ya tsaya mata a wuya.
Khadijah ta ƙara kyau farinta ya sake fitowa har wani ja take yi, ta sake cika ta murje abinta.
Zaliha batasan sanda wata ashar ta ƙwace mata ba, tace
"Khadija kece kika zama haka cikin sati biyu, ah lallai."
Kamar wace aka tunawa wani abu kuma sai tayi sauri ta canja fuska da murmushi, irin taji daɗin ganin ta ɗin nan. Tace"
Kai Masha Allah Khadija kinyi kyau fa."
Baiwar Allah Khadija babu komai a ranta ta samu waje ta zauna tana sakin murmushi,
"Kai Zaliha irin wannan ziga haka, ni banga wata canjawa da nayi ba. Haka shekaran jiya da Munnirah tazo tace na sake kyau."
Zaliha ta jijjiga kai cikin baƙin ciki, ta sake kallon Khadija zuciyar ta kamar zata fito saboda baƙin ciki.
Zaliha ba ƙaramin yaƙi tayi da zuciyar taba ta saita kanta, suka hau hira sai bugun cikin Khadijah take yi, ita kuma baiwar Allah zuciyar ta ɗaya take bata amsa.
Bayan sun ci abincin rana, Zaliha tace Khadija tazo tayi mata kitso ai batayi ta zama dakai a tsefe ba. Khadijah ta murmusa, "Ai kuwa Zaliha kamar kinsan inason amin kitson nan, amma Habibeey ya hana wai shi yafi son ganin gashin a haka, shekaran jiya dana damesa da maganar kitso kawai saiya kaini wajan saloon aka sake gyara min gashin."
Zaliha ji tayi wata masifa na mata yawo akai, kirjinta har wani zafi yake mata saboda baƙin ciki.
Can ta numfasa tace"
Hmmm kinsan tinda akayi Auren nan kina raina Khadija, ina taso nazo na same ki muyi magana sai kuma ciwo ya hanani fita."
Cikin tausayawa Khadija tace" ayya babu komai Allah ya ƙara sauƙi."
Zaliha ta sake gyara zama ta fuskanci Khadija, "Kindai san ina sanki duk abinda zai rabaki da Oga bazan so miki shiba shi yasa naso nazo da wuri, amma yanzun ma baki makara ba zaki iya gyara komai.
Khadijah ta kalli Zaliha cikin neman ƙarin bayani, dan bata gane abinda take san cewa ba, to ita maima zai rabata da Habibeey.
Zaliha ta katse mata tunani da cewa"
Kinga mazan nan musamman irin su Oga daba yan ƙasa ba basa son haihuwa da wuri, kinga duk wannan son da Oga yake yi miki in kina yarda kika haihu yanzu to fa taki ta ƙare, Khadija saidai kiji anayi. Dan haka nidai na faɗa miki gaskiya a matsayi na na ƙawarki mai sanki, karki je ki sakar masa jiki yayi ta naniƙar ki kina yin ciki ya tsallake ya barki da wahala. Mazan Larabawa kinsan ba wani tara yara suke ba."
Lokaci ɗaya hankalin Khadija ya tashi, taji wani tsoro ya shige ta, to amma kuma tinda suka yi Aure kullum cikin faɗa mata yake Allah ya bata ciki ta haifa masa mai sunan Ummisa, Khadija ta tuna jiya suna kwance take tambayar sa yaushe zai kaita taga Ummi, budar bakin sa yace mata "Kina haihuwa zan kaiki wajan Ummi.
Ganin ta shiga dogon tunani Zaliha ta sake gyara zama tace"
Hmmmm! Kindai san bazan faɗa miki abunda zai cuce kiba, nidai na faɗa miki kisan abun yi Khadija, ki rufawa kanka asiri karki yarda ki haihu da wanda baki san ƙasar su da inda danginsa suke ba."
