Share this page
komai zata rage mata zaman shiru, "ah ah Amarya kin ga yadda kika yi haske kuwa?" Zaliha ta faɗa, Khadija bata amsa mata ba suka shige cikin Falo suna hira tana ta bugun cikinta, Zaliha tace "jiya na kiraki ay wayar ta ki shiga." Khadijah ta ce "wajen yaushe?" "wajen 1 na rana." khadija tace "muna hanya lokacin ba za ki same ni ba." Da sauri Zaliha ta tambayeta "ina kuma kika je?" "Yankari muka je weekends." "lallai Amarya kina jin daɗi."ta faɗa, amma ranta baƙi ƙirin take jinsa, tayi murmushi mai ciwo tace "maigidan baya nan ko, nasan yanzu yana wajan aiki." Khadijah tace "wlh jiya bamu yi bacci ba." "kamar yaya? ta tari numfashi Khadija. "Kwana mukayi yana ta fama da ciwon kai." Kamar gaske tace "Ayyah Allah sarki." Khadijah ta ce "don Allah ki yi haƙuri abunda ya faru tsakanin ki da Munnirah." "laah haba ni na manta ma, ay ya wuce gashi har na zo dana riƙe ki a rai ba za ki ganni gidanki ba." Khadijah tace "haka ne nagode." "babu komai kina dai shan maganin ko?" Khadijah ta girgiza kai "kwana biyu ban sha ba Munnirah ta tafi da shi." "ta tafi da shi." Zaliha ta ƙara maimaita wa, wannan Shegiya tsinanniyar Munniran, ta faɗa a ranta, sai kuma tayi murmushin da yafi kama da yaƙe tace "babu komai akwai chemist a nan kusa bari na fita na karɓo miki wani." ta fita. Khadija kamar sokuwa Zaliha ta karɓo sachets biyu ta miƙa mata, tace "Amarya babu abinci a gidan ne yunwa nake ji.". "oh yi hak'uri wllh hankali na ne a tashe, kin ga abincin can nima na kasa ci, Habibeey bai ci ba." har ta miƙe za ta kitchen, ta ce "bar shi ma ɗan anjima na ci." Khadijah ta dawo ta zauna, Zaliha tabi kayan jikin ta da kallo, "kai ƙawata wannan kayan sun miki kyau a ina kika siyi atamfar?" "Mami ce ta ɗinko min su daga lagos." "wlh da zaki ara min dana ji daɗi muna da biki a dangin Baban mu na rasa kayan da zansa abinka dame ƙaramin karfi." "haba dai na baki aro Zaliha sai dai na baki wasu kyauta wannan Habibi yana sonsu dana baki." "kai wlh babu komai hakan ma nagode." Zaliha ta fada. Khadija ta tashi ta shiga ɗaki bata daɗe ba ta fito da kaya set 3 ta zuba su a leda tabawa Zaliha, Zaliha ta karɓa tana ta godiya, sai kuma ta mike tace kinga bari na tafi gida Mama tana jira na zan rakata siyan gudummawar da zata kai bikin, na zo nan na rashe, bani abincin ma ko a roba ne zuba min idan naje gida na ci." Khadijah ta tashi ta shiga kitchen ta fito da leda a hannun ta ta zuba wa Zaliha abincin mai yawa, Zaliha ta karɓa, ta ce "nagode." har ta miƙe ta dawo, tace "oh Khadija wlh na ji kunya maganin nan dana siya miki shikenan kuɗin canjina dan Allah taimaka min da na mota " Khadijah ta shiga ɗaki ta ɗauko 3000 ta bawa Zaliha, ta karɓi kudin da murna. Daga gidan Khadija, bata zarce ko ina ba sai wajen malam na Zaure ta basa duka kayan. Ya karɓa yana dariya yace "lallai da gaske kike." Kwana biyu abun duniya yayi wa Khadijah yawa tun daga ciwon kai ta kasa gane kan Tahir, idan ya shigo sai muzurai yayi ta haɗa mata rai, idan ta kawo mishi abinci yaƙi ci, yadda ta ajiye haka zata dawo ta ɗauki kayanta, sai ya zama na kwata kwata baya zama a gidan yanzu, kullum sai ta kwanta zai dawo, yau dai ta ƙudiri sai ta jira shi ya dawo ta tambaye shi ko wani laifin ta yi masa bata sani ba, tana nan a zaune tana gyangyaɗi ta bude ido taga 11:30 na dare ta shiga Toilet ta yi