Share this page
Bichi ina jinka ya akayi?" Commissioner ya faɗa, Baban sama ya faɗawa commisioner abunda ya faru, commisioner ran shi a bace yace "pls Bichi handle the matter and punish the culprit." "yes Sir.' ya ajiye wayar suna shiga aka hau Sara mishi yace "ina yaran da aka kama?" wani ɗan sanda yace "suna waje ana kiran Dpo ne sabida cell ɗin yayi kaɗan." Suka fita da Baba, suna zuwa wajen motar mutane a tsautsaye Umaimah na ganin Baba ta tafi da gudu ta rungume shi, "Hakimi Baban sama ya kira "ismael ku je mota." Baba ya mika musu key "ba suyi muku komai ba ko?." Baba ya tambaye su, Umaimah ta ɗaga kai. "Muhammad tafi dasu gida bari na gama da case ɗin nan." Baban sama ya faɗa, ya kalli yaran da aka kama yace a mayar da su inda aka ɗauke su, Baba yace "zan dawo na ɗauke ka "ah ah commisioner zai zo zamu shiga meeting don't mind." "okay mu tafi." Umaimah ta riƙe hannun Baba "pls Baba ka taimakawa bawan Allah nan." ta nuna masa Almajirin da ko sunan shi bata sani ba, "me zan mishi? "ya zauna tare damu Baba." Almajirin ya durƙusa ya gaishe da Baba, "toh mu je gidan ayi maganar." ***** Khadijah tunda suka zo ta dage ibadah kawai ta ke yi sosai ta ke yin addu'a Allah ya basu zaman lafiya yasa ta yi auren nan kenan, duk wani abun ki Allah yayi mata maganin shi. Munnirah ta fito daga Toilet tace "my sis ki yi sauri ki shirya mu wuce Jumma'a ce da wuri su ke rufe hanya. "ay na gama." Khadijah ta saka hijab ta rataya jakarta, "oh jiya till down kuka yi da Ahmad a waya tun ina jin ki har bacci ya kwashe ni." Munnirah ta faɗa, Khadija ta yi mata banza har sun kai ƙofa Khadija ta koma ta ɗauki sallaya koda cikin harami ya cika sai su yi sallah a haraba, suna isa aka tada sallah suna sallamewa Askar suka fara kora "Tariq HajiyaTarinq." ga shi ana ƙwalla rana, Munnirah tace "mu ƙarasa cikin harami wasu yanzu za su fito tunda an idar da sallah." Khadijah ta tashi suka tafi tana mita ko addu'a ba su yi a nutse ba, suna shiga sun zauna ke nan wata gajiyayyar tsohuwa ta matso kusa da su, "sannun ku. "yawwa sannu." suka amsa, "baku gane ni ba ko? Munnirah ta kalle ta Khadija ta ƙura mata ido a tare suka ce "wlh ba mu ganeki ba." "ikon Allah." sai kawai ta fashe da kuka har da shassheka, wani irin gunjin kuka take yi jikinta har rawa yake yi, "Baba yi haƙuri ki yi mana bayani, idan rashin gane ki da muka yi ya ɓata miki rai kiyi haƙuri." Khadijah ta faɗa, "ah ah ah baku ɓata min rai ba shi Allah ba Azzalumin sarki ba ne, ku yafe min ƴaƴana, na san an zalunce ki Khadijah." Khadijah ta kalle ta, kan su ya kara kulle wa suka kalli juna "kin saka mu a duhu Baba yi mana bayani yadda zamu gane." ta rufe fuska da tafin hannunta ta kara fashewa da kuka "Mama ce, Maman Zaliha mai ƙosai." gaba ɗaya su Khadija suka sandare a zaune, "Mama." Munnirah ta maimata, ta gyaɗa Kai, "ku yafemin ku yafewa Zaliha alhakin Khadijah sai bibiyar mu ya keyi." Munnirah ta ce "Mama mu futa daga waje nan ba wajen zance ba ne." Jikin Khadijah a sanyaye ta kasa tashi sai da Munnirah ta ɗago ta suka fita. "Ni daga ina zan fara daga farko dai nasan Zaliha nasan son Mijinki na yi ƙoƙarin hana ta, daga baya sai