viva. Umaima ta karɓa ta cika tace "masha Allah, toh sauko yayi haka"
Sadiq ya sauko yana kaɗe jiki yace "ina nawan? ya tambaya. Umaimah ta nuna mishi viva. Yace
"ke fa yar rainin wayo ce wlh. Umaimah tace "Toh naga dai ni na ce kazo mu je, ina rakiya ka yi min? Sadiq yace "Haka za ki ce? Gobe ma rana ce." Sai kuma tace
"haba nawan kasan ni da kai bata baci."
"ba wani nan"
"Toh ni wlh ma yara na zan bawa, na je mu yi Nishadi, lada fah zaka samu."
"Smart Allah ya yafe miki, daɗin bakin ki wanne ne ban sani ba, kyau ki yi aikin gidan redio. Sadiq ya faɗa.
"redio dai, wacce irin redio? ni da zan yi Babban aiki, da zan din ga juyi a kujera ana madam sama madam ƙasa."
Yace "Dan Allah mu tafi." suka rankaya Aminu yayi musu rakiya suka samu dan sahu dai dai junction din tarauni Sadiq ya sauka, ya bada 400 yace a karasa da Umaimah har gida tunda tana da kaya, magen sai kuka take suna yin gaba kaɗan tace ya sauke ta, tace "bani kuɗi na zan ƙarasa da ƙafa."
Mai mashin ya Ciro 50 ya bata. Tace "Haba mallam 100 zaka bani.
yace "me yasa baki sauka ba tun ɗazu?"
Sunata rigima dame Adaidaitan har wani mutum ya zo zai hau, ƙarshe shi ya kashe rigimar ya bata 50 naira dan cewa ta yi baza ta fita ba, ta doro kwalin mage a kai, ɗaya hannunta kuma rike da buhun Mangoro, tana tafiya tana hutawa, ta gaji sosai ta samu waje ta zauna bakin bishiya ta huta, ta ƙara tashi ta cigaba da tafiya, ta hau kan titin Sultan Road kenan Allah ya taimake ta taga Uncle Isma da abokan shi kamar rakiya yayi musu, tace "yauwa Uncle Isma taimaka min."
"daga ina?" Isma'il ya tambaye ta.
"kai dai taimaki baiwar Allah Uncle Isma"
Yana ƙoƙarin sauke kwalin kanta ta ce "ah ah bar min wannan, buhun ya fi nauyi shi zaka ɗauka." Yace "see you, kuma sai ki bani mai nauyin? ya karɓi buhun suka jera tare suka tafi gida.
******
Comment, we want to see alot of reaction thank you.
💫UMAYMAH 💫
✍️A&A PEN
Follow our Whatsapp group via this link https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3
https://wa.me/+2348039352724
VOLUME ONE
EPISODE 1️⃣4️⃣
Umma ce ta sakko ƙasa tana jajen Umaima "bayin Allah babu wanda ya gaa Umaimah ne? tun da kuka dawo daga makaranta ban saka ta a ido na ba." Amira ta ce
"nima ban ganta ba, ko tana dakin baba?"
Da yake wani lokacin sai ta yi tafiyar ta can ɗakin Baba tayi kwanciyar ta ayi ta nema ta a rasa, babu wanda yake kawowa tana can tunda ba wajen zaman mutane ba ne, sai daga baya aka gano tana shiga ta kwanta.
Umma tace "Amma Baban Khadija baya nan, je ki duba can ɗin ko tana nan."Amira ta miƙe ta nufi ɗakin Baba.
"Assalamu alaikum, sallama alaikum." muryoyin yara ya karaɗe falon, yan yara ne baza sufi shekera 4,5,6 zuwa 7years ba sai shigowa su ke. Umma tace "ah ah mutanen Umaima sun zo, sassannuku da zuwa to, ko kuna tare da Umaiman dama?" Umma ta tambayi Ikram wadda ta ke da ɗan wayo acikin su.
Tace wa Umma "Yanzu muka zo." Dai dai lokacin kuma Amira take sakkowa daga sama tace wa Umma "Bata dakin Baban."
Umma tace "toh ina yarinyar nan ta shiga kuma, Khadijah bata dawo ba balle nace ko suna tare, Amira duba min ɗakin Hakimi ki gani ko tana can." Amira ta tashi ta tafi dubawa.
