a ranki zanyi masa magana akan ganin Dr, I'm sure bazai yi denying ba ok. Kinga ina ta kiran Muhammadu ma ba na samun shi, Please kira min Maryama na ji ko lafiya?"
*****
Amira ta shigo kitchen Umma na tsaye tana duba abinda akayi na karyawa ta durƙusa tace
"barka da safiya Umma" Umma tace
"ah ah Autar Umma an tashi lafiya?
"lafiya ƙalau Umma"
Umma tace
"ke har kin shirya ita waccar galmasurar sai yanzu ta ke wanka."
Amira ta zauna ta fara breakfast ɗin ta tace "Umma dama kun saba ai kullum"
Ba dadewa Aliyu ya shigo cikin falon Amira ta gaishe shi ya amsa fuskar nan tasa a haɗe. Umma ta fito daga kitchen suna gaisawa da Aliyu Khadija ta sauko ta yi joining din shi ya gaisheta sannan suka gaisa da Umma.
Umma ta ce "Khadija har kunun gyaɗa kika dama sannu da aiki. Khadijah tayi murmushi tace
"Umma na san kina so shi yasa nayi sa, tunda na tashi da Asuba ban koma ba saidai na gama na bar Baba Rabi ta soya doya"
"sannu da ƙoƙari Khadijah Allah yayi miki albarka"
Aliyu ya mike ya kalli Amira yace "na ba ku 10mins ku same ni a mota"
"toh yaya" Amira ta amsa, a ƙofar fita suka yi clashing da Ibrahim zai shigo cikin falon Ibrahim yace
"ah bro har zaka fita yau da wuri haka, ya kalli agogo hannun shi quater to 7."
Aliyu ya ce "yeah, yau akwai baƙi daga regional office sun bukaci za a yi meeting by 7:30, I have to be there on time"
Ibrahim yace
"eh gaskia ne, goodluck then,"
"thank you" Aliyu ya faɗa yayi waje.
Ibrahim yana shigowa Amira ta miƙe fuskarta fal fara'a tace "ina kwana Yaya"
Ibrahim mai sauƙin hali ne ba kamar Aliyu ba, mutanen ta ne shi da Khadija.
ya amsa gaisuwar ta yana gaishe da Umma da Khadija, Umma ta ce
"an fito" ya amsa da "eh" yana zama kusa da Khadija, yace
"jiya ban shigo ba Yaya Khadija wani aiki ne ya rike ni" ta yi murmushi ta ce "yau ma yi maganar"
Kana ganin yadda suke maganar kasan akwai shaƙuwa kwarai da gaske a tsakanin su.
Aliyu shi ke bi ma khadija banker ne mai riƙe da muƙamin Manager a GT Bank anan branch ɗin su na Murtala Muhammad way duk da ƙananun shekarun sa, akace wai in ilimi ya haɗu da gata yara ne manya.
Shekara ɗaya ne tsakanin su da Ibrahim, haka shekera ɗaya ne tsakanin Aliyu da Khadija kusan Umma dab da dab ta yi haihuwar nan uku.
Khadijah yanzu tana at her 30s, Aliyu shekera shi 29, Ibrahim ya na da 28, Ibrahim yana karatun likita BUK, ya fito housemanship (sanin makamar aikin likita) a asibitin Malam Aminu Kano.
Daga kan Ibrahim kuma sai haihuwar ta tsayawa Umma sai bayan 11years ta haifi Ismael, Ismael yana shekara ta karshe a Sec school bana zai rubuta waec da neco, yana karatu a makarantar maza ta St Thomas Sec sch. sai Amira da take da shekara 13, shekara huɗu ne a tsakanin su da Ismael ita da Umaimah sa'an nine wata uku Amira ta bawa Umaimah.
Su Amira suna js 3 a bright future Academy dake UDB Road.
