dukkan ku, ok then" sukayi Sallama ya ajiye wayar.
Daddy ya kalli Mami yayi smiling, tace "kai da sa'ad ne?"
"yeah" kin ji conversation din na mu ay, I'm restless nasan Dada kiranta akan yaran nan ne da Khadijah, nafi tausayin Khadija, atleast yanzu ta ɗan samu nutsuwa" Mami ta miƙa mishi tea ya karɓa ya yi murmushi ya hada da hannunta "matso kusa mana your highness" nan suka cigaba da tattaunawa.
******
Ya ku ka ji episode ɗin? manyan nan fah sun iya soyayya Baba da Umma ne ko kuwa Daddy da Mamy, soyayyar waye ya fi burge ku please comment.
💫 UMAIMAH 💫
✍️A&A PEN
Follow our Whatsapp group via this link https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3
https://wa.me/+2348039352724
VOLUME ONE
EPISODE 1️⃣2️⃣
Daddy yace "har gwara Sa'ad he is fit for aure, amma Dattijo yanzu ayi mishi zancen aure ma kamar an ɗauko dala da gammo ne, Mami ta ja numfashi tace "I wish I can change his condition, i pray he overcome change ɗin (COD) ta faɗa a raunane "is his destiny" Daddy ya faɗa yana kwantar da ita a jikin shi yana dan buga bayanta. "he will in sha Allah" ta kara maimaitawa.
"in sha Allah."
Shi kansa Daddy matsalar ɗan nasa mafi soyuwa a cikin ƴaƴan sa tana damunsa, kawai jarumta ce irin ta maza yasa yake nuna ciwan nasa ba komai bane, saboda ya kwantar wa Mami hankali, Daddy ya sauke ajiyar zuciya yana sake tuno bayanin likita akan cutar OCD.
"Alhaji Obsessive-Compulsive Disorder (OCD) is a mental health condition characterized by recurring, intrusive thoughts (obsessions) and repetitive behaviors (compulsions) that an individual feels compelled to perform. These obsessions and compulsions can cause significant distress, anxiety, time consumption, social isolation and impairment in daily life.
Common symptoms:
CONTAMINATION OCD: Excessive cleaning or handwaship.
CHECKING OCD: Repeatedly checking locks, appliances, or other things.
Intrusive thoughts or images.
JUST RIGHT OCD: A need for symmetry, order, or exactness, often accompanied by repetitive behaviors like arranging objects.
Treatment options, such as Cognitive Behavioral Therapy (CBT), Exposure and Response Prevention (ERP) and Medication, can help manage symptoms and improve quality of life.
Ataƙaice.......
OCD ( Obsessive Compulsive Disorder)
Matsala ce da ta ke sa mutum yawan maimaita abu fiye da sau ɗaya, misali yawan wanke hannu akai akai yana cikin alamomi na OCD yawan tunani mara fasali, haka kawai tunani mara fasali za su yi ta ratso wa mai ciwon wato (Obsessive Compulsive Disorder), ciwo ne na tunani da ayyukan da ake maimaita shi (is a mental and behavioral condition characterize by intrusive thought, obsession and repetitive behaviour).
Haka kawai mai ciwon zai ji tunani mara muhalli yana kutso mishi, zai ji zuciyar shi na raya mishi abubuwan da idan be aiwatar dasu ba ba zai samu nutsuwa ba, masu ciwon basa shiri da ƙazanta, rashin tsafta nasa su shiga cikin wani hali, suna da kyankyami sosai, suna da yawan wanke hannu fiye da ƙa ida, suna son arranging komai na su, ba sa son hargitsi, komai sai an jera shi.
Suna da bin kwakwafi ko maimaita ayyuka, sunada mantuwa ko saurin shiga kokonto, misali idan sun yi abu sun din ga tashi suna dubawa ko sun yi kuwa. Misali mai cutar inya rufe ƙofa, sai yayi ta sake komawa yana duba wa ko ya kulle kofa kuwa, Ah ah ya kashe switch ɗin kuwa, gas ɗin ya kashe shi kuwa, suna rasa nutsuwar zuciya, suna da yawan maimaita kalma (repeatedly), misali in sun faɗi magana sai sun sake maimaita wa, suna da tsoron kar su cutar da wani, ko su a cuce su, haka kawai tunanin yake ratso musu.
