Share this page
je I was in Bichi two days ago." "What?" Sa'ad ya faɗa, "amma baka kyauta min ba, wai kai haka ake yi ko shiyasa Daddy ya ke min dariya yace na same ka mu yi magana, amma ba ka yi ba wlh." Fahad ya hau gado ya ja blanket, "pls switch off the light when leaving." ya lumshe ido alamar bacci zai yi Sa'ad yayi ƙwafa ya fito daga dakin bayan ya kashe mishi fitila. Umaimah keta daru jin Amminta zata Umara bata sani ba "Wallahi ba wanda ya fada mi." Munnirah sai rarrashinta ta ke yi zasu tafi airport, Khadija da lallashi tace "yi hakuri ki faɗi duk abunda kike so na siyo miki sati biyu kawai zan yi." Sa'ad yace "haba mutuniyar yi haƙuri muma zamu je ne ke mai neman kudi ma." ta share hawayenta "kuma haka ne." su Daddy sun fito suma za su wuce Lagos, Sa'ad kuma za shi Pothacourt, suna tsaye Aliyu ya fito shi zai kai su Khadija airport, Baba kuma shi zai tuka su Daddy, sai Ibrahim daya ɗauki su Umaimah. Suna isa airport aka raka Khadija International wing har an fara boarding za su tashi jirgin Egypt za su bi, "ki siyo min camera dan Allah." Umaima ta faɗa tana rike da hannun ta, Khadijah ta amsa da "in sha Allah." aka yi musu fatan Alkhairi suka shiga domestic wing, su Daddy sun dan jira kamar na awa ɗaya sannan suka tashi familyn biyu suka yi sallama ci ke da kewa. LAGOS Ya daɗe yau yana aiki a system ɗin shi dan lunch ma Mami ce ta aiko Deborah ta kawo mishi daya ke ba maabocin cin abinci ba ne sosai, sai ya yini be ci ba, sai dai coppee da biscuit har mamaki Mami take yi daa bashi da ulcer, kuma idan zai cin kamar na yaro karami, ya tashi ya je yayi sallah ya dawo ya tarar da mail a inbox ɗin shi ya buɗe content mail ɗin he was shocked and surprise offer ce ta aiki aka turo mishi na wani construction company a UK, yana yawan saka ayyukan da yayi a shafukan sada zumunta tare da email ɗin shi, don har ya fara tunanin kafa na shi company anan Lagos ya buɗe a hankali kafin ya mike, ya zurawa mail ɗin ido Dear ismael Ibrahim Bichi, Morgan sindall Group. We are pleased to offer you a job as asisting manager at morgan sindall group as outlined above. please confirm your acceptance by signing and returning one copy of this letter to us on time. Sincerely Mr Williams Group manager Morgan sindall Group. Ya rasa murna zai yi ko akasin haka sabida shirin shi yayi nisa sosai he wants to be independent dan har sunan company shi ya fitar. Sa'ad ne ya shigo ɗakin da sallama yana goye da jaka a bayan shi, "Guy guess what? Sa'ad ya faɗa yana kallon Fahad he looks absent minded kawai ya kalli Sa'ad ya ɗauke kai, Sa'ad ya miƙa mishi takardar da ya fito da ita daga aljihu, ya karanta ya kalle shi da sauri ya rungume shi "congratulations brother ya mika mishi hannu su ka yi musabaha." Fahad yayi mishi murna sosai ko bai faɗa ba fuskar shi ta nuna hakan, "thank you." Sa'ad ya faɗa, sai kuma yace "wlh I never throught wai offer za a bani I'm sooo happy." ya kwanta a gadon Fahad da yake a gyare, Fahad ya harare shi ya san me yake nufi yayi dariya yace "ba wanda na faɗawa sai kai, infact ba wanda ya san na dawo, mun dai yi waya da Daddy, bari na shiga ciki ya tashi, Fahad ya kura mishi ido yana so ya faɗa masa shima ya samu aiki amma kuma maganar