe bane al'adun mu da tsarin rayuwar mu duka ba iri ɗaya bane. Amma dai kamar yadda nace musun zanje na samu Babancikin gida na faɗa masa sai naji abinda zai ce."
Umma tace to hakan yayi, Allah ya zaɓa mana alkhairin sa."
Cikin kwanakin nan Khadijah gaba ɗaya ta canja har wata ƴar rama tayi saboda damuwa. Sauda dama tana tambayar kanta dama wai ana haka, lokaci ɗaya ka fara san mutum irin wannan? Harka kasa samun nutsuwa.
Umma ta kula da rashin walwalar Khadija da yadda ta rame komai sukuku take yinsa, Umma ta kasa hakuri ta ritsa Khadija ta tambaye ta me yake damun ta, Khadijah ta kasa bawa Umma amsa guda ɗaya sai kame kame.
To me zata ce, kawai sai tace san Tahir ne da tunanin sa ya hanata sakewa, ina bazata iyaba, banda abun zuciya ma duka duka yaushe ta sanshi.
Haka Umma ta gaji da tambayar Khadijah tasa mata ido saidai tana yawan kula da duk abinda take yi.
Duk wannan abun da ake yi Zaliha bata da labari, tana zuwa gidan su Khadijah, har lokacin babu abinda ya canja, amma babu wani abu daya danganci Ogan su data gani, saboda Baba ya riga ya hanasa zuwa yace ya jirasa tu kunna. Ita kuma Khadijah bata taɓa bata labarin halinda suke ciki da Tahir ba.
Munnirah kuwa dama ba'a maganar ta dan har yanzu basa shiri da Zaliha rashin jituwar su saima abinda ya ƙaru.
Ranar jumma'a Baba ya tafi Bichi da wuri, ya ɗan yi zaman faɗa har lokacin Sallar jumma'a yayi suka tafi masallacin dake nan jikin gidan Hakimi.
Bayan sun idar da Sallah suka samu zama shida Babancikin gida anan ne Baba yake yi masa bayanin abinda ya kawo sa, ga mamakin Baba sai yaga Hakimi yayi na'am da abun, sai cewa da yayi
"Madallah Magaji indai mutumin kirki ne kuma ita Khadijan tana sanshi ai sai a bashi, babu wata damuwa a tare da hakan, shi Aure ai babu inda baya kai mace. Yanzu inka koma saika turo min ita Khadijar ka kuma bani number shi Alhaji Isah.
Baba jikin sa yayi sanyi yama rasa abinda zai faɗa wa Hakimi, harga Allah shi ya cewa su Baba Isah su bari ya faɗa wa na gaba da shi ne saboda ya samu ya kufce musu, ko kaɗan bai taɓa kawo wa ransa Hakimi zai yi na'am da wannan zancen ba.
Hakimi da kansa ya yiwa Dada bayanin abinda ke tafe da Baba, Dada ta tsaya daga ƙoƙarin haɗa wa Hakimi furar da take yi, ta kallesa tace
"Mai gida wani zance kake haka ban gane maka ba?"
Hakimi ya sake gyara zama ya yi mata duk bayanin da Baba yayi masa.
Ai Dada sai tahau faɗa da kumfar bakin ita bata cikin wannan lamari, yaushe za'a ɗauki yarinya ƙarama kamar Khadija a bawa wani can baƙon haure da basu san asalin saba. To wallahi babu hannunta.
Hakimi bai cewa Dada komai ba saida tayi faɗan ta san ranta, sannan yace mata. Bafa auren aka ce an bashi ba cewa yayi a turo masa Khadija yaji daga bakin ta, sannan shi ma Yaron zai kira sa ya zo.
Ina hakan ma bai yiwa Dada ba dan ita a faɗin ta bata ga amfanin kiran nasu ba, kawai ace masa yayi hakuri, yaje ya nemi ƴar ƙabilar su ya aura.
Hakimi ganin Dada bazata fahimce saba kawai saiya rabu da ita.
Kafin Baba ya baro Bichi Saida Dada ta sake yi masa kashedin babu Khadija babu wani baƙon haure ita dai bata amince ba.
Baba ya baro Bichi jikin sa a sanyaye ya shigo gida.
Da daddare bayan sun kwanta Baba ya yiwa Umma bayanin yadda sukayi da Babancikin gida ita ma tayi mamaki, amma haka sukabi lamarin da addu'a.
