sakon mutuwa, tayi kicin kicin. Munnirah tace "Allah ya sauwake miki, toh saki fuskar."
Ta buɗe wardrobe ta ɗauko riga da wando na bacci silk copee brown ta saka ta koma ta fesa turare, har Khadijah ta kwanta tana kokarin rufe ido. munnirah tace "wai bacci? Khadijah tace "Toh me zan yi yau ban je shago ba nayi aikin turare na gaji, ga month ya zo karshe".
"hmm haka ne"
Munnirah ta kwanta a ɗaya barin, ta kira Khadijah, tunda ta ji ta kira ta da sunan ta kai tsaye ta san da magana a bakin ta "Na'am" ta amsa. Munnirah tace
"ina wannan Abokin Dr da kika zo gida na kuka hadu ranar da kika zo gida na ɗaukan Umaimah? Khadijah ta tuna sarai don ita ma tayiwa Munnirah zancen ta tsargu da kallon da yake mata. Munnirah tace
"kin yi shiru? Khadijah tace
"me zan ce to?
"kin ga ne shi? Munnirah ta tambaye ta,
"bangane shi ba" khadija ta fada.
"nasan haka zaki ce. Munnirah ta faɗa tana jawo wayar ta a bedside ta bude, ta shiga gallery tayi scrolling ta tsaya akan hoton shi, ta fuskanci Khadija ta nuna mata a fuska, Munnirah tace
"wlh mutum ne har da rabin mutum sunan shi Usman Usman Bebeji, yana da mata 1 da yara2 tunda ya gan ki ya dami Dr, Dr ya fada mishi kin taɓa aure, amma ya nemi soyayyaki idan kin amince sai yafi kowa farin ciki"
Khadijah ta numfasa, idan ba munnirah ba, babu wanda take irin wannan maganar da shi, sai ranar da Ibrahim yazo mata da wata baudaddeyar magana, toh bauddiya mana, a nan Sultan road ɗin neighbours suke da maigidan be fi gida 2 zuwa uku ba a tsakanin su, ya turo Ibrahim ya na neman Soyayyar ta idan ta amince zai samu Baba da zancen, shi ba yaro bane, maganar ba ƙaramin girgiza ta tayi ba, gidan Khadi Habib fah babban mutum irin wannan, matar shi suna kirki sosai da Umma ranar ta yi matukar mamaki, su maza babu ruwan su da abinda zai je ya zo, ba babba ba yaro, kawai su idan abu ya musu shikenan.
Munnirah ta katse ta da cewa "yana ji kin yi shiru? Khadijah tace
"Toh me zan ce miki my sis?"
I hope kun ji daɗin Episode ɗin?
pls encourage us with your comments.
💫 UMAIMAH 💫
✍️A&A PEN
Follow our Whatsapp group via this link https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3
https://wa.me/+2348039352724
VOLUME ONE
EPISODE 1️⃣0️⃣
Please my sis ki yi tunani, zaman ki haka ba shi da wani amfani, kinsan komai daran ɗaɗewa ba za ki yi ta zama babu aure ba, kawai an daga miki Ƙafa ne saboda halin da kika shiga abaya, amma bawai dan su Umma basaso kiyi wani Auren ba, kuma yanzu is high time daya kamata kiyi removing komai and more on is part of life Khadijah, anayin fiya da haka you know, ga Umaimah nan a js3 take yanzu, girman mace ba wuya before you know zaki ji muna maganar ɗaukar siriki, gidan auren dai shi ne cikar mutuntaka, Please and please my sis ki buɗe zuciyar ki, move on,Tahir idan yana raye ya kai har wannan lokacin be waiwaye ki ba kinsan he has moved on already, ki saka a ranki rabon UMAIMAH ne yasa abunda ya faru ya faru, Please stop punishing yourself and give your heart a chance to love someone ko ba Usman Bebeji ba, there are good men around dan ba ki yi sa a ba ne, ba'a ce shi kenan mazan ƙwarai sun kare ba, you might not know the right person may be close to you, pls open your heart, I pray u meet Mr right soon. my sis kin yi shiru?"
Munnirah ta faɗa tana kallon Khadijah da idon ta ya kaɗa yayi jaa kamar zata yi kuka.