na kasa tsawatar mata, abun baya mun daɗi har ga Allah." "amma Mama me yasa ba ki neme mu ba? Munnirah ta katse ta, Mama ta share hawaye "wlh daga farko nauyi na ji da kunya na kasa zuwa daga baya kuma naje unguwar kwata kwata ta canja na rasa inda zan same ku." Ta riƙe hannun Khadijah "ki yafe mana wlh tunda Zaliha ta haɗa kai da Suwaiba shike nan ta zama wata iri, ni nasan Suwaiba shedaniya ce gashi Zaliha yau shekara 5 ke nan bana samunta a waya na gaji da yawo da hankali da ake min na taho ne manata, Suwaiban ita ta karɓi gidan mu ta shirya min tahowar yau wata na 6 ina walagigi ban same ta ba sai yawo ake min da hankali." tausayin Mama ya kama Khadija tace "babu komai Mama na yafe ni tuni." "nagode nagode." Mama ta faɗa "ku yi haƙuri." Munnirah ma tace "ya wuce Mama." Khadijah ta bawa Mama riyal 1000 "zamu koma masauki." don ba zata iya wani abu ba kuma, sun so sai bayan isha'i sun koma amma ganin Mama da Khadija ta yi ya fama mata ciwon da take ta kokarin danne wa, "Allah yayi muku albarka." Mama ta fada, "Amin." Munnirah ta amsa, har zasu tafi Mama tace su bata kwatancen inda suka koma Munniran ta rubuta mata a takarda suka barta, suka tafi tana hawaye. LAGOS Fahad tunda ya fito daga Asibiti he is restless yau Baba ya kira shi a waya yake faɗa mishi sun tsayar da date din auren su, ya ɗauko waya ya fara typing message. *Hi, Hope this meet you well, Aysha I need to be honest with you, I want to make it clear that we were never in a romantic relationship, and I'm not ready for marriage I think it's essential to be upfront with your parents about this,.so please let them know we are just friends, and not lovers o hope you understand I appreciate.* Daya ke rubutu ne yayi typing da yawa ya tura message ɗin. Ya fara sana'ar ta shi ta arranging kaya a wardrobe. Aysha na wajen saloon taji ƙarar message, tun safe wani nishaɗi take yi tunda Daddyn su yayi mata bayani an je neman auren ta kuma an bayar, sun karɓi dukiyar aure take murna, ga ance Uncle ɗin shi Abokin kanin Daddy ta ne har sun nemi alfarma za a haɗa ɗaurin auren a Bichi ayi gaba-daya dana ƴar su kuma sun amince, idan bata ɓata lissafi ba yau saura 2weeks ta zama Amaryar shi, taji daɗin labarin ba kaɗan ba, Sa'ad ne ya faɗa mata Fahad baya nan ya je documentation, wani farin ciki take ji mara misali, saidai tinda aka saka musu ranar auren Fahad be taɓa kiran taba, amma babu komai tasan halin shi dama she pray she is not making the wrong decision don gaskiya tana son Fahad ba kaɗan ba, wuyar ta ayi auren zata koya mishi sonta. tana cikin wannan tunanin ta ji ƙarar text ya shigo wayar ta kamar ta share sai kuma ta dauki wayar ganin saƙon daga Fahad ne jikin ta na rawa ta buɗe. 