Wannan cuta tana kawo wa mai ita cikas a gudanar da rayuwar shi ta yau da kullum, rayuwar makaranta, aiki, ko relationship. A takaice OCD ciwo ne na rashin sukunin zuciya da ƙwaƙwalwa, shiyasa masu shi basu cika son shiga cikin mutane ko mu'amala da mutane ba, suna keɓance kansu (isolation) daga mutane gudun kar su cutar, ko a cutar da su, kamar yarda tunanin yake musu kutse." Liki ya numfasa yana kallon Daddy yace
"Cutar OCD ana bada magani kuma yana daidaita yana yin su, idan ka dage da shan maganin da shawarwarin likita
(Fluoxetine, sertraline, antidepressants).
Yawanci mutane masu tsananin tsabta suna da wannan ciwo ba tare da son sani ba, tsabta ta su is extreme, ko pillow ya karkace sai sun dawo da shi daidai hankalin su zai kwanta."
(Akwai wata Mata da na sani Ibn kwata ake kiranta, mace ce amma kwatar ƙofar gidanta ita ce ta ke gyarawa, gidanta kika shiga ko allura ta fadi zaki dauka saboda tsabar tsafta, kina fitowa daga gidanta tana bin ki da tsintsiya tana sharewa)
Daddy ya sauke ajiyar zuciya yace "ya Rabb ka dube mu."
~~~~~~~*
Aliyu na ajiye su a makaranta Umaimah ta kalli Amira, tace "Alfarma nake nema a wajenki Please Uwata? "wacce Alfarma" Amira ta tambaya.
Umaimah ta buɗe jakar ta ta fito da gullisuwar da suka yi jiya da daddare ita da Uncle Isma, da yawa a cikin leda. Amira ta buɗe baki tace "a ina kika samu?"
Umaimah tace "na samu ko na yi dai, ungo idan an tashi break Please ki siyar min zan baki wani abu." Amira tace
"ta nawa ce? "ta 700 ce" Umaima ta faɗa.
"ina da 200 aciki"
"kai Amira ay kin cinye ribar, ki bari idan nayi ƙarfi tukunna" Amira ta karɓa tasa a jakarta, Kowa ya nufi class ɗin su.
Tana shiga ta zauna, Sadiq yace "yau kin zo da wuri. "Baba ne ya kawo mu ya je wajen social studies teacher an dauka ƙarya na ke da nace taban 1K jiya.
Aminu ya shigo yace "Smart naga Babanku a staff room" ta ce "shi ya kawo mu, yawwa ku zo ku ji. suka haɗa kai a desk ta fito da gullisuwa, tace "toh ku yakamata ku fara min ciniki" "Smart da son kudi kike" wizard ya faɗa, "nuna min bolar su" Umaima ta faɗa tana harara shi. "bari na yi announcement, 'yan aji muna siyar da gullisuwa mai so ya zo ya siya 50 50Naira."
Anisa ita ta fara zuwa siyan ta 100, kafin kowa ya fara siya, wizard yace "ni ne cashier"
Yana karbar kuɗi, Aminu genius yana ƙirgowa mai siya, ƙarshe dai suka siyar mata da gullisuwar suka haɗa mata kudinta cas ta anshe tasa ajaka.
