ne?"
Ita wlh ta manta da zuwan shi, ya kira ta ɗazu wajen 11am na safe, yace mata ya shigo Kano zai bullo mata anjima, to ita ta ɗauka sai dare zai zo.
Umma be faɗa min lokacin da zai zo ba, ban yi tsammanin yanzu zai zo ba, na ɗauka ko sai dare."
"Toh tashi maza ki shirya, dan Allah kar ki bar shi yayi ta jira."
Sai da Umma ta ga ta shiga toilet sannan ta bar ɗakin.
Umma na sakowa ta wuce kitchen ta soya samosa da springrolls, daya ke ta kan ajiye a fridge saboda baƙin bazata, dan ma Umaimah da Hakimi su na mata ɓarna a zaman daren da su ke yi.
Umma na gama haɗa wa ta kira Baba Rabi tace "Baba Rabi ɗauki tray ɗin nan ki kai falo akwai baƙon Yayarsu." Baba Rabi ta karkace ta yi guda, tace "kai masha Allahu abun ya zo kenan?
Umma ta yi murmushi, Baba Rabi tace "na kusa barin ki Hajiya ƴata zan bi, muje mu yi zaman mu tare."
"kin kama Gaibu kuwa don ba a ƙasar zata zauna ba."
"ikon Allah za a bar mu da kewa."
ta ɗauki tray.
Baba Rabi ta shiga falon da sallama, da sauri ya ɗago kan shi, ɗan zaman da yayi ya ƙagu ya ganta, bai so zuwa yanzu ba, ya so sai dare ya zo, amma zuciyar shi ta ki bashi haɗin kai, dole ya taho ya ganta.
A mutumce suka gaisa da Baba Rabi, ta ce "an zo lafiya? ya amsa da lafiya ƙalau, mun same ku lafiya? "lafiya ƙalau wlh, uwarɗakin nawa tana nan zuwa, sannu da zuwa." ta ajiye tray ɗin ya debo kuɗi masu yawa ya bata,
"ga shi Iya kya si yi goro." Baba Rabi ta washe baki "a'a ayi haka kuma Alhaji? toh Allah ya amfana." ta karɓa ta fito tana ta murna.
Khadijah na fitowa daga Toilet ta nufi dressing mirror, lotion kawai ta shafa sai powder da lip gloss, ta saka kohl, tasaka doguwar riga sakakkiya ta material, ta fesa turare, ta ɗauko jilbab purple colour ta saka, har zata fita sai kuma ta dawo ta ɗauki wayarta.
Hakimi ya shigo ɗakin da sallama ya ce "Yaya Umma tace ki fito kar ki ɓata mi shi lokaci."
"gani nan fitowa."
Ta sauko ta tarar da Baba Rabi da Umma suna hira, Baba Rabi na ganinta ta taho wajenta da sauri, ta ce "masha Allah uwarɗakina Allah ya sa yin na Allah ne wlh, masha Allah, kalli abin alherin daya min, ga shi da fara'a." Umma ta ce
"Baba Rabi ƙyaleta ta je."
Idon Khadijah har ya fara tara ruwa, Umma ta ce "je ki Allah ya yi miki Albarka Khadijah, ba wani sabon abu ba ne in sha Allahu mu na addu'a babu abunda zai faru sai alkairi."
Khadijah ta juya ta nufi falon jikinta a sanyaye.
Ta dade tsaye a kofar falon tana tunanin yarda zata shiga, Aliyu ya zo wucewa ya gan ta tsaye, yace
"kar dai tun ɗazu ki na nan Yaya? me kike jira Dan Allah?" ta kalle shi murya a karye, ta ce
"yanzu zan shiga."
"haba tun ɗazu fah ya ke jiran ki." Ya wuce, ita kuma ta shiga falon da sallama.
