Umma komai akan yadda Zaliha ke yawan kushe ta ba, ita a ganin ta waɗannan ba su isa wani hujja ba da za a ce Zaliha bata sonta, kawai tana ganin matsin lambar Munnirah ne dan ba sa shiri.
💫 UMAYMAH 💫
✍️A&A PEN
Follow our Whatsapp group via this link https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3
https://wa.me/+2348039352724
VOLUME ONE
EPISODE 3️⃣3️⃣
Wata ranar Alhamis sun taso daga makaranta Zaliha tace zata wuce gida akwai abinda zata yi, ranar Juma'a ma haka bata zauna a gidan su Khadijah ba, har Umma ta tambaya ko faɗa suka yi, Khadija tace a'a babu komai kawai haka tace zata gida. Umma bata sa ke maganar ba suka ci gaba da sabgogin su.
Tsawan sati biyu a jere ke nan duk Alhamis da Juma'a Zaliha ta daina zuwa gidansu Khadija, ita ma Khadija sai bata wani damu ba tunda tasan ba faɗa suka yi ba.
Ranar Monday Zaliha ta ke faɗa wa Khadijah wani dan unguwar su ne Alkasim ya samo mata aikin kamfani, kuma babu laifi kullum ana basu 1000 idan an tashi, toh daya ke ita tana zuwa makaranta sai ta ce ranar Alhamis da Jumma'a zata rinƙa zuwa, kuma wannan 1000 ɗin tana taimaka mata.
Khadijah taji mata daɗi tayi mata fatan Alkhairi, Ranar weekends su ke yin kitso, Umma bata sangarta Khadija ba, duk da suna da mai musu wanki, amma duk a weekends ita take wanke musu uniform ɗin su, har na Ibrahim da Isma'il, shi Aliyu boarding school yake yi a FGC DAURA.
Umma ke yi wa Khadija kitso, amma da taga Zaliha ta iya kitso sai take cewa taje Zaliha za yi mata ita ma ta huta.
Zaliha tana yawan yi wa Khadijah kitso, idan tayi mata kitso kamar an zana shi saboda kyau, Munnirah bata taɓa bawa Zaliha kan ta ba, ta kan ce gashin ka sirrinka ne ita ba ta yarda ta bawa Zaliha kanta ta kitsa mata ba.
Normally Munnirah bata da yarda musamman in jinin ku bai haɗu ba, ta kan ce wa Khadijah ita kawai akwai wani abu a tattare da Zaliha da be mata ba.
Ranar wata weekends Khadija ta yi ta jiran Zaliha bata zo ba har ta gama wankin uniform ɗin su ta yanke farce, ta gaji da jira ta cewa Umma za taje gidan su Zaliha ta duba ko lafiya.
Khadijah ta biyawa Munnirah su tafi tare Munnirah tace ita babu inda zata, Khadija ta kama hanya ta tafi.
Bata sami Zaliha ba sai Mamanta ta samu ta faɗa mata Zaliha ta tafi kamfani, yanzu ta fara zuwa har Asabar da Lahadi. kwana hudu kenan a sati yanzu take zuwa. Bata jima ba ta dawo gida, ƙarshe sai Umma ce ta yi mata kitson.
Tun da kuɗi suka fara shiga hannun Zaliha sai ta fara canjawa, ta fara shafe shafe na yammatan zamani masu bata fatar jikin su da bleaching, ta fara kitson attachment, tun wata rana da Umma ta gani ta yi mata faɗa Zaliha bata ƙara cire Ɗankwali a gidansu Khadija ba.
Ranar wata Wednesday an fito break Zaliha ta yi wa Khadijah tayin rakata kamfani, tace babu damuwa zata tambayi Umma inta barta sai suje ranar Alhamis. Khadijah ta tambayi Umma bata hana taba, ranar Baba baya nan ya je Bichi an yi Rasuwa.
Ranar Alhamis su ka hau Napep suka tafi, Company yana can kan titin Ƴankaba, dake wajajen akwai ƙananan ƙyauyuka irin su Ɗan sarai, Gunduwawa da Tokarawa, akwai kamfanoni sosai a wajan.
A Kamfanin zoɓo take aiki, Khadija taga yarda ake gyara zoɓo ayi packaging ɗin shi zuwa ƙasashen waje. akwai yan mata har da tsofaffi a ma'aikatan, ana gamawa aka basu 1000, Zaliha ta kwaɗaita wa Khadijah aikin ko tana so ta faɗawa Alkasim ya samo mata.