ke masa wahala. Sa'ad ya faara gyara mishi gadon ya mike har ya kai kofa yace "wait." ya miƙe ya kashe system ɗin suka jera suka fito. Mami da Daddy suna kallon Aljaxeera a palor suka Shigo "barka da yamma Daddy, barka da yamma Mami." Sa'ad ya faɗa ya zauna a ƙasan carpet, "ah ah yaushe ka dawo?" Mami ta tambayi Sa'ad, "not long ago." ya faɗa, Fahad ya zauna a kusa da kafar Daddy, ya shafa kanshi very calm yace "good evening sir, evening Mami." Suka kalle shi, shi gaisuwar shi kenan. Fahad bature ne mafi yawancin lokaci ya fi yin turanci akan Hausa, "sannun ku bari Deborah ta kawo maka abinci." Mami ta faɗa tana kallon Sa'ad, "no Mami I'm okay." Daddy yace "ya ka bar su Surayya da maigidan ta? "suna lafiya." ya miƙa wa Daddy takardar hannun shi "toh me muka samu?" Daddy ya faɗa, "Darsha miko min glass ɗina." Mami ta mika mishi ta zauna kusa da shi Daddy yana karantawa yana murmushi ya miƙawa Mami takardar "Alhamdulillah, Masha Allah, shi Dr ɗin ne ya sama maka aikin." Sa'ad yace "eh." "zan kira nayi mishi godiya, waje ne mai kyau NNPC fah daga yaran gwabnoni sai masu mulki ake bawa aiki a wajen Allah ya sa albarka." Amin su ka amsa Mami tace "ay Nigeria kullum baya mu ke yi Allah ya kyauta." "naga sun saka on 14th ka yi reporting Allah ya taimaka bari na kira Dr nayi mishi godia." yayi dialing number not reachable, "anjima na kira." Daddy ya faɗa yana aje wayar a gefen shi. Fahad ya buɗe mail a wayar shi daya ke ya sauke mail ɗin a waya ya miƙawa Daddy wayar ba tare da yayi magana ba, Daddy ya karɓi wayar yana kallon shi sai kuma ya maida idon shi kan screen ɗin wayar, ya karanta da sauri ya ɗago kai ya kalli Fahad "Morgan company is one of the best Company in UK fa." Sa'ad sai ya zama lost, Daddy daɗi ya ishe shi Sa'ad ya karɓi wayar ya karanta ya zo ya rungume Fahad da sauri, "wannan good news ɗin kaƙi faɗa min da baza kayi magana ba ai saika nuna min." Sa'ad ya san ba magana zai yi ba, Mami tana ta murna tace "Allah ya sa Albarka yasa ku amfana." Daddy yayi gyaran murya hankalin su ya dawo kan shi, "Alhamdulillah. ya kalli Fahad yace "ka yi accepting aikin? "not yet Sir." ya bashi amsa, "ya kamata ka yi Allah ya sa albarka, and again Dada tana ta ƙorafin ajiye iyali, nima kuma is high time gaskiya ga shi kun samu aiki saboda haka sai ku fara kokarin settling down." Sa'ad yana murmushi yana shafa kai Mami ta ce "kowa ya san you are ready." ta fada tana dariya, "Kodayake Fahad ma Aysha ta zo kafin mu je kano." Fahad ya kalli Mami "No Mami is not what you think." Daddy yace "to yi mana bayani." da kyar yace "she is just a friend nothing more." "dama akwai wani abu tsakanin mace da Namiji na abota? don't bother yourself I understand mu iyayenka ne kar ka ji kunya sunnar ma'aiki za a raya." shi Daddy duk ya ɗauka Fahad kunya ya ke ji, "No Daddy." ya ƙara faɗa kamar ya fashe da kuka, "ba haka ba ne Aysha is my friend." Daddy yace naji she is your friend, and only your friend can tolerate you, is a good thing ta san yanayinka I guess she can cope with the challenges, so is not a big deal." Fahad ya buɗe baki zai yi magana Daddy ya ɗaga mishi hannu, "enough I understand you can go." suka miƙe Fahad da ganin shiya koma dishi dishi tsabar tashin hankali Sa'ad yayi mishi jagora su ka fita. Daddy ya kalli Mami "don Sa'ad sun buƙaci yayi reporting da wuri amma ni tunani nake idan komai ya kammala a haɗa auren su da na Khadija kawai a huta, Mami tace "hakan yayi." "Okay zan kira yan uwa na mu tattauna su je su nema musu auren ayi a huta gaba-daya." Daddy ya faɗa yana dialing number Baba. 