"wai ku ba kwa rabo da faɗa ne? Sai kace Kaji. Amira cika ta" wadda aka kira da Amira ta cukwukuye hijab ɗin dayar ta cika baki da iska tace
"wallahi Umma haka kawai ta din ga dariya tana min gwalo wai dan mallam ya zo karɓar hadda ban iya ba yayi min bulala" ta faɗa murya a karye.
Wacce aka riƙe wa hijabin ta harare ta da lulu eyes ɗin ta kamar zasu faɗo ƙasa, tace
"Ƙarya ta ke yi ta dai fadi gaskiyar abinda ya faru, kuma Allah in baki sakar min hijabi naba bazan koya miki assignment ɗin ba ai gobe Monday"
Umma ta dafe kanta tace "Naji yanzu dai ke Umaimah faɗa min ya aka yi" Umma ta tambaya cikin san kashe rigimar tasu.
Saida Umaimah ta cuna baki gaba kamar na tsusa sannan tace
"kawai an fita Sallah na cire hijabi na ina shan iska ta jaa min ɗankwali su Sumayya na ta min dariya wai kitso na ya tsufa"
Umma ta girgiza kai tace "hmmm Allah ya sauwaƙe mu ku, kema maganin ki kenan, ace Umaimah kullum sai na sha fama da ke akan kitso ga ki da son jagwalgwala na mutum, amma ke sai dai ki nade kai kamar kullin magani kice baza a taɓa ba, banda Allah ya yiki da gashin ma ai da zuwa yanzu an sara na
kitsawar da kika tsana."
Umma na rufe bakinta Umaimah ta fara bubbuga ƙafa a ƙasa tana cewa
"kai Siyama kai Siyama me kike so ki ce, ƙazama ce ni?"
"Eh shi ne abunda na ke son faɗa" cewar Umma
"wlh ni ba ƙazama ba ce.
"Dan Allah tafi can, haka kika iya, Allah kika kaini bango kawai aski zan miki kowa ma ya huta"
Umaimah najin haka ta rike hannun Umma cike da gaɓun ta tace "dan Allah Siyama da gaske? wallahi a aske shi ni dama na gaji da shi ya ishe ni"
Takaicin maganar ta ya ƙara kama Umma, dama in dai Umaima ce bata san barazana da gatse ba, Umma cikin raba kanta da wahalar Umaimah tace
"Naji maza ku je ku cire uniform" Amira ta yi gaba abinta tabar Umaimah anan.
Umaimah mai makon ta tafi sai ta zagayo ta bayan Umma ta ɗane bayan ta tace
"Siyamata yau me kika dafa ne, naji gidan kamshi yake"
Umma tace
"oho miki idon matambayi"
"kai Siyama dan ma na tambaye ki, Allah dai ya dawo da Baba lafiya, ya baki amana ta, yace ayi min komai nace inaso kar a bata min rai, har wanka yace ki ringa yi Min, ya baki kudin ice cream ɗina a rinƙa siya min, amma sau ɗaya kawai kika siya min tinda ya tafi, ina lissafi fah Siyama, Allah ki lallaɓa ni idan ba haka ba in Baba ya dawo sai an bani hakkina."
Umma ta ture ta daga bayanta tace "Dalla tafi can ci dai, baki da aiki sai ci kamar gara, ni mamaki ma nake da kike gane karatu, har mazan gidan nan kin fi su ci."
sallamar Dodanta ne ya sa ta saki wuyan Umma ta taka da gudu tayi sama, ta dai ce mishi sannu da zuwa Uncle Aliyu, be ko nuna ya ji ta ba, ya bi ta da harara ya samu waje ya zauna yana yi wa Umma sannu da gida.
Umma tace "har ka dawo daga Bichin Babangida? Yana sauke numfashi yace
"Na dawo Umma, Dada tana gaishe ki. Umma tace
"Allah sarki uwata ya jikin nata?
"bata da lafiya ne? Aliyu ya tambaya. Umma tace "A'a jikin girma, ai baka raba su da ciwo" ya taɓe baki yace
"ni ƙalau na gan ta, wannan tsohuwar mai rigima tun da naje mita take yi har na taho, wai Baban Lagos ya ɗaurewa Yaya Khadija gindi taƙi aure, shekera nawa da fitowar ta wai an zura mata ido, kai wannnan mata da mita ta ke.
ungo nan" Umma ta jefe shi da throw pillow "uwar tawa Babangida"
ya cafe pillow yana murmushi Aliyu ke nan,
Idan kana son ganin murmushi Uncle Aliyu to da Umman ne kawai. Shi kuma haka yake duk ciki yaranta yafi kowa shaƙuwa da sakewa da ita.