Gaba daya yanayin Khadija saiya canja ta shiga saƙawa da kuncewa, Zaliha bata kyale Khadijah ba saida ta cusa mata ra'ayin ƙin yarda da Tahir, tace mata"
Ki kwantar da hankalin ki gobe zan biyo na kawo miki maganin da zaki rinƙa sha wanda zai hanaki ɗaukar ciki da wuri har saiya kaiki wajan danginsa kin sansu tunnna."
Zuciyar Khadija na rawa da tsoran rasa masoyi ta amince da shawarar Zaliha, a take Zaliha ta ware ta tsara mata yadda zata rinƙa ɓoye maganin dan karya gani. Khadijah cikin rashin sani da rashin wayo ta amince da duka shawarwarin Zaliha.
💫 UMAYMAH 💫
✍️A&A PEN
Follow our Whatsapp group via this linkhttps://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3
https://wa.me/+2348039352724
VOLUME ONE
EPISODE 4️⃣0️⃣
Zaliha saida ta wuni sir a gidan Khadija tana famfata duk da burin ta bai cika na samun gashin kan Khadija ba, amma ta barwa ranta zata samu ne gaba kaɗan, yadda ta ɗora Khadija akan keken ɓera tahau ta zauna ba ƙaramin daɗi yayi mata ba.
Zaliha na shirin tafiya Tahir ya dawo, fuskarsa a sake suka gaisa da yace"
Zakiyya sannu da zuwa gidan mu duk da kinyi lattin zuwa"
Wani baƙin ciki ya sake kume Zaliha, wato har yanzu ya kasa riƙe sunan ta ma, saboda tsabar wulaƙanci, a ranta tayi ƙwafa tace zaka shigo hannu ne.
Khadijah tayi murmushi tace" Habibeey bafa Zakiyya ba ne Zaliha ne."
Ya kalle ta idanunsa cike da soyayyar ta yace"
Oh! Zakiha."
Khadijah bata san sanda ta kwashe da dariya ba, Zaliha sai taga kamar izgilanci suke yi mata, wato su masoya ko.
Ranta a ɓace tayi musu sallama ta tafi Tahir ya bawa Khadijah kuɗi yace ta bata tahau mota, Khadijah ma ta bata kyautar turaruka da kayan kwalliya.
Zaliha na fitowa ta tsaya a bakin titi tana sauke numfashi wasu hawayen baƙin ciki taji suna zubo mata, cikin baƙin ciki tace "in banga bayanki ba Khadija ba zan taɓa farin ciki ba.
A wannan daran Khadija ƙin yarda tayi da Tahir abun ya basa mamaki dan abun ne dabai taɓa faruwa ba tinda suka yi Aure. Amma saiya dauka ko ta gaji ne, Tahir bai kawo komai aransa ba ya rungume ta suka yi bacci, bayan ya dawo daga Sallar asuba ma Khadija fir ta juya masa baya daya matsa mata ma saita saka masa kuka, abinka da Balaraben mutum hankalin sa a tashe ya fara tambayar ta ko bata da lafiya ne ko kuma yayi mata lefi.
Khadijah taji tausayin shi amma huɗu bar Zaliha ta riga ta shiga ranta ta zauna, bata jin zata sake yarda dashi inba maganin nan ta fara shaba.
Haka Tahir ya fita ranar jikinsa a sanyaye, bayan fitarsa ya kira Khadijah ya tambayi lafiyar ta yafi a iriga, can wajan ƙarfe 12 na rana daiga Zaliha ta kawowa Khadija maganin ta sake jaddada mata tafa ɓoye da kyau karya gani ta kuma dage dasha inba haka ba tanaji tana gani zata rasa Tahir, Khadija ta karɓi maganin tana ta yi wa Zaliha godiya.
Zaliha na tafiya ta ɓalli ƙwayar maganin guda ɗaya kamar yadda Zaliha ta faɗa mata haka tasha, ta samu waje ta ɓoye a kitchen.