Khadijah tace ta bari ta faɗawa Umma tukunna, ko da Khadija ta faɗawa Umma, cewa tayi bata san me ta rasa ba da zata ce zata yi aikin kamfani, kar ta ƙara yi mata zancen.
Zaliha na zuwa gidan su Khadijah tace mata ba a bar ta ba, a wannan lokacin ne kuma suka shiga ss2, Khadija ta ƙara zage damtse sosai wajan karatu, sunan ta ya ƙara fitowa a makaranta, duk wani quix da debate idan makarantar su zata je dole da sunanta.
Haka Khadija ke satar jiki ta raka Zaliha aikin company, sun sha faɗa da Munnirah idan ta faɗa mata inda suka je, don gaskiya tunda Umma ta nuna bata so, mafi yawancin lokuta ce mata take yi zata gidan su Zaliha, Umma bata hanawa daga nan kuma sai su wuce kamfani.
Ana haka Alkasim ya ce wa Zaliha akwai wani kamfani sun fi wannan da ta ke aiki biyan kudi, na Lebanese ne idan tana son zai nema mata.
Sunan kamfanin FARASHA (butterfly) suna bukatar ma'aikata, Babba ne kamfanin suna yin sabulun wanka da na wanki, turare, da liquid soap, sashi sashi ne Company kowane sashi da ma'aikatansu.
Zaliha tana ta murna ta ce masa tana so, aka saka sunanta cikin wanda zasu fara aiki a FARSHA. Company bashi da nisa da wanda ta ke zuwa.
Kwanci tashi Zaliha ta fara zuwa FARSHA, kuma Alhamdulillah tana samu sosai, dan har tana iya mora musu abu na kuɗi idan an fito break, sai ya zama na ta rage cin abincin da Khadija take kawo musu, tunda tana da yan canjin ta yanzu,.sai ta koma cin su meatpie, ice cream na fan ice, Awara da sauran su.
Hatta pad da su turare da Umma ta ke siya mata, ta ce Khadija ta faɗawa Umma ta daina siya mata yanzu tana aiki, Umma ta kirata tayi mata faɗa sosai, ta ce sai dai idan bata dauke ta uwa ba, duk abinda ta yi mata ta yi ne a matsayin uwa, Umma bata fasa yi mata komai ba kamar yadda ta saba.
SANADI....
Wata rana Khadija ta saci jiki ta raka Zaliha Farsha, sabon Company data fara aiki, bayan an tashi sun daɗe basu tafi ba, Khadija ta cewa Zaliha wai me suke jira ne, Zaliha tace ba a sallame su ba ne.
Sun daɗe suna jira kafin ayi kiran su, yana zaune yana raba wa ma'aikata kuɗi, har ya zo kan Khadija ya miƙa mata kuɗin taƙi karɓa.
Yana ta miƙawa jin ba'a karɓa ba ya ɗago kai yana yarfe hannu alamar gajiya, dai dai lokacin idon su ya faɗa cikin na juna.
Wannan haɗuwar ita ce silar komai daya faru da Khadija, wannan haɗuwar ita ce tattare da zanen ƙaddarar ta, wannan haɗuwar ita ce rushewar burin ta na zama cikakkiyar lawyer, wannan haɗuwar ita ce ta haifar da sanadin zuwan Umaimah duniya.
Ya kafe ta da ido, itama saita kasa ɗauke idon ta a kanshi kamar mayen karfe, har sai da Zaliha ta zungure ta, cikin sarkewar murya Khadija tace
"Rakiya na yi."
Ta zaci bai gane me tace ba, sai kuma taga ya yi murmushi, ya cewa Zaliha ta tsaya ya sallami sauran.
Daya ke yamma ta yi sosai, kowa ya ƙosa ya tafi gida ba a samu yan sa ido ba.
Bayan ya gama ya kira Zaliha ya ce ta same shi a office, har sun fara tafiya Khadija ta kira sunan Zaliha, suka juyo tace ta yi sauri magariba ta kusa.
Ya ƙara yi mata murmushi suka tafi, bata daɗe sosai ba sai gata ta dawo tana ta yi wa Khadijah murmushi, anan take faɗa wa Khadijah wanda ya raba kuɗi shi ne mai kamfanin, akwai accountant da shi ya ke raba kuɗi, sai aka kama shi da Almundahana, shi ne aka sallame shi.
Khadijah ta girgiza kai, "mutane ba su da tsoron Allah."