Umma ta kalli yaran tace "Toh ku zazzauna mana, ah ah wannan ɗaurin fah Isi? inye Isi yammata. Suhaila tace "Maman mu tace tana gaishe ki." "ina amsawa, Khalifa wannan hular za a bani aronta?" Ya gyaɗa Kai yace "Baban mu ne ya siyo min.
"kaaaai na siyi wankan nan gaskiya."
Sallamar Aliyu ce ta katse Umma da yaran, ya shigo cikin falon Umma tace "Ah ah Babangida yau da wuri ka dawo lafiya dai ko? Aliyu yace "Umma lafiya Alhamdulillah tun ɗazu na dawo ma, wlh stress ne ya min yawa, kaina ne yake ciwo, naɗan jima da dawo ma a nan nayi sallar juma'a,." Da kulawa Umma tace "Allah ya sauwaƙe, ka sha magani? "Na sha Umma."
"To saika kwanta ka huta."
"Umma bata can ma" cewar Amira data dawo daga ɗakin Isma'il. Cikin jimami Umma tace "toh ni Maryama ina ta shiga?" "Wa ake nema" Aliyu ya tambaya. Umma tace "Umaimah ce tun da ta dawo daga makaranta ban sa ta a idona ba." Ran Aliyu a bace yace "hmmm duk abinda na yi wa yarinyar nan bataji ba ke nan? Umma dan Allah kar ki saka baki zanji gidan uban wa ta tafi. Umma tace "wa ya sani gaa yara nan sun shigo tun dazu su na jiranta, ina ganin bari na sallame su kawai Allah dai ya shirya"
Aliyu bai sake magana ba ya nufi compound ya kafa kujera ya zauna yana jira. Bari na gaa ta inda zata bullo ya faɗa a ran shi.
~~~~~*
LEBANON BEIRUT
Tahir ne a ɗakin shi yana ta bincika cikin wata ƙatuwar baƙar jaka, yana ta wasi wasi a zuciyar shi anya hotunan nan ba sa cikin jakar nan kuwa, a satin farko na auren shi da Zaliha ta tattare duk wani abu daya danganci Khadijah ta ƙone su saboda yawan kallo da dayake yi, waɗannan ma daga baya ya gansu acikin jakar.
Wani tsohon al amari ne daya faru dashi a shekarun baya kamar mafarki duk abubuwan da suka faru da shi suka rinƙa dawo masa, ganin abun yake kamar a bacci haka ya ke ganin su suna dawo masa, kai gaskiya ba a cikin hayyacin shi ya ke ba ya sani "HAYATEE" ya faɗa a hankali.
Wani sunane da ita kaɗai yake faɗawa. Ya zuge zip din bayan jakar da ya ke irin jakar nan ce ta matafiya tana da zurfi, yana zura hannun shi yaji kamar ya taɓa wani abu kamar takarda, ya zaro envelop ce fara, cike da fata a ranshi yace "Allah ya sa su ne."
Ya daɗe yana neman pictures ɗin amma ya rasa su sai yanzu ya tuno da wannan jakar, yana buɗewa hotunan suka faɗo, kala hudu ne hotunan biyu shi da Khadijah ne ajiki.
Ya kafe hoton da ida nunsa yana tuna ranar da sukayi hotunan, wata fita ce da suka yita a lokacin tana Amarya suka ɗauki hotonan a Studio 24, ta saka baƙar Abaya shi kuma da farar jallabiya a jikin shi.
Ɗayan ya ɗago yana kallo, ida nunsa har sunyi ja atamfa ce koriya mai jajayen flowers a jikinta, shi kuma shadda ce a jikin shi ruwan toka, sun yi dariya shida ita, sun yi kyau sosai, sauran biyun kuma duka Khadijah ce ita kaɗai ta saka wani orange lace rigar doguwaa ce mai buɗaɗɗen hannu kayan sun matukar haska ta ta yi ƙyau sosai, aka yi mata ɗaya hoton a zaune ɗayan kuma a tsaye.
Ya daɗe yana kallon kyakkyawar fuskar ta, ko a mafarki be taba kawowa ransa abinda ya faru zai faru ba, Amma shi mai tsakanin laifi ne a wajan ta ya sani, kuma yayi sakaci da Addu'a, kamar yadda Ummi ta ce.
