Share this page
sauri Uncle Isma kuma ya shige ɗakin shi. Basu daɗe da shigewa ba Fahad ya turo ƙofar falon kamar baya so yayi sallama, falon yayi shiru babu kowa a ciki, can yake jiyo haya niyar mutanen gidan a falon Baba. Tea yake son yasha tin ɗazu Ibrahim yakai masa abinci, tinda aka kai ko takan abincin baibi ba sai yanzu ya taso, yaɗan tsaya a falon yana tunanin yadda zai samun tean, daga ƙarshe yayi hanyar kitchen, yana shiga ya fara duba tukunyar da zai iya ɗorawa, plate ya gani a rufe harya ɗauke kanshi sai wata zuciyar ta rinjaye shi ya buɗe, yaɗan tsaya yana kallon indomien, tayi masa kyau a ido ga wani ƙamshi mai daɗi dake tashi, kawai Fahad saiya ɗauki plate ɗin indomien ya ɗauki pock ya wanke ya buɗe fridge ya ɗau ruwa mai sanyi ya fita ta kofar baya ya koma Chalet ɗin su Aliyu. 💫 UMAYMAH 💫 ✍️A&A PEN Follow our Whatsapp group via this link https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3 https://wa.me/+2348039352724 VOLUME ONE EPISODE 5️⃣1️⃣ A falon su Aliyu Fahad ya ya ajiye plate ɗin akan study table ya wuce ɗakin Aliyu, daya ke a ɗakin shi ya sauka dan shi ne bashi da haya niya and psychologically tasu tafi zuwa ɗaya, Sa'ad kuma yana ɗakin Ibrahim dan yace Allah ya ba shi lafiya ba za'a hanashi zance ba. Toilet ya wuce ya wanke hannun shi sosai sannan ya sake wanke fuck ɗin ya fito, falo ya dawo ya zauna, tin a spoon ɗin farko yaɗan tsaya yana tunanin daɗin indomien ya ratsa shi, cin indomien kawai yake cikin jin daɗin ta, gaskiya ya daɗe baici abinci mai daɗin wannan ba, saura kaɗan ya cinye Sa'ad ya shigo falon yana amsa waya da alama da Farida yake wayar, a kujerar da ke kallon sa ya zauna, har ya gama cin abincin bai gama wayar ba. Fahad ya kalli plate ɗin indomien daya tashi dashi a ranshi yace "yaushe rabon naci abinci mai yawan wannan." ruwan sanyi ya buɗe saida ya shanye ruwan tas sannan ya ajiye robar. Sa'ad ya sauke wayar yana kallon shi "bro maika samu ne kake ci haka? Ga wani ƙamshi mai daɗi yana tashi." Fahad ya kwantar da kanshi a jikin kujerar yayi shiru. Ganin bazai kula shiba Sa'ad ya taso ya zo kusa da shi ya kalli plate ɗin "ah a ina ka samu indomie haka?" "Wai kai meye matsalar ka dani ne?" Fahad ya faɗa, Sa'ad ya ɗaga hannu sama alamar sarandar "babu, taɓ amma gaskiya duk wanda yayi girkin nan ya kamata a yi masa kyauta, wai duka plate ɗin nan ka cinye?" Sa'ad yayi maganar yana sake kallon plate ɗin. Fahad ya miƙe tsaye kamar ba zai kula shi ba, yayi kamar zai wuce ta kusa da shi kawai saiji yayi ya take masa ƙafa, ihu Sa'ad yayi, Fahad yayi murmushin mugunta ya wuce ɗaki yabar shi anan yana duba ƙafar shi, da ƙarfi yace "Allah bashi kaci, mugu kawai." Sa'ad bai daɗe a falon ba ya ya fito dama wayar ce ta fito dashi, falon Abba ya koma wajen su Ibrahim sukaci gaba da hira. ****** Umaimah na fitowa daga wanka ko mai bata shafa ba tasa doguwar riga ta fito da sauri, a