Zaliha tace "akwai masu amanar fah, dan akwai Manager Alhaji Isan an ce Aminin Baban shi ne, kinsan me yace wai? ya yaba da hankalin ki da wata ce karɓa zata yi tunda shi ba sanin ma'aikatan yayi ba, shi ne ya bamu wannan."
ta fito da 500 note sababbi guda 10.
"Yace mu raba wannan kyauta ce ya bamu." Zaliha ta ƙirga 2500 ta bawa Khadijah. tace ta riƙe ita aka bawa ita yar rakiya ce, shike nan Zaliha ta mayar da kudinta jaka babu yar jayaryarnan.
Khadija tun da ta dawo gida take tunanin bawan Allah nan har Umma ta so ganewa, ta rinka tambayar ta menene ta ce mata babu komai.
Kai hatta cin Abincin Khadija saida ya ragu, karsashin ta ya ragu har a makaranta malamai sun gane, sai da class teacher ya kira ta staffroom ko tana da matsala ne tace babu komai, A zahiri ita ma ba za tace wani abu ya na damuta ba, dan gaba ɗaya tunanin ta ya kwance, idan ta rufe idonta murmushin shi kawai ta ke gani, haka ta rinƙa Allah Allah weekends ya zo ta raka Zaliha kamfani.
Ranar Asabar da wuri ta gama aiyikan ta tana ta sauri har Umma ta so ganewa, da farko ma hana ta fita tayi sai daga baya tace ta je amma kar ta daɗe.
Khadijah ta sheƙa wanka tayi kwalliya ta fito Umma ta ce "anya kuwa gidansu zaleeha za ki?
Khadijah tace wlh can zata, Umma bata tsaurara bincike ba ta ce sai ta dawo.
Khadija tayi rashin sa'a ta je ta tarar da Zaliha tana kwance bata da lafiya, da yake tanada ulcer, kuma inta tayar mata bata mata da wasa, har nurse aka kira ta zo gida ta yi mata allura aka saka mata ruwa, jikin Khadijah a sanyaye ta koma gida babu biyan buƙatar.
Zaliha sai da ta kwashe sati guda tana jinya bata zuwa makaranta bata zuwa Company, sai da Khadija ta lallaɓa Munnirah sannan ta yarda sukaje ta duba ta.
Satin da ya zagayo ma haka aka yi rashin sa'a tun ranar Wednesday Zaliha ta faɗa wa Khadijah an yi musu rasuwa a ƙauyen Baban su za su je gaisuwa gaba ɗaya gidansu, bayan sallar Jumm 'a da aka tashi daga makaranta, su Zaliha suka tafi daya ke Baban su mutumin wudil ne, tafiyar tasu babu nisa.
💫 UMAYMAH 💫
✍️A&A PEN
Follow our Whatsapp group via this linkhttps://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3
https://wa.me/+2348039352724
VOLUME ONE
EPISODE 3️⃣4️⃣
Khadija ta rinƙa tunanin mutumin da ko sunan shi bata sani ba, kullum da tunani shi take kwana ta ke tashi, Munnirah har ta gaji da tambayar me ya ke damunta, kullum amsar ta babu komai.
Ranar weekends Baba ya shirya musu tafiya Bichi, Munnirah ta tambaya aka bar ta suka tafi tare, shigar ta cikin mutane ya rage mata damuwa, amma ba wai tunanin shi ya bar ranta ba ne.
Kullum suna gidan Baban sama yaran shi duka mata ne sun girme wa Khadijah sosai, yaya Hindu da yaya Anisah, mai bi mata me sunan Dada Fatima ita ce kusan tsarar Khadija, amma ta girme musu ita da Munnirah, yaya Anisah ce mai yi musu karatun littafin Hausa, sosai tunanin shi yayi wa Khadijah sauƙi.
Allah Allah Khadija take su dawo gida tabi Zaliha Company danta ganshi.
Ranar Lahadi da yamma Dada ta cika su da tsarabar fura da nono da yawa dasu cukwui, busasshen kifi, mangoro daya ke lokacin shi ne, suka dawo gida niƙi niƙi da tsarabar Bichi.
Umma ta raba tsarabar ta bawa Hajiyar su Munnirah, dan suna haka sosai a tsakanin su, har sakakken abinci in sunyi suna kai ƙwarya a tsakanin su.