Yana zaune, yana ganin ta ya miƙe da murnar shi, fuskar shi ɗauke da fara'a yace "sannu da zuwa. Khadijah ta zauna tace "kai za a yi wa sannu da zuwa." ta ji wata kunya ta rufeta saita saukar da kanta ƙasa, tace
"barka da yamma." Yanata kallon ta cike da burgewa yace
"barka kadai Amarya."
Tun da ta shigo bata
kalle shi ba, kanta yana ƙasa har yanzu, yace
"dan Allah ɗago idonki ki kalli Angonki, kar kiyi min rowar ganin kyakkyawar fuskar ki."
Khadijah ta ɗago a hankali, idon su ya faɗa cikin na juna, ta kawar da kai, yayi murmushi ya ce
"masha Allah, kamar yarda na faɗa miki kar muyi ta maimaita zance na taba aure matar ta rasu,.muna da yara biyu, Abunda ban fada miki ba shi ne health status ɗina, ina ganin haƙƙin ki ne ki sani, bayan rasuwar Maman yara na Allah ya jarabce ni da hawan jini, na sha wahala kafin ya yi stabiling, kin san hawan jini, idan ka fara shan magani ka yi ta sha kenan, an ɗora ni a akan drugs for life, ina fatan mu zauna tare mu shinfiɗa kyakkyawar rayuwa, Bahaushe yace zo mu zauna zo mu saɓa, pls khadija idan a zaman mu kika ga wani abun da be yi miki ba pls ki yi min magana, kinsan communication is key, duk abun da na yi miki mara daɗi toh sai dai ajizanci irin na ɗan adam."
A take jikin Khadijah yayi sanyi ta buɗe baki a hankali, ta ce "Allah ya baka lfy madawamiya, Allah ya bamu zaman lafiya." kawai haka ta ji bakin ta yana faɗa.
Ko a yadda ya Amsa da Allahuma Amin, amin amin kasan ya ji daɗin maganar ta har ƙasan ran shi.
"zan ɗan kwana biyu a Kano,I hope za a sake bani lokaci?
ta yi murmushi ta ɗaga mishi kanta, yace "yauwa bari na bar ki, kar na cika ki da surutu.
ta ce "baka sha ruwa ba. Yayi murmushi "ay baki ba ni ba."
Ta dawo kusa da shi ta durƙusa ta zuba ruwan ta miƙa mishi.
" Allah yayi albarka" ya karɓa .
****
Sai da ta gama al'adarta kamar yadda ta saba kafin ta kwanta barci, har ta kashe switch duhu ya mamaye ɗaki, tayi addu'a ta shafe jikinta, amma tunani sai ratso mata yake yi, ita ba za ta ce tana jin makamancin yadda ta ji a aurenta na farko ba, amma kuma wani yanayi take ji a tattare da Ahmad da ya fi kama da tausayi, tunda ya faɗa mata yana shan magani for life, taji tausayin shi ya kamata, Ahmad ba mummuna ba ne he is good looking, kuma dai an ce alamar ƙarfi tana ga mai ƙiba, a haka dai kamar ba shi da matsala, wata zuciyar ta kwaɓe ta da cewa shi ma Tahir kin taɓa tunanin haka daga gare shi ne? Haka Khadijah ta yi ta juye juye, tana son yin baccin, amma tunanin Rayuwar ta sai kutso mata kai yake tamkar a majigi take ganin abubuwan da suka faru na dawo mata ɗaya bayan ɗaya..
TUSHEN LABARIN
Asalin su Danejawa ne, Danejawa na daga cikin muhimman ƙabilar fulani, Kakansu Muhammadu Danejo sun yi kiwon fararen shanu zalla, daga Ƙasar Chadi suka yi hijira zuwa Ƙasar Hausa, suka sauka a garin Shanonon local government ɗin jihar Kano, wasu daga cikin yan uwa sun tashi daga Shanono zuwa Bichi da ke arewa maso yammacin Kano inda suka ɗauki sarautar Hakimci, kafin yanzu da aka naɗa mata Sarki, wasu suka koma cikin birin Kano suka kafa rukunin Daneji (unguwa ce a cikin gari) kusa da fadar Sarkin Kano, wasu kuma suka koma Kasar Katsina da zama.