Tun fitowar shi daga Asibiti daya sake samun nutsuwa Ummi ta rutsa shi sai ya faɗa mata ina matar shi Khadijah, dama tun yana jinya Yasir ya faɗa mata sun rabu saboda yawan tambayar shi da take yi.
Ummi ta yi faɗa sosai irin wanda bata taɓa yi masa ba, ya ga ɓacin ranta kwarai da gaske har fiya da tunanin sa, dan haka shi yanzu neman hanyar da zai je ga Khadija ya ke yi kamar yadda ya yiwa ransa da Ummi alkawarin zai nemota ya dawo da ita cikin rayuwar su in sha Allah.
"Zaliha Zaliha Zaliha (lan aghfir laki abadan) I won't forgive you. I betrayed the love of my life because of you. (La'a natulllahi alaiki)."
Ya tuna good old memories ɗin su lokacin da tana Amarya, suka je yankari game resort, it was a memorable event, "Ya Allah" ya faɗa a ran shi, ya tuna wata rana da ya dawo daga company ranar wata Alhamis Zaliha bata san ya shigowa ba a wannan Ranar komai ya warware masa, a wannan ranar kullin da tayi masa ya kunce, a wannan Ranar lulluɓin da aka yi mishi ya yaye, a wannan ranar ne kuma ya jefar da kwallon mangoro ya huta da ƙuda.
Ya rufe idanunsa zuciyar sa na masa zafi, zalinci na karshye an yi mishi, wannan wayar ita ta warware tuggun zaluncin da aka yi musu, ba zai ce Khadijah kaɗai ba aka yiwa, don duk abinda yake aiwatarwa a lokacin kamar amfani ake da zuciyar shi ana basa umarni, wani abun idan yayi can ƙasan zuciyar shi baya jin daɗi, amma sai yaji wani ɓangaren na zuciyar shi yana Ingiza shi a kan dole sai yayi, duk lokacin da yaji haka idan be aiwatar ba to bashi da kwanciyar hankali har sai yayi.
"Zaliha kin cuce ni kin raba ni da Masoyiya ta "Ya Rabb! Ya Rabb! Ya Raaabb!!!."
Ko lokacin da yake cikin doguwar jinyan nan yana fara samun sauƙi soyayyar Khadija ta dawo masa sabuwa, saiya zama na kamar bita ake yi mishi, kullum acikin kewarta yake, duk tsawon lokacin nan gangar jikin shi ne kawai a nan amma ruhin shi yana Nigeria.
Ya sake tuna wancan shekarun daya dawo gida wanda dawowar tashi yazo ne da niyyar ya ɗauki Ummi su koma Nigeria ya kaita har gaban Iyayen Khadijah su basu hakuri, yasan ba zai iya zuwa shi kaɗai ba, dan bashi da ƙwarin gwuiwar tunkarar family Khadijah shi kaɗai.
Tabbas yayi kuskure mai wahalar gyrawa dan har wanda ya karɓa mishi Auren ta Baba Isa saida ya saka baki akan yayi hakuri ya dawo da Khadijah, amma yayi kunnen uwar shegu dashi. Wannan dalilin da kunyar abinda ya aikata yasa bai tunkare saba ya yanke shawarar tahowa gida ya samu Ummi, ashe zuwan nashi tsautsayi ne ya ke ta fe da shi, don a ranar da abun ya faru, yana tafiya ne yana tunanin Khadijah da tunanin hanyar da zai fara nemanta, dan ko a waya baya samunta, duk yarda a ka yi ta canja layi.
Kaai dole ma Ummi ta bar shi yanzu yaje gaa Masoyiyar shi, ay jikin nashi yayi sauƙi tunda yau satin sa biyu kenan da fitowa daga Asibiti, ya sake rike hoton ya kura mishi ido yadda ta fito a hoton kamar ya kira ta ta amsa. wani abu kamar ruwa ya diga a jikin hoton ya shafa yana tunanin ina ya sami ruwa, sai da ya shafa fuskar shi ya gane ashe shi ne yake hawaye, shi kaɗai yace "Khadijah, ki yafe min, ki yi min Afuwa, ki dawo mu shimfida kyakkyawar rayuwar farin ciki"
Wata zuciyar ta ce toh idan tayi aure fah? yau shekara nawa rabon shi da ita? zuciyar shi ta doka "subhanallah" ya faɗa da sauri yana rintse ido cikin ƙunar zuciyar ya furta
"Allahuma laa sahlaa ilaama ja'altahu saahlah wa anta taj'alaal haxna ilaa shi'ita sahlaa. Ana qadim ilayk (im coming for you)."