Ranar Monday Khadijah suka haɗu da Zaliha tsabar zumudi tun Monday ɗin ta faɗa mata ranar Alhamis zata raka ta kamfani, Zaliha tace "wlh ki zo muje ai zuwan ki ya ja min alkhairi, na samu kuɗi, Allah ya sa mu kara ganin shi." Khadija ta amsa da amin a zuciyar ta.
Khadijah bata san sanda ta tambayi Zaliha yaya sunan shi ba, Zaliha ta ce wlh ita ma bata sani ba, "me yasa kike tambayar sunan sa." Khadija tace babu komai, kawai ta tambaya ne.
Suka ci gaba da hirar su, Munnirah tace wa Khadijah eyasa take san bin Zaliha kamfani bayan Umma ta hanata zuwa. Tace wallahi in bata daina bin Zaliha ba saita faɗa wa Umma.
Ranar Khadija saida suka yi faɗa da Munnirah abinda ba su taɓa yi ba, abu kamar wasa har aka tashi a makaranta basa kula juna, basu taho tare ba, Munnirah ta yi fushi bata jira Khadija ba tayi tafiyar ta.
Zaliha sai ƙara zuga Khadija take yi wai ta cika tsoron Munnirah ita ce mai tsara mata rayuwa, ina ruwanta da ita, kamar wata uwar ta.
Tsawan kwana biyu babu wanda yake kula kowa acikin su har Umma ta gane ta kira su, tace wlh idan basu faɗa mata me ya haɗa su ba zata faɗawa Iyayen su maza tunda su sun raina su, har Munnirah ta buɗe baki zata yi magana Khadija tayi sauri ta rufe mata baki, ta ce "meye haka my sis."
Khadijah ta kalli Umma ta ce "mun shirya insha Allahu haka ba zata ƙara faruwa ba."
Shike nan ƙarshen faɗan ya zo suka shirya, abin be yiwa Zaliha daɗi ba don fuskarta saida ta nuna haka.
Kwanaki suna ta gangarawa har ranar Alhamis tazo Khadija ta tambayi Umma zuwa gidan su Zaliha tace ta tsaya tana da saƙon da zata tafi wa da Maman Zaliha, kayayyakin kadi ne su kuka, kubewa, zogale da busashen kifi.
Khadijah ta fito sanye da doguwar rigar atampa chiganvy pink colour dinkin yayi mata kyau sosai, ta yafa mayafi ta fesa turare, tasa takalmi flat ta tafi gidan su Zaliha, ta ci sa'a ta sameta tana shirin tafiya kamfani. Suka gaisa da Mama ta bata sakon Umma, Mama ta karɓa tana ta murna dasawa Khadija albarka.
Suna fitowa me Khadija zata gani numfashin ta kamar ya ɗauke saboda gudu, shita gani tare da Alkasim a tsaye a jikin mota ƙirar toyota a kofar gidansu zaliha.
Alkhasim na ganin su yace "Yauwa ina ganin ita ce wannan ko yallaɓai?" Alkasim ya fada yana kallon shi, wata ajiyar zuciya ya sauke "ita ce" ya fada ƙasa ƙasa.
Kan Khadija a ƙasa Alkasim ya kalli Zaliha ya ce "haka ake yi daga fara aiki sai fashi kusan satin ki biyu." suka gaishe su Alkasim dai ya amsa, amma shi bata ji ya amsa ba kawai sai kallonta ya ke yana murmushi.
Alkasim ya kalle shi ya ce "Allah yasa ba laifi ta yi ba?" sai a lokacin ya numfasa yace "laifi tayi mana, haka ake aiki ana fashi." Zaliha ta rikice ta fara yi mishi bayanin rashin lafiyar da tayi da kuma rasuwa da aka yi musu. yayi murmushi yace babu komai ta yi maza ta tafi wajen aikin ta.
Jikin Zaliha na rawa ta amsa da "toh yanzu ma can zamu tafi." ya ce "ki je ke kaɗai ina san ganin yar rakiyar ta ki, yana faɗar haka Zaliha sai cewa ta yi "kamar yaya." nan da nan fuskar ta ta canja, "kar ki damu babu abunda zai same ta." ya bata kuɗi masu yawa yace "gashi ki shiga mota." Hannun ta na karkarwa ta karɓe kuɗin tayi gaba, ya sallami Alkasim duk Khadija na tsaye tana jinsu kamar an dasata, Zaliha tana tafiya tana waiwayo su har ta haƙura ta nemi abun hawa.
