waje da zani gobe shi aikin shi kamar yankan wuƙa yake, ina tabbatar miki a kwana biyu anyi an gama Jaah Zuga ai bala'i ne, ki fito da kuɗi kawai a wuce wajen."
"baki da matsala. Zaliha ta jawo jakarta ta fito da sabbin 500 notes da yawa ta bawa Suwaiba, Suwaiba ta ce "kar kiji komai duk yadda muka yi dashi zaki ji, gobe da sassafe zan tafi wajen shi a akan Dutse ya ke, irin arnan kan dutsen nan ne aikin shi mai zafi ne, ki fara shiri kawai Amarya." suka yi dariya suka tafa.
*****
Juyi take tayi acikin barcin tana sharɓa gumi, Khadija ta gani a wani mawuyacin hali tana ta kuka, tayi wani irin ɗashewa kamar babu jini a jikinta, sai kuma ta ga ta zura da gudu kamar ana binta, sai kuma ta daɗi a kasa tana ja da baya, wani baƙin hayaƙi tagani yana turnike wajen da Khadija ta faɗi har bata iya ganin fuskar ta, sai kuma ta ji wata murya kamar ta san muryar tana cewa "Khadija na yi miki illah, sai na ga bayanki, ke ɗin banza." Khadija ta sake gani ta na ta maimaita innalillahi wa inna illahirrajiun hawaye yana bin fuskarta, a hankali hayaƙin ya fara washewa, sai ta ji muryar ta kwashe da dariya, tana ganin inuwar mai dariyar sai kuma ta ɓace.
Firgigit Umma ta farka da salati, Baba yayi sauri ya riƙe ta yana tambayar ta "lafiya?"
Ashe da ƙarfi ta yi salatin, Umma ta faɗa jikin Baba ta fashe da kuka, Baba hankalin shi a tashe yake tambayar Umma meya faru, jikin ta sai rawa yake yi tana karkarwa ta kasa magana .
"menene?"
Baba ya sake tambayar Umma, yana jijjiga ta.
"Khadija ce."
"Khadija kuma? me ya same ta? Kinga nutsu ki faɗa min."
Sai da Baba ya bata ruwa ta sha ta samu nutsuwa Sannan ta faɗawa Baba duk abinda ta gani a mafarkin da ta yi, Baba yace "sharrin mafarki ne."
"Ni dai ina son ganin Khadija Baban su."
"ki yi haƙuri hutun ma ya ƙare jibi in sha Allahu zamu koma, kinga ta shi mu yi nafila mu yi mata addu'a, Allah ya kare dukkanin sharri."
*****
Suwaiba ta korawa Zaliha bayanin yadda sukayi da Jaa Zuga tace "ke tin kan nabar wajan ya fara yi miki aiki, amma yanzu yace yana son akai mishi hoton ta."
Bakin Zaliha har kunne, tace "Bari na lalubo miki hoton ƙawata, akwai wani hoto da muka ɗauka ran wata ƙaramar sallah, Umman Khadija ta yi mana wani dry lace mu uku muka je gidan hoto aka yi mana a tare sai kuma kowa yayi shi kaɗai to na Khadijah yana waje na, bari na dubo shi."
Zaliha tahau binciken kaya, can cikin wata jaka dake rataye ta gano shi, "yawwa ga shi nan." ta miƙawa Suwaiba, Suwaiba ta kalli hoton "kai kyakkyawa da ita kuwa." Zaliha ta sha kunu,
"meye na wani haɗe rai, sha kuruminki Amaryar Tahir anyi an gama, yace da yayi aiki akan hoton ta shi ke nan wata halitta daban Tahir zai rinƙa gani ba ita ba, kuma zai ji idan bai rabu da ita ba mutuwa zai yi."
"nan da yaushe za'ayi aikin? Zaliha ta tari numfashin Suwaiba."
"yace kwana biyu."
"Allah ya nuna mana."
Suka miƙe, a tare suka fito daga ɗaki ta raka Suwaiba ta tafi.