Al'ummar Bichi riƙaƙƙun yan Boko ne, zaka same su suna nan da yawa a ma'aikatu a waje ƙasar da cikin garin Kano, an yi ittifaƙin babu wata local government a Kano idan aka cire cikin gari daya kai Bichi yawan yan Boko.
Khadijah ɗiya ta farko a wajen Umma da Baba, Baba ɗankanwar Dada ne da ta rasu ta bari (kamar yarda ku ka ji a baya ) aure ne na zumunci sukayi, tun Umma tana ƙarama Baba ya ke nuna wa Umma kauna, Hakimi da Dada sun fahimci yadda yake sonta, amma su ka yi shiru saboda lokacin suna karatu a jamiar Bayero University Kano BUK, shi kuma Ibrahim (Daddy) yana karatu a Ahmadu Bello University (ABU Zaria). Cikin hukuncin Allah suka kammala, Daddy ya riga Baba aure inda ya auri Darsha shuwa Arab ce, Daddy ya fara aiki a ƙaramin ma'aikaci a Lagos da ya ke International relations ya karanta har suka haifi Surayya, Amal, Fahad da Sa'ad da shekara ɗaya sannan Baba sukayi aure da Umma bayan ya samu aiki a ministry of Environment, aka kai Umma cikin garin Kano a Rukunin gidajen Sulaiman crescrent suka fara zama, gidaje ne na gwabnati G P (government property) da ake cirewa a cikin Albashinsu duk wata.
Khadijah ta taso cikin so mai tarin yawa, yar gata ce gaba da baya, kasancewar Umma ita kaɗai ce mace a wajen Dada, bayan an haifi Khadijah saiya zamana duk soyayyar da takewa Umma ta koma kan Khadija. Dada kullum cikin aike ta ke yiwa Khadijah, saƙon ta kullum yana tafe, kayan kwalliya ne, sarkoki, kayan sakawa lalle da sauransu, haka Dada zata ƙulle tace a kaiwa Hadiza.
Darsha (Mami) ita da Umma Aminai ne tin bayan auren Mami da Daddy Allah ya haɗa jinin su da Umma, kusan duk abunda ta siyawa su Amal saita siyawa Khadija, duk da gaba su ke da ita sosai.
Khadija bamai hayaniya ba ce tana da sanyin halitta, shiru shiru ce, tana da kyakkyawar alaƙa. Ko a makaranta malamanta na sonata saboda kwazon ta, primary da secondary school duka a kusa da gida ta yi su anan makarantar Da'awa dake Sulaiman crescrent, a ƙafa take zuwa makaranta saboda is just a walking distance.
Block ɗin su ɗaya da Aminiyarta Munnirah a block 12 su na hawa na ƙarshe, su Munnirah suna ƙasa, akwai shaƙuwa sosai a tsakanin Munnirah da Khadijah har ta shafi Iyayen su, Munnirah ita kaɗai ce a wajen Iyaye ta, sau da dama Umma tare ta ke yi masu abu, haka a gidan su Munnirah. Tare suke zuwa makaranta su dawo tare, Ajinsu ɗaya saboda haka kullum suna tare, A ajin su Allah ya hada jinin Khadijah da Zaliha sale ta dalilin tausayin da take bata, Khadijah tunda ta gane masu ƙaramin karfi ne take tausaya wa Zaliha, Babanta ya rasu marainiya ce, ita a Badawa take, Maman ta na sana'ar Koko da ƙosai da safe, sana'ar nan da ita suka dogara. Tun farkon haɗuwar Zaliha da Munnirah ba sa shiri sam Munnirah haka kawai Zaliha batayi mata ba, sometimes ta kan ce
"ba sa'ar mu ba ce, Tarbiyyar mu ma ba iri ɗaya ba ce."