Khadijah gaban ta sai faɗuwa yake, ya ce "babu gaisuwa, haka ake karɓan baƙo." sai sannan ta gaishe shi, be amsa ba sai ƙura mata ido da yayi, duk sai taji ta takura, ta sake yin ƙasa da kanta tana wasa da bazar mayafin ta, mutane suna ta wucewa suna kallon su, duk Khadija saita takura, Muryar shi ta katse mata tunani da cewa
"ko zamu shiga ciki ne." yayi maganar yana nuna Ƙofar gidan su Zaliha, kamar an saka wa Khadijah remote kawai ta juya ta shiga Soron ya rufa mata baya.
Ya kalli Khadijah sai kuma yayi murmushi, yace "ta ina ma zan fara, Allah ya jarabce ni da son wacce ko sunan ta ban sani ba." Khadijah ta sake sunkuyar da kai, "ko bata magana ne?" Ta girgiza kai, "dan Allah ki faɗa min sunanki."
"Khadijah" ta faɗi sunan a hankali, kawai sai cewa yayi "Ana hubbu ki (I love you), ajabani ma arahu (I like what I'm seeing)."
Da sauri Khadijah ta rufe fuskarta, yayi dariya, yace "ko dai kina jin Larabci ne." ya faɗa da Hausa, ta ɗaga masa kai, "Masha Allah, what a coincidence." yayi murna dajin haka.
Ya fara yi wa Khadijah bayani tun ranar da ya ganta ya kasa sukuni, gashi ko sunan ta be sani ba, haka yayi ta neman ƙawar ta, ita ya ji sunanta randa ta yi kiranta, yace
"naji kin kira sunan ta amma na manta, inata tunani a ƙarshe na kira Malam Hashim, shi ne mai kawo ma'aikata na yi mishi bayani yace be gane ta ba, duk yadda nayi ƙoƙarin kwatanta mishi ita ya kasa ganeta, sai yace min bari ya nemi Alkasim ya kawo wasu ma'aikata kila tana cikin su, akai ta kiran wayar shi bata shiga saida Malam Hashim ya je gidan su ya ke faɗa mishi layin sane ya samu matsala, suka taho suka same ni a FARSHA, shima duk bayanin dana yi masa be gane taba, haka na haƙura ina ta addu'ar Allah ya haɗa mu. Jiya da daddare na dawo daga kamfani sai kawai na tuno sunan ƙawarki kamar Zakiyya, na kira Alkasim na faɗa mishi na tuno sunan Zakiyya, yace min Zaliha dai, na ji wani daɗi kamar an yi min bushara da Aljanna, nace ya zo ya same ni a Kamfani tinda yace unguwar su ɗaya da ƙawartaki, Alhamdulillah gashi na same ki."
Ya faɗa yana murmushini, Khadija dai wani iri take jinta ta kasa magana, amma zuciyar ta kamar takarda take jinta dan farin ciki, tunani take a ranta ashe shima ya shiga yanayin data shiga. Ya katseta da cewa
"ina so ki bani dama." (duk maganar nan da larabci su ke yinta).
Ya tambayi ya aka yi ta iya larabci da kyar ta iya faɗa mishi a makaranta ne, ya tambayi gidan su ta faɗa mishi, babu nisa tsakanin su da su Zaliha, yace "tsallaken Niima guest Palace kenan? wanne block kuke?" ya tambaya, kawai Khadija sai tsintar kanta tayi tana faɗa mishi gidan su.
Ya sake tambayar ta yaushe zai zo dan shi fah da gaske yake don gaskiya ya ga matar aure, Khadija ta sunkuyar dakai tace "da wuri haka?" yace
"mai za a jira." shi da gaske yake, tace "zata gida."
Maman Zaliha ce ta fito zata fita unguwa ta gansu ya gaishe ta, tace "kina nan Khadijah."
Khadijah taji kunya, Mama tana ta murmushi daga yanayin fuskar ta, ta ji daɗin ganin su, tace "Madallah."
Khadijah tayi mata a dawo lafiya, ya kalle ta yace "ina ta jira ki tambayi sunana kin kasa, toh sunana Tahir Fadoul Al-arabey." ya faɗa yana dariya.
Da ƙyar Khadija ta ƙara ce mishi taza wuce gida kar a nemeta, yace "da ba rakiya zaki yi ba?" Yace bari ya sauke ta a gida, tace ah ah, babu yadda be yi da ita ba taki yarda, haka ya hakura ya ƙyale ta.
Bayan ya tsayar mata da ɗan sahu ya ciro kuɗi masu yawa ya ɗora mata a kan jakar ta yace sai ya zo gobe, sai da ya ga sun yi nisa sannan ya shiga motar shi ya tafi.