Tahir da wuri ya dawo gida, bayan yaci abinci ya huta ya sanar da Khadija jibi zasu yi tafiya zuwa Abuja, dan haka gobe ta shirya ya kaita gida tayiwa su Umma sallama, Khadija cikin jin daɗi da murnar zata gida ta Rungume shi tana dariya.
Suna haka kiran Ummi ya shigo wayar Tahir, ya ɗaga suka gaisa da Ummi, ya miƙawa Khadija wayar suka gaisa, Ummi nata janta da hira kamar ba suruka ba.
Khadija da Ummi sun saba sosai, suna yawan yin waya da ita, Ummi nason Khadija sosai haka kawai zata kirata tace tanason jin lafiyar tane, tin Khadija najin kunyar Ummi harta sake. sun jima suna hira da Ummi har Tahir yayi wanka ya fito suna wayar, sannan su kayi sallama.
Washegari Tahir yakai Khadija gida, tinda Khadija ta shiga gidan Umma take binta da kallo, a ranta take faɗin masha Allah, yadda taga Khadija ta canja tayi kyau abun ba ƙaramin daɗi yayi wa Ummi ba, farin cikin Umma yaƙi ɓoyu wa, anan suka wuni da Munnirah suna ta hira har Baba ya dawo, ko Baba bai faɗa ba fuskar sa ta nuna jin daɗin yadda yaga Khadijah.
Bayan Sallar magriba Tahir ya dawo daukar Khadija, Baba ya sake yi musu nasiha da saka musu albarka, Tahir ya fito waje shida mutumin sa Ibrahim, Aliyu kuwa gaisawa kawai suka yi dashi ya wuce ciki, Khadija na fitowa tace masa zata shiga wajan Hajiyar Munnirah su gaisa ya ce babu komai taje amma tayi sauri.
Bata wani jima ba ta fito da tsarabar da Hajiya ta bata.
Washegari da safe Khadijah da Tahir suka tafi Birnin tarayyar Nigeria Abuja. Tahir yaje duba wani Company ne da yake son fara harkar kasuwanci dasu.
Zaliha lokacin da ta samu labarin tafiyar Khadija Abuja saida tayi ciwo saboda baƙin ciki da tashin hankalin data shiga, hankalin ta a tashe ta koma wajan na Zaure, wannan karon ko Suwaiba bata nema ba tayi tafiyar ta. Na Zaure ya kalle ta duk ta wani firgice, yayi dariyar sheɗanci sannan, yace mata ta tashi taje shi bashi da abinda zai yi mata saita kawo abinda ya buƙata. Gwiwar Zaliha a sanyaye ta baro wajan sa.
Tafiyar sati ɗaya saida ta kwashe su tsawon wata biyu, faɗin irin rayuwar da Tahir da Khadija sukayi a Abuja ma bata baki ne anci soyayya kamar babu gobe, duk tsawon wannan lokacin kuma Khadijah na maƙale da maganin ta. Allah Allah take su dawo gida dan magajin ya kusa ƙarewa, dan baifi sha biyu ba ya rage mata ba.
Khadijah sun dawo Kano lafiya, kwanan su biyu da dawowa Tahir ya sake kai Khadija gida, a wannan zuwan Umma kasa shiru tayi saida tace wa Khadijah"
Oh Khadija me kike ci ne haka, ashe zakiyi jiki Masha Allah, Allah ya sake haɗa kanku." Khadijah bata ce komai ba sai sunkuyar dakai da tayi tana murmushi.
Shi kansa Baba da yaga Khadijah saida yace "Masha Allah."
Washegarin da Khadija taje gida saiga Zaliha da rana tsaka, Khadija ta karɓe ta da murna, Zaliha tace mata ai taje gidan su wajan Umma ne tace mata sun dawo, kuma tana ta kiran wayar ta bata samu. Tazo a bata tsarbar Abuja.
Khadijah tace layin ta ne ya samu matsala amma ta canja wani.
Zaliha bata bar gidan Khadija ba saida ta yarfa mata kitso kamar bada hannu tayi saba. Sunayin kitson Zaliha najan gashin Khadija da gangan tana tarawa a matse matsin zanin ta.