falo suka haɗu da Uncle Isma, "Yawwa muje dan Allah cikina ya fara kiran Bichi." Suna shiga kitchen plate ɗin indomie yace ɗauke ni inda kuka ajiye ni, Umaimah da Ismael har haɗa baki suke wajen tambayar juna ina indomien. Umaimah ta kalli Ismael "dan Allah Uncle Isma yanzu ba lokacin wasa bane Allah yunwa nake ji, nina ɗauki bread ɗin ka taho mana da indomien." Umaimah bata jira mai Uncle Isma zaice ba ta fita daga kitchen ɗin, dan da gaske yunwa take ji, Ismael bakin shi buɗe yabi bayan ta da kallo, sai kuma ya ɗauki wacce ta zubawa Sa'ad ya bita da sauri. Harta shiga falon Baba, Daddy na ganin ta yayi murmushi "yau nima gaskiya zanci girkin nan naki Amaryar." Umaimah tayi murmushi tace "gaskiya Daddy bamu yi da kaiba amma dai zan samma one spoon, Yawwa Uncle Sa'ad bari na dakko ma naka yana kitchen.. tana juyawa Uncle Isma ya shigo, plate ɗin hannun shi ta karɓa ta bawa Sa'ad ya karɓa yana ta murmushi yace "thank you daughter." "Yawwa Uncle Isma bamu tabu muci." Umaimah ta faɗa tana gyara zama akan carpet, "kinsan Allah bani na ɗauka bafa." Umaimah tabi bakin shi da kallo kamar wata sokuwa tace "ban gane bakai ka ɗauka ba?" Ismael ya zauna kusa da ita "Allah Umaimah ban ɓoye ba ai kinsan bama haka dake." Umaimah ta wani ƙwalalo ido waje sai hawaye, Isma'il bai kula ba tayi fatali da plate ɗin bread din, ta fasa kuka, gaba ɗaya hankalin jama'ar falon ta dawo kanta, kuka take tsakanin ta da Allah, Daddy yayo kanta da sauri yana tambayar meya same ta. Umaimah birgima take bil haƙƙi tana zundima ihu, Daddy yayi yayi da ita tayi shiru ta faɗa masa mai aka yi mata taƙi, sai birgima take tana kuka, taki sauran kowa, abin ya ɓata wa Aliyu rai ganin yadda kowa ke kokarin lallaɓar ta tana butsare wa, kanta yayo ransa a ɓace Daddy ya taresa, "a'a Babangida karka taɓa ta." Aliyu ya koma baya yana ƙwafa, Daddy ya kalli Ismael da duk fuskar sa ta canja da ɓacin rai, shi kanshi baiji daɗin abinda aka yi musu ba, gaskiya ko waye ya ɗauke musu indomien nan bai kyauta musu ba, haba dan Allah girkin da tin da suka shigo gidan take shirin yinsa, kuma saida suka gama a ɗauke musu dole ma Umaimah taji babu daɗi, Muryar Daddy ce ta katse wa Ismael tunani, "Hakimi faɗa min maiya same ta, naga yan zun nan kuka shigo tare lafiya." Ismael ransa duk babu daɗi yace "Daddy wallahi indomien da muka dafa ce bamu gani ba, kuma a kitchen muka ajiye akan sai Umaimah tayi wanka zamuci." Umma taja tsaki "kai amma Umaimah Allah ya shirye ki yanzu akan indomien kike wannan rusa kukan kamar wacce aka yi wa duka." "A'a Azumi dan Allah zancen nan ba naki bane, ba dole tayi kuka ba duk ma wanda ya ɗauka mata indomien ta maza a fito mata da shi banason rashin adalci." Daddy yayi maganar yana kallon mutanen falon, kowa yace bashi ya ɗauka ba, Daddy ya hau faɗan indomie zata cinye kanta ne. Umaimah najin faɗan da Daddy yake tadan tsagaita kukan amma sai