In ka cire Umma ko Baba Aliyu bai fiya yi masa dariya ba, bare kuma sauran ƙannen sa, Boss ne na gaske, dan haka suke tsoransa gwanda ma Ibrahim sometimes yakan ɗan mayar masa, da yake shike binsa dole akwai ɗan rainin nan na mabiyi da mabiyi tsakanin su, sai dai shiɗin ma ba wani mai yawa bane wasan, saboda Uncle Aliyu Alin ne da gaske bashi da daɗi.
Umma na shigowa ɗakinta da uniform ɗin Umaimah ta fara karo "Allah ya shiryaki Umaima yanzu uniform ɗin da kika cire anan zaki watsar min. wai me yake damun kine, wannan yarinya an yi ballagaza" Umma faɗa tana tattara uniform ɗin.
Sallar magrib ta shigo zatayi taci karo da uniform ɗin Umaima yashe a ƙasan ɗakin ta. dama haka take yi, ɗakin su daya da Amira, rabin kayanta yana ɗakin su rabi a ɗakin Umma, duk inda ta ga dama ta shiga tayi uzurin ta, duk abinda ta ɗauka ya gama mata amfani bata san ta mayar da shi muhallin shi ba, a'a anan zata jefar dashi tayi gaba. Kullum faɗan su da Amira kenan, har Umma ta kabbara sallah ta sallame ta kalli Umaima data shigo ɗakin hannunta riƙe da plate ta shaƙo sa da abinci, ga nama zuƙu zuƙu akai. Tace
"yanzu Umaima ba wanda ya ci abincin nan kika ciko paranti haka? daɗi na da ke rashin saiti"
Umaimah ta zumɓura baki gaba tace
"ni gaskiya Siyama kin saka min ido, Allah ya dawo da Baba lafiya na huta" ta sami waje a kasan carpet ta zauna, ta dau remote zata kunna TV Umma tace
"kar ki kunna min tv sallah zan yi.
Umaima ta ɓata fuska tace
"Wannan mata da iko kike, dan ma kin samu na zo ɗakin ki. Umma da sauri tace
"Dan Allah je ki ban gayyato ki ba ta kabbara sallarta.
Umma na idar da Sallah ta kalli Umaima da ta gama cin abincin ta ta miƙe a tsakar ɗakin, tace
"Tashi wallahi baki isa ba, tashi ki kiyi sallah ko ran ki yanzu ya ɓaci"
Umaimah ta ringa birgima daga edge din gado zuwa two sitter
"wallahi Siyama kina da damuwa, wai nace ba zan yi ba ne? Umma ta haɗe rai tace "Allah dai ya kawo miki hankali, bari na kira Babangida" ba shiri Umaimah ta afka toilet tana cewa
"rabani da wannan Azzalumin" ta faɗa ciki ciki.
Umma tace "me kika ce? Ah to kinsan halin shi, yanzu nan ya jibgi mutum" Umma ta faɗa tana naɗe sallaya.
****
Khadijah ta shigo gidan cikin nutsuwa sallama ɗauke a bakinta ta shiga falon, Amira ce kaɗai a kasa tana canja channel ta amsa, da sauri ta rungume ta, tace
"oyoyo Yaya Khadija"
Khadijah tace "Autar Umma ke kaɗai ce a ƙasa?" ta nemi kujera ta zauna, Amira ta wuce kitchen ta fito da tray ta ɗora ruwa da zobo mai sanyi a tray ta ajiyewa Khadija a gabanta. Khadijah ta kalli trayn tace
"kamar kinsan a gajiya na ke autar Umma" ta ɓalle murfin ruwan ta kafa baki tasha, kaɗan ta rage ta jingina da jikin kujerar ta lumshe ido.
Amira tace "Yaya ko na zubo miki abinci? daga kishin giɗen da take ta kalli Amira tayi mata murmushi ta ce
"A'a gajiya ce kawai na debo"
Da tausaya wa Amira tace "sannu Yaya Khadija"
Khadija ta riƙo hannun Amira ta rungume ta ajikinta, tana son Autar Umma dan tana da yawan damuwa da ita, ita kan ta Amiran kafin ta nufi kowa da matsalar ta tazo wajen Yaya Khadija, ko da Umaima su ka yi faɗa wajen Khadija ta ke zuwa, shaƙuwar su kamar ta ƴa da uwa ce ba Yaya da ƙanwa ba.