"Are you angry at me?" Munnirah ta tambaya
"not really, thank you my sis, Khadija ta ce you are a good friend, I didn't have a sister, but I saw a sister in you, you were my backbone, my strength, we fought my battle together, you encouraged me when I'm down, you pushes me when I'm scared, you advices me when I'm confused, Thank you sis" ta matso ta rungume ta tana kuka.
Daga jin kukan kasan daga kasan zuciyar ta take yin shi, kuka ne na shekaru masu yawa, kuka ne na ciwon da zuciyar ta take yi duk lokacin da magana makamanciyar wannan ta ratso kuka ne na danasanin amincewa Auren Tahir.
'its okay."
Munnirah ta faɗa tana shafa bayanta. Khadija tayi shiru tana sauke ajiyar zuciya kamar ta fara bacci. sai Munnirah ta ji ta ce
"shi kaɗai na so kin sani, bayan shi ban sake soyayya ba,Tahir yayi min mugun rauni a zuciya, ya ci Amanar ƙauna Munnirah, he betrayed me, innahu kasara qalbi ( he broke my heart), he cheated me with my friend, Munnirah how could I forget that? the pain is still in my heart"
"I know is not easy Allah is in control in sha Allah. Munnirah ta faɗa.
"in sha Allah" Khadija ta ƙara maimaita wa.
"will you give him a chance? Munnirah tayi maganar tana kallon Khadijah. Khadijah tace "Please give me sometime" Khadijah ta bata amsa a hankali.
Munnirah bata takura mata ba ta yi murmushi "thank you"
Wayar munnirah ta yi ringing "Mon Amour (mylove)" ta yi murmushi ta juyawa Khadijah baya ta daga wayar maigidanta ne Yusuf Ismael Bichi (Baba Dr)
"har na yi fushi yau baka kira ni ba, na kiraka kuma wayar ka switch up" daga daya bangaren shi kan shi he misses her ya ce "ayi min afuwa na shiga theare ne. "apology accepted" sukaci gaba da fira tana murmushi tana bashi amsa daga gani masoyan suna missing junan su, wani abun idan Khadijah ta ji Munnirah ta faɗa sai ta rintse ido saboda kunya wai Baban ta ake wa wannan taɓarar. ita kuwa Munnirah tama manta da wata Khadija a ɗakin, ƙarshe dai Khadija ta kasa bacci ta tashi ta ɗauro alwala tana ta jera nafila tana kai kukanta ga Allah, ta idar ta zauna tana lazimi, tuni Munnirah ta yi bacci, abubuwan da su ka tattauna da Munnirah suka rinƙa dawo mata, wai har yanzu tana jiran Tahir, ita ba jiran shi ta ke yi ba, ah ah kawai yadda za a yi ta iya saka soyayyar wani ne a cikin zuciyar ta ne aiki, tana zaune har aka kira Assalatu, ta tashi ta yi Raka'atanil fajr.
Ta tashi Munnirah ta yi sallah sai bayan ta sallaci asuba ta ɓingire a kan sallayar barci ya ɗauke ta.
*****
Isma'il yayi knocking ya shiga ɗakin da sallama, Umma ce ta ritsa Umaimah ta gyara kayan ta.
"Ɗakko wannan skirt ɗin, to nemo rigar shi da ɗankwalin sai ki haɗa su waje ɗaya" Umma tayi maganar tana directing ɗin ta, "wai Siyama tun ɗazu ina abu ɗaya nina gaji wlh, ban san fitar Baba ba da na bi sa." Umma tace
"ki fi ruwa gudu, duk inda kika je zaki dawo." "bari na taya ki" Isma'il ya faɗa yana ƙarasowa wajen sif ɗin, Umma tace "oho muku amma dole a gyara kayan nan yau"
Isma'il ya rinƙa ware masu datti gefe duk ta haɗa da masu wanki da masu datti, yace "ke Umaima kalli kayan ki kamar bola? "Allah bana so Uncle Isma." Umma tace
"yawwa kun fi kusa ƙila idan shi ya fada miki kya yarda, idan ba haka ba ki tattara kayan ki ki mayar da su ɗakin ku bana son kazanta"
"Siyama kiyi ta min gorin daƙi, Watarana gidan ma zan bari"
"ina zaki? Ismael ya tambaye ta, Kai tsaye Umaimah tace "gidan miji na mana, nayi ta zama gaban Siyama ne tana baza min iko? Ismael yayi daria ya ce "Allah ya nuna mana mijin Umaima."