Baba ya kira Daddyn Lagos washegari yayi masa bayanin abinda yake faruwa da yadda suka yi da Hakimi, budar bakin Daddy sai cewa yayi
"Masha Allah, Allah yasa mutumin kirki ne Muhammad, ni wannan Auren na sai an gama degree ba wani goyon bayan sa nake ba, kaga su Surayya nan kullum cikin faɗa musu nake duk wacce ta samu Miji ta kawo min shi."
Kawai sai Baba yayi loosing confidence, dama ya kira Daddy ne saboda ya goya masa baya wannan magana a barta, dan ɗazu da safe Alhaji Isah ya kirasa yace Babancikin gida ya kira su yace suje ranar Asabar, to shima kuma Daddyn da yake sa ran zai goya masa baya ga abinda yace.
A haka sukayi Sallama da Daddy yace masa shima zai shigo Kano next week.
Tsawan kwanakin nan Khadijah bata da wata cikakkiyar walwala, komai yinsa take wani iri kamar mara lafiya abun har ya fara damun Umma.
*****
Ranar Jumma'a Baba ya tura Khadija Bichi kamar yadda Hakimi ya buƙata.
Khadijah ta isa Bichi lafiya ta samu kyakkyawar tarba daga Dada, kamar zata maida ta ciki, komai ta rarumo tace gashi Hadiza.
Bayan Khadija ta huta Dada ta sata agaba da tambayar maiya sameta taga ta rame kuma tayi sanyi haka. Duk da Khadija ta cewa Dada babu komai saida Dada tayi mata faɗa akan maganar Tahir, sannan ta ja mata kunne akan karta yarda ta auri wanda bata sani ba bata san danginsa da ƙasar suba, kuma ba Bahaushe ba.
Dada bayanin ta kawai takeyi amma Khadija ba wani fahimtar abinda take faɗa take ba.
Da daddare Babancikin gida ya zaunar da Khadija ya tambaye ta waye Tahir? mene a tsakanin su kuma a ina suka haɗu?
Khadijah tayi shiru cike da mamakin tambayoyin Hakimi, dan bata da labarin sanar da su da Baba yayi. Tadai samu labarin zuwan Tahir da Baba Isah wajan Baba, da kuma yadda suka yi da shi, Umma ta faɗa mata Baba ya ce ba zai yi mata Aure yanzu ba saita gama karatu, wanda jin wannan labarin yana ɗaya daga cikin abinda ya sake sakata damuwa.
Ganin ta shiga dogon tunani Hakimi ya katse ta da cewa
"Hadiza Magaji yazo nan yayi min bayanin komai, amma inason na sake ji daga bakin ki, ki saki jikin ki kiyi min bayani, idan har kina sanshi kuma bamu sameshi da wata matsala ba in sha Allahu zamu bashi Auran ki.
Khadijah najin haka bata san sanda da ta saki wani murmushin da ita kanta bata san lokacin da ya kwace mata ba.
Hakimi ya bita da kallo ya girgiza kai irin nasu na manya, yace "na'am Hadiza ina jinki.
Khadijah tace daman a wajan akin su Zaliha muka haɗu dashi shine.......... Khadija ta kwashe duka labarin yadda aka yi ta haɗu da Tahir, da yadda ya biyo ta har gida, da abinda yace mata duka ta faɗa wa Hakimi.
Hakimi yace "masha Allah. Hadiza kin yarda kina sanshi zakuma ki Aure sa?
Khadijah tayi shiru ta sunkuyar dakai, Hakimi ya sake maimaita mata tambayar, amma ta kasa bashi amsa.
Dada da takaici ya ishe ta ta tace "amma Mai gida wannan maganar duka mene amfanin ta? tinda dai ba basa Auran ta za muyi ba, sannan duka yaushe Hadiza ta sanshi harda zata soshi."
Hakimi ya girgiza kai, "amma Bintu in jikiko? Nidai Sama'ila nasan bance miki bazamu bashi auran Hadiza ba, saidai munce idan muka samu wani abu mara daɗi a tare da shi tabbas baza mu bashi ƴar mu ba."
Dada tace" amma Mai.......... Hakimi bai bari Dada ta ƙarasa ba ya ɗaga mata hannu.
"Bintu" Hakimi ya kira sunan Dada, dole badan taso ba tayi shiru.
Hakimi ya yi wa Khadijah duka tambayoyin da ya kamata sannan ya sallame ta yace taje ta kwanta.