fitsari, ta fito ta ƙara gyara fuskarta ta fesa turare ta dawo ta sake zama a falo tana jiran shi, bata daɗe da zama ba ta ji buɗe kofar shi ya shigo ta tashi ta nufe shi da sauri tana mishi sannu da zuwa, tana kokarin karɓar jakar hannunshi yace ta bari, ta ƙara cewa sannu da zuwa yanzu ma be amsa ba, ya wuce ya nufi ɗakin shi, zai rufe ƙofa ta rufa mishi baya, "Habibi." ta ƙara kiran sunan shi, ya kalle ta kwana biyun nan har ta faɗa mishi, wani abu kamar tausayinta yaji ya ratsa zuciyar shi, sai kuma yaji wani abu ya zo ya danne wannan tausayin ya kalle ta, yace "fitar min daga ɗaki." Idon Khadijah harya tara hawaye tace "Habibi magana nake so muyi." Ya daka mata tsawa "get out of my sight." ya faɗa da karfi, jikinta har rawa ya ke yi ta fita da gudu ta yi ɗakinta, tana fita ya zauna abakin gadon shi yana maida numfashi kan shi yaji yana sara mishi da wani irin ciwo, ya rasa me ya same shi kwana biyun nan, ya kwanta da baya ko takalmin ƙafar shi bai cire ba, yau abinda ya faru a company ya dawo masa. Zaliha ce ta kawo mishi breakfast kamar ta san be karya ba, kuma ya ji dadin abincin, ba zai yi karya ba shi wlh sai yau ma ya ƙarewa Zaliha kallo Khadijah ta fita komai nesa ba kusa ba, amma sai yaji zuciyar shi na kimtsa mishi wani abu daban akan Zaliha. Washegari da safe Khadijah na kwance damuwa ta ishe ta wayarta tayi ringing, jikinta kamar mai zazzaɓi ta yunƙura daga kwancen ta ɗauki kiran Umma ce, suka gaisa "Khadija yana ji ki wani iri?" Umma ta tambaye ta, "Wlh zazzaɓi na ke yi Umma." Khadijah ta samu kanta da faɗar hakan. "kin je Asibiti ko." ta ce "eh na je Umma." "Toh Allah ya sauwaƙe ki daure ki zo ki duba Hajiya fah." Tace "toh Umma in sha Allahu." Khadijah tace "Umma ki turo min Ibrahim ya zo." "sai dai gobe babu islamiyya sai ya zo." Khadijah ta amsa da to, amma ba haka ta so ba, suka yi sallama. Umma ta ajiye wayar tace "Allah ya raba ku lafiya." ita a tunaninta ciki ne da khadija, wannan shi ne ya kwance uwa kwance, Umma ta faɗa, in sha ALLAHU daga wannan cikin dai ta bar wa Khadijah haihuwa, ay sai ayi abin kunya. Tunanin Umma ke nan, batasan har lokacin Khadija tana shan pills ɗinta ba kamar ibada duk halin nan da take ciki ko manta wa batayi. Rana ɗaya Tahir ya zo ya kwashe kayan abincin gidan kaf babu abinda ya bar mata a store, kwata kwata ya canja bata sanin fitar shi da dawowar shi, idan ta jira shi ta rinƙa bashi hakuri, tana rarrashi idan laifi tayi ya faɗa mata sai yace mata babu komai kar ta dame shi, a haka ta daure ta tambaye shi zuwa dubiyar Hajiya, budar bakin shi sai cewa yayi "idan kika fita daga gidan nan kin fita kenan." Abun duniya yayi wa Khadijah yawa ta rasa abunda yake mata daɗi wannan damuwar da take ciki yasa kwana biyu ta manta da pills bata sha ba, Allah cikin ikon shi wata rana tana ɗaki a kwance yunwa take ji sosai, da ƙyar ta iya ɗauko sauran kayan gararta, su dubulan ne da Alkaki, su ne rufin asirinta yanzu, idan ta ji yunwa su take ci ta sha ruwa a kitchen, dan ko pure water babu a gidan sai dai ta sha a kitchen, tana cikin wannan halin kawai sai ganin Tahir tayi ya fado ɗakin ta tsorata da farko ta ɗauka ma dukanta zai. A wannan ranar cikin ikon Allah cikin Umaimah ya shiga, ba ƙaramar wahala Tahir ya bata a ranar ba, yadda kasan ba mutum ba haka yayi mata, neman ta yake kamar wanda baya cikin