Tana gama yi mata kitson tayi mata sallama tabar gidan da sauri murna kamar ta taka rawa.
💫 UMAYMAH 💫
✍️A&A PEN
Follow our Whatsapp group via this link https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3
https://wa.me/+2348039352724
VOLUME ONE
EPISODE 4️⃣1️⃣
Daga gidan Khadija direct Zaliha wajen Malam na Zaure ta wuce ta tarar da layi, tana zaman jira wayar ta ta yi ringing Suwaiba ce suka gaisa, Zaliha tace gata a wajen Malama, Suwaiba tace
"shegiya ƙawata haka na ke so ki mayar da hankali an jah lokaci fah, daga sati ɗaya yau aure kusan wata uku." "haka ne zan dage ƙawata komai ya zo karshe." Zaliha ta faɗa, su ka yi sallama, layi ya zo kanta ta shiga.
Tana shiga da murnar ta bawa Malam na Zaure yayi dariyar mugunta yace mata
"ki je nan da kwana biyu ki dawo, wannan shi ne matakin farko na aikin mu kafin na gaba." tayi godiya tana ta murna kamar an ce mata Khadija har ta fita ita zata shiga.
Zaliha na zuwa gida ta tarar da Alkasim zaune a dakalin gidan su yana jiranta, da fara'ar shi suka gaisa ya tambaye ta "daga ina haka?" Tace "wlh gidan khadija na je." Alkhasim yace
"idan babu damuwa mu shiga daga Soro, zance ne mai muhimmanci ne." Zaliha ta shige Soron ya rufa mata baya.
"toh ka yi shiru kuma?" Zaliha ta faɗa tana kallon shi, ya numfasa
"wato malama Zaliha ni dai ba yaro ba ne, a gaskiya tuntuni na daɗe ina ƙaunar ki na daɗe ina son yi miki maganar toh ganin kina makaranta shiyasa ban furta miki ba, kamar yadda kika sani na kammala jami'a, aikin kamfani da na ke yi dan na tallafawa karatu na ne kuma Alhamdulillah kwaliyya ta biya kuɗin sabulu duda mu masu ƙaramin karfi ne, kin kammala secondary school ɗin ki ina so ki bani dama mu fuskanci juna."
Tun da ya fara magana wani baƙin ciki ya kume Zaliha, ta mishi wani kallon kaskanci, shi kuwa sai zuba ya ke, sai da ta ji yayi shiru, tana kallon shi sama da kasa tace
"kai yanzu dan Allah idan aka ce zan aure ka sai ka yarda, wlh yadin ba kalar zaren ba ne, ni matar manya ce, bar ganin mu na mutunci wlh sai na rufe ido na yi maka kaca kaca in banda wulakanci, banda zarmewa irin taka wlh ni ba sa'ar auren ka ba ce." ta ja tsaki ta bar shi a wajen, yayi shiru jikin shi yayi mugun sanyi wlh be taɓa tunanin haka take ba, amma ya godewa Allah shima ba irinta ya ke nema ba, matar rufin asiri ya ke nema haka ya bar ƙofar gidan su Zaliha yana ta zancen zuci.
Baba ne yake ta faɗa ya dubo jamb ɗin su Khadijah dukka su ukun babu wanda yaci abun arziki, points ɗin su babu jami'ar da zata ɗauke su, ya kira Ibrahim yace ya je ya kirawo mishi Munnirah, Umma tana gefe ta yi tagumi itama abin be yi mata daɗi ba.
Ba a fi minti 5 ba suka shigo tare da Ibrahim, ta tsugunna ta gaishe da Baba da Umma, Baba be amsa ba ya balbale ta da faɗa sosai yake mata faɗan
"babu jami'ar da zata ɗauke ku da wannan result ɗin, dole sai kun maiamaita wata shekerar, kuma ki je ki faɗawa yar uwarki lallai ta mayar da hankalinta ta yi karatu dole ku maimaita wata shekarar, yace zan ma kira ta a waya." Munnirah ta ce "in sha Allahu zamu dage."