Bayan kwana biyu Suwaiba ta kira Zaliha tana dariya tace "Amarya aiki yayi kyau, Jaa zuga yace yanzu umarnin sakin ta kawai zaki bashi, zakiga aiki da cikawa."
Zaliha bata san lokacin da ta miƙe zaune ba ta saki shewa harda buɗa tace "yanzu kuwa zan ƙarasa wajan sa a Company."
Mama ta leƙo ɗakin tace "Magajiya (Mama haka take kiran Zaliha saboda sunan Kakarta taci) lafiyar ki kuwa kike buga irin wannan shewa haka." Zaliha ta zumɓura baki babu kyaun gani "gaskiya Mama ki dena cemin Magajiyar nan."
Mama bata ƙara bi ta kanta ba ta koma kan aikin ta, shaf shaf ta shirya ta nufi Company.
Tana zuwa direct office ɗin Tahir ta shige kai tsaye ko knocking babu, yana zaune akan kujera dafe da kanshi ta shigo.
Ya ɗago kai ya kalle ta, bata jira yayi magana ba ta wani tsare sa da idanu, kamar uwarsa tace "umarni ne ba shawara ba, ina so ka koma gida ka sallami Khadijah yanzun nan ka sake ta ta koma gidan su."
Wani dum yaji saukar maganar tata, sai kuma ya ɗaga mata kai da sauri, ya zari mukullin motar shi yabar Company.
A fusace ya shigo cikin falon, Khadija na kwance a ɗaki bataji shigowar motar shiba kawai sai bugun ƙofar shi taji.
Yana tsaye a bakin ƙofar yayi Knocking har wajan sau uku kafin cikin husky voice yace
"Khadijah buɗe ƙofar nan kar ranki ya baci" yayi maganar cikin harshen larabci. can na hangota a ƙarshen gadon a cure tana motsi, ashe da mutum a ɗakin.
"Khadijah"
ya ɗaga muryar, a fusace wannan karon ya kira sunan ta, sai kuma yaja tsaki yana barin ƙofar ɗakin yace
"ki fito ki same ni a falo yanzun nan kar ki ɓata min lokaci.
A hankali ta yaye bargon data rufa dashi ta fito, kana ganin ta zaka gane a tsotse take, tayi duhu, ga wani kashin wuya tsab wasu kwandaloli za su ɓata (su samu wajan zama) a wuyan ta, idanuwan ta sun wani jeme (sun koɗe) sun ƙankance sun yi ja, da alama dai tasha kuka, koma nace kukan ma ta ke yi, bakin ta a bushe kamar wacce ta fito daga rana, fatar jikin ta ta ɗashe tayi wani irin fari kamar mai ƙaramin Yaron ciki, kanta babu ɗankwali kalaba ce a kanta ta tsofa sosai ta zubo har kafaɗun ta, laushin gashin saiya ƙara fito da tsufan kalbar, riga da wando ne a jikin ta pink color da fararen flowers a jiki, ƙafafun ta sun yi sirara a cikin wandon.
Ta mike da ƙyar ta buɗe wardrobe ta ɗauki hula ta saka, tana tafe tana bin bango, ta buɗe kofar kenan ta kara jiyo muryar shi yana cewa
"wallahil azeem na taso yau sai jikin ki ya faɗa miki"
Da ƙyar ta ƙaraso jikinta har rawa yake ta fito palour, yana zaune akan one sitter hankalinsa kwance kamar ba shine yayi mata ihun ba, yana riƙe da remote a hannusa yana canja channel, da ƙyar ta ƙaraso ta durƙusa a gaban shi, sai da ya kai kamar minti biyar tana tsugunne bai ce mata komai ba kafin ya bude bakin shi yayi mata magana cikin isa
"Dago kan ki magana zamu yi" kana jin hausar tasa kasan ba cikakken bahaushe ba ne.
"Khadijah"!