hayyacin shi, yana gama biyan buƙatar sa ya tashi ya bar ta yashe a wajen ko kallo bata ishe shi ba, da ƙyar Khadija ta yunƙura da rarrafe ta shige banɗaki tana kuka ta kyara jikin ta. Umma tana yawan kiranta a waya taji ya jikin ta, ranar dai Umma ta ajiye kunya ta tambayi Baba za su je gidan Khadija da yara su yini, Baba yaso ya hana su Umma tace "Baban Khadija, Khadija fa bata da lafiya ka manta ranar na faɗa maka, kaga ko dubiyar Hajiya bata iya tazo ba. sai nake ganin kamar ya kamata muje mu dubo ta." Baba ya numfasa "haka ne, kuce ina yi mata sannu." Umma suka taho gidan Khadija gaba-dayan su, Umma bata ji daɗin yadda taga Khadija ba, gaba ɗaya ta wani rame ta sake koɗewa, Umma tace "anya kina cin abinci kuwa Khadija?" Khadijah ta yi shiru. Umma tace "ya kina wannan halin ba kya cin abinci, idan wani abun kike sha'awa ki faɗa min sai nasa Ibrahim ya kawo miki, kinsan kowa da yanayin laulayin sa, ki rinƙa kula." Khadija ta sake sunkuyar da kai. Gidan dai ga shi tsab a gyare amma ita a zuke, Umma ta kalli Dinning, "ko girki ba kya iya yi kenan, ay sai ki faɗa a kawo miki." ita dai babu bakin magana, Umma ta kawo mata ɗan abun taɓa wa harda peppersoup tayi mata irin dai uwa tazo duba ɗiyar ta mai ciki, Umma har da kayan fruits mai yawa ta kawo wa Khadija, dan ita Umma tinda tayi waya da ita taji bata da lafiya ta sawa ranta ciki ne da ita. "ko ba za ki iya cin abincin ba ki rinƙa daure wa kina haɗa fruit salad kina sha zai rinƙa baki energy, kuma abinda kike tare dashi zai samu kuzari." Khadijah dai Allah Allah ta ke yi kar Umma ta fahimci ko ruwan pure water babu a gidan, Allah ya taimake ta Mami ta kira Umma a waya tace mata sun sauka a airport yanzu zasu taho gida daga nan zasu wuce Bichi suyi kwana biyu, an tura Daddy UK sallama suka zo yi, da sauri Umma suka tattara suka tafi, ta ƙara jaddada wa Khadija ta rinƙa cin Abinci fa. 💫 UMAYMAH 💫 ✍️A&A PEN Follow our Whatsapp group via this link https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3 https://wa.me/+2348039352724 VOLUME ONE EPISODE 4️⃣3️⃣ Tun daga ranar Khadija ta samu sauƙin abinci, kullum Umma take aiko Ibrahim ya kawo mata. yana dawowa daga Boko kafin ya tafi Islamiyya yake kawo mata, ranar weekends kuma wajen 11 na safe ya ke kawo mata, duk zuwan da ya ke yi ba su taba haɗuwa da Tahir ba, Khadija sai ta samu sauki ta ɗan warware. Abinci mai yawa Umma take aiko mata dashi, sai take sawa a fridge in zata ci saita dumama ta ci da safe kafin a kawo mata wani. Kullum take shiga ɗakin Tahir ta gyara ta wanke mishi Toilet, yanzu bata da damuwar yunwa sai rashin kwanciyar hankali da nutsuwar zuciya, duk ta firgice ta fita hayyacinta, tana yawan kiran Munnirah tasa ta haɗa su da Hajiya a waya su gaisa, tun a waya munnirah ta so fahimtar akwai wani abu a tare da Khadija, ta tambaye ta, dan karta ƙara mata damuwa tace mata babu komai. Yau weekends tun safe taji fitar motar Tahir ta kalli agogo taga ko 8am batayi ba, ta fito ta gyara gidan, tana gamawa ta shiga wanka ta fito ta shirya ta saka riga da skirt, rigar sai faɗuwa take yi, ta kalli kanta a mirror, lallai ta rame ba kaɗan ba babu shiri ta canja kaya zuwa bubu ko zata boye ramar jikinta. Kira ne ya shigo wayarta Umma ce suka gaisa Umma tace gasu nan zuwa ita da Mami za su gaisa, hankalin Khadija a tashe ta ɗeɓo kayan gararta