AMERICA
Wani Sardeden Saurayi ne ya fito daga wanka, a ƙiyasi zai yi shekara 32years dogo ne kakkaura ba jiki ne dashi ba amma bashi da rama yana da zubin jaruman maza, jikin sa a murje yake, wani irin baki ne mai ɗaukar ido smooth, akwai baƙi mai kyau barin wanda ya hadu da hutu, zaka gaa yana daukan ido, yana da idanuwa masu haske da girma yanayin idan shi kamar mai jin bacci, dogon hancin shi daidai da shape din cikakkiyar fuskar shi, lebban shi masu cika ne (kissable lips) kana ganin shi duk Inda ingarman Namiji ya ke ya kai, gashin kan shi a cike yake mai laushi ne ainun, yana da yawan gargasa (gashin jiki) kwance lub a jikin shi, musamman kirjin shi, jikin sa a murmuɗe da guru gurun (six packs) duk yadda aka yi ma'abocin motsa jiki ne, yana da wani irin kwarjini dake hana ƴan mata kawo masa wargi kai harda mazan ma, Arch Isma'il Ibrahim Bichi ke nan (Fahad) matashin Saurayin dake ji da tashen kyau ilimi da kuruciya, fitowar shi kenan daga wanka yaji wayar shi na ringing, ya nufi wayar ya daga "Mum" ya gani, ya daga da kasalalliyar muryar shi kamar an yi mishi dole yace
"Assalamu alaikum" daga tacan ɓangaran Mami tace "Wa alaikumussalam Dattijo, yaya karatun?" bai amsa ba sai cewa yayi barka da lokaci Mami. ta amsa da "Barka ka dai Dattijo, Ay karatun ma kun karkare ko, Alhamdulillah duk kun kammala masters ɗin ku kai da dan uwanka, duk challenges ɗin nan especially you da ka yi encountering da su, but Alhamdulillah, Dattijo are you there?" Mami ta tambaya dan tasan halin shi ko ka kira shi sai dai ka yi ta hirar ka yana jinka, saɓanin twins brother ɗin shi Sa'ad da za a yi zance da shi sosai.
Ya nisa yace "am with you Mami" Fahad ke nan dama shi abokin hirar shi twins brother ɗin shi ne. In kaji Fahad na hira to da Sa'ad ne, daga shi sai Daddy kawai yake ɗan taba hira da su, hirar ta shi is either eh ko ah ah, is hardly ya buɗe baki yayi magana saboda matsalar shi ta maimaita magana, ba ya son yanayin da yake shiga in yana magana na maimacin zance, Wannan dalilin ne ya ƙara sa wa ya zama miskili na sosai da sosai fiya dana dabi'a.
Architecture ya karanta a Carnegie Mellon University, ita ce No 1 ranked in the world a wannan fannin, a North America ta ke lokacin da Daddy ya samu opportunity daga office aka tura shi America su Fahad su ka yi first degree ɗin su acan, yanzu haka sun haɗa Masters ɗin su inda shi yayi nasa a Masssachusset Institute Of Tecnology ita ma a North America.
Tun tashin shi Fahad yana son drawing is his hobby, wannan ne ya sa ba shi da friends sai drawing materials ɗin shi, su sketching pencils, Masters, fine tips, brush tip, pastels, soft pastels, oil pastels, water colour and paper sketch books drawing board duka Daddy ya yi mishi proving saboda passion ɗin shi na drawing tun kuruciya. Fahad inya kulle kansa a ɗaki sai ya yini yana zane, Akwai time din da ya zana wani family picture ɗin su kwabo da kwabo kamar ba zane ba, Daddy ya kafeshi a falo kana shiga falon zaka ga zanan hoton gwanin sha'awa, shi dai a siya mishi kayan zane.
Shi kuwa twins din shi Sa'ad oppsite ɗin shi ne, kamar su ɗaya banbancin su Sa'ad shi fari ne dan ya ɗauko hasken fatar Mami, cikin ikon Allah kamannin su na Mahaifin Daddy ne ( Hakimi) musamman ma Fahad daya ke shi baƙi ne sai kamanin shi da Hakimi ya sake bayyana fiya da Sa'ad, gashi kuma yaci sunan Hakimi Isma'il, shiyasa ake kiran shi Dattijo, baya son a kirashi da dattijo tin suna yara, in kana so kaga ɓacin ranshi to kace mishi dattijo wannan yasa sisters ɗin shi suka saka mishi Fahad.
Sa'ad chemical enginering ya karanta a Massachusetts Institute Of Tecnology North America, yanzu haka suna shirye shiryen dawowa gida bayan kammala karatun su cikin nasara.
Mami tace "are you there? A hankali yace "im with you Mami. "shikenan yaushe kuka saka ranar tahowa? "Ah ah da saura ni ban kammala project ɗina ba. "ok Allah ya taimaka. "Amin" ya amsa. Mami tayi hanging wayar.