💫 UMAYMAH 💫 ✍️A&A PEN Follow our Whatsapp group via this link https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3 https://wa.me/+2348039352724 VOLUME ONE EPISODE 5️⃣4️⃣ Daddy ya yi wa Baba bayanin komai a waya "Alhamdulillah Alhamdulillah, amma na ji dadin labarin nan, toh nima da labari na zo maka ɗan ka mai sunan ka ya samu offer a National hospital." Baba ya faɗa cike dajin daɗi, Daddy yace "kai masha Allah abu yayi kyau Allah ya sa mu su albarka, sai ya zauna a gidan Baban shi likita." Baba yayi dariya "yanzu muka yi waya da Dada nace mata sai ya zauna wajen likita tace salon Zainab ta yi mishi horon yunwa da dai Munnirah ce a Abuja sai ya zauna acan ita ma data je bata ji daɗin zaman ba." Daddy yace "Hajiya Dada kenan Allah dai ya ja kwana." "Amin." Baba ya amsa, Suka karkare akan za su nemi magabatan Amaren a tsayar da magana tunda dai sun fuskanci juna. Baba ke ta jinjina maganar Fahad Daddy yace rabu da dan yau Muhammadu da baya so ya kula ta? har ya iya yi mata kwatancen gida, a hali irin na Fahad wai mu zai yiwa wayo haba yaushe aka haife shi, idan kaga ba a ɗaura auren nan ba toh sai dai wani ikon Allah, zan kira Amal ɗin an ce ita ta karɓi lambar wayarta, ta tambayi kwatancen gidan nasu an ce a nan Lagos iyayenta su ke zama, shi kuma ɗan naka sai kumburi ya ke yi ɗazu da ya fita, na san ba za a kwashe ƙalau da shi ba amma na shirya mishi." Baba ya girgiza kai " lamarin Dattijo sai addu'a Allah dai yasa abokan arzikin sune." Daddy ya amsa da Amin. LEBANON Tinda Tahir ya dawo Lebanon basu samu kwanciyar hankali ba saboda mutuwar kakar su, wanda zafin mutuwar ya tayar da hawan jinin Ummi, yau tsawan sati biyu ke nan da rasuwar Jadda amma har yanzu suna asibiti da Ummi. Tahir yayi shiru ya dafe kanshi Yasir ya kalle shi da tausaya wa, yace "Akhi ka yi haƙuri Ummi ta ƙara warware wa tashin hankalin da ta shiga Rasuwar Jadda (kakarsu )shi yasa jinin ta ya hau sosai and kaima ba na jin daɗin ganin ka a haka ka kwantar da hankalin ka komai zai yi daidai in sha Allah, ka ƙara kiran Baba Isah mana." Yasir ya faɗa yana kallon shi,Tahir ya motsa baki da ƙyar "shima har yanzu ba a dace ba, jiya mun yi waya." "Toh ko matar da ka aura zaka tambaya? Shi yanzu ina ya san inda ta ke ma, ya ma manta da wata Zaliha duk halin da ya shiga ita ce silah ,ba zai taɓa yafe mata ba, ya kalli yaseer yace "ina jiran Ummi ta samu sauki sai mu tafi Nigeria tare duka har da kai, Naso na fara ganin Khadija kafin na je ga iyayenta amma haka zan je Bichi kawai, shi ma Baba Isah cewa yayi ba zai iya zuwa shi kaɗai ba yana jin Nauyin su." Tahir ya faɗa wata jijiya ta fito radau a gefen kan shi, abunka da farin mutum idon shi yayi ja. Tarin da Ummi ta yi ne ya saka suka yi kanta da sauri Tahir ya taɓa kanta ta buɗe ido, yace "kayfa haluk ya Ummi (how is your condition Mom)?" ta motsa baki a hankali