ajiyar zuciya take, Sa'ad ya kalli plate ɗin indomien gaban shi ya sake kallon Umaimah wani tunani ya faɗo mishi da ƙarfi yace "kut, kardai ita ce br........." sai kuma ya rufe bakin shi da sauri, Daddy ya kalle shi "kasan wanda ya ɗauka ne?" Da sauri ya hau girgiza kai, Mami ta kafe shi da ido yayi sauri ya dauke kai. Aliyu falon ya bari sabo da takaici, Khadijah na zaune duk wannan rigimar da ake yi ta tafasa bata ce ba. Da kyar da siɗin goshi Daddy da Baba suka lallaɓa Umaimah tayi shiru, amma tana ta ajiyar zuciya dan ba kaɗan ba tasha kuka, Daddy ya tambaye ta ta faɗi duk abin da take so yasa a siyo mata, taƙi faɗar abin da take so dan ita indai ba indomien ta za'a dawo mata da ita ba to ba'a biya taba. Daddy ya tashi Ibrahim da Sa'ad yace maza suje su nemo mata abinda zata ci, a kan cinyar Daddy ta ɗora kanta kamar mai bacci tayi shiru, su Amira ma duk basu ji dadin abinda ya faru ba saboda su kansu sheda ne tin a Lagos take practical ɗin yadda zatayi dahuwar indomien gaskiya duk ma wanda ya ɗauke mata bai kyauta ba. 💫 UMAYMAH 💫 ✍️A&A PEN Follow our Whatsapp group via this link https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3 https://wa.me/+2348039352724 VOLUME ONE EPISODE 5️⃣2️⃣ Ismael ya matso kusa da Umaimah yayi mata raɗa a kunne ba shiri ta mike, "da gaske kake" ya gyaɗa mata kai bata yi wata wata ba ta mike ya rufa mata baya Daddy yana shikenan Amaryar kin huce? Baba ya girgiza Kai "uwata da rigima, ta zama yammata tana shirme." Daddy yace wa Baba "Muhammad ina ta wani girma, ajin su nawa ne yanzu? "ss1 za su shiga" "ikon Allah lokaci baya jira. Daddy ya cewa Baba "gaskiya Muhammadu yakamata fah mu nemi uban yarinyar nan ya kamata ya san da zamanta, idan ta ƙara girma dole zata nemi sanin mahaifinta." "Hmmm ai harta fara sai da nayi mata babu daɗi sannan muka shirya." "ka gani ko Muhammad." Daddy ya faɗa, "kar gaba ta kullace mu fa, duk lalacewarshi duk yadda muke ganin ya ɓata mana dole dai shi ne ubanta, ko saboda aurenta idan ya taso dole muna bukatar sa." Baba ya ja fasali yace "haka ne mu gama da batun uwarta tukunna ma waiwayi wannan daga baya." Baba ya faɗi hakan ne kawai dan kar Daddy ya jaa maganar amma bayajin har abada zai iya neman Tahir. Suna hira aka ƙwalla kiran sallar Azahar su ka miƙe. "Allah Uncle Ismah" bakin ta yaƙi rufuwa, "toh zauna mana." Isma'il ya faɗa yana kallon yadda ta riƙe kuɗin, "ya zan zauna waɗannan mazajen kuɗi haka." Sai ta daga hannu sama "Allah nagode maka, toh amma ya zamu yi da Nafdac ɗin?" tayi zaman dirshan ta fara kirga kuɗin sai ta gama ta kara tisawa, tun abun yana burge Ismael har ya fara gajiya da halin ta, yace "Dan Allah ya isa haka, yanzu dai kin ji yarda muka yi da su, idan kina so su karɓa sai an yi Nafdac, kuma gaskiya kuɗin da tsada, idan kuma da ribar za a yi toh ki yi shawara." Da sauri ta tari numfashin shi "Uncle Ismah shawara idan ta wuce