Ya cigaba da shiryawa har ya gama shirin sa yaɗan tsaya yana ƙarewa kansa kallo ta cikin mirrorn shi sai kuma ya ɗaga fine hannayen sa ya kalla, toilet ya koma ya fara wanke hannun, yana fitowa daga toilet ɗin har ya zauna ya tashi ya fara gyara ɗakin wanda is very very cleaner, white bedsheets, komai white color ne har gadon da wardrobe, da alam yana son white color ko kuma hakan nada nasaba da ciwon sa, don hatta singlet di shi da boxers duka farare ne and are effortlessly clean.
Ya kuka ji?
Hope kun gane menene cutar OCD? And da yawa acikin mutane akwai irin Fahad da su kan su ba su san ciwo ba ne, sai ka ji ana wane tsabtar shi ta yi yawa, Allah ya kara mana lfy.
💫 UMAYMAH 💫
✍️A&A PEN
Follow our Whatsapp group via this link https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3
https://wa.me/+2348039352724
VOLUME ONE
EPISODE 1️⃣3️⃣
Ranar Juma'a ce yau, samarin gidan ba sa nan duk sun tafi masallaci, Umaimah ta lallaɓa ta faki idon Umma ta fita.
Sauri take tayi ta isa gidan su Sadiq (wizard) da wuri, akwai abinda zata je yi acan, ta fito ta kwanar Nol hospital ta miƙe ta hau kan titin Lamiɗo crescent, ta tsallake titin za ta shiga Tarauni, a kusa da kwanar kasuwa gidan su Sadiq yake.
Gida su Sadiq gida ne baban gida red bricks, mai ƙaton farfajia motoci da yawa an yi parking ɗin su, gida ne na jama'a kasancewar mahaifin su Sadiq ɗan siyasa ne.
Ta miƙe ta shiga ta entrance door tayi sallama aka amsa mata daga cikin falon, Mace ce yar siritiya mai doguwar fuska a kiyasi zata yi shekara 50 ko 51, daga gaininta mahaifiyar Sadiq ce dan suna kama, tana zaune tana jan carbi, tana sauraren karatun Alqur'ani a tashar SAUDIA, shigowar Umaimah ce tasa ta rage volume.
Fuskar ta wadace da murmushi tace
"Ah ah Fatima ce yau a gidan mu?"
Umaimah ta durƙusa ta gaishe ta.
"ya mutanen gidan naku? suna lafiya. Umaimah ta faɗa.
"Masha Allah, mutumin naki ya ta fi masallaci, ki jira shi yanzun nan zai zo, nan masallacin Bello maitama ne ba nisa."
Mama tana maganar tana kallon ƙafar Umaimah da ta yi busu-busu, tace
"Fatima shiga ciki ki yi alwala, an sauko daga masallacin ma ki yi sallah, bari na kawo miki abinci"
Umaimah babu filaƙo tace "Toh Mama" ta mike tayi cikin, dan gidan su wizard ba baƙon ta ba ne, akwai passage tsakanin Bedroom da siririn ƙaramin toilet na baki a wajen ta shiga ta ɗauro Alwala, ta fito Mama ta bata hijab ta saka ta kabbara sallah.
Mama ta shiga kitchen ta hadowa Umaimah abinci ta dawo, har Umaimah ta idar da sallah, Allah Allah kawai ta ke yi a kawo abincin tunda Maman ta yi maganar abinci yunwa ta taso mata, dama lokacin da ta fito ba a gama ba, gashi a ƙafa ta taho duk cikin ta ya zazzage, ita gani take babu nisa duk dan Adaidaitan data tsayar cewa ya ke 100 ita kuma tace taɓ ribar gullisuwar za a karɓe mata, gara ta tafi a ƙafa.
Maama ta ajiye wa Umaimah abinci, Umaimah babu baƙunta ta hau bubbuda coolers, jellop din shinkafa ce ta ji vegatables ga mutuniyar ta kaza a bowl an yi peppersoup, ga maltina da ruwa an dora a tray, saida ta cika plate sannan ta hau ci tana zuba loma, tace
"Mama abincin nan yayi daɗi."