Kasancewar Badawa akwai kabilu iri iri, saboda haka wani abun a sani ko a rashin sani, Hausawan mu suna samun gurɓacewar tarbiya saboda haɗakar ƙabilu, dole ka na Bahaushe za ka ga wani abun be yi dai dai da taka al'adar ba.kullum a faɗa Munnirah da Zaliha su ke, dan da gaske Munnirah bata san Zaliha.
💫 UMAYMAH 💫
✍️A&A PEN
FOLLOW OUR WHATSAPP GROUP VIA THIS LINK https://whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3
https://wa.me/+2348039352724
VOLUME ONE
EPISODE 3️⃣2️⃣
Sau da dama idan suka tashi daga makaranta Zaliha na bin su gida, a nan za ta yi sallar Azahar su ci Abinci tare sai sun fara shirin tafiya Islamiyya take tafiya gida Zaliha, kullum haka ake yi, daga baya Umma ta tambayi Zaliha ita bata zuwa Islamiyya ne? Ta amsa wa Umma da cewa bata zuwa saboda ɗawainiya ta yiwa Mamanta yawa, baza ta iya biya mata kuɗin ba.
Zaliha tana da ƙanne biyu kuma ita ce babba, don ma mai bi mata yana kanikanci ana sallamar shi kullum, sannan Zaliha ta iya kitso sosai har na attachment tana yiwa ƙabilun anguwar su, da taimakon kuɗin kitson dana kanikancin ƙanin ta suke harhaɗawa su biya buƙatun yau da kullum.
Umma ta ce Zaliha ta faɗawa Mamanta in ta yarda zata saka ta a Islamiyya, Zaliha ta tafi gida da murna ta faɗa wa Maman su. Bayan kwana biyu Mamanta ta zo har gida ta yi wa Umma godiya, zuwan Maman Zaliha gidan mu Umma ta sake ganin halin da suke ciki, dan koda tazo godiya suturar jikinta ta tsufa sosai ta koɗe har fari fari take yi da alama ta sha wanki sosai.
Tun daga lokacin Umma ta daina aika wa da kayan sawarta Bichi, in za ta bayar sai dai ta ba wa Maman Zaliha, Umma ta ɗauki nauyin kuɗin Islamiyyar Zaliha ta ɗinka mata uniform da litattafai, Zaliha ta fara zuwa Islamiyya, sai dai ba a saka ta a jin mu ba saboda mun yi mata nisa sosai.
kuɗin kashewa na Islamiyya Umma ke ba mu, wata rana kuma a ba mu a gidan su Munnirah amma ba kullum ba.
Wata ranar weekends Zaliha ta zo gidan su tana kuka, Umma ta tambaye ta kukan me take yi haka? Zaliha ta cewa Umma matar da su ke yin haya a gidanta ce tazo za ta tafi da Maman su charge office ɗin Badawa division, saboda basu biya kuɗin haya ba, yanzu haka ƙaninta sun tafi da Mama policetation ɗin, shi ne ita ta zo nan.
"Subhanallahi" Umma ta faɗa.
Allah yasa ranar Baba yana gida Umma tayi masa bayanin halinda su Zaliha suke ciki, nan da nan Baba ya ɗauki Zaliha a mota ya je ya kashe case ɗin, ya yi settling bills ɗin.
Bayan kwana biyu dayin haka Maman Zaliha ta zo gidan su da gero kwano ɗaya wake kwano ɗaya ta kawowa Umma a matsayin tukuicin abin alkhairin da Baba yayi musu, wataƙila a cikin na sana'ar ta ne ta ɗebo.
Baba yayi mata faɗa sosai, ya ce yayi mata ne dan Allah kar ta ƙara irin haka, ta yi ta godiya, ba yadda bata yi da Umma ta karɓi waken da geron ba amma Umma ta ƙi karɓa.