💫 UMAYMAH 💫
✍️A&A PEN
Follow our Whatsapp group via this linkhttps://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3
https://wa.me/+2348039352724
VOLUME ONE
EPISODE 3️⃣5️⃣
Da murna ta shiga gidan, Umma na ganin ta tace
"A'a harkin dawo?" Bakin Khadija kamar zai yage saboda murna tace
"eh Umma."
Tana bawa Umma amsa ta shige cikin ɗakinta, ta cire mayafi ta cire dankwalin ta, ta tsaya a tsakar ɗaki ta wani riƙe ƙugu, ta rasa inda zata saka kanta dan murna. Kan katifar ta ta faɗa ta wani ƙudun dune ta rufe fuska kamar yana ganin ta har yanzu, babu abinda take tunawa sai murmushin sa da yadda yace yana santa, wani irin daɗi take ji acikin zuciyar ta.
A ranar haka Khadija ta wuni a gida tana ta murmushi, ita kaɗai kuma saita rufe fuska, har Umma ta kula da yadda take ta fara'a, tace
"Oh Khadija kodai kyautar kujerar Hajji akayi miki yau ne, irin wannan fara'a da murmushi haka."
Khadijah dai bata cewa Umma komai ba sai wani murmushin data kuma saki mai sauti. Ana haka Munnirah ta shigo gidan suka ƙule a ɗaki.
Zaliha na dawowa daga Company direct gidan su Khadijah ta taho, ta shigo gidan a gajiye, suka gaisa da Umma, sannan ta tambayi Khadijah dan bata ganta ba. Umma tace mata tana gidan su Munnirah.
Sak Zaliha tayi, bataji daɗin haka ba, taso ta sami Khadijah a gida, dan bata jin yau zata iya rintsawa in bataji maiya kawo Ogan su wajan Khadijah ba, kai mema suka tattauna. Yau gaba ɗaya wunin fargaba tayi ko a Company bata yi wani akin kirki ba, gaba ɗaya hankalin ta yana gida. Allah Allah take ta dawo taji maiya kawo shi wajan Khadijah. Haka kawai inta tuna ta bar Khadija da Ogan su a gida suna zance sai taji gaban ta ya faɗi, wani abu mara daɗi ya tsaya mata a wuya.
Jikin Zaliha a sanyaye ta bar gidan su Khadijah ta tafi gida dan bazata iya zuwa gidan su Munnirah kiran Khadijah ba, tasan in taje ma ranta ne zai ɓaci. Dan haka ta barwa ranta zasu haɗu gobe zata ji koma menene.
Washegari da sassafe Zaliha ta zo gidan su Khadijah, tare suka karya Zaliha sai bugun cikin Khadijah take taji mai ya haɗa ta da Ogan su, kuma mai yace mata, amma cikin ikon Allah sai Khadijah tace mata yazo yi mata tayin yin aiki a Company ne shine tace Babanta ba zai barta ba, wanda hakan kuma tsarin Munnirah ne.
Tun jiya da Khadija ta bata labarin yadda suka yi da Tahir ta tsara mata haka, ta kwaɓe ta akan saura ta kwashe yadda suka yi da Tahir ta faɗa wa Zaliha.
Hankalin Zaliha bai kwanta ba saida taji ba abinda take zargi ne ya kawo shi wajan ta ba, har wata ajiyar zuciya ta sauke.
A ranar da yamma wajan karfe biyar duka suna gida dan yau Baba ma da wuri ya dawo, wani Yaro ya shigo yace ana kiran Khadijah a waje. Baba da Umma suka kalli juna da mamaki, ita kanta Khadijah sai taji zancen wani iri, dan tasan bata kula Samari.
Zaliha ce mai kula kulan Samiri a cikin su, amma ita da Munnirah koka tare su basa tsayawa su saurare ka bare ma ka biyo su gida.
Baba ya yunƙura yace bari yaga wane, Baba yana fita yaga Tahir a tsaye a jikin motar sa yasha jallabiya white color mai dogon hannu ya yafa shirami a saman sumar sa, saiya fito a Balaraben sa sak.
Baba suka gaisa da Tahir a mutumce, Baba yace masa shine mai neman Khadijah. Tahir ya sosa kai yace eh shine.
Abunka da Balaraben mutum babu wata kwana kwana ya faɗawa Baba inda yaga
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 18 Chapter of 29