💫 UMAYMAH 💫 ✍️A&A PEN Follow our Whatsapp group via this link https://whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3 https://wa.me/+2348039352724 VOLUME ONE EPISODE 5️⃣6️⃣ Aysha ta zuba wa wayarta ido ta karanta massage ɗin yafi a irga, tayi wani murmushin mai ciwo saidai tayiwa kanta alkawarin zata bawa Fahad mamaki. Ita a tunaninta gani take wuyar ta ya shigo hannu a matsayin ta na mace mai ilimi shekaru da waye wa tana ganin zata iya amfani da damar ta tajuya shi duk wannan zafin kan da halin shariyar da yake mata dole zai dena wuyar ta dai ayi Auran. A tunaninta fa ke nan. Wannan tunanin nata yasa tayi murmushi kawai ta share shi taci gaba da babgoginta ta. Su Khadijah sun sauka lafiya karfe 4 na yamma suka iso gida, lokacin su Umaimah na Islamiyya sai dawowa suka yi suka tarar da su murna a wajen Umaimah ba a magana, "Ammina ina saƙo na." Umaimah ta tambaya, "haba kya bari ta huta tukunna ta kwaso gajiya, mutum yayi tafiya daga dawowa ki dame shi." Umma tayi maganar tana harararta, Munnirah ta ce "zo nan ki ji." ta koma kusa da ita, Amira na shigowa taje ta rungume Khadijah, "ina kika tsaya Autar Umma." "hadda na tsaya bayar wa." "Masha Allah, ina Hakimi? "Yana hanya sun tsaya da abokin sa Abbas." Umaima ta faɗa, Khadija ta ce "mun yi waya da Ibrahim yace shima zai zo weekends." Umaimah tayi tsalle akan kujera "yeah pull house wlh Ammi da ba kwa nan gidan babu dadi." Umaimah tunda suka dawo daga Lagos tayi noticing kirginta ya sake fitowa, amma ita wa zata faɗawa ita kaɗai take tunanin ita mafa ya ci ace ta fara saka bra, in taga Amira ta saka burge ta take yi, gaskiya ita ma tanaso ta fara sawa dan nonon ta yafi na Amira girma kawai dan bata da manyancen tane. yanzu su na ss1, karatu harya fara nisa Umaimah na science class, Amira tana Art, friends ɗin ta su Anisa har sun fara period amma ita har yanzu shiru Amira ma ta dade da farawa, ganin haka yasa komai na yamma ta sai a siyawa Amira banda ita, ko Ammi da ta dawo daga ummara ta siyo mata bras masu kyau amma ita aka kwaso mata su Teddy bear, Wato ita a yarinya su ke kallon ta har yanzu, ita kaɗai ke zancen zucinta sai kuma ta mike bari dai taje wajen Umma. Tana zuwa ta samu Umma tana jan carbi bata jima da idar da sallar walaha ba, Umma ta kalli yadda ta tsaya mata akai "me ye kika tsaya min a ka?" Umaimah ta wani juya ido "Wai Siyama baki gane ba?" me zan gane? Umma ta faɗa still tana kallon ta, "hmmmm baki kula da wani abu ba." "Umaimah bana son shirme fa wanne abu zan kula da shi? Umaimah ta nunawa Umma kirjinta da yatsa, still kumma bata gane ba "Siyama ba ki dauki haske ba? Umaimah ta faɗa tana ɓata fuska, "Ni ban gane ba idan zaki buɗe baki ki yi magana toh idan kuma ba zaki yi magana ba je ki kar ki tayar min da hankali, har kinsa na ɓata lissafi." ta zumɓura baki "kin karya kumallo ma kuwa? Umma ta tambaye ta, Umaima ta kwashe da dariya "meye kuma kumallo? Siyama gaskiya gargajiya ta bi jikin ki, a Lagos Mami sai dai ta ce kun yi breakfast, ko tace ku fito ku yi dinner irin na yan gayu." "ni ay ba yar gayu bace." "toh kuwa dole Baba ya auro yar gayu ma'aikaciya." Umaimah tayi maganar tanawa Umma dariya, "Yawwa Siyama yaushe Uncle Ismah zai dawo daga lectures? "ke zan tambaya ai kunfi kusa." Isma'il tini ya samu admission a BUK yana karantar electrical enginering, ya Aliyu ya siya mishi mota 206 saboda zuwa makaranta, amma saida ya buga mishi warning ɗin duk randa yaga Umaimah a driver seat to zai ƙwace motar, Baba ya siya mishi waya. "gaskiya yayi ya dawo." yayi miki me? "Sirri ne. ta faɗa, Umma tace "Dan Allah