Ya kira sunan ta, ta ɗago kai ta kalle shi cike da kokonto dan suna ne da ba zata iya tuna randa ya kirata da shi ba, amma yau Khadijah gatsal tunanin tane ya katse jin yana cewa
"yau ce ranar ki ta ƙarshe a gidan nan" da hanzari ta dago kanta ta zuba masa ido, nan da nan hawaye suka wanke mata fuska, karon farko ta buɗe bakin ta tayi magana muryarta na karkarwa saboda kuka tace
"Habibi me nayi maka? Na tambaye ka laifina har bansan adadi ba, amma sai kace ba komai. Dan Allah dan son ka da Manzon Allah kayi hakuri kayi min bayanin abinda nayi maka, nayi maka alkawarin zan gyara kuskure na Habibi, so yana zama ƙiyayya ne dama? Kai kadai na ke so a rayuwata, kai ka nuna min so, ba zan iya rayuwa babu kai ba Habibi dan Allah kaji tausayi na" ta ƙarasa maganar tana shesshekar kuka, yadda take rusa kukan tana roƙon sa yayi hakuri saida zuciyarsa ta motsa, yaso yaji wani abu a ransa mai kama da tausayinta, tsayawa yayi yana saurarenta kamar ba zai yi magana ba sai kuma yace
"Khadijah khuruj min hayati (get out of my life).
Cikin kuka ta tari numfashin sa da cewa
"Anta li wa ana laka (you are for me and i am for you).
Kanta ta kife akan cinyarta ta saki kuka mai cin rai, tin daga ƙasan zuciyar ta take jin wani irin ciwo yana taso mata.
"Ƙararati laa yumkin taghiruhaa (my decisions cannot be changed)."
Cikin kuka tace "anaa asif arjuk a tini farsah thaniyah (I'm sorry please give me a second chance)."
"na kiraki na baki takardar ki ne, ban kira ki dan ina son kallon fuskar ki ba, har yanzu you are a young girl find someone I'm no more interested, kamar kullum na faɗa miki ba ki yi min komai ba, Na gaji da zama ke ne kawai, nima zan auri wadda ta dace da ni."
Shi kansan yasan hundred percent abinda yake faɗa ba shine a ƙasan zuciyar saba, to amma furta kalaman ga Khadijah kamar wani umarni ne dake riƙe da ransa wanda sam ba zai iya ƙinfaɗar suba.
Da sauri ta dago kai ta kallesa, jajayen idanuwanta da suka kumbura ta zuba masa ta ƙara maimaita "wata kuma"
Ina Alkawarin mu? habibi pls na roƙe ka ka yi haƙuri mu rayu da juna, Habibi dan Allah ka janye zancen sarkin nan, zan cigaba da zama dakai koda ba zaka bani abinci ba kamar yarda muke a yanzu, auren mu just six month na koma gida, na zama karamar bazawara kenan? Saboda kai ban cigaba da karatu ba, Babana baya son auren mu ka sani, ka manta yadda Hakimi ya shiga maganar auren nan? iyayena suna son nayi karatu. Ka san 'yan boko ne, gaba ɗaya dangin mu babu wanda ya taɓa yin aure a kananan shekaru sai ni.
Da sauri ya katse ta da cewa "Ban manta ba Khadijah, ina zan manta yadda iyayenki suka amince da kyarata, da yadda suka rinƙa ce min baƙon haure, duk da mahaifi na ya dade a Kano kafin ya koma ƙasar mu gaba ɗaya, amma haka iyayen ki suka ce mana baƙin haure, yanzu sai ki koma gida ki auri ɗan 'uwan ki Bahaushe" ya daga kiran daya shigo wayar shi
"eh ina gida ki ƙaraso."