Munnirah bata ji daɗim faɗuwar su ba, haka taje ta faɗawa iyayenta, Babanta har ya fi Baba yin faɗa, sosai yayi mata kaca kaca, yace Idan itama auren take so gara ta faɗa yayi mata, "mutanen nan suna ta kokari a kan ki, kina wasa dan ni babu abunda zan ce da Alhaji Muhammadu sai Allah ya saka da alkhairi."
Tahir ya shigo falon da sallama a bakin shi ta amsa daga kitchen, ya samu waje ya zauna ta taho da tray a hannu ta ajiye a gaban shi "sannu da zuwa." Khadija ta faɗa "yawwa sannu Hayateey." ya amsa mata da kulawa, ya miƙa mata hannu ta sunkuyar da kai ta ƙaraso ya zaunar da ita a kan cinyar shi, yayi mata kiss a wuya ya shaki kamshin turarenta,
"Barakallahu fiyki (God bless you)." ta yi murmushi, ya ɗago da fuskarta yana kallo jakar da ya shigo da ita ya janyo ya buɗe ya Ciro wani karamin boxes abun sha'awa ya miƙa mata, "hadiyah saghirah min qalbi (a small gift from my heart)." ta karɓia sarka ce mai chain da ɗan kunne da zobe na gold, ta rungume shi da murnar ta ta ce "shukran min qalb (thank you from my heart)."
"Haayatee"
ta kira shi shi, ya kalle ta, "an saka min a lefe fah." yayi mata wani kallo kamar harara yace "wannan is a special gift from me to you." ya raɗa mata wani abu a kunne ta tashi da gudu ta yi ɗakii, ya gaji da jiranta ya bi bayanta, yace ta shirya gobe jumma'a za su je yankari su yi weekends acan, ta tashi daga kwancen da take, "Hayateey ka yi concentrating a company yaushe muka dawo daga Abuja?" Ya ja kumatun ta, "everything for you Hayateey." "thank you." ta faɗa, yace "bari na koma Company na bar aiki."
"ka tsaya ka ci abinci." "No sai dai na tafi dashi."
Ta haɗa mishi komai a basket ta rako shi mota yana fita har takoma ta zauna ta ji Knocking kofa ta je ta buɗe Munnirah ce "my sis ta rungume ta." sai ta kula Munnirah jikinta duk yayi sanyi "me ya faru my sis?" Khadijah ta tambaya,
"hmmm mu shiga ciki." Munnirah ta faɗa suka shiga Falon, sunna zama Munnirah tace "my sis results ɗin mu na jamb be yi kyau ba." Khadijah ta dafe kirgi idonta yayi ciko da hawaye ta yiwa Baba da Daddy alkawarin good results don ma sun ci waec da neco, duk information ɗin su da scratch cards na jamb yana wajen Baba, "innaah lillahi wa inna illahirrajiun." Khadijah ta ke ta maimaita wa har ta fi Munnirah tashin hankali, Munnirah tace "mu ɗauki kaddara, za mu sake maimaita wa next year, Baffah ma yayi faɗa sosai, in sha Allahu za mu ci next year sai mu shiga extra lesson." Khadija ta ce "haka ne."
Munnirah ta na ɗan jan ta da hira har suka yi sallah, suka shiga ɗora girki, Munnirah ta jawo wata drawer ta ga sachet ɗin magani ta juyo rike da maganin a hannunta tace
"wannan maganin meye? Khadijah ta karɓe maganin da hanzari, 'pills ne"
"pills"
Munnirah ta ƙara maimaita wa "na hana daukan ciki?" Khadijah tace "eh." kan Munnirah ya ƙulle, "saboda me kike shan pills."