"Allah ya sa zamu gani, ƙila shima ƙazamin ne, dan ƙazami sai ƙazama irin shi, wannan ruwan gidan ku ba zai shawo ba" Umma na rufe baki, Umaima ta fara dirza ƙafa a ƙasa "Allah bana so, wlh Siyama tun daga gate zan ce ki koma bana bukatar ganin ki" Umma tace
"oh ashe har da gate a gidan naki, ay ke a Bichi zamu bayar da ke sadaƙa Baban cikin gida ya nemo wani haka sauwa sauwa mu bashi sadaƙa, shi kenan kin zama matar ƙauye."
Umaima ta yaye baki bil hakki da gaskia ta din ga kuka kamar an ce an daura mata auren.
Isma'il tun yana daurewa har dariya ta ƙwace masa ya kasa rike ta, yayi ta dariya, nan fa faɗan ya dawo kan sa, "kuma wlh sai na fadawa Baba kun haɗu kai da Siyama kuna min dariya, tana bubbuga kafa tana kuka kashirɓan.
Baba yayi sallama ya shigo suka amsa da gudu ta yi wajen Baba "wa ya taba min uwata? Baba ya tambaya, tace "Ba Siyama bace wai sadaƙa za a bayar dani a Bichi." Baba yace "ban gane ba" "eh auren sadaƙa za a yi mata da ƙazami dan uwan ta" Baba ya gane abunda ake nufi, Ismael ya ce "wasa fah ake mata"
Tace "ba wani nan, ba da kai ake min dariya ba." Baba yace "yau ke da Hakimi uwata lallai na gano ku a rana. Umaimah tace "ay zamu shirya amma ya ɓata min rai maimakon ya rama min sai ya biye wa Siyama"
"Sannu da zuwa." Umma ta faɗa tana maida hankali ta wajan Baba, "yawwa sannun ku tsokanar min uwata."
Umaimah ta share hawayen ta tace "ka huta Baba akwai Rahoton kowa zan baka" Baba yayi dariya yace "ina sane da shi"
Umaimah kamar cctv take duk abinda ya faru a gidan idan Baba ya dawo kamar yana wajen aka yi saita faɗa masa komai ko manta wa batayi.
Baba ya kama hannunta yace "zo muje ga tsarabar ki can a ƙasa. Siyama a kawo min tea" Baba ya faɗa, suka fita daga ɗakin yana rike da hannun ta.
Umma ta amsa da "toh" ta miƙe ta ce wa Isma'ill ya ƙarasa gyaran kayan yace "toh Umma" yana yin gyaran yana mitar kayan Umaima a ran shi.
Shawarma ce da ice cream da yawa Baba ya siyo, kusan kullum Baba ya fita da abunda zai shigo da shi saboda Umaimah, shi yasa take yin Baba over, Umaimah jikinta har rawa yake ta debo guda biyar.
"bana son haɗa ma" Umma ta faɗa, tace "har da Uncle ismah na ɗaukar wa"
"Abokin cin mushen naki?" tazumɓuro baki gaba, Baba yace "zo nan, dama naki ne duk wanda be samu ba ya ci girma" Umma tace
"nasan su Khadija sun kwanta yanzu karɓi ki saka musu a fridge Amira, Babangida baya cin shawarma ku ajiye musu ice cream ɗin, Ismael saka musu a fridge"
"gaa naka Uncle Isma" in ji Umaimah, yace "ajiye min ina zuwa"
"Radion Baba zo mana naji waya bata miki rai da bana nan?" Ya faɗa yana mata murmushi.
"yauwa Baba" tana cin shawarma ta na lumshe ido. Baba yace "ina jin ki Uwata" tace
"Siyama sau ɗaya ta siya min ice cream tun tafiyar ka, ka ƙarɓi kuɗin ka, kota biya ni hakkina, ta dai biya ka kuɗin ka ma kawai." Umma ta ce "kajin da kika Ci fah? Umaimah tace "pepper chickhen, toh ay Baba da yawa ya ke siyan Kaji kuma Uncle Aliyu ma yana kawo kaji, har food stuff da yawa,Toh na Baban ya ƙare ne?" Umma ta ce "Naji wannan ƙorafin, sai kuma wanne? Umaimah tace "wannnan ba ƙorafi ba ne Baba kasan duk abunda ya faru nake faɗa maka. Ammina ta samu order da yawa, aiki yana mata yawa saboda bukukuwa a December." Baba yace "Masha Allah wannan abu ne mai kyau" "Nima shi yasa nake son dogaro da kai na, Au sai ta rufe baki da sauri ta kallo Ismael.