ka ai babu sirri, toh yanzu dai ya za a yi? sai kuma tace "bana son na nemi taimako mutum yayi tunanin ya saka wani abu yana da wani percentage a business ɗin nan." Ismael har zai shiga toilet ya juyo yace "kamar yaya." "toh Uncle Ismah idan na nemi taimako ba sai ka ji ana ƙoƙarin yi maka iko da dukiya ba? Ta kafe shi da ido "eh haka ne." ya faɗa yana murmushi, "Dan ni tsakani na da Allah idan ba kai ba duk wanda yaci kuɗin nan laaa shakka zan mishi fatalwa." Umaimah ta faɗa hankalin ta kwance, Isma'il ya girgiza kai "Allah ya sauwaƙe miki Umaimah sai ana maganar arziki da ke ki kawo shirme." Ta katse shi da cewa "Yauwa uncle Isma na samu idea." ya dawo ya zauna "ina jin ki." "bashin banki zan nema idan na samu ribar na mayar musu da kuɗin su, shikenan asiri ya rufu." Ismael ya kalle ta a ran shi yana mamakin wauta irinta Umaimah, amma bari yayi mata wayo, kamar da gaske yace "hakan yayi sai ki yi wa ya Aliyu magana tunda a bank yake ina zamu tafi yawon neman rance banki ga shi a gida." tayi shiru "ina tsoron Allah ina tsoron ɗan uwanka ba shi da daɗi." "Ah to ni sauƙi na nema miki." "toh shikenan amma kai zaka tambaya mana shi ko?" ya harare ta, ta yi dariya, Isma'il ya ce "ki faɗawa Baba sai ya yi mishi magana." "Excellent idea" ta yi mishi jinjina, "Rayuwa babu Uncle Ismah ai lami ce." "see you mai daɗin baki, ni an kira sallah kin tsare ni da surutu." yayi maganar yana shiga toilet ita ma ta mike ta fita. ****** Khadija na idar da sallah wayarta ta yi kara ta ɗauka ta gane number Ahmad ce, bata yi saving number ba amma ta gane ta, ta ɗaga da sallama, yace "Ranki ya daɗe." Murmushi ta yi "an yini lafiya? "Lafiya ƙalau Alhamdulillah." ya bata amsa, "yaushe za ku tafi ne? ina tunanin zuwa mu yi sallama." Khadijah ta buɗe baki kamar yana ganin ta "Allah da ka yi zamanka ba sai kazo ba, akwai wahala kana ta zirga zirga." Tana jin sautin murmushin sa "Ah ah duk inda iyalinka suke ai babu wahala." Khadija ta sauke ajiyar zuciya ta ce "tafiyar ta mu jibi ne fa." "jibi" ya maimaita "kash amma ban so haka ba, zamu je retreat Abuja bazai yiwu nazo kafin tafiyar ba, ba ki kyauta min ba naso na ƙara ganin ki kafin ku tafi amma babu komai." ta yi murmushi "kamar yau ne ai ba ɗaɗewa zamu yi ba." "haka kika ce, na kira Munniran mun gaisa tana da kirki nasan zata kular min da ke Please banda shiga turmutsutsu wajen ɗawafi." Khadijah tayi murmushi "In sha Allahu." "sannan ayi mana addua." "in sha Allahu" ta ƙara faɗa, "toh bari na bar ki haka." har zai ajiye wayar yace "Dear har yau ba ki haɗa ni da ƴa ta mun gaisa ba." Khadijah tayi ƙasa dakai "yanzu bama tare amma in sha Allahu zan haɗa ku." Suka yi sallama ta ajiye wayar ta na ajiyewa ta ga text biyu sun shigo ta buɗe na farko alert ne daga Ahmad dayan kuma text ne ta buɗe ta karanta Dear babu yawa umara mabroor. Khadijah ta ji daɗin kyautar dan Bahaushe ya ce sadakin so