Ibrahim yace "kin tashi lafiya Amirori ina daughter?" tana saƙala jakar ta ta goyo tace "tana sama"
"hau maza ki kira ta Aliyu sauri yake"
Umma ta ce "tana can tana shiririta"
Amira ta shiga ɗakin Umma ba kowa, ta dawo na su anan ta tarar da Umaima tana hargitso kaya a wardrobe Amira tace
"wlh kiyi sauri yaya zai tafi ya barki"
Umaimah tace "yafi ruwa gudu, shi ay kullum a sauri ya ke kamar shi ne bankin gaba ɗaya."
kafin ta rufe baki suka ji horn din motar sa, da sauri Amira ta sauko da gudu, Umma tace "ina Umaiman?"
Amira tace "wlh tana ta burkita kaya" ta fita da sauri.
Khadija ta girgiza Kai a ranta tana mamakin hali irin na Umaima, Umma ta miƙe tace "bari na hau ko ta sauko"
Khadijah tace "idan na ƙarasa zan wuce shago"
"ah tsaya kar ki tafi nasan Babangida ba jiranta zai yi ba sai ki sauke ta. Umma ta faɗa tana haura sama.
Amira ta bude bayan motar zata shiga, Ismael yana gaba. Aliyu
yace
"ina Umaiman" Aliyu ya tambaya "gata nan zuwa.
"bari na je na kira ta" ismael ya faɗa.
"rufe min ƙofa" Aliyu ya faɗa a zafafe.
Baba Idi ya buɗe masa gate ya cilla motar waje kamar za su tashi sama. Ismael ya saci kallon sa ta gefan Ido a ransa yace "almasifatu."
💫 UMAYMAH 💫
✍️A&A PEN
Follow our Whatsapp group via this link https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3
https://wa.me/+2348039352724
VOLUME ONE
EPISODE 0️⃣6️⃣
Umma ta tarar da Umaimah tana ƙarasa shiryawa, takaici ya kama ta, tace
"yanzu tun ɗazu kina abu ɗaya, har suka tafi suka barcki"
Umaimah baki a tunzure tace "to ni wai ya zan yi ne, tie ɗina ne ban gani ba sai na Amira na ara."
Umma kawai ta bita da kallon takaici, to tama rasa me zata ce mata. Umaima ballagaza ce ba adani kullum cikin faɗan kaya suke da Amira, tinda komai iri ɗaya ake yi musu.
Hatta haɗa kayan wanki Amira ce ke yi, ita Umaima sai ta gaa bata dana sawa sannan take bada wanki, sai tayi ta saka na Amira ayi ta rigima da ita, don ma ana ɗan ƙarawa Amira inch kadan, Dan tafi Umaimah tsaho kaɗan.
Amira chocolate colour ce, duka yaran Umma kalar su kenan Khadija ce kawai ta ɗako farin fatar Baba dan shi jajir ya ke.
Umaimah fara ce tas farin ma ba irin na Hausa fulani ba, kana ganin ta kaga half cast, tana da tsayi da idanuwa farare tas masu ɗaukar hankali (sexy eyes) tana da baby round face wacce kana ganin ta kasan yarinya ce, yanayin jikinta lukwui lukwai irin na yaran Larabawa, hancinta yana da tsayi dai dai fuskar ta abun shaawa, gashin girarta a cike yake gwanin sha'awa kamar tayi shaping ɗin sa, tana da yawan gashin kai mai tsayi sosai da sulɓi daya sirka da brown ba baƙi ba ne wuluk, lips ɗin ta pink masu kyau da tawadar Allah a haɓarta baƙaƙirin kamar ta tisata da kwalli wanda ta ƙarawa cikakkiyar fuskarta kyau, ko a yanzu da maƙerin budurci bai gama ƙera Umaimah ba kana ganin ta kasan za a yi mace.
Umma ce ta kawo karshen rigimar kayan su take musu sheda da bakin zare Amira a saka A, Umaima a saka U, dan ko ance za a raba musu kala basa so, gashi dai kullum cikin rigima suke amma kuma kansu a haɗe yake Aminan juna ne na gaske.