"me ake boyewa?"
"ba komai" ta tari numfashin Baba. "shikenan idan ta yi wari ma ji"
"Yawwa kuma Uncle Aliyu ya tafi ya bar ni a gida ranar Wednesday sai Ammina ce ta kai ni makaranta"
"Babangidan" Baba ya maimaita.
Tana rufe baki Aliyu da Ibrahim suka yi sallama suka Shigo, sai ta fara rarraba ido, Aliyu ya harare ta ta ɗauke kai, A tare Suka ce
"Barka da dare Baba, Umma barka da gida" Baba yace "yauwa sannunku. Amira ta miƙe ta ɗakko musu ice cream ɗin su, aka cigaba da hira.
Baba yace "ina jin ki Matar" Duk kuma sai taji takura da zaman Aliyu a wajen, ta kiftawa Baba Ido alamar abar maganar yanzu, Baba na ganin haka yayi dariya yace "toh shikenan ni zan shiga na kwanta, mu kwana lafiya. Baba yana tashi Umaimah ta bi bayan shi suka haye saman tare
*****
Mu na fatan kun ji daɗin Episode din? nan mu je zuwa labari yana gaba.
💫 UMAYMAH 💫
✍️A&A PEN
Follow our Whatsapp group via this link https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3
https://wa.me/+2348039352724
VOLUME ONE
EPISODE 1️⃣1️⃣
Babu wanda ya farga da shigowar Aliyu, sai gani a kayi cak ya ɗauki Umaima yayi waje da ita, "ko me ta yi masa" Umma ta faɗa, Khadijah ta tashi ta yi hayewar ta sama, Umma sai leƙe ta ke ta window, Ismael ya fita, Ibrahim ya ce
"yau an gama tara ta kenan" Umma ta ce "Dan Allah je ka kar ya yi mata rauni. Uncle Ibrahim yace "Umma kinsan idan yana mata hukunci baya so a je wajen, ke kan ki ba so ya ke ki yi magana ba." Umma tace
"Nasa ni shi yasa na ce ka je dan Allah."
Ibrahim ya yunƙura ya fita, "Babangida ya cika zafin zucia" Umma ta faɗa zuciyar ta ba daɗi, tana tsaye Ibrahim ya shigo yace "Umma sai dai ki je da kan ki."
"kneel down, close your eye, raise up your hands Ko moving na ga hannunki yayi I will see the other side of me. Cewar Uncle Aliyu.
"na yaushe kuma" Umaimah ta faɗa a ranta, ta yi duk yarda ya ce.
Ya dauko ipad ɗin shi ya zauna a farar kujerar roba yana daga inuwa, Umaimah tana rana, gashi Baba baya nan, kowa shakkar yi mishi magana yake ko Baba sai dai ya lallaɓa shi, duk hukuncin da ya yan ke akan yan uwan shi Baba goya mishi baya yake yi, akan Umaimah ne ma idan ya gaaa abun yayi tsanani ya ke cewa "Babangida a sassutawa uwata"
Har aka kira sallah ya tashi Umaimah na cikin ranar, yana tashi Ismael yayi maza ya ƙaraso wajanta yace "wai me kika yi mishi?
Tace "wlh na manta. Isma'il yayi shiru yana tunani, yace "kin je kin same shi lokacin daya ce ki je ki same shi, kin je?"
Sai yanzu ta tuno da kiran, shi ne laifinta ta ke nan. Ta girgiza Kai idonta a rufe. Isma'il yace "karɓi ruwa ki sha" ya miƙa mata robar ruwa. ta karɓa ta fara sha, sai ga Aliyu ya dawo Ismael yayi zuru zuru da ido.
"join her" Aliyu ya faɗa ya koma ya zauna.