kyauta, amma ina ya samu account number ɗin ta, kodayake ya ce mata sunyi waya da Munnirah definitely tasan ita ta bashi, kamar mai jira kiran Munnirah ya shigo ta ɗaga "my sis ya shirye shirye." Munnirah ta faɗa daga bangaren ta, "wlh ni ban haɗa komai ba." Khadijah ta bata amsa, "yaushe zaki shigo ki taya ni nawa shirin? "Gobe zan shigo in sha Allah dama Ahmad ya bamu kuɗin guzuri ke kika bashi account number na? "Ni na bashi gaskiya yana da kirki duk Friday sai yayi min text." Munnirah ta hau guɗa tana dariya khadija ta katse kiran tasan tsokana ce zata biyo baya. Gabadaya family biyu suna zauna a falon Baba za a yi dinner, Fahad ne kawai baya nan ya fita a motar Aliyu tin dazu sai su Amira da Umma ta cewa Umaimah ta je ta kira su a daki, bata jima ba sai gata ta dawo da Sasi a hannu Mami ta kalli Umaimah tace "suna ina? "Wlh Mami ina ta kiran su sun yi min banza." "shi kenan cikin su ne ai." Mami ta faɗa, Umma tace "ko kwalliyar su ke yi? Amira dama gwana ce kamar me yar kwalliya." Umaimah ta yi dariya, Daddy yace wa Umaimah "zo ki ci abinci ga saƙon ki ma " Umaimah ta girgiza kai "hmmm Daddy ba na jin yunwa." Baba ya kalle ta kowa ya san Umaimah da Abinci kuma ga rikicin indomien ɗazu "me kika Ci? Umma ta tambaya, "wlh Siyama daɗi da farin ciki ne kawai ya cika min ciki." Babangida yayi tsaki ciki ciki Sa'ad ya kalle shi "ya dai bro? "babu komai." Ya faɗa, "Baba da Daddy ku kammala saina faɗa muku kar daɗi ya hana ku cin abinci." Daddy ya ce "to uwata." Ta koma gefe sai wasa suke yi da Sasi tace je kira su Amira, abun mamaki sai kawai Sasi ta yi sama da gudu ba jimawa sai gata ta dawo ba a cika 3min ba sai ga su Amira sun sauko, mamaki ya cika su. Daddy yace "lallai magen ta ki na jin magana." Hidaya ta ce "a bakin ƙofa ta yi ta kuka sai da muka fito.." Sa'ad yayi murmushi, "ko za a bani ina son mage?" "Ah ah ka bari idan ta haihu na baka wannan baby na ce." "baby Sasi." Sa'ad ya faɗa yana dariya, daddy ne ya dawo da hankalin su gare shi yace da Umaimah "mun kammala zo ki faɗa mana farin cikin da ya hana ki cin abinci." ta matsa kusa da Daddy da sauri "yi a hankali ni zaki taka ni." Umma ta janye kafarta. Baba da Daddy suka mayar da hankalinsu kan ta ta ce "Uncle Ismah ɗauko su Daddy su ga dahir, kar a ɗauke mu da wasa." kamar remote control Isma'il ya miƙe, Aliyu sai harararshi yaa ke, ya ɗauke kai, Sa'ad yana ta dariya shi son shirmen ta ya ke yi ko ba komai kana tare da ita ba ka da takaici, Isma'il bai jima ba sai gaa shi da abu a leda, ya miƙawa Umaima ta karɓa ta buɗewa su Daddy, Daddy ya kama baki "kai kai kai a ina kika samu kudi haka? "riba ce" "riba ce? Daddy ya maimaita maganar "ah ah Amaryar ai kin fini kuɗi ma, shikenan na zama mijin Hajiya." Umaimah tayi murmushin jin daɗi tace " Owonikoko (Kuɗi sune komai), wlh kuma kai ɗan gatan Hajiya ne Daddy." Daddy ya kwashe da dariya yace "lallai Amaryar