tace "Alhamdulillah. "shifakillah (may Allah heal you)." Yaseer ya matso yayi mata kiss a goshi ya cewa Tahir bari ya kira Dr yace idanta farka ya kira shi. ******* LAGOS Tun jiya Fahad yake jin jikin shi haka dai kamar mara lafiya jikin shi ya ɗauki zafi kamar mai zazzabi, ga wani yawu mai daci a bakin shi, Sam ba shi da appetite kan shi ba karamin ciwo yake mishi ba, he is not ready a bar shi da yanayin da ya ke damun shi za a ƙara mishi liability for God sake, dole yayi wani abu a yadda Daddy yayi maganar jiya ya san he is serious about it, Daddy kaifi ɗaya ne idan yace eh to shi ne final, idan yace ah ah toh ah ah ce, ya sauko daga kan gado ya shiga Toilet ya fito da rigar wanka a jikin shi, ya tafi wajen wardrobe ya dauko fararen boxes da singlets ya ɗau turare yana ta fesawa, Sa'ad ya shigo da sallama ya amsa be kalle shi ba yace "Guy what happened? you look sick. kamar wanda yayi cuta ,ka gan ka kuwa are you OK?". Ya matso ya taba jikin shi ya ji zafi sosai ya dauke hannun shi da sauri "your temperature is high." Kawai Fahad sai ya fara ganin dishi dishi kamar wasa ya yanke jiki ya tafi zai faɗi Sa'ad ya taro shi da sauri ya fada a hannun shi yayi mishi nauyi sosai ya zame suka zauna a kasa, ya saka mishi pillow hankalin shi a tashe ya fita daga dakin da gudu. Yana kwalawa driver kira. Yau kwanan shi ɗaya a St Nicholas hospital. Yana kwance a kan gadon marasa lafiya, yana bacci Sa'ad na kan kujera yana browsing a wayar shi yana duba side effects ɗin wani magani da aka bawa Fahad, maganin ya saka shi ya zama very weak, yayi wa likitan complain yace babu komai ana so kwakwalwar shi ta samu hutu ne shi yasa yake yawan bacci dole zai ji rashin karfin jiki. Yana zaune su Daddy suka Shigo tare da Mami Hidaya ta riƙo basket ɗin Abinci, suna shigowa Sa'ad ya ɗaga call ɗin daya shigo wayar shi yana directing dakin da su ke, ba a dauki time ba aka yi knocking "yes." Sa'ad ya amsa, Aysha ce ta shigo, Sa'ad ya bata waje yana mata sannu da zuwa sai sunkuyar da kai take yi da wasu yamma ta a bayanta da gani kannenta ne don suna kama. Suka gaida su Mami, sun kawo maltina da ruwa da fruits da yawa. Mami ta gane ta, ta ce "matso ki gan shi bacci yake yi." kunya ta rufe ta, ta kasa ƙarasawa inda yake, ta durƙusa har ƙasa ta gaishe da su Mami da Daddy Hidaya kuma ta gaishe ta ta amsa da murmushi a fuskarta, Sa'ad yace "antinmu sannu da zuwa." Tayi murmushi ta sunkuyar da kai ƙasa, "ku zo ku zauna mana." Mami ta ba wa ƙannen ta waje. "surukar ka ce fah." Mami ta faɗa tana kallon Daddy, abinka da ɗan boko, Daddy yace "daughter zo nan ki zauna." ya nuna mata kusa da shi, "saboda jikin shi ne ma da tuni yan uwa na sun je gidan naku." Aysha sai ta zama speechless maganar tana mata yawo arai amma ranta kamar takarda, rashin sakewarta ya saka Daddy fita daga ɗakin, ana haka Fahad ya farka da Aysha suka fara haɗa ido, ko daga kallon da yayi mata tasan she is not welcome kamar mai koyon tafiya ta matsa kusa da gadon tace "sannu." sai ya juyar da kai ɗaya gefen, Mami da kunya ta kama ta, tace "haka yake yi kwana biyun nan ba ya son magana." "Allah ya bashi lafiya." Aysha ta faɗa, suka miƙe zasu tafi Mami tace "har zaku tafi, ki gaishe da maman ku