Shikenan tin daga lokacin biyan kuɗin hayar su Zaliha ya dawo kan Baba, duk shekara shi yake biya musu, duk da ƙaramin gida ne suke hayar, duk shekara Baba yana biya musu 40k na wancan lokacin da kuɗi suke da daraja.
Haka duk suturar da aka gani a jikin Zaliha kayan Khadija ne, dai dai da pant ɗauka ta ke tabawa Zaliha, sai ya zamana yaran Umma sun zama su uku, Khadijah, Munnirah da Zaliha, in dai ba Mami ce ta aiko wa Khadijah da kaya ba ko daga Bichi Dada ta aiko mata ba, to komai iri ɗaya Umma take yi musu, sai kayan sawar su ya zama babu bambanci.
Zaliha ta zama kamar yar gidan su Khadijah yawanci bacci ne kawai yake kaita gida.
Gidan su Munnirah ne kawai ba a haɗawa da Zaliha, dan tin haɗuwar su da Zaliha Hajiya (mahaifiyar Munnirah) ba ta sakarwa Zaliha fuska ba, sauda dama Hajiya kan ce mana itafa wannan yarinyar bata yi mata ba.
Haka Zaliha ta sha faɗa wa Khadijah ita bata son zuwa gidan su Munnirah, Hajiyar Munnirah bata son ta, Zaliha ko gidan su Khadijah ta zo neman ta indai Umma tace mata tana gidan su Munnirah to sai dai ta maƙale a waje har sai ta fito, idan bata fito ba kuwa sai dai ta gaji da jira ta tafi gida.
Khadijah da Munnirah suna da ƙoƙari sosai, Da'awa Arabic school ce, amma ana haɗawa da boko, Arabic ɗin ya fi ƙarfi ne kawai, da yake Khadijah nada basira saita mayar da hankali sosai wajan koyon harshen Larabci, mafi yawancin lokuta ma Arabic teacher ɗin su da Larabci ya ke yi mata magana.
Munnirah bata mayar da hankali kan Arabic ba, ta fi ga turanci, ita kuwa Zaliha sai a hankali, dan ko assignment aka bayar Khadija ce take mata, haka class work ita keyi mata, Munnirah tayi ta jin haushi, amma haka Khadija zata yiwa Zaliha, a exams ne kawai bata samun damar taimaka mata, saboda da tsaro.
Munnirah ita ke ta biyu, Khadijah tayi ta ɗaya, Zaliha kuwa wajen ta 20 ta ke ɗauka.
Wata rana aka bawa su Khadija wani assignment na discriptive essay akan Almustashfa (hospital), Munnirah ta yiwa Zaliha jan ido akan wlh Khadijah ba za ta yi mata ba, wannan dai essay ce, ba za ta yi amfani da basirar ta ba, sai dai ta yi da kan ta, ranar Munnirah da Zaliha su ka yi kaca kaca, har su ka tashi daga makaranta Zaliha na ta kumburi, Khadija ce mata ta yi hak'uri babu komai, ta karɓi littafin ta ta ɗan rubuta mata points ta bata, amma duk da haka Zaliha bata ji daɗi ba, ranar Alhamis ce a ka'ida bata tafiya gida, a gidan su ta ke yini tunda babu Islamiyya, Khadijah ke bata kayanta ta canja, amma ranar sai cewa tayi ba zata tsaya ba gida za ta tafi, Munnirah ta harare ta, tace
"ta fi nono fari".
Ranar da za a yi submitting assignment Khadijah ta san yana cikin jakar ta, amma saita neme sa ta rasa, gashi ita ce class captain Arabic teacher ya ce ta haɗo mishi assignment, tana ta laluben littafin Munnirah tace
"my sis wai me kike nema?" Khadijah tace mata Assignment ɗinta ne bata gani ba.
