"Yayana mu na da rauni, pls sai ana lallaɓa mu."
"in sha Allahu babu nadama, fatana dai abani dama mu fuskanci juna.
"ba ka da matsala, duk da dai candidate ɗina yayi loosing." Da sauri yace "nima candidate ɗinki ne our friend."
Munnirah tayi dariya "I'm not only her friend, I'm also her Aunt, ina auren Yusuf Isma'ill Bichi.
"oh really? ah Maman mu ce ashe, pls ina kama ƙafa.
"baka da damuwa. "toh bari na bar ku, anjima zan kira.
"ok then" Munnirah ta faɗa, tayi hanging wayar. Khadijah ta fito daga Toilet, Munnirah ta hau yi mata guɗa, bata kula ta ba ta shinfiɗa sallaya ta tayar da sallar walaha.
******
Uncle Isma na kwanto kura wlh ta faɗa a sanyaye, Ismael ya kalle ta, duk sai yaga tayi kalar tausayi, abinda zai sa Umaimah ta yi laushi haka ba ƙarami ba ne, yace "faɗa min me kika yi mu nemo takunkumi mu sakawa kurar."
Bata iya yin magana ba sai miƙa mishi letter da tayi. ya karɓa ya karanta, ya ɗago ya kalli Umaimah "me kika yi aka baki suspension." Ta fara inda inda.
"ki faɗa min gaskiya mu san yadda zamu shawo kan matsalar, dan gaskiya wannan ya fi ƙarfi na.
Umaimah najin haka ta fashe da kuka, Isma'il duk sai yaji babu daɗi, yace "ya isa, ki yi shiru mu nemi mafita." ta fara goge hawayenta, ya kuma cewa.
"me kika yi?
Umaimah ta yi mishi bayanin komai. Ya sauke ajiyar zuciya yace "yaushe Principal ta ke barin school"
Actually ban sani ba, amma dai tana ɗaɗewa after school."
"taso mu je kafin lokacin Islamiyya."
Da sauri ta miƙe su ka fito. Umma na kula da yanayin da Umaimah ta shigo gidan, jikin ta a sanyaye ga damuwa a tare da ita, yau ko ita bata kula ba, Sasi ma da tazo wajenta tana kaɗa mata jela, ƙin kula ta tayi, kai yau har abinci bata nema ba.
Suna fitowa suka yi hanyar fita, suka ji muryar Umma na cewa
"A'a ina za ku ko uniform ba ki cire ba? Ismael ya ce akwai abunda ta manta a makaranta zan rakata ta ɗauko. "
shi abun bashi da suna? Siyama computer da Baban ABU ya bani na manta a School. Umma tace "Ah to maza rakata ta ɗauko, Ibrahim yana nan bari nasa Baba Rabi ta kira shi ya kai ku." "Baba Rabi" Umma ta ƙwala mata kira.
"Umma ki bar shi, Abbas abokina yana waje zai ajiye mu."
"To shikenan sai kun dawo."
Suna zuwa Allah ya taimake su motar principayl tana nan, suka yi knocking office ɗin ta "yes come In" suka shiga, Isma'il ya durƙusa ya gaishe ta, Umaimah ma ta durƙusa ta yi shiru
"how may I help you? principal ta tambaye su.
Uncle Isma ne yace "Mah pls she is deeply sorry for her actions and she promised not to repeat it again, pls maah." ya hada hannu pledgedly.
Isma'il ya faɗa hopefully ko principal zata yafewa Umaimah.
"I'm very sorry maah pls find a place in your heart to forgive me pls." Umaimah ta faɗa a karye.
"it's okay, but I want to see some one elderly not your immediate brother." Umaimah ta ce "he is my Uncle maah.
"oh really? but I want to see someone elderly, apology accepted."
"thankyou maah, thankyou." Suka haɗa baki.
Suka fito daga office ɗin suna ta murna, amma tace some one elder yanzu ya ya kenan?
Readers mu ma tambaya muke, yanzu ina Umaimah zata sa kanta? wanda ya san solution ya faɗa mana a comment section.
💫 UMAYMAH 💫
✍️A&A PEN
FOLLOW OUR WHATSAPP GROUP VIA THIS LINK https://whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3
https://wa.me/+2348039352724
VOLUME ONE
EPISODE 2️⃣6️⃣
Akan hanyar su ta dawowa gida Umaimah tayi shiru, tunani take yanzu ya zasu yi gashi gobe akwai makaranta, kuma dole ne in zata je goben sai sun tafi da wani daga gida kamar yadda Principal tace.