je ki kin sa na ɓata a lazimi." Khadija ta shigo da waya a hannunta ta miƙawa Umma Dada ce, Umma ta karɓa sai salallami ta ke yi. Uncle Isma tun ɗazu nake jiran ka. Umaimah ta faɗa tana kallon sa, "me zan miki? A gajiye na ke pls ki barni na huta." "taimako zaka yimin fa." "ina jin ki." "ka ga." tayi masa pointing kirjinta kamar yadda tayiwa Umma bata gane ba, "mene ne?" "rakani kasuwa zaka yi? Me zaki siya? "Abu zan siya tunda ni Allah ya sa ba cima zaune ba ce sai na siyawa kaina." Isma'il yace "wai me zaki siya ne?. Ta ƙara nuna mishi kirjinta, "Uncle Isma wai kaima baka gane ba?" ya tsaya yana kallon ta "ni bangane ba. ta ƙara nunawa yace "rigar wuya? ta girgiza Kai "ah ah ka kusa." "rigar kirji ke dalla ni fa ba mace ba ne ki nemo Amira ku je ta raka ki." sai da yace kirji ya gane me take nufi, yafi kowa gane Umaimah shi Wallahi kunya ma ta bashi. "shi ke nan Uncle Isma." tayi kalar tausayi har zata fita yace "tsaya na kai ki ina ne? "Sabon gari." Ta faɗa da murnar ta, yace "kirawo Amira mu je tare sabgar mata ce wannan." "Uncle Ismah dan Allah mu je mu kaɗai, kana gani ba ta ni suke yi ba." "Toh naji shirya ki same ni a mota." Kawai Umma sai ganin ta tayi ta saka hijabi tace ina zuwa? "Ina zuwa Siyama." da sauri ta fita, Umma bata damu ba tunda ta ga Hakimi ya fita tasan tare za su fita, ko siyan kayan sana'ar tasu zasu oho dan tare su ke zuwa abinsu, ko kai wa Barakat store ma tare suke zuwa, dan yanzu kusan stores uku na karɓan kayanta. Suna zuwa tace "Dan Allah mu shiga tare." ta rinƙa yi mishi magiya ba yadda ya iya doke ya bita suka shiga shagon wani Inyamuri ta ɗauki guda uku ta shiga inda ake gwadawa ta gwada ta fito sun yi mata kowacce ɗaya akan 1500 ya siyar mata ta rinƙa ciniki "haba oga I'm your customer." dole ya rage mata 200." karshe dai Isma'il ne ya biya kuɗin suka fito. ko da suka fito yamma ta yi sosai sun kamo hanyar gida tace ya kai ta gidan su wizard zata karɓi note book ɗin ta yace karta zauna magrib ta kusa. Umaimah ta tarar da Maman su Sadiq da yayan shi har da Sadiq suka rike ta da hira tace tare da Uncle Ismah suke yana waje, suka ce ya shigo da ƙyar ya shigo aka haɗu da Huzaifa yayan Sadiq nan suka shantake har bayan isha'i, Ismael ya manta wayarshi a silent sai can ya farga ana ta kiran shi yaga 10missed calls Umma 3, ya Aliyu 4, Khadija 1 sai Baba 2, Isma'il ya ce "zamu wuce". Huzaifa yace "tun yanzu? ya kalli Umaimah yace "bani digits ɗinki." "bata da waya." wizard ya faɗa, ta harare shi ta bashi ta Uncle Ismah suka fito. Gaba ɗaya suna zaune a falo har Ibrahim da ya iso tin ɗazu. Suka yi sallama suka Shigo, "daga ina kuke? Aliyu ya tambaye su da tsawa, Baba yace "Hakimi ina wayar ka? kun ɗaga mana hankali." Kansa a ƙasa yace "tana silent ne." Umma tace "haba Ubana da girman ka kake biyewa Umaimah." suka durƙusa a tsakiyar falon Sasi ta zo wajen Umaimah ta ja ledar hannunta ta yaga bras suka zubo Aliyu ya kalli Ismael, ya kalli bras ɗin "meye wannan?" ya kafe Isma'il da ido, Ismael ya sunkuyar da kai yace "na Umaimah ne." Umma jikinta yayi sanyi ko shi ne ɗazu ta zo tana mata Inkiya bata gane ba, Umma ta ji babu daɗi, tsam Khadija