Haka ta haɗa na yan class ta kai sai cewa malam tayi ta manta nata a gida. yace babu komai gobe ta kawo masa.
Tana dawowa ta faɗawa Munnirah yadda suka yi da Arabic teacher, sai taga tayi shiru tana tunani, can ta ce zata faɗawa Zaliha idan an tashi break ta je gida ta karɓo musu kuɗin break a wajen Umma, tace wanda aka ba mu ya faɗi, sai kuma tace "Kodayake ma ke zaki faɗa mata, kin san ni ba wani shiri mu ke yi ba, za tafi zuwa aiken ki." Khadijah tace
"saboda me?" Munnirah tace
"saboda haka nace." Ta faɗa tana shan kunu.
Duk ranar juma'a saboda gajeriyar rana ce basa zuwa da abinchi kuɗi ake basu, ana fitowa break Khadijah ta faɗawa Zaliha taje ta karɓo musu kuɗin break kamar yadda Munnirah ta tsara mata.
Zaliha ta karɓi pass a gate ta tafi gida, tana fita Munnirah ta hau bincika jakar Zaliha to her surprise sai ga littafin assignment ɗin ta a jakar Zaliha, Munnirah ranta a ɓace tace
"wlh bari ta zo sai na tsuye ta."
Khadijah tace kawai ta bari dan Allah, amma deep down ta yi mamaki, toh me Zaliha ta ke nufi da ita?
Ta je tayi submitting assignment, ko da Zaliha ta dawo Khadijah ta roƙi Munnirah kar ta nuna mata komai, suna kallo tana ta bincike a jakar ta, basu yi mata magana ba, sai can da kanta ta magantu, da yake mai wayo ce sai cewa tayi, wai gwada ta take son yi ta gani ko za tayi kuka kafin ta bata.
Munnirah ta yi mata tas, tace "babu wani nan kawai hassada ce ay ba yau ta fara ba." dole saida Khadijah ta shiga tsakanin su dan kamar zasuyi dambe.
Haka rayuwa taci gaba da miƙawa, sai kuma hassadar Zaliha ta ƙara fitowa fili, ita Khadijah gaskiya a lokacin bata ganewa.
Idan daga Bichi aka kawo mata kaya Zaliha ta rinƙa kushewa ke nan, tace be yi kyau ba, haka dai take haƙuri da ita.
Duk lokacin da Munnirah tayi magana akan halin Hassadar Zaliha, Khadijah ta kan ce ra'ayinta ne, munnirah sai tace
"idonki ya rufe my sis in dai akan Zaliha ne."
Duk da haka abun baya damunta, kuma Iyayen ta basu fasa kyautata musu ba, duk Sallar layya Babancikin gida (Hakimi) yana aikowa da Baba Raguna manya daga Bichi, Daddyn Lagos kuma ya aiko masa da kuɗin Rago, ban da wanda Baba zai siya, sannan ana ba su a office, dan haka Baba duk sallah sai ya aika da rago gidan su Zaliha, daga baya ma kuɗin makarantar bokon Zaliha kacokan ya dawo kan Baba, karshe ma dai kayan abinci sosai Baba ya ke aika wa gidan su Zaliha saboda yawan zancen basu dashi da Khadija keyi masa.
Babancikin gida yana noman shinkafa Sosai gero, wake da alkama, Baba ya kan cewa Babancikin gida ya daina aikowa musu da kayan Abinci yanzu sun girma ana ta yi musu dawainiya, duk lokacin da Baba yace haka Babancikin gida sai ya haushi da faɗa,
"ko Sulaiman (Babansama ) yaro na ke ganin shi balle kai Muhammadu nawakake, idan ba kwa so ku zubar."
Haka zaiyi ta faɗa da kyar Baba yake shawo kan shi, yawanci waɗannan kayan abincin idan an kawo Baba gidan su Zaliha ya ke aikawa da su.
Khadijah bata taɓa faɗawa
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 17 Chapter of 29