ta zuba a plate, ta rasa abunda yake mata daɗi, ana haka taji Almajiri yana bara da sauri ta je bakin gate ta yi mishi magana, ta karɓi robar shi ta aike shi shago, tace ya siyo mata zoɓo, ragowar kuɗin hannunta 700 ta bashi 500 ta tsaya jiran shi ya dawo, yana kawo mata ta karɓa ta bashi ladan 100 ta yi mishi godiya, ta je ta haɗa zobo ta zuba a jug ta saka a fridge yayi sanyi. Tayi shiru tana tuna yadda Tahir yake san soɓo kullum da daddare sai ya sha, taga yanzu yana yawan dafa tea, don da safe tana ganin tea pot ɗin da yake amfani dashi, komai babu na girki a gidan amma akwai kayan tea, shiyasa ta samu sugar ta zuba a zoɓon. Tana idar da sallar Azahar bacci ya kwashe ta a wajen, kamar a mafarki ta ji ana buga ƙofa firgigit ta tashi ta je ta buɗe, ganin iyayenta sai wani hawaye mai zafi ya zubo mata, Umma ta riƙe baki tace "To ko anan zamu tsaya ne." Khadija ta ba su hanya suka shigo, suka shiga Falon suka zazzauna, Mami tace "daughter haka kika koma? me yake damunki? anya kina cin abinci kuwa." Khadijah dai tayi shiru sai kuma tasa musu kuka, Mami tace "ko dai akwai matsala ne na faɗawa Daddyn ki? ko baki ji daɗin ganinmu ba." sai a sannnan ta samu nutsuwar share hawayen ta ta gaishe su, ta miƙe ta kawo musu kayan gara da zubon da tayi. Tana tashin Umma ta cewa Mami "ciki ne da ita. "haba har hankali na ya kwanta, duk ta yi wani iri ta fita hayyacin ta ashe laulayi ne." Mami ta faɗa. Umma sai bin Khadija take da kallo, Mami ta sha zoɓon sosai abinka da mai ciki da yake lokacin tana da cikin Hidaya, Umma cup ɗaya ta sha tace ya ishe ta. Mami sai ƙara kwantar wa Khadija hankali ta ke, tayi mata faɗan cin abinci sai sannnan su ka tuna sun manta abincin da aka taho mata dashi a Mota, Umma ta kira Aliyu tace idan zai zo ɗaukan su anjima ya daho da abincin da suka manta a mota. Anan su Umma suka wunar mata sai La'asar Aliyu ya zo ɗaukan su, Mami ta ƙara yi mata faɗan ta kwantar da hankalinta babu komai, su duk sun ɗauka laulayin ne ya maida ita haka. Khadija a ranta tace hmmmm ni a ina naga mijin ma bare nayi ciki, Tashin hankalin da ta ke ciki ma ya mantar da ita zancen ciki gaba ɗaya, tama dena shan pills din dan bata ga wani anfanin shan saba yanzu. Bayan tafiyar su Umma ta koma ɗaki ta kwana akan tilas kamar yadda ya zame mata jiki yanzu, Tahir ne ya shigo ɗakin da Sallama, kamar wanda aka yiwa dole, yace "magana zamu yi." ta ɗago kai ta kalle shi "inaga zaman nan naki ba shi da wani amfani gara mu hakura da juna kawai." Tun da ya fara mata magana ta sandare take binshi da kallo, wata zuciyar tace mata anya Habibin ta ne kuwa? Gashi dai a gabanta, amma kamar mutum mutumi haka ta zama, gaba ɗaya kanta ya kulle, da ƙyar ta iya buɗe baki ta ce mishi "meyasa? me na yi maka?." Idon ta yayi jaah, idan bata manta ba jiya jumma'a auren su five month kenan, ya katse mata tunani da cewa "nifa kawai ba zan iya ci gaba da zama da keba." Yadda ta kafe shi da ida nunta ko kiftawa batayi sai yaji wani iri, wata zuciyar tace mishi "anya kuwa ka kyauta Tahir, kamar Khadija bata cancanci kayi mata haka ba." Sai kuma da sauri wata zuciyar ta danne wannan tunanin da cewa "toh haka zaka zauna ka hana kan ka abunda kake so". "kai inaah" ya faɗa a fili yana kallon yadda hawaye kebin fuskar ta, fuskar ta ta yi jawur abinka da farar mace. Kawai saiya juya mata baya