ta miƙe daga wajen. "kai jama'a gara dai tayi auren nan ta huta taɓ har Umaimah tasan ta siyo bra lallai ta girma." Khadijah ta faɗi haka a ranta tana wa kanta dariya ta haye sama. Sam Aliyu ya manta Baba yana wajen yacewa Isma'il "Dan ubanka Daudu zaka yi? Nace daudu zaka yi? Me ya haɗa ka da kayan mata?" Baba ya girgiza Kai yace "basu da laifi Babangida, uwata tashi ki je." Aliyu ya cewa Isma'il "kaima jeka jirani a waje." Ibrahim ya fita yana guntse dariya ga kunya ga dariya, kai wannan ƴa tasu. Baba ya kalli Umma yace "hau sama ki ɗauko min hula." ta tana tashi ya cewa Aliyu "ka yi haƙuri ba su da laifi, abunda ya kamata Ummanka ta yi ne." fuskar shi a haɗe yace "toh Baba." "Yawwa kar ka yi mishi komai." ya amsa wa Baba ya fita. Umma na dawowa Baba ya balbale ta da faɗa "yarinya ta fara girma saboda sakaci irin naki har taje ta faɗawa Hakimi, irin waɗannan abubuwan na mata ba kya saka mata ido sai Hakimi ita uwarta tana kawaici ta bar miki ita, nan da sati ɗaya ma bata nan kece dai tare da ita." Umma tace "ayi haƙuri na karɓi laifi na zan gyara, nima ban ji daɗi ba. Kallon yarinya nake mata har yanzu shi yasa." "yarinya? ba sa'ar Amira ba ce?" "haka ne, ko dan Amira tafi ta manyance ne yasa nake mata kallon yarinya saboda shirmenta ba a ganin girman." ***** Saura sati ɗaya bikin su Sa'ad har an kai lefe an gama komai sai jiran lokaci waliyin Fareeda ya kira Baban ABU akan su yi haƙuri Fareeda ta ce ita ta fasa auren shi, abun ya kiɗima su sosai, Sa'ad ya shiga damuwa, Iyayen Farida kananan mutane ne, da sun san bata son ɗan su suka amsa musu, lokacin da suka kira Baban ABU akan za su zo shiya ɗauka canja lokaci zasuyi ko basu gama shiri ba, kawai sai ganin su yayi da kaya sun dawo da lefe da sauran kuɗin Aure, hankalin Baban ABU a tashe ya kira Daddy, yayi masa bayani, Daddy yaji babu daɗi sosai dan duk sun san yadda Sa'ad yake san Farida sam shi bai iya boye abinda yake soba ba kamar Fahad ba da ba'a gane cikin shi. Daddy yana faɗawa Dada yadda akayi tace shike nan sai ya auri yar Uwar shi zuwaira, Daddy yasan tunda ta faɗi haka babu mai iya sako da ita sai Magaji (Baba) shi kaɗai ne a cikin su in yayi magana Dada take sauran shi. Baba lokacin da ya samu labarin fasa Auran Sa'ad a wajen Daddy abun sam baiyi masa daɗi ba ya tausaya wa Sa'ad, a ƙalla a ba shi lokaci ya nutsu duk wacce ya aura yanzu ma ba lalle ta samu nutsuwa dashi ba. Wannan yasa Baba ya kira Dada yana sake bata hakuri dayi mata bayanin halin da Sa'ad yake ciki, ya tausasa murya yace "Dada kin ga kuma zuwaira ƴar mu ce kar azo a ɓata zumunci." Dada ta sauke zuciya, "shike nan Magaji Allah ya sa hakan shi ne mafi alkhairi." "yawwa Dada wani baya auren matar wani." "haka ne Magaji Allah yayi maka albarka." da haka Baba ya lallaɓa Dada tabar maganar. LAGOS Amal keta bawa Sa'ad baki duk irin dauriyar sa sai da ya zubar da hawaye. "Ashe ni kaɗai na ke abuna Farida bata sona me mata suke so a wajan na miji da bani dashi? Amal did I deserve such betrayal from her? I love her with my heart, but she rejected me, What is that women want? I'm confused and hurt." ya faɗi maganar hawaye ya zubo