Tazarar dake tsakanin Khadijah da Amira mai yawa ce dan ɗiyar farko ce da ɗiyar ƙarshe.
"Allah ya yi miki Albarka Amirori" Khadija ta faɗa, Amira ta sake lafewa a jikinta tana dariya.
Khadijah tace "ina ƴar uwar taki? Khadija ta tambaya. Amira tace
"mhmm chewgum ɗin Umma suna tare da ita a sama" Khadijah ta yi murmushi tace
"ke da Umaimah sai Allah, Amira ki cigaba da hakuri da halin ƴar uwar ki, ke ƙaramar uwa ce, duk da dai tsararki ce (mate), amma kin fita Hankali, kin ji yarinyar kirki."
tana magana tana shafa bayan ta, Amira bacci kike"
Amira ta girgiza kai. tace "toh ɗaga ni na kwaso gajiya bari na watsa ruwa" ta miƙe tayi sama, Amira ta bita da handbag dinta da jilbab ɗinta suka haura saman a tare.
Kamar yadda yake al'adar gidan duk bayan sallar isha'i jama'ar gidan sukan hallara a main palour gidan a Dinning area danyin dinner, wannan wata al'ada ce da Baba ya assasa ta ko yana gari ko baya nan tilas dinner a ci tare, safe da rana kuma kowa da uzuririkan shi mabanbanta. Da ranan ma kusan Baba Rabi ce kaɗai a gidan sai sauran ma'aikata.
Yau da Baba ba ya nan Umma ce a zaune gefen ta Khadija, Aliyu, Ibrahim da Ismael, Amira tana daga hannun daman Khadija, kowa yayi shiru ana cin abinci. Dukkanin su ƙanne ne ga khadija.
Umaimah ce ta taho da sauri tana cewa "kar dai ayi min ƙwaitama, dan ban ƙoshi ba"
shiru wajen amma daga zuwan ta ta fara karaɗi, Umma ta riƙe baki tace
"Umaimah duk abincin da kika ci ɗazu, ina kike zubawa ne?" Umaimah tace
"Allah ban kai geji ba, bana yi sallah ba, da kayi sujjada kuma duk abincin da kaci jirkicewa ya ke yi" Umma ta buɗe baki
"oh! Ni Maryama ya jirkece ya tafi ina?"
Khadija ta ƙware da abinci jin shirmen Umaimah, da sauri Umaimah ta nufe ta da ruwa tace
"sannu Ammi ta" ta miƙa mata ruwan, Khadija ta karɓa idonta har ya kaɗa, duk aka hau yi mata sannu, Ibrahim yace
"a wacce ruwayar aka faɗa miki haka Umaimah? yana dariya yace "ban taɓa ji ba."
Aliyu fuskar nan a murtuke yace "zaki nutsu ko sai an nitsar dake? Khadija ta girgiza Kai kawai tana fatan Allah ya sa wautar nan ta Umaimah ta tsaya a iya yarinta, don su Umma da Baba ke biyewa shirmanta shiyasa ta ke jin daɗin yinsa san ranta.
Aliyu ne kawai bayayi mata da wasa, idan ba dan shi ɗin ba da an samu matsala.
"Zo mu ci nawa" inji Isma'il na hannun daman ta ne, ƙaramin uba, marufin asirinta in ta yi tabargazar ta tare suke kashe wa su binne ba me ji, mafi yawancin lokuta ma Aliyu tare yake musu hukuncin da Ismael, ya kan ce bakin su ɗaya, tunda shi babban banza ne, wani lokacin ma horon na shi ya fi tsanani akan na Umaimah, wahala sosai Aliyu ya ke ba shi, amma duka ya shanye a kan Umaimah.
Tana murmushin jin daɗi tace "toh Uncle Isma, oh na manta Uncle Ismael" ta yi sauri ta gyara sunan, saboda mugun kallon da Aliyu yayi mata, saboda ya hanata cewa Uncle Ismael Isma wai kamar sunan mata.
Ta kalli plate ɗin Uncle Ismael tace
"wanna yayi mana kaɗan" sai ta hau bubbuɗa coolers, abincin ta ƙara musu har ta zauna kusa da shi tayi mishi raɗa a kunne suka tashi a tare suka bar dining ɗin.