yana cewa "na baki just 2 days kiyi tunani." Yana gama faɗar haka ya fita ya bar mata ɗakin. Yana fita ta kifa kanta a cinya ta fashe da wani irin kuka mai cin rai, ta daɗe tana kukan, ta ji ana kiran sallar isha'i da dafa bango ta lallaɓa ta shiga toilet ta ɗauro Alwala a zaune ta gabatar da sallar dan wani jiri take ji. tana idar da Sallar ta ɗauko Alqur'ani, ta fara karatu hawaye yana zuba, ta daɗe tana karatun har saida taji zuciyar ta tayi sanyi. bata jin yunwa ta riga ta ci abinci ɗazu, a ranta tace yaushe rabon daya dawo gida da wuri, wata zuciyar ta ce "dan ya faɗa miki ya gaji da zama da ke ne ya dawo." Ta girgiza Kai sai kuma taji tashin motar shi ya fita daga gidan, Habibi da baya yawon dare, daga Company sai gida, amma yanzu sam baya zaman gida. Washegari Khadija tana zaune taji ana Knocking ta lallaɓa taje ta buɗe, Ibrahim ne suka shigo tare, yace "yaya khadija Allah kina tare da damuwa ki faɗa min mana dan Allah, gaskiya ba rashin lafiya ba ce kaɗai take damunki ba, kawai ki faɗa min abunda yake damun ki, kin ga ramar ki kuwa?" Khadija tayi shiru tana tunani Munnirah kaɗai take iya faɗawa damuwarta, gashi itama ta kanta take yi tata damuwar ma ta ishe ta, tinda Hajiya ta kwanta jinya basu haɗu ba, Ibrahim ya kuma cewa "Yaya Khadija." Firgigit ta dawo daga tunanin data tafi, tace "babu komai Ibrahim." "Hmmm babu komai yaya Khadija, amma kinsan wlh zan riƙe miki sirri, ko ba zan miki maganin matsalar kiba zan taya ki da addu'a." Baiwar Allah Khadijah maganar Ibrahim ba ƙaramin karya mata zuciya tayi ba, taji daɗin maganar shi, ta share hawayen daya zubo mata "ka taya ni da addu'a Ibrahim Allah ya daidaita min Al'amurra na." Badan Ibrahim yaso ba yabar maganar yace "Yaya Khadija an yi hutu Baba yace Bichi zamu tafi dukkan mu, har ya ɗauki leave." Maganar ba ƙaramin dukan ta tayi ba wani kuka ne ya taso mata ta ɗaure don kar ya gane halin da take ciki. Tasan ta shiga uku idan yan gidansu suka tafi Bichi, "Yaya khadija." muryar Ibrahim ta sake dawo da ita daga tunanin data tafi, bai jira ta amsa ba yace "ya na ga kin canja fuska, tinda bakya iya girki ya zaki yi da abinci idan muka tafi?" Tayi murmushin da yafi kuka ciwo "babu komai zai na yi mana takeaway." Ibrahim mutumin Tahir ne kafin auren su da Khadija in yazo hira kafin ya siya mata waya daya ga motar shi zai zo su gaisa, ya je ya faɗa mata, kawai saijin Ibrahim tayi yana cewa "ko dai Yaya Tahir ɗin ne ya canja miki, na ga duk kin damu dajin maganar tafiyar mu Bichi. Khadija ta daure tace mishi "babu komai." Ibrahim befi 5mins da da tafiya ba Khadija ta ji ana Knocking ta dauka ma shi ne ya dawo ko yayi mantuwa. Tana buɗe ƙofar taci karo da Munnirah a tsaye ita ma ta rame ta sake baƙi, duk da chocolate colour ce dama, amma jinyar mahaifiyar ta ya saka ta sake yin duhu sosai, kana ganin ta kasan tana cikin damuwa. Suka rungume juna ita da Khadija kowa da damuwar dake cin ranshi, Munnirah ta ce "my sis me ya same ki haka? Baki da lafiya ne?ko wani abu na damunki?" kamar Khadija jira take ta tambaye ta sai ta hau yi mata kuka kamar ranta zai fita, Muryar Munnirah na rawa tace "ina cikin damuwa Khadija amma ganin ki a haka ya firgita ni, me yake damun ki?" Wani tunani ne ya faɗo wa Khadija kawai sai ta yi shiru ta fara share hawayen ta, bai kamata ta ƙara wa Munnirah damuwa akan