******
Suna turo ƙofar gate ɗin da shi suka fara tozali ya kafa ya tsare yana jiran ta inda za ta shigo, idon su ya sauka a kan shi, Aliyu yace "shashasha wato har da shi. ya faɗa tare da jan tsaki, Ay Umaimah tunda suka Shigo kamar tayi fitsari a wando don tsurewa "yau na shiga dubu" tace da Uncle Isma da shi ma ya sha jinin jikin shi, amma da ke shi namiji ne sai be nuna karaya ba kamar Umaimah.
"Come here" suka ji muryar shi daya buɗe ta da fushi, Umaimah zare ido take ga kwalin mage a kanta meow meow meow magen kamar ta san kiran su ake yi tahau kuka. Aliyu yace "zo nan" ya kalli Umaimah
"kneel down my friend." hannunta na rawa ta sauko da kwalin magen ta yi kneeling a gaban shi "and you, sai na ce ka rage tsaho ko?" ya faɗa yana kallon Ismael "I will deal with you." shima yayi kneeling a gaban shi kamar masu neman gafara ya ajiye buhun a jefe"
"me ye a kwalin?" ta ji Uncle Aliyu na tambaya. Budar bakin Umaimah sai cewa tayi
"Ayya Baiwar Allah ce." ta faɗa tana rarraba ido.
"Assalamu alaikum, Anti Umaimah?" Suna ganin ta suka fara yowa wajan ta, Umaimah sai kifta musu ido ta ke yi, amma inaaa basu ko kula ba, yaranta ne ƴan Friday party, da taga da gaske su ke wajanta zasu zo, kafin su ƙaraso ta din ga yi musu nuni da hannu su shiga gida suka kwasa "yau a falo zamu yi?" Umaimah ba bakin magana ta dinga gyaɗa musu kai, bayan har suka wuce.
Uncle Aliyu yace "I don't want to repeat myself meye a kwali." magen kamar ita aka tambaya tahau kuka meow meow. "buɗe kwalin" ya faɗa a fusace. Hannuta na rawa ta buɗe kwalin, tana buɗewa mage ta kwasa da gudu. Aliyu ya kalli Magen yace ta tafi ta kamo ta.
Umaimah tabi magen da gudu, mage ita ma ta dage tana gudu, haka suka dinga zagaye cikin gidan har mage ta shigo cikin gida ta back door Baba Rabi tana aiki a kitchen ta gaa Mage ta shigo da gudu, Sai gaa Umaimah ta shigo da gudu tace
"Baba Rabi ina ta yi?" "Ciki ta shiga" ta bata amsa. Umaimah ta yi falo da gudu..
"subhanallah ke meye haka" ina bata san ma Umma tana yi ba, nan yara suka hadu suka hau bin Magen tana zillewa, su abun saiya zame musu kamar wasa, Umaimah tace
"yawwa ku taya ni, ku taya ni na kamata"
Suka yi ta zagaye falon Mage taki kamuwa ta basu wahala duk sun birkita falon. Umma ta koma gefe ta tsaya tana kallon ikon Allah, to sai magana take musu amma basa jinta, ta kama Magen kawai suke yi, da kyar aka kama magen nan, ta gama jigata Umaimah.
Umaimah tana fita da Magen yaran suka rufa mata baya. Yana zaune inda ta bar shi ta dawo ta tsugunna da Magen a hannu. Sai ga Amira ta fito da packs din sweet ta nufi yaran tace
"toh yara Umma ta ce a raba muku sweets yau antyn ku ba halin yin party."
Umaimah sai hararar Amira ta ke yi, ta rarraba musu duk wanda ta baawa sai su yi waving Umaimah "bye bye anty Umaimah."
Da alama akwai sabo a tsakanin su da yaran ta ƙarshen ce Ikram ta yi tsaye bayan ta karɓi sweet ɗin taki tafiya da yake tana da wayo ba kaman sauran yaran ba, sai da ta je wajen Umaimah har da jan hannunta tace "me kika yi anty Umaimah? Umaimah tahau kifta mata ido, amma yaro ba ruwanshi, tayi banza da su har Ismael ɗin kamar basa wajen. "Ikram wuce ki tafi gida" Amira ta faɗa.