Shiru falon ya ɗauka sai Tv da ke aiki kamar mintuna sha biyar aka yi sallama wata Matashiyar budurwace ta shigo zata bawa Khadijah shekaru ɗaya zuwa biyu, riga da skirt ne a jikin ta na atampa matsattsu ta yafa siririn mayafi a wuya da takalmi mai tudu baki da bakar jaka, bata da tsaho, tana da dan haske amma daga gani ana shiga kanti sosai tana bleaching, dan fuskarta ta yi wani dabbara dabbara da pink, kamar tana da dan budewar ido, idanuwanta kanana ne hancin ta gajere bata da diri ko kadan daga saman ta kirjinta a cike yake sosai har yayi mata yawa.
Khadijah na ganinta ta miƙe da sauri cike da ƙarfin hali tace "yauwa Zaliha zo ki roƙarmi Habibi yayi hakuri dan Allah" ta rike mata hannun. tace
"Dan Allah Zaliha idan aka ce miki Habibi zai rabu dani za ki yarda?"
Zaliha ta kalli hannunta da Khadijah ta rike ta zame hannunta tana mata wani irin yi mata kallon kyama ta wuce ta, kai tsaye ta tafi kusa da shi ta zauna kamar zata shige jikin shi.
"Kin ƙaraso, kin bar ni ina ta jira? amma mun kusa kai wa ƙarshe"
Da mugun mamaki khadija ta juya tana kallon su su biyun, me ke nan, me suke nufi? ta tambayi kanta, Zaliha fah ƙawarta take gani a kusa da mijinta a zaune? me hakan yake nufi? dama Zaliha ta san zancen sakin ke nan, to amma ta yaya? Habibi ya dade yana mata barazanar saki, toh barazana mana zata ce, kwata-kwata auren nasu wata shida, wata uku ne kawai tayi su a kwanciyar hankali.
Muryar Zaliha ta katse mata tunani da cewa "Malama ba mu da lokacin zaman jiran ki."
Zaliha ta mike ta ƙaraso har inda Khadijah ta ke, ta kalle ta ta yi wani murmushin mugunta tace "Khadija kenan 'yargata kuma 'yar so hmmm! ki na mamakin na san maganar saki ko? ta ƙara faɗaɗa murmushinta
"Dama tun farko ta dalili na kika hadu da shi Khadija da alama kamar kin manta hakan ko?"
Khadija ta kalle ta baki buɗe kamar mutum mutumi (robot) da mamaki sosai a fuskar ta
"rufe baki baiwar Allah" sai da Zaliha ta faɗi haka sannan ta san bakin ta a bude yake tsabar mamaki.
Zaliha ta juya wajan sa cikin gadara tace "Ka rubuta mata takardar sakin ne? Jikin sa na rawa yace "yanxu zan rubuta mata" ya miƙe ya shiga ɗakin shi.
Khadijah ta bi bayan shi da kallo, sai kuma ta fara tari kamar wadda aka shaƙe.
Zaliha nayi mata dariyar mugunta tace "Ay baƙin ciki yanzu za ki fara gani Khadijah, komai ke Allah zai bawa kin fini kyau, kin fini ilimi, kin fini gata, iyayen ki masu rufin asiri, kin auri miji na gani na fada, sutura sai kin cire ki bani kwance (kyauta).
A makaranta ke ce mai farin jinin Malamai da ɗalibai, kowa inya buɗe baki sai dai yace Khadija, Abinci ma Ummanki ke bamu, wallahi Khadija kullum zuciya ta tafasa takeyi da waɗannan ni'imomin da Allah yayi miki, duk lokacin da kike walwala kunci na ke yi."
Wani zazzaɓi ne ya rufe Khadija, lokaci guda miyau (saliva) ɗin baki ta ya ƙafe da ƙyar ta kalli Zaliha tace "ashe ba da zuciya ɗaya kike zaune da ni ba? ashe alkhairi yana zama sharri, kar ki yi min haka Zaliha kinsan ina san Habibi, karki cutar da zuciya ta da babu komai acikin ta sai alkhairi, soyayya da kyautatawa, ban san kiyayya ba Zaliha, ke da Munnirah ɗaya ku ke a waje na, bani da Aminai sama da ku."