Yadda Umaimah kecin abincin hankali kwance, kamar tana gida, in baka santa kasan gidan suba zaka ɗauka yunwa ce tasata ko rashin samu, amma ga wanda yasan Umaimah da gidan su yasan ina sun wuce haka, hali ne kawai irin tana.
Mama tayi murmushi, ita Umaimah na burgeta bata da dubun kai.
"Masha Allah" Mama ta faɗa.
"Wato Mama ba ƙaramin horon yunwa Siyama ta ke min ba" "haba dai" Mama ta faɗa.
Umaimah tace "hmmm kar ki ji zancen wasa Mama da gaske nake." Mama ta ce
"wace ce Siyaman ne? kullum ina jin sunanta a bakin ki. "Kaka ta ce fa"
"Ayyah watarana dai zamu gaisa in sha Allahu. kuna ta zumunci da Sadiq yakamata na ziyarci Siyama gaskiya. Umaima ta ce
"Mama kin ga abincin nan da kika zuba min ko? Toh rabon mutum uku ne a gidan mu, su basa cin abinci ni kuwa ina zan iya ace mutum ba zai ciba"
Mama tayi dariya tace "haba dai Fatima" "kar ki ji zancen wasa, horon yunwa su ke min, wai na cika ci."
Umaima ta share abincin tas ta bude cooler zata ƙara sai kuma ta kalli Mama, Mama ta yi maza ta juyar da kai dan kar ta yi dariya, tace "Ni kam ban gani ba"
"Ay Siyama da iko ta ke saidai kiji tana cewa "ke Umaimah duk ke kaɗai zakici wannan? babu wanda ya ci fa, daɗi na dake rashin saiti, Umaimah ba na son haɗa ma, kumafa Mama kinsan wani abu? Mama ta girgiza kai, Umaimah tace "to store ɗin gidan mu a cike yake, Mama dan Allah tunda na shigo kin gaa wani abu na rashin hankali da na yi?"
Mama na ƙunshe dariyar ta ta ce "ah ah kina da hankali Fatima." "yawwa Mama dan Allah idan bana ci ina koshii ina karatu zai zauna? "Tabbas ba zai zauna ba" Mama ta faɗa.
Umaimah ta cinye Kaza tas har kamar ta kafa baki ta sha romon sai kuma ta haƙura "Mama idan da wani lemon a canja min ni maltina daci ta ke yi min." Mama tace "toh Fatima bari a canja miki."
Ta yunƙura ta koma kitchen, fitar ta ke da wuya mage ta shigo falon da yaranta suna biye da ita, Umaimah ta tafi wajen magen, yaran baƙaƙe guda uku sai fara mai orange kala biyu ta ɗauki mai fari da orange ɗin tana shafa ta, Mama ta shigo da fanta a tray. Umaimah tace "Mama ina son wannan." Mama tace "An baki Fatima. "Nagode Mama wlh kina da sauƙi da kirki Mama, ni gidanmu basa barina na sha iska, Baba ne kawai yake ta tawa, sai Uncle Ismah." Umaimah na rufe baki.
Sadiq yayi sallama da sallaya a hannun shi tare da wani saurayi, daga gani yayan shi ne.
"Smart" Sadiq ya faɗa yana dariya "kin zo ke nan? "Tun ɗazu nazo fa har na ci abinci" Umaimah ta fada.
Saurayin ya kalle Umaimah, tace "ina yini? yayi murmushi ya ce "lafiya." Mama ta ce "kun dawo sannun ku da zuwa. "yauwa Mama sannu da gida". cewar Hafiz Yayan Sadiq.
"to taso mu tafi. Sadiq ya faɗa, Umaimah ta ce "bani kwali Mama, Siyama ta tsani mage." Sadiq ya fita ya ɗauko kwalin ya dawo, aka saka magen a ciki yayi mishi huji yadda iska zata shiga ciki, uwar kamar ta sani ta dinga kuka.
Umaimah tace "Allah ya taya ni riko." Mama ta amsa da "Amin, toh yaushe za a ƙara zagayo ni? "Ay dan gobe Bichi za mu tafi, daa gobe ma zan dawo." Hafiz ya yi murmushi "what a funny girl." ya faɗa a ran shi.