mungode, Hidaya raka su mota." Mami ta faɗa, suka fita Sa'ad ya rufa musu baya. ****** Baba ke yiwa Daddy bayanin yadda suka shirya tafiyar "tunda waliyin matar Fahad a Kano yake ni da Yaya Sulaiman sai mu je, ya zo nan sai mu je a yanke magana kawai, zamu tafi da dukiyar aure sai a tsayar da lokaci, sannan zamu roƙi alfarmar kar a tsawaita mu na so mu haɗa dama yar mu lokaci ɗaya, na Sa'ad kuma likita da Yaya Abubakar ( Baban ABU) sai suje tunda waliyin nata yana Abuja." Daddy ya jinjina kai "Magaji sarkin hidima ga shi har ka tsara komai, Allah dai yasa albarka yasa zamu gani, shi wancan ya gama ciwon shi ban kula shi ba wai zai je documentation, na dai ce kar ya wuce sati biyu, dan ƙarshen March offer ta shi ke reading kafin nan komai an kammala sai su wuce da matar shi." Baba yace "ina ganin jibi 1st Jan sai muje wajen magabatan na su duka bari na kira su ma duk da na riga nayi musu bayani." da haka su ka yi sallama. Uncle Ismah ka siyo mana knockout ɗin? ke me yasa ki ke haka ne? "au sai ta rufe baki." Tana dariya. "me rawar kai da me karambani me ake faɗa ne an haɗa kai." Umma ta faɗa tana kallon yadda suka haɗe kai suna ƙusƙus, "kai Siyama gaskiya kin sa mana ido." Umaimah ta faɗa tana tura baki, "Au haka kika ce shikenan na cire idon." "gara dai haka Siyama." Baba Rabi ta shigo ta fara jera coolers a Dinning, "wanne delicious aka hada mana." Umaima ta tambaye ta, "meye delitiyous? Baba Rabi ta tambaya, Umaimah ta yi dariya "wanne abun daɗi kika dafa mana to?" "Ayyo toh kinsan ban iya turanci ba Tuwon Alkama ne Hajiya tace a dafa." "tuwo kuma" Umaimah ta maimaita, "haba Siyama dan Allah me na yi miki? wai ba kya gajiya da tuwo ne fisabillahi." Umma tace "eh sai kin yi min wani abu? Ke kika ɗauki tuwo abun banza wasu shi su ke so, yayan Bichi ne yazo suna tare da Baban Khadija anan zai ci abincin dare shi ya ke son tuwon Alkama shi yasa nace ayi." "Dan Allah Baban sama ya zo? Umaimah ta faɗa da murna, "yazo mana ɗazu da yamma sun fita da Baba." Ismael ya faɗa, Umma ta hau Dinning, "mai ci ya ci mara ci ya nemi wani abun babu dole." Wajen karfe 10:30 na dare suka fito kofar gida babu wanda ya sani, Dan Umma tuni ta haye sama, ta daɗe tana jiran dawowar Baba ta ji shiru ta kira shi yace ta kwanta kawai waliyin Aysha tsohon Abokin shi ne tare suka yi Rumfa college, tsohuwar Abota ce Allah ya yi silar haɗuwar su, yace wa Umma sun ci Abinci ma. Amira ce ta duba bata ga Umaimah ba, sai ta ji kara sosai daga waje don Yaya Ibrahim ya tafi Abuja, sai ya Aliyu kawai gidan sai yayi shiru, ta buɗe window tana kallo fireworks ne yake tartsatsi a sararin samaniya celebration na New year ake yi ita ta manta ma ga mutane da yawa a waje anata kallo, da gudu ta fito ita ma ta haɗu da Umaimah da Ismael sun shige cikin mutane, opposite Las Vegas ana ta kwabo da mota, Umaimah ta rinƙa buga knock out. Dan Nagari kuma countdown ake yi na wakokin da suka yi fice a shekarar, wajen ya cakuɗe da mutane, Amira ta matso kusa da Umaimah "nima bani knock out ɗin." Ismael ya ce mata "shiga gida ki taho min da ruwa." ta juya ta koma gida, ba a daɗe ba sai ga motocin yan sanda sun shigo layin suna kamen masu buga knock out, ashe an sanar ayi celebration amma banda