Amira ta ci sunan Dada ne mahaifiyar Umma Fatima, ita ma Umaimah da aka haife ta Baba yasa mata Fatima dama kuma shine ra'ayin Amminta Khadijah.
Fatima Muhammad Bichi da Fatima Tahir Al-arabey.
"kinga maza ƙarasa shirin Ammin ki ta kai ki makarantar na barta tana karyawa a ƙasa" Umma ta fada tana kallon Umaimah da ke saka tie, tana gama ɗaurawa ta ɗakko farin takalmin ta da hijab ta saka.
"dama fah ganin idon Baba ne yasa ya ke ɗauka ta a motar shi, duk gidan nan ya tsane ni" Umaimah tayi maganar tana saƙala jakarta a ciki.
Umaimah ke nan Ita dai komai nata daban dana kowa. Umma tace
"ke dai yi sauri je ki tana jiran ki"
Umma na rufe baki wayar Umma ta hau ringing da sauri Umaima ta ƙarasa ta ɗauka tana cewa "bari mu gani ko Baba ne"
"Yaya Darsha" ta gani sunan ya fito tace
"oh Mamien Lagos ce" da sauri ta daga tace "Mami ina kwana"
"Ah ah kishiya ce ina school din?
Umaimah tace "Uncle Aliyu ne ya tafi ya bar ni.
"Amma Aliyu be kyauta ba" Mami ta faɗa daga ɗaya bangaren, da sauri Umaima tace "Mami ina Daddy ?
Mami na murmushi tace "bari na bashi" yana karɓar wayar yace "Amarsu yau soyayya ta motsa da safen nan, lallai Ango na ke, Umaima tayi daria tace "kai Daddy, Daddy yaushe za ku zo Kano? Ina Hidaya?
Daddy yace "Ahto ni ake san gani ko Hidaya? Umaimah na masa dariya tace
"both of you Daddy"
Daddy yace "idan Amarya ta yi kira dole na amsa kiran, yaushe ake son gani na?
Tana jin muryar Mami a background ɗin tana cewa "yau za a yi min kwacen miji da sanyin safiya"
Daddy yace "Yanzu dai ba wannan ba ma ina school ɗin najiki a gida? Cike da shagwaɓa tace "ba Uncle Aliyu ne ya tafi ya bar ni ba" Daddy yace
"zamu gamu da shi kuwa, ina Azumin?
Umaimah na dariyar sunan tace
"wacce Azumi kuma Daddy? ay na canja mata suna tinda ta ce min dan an haife ta a watan Azumi ne Dada take ce mata Azumi. Shine na canja mata sunan dana zamani Siyama, Siyama zaka ce Daddy"
sosai Daddy yake dariyar maganar Umaimah, kai jama'a wai "Siyama" Daddy ya sake maimaita sunan yana kwasar dariya, yace
"Siyama kamar wata yarinya"
Umaimah tace "eh mana yafi dadi Daddy, Baba ma fa yanzu Siyaman ya ke cewa. Daddy yace
"eh shi Baban zai iya faɗin haka, amma ni dai Azumi zan ce ko na kira ta da sunan ta na yanka Maryama."
Umma da ta gaji ta kwace wayar a hannun Umaimah ta nuna mata kofar fita, Umaimah har ta kai ƙofa zata fita Sai kuma ta waiwayo tayi wa Umma blowing kiss tace "i love you Siyama." ta fita da gudu. Umma ta kara yawar a kunnen ta tana gaishe da Yayan nata.
A compound ta samu Khadijah a tsaye a jikin motar ta Blue blue ƙirar vibe tana riƙe da key ɗin motar, maroon jilbab ne a jikin ta da bakar handbag da bakin takalmi. Shigar tayi mata kyau sosai kuruciyar ta ta sake fitowa, babu yadda za'ayi kace Khadijah ce ta haifi Umaimah in ba sani kayi ba, dan ko cewa akayi ita ce Amminta mutane da yawa basu fiya yarda ba.
Khadijah Motar ta bude ta shiga bakinta dauke da adduar da Annabi ya umarce mu dayi idan zamu hau abin hawa, Umaima na ƙaraso wa ta buɗe gaban motar ta shiga.