kinsha Lagos harda yarabanci." Mami ta ce "an fah sani a duhu za a kwace min miji da daren nan." "Darsha sai dai haƙuri ni na auru a nan." Baba yayi dariya, maganar ta ce ta katse su "taimako na ke nema Daddy." Daddy ya gyara zama "wanne irin taimako? Faɗi ko meye zan miki naga fah da gaske kike yi." "Da gaske na ke Daddy so nake a ce na fi kowa kuɗi a masu shekaruna a Kano, na yiwa sa'o'ina fintinkau da kuɗi da ilimi." " A Bichi dai ba Kano ba." Amira ta faɗa, "ta dai fi ku ba ku iya komai ba sai kwalliya." Daddy ya faɗa yana kallon Umaimah "ina jin ki me kike so? "Daddy bashin banki na ke so." Daddy ya gyara zaman glass ɗin idon shi ya kalli Umaimah da kyau, ta cigaba da cewa "Barakat store ne za su karɓi gullisuwa da alawar madara amma sun ce sai na yi Nafdac sabida babban waje ne, idan zan yi gaskiya zai girgiza jari na." Ran Aliyu ya ɓaci ya miƙe zai fita, "dawo ka zauna." Baba ya faɗa yana kallon sa. Khadijah ta yi shiru tana kallon ikon Allah, jini fa ba ƙarya bane Umaimah ta fara bata mamaki exactly haka ubanta yake da zafin nama da jajircewa wajan nema, akan harkar kasuwanci sam Tahir bashi da wasa, a tsaye yake da ƙafafun shi duk yadda zai juya biyar ta zama goma ya sani. Daddy ya ce "ina proposal ɗin loan ɗin." "me kenan? Umaimah ta tambaya, "haka ake bada loan ɗin babu bayanin kasuwancin naki? bayanin ribar da kike samu? da yaushe za ki mayar musu da kuɗin su, dole kuma zaki basu wani abu duk sai an yi yarjejeniya, sannan zaki bayar da guarantor ko da wani abu zai faru idan wa'adin da aka baki ya cika dole a nemo guarantor ɗin ki tunda shi ya tsaya miki." Umaimah ta zare ido "abun da wuya ashe." Baba yana mata dariya yace "ko manager zaki bayar a guarantor?" Umaima ta girgiza kai "ah ah sai dai na bada Siyama idan wani abu ya faru Daddy zaku karɓo ta." Sa'ad saboda dariya har da hawaye, Daddy da Baba daria kawai su ke yi, Umma tace "sai dai ki bada uwarki khadija, ni kika raina ga Baba nan ga kowa saini kika gani." ta zumɓura baki gaba, Daddy yace wa Aliyu "toh Babangida ai harkar ku ce, ta ina zata fara? Aliyu yayi yaƙe kawai be ce komai ba, Daddy ya cewa Umaimah "Amaryar kar ki damu ga Iyayen ki nan." ya nuna su Sa'ad ya fuskance su ya ce "ayiwa uwata registration ɗin duk abunda ya kama na kuɗi zan biya." "ah ah Daddy nizan mata." Sa'ad ya faɗa, "toh shikenan mu na godiya, dan naga alama wata rana ita Zata rike mu." Da sauri Umaimah tace "wlh Daddy in sha Allahu." Aliyu ya harare ta, daɗi ya cikata tace "Baba Daddy, Siyama da Mami a taya ni godiya, Uncle Isma. ta tafi da gudu ta rungume shi suka yi dariya. 