Ismael ya je ku sa da Umaimah ya ɗaga hannu shima yayi yarda Umaimah ta yi. Aliyu ya ƙara tashi ya nufi chalet ɗin su, Umma ta zo tace "me kika yi mishi? kai ma laifin ka yi? Ismael yace "Umaimah na bawa ruwa" "sai yanzu zaki zo tun dazu na yi awa anan. Umaimah ta faɗa. "oh haka kika ce, ki daɗi abunda kika yi na roƙa miki afuwa. Umma tayi maganar tana kallon Umaimah, "ko kallon shi na yi ay laifi ne a wajen shi"
Umma na nan a tsaye mota ta shigo cikin gidan, Munnirah ce, sai gashi ya dawo ya ƙara ɗaure fuska, Umma ta ce "Babangida ayi musu afuwa, Munnirah ta ƙaraso wajan tana cewa "Uncle Aliyu muna roƙon Afuwa"
"kin dawo Munnirah?" Umma ta tambaye ta, "Eh, sannu da gida Umma" Yawwa sannu da zuwa.
Aliyu ya kalli Munnirah ya ce "sannu da zuwa" tace "yawwa Uncle Aliyun mu, muna roƙon Afuwa, ayi haƙuri mun tuba" ya ce
"wannan yarinyar har abun nemawa afuwa ce?
"Ayi hakuri dai a bar ta."
Hannun Umaimah na lilo a sama ga gwuiwarta ta gaji, ga garin yau ana rana. Yace "ku shaida idan ta ƙara rashin hankali nan da sati kai kwana uku ma wlh zan ɗauki mummunan mataki a kanta. Yana gama faɗar haka ya kalleta, yace "keee ɓa ce daga nan, tashi ka tafi kai ma shashasha kawai"
Suka tashi, Ismael ya miƙar da Umaimah, Aliyu ya harare shi ya cika ta, Munnirah ta ja ta suka rankaya cikin gidan a tare.
~~~~~~*
Umaimah tinda suka shigo tayi ɗai ɗai akan kujera tana maida numfashi ita a dole jikin ta ciwo yake, tace "Siyama nan zaki matsa min."
Umma sai da ta yi da gaske sannan tayi wanka. Dan cewa ta yi sai dai Umma ta yi mata wankan. Umma kuma ta ce "Allah ya tsare ni da ganin tsiraici ba kya kunyar a kalli jikin ki, kin fara kirgen dangi fa Umaimah tace "menene ƙirgen dangi kuma? "ban sani ba" Umma ta faɗa.
"Kina zama budurwa kina shashanci." "budurwa fah kika ce Siyama? Umaimah ta shafa kirjin ta ta ce "ay nonon nawa ba sa fitowa." Umma tace "oh oh oh ni Maryama Allah ya kawo miki hankali Umaimah, zaki yi wankan ko nayi nawa waje?"
"kar ki tafi dan Allah wlh jikina ciwo ya ke" ta shiga Toilet.
Amira da Ismael suka Shigo da sallama "ina Umaimah? ismael ya tambaya. Umma tace"ta na wanka"
ya samu waje ya zauna, Amira ta haye gado, Umma ta ce "Auta ya aka yi?" "ba komai Umma assignment zamu yi na maths, yaya Ismael zai koya mana" Umma tace "to Allah ya bada sa'a"
Da yake Idan maths ne shi ke koya musu, kuma shi kaɗai ake koya wa Umaimah, shima maths ɗin yana nuna mata yadda zata fitar da amsar shi ke nan zata yi da kanta ta kawo masa ya duba mata koda gyara.
Umaimah ta fito daga banɗakin tana jan kafa ɗaure da towel a kirji, Amira tace mata
"Zamuyi assignment ki shirya." Ta wani ɓata fuska tace "wlh ba zan iya ba, ku yi kawai" "Har yanzu jikin yana miki ciwo ne?" Ismael ya tambaye, ta ce "sosai ma"
Isma'il yace "toh shirya nayi miki tausa"
Umma ta makawa Isma'il harara tace "Yau naga abunda ya dame ni, kai ma fah wani lokacin kan naka babu saiti Umaimar zaka yiwa tausa?"