"Uncle Isma yanzu ya zamu yi?" Isma'il ya sauke ajiyar zuciya "Umaimah bakya jin magana, jiya na gama yi miki faɗa akan tsokana, da ƙyar na bawa Ustaz haƙuri, amma yau kin sake ɗakko wata maganar, shi ke nan ni nayi miki iya abunda zan iya, wallahi babu ruwa na sai kisan yadda zakiyi tinda ke bakya jin magana."
Umaimah idanunta suka tara ƙwalla, barin ma inta tuna Baba baya nan, sai taji hankalin ta ya sake tashi. Kawai saita fashewa Uncle Isma da kuka dan wallahi bata san yadda zata yi ba, tsoranta Allah tsoran ta Uncle Aliyu yaji abinda ta yi wallahi tasan saita daku.
Aliyu bai fiya duka ba kafin ya dake ka za'a daɗe, yafi gane ya baka Punishment ɗin da gobe in akace kayi lefin ma baza kayi ba, saboda wahala. Yasan different types of punishment masu ladabtar da mutum cikin sauƙi, kodan boarding school yayi, amma fa duk randa ya riƙe ka da sunan duka lallai zaka faɗa wa ƴan garin ku, shi yasa shi aka ran kansa baya son yin duka, dan yasan bai iya yinsa ba.
Yadda ta kife kai tana kukan ba ƙaramin tausayi ta bawa Uncle Isma ma ba, to amma shi kansa bai san yadda zasu yi ba. Can wata dabara ta faɗo wa Uncle Isma da sauri yace "kiyi shiru na samo mana mafita." Tana jin haka ta share hawayen ta da sauri, ta zuba masa ido tana neman ƙarin bayani.
Uncle Isma a ransa yayi dariya yace lallai yau abun na gaske ne, Umaimah ke kukan gaskiya ba fake one ba.
"Yanzu dai kinsan yadda za'ayi?" Da sauri ta girgiza masa kai "mu samu Yaya Ibrahim mu roƙe sa goben ya rakaki." Umaimah tayi shiru tana tunani "amma Uncle Isma kasan Uncle Aliyu ne yake kaimu makaranta, taya zamu bi Uncle Ibrahim?"
Uncle Isma yayi shiru, shifa kansa ya kulle, wallahi sai yanzu ma data faɗi haka ya tuna Aliyu keda alhakin kaisu makaranta kullum.
Umaimah ta sake yin raurau da idanu zata sake kuka yace "kinga ki bari in muka je gida zan yi mana tunanin yadda za'a yi."
*****
AMERICA
Fahad ne zaune akan sofa ya miƙe ƙafafunshi yanata operating system, tinda ya tashi yake akin, wasu important document ɗin shi yake so ya gama haɗa wa. Sa'ad ne ya shigo ɗakin ya kalli Fahad ɗaya duƙufa yana aikin shi.
"hi guy, har yanzu baka gama shigar wa bane? harna dawo fa." Fahad bai kula saba yaci gaba da aikin sa, Sa'ad yayi murmushi a ransa yace yanzu zan saka ka magana. Tsalle yayi ya faɗa kan gadon Fahad da yake a gyare kamar ba'a taɓa kwanciya akai ba, tsabar yadda ya gyara gadon zaka ɗauka ba'a taɓa hawan saba. Fahad najin faɗuwar abu ya ɗago kai yayi Ido biyu da Sa'ad akan gadon shi ya wani baje yana sauke numfashi, a ƙufule yace "dalla Malam fitar min daga ɗaki?"
Sa'ad ya sake juyawa akan gadon yace "anƙi a fita ɗin, hey, bari kaji duk wannan fushin da kake yi bashi zai hana na haɗa ka da Daddy ba, wallahi gobe indai baka bini munje munga Dr ba, Allah saina faɗa wa Daddy."