tata ba, dan haka kawai saita haɗiye tata matsalar ta cewa Munnirah "kulle Habibi ya ke yi min my sis gashi bani da cikakkiyar lafiya, shi yasa ma banje duba Hajiya ba, kiyi hakuri my sis babu yadda zan yi ne, kinga Zaliha ma yanzu bata zuwa, nakai wajan 2 months rabona da ita, inna kirata bata ɗauka kuma bata biyo baya, kaɗaicin duk saiya min yawa." Da tausaya wa Munnirah tace "haba my sis kuma sai ki daga hankalinki akan wannan, kina kallon kan ki a madubi kuwa? kinga wannan shi ne auren ki kwantar da hankalin ki, kullum kina raina my sis, yanzu ma zuwa na yi na miki sallama, Hajiya sai an yi mata Transplant na kidney saboda haka zamu tafi da ita Egypt Ni zan yi jinyarta, Baffah ne zai bata tashi ƙodar." Munnirah takai karshen maganar tana share hawayen fuskarta. Khadija na ganin haka itama kukan ta ya dawo Sabo, haka suka haɗa kai su ka yi kuka mai isar su, babu mai rarrashin wani a ciki su, kiran daya shigo wayar Munnirah ne ya katse musu kukan. Daga Asibiti ne aka kirata wani results ɗin Hajiya ne ya fito, dama sun ce idan ya zama ready za su kirata, Munnirah tace wa Khadijah "my sis ara min wayar ki na bi kiran nan kinga ya katse muna magana kuma waya ta babu credit." jikin Khadijah a sanyaye ta ce "ba ni da credit." Munnirah ta yi shiru sai kuma ta ce "shi kuma Tahir haka yake ba ya bada kuɗi, wasu mazan dama daga ka shiga ciki sai a hankali." Munnirah bata kawo komai aran ta ba ta cewa Khadija "naga wani shago a kusa bari na karɓo." ta fita bata daɗe ba ta dawo, ta bawa khadija credit ɗin 1000, da zata tafi kuma ta bata 5000 a cikin kuɗin da ƴan dubiya suke kawowa. Da farko Khadija ƙin karɓar kuɗin ta yi sai da Munnirah ta nuna ranta ya ɓaci Sannan ta karɓa tayi mata godiya, da ƙyar suka rabu suna ta koke koke, Munnirah ta ce zata kira Zaliha ma su yi sallama don jibi jirgin su zai tashi. Umma suna kallon News da Baba tace mishi "wlh jiya da muka je gidan Khadija da Mami, duk sai naga yarinyar nan ta fita hayayacinta kamar akwai abinda ke damunta." Baba bai bari Umma ta ƙarasa maganar ba ya hauta da faɗa "ku fa mata kun cika ƙananan maganganu, nan ta zo gidan nan gwanin sha awa, ke ma kin ce ciki gareta laulayi take yi ba dole ki ganta haka ba, ina nan ke lokacin da kika samu cikin ta wanka ma sai na yi miki, ba kya iya yin komai da kanki, kuma kin ce gidan ta kullum tsab yake, to kin gani kawai abinci ne zaki yi mata fada ko bata so ta daure ta rinƙa ci." Umma ta ce "Au abin har da gori kuma" 💫 UMAYMAH 💫 ✍️A&A PEN Follow our Whatsapp group via this link https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3 https://wa.me/+2348039352724 VOLUME ONE EPISODE 4️⃣4️⃣ Suwaiba ni fa aikin Na zaure yayi min amma me yake kawo tsaiko a raba auren nan ne har yanzu? Zaliha ta faɗa tana kallon Suwaiba, "Amma babu wani cigaban bayan wannan? Suwaiba ta tambaye ta, "toh akwai dan yanzu ni ke ba shi break fast, kuma kullum muna tare, ya ce min ma zai rabu da ita, Amma har yanzu shiru nake ji" Suwaiba ta yi shewa "lalle mutuniyar kina zamani" Zaliha ta yi murmushi ta ce "ina faɗa miki ya buɗe min bakin Aljihu sosai wlh, kullum shi ya ke kawo ni gida. Mama ce ma ta fara zargin wani abu a tsakanin mu tuni na sa aka rufe mata baki karta bani matsala, kinsan Mama yadda ta ke son mutanen nan." "tunda akwai kuɗi a hannunki yanzu akwai wani

Chapter 22 of 29