Khadijah na fita Hakimi ya kalli Dada data cika fam kamar zata fashe, yace
"Bintu kinga lamari na Aure irin wannan ki cire kanki a cikin sa kiyi fatan alkhairi, saboda ba kasan mai Allah yake nufi ba, sannan kina jin yadda kwanakin nan nake fama da cases ɗin Auran dole da aka yi wa yara. Kina ganin dai abinda ya faru da Sarkin Noma a garin nan, ƴarsa tabi saurayinta sun gudu, saboda an hana shi auran ta, to ƙyauye ma fa ke nan, bare kuma cikin gari. Kuma gashi baɗan ƙasar nan ba ne komai na iya faruwa, ni hankali na yafi kwanciya mu bincika indai mutumin kirki ne kawai mu bashi auran ta, kada muje abinda muke ji a nesa ya faru a kanmu tinda tana sanshi, komai na iya faruwa, ba fata muke ba, amma kar mu bada ƙofar da wani abu mara daɗi zai faru da kanmu tinda ba haramun bane. Sannan kina ganin Hadiza kinsan tana san Yaron nan hmmm, lamarin yaran yanzu sai addu'a Bintu, muda muke tare da mutane kullum mu kaɗai muka san abinda muke ganin. Dan haka bana son sake jin wata magana, dan Allah kiyi mata addu'a kawai Allah ya zaɓa mata alkhairin sa.
Dada jikin ta yayi sanyin da maganganun Babancikin gida, amma duk da haka hankalin ta ba wani kwanciya yayi da wannan maganar Auran ba, kawai dan dai bata da yadda zata yi ne.
💫 UMAYMAH 💫
✍️A&A PEN
Follow our Whatsapp group via this link https://whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3
https://wa.me/+2348039352724
VOLUME ONE
EPISODE 3️⃣7️⃣
Washegari Tahir da Baba Isah suka je Bichi kamar yadda Hakimi ya buƙata, Tahir yasha bincike ba kaɗan ba, duk wani bayani da Baba Isah da Tahir suka yiwa Hakimi ya haɗa ya bawa Daddyn Lagos ya kuma ɗora masa alhahakin bincike akan Tahir, Baban ABU yana jin maganar auren Khadija kai tsaye ya nuna rashin amincewarsa, amma dole suka hakura saboda Hakimi ya riga ya gama magana.
Tahir bai samu damar yin magana da Khadija ba sai daga nesa ya hango ta lokacin data bito Sarkin Mota zai dawo da ita gida, Umma dai bata ce komai ba, tana ta taraddadi toh Khadijan nawa take ita dai tunanin yadda abin zai kasance ta ke yi, ko cikin yaran yan uwanta ba wacce ko zancen aurenta ya gitta, amma dai kowa da lokacin auran shi.
Baba yayi kiran Baba Isah da yamma ya zo ya same shi har gida, suka ƙara gaisawa cikin mutumtaka, Baba yace
"gaskiyar magana ni a son raina naso Khadija ta shiga jami'a ko bata kammala ba, ace tana aji uku ko hudu sannnan na aurar da ita, amma kana naka Allah yana nashi, mu kawai muna fadar ra'ayin mu ne tsarin Allah shi ne dai dai."
Baba Isah yace "Tabbas ka yi magana Alhaji."
"an bawa yaron dama ya fara zuwa zance su fuskanci juna, amma ba da daddare ba."
Baba ya bashi ranar Jumma'a da yamma sai Lahadi da yamma sau biyu a sati ke nan, ya ƙara da cewa "kuma auren da zarar ta gama makaranta za a yi da sharadin zata ci gaba da karatun ta a gidan shi." Baba Isah yace dukka sun amince da sharuɗɗan Baba kuma in sha Allahu za su kiyaye.
Da yamma Daddyn Lagos yayi musu zuwan bazata, don ko Baba be san da zuwan shi ba, bayan ya huta yace da Baba "kira min yaron nan zan mishi magana." Baba yace "ɗazu Aminin Baban shi ya bar nan bari na kira shi."
Baba ya kira Baba Isah ya faɗa masa Daddyn Khadija na neman Tahir, yana son ganin shi yanzu.
Tahir yana wajen aiki saƙon kiran ya same shi, dama ba su daɗe da waya da Baba Isah ba ya faɗa mishi yadda suka yi da Baba.
Faɗar irin murnar da Tahir yayi ma ɓata baki ne, ya kamo hanya ya zo ya sami Daddyn Lagos, Daddy ya sake yi mishi duk tambayoyin da suka dace, ya kara jah mishi kunne, yace
"karka bani kunya Tahir, nine uban Khadija duk abunda ya faru ni zaka nema, kuma ka riƙe mana ƴar mu amana."