Khadijah ta kwashe yadda suka yi da Zaliha ta faɗa wa Munnirah, Munnirah ta tsaya tana kallon ta, ta rasa wannan rashin wayon na Khadijah na menene anya na yar farin ne kawaai, ita kaɗai ce a wajen iyayenta, amma bata shirmen da Khadija ta ke yi, idan ma iskanci ne zata yi maganinta, kawai sai ji tayi Munnirah ta warce maganin tace
"wlh sai na nunawa Umma wannan wacce irin masifa ce." ta lailayo Ashar ta dannawa Zaliha "sai naci ubanta shegiya yar sharri, wato so take ta cuce ki, ta kashe miki aure saboda tana baƙin cikin bata samu miji kamar naki ba zan yi maganinta."
Munnirah ta faɗa tana huci, "pls my sis ki yi haƙuri dan Allah kar mu yi haka da ke ki rufa min asiri." Idanuwan ta har ya tara ruwa, Munnirah ta ƙura mata ido ta ce "ki yi min Alkawarin duk abunda Zaliha ta saka ki zaki kirani ki faɗa min, wlh ki fita harkar tsinanniyar yarinyar nan, na faɗa miki ba son ki ta ke yi ba."
"Nayi Alkawari, nayi Alkawarin." ta faɗa da sauri, sai ta bawa Munnirah tausayi.
Zaliha ta samu Khadijah mai sanyin hali da rashin wayo ta ke juya ta son ranta, haka suka yi girkin kowa da tunanin da ya keyi a rainshi, ba yadda Khadijah ba ta yi da Munnirah ta tsaya su mayar da ita ba ta ƙi, Abincin ma taki ci, tace zata dawo wani lokacin.
Fitowar Munnirah bata zarce ko ina ba sai gidan su Zaliha, sun gaisa da Maman ta a bakin titi tana kosan yamma hakan yayi mata daɗi sosai, ta shiga gidan da sallama, Zaliha ta amsa ta fito suka haɗu a tsakar gida dan ta gane Munnirah ce. Munnirah bata yi wata wata ba ta ɗauke Zaliha da mari, Zaliha ta dafe kuncin ta, ta yunƙura za ta rama Munnirah ta riƙe hannunta, tace
"wlh sai na karya hannunki na karya banza mara mutunci macuciya maciya Amana maha'inciya, me Khadija ta yi miki? me ta tsare miki? wlh wlh wlh kin ji na rantse idan wani abu ya faru da Khadijah wlh sai an ɗaure ki har igiya ta yi saura, ki kiyaye ni ki fita a ido na, idan kika taɓa Khadija ba da ita kike ba ni kika taɓa wlh har gara ni ki taɓa ni, amma my sis." sai tayi murmushi tace "is no go area." ta yarfar da hannun Zaliha tace
"idan kunne ya ji jiki ya tsira" ta juya ta fita ta bar Zaliha a tsaye dafe da kumatu.
Taso ta kama ta da kokawa amma jin maganar da suka yi da Khadijah ta kwashe ta faɗawa Munnirah sai hankalin ta ya tashi, idan Khadija ta faɗawa iyayenta fah, ba shiri ta ɗauki wayarta ta kira khadija tana kuka, Khadijah hankali tashe take tambayarta menene?
"Haba Khadijah daga taimako sai ki faɗawa Munnirah ta zo gida ta ci min mutunchi har gida ta zo tayi min duka." Khadijah ta rikice tayi ta bawa Zaliha hakuri suka yi sallama jikinta a sanyaye.
Sun tafi yankari game resort tun Khadijah cajin kan ƙawayen ta na damunta har ta saki jiki suka more weekends ɗin su, wajen ya kayatar da Khadijah it was a memorable event, Namun daji ta koina ta sha kallo. Tahir ya shiga swimming pool ɗin su Khadijah ta rinƙa ɗaukan shi a hoto.
Bayan sun dawo daƙi yake faɗa mata idan ta haifi mace sunan Ummin shi zai saka (Fatima) zaina kiranta da Umaimah duka sunan Ummin shi ne Umaimah haka mahaifiyar Ummi (Jadda) ta ke kiran Ummi, Khadija ta yi shiru tana tunani ita duk sun raba mata hankali.