buga knock out, Umaimah bata fasa ba taci gaba da bugawa, ta dage ta buga knock out ta buɗe murya tana happy newyear, wani ɗan sanda ya damke ta ya saka a mota Isma'il ya bi ta yana kira aka haɗa da shi, Amira ta taho da gudu da ruwa a hannu sai ganinsu tayi a bayan motar yan sanda ana danna mutane harda Almajirai yan kallo duk an tattare su. Amira ta tafi da gudu tana bin motar tuni har sun yi nisa har ta sare ta tsaya, ana ta tattare mutane da kyar ta shiga gida fuskar ta sai yaji ta ke yi ashe teargas aka buga ana kora mutane da shi, tana haki ta hau sama da gudu ɗakin umma ta shiga ta fara kokarin tashin ta. 💫 UMAYMAH 💫 ✍️A&A PEN Follow our Whatsapp group via this link https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3 https://wa.me/+2348039352724 VOLUME ONE EPISODE 5️⃣5️⃣ Umma firgigit ta tashi, "kai wlh Amira kin ba ni tsoro na ɗauka ma Umaimah. ce hankali tashe Amira ta faɗawa Umma an kama su Umaimah, da sauri ta sauko daga gado "ban gane ba." Umma sai tafi Amira rikicewa, "me ya faru? "celebration ɗin New year muka fita." Umma tace "maza kira Babangida ya bi su, bari na kira Babanku." Umma ta kalli agogo 11:30 lalle hira ta yi daɗi, tana dialing Baba ya ɗauka yace "gamu a hanya mun kusa..... Umma ta katse sa ta faɗa mishi abunda ya faru. innalillahi kawai yake maimaita wa "ina Babangida? ya tambaya, "yanzu na aika Amira ta kira shi. "Okay gani nan. ya katse wayar. Amira sai buga ƙofa ta ke yi ba a buɗe ba ta ƙara daga hannu zata buga ya bude a fusace "ke lafiya?" Ummm..... Umma tace na faɗa maka an kama su Hakimi." "what?" ya faɗa, sai kuma ya koma ɗaki ya saka jallabiya ya ɗau wayarshi da key ɗin mota a hannun shi ya fito, wayar shi tayi ringing Baba ne, yace mishi wanne Station za shi yace Badawa division tunda babu nisa kila can aka kai su. "hakan yayi bari mu tafi bomfai." ya fito ya shiga mota Malam Idi ya buɗe gate ya fita kamar zai tashi sama, "waɗannan yaran basa jin magana." Ya faɗa a ranshi, yaje Badawa division be same suba. "Mun shiga uku Uncle Isma kamar wasu ɓarayi, wlh Uncle Aliyu na ke jin tsoro sai ya zane ni, me muka yi zasu kama mu a ƙofar gida mu ke fah." "ku sauko." Muryar ɗan sanda ta katse su, kafarta ta sage wani daga ganin shi Almajiri ne ya kasa saukowa, Ɗan sandan yace "ba zaka sauko ba." da Ƙyar ya miƙe ɗan sandan ya ɗauka iskanci ne ya kifa mishi mari, "haba mallam ba ka kalli ƙafar shi ciwo ta ke yi ba?' Umaimah ta faɗa ranta a ɓace, "au rashin kunya zaki yi min kenan?" Ɗan sandan ya faɗa, "ga ɓarayi, ga armrobbers suna yawo a gari kun gagara kama su sai mu masu celebrating Newyear." "zaki gane baki da wayo.' ya jijjiga kai, Islam yace "pls ki yi shiru kar ki jawo mana wata matsalar kuma." Umaimah ita akwai ta da tausayi, ta kalli Almajirin ba yaro ba ne amma a gajiye yake, gashi bashi da Zafin kai. "Baba naje Badawa basa nan. Aliyu ya faɗa, Baba yace "je ka gida kar ka damu yanzu zamu shiga bomfai." Ran Baban sama ya baci, wannan an yi abusing profession ɗin shi, yasan dai commisioner ya tsawatar akan buga knock out amma ba ace ayi kame ba dole a ladabtar da wanda yake da hannu a kamen na, ya kira commisioner, Baban sama Dcp ne daga commisioner sai shi a rank "yes

Chapter 27 of 29