Zaliha ta ɗaga mata hannu "Ke dan Allah tsaya kar ki ɓata min rai, wannan munafukar wadda ta tsaya min a wuya, ba dan ita ba da tuni ma ba a zo nan ba, da tuni na shafe babinki Khadija, akwai yar iska irin Munnirah Algunguma na dade ina neman dama akan ki shegiyar ta kafa ta tsare kamar uwar ki, duk abinda tace miki shi kike yi, sai yanzu Allah ya kawo silar da ta tafi ta bar ki, Khadijah nafa san duk shawarwarin dana ke baki ita ce take ɓata min aiki, haka kuke wani cewa juna my sis, itama tace miki my sis, kun ware ni a gefe ga matsiyaciya ko? ko kin taɓa kirana da wani suna bayan Zaliha? Munnirah ta sha daƙile ni tsinanniya sai ga shi ta kira ni tana kuka Mamanta bata da lafiya zata yi tafiya, to bari na faɗa miki ba ƙaramin daɗin labarin tafiyar tata naji ba, dan nasan yanzu ne zan iya yin maganin ki cikin sauƙi, Allah yasa daga can uwar ta mutu, Annamimiyah"
A wannan lokacin Khadija komai kwance mata yayi, sai ta buɗe ido ta rufe, daga kwancen da take cike da fata tace "Allah yasa duka wannan mafarki nake yi"
"buɗe idon ki da kyau ba mafarki ba ne" Zaliha ta ƙaraso gaban Khadija dai dai saitin fuskar ta, ta daga hannu ta shafa fuskar tace "wannan kyakkyawar fuskar taki na riga nayi mata illah Khadijah, ba ita yake gani ba yanzu, koda yake babu amfanin yi miki wani dogon bayani, ki gafarce ni na kamu da son abinda yake mallakin ki ko?" Zaliha tayi maganar cikin izgilanci.
Khadijah ta ƙura mata ido "mamaki kike yi ne? zaliha ta tambaya. dai dai lokacin kuma ya fito daga ɗaki hannunsa riƙe da farar takarda ya nufo su jikin shi a sanyaye, fuskar shi ba wani karsashi, kana ganin sa kasan yana cikin tashin hankalin dashi kansa bai san kona meye ba, amma kuma ba zai iya tsallake umarnin da zuciyar shi take basa ba.
Da sauri Zaliha ta tare shi ta karɓi takardar ta buɗe ta karanta, sai ta ɗago ta kalle shi tace "Amma D ay daka cike mata ukun kawai" sai kuma tayi murmushi ta linke takardar ta nufi Khadija dake yashe akan tilas ta buɗe hannunta ta saka mata takardar tace "Allah ya raka taki gona" ta faɗa tana sakin murmushin jin daɗi.
💫 UMAYMAH 💫
✍️A&A PEN
Follow our Whatsapp group via this link https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3
https://wa.me/+2348039352724
VOLUME ONE
EPISODE 4️⃣5️⃣
Khadijah da ƙyar ta miƙe jiri na ɗaukan ta bata da ƙarfin gwuiwar karanta ko menene a takardar, tana dafe bango ta shiga ɗakinta, hijab ta ɗauka a kan sallaya, ta ɗakko ragowar 300 canjin kuɗin da Munnirah ta bata, wadannan kuɗin sun taimaka mata ba kaɗan ba.
Dasu take siyan Awara, da farko leƙa wa take ta kira su, tinda suka gane tana siya kuma sheke nan suke kawo mata talla, tsawan kwanakin nan dasu Umma suka yi a Bichi Awara Khadija ta rinƙa siya tana ci ta sha ruwa a kitchen, ta na gama ci kuma take kwarara amai mai azabar zafi dan baƙogwaron ta har fashewa yake yi, a cikin wannan halin ta kawo har yau.
Tana ƙoƙarin saka hijabin aka shigo ɗakin a fusace Zaliha ce ta shigo Khadija bata juyo ba taji tana cewa
"dalla malama jiran ki mu ke yi." ta tsaya a bakin ƙofar irin zoki wuce ɗin nan.