mishi, "just one week to our wedding tace ta fasa aure na." Fahad ya rungume shi, he hate to see his brother sad, his brother is a happy person ya buɗe baki da ƙyar yace "Ad take heart is okay please." Yayi maganar yana buga bayan shi, sai ajiyar zuciya yake yi a jikin Fahad, he wish shi ne Aysha tace ta fasa Auran duk messages ɗin da yake tura mata she ignore him, "why me? why me?" Kukan Sa'ad ya dawo dashi daga tunanin daya tafi, da sauri ya saka ɗan yatsa a lips ɗin shi alamar yayi shiru. Amal ta miƙe ta haura sama jiki a sanyaye ita kanta kukan ta ke yi ba ƙaramin tausayi Sa'ad ya bata ba, ita zata bawa kowa labarin san da Sa'ad yake yiwa Farida dan tinda aka sa Auran nan itace abokiyar shawarar sa. Komai ya gani yace wannan zaiwa Farida kyau Please ku haɗawa Farida da kaza tana so. ***** 💫 UMAYMAH💫 ✍️A&A PEN Follow our Whatsapp group via this linkhttps://whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3 https://wa.me/+2348039352724 VOLUME ONE EPISODE 5️⃣7️⃣ Yau laraba ana ta shirye shiryen bikin su Khadijah, gobe Alhamis kamu, da walima za a yi yan uwa sun hallara, Sa'ad ne me yiwa Fahad gayyar daurin aure, a fadar Babancikin gida za a ɗaura auren su Yaya Surayya, Ya Amal, yaran Baba sama su Yaya Hindu da samarin Baban ABU Farouk da Fa'iz dukan su sun zo, iyayen su mata ma duka sun zo duk da Aunty Maimuna matar Baban ABU, da Aunty Zainab ba su sauka a gidan Baba ba, suna gidan yayar Aunty Zainab, Dan ita Zainab matar Dr haushin Umma take ji, cewa ta ke ita ta bawa mijinta kawar yar ta ya aura, Mami da Aunty Bilki matar Baban sama su ke tare da Umma, Hajiyar Munnirah ma tazo sun fita da direban Baba Mal Musa zuwa wajen da aka kama na walima. Baban sama ya haɗa kan yaran su maza yana musu nasiha, matan suna ɗakin Khadijah, Daddy ya karɓi zancen ya kalli Fa'iz da Farouk da Ibrahim yace "kuma ya kamata ku motsa nan da wani lokaci, ku san me kuke ciki tunda dukan ku aiki ku ke, a cigaba da rike amana." Baba ya kalli Fahad, "Dattijo ka yi haƙuri ba takura maka muka yi ba, wannan shi ne cikar mutuntaka." ya gyada Kai da kyar yace "Nagode." Sa'ad baba ya kira shi yace "ka yi haƙuri ka ji, babu komai dama Allah be kaddara matarka ba ce wani baya auren matar wani." "Tabbas." Baba Dr ya faɗa, Sa'ad da kana ganin shi kasan ya rame yace "Nagode Baba." "Aliyu Zakin ma'aiki Ibrahim mantawa ka yi da wannan tuzurun ne? ɗazu ka ke yiwa kannen shi magana." Daddy yace "haka fah." Baba yace "gara dai ku faɗa mishi." ya sunkuyar da kai, "kullum fuska a tsume matan ma tsoron shi za su ji." Baba ya faɗa, aka yi dariya, Daddy yace "rabu da iyayen ka duk wacce ka gani kana so ka zo kawai mu yi magana." Aliyu yayi yaken da be kai zuci ba. ****** Su Amal suka haɗu dasu yaya Hindu cousins ɗin Khadija suna ta yi mata tsiya, ita dai ta na kallon abun kamar da gayya so su ke tayi kuka duk daurewarta, Yaya Surayya ce mai cewa ta taho mata da kayan bacci zafafa, "wannan duhun kan naki dole fah ki ajiye, haba ga ki kalar shanawa." "ay na taho mata da English wears da zata tashi kai, kisan wancan auren na kuruciya ne." cewar Amal, duk da dai kin riga mu shiga kwaryar manya."

Chapter 28 of 29