Sa'ad na faɗin haka kuma saiya tashi daga kan gadon, ransa a ɓace yace "koda yake ma babu komai bazan faɗa masa ba, Isma'il kayi duk abin da kake so, ni me ne ya dame ni, ba rayuwar ka bace? Mallam Bahaushe dai yace, kowa rai ya yiwa daɗi baya meshi ba. Amma ni nasan ina sanka, na kuma damu da kai da lafiyar ka shi yasa kullum burina naga ka samu lafiya ka dawo kana rayuwar farin ciki kamar kowa. Isma'il ina burin naga wata rana mun haɗu in one plate munacin abinci tare kamar ko wasu ƴan uwa, saboda ni bani da kowa sai kai, kai kaɗai ne ɗan uwa na kuma Aboki na. Amma tinda muka taso nake cikin maraici jina nake kamar ni kaɗai su Mami suka haifa, saboda baka da nutsuwar zuciyar sakewa dani yadda ya kamata, Isma'il imagine ina da ɗan uwa ace ban isa na taɓa kayan saba, ban isa nasa kayan kaba, saboda inna sa sai dai kai ka hakura da shi gaba ɗaya ba zaka iya sake amfani da shi ba. Ina so ace mun haɗa ɗaki ɗaya, gado ɗaya abun rufa ɗaya, kamar dai sauran ƴan uwa maku santa, amma duka wannan ba zai taɓa yiwuwa ba, Fahad bazaka iya haɗa ɗaki dani ba, inna shigo ɗakin ka ina fita kake sake gyarawa, ban isa na shiga toilet ɗin kaba, duk randa na shiga Isma'il wuni kake kana wanke wa. Ƙasa ɗaya muke karatu, a inda babu Iyayen mu, babu kowa namu sai mu kaɗai, amma a ɗaki daban daban muke rayuwa. Isma'il Ibrahim Bichi ka faɗa min yau, bayan sunan ɗan uwana da kake amsawa menene na ɗan uwan taka dake tsakani na dakai?"
Sa'ad yaɗan dakata da magana, idan sa yayi ja, har cikin ransa yake jin ciwon halin da Fahad yake ciki. Abinda yafi damunsa, ya kuma damu iyayen su, shi ne. Shi kan shi Fahad yaƙi yarda da matsalar sa, bare ya taimaka wa kansa, wajan ganin ya samu lafiya kamar kowa, yasha ganin masu matsala irin tasa, sun warke sunci gaba da rayuwa, kamar dai sauran mutane, amma mai yasa shi ba zai basu haɗin kai wajan ganin ya samu lafiya ba.
Sa'ad yaji an dafa shi, yasan Fahad ne, amma sai yaƙi ɗagowa ya kalle shi.
A hankali Fahad yace "why are you talking like that Ad?"
A ƙufule Sa'ad ya kaɗar da hannun shi daga kan kafaɗar shi "abinda zaka cemin ke nan ko?" Kafin Fahad ya haɗa abinda zai cewa Sa'ad har ya kai bakin ƙofa zai fita, cikin zafin nama yasha gaban shi, zai iya rantse wa da Allah tinda suka taso bai taɓa ganin ɓacin ran Ad irin na yau ba. Bashi da abokin hira sai Ad, amma kullum cikin lallaɓashi yake, ko kowa yaƙi yayi supporting nashi akan abu, Ad is the one person dake goya masa baya. Bayan Ad ɗin shi baya jin akwai wanda yake iya zaman 30minutes dashi. Yana hira da Daddy, amma ko kusa ba kamar yadda yake yi da ɗan uwan shi ba.
"Malam ka saka ni a gaba kana ƙaremin kallo, matsa na barma ɗakin ka, dama ai haka yana cikin burin ka, kayi ta zama kai kaɗai cikin ƙuncin zuciya da rashin farin ciki."
Fahad ya buɗe duka lusassun idanunsa ya kalli Sa'ad, ya sake gyara tsaiwa a bakin kofar hannun sa ya tura a cikin sumar kansa yana murmushi yace "wai yaushe ka iya drama ne Ad? Common bro yanzu dai yi haƙuri."
"Anƙi a haƙuran, Kum......... Fahad bai bari ya ƙarasa maganar ba ya rungume shi yana ɗan bubbuga bayan shi yace "it's okay, you know i love you bro, i don't want you to be angry with me, so i will follow you tomorrow in sha Allah." Fahad zai sake maimaita maganar as usual kamar yadda yake a tsarin ciwon shi in yayi magana saiya sake maimaita wa (Repeatedly), Sa'ad ya ɗago yana murmushi ya rufe masa baki "karka maimaita."
Fahad ya kalli idanun ɗan uwan shi, sai yaji wani abu mara daɗi na taɓa zuciyar shi.
Ad kaɗai yake iya yin dogowar magana dashi, ya jisa freely, haka zaita maimaita masa magana ɗaya (Repeatedly), amma bai taɓa nuna masa gajiya ko ƙosawa ba, yadda yanzu ya hanasa maimaita maganar sai yaji kamar ko shima ya fara gajiya da halin sane.
Kamar Sa'ad yasan me Fahad yake tunani yace "hanaka maimaita maganar da nayi yanzu is part of your therapy, will you remember?"