Basu jima da fara tafiya ba Umaima ta juyo ta kalli Khadijah dake tuƙi a nitse, tace
"Ammi na"
Khadija ba tare data ɗago ba ta amsa da "Na'am Umaiman Baba ya akayi ne?"
"Dan Allah Ammi ina Daddy na yake yaushe zai dawo? kullum inna tambaye ki sai ki ce ya tafi Ƙasar su zai dawo, yaushe zai dawo to?"
Wani wawan burki Khadijah ta taka a tsakiyar titin, dan ma Allah ya tsare babu mota a bayan ta, hannunta ya fara karkarwa zufa harta jiƙa mata fuska da taimakon Allah ta nemi gefen hanya tayi parking.
Hankalin Umaimah a tashe tace "lafiya Ammi ba ki da lafiya ne?
Umaimah maganar ta kawai ta ke yi amma Khadijah ba gane abinda take cewa take ba.
Idanu wanta da suka kada suka yi jajur ta ɗaga ta dubi Umaimah, Umaimah da tsoro ya nuna a fuskar ta tace
"Ammi me ya faru? baki da lafiya dama?"
Har an fara zuwa wajan ke nan? wannan ita ce ranar da take tsoron zuwan ta. Khadijah ta ayyana haka a ranata.
"Ammi"
Umaimah ta sake kiran sunanta tana taɓa ta.
Khadijah ta ƙakaro murmushin da be kai zuci ba, tace "kaina ne ya ke ciwo" Umaimah na ɓata fuska tace "sannu Ammi, ko mu koma gida tinda ba mu yi nisa ba? Khadijah tace
"Ah ah zan iya kai ki ciwan ba sosai bane"
Wannan hali da Umaimah taga Amminta aciki shi ya mantar da ita zancen Daddyn ta. Bayan ta ɗan samu nutsuwa ta ja motar suka nufi school ɗin, ko da suka je an tsayar da ƴan latti, Umaima ta sauko ta yiwa khadija waving, Khadija tace "Ayi karatu sosai banda tsokana" saida Umaimah ta shige cikin makarantar sannan ta jaa motar ta tafi.
******
Idanuwa Umaimah ta fara rabawa tana kallon yadda ake zane ƴan latti. ta durkusa displine masters Mr Alade yana tabkar late comers, bayan ya dake ka sai ka tsallake wani layin daban wani punishment din za a ba ku after schl hours ko sharar compound, ko wankin toilet, ko watering flowers. Duk rashin jin Umaimah bata shiri da bulala dan kaha tana ganin maths teacher ɗin su ya zo ya daukewa Mr Alade hankali suna magana ta yi amfani da wannan damar ta tsallake daya layin da rarrafe ba wanda ya kula da ita. already an musu bulala ta shige cikin su nan ta haɗu da friends ɗinta Aminanta ƴan ajinsu Aminu Bello (genius) da Sadiq mukhtar (wizard) ita kuma (Smart ) haka yan class din su ke kiran su, saboda ƙoƙarin su, dan tabbas su ukun nan Allah ya yi musu baiwar hazaƙa da ƙoƙari, ga shi ba ji suke ba dan haka kowa ya sansu a cikin makarantar saboda tsabar ɗaukar maganar su, amma sometimes ƙoƙarin su na cetar su, suna samun Afuwa a lokuta da dama.
Aminu yace "yau Smart ta makara"
Umaimah na gyara zaman jakarta, tace "ay kasan ina zuwa da wuri kai kuwa habitual latecomer ne. Wizard (sadiq) bani hanky ɗin ka wajen nan akwai duwatsu" Sadiq ya miƙa mata yana cewa
"Amma ina Fatima Muhammad Bichi? Umaimah tace "Tahowa suka yi suka bar ni nasan tana class yanzu"
*****
Da kyar Khadijah ta ja motar ta tabar wajan, tunani fal zuciyar ta, yau kam bata da wani karsashin aiki kawai sai ta saka signal ta hau kan titin Korau road ta karya kwana ta koma Sultan road. Gara ta koma gida ba zata iya wani abun kirki ba ko ta fita, Umaima ta yi mata famin ciwon da ta ke ɗauke da shi shekara da shekaru a cikin wannan halin ta isa gida.