Mama tace "toh wani satin ina zuba ido. "in sha Allahu, in dai ba za ki gaji da ni ba za ki ganni, ay kin iya zubi." Umaimah ta faɗa tana riƙe kwalin mage.
"kar ki damu ai nan gidan ku ne, idan kika dawo ma ke za ki je kitchen ki zuba." sai a sannan Hafiz ya gane kan zancen, tana murmushi ta ce "Allah Mama?
Mama tace "In sha Allahu Fatima."
"Toh zaki taho mu tafi ko hira kika zo yiwa Mama? Sadiq ya faɗa, Hafiz ya harare shi.
"mu je nagode Mama" "Toh ki gaishe da Siyaman sai kin dawo."
~~~~~*
Suna fitowa tace "Ni muyi sauri mu je yarana nasan yanzu sun fara zuwa" "me ake yi a gidan naku? wizard ya tambaya.
Umaimah tace "ah ah nothing serious kawai yaran makwabta ne nake tarawa mu yi Nishadi, Duniya sai da nishadi" ya ce "haka ne, toh ki rasa nishadi sai wasa da yara? "eh mana mu ba mu da yara a gidan mu, ni kuma ina son yara, amma yanzu ga wata abun nishadin na samu" ta daga kwalin magen hannunta.
suna fitowa titi Sadiq ya tare musu Adaidaita sahu suka shiga "nan kwanar sabo nawa ne?" Sadiq ya tambayi me mashin, "ku bada ɗari hudu. Umaimah tayi sauri tace "haba mallam ina nan ina hotoro, wlh mu sauka in dai zaka kai mu 200 toh. mai adaidaitan ya ce "ku sauka ba za ni a 200 ba.
"mun ƙara 100" cewar Sadiq. ya ja suka tafi, Umaima tana ta hararar Sadiq tace "wlh ka zura jiki, tafiyar da be fi muyi da kafarmu ba, nina saba tracking.
"Ke smart ta ina? Sadiq ya faɗa yana kallon ta,
"Islamiyyar mu da nisa daga gida, da ƙafa muke zuwa mu dawo a ƙafa, gidan su Amani mun fi su nisa amma a mota ake kai su Islamiyya.
"idan ka samu waje nan yayi" wizard ya fada. ya bashi 500 ya karɓa, ya bashi canjin 200.
Umaimah tace "ya cuce mu." suka tsallake titi.
A ƙofar gidan su Aminu suka tsaya suna fara knocking gate ɗin aka bude, Aminu genius shi ya bude musu ƙofar da ke ya san da Zuwan su.
"sai yanzu? tun dazu nake jiran ku, Daddy ya so mu je cikin gari na ce ina expecting friends dina.
"kaga Smart ce ta ɓata mana lokaci ta tsaya hira da mama." wizard ya faɗa yana nuna Umaimah.
"toh mu je mu yi abinda ya kawo mu. Aminu yayi gaba suka bi shi a baya, bayan gidan suka nufa wajen ƙatuwar bishiya Mangoro.
"toh wizard ka hau ka fi mun tsaho sai ka tsinko mana, kuna da buhu? Umaimah ta faɗa tana kallon Aminu. yace
"ba za a rasa ba bari na dauko miki ya shiga cikin gidan su."
Sadiq ya kama bishiya ya haye can sama ya din ga kaɗo musu Mangoro Umaimah tana tarawa ,
"kai masha Allah, wlh sun nuna, dan wulakanci ma sai mun zo da kan mu, genius be yi ba mu ay ƴan Amana ne."
Aminu ya ƙaraso ya miƙa Umaimah buhun ta dinga tattara Mangoron tana zubawa a cikin buhun, buhun ƙarami ne, Sadiq yana daga sama, ya ce "da fatan an zuba min nawa? sai da ta cika buhun tsab, sannan ta cewa Aminu "samo mana wani a zubawa wizard."
Ba musu ya koma cikin gidan bai jima ba sai ga shi ya dawo da leda
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 7 Chapter of 29