💫 UMAYMAH💫 ✍️A&A PEN Follow our Whatsapp group via this link https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3 https://wa.me/+2348039352724 VOLUME ONE EPISODE 5️⃣3️⃣ Daddy ya ɗaga wayar Dada da sallama, "barka da dare Dada." Ta amsa da "yawwa, ta hau Daddy da faɗa "ibrahim Dattijo ya zo amma zuwan nashi ba shi da amfani gara ma be zo ba, idan wannan zuwan zai yi kar ya ƙara zuwa, mutum sai baƙin hali ya zo ya yi min kinkirin yana bude baki da kyar kamar an mishi dole, ni dama Sa'adu ne na waje na, wannan halin na shi kaf zuriyar mu babu me irin shi." , Daddy yace "ayi haƙuri Dada, dan uwan ma shi yayi ta jira su taho tare ashe shi har ya zo." "hmmm ka ji mugun halin ba, ya sha fura saboda iyayi sai ya kalli kofi ya kalle ni, haka na yi ta jelen wanke masa kofi, gaskiya na yarda wannan abun nashi ba ƙalau ba, shi da jikar Maryama dole a nema musu magani, kamar an tsikare shi ya tashi zai tafi ba yarda mai gida be yi dashi ba yaƙi tsayawa, ka fada mishi idan da gangan yaƙi tsayawa ayi maganar aure to ya shirya dole ya fito da mata ko na zaba musu ga zuwaira nan ta gama sakandare me ake jira." "Za a gyara Dada in sha Allah." Daddy ya faɗa, ta ja fasali tace "ahto ka ja mishi kunne sai anjima." "mu kwana lfy." Dada ta ajiye wayar, Daddy ya daɗe da waya a hannu yana jinjina hali irin na Fahad "Allah ya sauwake." A gajiye ya shigo gidan tun La'asar ya fita ,ya je wellcare siyan maganin shi, ya biya ta gusto ya sha coffee, ya daɗe a wajen, sai wajen magrib ya baro gusto a hanya aka kira sallah ya tsaya a masallacin Al furqan yayi magrib da isha sannan ya taho gida direct chalet din su Aliyu ya wuce ya wanke Toilet yayi wanka ya fito kenan Sa'ad ya shigo da sallama ya amsa mishi, Fahad duk rashin son maganar shi yana amsa sallama. Ya shigo ya zauna a kan kujera, "guy where have you been? tun ɗazu nake ta kiran ka a waya shiru?" bai saka ran zai amsa shi ba ya cigaba da magana, "yakamata mu je Bichi kafin tsohuwar nan ta waiwaye mu fa, Daddy ya ce na neme ka mu yi magana, ya kamata mu je kafin mu koma Lagos, dan ni ba na jin Lagos za ni, daga nan pothacourt zan wuce Yaya Surayya ta ce na kai mata credentials ɗina na ma tura mata da soft copy ɗin, kasan mai gidan ta babban mutum ne akwai connections, mun yi waya yace na yi ƙoƙari na je, yanzu kai nake jira yaushe zamu Bichi?" Yayi shiru yana kallon Fahad daya daga fararen kayan baccin shi sai fesa musu turare yake yi, Sa'ad yace "ya isa haka ai sai kayi mura." be kula shi ba ya shiga toilet ya fito ya bude box ɗin shi ya canja bedsheets white colour dama wanda ya cire ma shi ya saka, in dai ya zo Aliyu bar mishi ɗakin ya ke yi sai ya tafi, Sa'ad ya tsaya yana kallon shi ya shimfida bedsheets yayi kyau kamar mace, ya sake shiga toilet ya fito ya kabbara sallah duk Sa'ad ya na zaune, dan ma waya su ke yi da Farida tun da Fahad ya shiga Toilet kiranta ya shigo wayar shi, sai jin muryar Fahad yayi yana cewa "I need space pls." Sa'ad ya yi wa Farida sallama ya kalli shi "wato ga dan zaman banza ko tun dazu ina ta faman zuba abunda zaka ce min kenan, toh wlh idan baka faɗa ba anan zan kwana." ya gyara kwanciya a kan kujerar, Fahad ya kalle shi "na

Chapter 26 of 29