"Barka da dawowa" tace "yauwa sannu da aiki Baba Idi, ta fito ba kowa a falon shiru sai kai wa da kawo war Baba Rabi da ta jiyo a kitchen. Bata fatan ta haɗu da kowa a cikin wannan halin data shiga, Umma ma yanzu tasan tana makaranta da yake tana zuwa Wamy.
Ta haura sama ta shiga ɗakinta, ta wuce toilet ta daura Alwala ta shinfiɗa sallaya ta tayar da sallar walaha, mafi yawancin lokuta a shago take yi, da yake da office ɗinta a ciki da karamin toilet, bayan ta idaar da Sallah ta na Jaan carbi ta zame ta kwanta akan sallayar, ba bacci ta ke ba, amma idonta a rufe yake. Bata ji haushin Umaimah ba dan hakkinta ne ta san inda mahaifinta yake, tana yawan yi mata wannan tambayar, ta tuna wata rana da Baba yayi mata duka akan tambayar Daddyn ta. Ran Baba a ɓace yake cewa Umaimah "Me kika rasa? Kina da mu kina da uwa, mun ishe ki rayuwa wanne uba kike nema bayan yan uwan mahaifiyar ki, basu ishe ki ba, shin ban isa na zame miki bango ba, kar ki kara yi min zancen wani uba, ranki zai baci"
tun daga ranar Umaima take shayin yiwa Baba tambaya makamanciyar wannan, Allah sarki Baba ba asan zuciyar sa yayi mata wannan dukan ba ɓacin raine kawai, sai da yayi dukan ya dawo yana lallaɓa ta suka shirya.
Amma ita duk lokacin da su ke tare da Umaimah cikin tambayar ta maifinta take, sai dai idan wani abun ya dauke mata hankali, amma sai tayiwa Khadijah tambayar ina Daddyn ta.
Khadijah ta sake rintse idanunta tana tuno wasu kalmomi masu ciwo
"Bana bukatar ki, har yanzu da sauran kuruciyarki, kije ki auri Bahaushe ɗan uwan ki, nima na auri wacce nake so"
ta kara rintse ido, hawaye suka ringa gudu akan fuskarta kamar an kunna famfo, sai taji kamar yanzu yake furta mata kalaman.
"Zaliha"
ta samu kanta da furta sunan, ta buɗe ido kamar an watsa mata barkono, sai taga kamar Zalihan ce a tsaye a baganta tana yi mata murmushin mugunta kamar yarda ta yi mata a wancan lokacin.
Khadijah ta sake juyawa ɗaya ɓarin saboda gizo da Zaliha ta ke yi mata.
Baba abunda yayi ta nuna mata kenan a waccan shekarun amma idon ta ya riga ya rufe da so taƙi fahimtar abinda Baba yake nuna mata.
"Khadijah wannan yaron ba al'adun ku ɗaya ba, yaranmu kowa karatu ya ke yi, ke kin yarda ki yi aure yanzu? a san raina Khadija sai kin yi nisa a jamia kinsan ciwan kanki, kin cika burin ki na zama cikakkiyar lauya sannan zan yi miki Aure. Amma Babanki na Lagos yayi Na'am da shi bani da wani abun cewa yanzu wanda ya wuce Allah yasa alkhairi" Maganganun Baba suka sake dawowa Khadija kamar a lokacin yake faɗa mata su. Ina ma ana dawo da hannun agogo baya, tabbas da zaɓin iyayenta zata bi. Amma kash ba a tara sani da Allah.
Wani mawaƙi yace (can't turn back the hands of time).
Amantu Billah ta furta a hankali (l believe in Allah).