"Rakumi da Akala, Abokan gulma" Amira ta faɗa
Umma tace "wallahi ki kiyaye shi kinsan dai ba kwa kwashe wa lafiya"
Amira da Ismael basa shiri faɗa baya yi musu wahala, ko dan saƙo da saƙuwa ne, kullum a faɗa su ke, Ismael ya kan ce ta cika munafurci idan zata yi gulma bakin ta har karkarwa ya ke.
Umma ta kalli Khadijah tace "Yayar su yau kin daɗe?
"wallahi Umma mun tara ayyuka ne, december ta matso akwai bukukuwa sosai, shi yasa yanzu ba a rufe shagon da wuri mun karɓi ayyukan mutane da yawa, ga order na turarukan wuta na karɓa"
Umma tace "Allah ya taimaka" Khadijah ta amsa da Amin, cikin sanyinta na halitta ta miƙe tace "bari na shiga daga ciki, sai da safen ku"
"toh sai da safe."
Umma ta kalli Amira data miƙe ita ma, tace "dawo ki tattara wajen nan"
Ibrahim ya ce "yayarmu zan shigo mu sa labule ina zuwa kafin ki kwanta"
Khadijah ta ce "ay har ka shigoma ban kwanta ba"
"mu kwana lafiya." Ta wuce sama.
Umma ta bi ta da kallo a ranta tace Allah mungode maka da yarinyar nan ta dawo dai dai, Allah ka share mata hawaye, Umma ta tuno da wani shudaden alamari mara daɗi da suka riska a wasu shekaru, a baya sun sha wahala sun jigata kafin komai ya wuce gashi yanzu sai labari.
"lafiya Umma" Aliyu ya taɓa ta, ta yi nisa a tunani, maganar Aliyu ce ta dawo da Umma daga tunanin da take, ta kalli Aliyu ta ce
"ina tausayin Khadija ne tayi aure a ƙananan shekaru ba riba sai wahala, koda yake ba zan ce ba riba ba tunda gaa Umaima nan.
"Ƴar fadarki ba" Ibrahim ya faɗa. Umma tace
"fadar Baban ku dai, raba ni da Umaima gaa Auta ta nan ina ruwa na da ƴar karo.
"ah ah dai Umma Umaiman da idan bata da lafiya kece me rama" sai kayi kuma Umma ta ce da Ibrahim tana maida hankalinta kan Aliyu tace
"Babangida taɓo min baban ku ko lafiya yau tun safe ban same shi ba, ya kira ni ɗazu ba na jinsa ko matsalar network ne.
"Umma wajen da yake ne babu service, amma dazu mun yi waya da mallam Musa shi ma da ƙyar na same shi, ya haɗa ni da Baban yace sun shiga meeting.
"toh Alhamdulillah tunda lafiya.
"Umma dai missing Baba take, zan faɗa mishi uwargidan shi tana missing ɗin shi.
Umman tace "ka kiyaye ni, nifa ba kakar ka ba ce ban san Shaƙiyanci Ibrahim" Umma ta miƙe ta cewa Amira
"kedai Allah ya sauwaƙe miki laƙai laƙaitu, tattare plates ɗin ne ya zama aiki a wajen ki"
kafin Umma ta rufe baki Baba Rabi tayi sallama suka amsa tace
“leƙowa nayi naga ko an gama na kwashe kwanukan"
Aliyu yace "yi tafiyar ki Baba Rabi waɗannan yaran aikin me suke, ke dalla haɗa su ki kai kitchen" ya ce da Amira.
Umma tace
"sannu da ƙoƙari Rabi, bari na hau sama mu kwana lafiya"
Cikin girmamawa Baba Rabi tace "toh Hajiya sai da safe"
Umma tazo wucewa ta Umaimah da Ismael a zaune sun haɗa kai a falo suna kus kus, ko me su ke kullawa?
Mai rawar kai da me karambani in ji Umma
"me ake tattaunawa ne"
"Alkhari" Umaimah ta faɗa. Umma tace
"toh Allah yasa mu ji alkhairi"
Umma tace wa Ismael "uba na idan su Babangida sun fita ka rufe ko ina"
da yake shi ɗakin shi a ƙasa ya ke, su kuma a waje chalet ɗin su yake, can ƙarshe wajen masu aiki. ya ce
"toh Umma"
Umaimah tace "Siyama kar ki saka mukulli a wajen ki zan kwana"
Umma tace "kice yau akwai danbe kenan?