Mai makon ya basa amsa, kawai sai yaja hannun shi suka koma cikin ɗakin suka zauna. This is the first time da Fahad yake maganar ciwon sa da kansa.
Silently yace "My life is boring, I'm not happy at all. I believe that someone like me who's mentally disabled, i feel alone, I'm emotionally broken, you can't feel my pains, Ad you don't have idea how it hurts to be a person with COD ( Obsessive Compulsive Disorder). I know yadda kuke kallona a wanda bai damu da kansa ba, wanda bai yadda da ƙaddar saba, hmmm is not like that, but like i said, i will see the Dr in sha Allah. Shi ke nan ba?"
Sa'ad ji yayi zuciyar shi na wani irin bugawa kalaman Fahad ba ƙaramin melting heat ɗin shi su kayi ba, he's totally and completely speechless. Duk sai yaji sa wani iri babu daɗi. Jikin Sa'ad a sanyaye yace
"Please forgive me for the words i said to you, i don't mean it, i just want the best for you "
"Hi forget it, we will be happy together in sha Allah till death do us apart my dramatic brother."
Sa'ad yayi dariya yace "is not even close to drama, but I'm so happy al least you talked about it."
Fahad ya girgiza kai suka rungume juna, murya ƙasa ƙasa Sa'ad yace "i love you Dattijo." Da sauri Fahad ya ture sa yana hararar shi.
Sa'ad ya kwashe da dariya yace "Dattijo yada haka karka karya ni kayiwa my Ferry asara, ka hanani more angonci na nan da few months."
Fahad yace "Banza humanizer kawai."
"Naji na kuma yarda."
Fahad ya tsani ace masa dattijo, tin suna yara in Sa'ad nason tsokanar shi to yace masa Dattijo yanzu zasu haura.
💫 UMAYMAH 💫
✍️A&A PEN
Follow our Whatsapp group via this link https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3
https://wa.me/+2348039352724
VOLUME ONE
EPISODE 2️⃣7️⃣
Da daddare suna gamayin dinner Umaimah ta kalli Uncle Isma'il irin how far ɗin nan, ya nuna mata Uncle Aliyu da ido yayi mata alamar ta basar, Umma dake kallon yadda suke wa juna magana da kwatance kamar marasa gaskiya tace "wai Hakimi me kuke ƙullawa ne kaida ƴar taka?"
Umaimah tayi sauri tace "Allah Umma kinsa mana Ido, babu dama muyi zumuncin Allah sai kinyi magana."
Umma ta kama baki "au haba, ni naga kashin awaki ma, kude ƙulla alkhairi."
Aliyu ne ya fara yiwa Umma sallama ya fice, yana fita Umaimah ta sauke ajiyar zuciya tace "Allah har naji wata iska mai daɗi ta shigo."
"Da Babangidan ya fita ne kikaji iska mai daɗin ke nan? Gaskiya nidai Umma ba haka nace ba." Tana faɗin haka kuma saita juya wajan Ibrahim ta wani kwantar da murya
"Uncle Aminin Baba dan Allah zamu saka labule." Ibrahim ya kalleta da ɗan mamaki yace "tofa yau kuma dani za'a saka labulen, anya kuwa ba manta wa kika yi ba Umaimah? Kodai Isma'il kike son cewa?" Umaimah ta wani ɓata fuska "haba my second father ya zaka ce haka." Uncle Ibrahim ya juya gefe da gefen sa yana leƙe kamar me neman wani abu yace "wai dawa Umaimah take ne jama'a?. Umma tayi dariya "ahab nidai nasan wannan haɗa kan da suke da Hakimi tin rana dole akwai wata a ƙasa." Gaskiya dai Umma Allah ki daina shiga tsakanin zumunci.
"Nayi shiru to. Khadija ta miƙe tace Umma saida safe Amira tabi bayan ta.
Uncle Ibrahim ya gyara zama yace "to tunda dai naga da gaske dani kike, yau nima na ɗana set ɗin Uncle Isma, ina jinki ya akayi?" Ta kalli Uncle Isma ya girgiza mata kai, tace "Uncle Aminin Baba ai maganar sirri ce iya mu uku zamu yi ta nida kai da Uncle Isma." Umma ta buɗe baki.
"a takaice dai ana nufin na tashi ke nan?" Umaimah tace "yawwa Umma kin gane ashe." Ibrahim yayi murmushi "lallai maganar babba ce, to Umma saida safe a asibiti zan kwana yau 9:30pm zan fita. Ku kuma muje naji menene." Umaimah tayi sak jin yace a asibiti zai kwana. "Muje mana 9pm ya kusa karna makara. Uncle Isma ya kalli Umaimah yaga ta wani ɓata fuska.