*****
Hellooooooo nace hello! Readers muna son ganin reaction da comment hope kuna enjoying yanzu mun ɗan fara shiga cikin labarin kaɗan.
⚡ UMAYMAH ⚡
✍️A&A PEN
Follow our Whatsapp group via this link https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3
https://wa.me/+2348039352724
VOLUME ONE
EPISODE 0️⃣7️⃣
Khadijah ta juya ɗaya ɓarin hannun ta na dama ya ƙage saboda kwanciyar da tayi a kansa yayi tsami, ta daga ido ta kalli agogo karfe hudu da Rabi, tace
"Subhanallah" ta yi sauri ta miƙe, ashe ba karamin bacci ta yi ba bata sani ba, lokaci har ya jaa haka.
A gurguje ta shiga Toilet ta dauro Alwala, ta fito ta rama Sallar Azahar data kubce mata, sannan tayi La'asar ta dade tana Azkar sannan ta koma Toilet ta yi wanka da ruwan dumi, tana fitowa ta nemi sasauƙar rigar material ta saka, ta ɗauki hula ta saka ta shafa humra da perf mai sanyi, ta buɗe wardrobe ɗin ta inda take ajiyar madarar turare da iccen turaren wuta, ta ɗauka ta fita daga ɗakin.
Ƙasa ta sakko suka gaisa da Umma taci abinci sannan ta wuce bayan gida inda take hada turaren wuta, tana hada turaren wutar Baba Rabi na taya ta da iza wuta, Akwai wani katon fili a wajen kamar kango ansa masa ƙofa, amma a kulle yake, Baba yace zai yi kiwo a ciki Amma saboda sabgogi be yi ba. katon fili ne babu komai a cikin sa sai dai in yayi ciyawa a bude wajen a nome.
Suna cikin aikin suka ji sallamar Munnirah, Khadija ta daga ido ta kalle ta, tayi mata murmushi tace
" My sis yanzu nake maganar ki a raina" Munnirah ta harare ta tace
"my sis kenan wlh ba ki da kirki yaushe rabon da mu yi waya dake? yau 2days fa ke nan, ni kuma aiki ne yayi min yawa na karɓi cases da yawa sai a hankali" Khadijah tace "Ayyah sorry my sis" Munnirah ta zauna a kan kujerar robar dake kusa da Khadija tace
"ina kika saka wayar ki? nayi ta kira tana ta ringing amma ba ki dauka ba? ke kam da waya idan abun emergency ne wlh mutum zai bushe, ko abunda zai faru sai dai ya faru baki ɗauka ba" Khadijah tace "yi hakuri my sis tana cikin jaka ne.
Munnirah tace "hmmm ke kullum wayar ki a jaka, handset aka ce ba bagset ba, kyau a samu zare a haɗa miki da wayar ki ringa ratayawa a wuya" Baba Rabi ta yi dariya tace "ayi haka kuwa?"
Khadijah ta ce Afuwan my sis zan gyara."
Munnirah tace "maybe in....hmmm nadaiyi shiru, Turaren nan yayi daɗi tun daga gate nake jin kamshinsa".
"Na Amare ne na karɓi order ɗin su, na ɗauka ina da time, lokaci naga zai kure min shi ne nace bari na fara rage aikin yau" anan Munnirah ta zauna suka hau hiri ko cikin gidan bata shiga ba.
Munnirah ta kalli idon Khadijah tace "My sis ko dai an yi sana'ar ne?
Khadijah ta haɗiye yawu, saboda ta san Munnirah ta santa ciki da bai, ko Umma ba kullum take gane yanayin ta ba, Amma Munnirah sai dai in bata kalli idonta ba.
Sai dai in Khadija ta ƙarya ta Munnirah ita kuma kawai saita rabu da ita, dan kar tayi mata fami, amma badan ta yarda ba kukan tayi ba.
"Me kenan? Khadijah ta tambaya.
Munnirah tace "kin fi ni sani, please bana son wannan yanayin baki."
Khadija dake ta dura turaren wuta a kwalabe ta ce da munnirah
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 4 Chapter of 29