Ismael ya yi dariya yace "rabu da Umma wasa take miki.
"wanne wasa, a lafta min ƙafa a jiki haka zan tashi jiki yana min tsami, ta baro ɗakin su, taa baro na uwarta ta zo ta uzzira min"
Umaimah ta zumɓuro baki gaba tace "toh ba Baba yace idan baya nan na rin gaa kwana da ke ba"
"Ni kin gaa tafiya ta sai kin shigo, ki dai saka dogon wando bana son tashi ina ta gyara miki kwanciya, ta haye sama.
💫 UMAYMAH 💫
✍️A&A PEN
Follow our Whatsapp group via this link
https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3
https://wa.me/+2348039352724
VOLUME ONE
EPISODE 0️⃣5️⃣
Umaimah! Umaimah!! Umaimah!!! Umma ta gaji da jijjigata, amma Umaimah ko musti batayi ba saima sake gyara kwanciyar ta da tayi ta sake jan bargo, Umma cikin takaicin ta tace
"wlh dadi na da ke kenan wannnan nauyin baccin naki"
Umma ta dage ta ɗaka mata dundu da sauri ta bude ido tana kallon Umma, tace
"menene?"
Umma ta harare ta tace
"Idan ba haka na yi miki ba, ba tashi za ki yi ba, ke kullum sai an yi ta fama dake akan tashi daga barci, kamar wani daren za a sake miki"
Yadda kasan Umma bada ita take magana ba, ana ƙwalla kiran sallah za a shiga masallaci Umaimah ta ƙara juyawa zata koma barcinta.
Umma tayi ƙwafa tace "kinsan dai ba mallam Musa ba ne zai kai ku makaranta ba, balle ya jira ki, Babangida ne, tinda bazaki tashi ba babu ruwa na duk abinda za ki yi kiyi kina sani."
Umaimah najin haka babu shiri ta diro daga gadon ta shiga Toilet, ko data shiga Toilet ɗin sit ta samu tayi zaman ta, taci gaba da gyangyaɗinta daga zaune, har Umma ta iddar da salllah ta fara Azkar bata fito ba.
Umma ta ji shirun yayi yawa ta leƙa toilet ɗin ta gaa abinda ta ke yi.
"zan kira Babangida fa"
Umma ta faɗa tana rike da handle din kofa.
Haka ake fama da Umaimah kullum da safe, tana da nauyin bacci ita sabgar ta ta dare ce sai kowa ya kwanta ta ke harkokin ta yadda kasan aljana, tin Umma na faɗa harta gaji tasa mata ido.
Umaimah ta ƙi kula Umma ta hau cire kayan baccin ta a gaban Umma.
"ke me yasa ba kya kunyar yin tsirara ne a gaban mutum?" Umma ta faɗa tana hararar ta.
Ai kuwa ta zumɓura baki gaba tace "ba shi kika tsaya kallo ba, inba haka ba a ina ake bude mutum a banɗaki?"
Umma ta girgiza Kai ta ja mata kofar ta sauka ƙasa.
*****
VICTORIA ISLAND, LAGOS Nigeria.
Mace ce fara doguwa take saukowa daga stairs din bene, murmushi dauke a fuskarta har ta ƙaraso Dinning inda maigidan nata ya ke breakfast tana zama kusa da shi tace
"yau ka ri ga ni saukowa Daddy" ya yi murmushi ya ce da ita
"ai naga kin gaji da yawa ne shi yasa na barki ki huta, ya ya su Dattijo kwana biyu ba na samun su a waya fa har gara shekaran jiya mun gaisa da Sa'ad, ya ce min yana ta ƙoƙarin samun appointment da wani therapist Dr da zai ƙara examining result ɗin Dattijon, kinsan shi ya ƙi bashi haɗin kai, sai faman binsa yake yana zillewa.
Mamie ta nisa tace "hmmm lamarin Fahad sai Allah, Allah ya yaye mishi wannnan matsalar astahfirullah kullum abu babu sauƙi, ya nutsu yaga Dr kuma yaƙi mutum sai baƙin taurin kai, kanayi masa magana kuma zai hau faɗa maka he's okay, he don't have any problems, ho ya Rabb" Mamie tayi maganar tana dafe kanta.
Daddy yayi murmushi irin na jaruman maza sannan yace "Amin ya Allah Habibty, karki saka abun
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 3 Chapter of 29