Khadija bata ce mata komai ba ta saka hijabin ta, tsabar tashin hankali a baibai ta saka hijabin ta fito, jikinta ya ƙara ɗaukan zafi kamar wuta ga wani jiri da ya ke ɗaukan ta, ta fito falon Tahir baya falon yanzu, tana hawaye ta fito cikin gidan Zaliha ta buɗe mata gate ta ce "a ƙara gaba."
Ita yanzu bata da wani muhallin yin dogon tunani, ta fito daga gidan har ta fara tafiya ta juyo ta yi wa gidan kallon ƙarshe randa aka kawo ta gidan ta faɗo mata sai ta sake fashewa da kuka, tana tafe ƙafar ta babu takalmi da ƙyar take iya jan ƙafar ta, ta kusa fitowa bakin titi ta ga motar shi ta zo ta wuce da gudu, Zaliha na Zaune a gaban motar, kanta ya ƙara sarawa, ikon Allah ne ya kawo ta bakin titi, mai mashin yana tsayawa ta shige, yana tambayar ta ina zai kaita ta kasa magana, mai mashin ɗin ganin halin da take ciki saiya samu waje ya tsaya da ƙyar ta iya ce masa "Sulaimanu crescent."
****
Umma ba su daɗe da shigowa gidan ba Ibrahim da Aliyu nata shigowa da kaya da tsaraba, Umma ta shiga ɗaki ta gaji sosai, amma gaskiya ba zata iya bari sai gobe taji halin da Khadija take ciki ba, Ibrahim ta kira tace "Maza tafi gidan Khadija ka dubo min ita, inata kiran layinta bana samu ko yaushe na kira saidai a cemin the number you are calling is not available at the moment pls try again later, kusan sati biyu fa kenan."
Ibrahim ya fita umma ta yunƙura zata shiga toilet ta ji ihun Ibrahim yana kiran "Yaya Khadijah."
Da gudu Umma ta fito ta ƙaraso inda Khadija take tsaye a tsakiyar falo. Tabbas ba dan ita ta haifi Khadijah ba da zata iya rantse wa da Allah ba ita ba ce, ta zama skeleton, Umma tana isa wajen, Khadija ta yanke jiki ta faɗi a sume, Umma ta yi maza ta taro ta jikinta ta rungume, tana ta jijjigata tana kiran sunanta, Baba ya fito daga ɗaki jin hayaniya da kukan Ismael, yana ganin halin da ake ciki yace "Babangida maza ba mu ruwa." dukan su a gigice su ke, Baba ya shafa mata ruwa ko gezau bata yi ba.
Umma ta cire mata hijabi Ibrahim ya ƙara gudun fanka Baba ya sake shafa mata ruwan amma ina ta yi nisan zango.
Ganin haka Baba ya ɗauke ta yayi waje da ita, Umma dasu Aliyu suka rufa mishi baya, kai tsaye asibitin Nassarawa suka kaita, duka gidan su anan suke ganin likita, suna zuwa aka karɓe ta.
Khadija ta farfaɗo amma ba a hayyacinta take ba, Baba yayi ta kiran wayar Tahir bata shiga, ya aika Babangida ya je ya dubo gidan ya je ya dawo ya ce gidan a kulle yake, sai da hankalin Umma ya dawo jikin ta sannan ta lura da takardar dake damke a hannun Khadijah, Umma ta cewa Baba
"naga takarda a hannunta bari na duba naga ko menene." Baba hankalin shi a tashe yayi wajen Khadija dake kwance a gadon Asibiti kamar gawa, cikin dabara da gudun karsu tashe ta daga bacci da tunda aka yi mata allurai take yinsa Baba ya zare takardar, duk ta dukunkune gumin hannunta ya jika takardar tayi laushi. Baba ya warware takardar.
"Ana Tahir utalliquk marratayn (I Tahir divorce you twice)
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 23 Chapter of 29