"Yaya kawai ma shike nan tinda kana sauri gobe mayi maganar." Uncle Isma ya faɗa. Ibrahim ya kalle su "kuma dai? Nima nayi ta Umma, anya kunada gaskiya kuwa?. Umma tace "bana faɗa maka ba."
To ai shi ke nan tinda kunce haka, Allah ya kai mu goben. Umma ni na tafi saida safe."
Uncle Ibrahim ya fita Umma ta bisa da addu'ar Allah ya bada sa'a.
Saida Umma ta haye sama sannan Umaimah ta kalli Uncle Isma tace "ya zamu yi ne? Uncle Isma yayi shiru yana tunani can yace "Yawwa ki samu Yaya Khadija ta rakaki goben, amma fa karki faɗa mata saikun je makarantar in ba haka ba ba zata rakaki ba.
Khadijah harta kwanta taji ana knocking ƙofa, tana buɗe wa Umaimah ta shigo jikinta sanye da riga da wando na barci kanta babu hula ta ɗaure gashin ta a tsakiyar kanta, Khadijah ta maida ƙofar ta rufe, kai tsaye Umaimah ta haye kan gadon ta, tayi ɗai ɗai, Khadijah ta bita da kallo.
Khadijah na hawa gadon Umaimah tayi mata shin kai da cinyar ta tace "Ammi alkawarin da kika yi mana nida Amira baki siya mana ba?
"Oh! Umaimah abinda ya kawo ki ke nan? Naji zan siya muku gobe inna fita, shi ke nan? Umaimah na murmushi tace "yes Ammina, amma fa anan zan kwana yau bazanje ɗakin Umma ba."
"Umma tasan kin taho nan?
Umaimah ta ɗaga kai "okay to kwanta kiyi barci lissafi zanyi karki dame ni ko na kora ki yanzun nan."
Tana kwance akan cinyar ta nata mata surutu, har tayi bacci, Khadijah tabi fuskar Umaimah da kallo tana ƙara girmama ikon Ubangiji, wato Umaimah babu inda tabar mahaifin ta, komai nasu iri ɗaya ne, yanzu da take barci a gaban ta, saita sake koma mata shi exactly, har yanda yake cure baki idan yana barci, wani abu taji ya taɓa zuciyar ta, sai kuma tayi sauri ta kauda tunanin a ranta.
Washegari da safe Umaimah taƙi ta shirya akan lokaci har su Amira suka tafi suka barta, dole Umma tace "Khadijah yi haƙuri ki sauke ta a makaranta."
Umaimah najin haka ta daka tsalle a ranta tace "yes" dama plan ɗin da Uncle Isma yayi mata ke nan.
Suna zuwa gate ɗin makaranta Umaimah ta zuge jakar ta ta ɗakko suspension letter ta bawa Khadijah.
Khadijah ta karɓi letter cikin neman ƙarin baya ni. Umaimah tace "Ammi ki duba zaki gani." Khadijah bata sake cewa komai ba ta buɗe letter, saida ta gama karanta wa tsaf sannan ta ɗago ta kalli Umaimah
"Umaimah bazaki canja bako? For how long zakiyi ta rashin jin nan ne Umaimah? Okay yanzu na gane, wannan shine dalilin da yasa jiya kika ce a wajena zaki kwana ko? Wato nice dai-dai rako ki inda kika yi rashin jinki ko Umaimah? Anyway babu inda zani tinda bakya jin magana, wanda kike gudun yaji abinda kika aika ta ɗin shizan faɗa wa." Khadijah ta buɗe jakar ta ta ciro wayar ta, Umaimah tayi sauri ta rike mata hannu.
"Ammi dan Allah karki kira Uncle Aliyu Allah duka na zai yi."
"Eh ai gwanda ya dake kin tinda mu duka kin raina mu, babu wanda ya isa ya faɗa miki kiji." Umaimah ta yarfa hannu idanunta suka cika da ƙwalla tace "Ammi dan Allah karki faɗa masa, Allah bazan sake rashin ji ba."
Khadijah kawai sai tayi shiru tana kallon Umaimah, yadda take yarfe hannu fuskarta a ɓace, sai ta tuna mata da wata rana, randa ta zame mata farko kuma ma farin haɗuwa da ƙaddarar ta, exactly haka ya rinƙa yafe hannu a ranar
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 14 Chapter of 29