Daddy ya ƙara jaddada. mishi zancen makaranta, Tahir yace in sha Allahu babu damuwa ya amince.
Bayan ya tafi daddy yace wa Baba "babu matsala zan ƙara bincika yaron ina da Aboki Mutallab ɗan Lebanon ne." Baba ya gyaɗa kai, ya gane shi yace "wanda kuke haɗuwa a wajen polo?" "kwarai ka gane shi Muhammadu, kasan lebanese ne, tunda Aminin Baban shi yace uban nashi dan kasuwa ne sosai nasan zai san shi, zan je har gidan shi na same shi, a nan Abbas road gidan shi ya ke." sosai Daddy suka tattauna da Baba.
Daddy ya kira Khadijah ya ƙara tambayar ta, yaya tana son shi, ta sinne kai tana murmushi, Daddy ya gane inda ta dosa, yace "shi kenan zamu baki ra'ayin ki Allah yasa yin na Allah ne, amma ki mayar da hankali a kan karatun ki, kinsan sai kin fito da sakamako mai kyau tukunna zaki samu gurbin shiga jami'a, kar ki bamu kunya kin ji yarinyar kirki." ta ɗaga kai, yace "ta shi ki je Allah yayi miki albarka."
Khadija taje gidan su munnirah ta kwashe duk yadda suka yi da Hakimi da zuwan Daddyn Lagos harda kiran daya yiwa Tahir ta faɗa mata, Munnirah tace
"oh my sis abun kamar wasa har an zo zancen aure?" Khadijah tayi murmushi "Nima mamakin maganar nake yi bantaba kawo aure ba yanzu har ga Allah." "ba wani nan Tahir ɗin nan kamar wanda yayi miki tsafi, ke mai cewa sai kin kammala jamia zakiyi Aure shi ne yanzu har kina maganar aure, toh kya dai haƙura mu gama secondary mu rubuta jamb ko." Munnirah ta faɗa da tsokana, "bansani ba." Khadijah ta faɗa tana harararta.
Umma ta shigo wajen Hajiyar Munnirah, ta faɗa mata abunda ya faru, Hajiya tace "ikon Allah, dama haka abun yake wani yana da nauyin jiki, wani kuma nan da nan daya taso sai maganar aure, Allah ya sa albarka." Umma ta ce "suna ina ne."
"tun ɗazu ina jin tashin muryar su a ɗaki." Umma ta girgiza Kai "wallahi yaran yanzu sai a bar su, Khadijah da soyayya."
Hajiya tace "magulmata tun ɗazu sun ƙule a ɗaki, sun samu abin yi, mu dai tsakanin mu da su sai addu'a, Allah ya sa gidanta ne."
Umma bata amsa ba, Hajiyar Munnirah tayi murmushi ta amsa da Amin.
Zaliha tana zaune tana yanke farce, Mama tana wanke wake tana baza shi ya bushe, ta kalli Zaliha, tace " ashe ranar nan ba tare kuka je kamfani da Khadija ba, nan na fito zani gidan Sabuwa yaronta ya kone na gan ta da wani Bature a Soro." Zaliha tace "ay shi ne mai kamfanin mu."
"Ikon Allah yana da mutunci kuwa, har ƙasa ya sunkuya ya gaishe ni, naga kamar da wani abu a tsakanin su." Zaliha ta kusa sharbe hannu da reza
"babu komai a tsakanin su." ta tari numfashin Mama, na tambaye ta, tace tayin aiki yazo yi mata."
Maman Zaliha ta yi shiru tana nazarin Zaliha ganin duk ta gigice ta rude, "toh me ye idan ma son nata yake yi? duk kin firgice daga jin magana." "Taɓ Wlh akwai, haba dai Mama ni ina nan a zaune ta auri Balarabe, kuma ni ke aiki a kamfanin shi, ya ma za a yi ya so Khadijah."
Mama ranta a ɓace tace "Toh sai ki hana in yace yana son nata, amma Zaliha idan kika yi haka wlh kin zama butulu Khadija fah ba ƙawar yar wa bace, yarinyar nan duk yadda iyayenta su ke ɗawainiya da mu ki rufe ido ki ce haka anya kuwa Zaliha, kawai na fada ne ban tabbatar ba, amma duk kin fita Hankalin ki, ke ba abun farin ciki ba ne ace ta samu miji ta dalilinki?"
Mama na ta mita har ƙanin Zaliha mai bi mata ya shigo gidan Mama ta mayar mishi da yadda aka yi, shi ma be goyi bayan Zaliha ba ya ce "ci da shan
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 19 Chapter of 29