Yace "me na yi Umma? "Idan ba rashin hankali ba ina kai ina yi wa umaima tausa?" "toh meye Umma ay ba wani abu." Umma ta sake hangame baki tace "ah ah ba a nan bah toh"
Umaimah ta fara ƙoƙarin cire towel ɗin ta, cikin zafin nama Umma tayi sauri ta dafe tace da Ismael "ku je ku yi karatun idan ta shirya zata fito.
"Ba ma zan iya fitowa ba su yi kawai" ta faɗa, suka mike suka fita aka bar Umma da yiwa Umaimah tausa, tana yi mata suna faɗa.
*****
Fitowa Umma tayi daga wanka, ta zauna tana shafa lotion Baba ya kalle ta yana daga kishingiden a kan gado, yace "uwargida sarautar mata" Umma tayi murmushi mai sanyi, "juyo mana na kalli murmushin na ki mai tsada" ta kara faɗaɗa murmushinta, ta kalle shi yace "Bainu ba kya tsufa, uwargidan Muhammadu Ali Bichi ikon Allah" Umma tayi wani murmushin jin dadi ta ce kuma "uwar Khadijah, kakar Umaimah duk ni kaɗai Rabin raina" yayi mata inkiya ta dawo kusa da shi, "sai wani basar da ni ake yi tunda na dawo, na yi kewar masoyiyata da yawa" Umma ta taso cikin nutsuwa ta zauna dab da shi ya riki hannunta yace "Allah ya taimake ki an yi kewar tawa ko dai a baki ne? Umma tace "haba dai a baki, baki ba zai iya faɗin kewar ba sai dai zuciya Sadauki na." Umma ta tuna mishi da sunan da take kiran shi dashi a wani zamanin daya wuce, zamanin da ƙauron baki yasa ya kusa rasa ta, kuma suna ne da a mafi yawancin lokuta idan suna tare kamar dai wannan lokacin take yawan kiransa dashi, ya jawo ta jikin shi ya rungume yana ta sakin murmushi, suka ji an yi knocking ƙofar "waye? Umma ta tambaya, "ni ce" suka ji muryar Umaimah, Umma tace "ya aka yi?
"Baba zan yi wa magana." Toh yayi bacci, kinga ya gaji ya kwanta da wuri a bar wa gobe da safe kin ji Amaryar Babanta."
Umaimah daga bakin ƙofar tace "ki ce Allah. Umma da ta fara jin haushi ta miƙe daga jikin Baba tayi bakin ƙofar, Baba yana ta dariya kasa ƙasa. A bakin ƙofar Umma ta tsaya tace "faɗa min saƙon naki na fara sanar mishi iya tashi.
Siyama jikina har yanzu yayi tsami ki faɗa mishi bayan ya fita da rana Uncle Aliyu ya saka ni punishment a rana. "toh zan fada mishi mu kwana lafiya" ta rufo ƙofar.
Yau yan gardamar ba sa kusa da duk yarda za a yi sai an buɗe ƙofar nan "uwata sarkin rigima." Baba ya faɗa, Umma tace "hmmm har tausa na yi mata sai da ta fara bacci na baro ta a ɗakin. Baba yace "lalle ba kya kishi, wa ya ke yiwa kishiya tausa, yauwa kar na manta mun yi waya ba Baban su na Legas ya ce Dada ta kira meeting jibi insha Allahu kowa da kowa har yara, Dada kenan wai harda masu auren idan sun samu dama." Umma tace "su Surayya kenan?
"Amma na roka musu a rabu da su, yanzu kamar Surayya ta yi nisa sosai duk abunda aka tattauna a faɗa musu a waya, ina ganin hakan zai fi.
Umma tace "hakan yayi daidai"
~~~~~~*
Daddy waya yake yi tunda ta shigo falon ta haɗa mishi copee, ta haɗa Green tea, duk wanda yake so ya sha, sassaukar kwalliya ta yi duba da dare ne, tana tashin kamshi ta ajiye tray ɗin a table ɗin kusa da shi.
"hakan yayi kyau Sa'ad make sure you monitor him, keep checking on him please, he is your responsibility tunda ba ma kussa, ko muna kusa ma you re responsible enough to take care of your brother, and Dada ta kira meeting nasan dai a kan maganar auren ku ne is high time, you settle down, this time around ba ni da wani excuse da zan bata karatu ne, and you are almost through
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 6 Chapter of 29