"sai next week ko ta ja hannunta su ka yi hanyar gate. Ikram tana ta waiwayowa tana kallon Umaimah ta fita.
💫 UMAYMAH 💫
✍️A&A PEN
FOLLOW OUR WHATSAPP GROUP VIA THIS LINK https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3
https://wa.me/+2348039352724
VOLUME ONE
EPISODE 1️⃣5️⃣
Uncle Aliyu ya kalle su ransa a ɓace yace "ku ne ciwon kan gidan nan ko? tukunna ma daga ina ku ke?" Umaimah na durkushe a gaban shi ga mage ta sha matsa a hannunta tace "uhhhm uhhhm, dama na je gidan su wizard ne sai ta yi shiru. ya harare ta "shi ne, shi ne daga nan muka je gidan su genius." Aliyu yace
"you are comfusing me waye wizard, waye genius? ko basu da suna?" Da sauri tace "Sadiq da Aminu.
"ok Aminu da Sadiq su ne kawayen ki? Baki da ƙawaye mata sai maza, saboda ke kan ki a kwance ya ke ko, idan ba rashin hankali ba ina ke ina maza, shima wannan da ke banza ne ya ke biye miki" ya kalli Ismael daya sunkuyar da kai. shiya rakaki kenan tare kuka je?" "ah ah ni kaɗai na je..
"wa kika tambaya? wa ya baki iznin fita? Tayi shiru tana zare ido, ya daka mata tsawa "ba da ke nake magana ba." tayi ƙiri ƙiri da ido cikin tsoro, ba ita ba hatta Ismael ya tsorata da tsawan da Aliyu ya buga musu. Addu'a take a ranta Allah ya ce ce su ya kawo Baba gidan nan yazu.
Aliyu ya katse mata tunani da cewa "Meye a cikin buhun? "Mangoro ne." Umaimah ta bashi amsa. "daga ina?" ya ƙara tambayar ta. Idanu wanta har sun ciko da ƙwalla ta fara ƙoƙarin mayarwa, yace
"oh tun ban taɓa ki ba kenan? Za ki yi mai dalili in dai kuka ne." "A gidan su Aminu muka tsinko." ta faɗa muryarta na rawa ƙiris take jira ta fashe da kuka.
yace "good, yana kallon ƙaramin buhun da aka zuba Mangoron irin ɗan ƙaramin buhun nan ne na shinkafa mai cin kwano biyu da rabi, saida ya gama ƙarewa buhun kallo sannan yace wa Umaimah
"ɗauki buhun ki daga shi sama close your eyes and raise your hands up."
Umaimah ta kalli buhun ta kalli Uncle Aliyu, tunani take a ranta yadda ta sha gudun kamo mage duk ta gaji, sannan kuma yanzu yace ta ɗaga wannan ƙaton buhun. Tana cikin tunanin taji yace
"bani magen." Ta miƙa mishi. Yace "itama a gidan su Aminun kika roƙa?
"ah ah" ta girgiza Kai.
Ya karɓi magen ta ɗauki buhun mangoro ta daga daƙyar dan da gaske ta gaji, ta rufe ido, ya juya wajan Isma'il yace "kai kuma dauko karfen dana ke execise ka daga, ka zo nan na baka 3min." ya tashi be dade ba ya dawo da karfen irin yan ƙananun nan ne na excuse amma suna da nauyi. Yayi kamar yadda Umaimah ta yi, Aliyu yaɗan jima yana kallon su kafin ya tashi ya shiga ciki ɗauke da magen a hannunsa.
Uncle Aliyu na shigowa falon Umma ta tare shi da cewa "Babangida wai magen waye ɗazu naga Umaimah ta shigo tana binta, ina ta mata magana bata kula ni ba tana ta gudun kama Mage." Uncle Aliyu ya miƙawa Umma Magen yana cewa "jikar ki ce ta roƙo, wai yarinyar nan na tambaye ta meye a cikin kwali sai cemin tayi Baiwar Allahce, yarinyar da har yanzu rainon ta ake yi shine ta karɓo mage."