💫 UMAIMAH 💫
✍️A&A PEN
Follow our Whatsapp group via this link https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3
https://wa.me/+2348039352724
VOLUME ONE
EPISODE 4️⃣2️⃣
Yau tunda ta tashi ta ke jinta wani iri kamar wani abu yana damunta sai ta alaƙan ta hakan da Tahir da ya kwana jiya yana fama da ciwon kai, tun dawowarsu daga Bauchi suka tsaya a Al Sultan restaurant suka yi take away Tahir yace su shiga studio 24 a ɗauke ta a hoto, da suka dawo gida abincin ma kaɗan yaci yayi ta amai, ya kama kai yana ta juyi haka suka kwana yana fama, sai yanzu bacci ya kwashe shi.
Khadijah ta rasa abunda ya ke mata daɗi ta fito daga ɗaki ta haɗa mishi breakfast, ta koma ɗakin tayi wanka ta shirya ta dawo palour ta zauna sai ta ji wayar ta na ringing, Munnirah ce ta daga hankali a tashe Munnirah ke faɗa mata Hajiyar ta an kwantar da ita a Aminu kano teaching hospital babu lafiya bincike ya nuna tana ɗauke da ciwon ƙoda, Munnirah tana kuka tana yiwa Khadijah bayani.
Ita da Khadija duk kukan su ke yi an rasa wanda zai bawa wani hakuri acikin su, daga ƙarshe dai Munnirah ta katse wayar.
Malam na Zaure yace "Yawwa yanzu ina so ki koma gidan dole akwai abunda yake faruwa, sai aiki na gaba ki karɓo abincin gidan ko ba yawa, ki karɓo suturar ta ko aro ce sannan kuɗin hannunta ko yaya ne ki tabbatar daga hannunta ya fito." "malam kuma me za a yi da waɗannan abubuwan?" Na Zaure ya sheƙe da wata irin dariya irin ta basawa yace mata "da su ne aikin mu zai tafi yadda mu ke so, yarinya menene jin daɗin Rayuwar in ba Abinci ba, ka fi ƙarfin shi da suturar sawa kafi ƙarfin ta, kafi ƙarfin kuɗin kwashe wa, rayuwa in babu kuɗin biyan buƙata ta tawaya." Zaliha ta gyada Kai "haka ne".
"ina tabbatar miki in kika kawo min su yadda nace miki, abinci ma sai ya hana ta balle kuɗin kashewa da sutura idan muka janye wannan zaman me zata yi? yanzu a hankali zamu saka tsanar ta a zuciyarshi, da ƙarfi zamu cusa masa kaunar ki, ina tabbatar miki nan da sati mun gama da wannan." Zaliha cikin jin daɗin bayanin na Zaure ta Ciro kuɗi a jaka 20k data ke tarawa ta ajiye mishi.
Yace mata lallai daga yau zuwa gobe ta kawo mishi ta amsa da yanzu kuwa ta fito.
Tunda ya tashi ta ke fama da shi ya ɗaure yayi break fast ya ƙi, yana ta wani ɗaure fuska tana ta lallaɓa shi yana dagewa sai tayi tunanin duk zafin ciwo ne, kwata kwata ya ƙi sakar mata fuska ƙarshe ma tashi ya yi ya shiga ɗaki ya barta anan, tana zaune abun duniya yayi mata yawa ga jinyar Hajiyan Munnirah ta tsaya mata a rai, tana son mishi zancen zuwa dubiya babu fuska, ga wannan ciwon da Tahir ya ke yi, don ita a ciwo ta ɗauke shi, kowa da yadda ya ke yi idan ba shi da lafiya, tana nan zaune ta ji Knocking gate ta tashi ta je ta duba Zaliha ce, ta yi murna ganinta ko ba
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 21 Chapter of 29