Umma bata son Mage amma tinda Umaimah ce ta karɓo haka ta karɓe ta tana cewa "wannnan dai ni aka kawowa aiki kawai, ba wani abu kiwon mage ay lada ne dashi." Aliyu ya girgiza kai "Umma ku kuke ɗaure mata gindi, na ɗauka za kiyi faɗa ko ki ce a mayar da ita tinda bakya so? bana son cewa a mayar tun farko bansan me zaki ce ba, yanzu na ji ra'ayin ki, shi ke nan Allah ya taya ki riƙo." Umma ta ce "ya zan ce a mayar tinda tana so."
Aliyu yace "ay gata nan, yanzu jikokin naki sun zama biyu." "ina Umaiman? Umma ta tambaya. "tana waje." yana faɗan haka ya fita da sauri dan kar ma Umma ta ce mishi wani abu.
"Wannan mutumin akwai takura wlh ina tausayawa yaran shi da za su zo." Umaimah ta faɗa tana ajiye buhun hannun ta.
"wallahi hutawa zanyi kanya dawo." Ismael da idon shi yayii jaa dan wahala ya ce "maza gara dai ki mayar wallahi kafin ya zo ya ƙara miki wani hukuncin." ya na rufe bakin shi sai ga shi ya fito, Umaimah ba shiri hannu na karkarwa ta ɗauki buhun ta daga sama.
Aliyu yace "oh ajiye wa kika yi kenan? ya kalli agogon hannunshi "kin ƙarawa kan ki 30mins." ya koma ya zauna yana danna wayar shi.
Horn akayi Mallam Idi ya buɗe gate mota ta shigo, Umaimah kamar ta taka rawa ganin motar Baba ce ta shigo.
Uncle Aliyu ya miƙe yaje ya buɗewa Baba mota, "sannu da zuwa." "yauwa Babangida. Baba ya amsa hankalin shi na kan su Umaimah. Baba ya ce "wanne laifin Uwata da Hakimi su ka yi ne? ay Umaimah na jin Baba ya tambaya yiff ta watsar da buhun Mangoron ta kwanta tana mayar da numfashi, da sauri Baba ya zo kansu yace "kai Hakimi ajiye karfen nan ku same ni a falo." Ismael ya miƙe.
Baba ya jijjiga Umaimah ta yi likimo taƙi tashi "uwata, uwata." tana ji ta ki motsi Baba kawai saiya ɗauke ta ya shiga da ita cikin gidan. Umma na ganin su ta taso da hanzari "lafiya Baban Khadijah? Babangida me ya faru?" Ismael ya shigo falon idon shi ya kaɗa yayi ja, ya zauna a ƙasan carpet.
"Babangida yarinyar nan har da kuruciya fah, a dinga binta a hankali zata daina." Umma ta faɗa tana sake kallon Umaimah da ta wani saki jikin ta a hannun baba.
Baba ya kalli Umma ta yi shiru, yace "bani ruwa ki gani." Umma ta kawo ruwan ya shafa mata ta ki motsawa. Aliyu a ransa yace lalle yarinyar nan yar rainin hankali ce, abin haushin kuma kullum idan zai yi mata hukuncin Kakanninta su hana shi, amma ba komai za su haɗu ne wani lokacin. Uncle shi kaɗai yake maganar a zuciyar shi.
Baba ya kalli Umaimah yace "Shikenan Hakimi ku dauki tsarabar nan kai da Auta, tinda ita wannan har ta yi baccin gajiya. zumbur Umaimah ta miƙe tace "ina tsarabar?" Baba yace "au da kina ji na kika yi shiru?" ta ɓata fuska.
Yace "shikenan Hakimi ku shiga ciki zan kira ku an jima, ku karɓi tsarabar."
Umaimah tace "wlh na gaji Siyama ko zaki dauke ni? Umma tace "haram wlh ba zan iya ba." zata fara taɓara suka haɗa Ido da Aliyu, ita gaba ɗaya ta manta yana nan ma, suna hada ido ta haɗiyi maganarta ta yi ciki da sauri.
Tana barin falon Baba yace "Babangida kai ne a matsayin uba, ina jin daɗin yadda ka ke yiwa na kasa da kai tarbiyya ba abinda zan ce maka sai dai nace Allah yayi maka albarka."
Umma dai ba haka taso Baba yace ba taso yayi masa faɗa, tasan Umaimah ba saiti, Amma wani lokacin hukuncin Babangida
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 8 Chapter of 29