Share this page
office ɗin. Sa'ad yana ganin shi ya fito ya nufe shi da sauri yace "Guy how far? ya kuka yi?" Fahad ya yi mishi banza kamar ba zai amsa ba sai kuma, ya ce "he changed medication for me?" "wanne ya ba ka? be kalle shi ba kawai sai ya miƙa mishi takardar. Sa'ad yace "bari na karɓo maganin a pharmacy, you wait for me here." ya tafi siyo maganin. ya karɓo maganin ya dawo ya nemi Fahad ya rasa, ya kira wayar shi tana ringing no response, ya san halin kayan shi sarai, tafiyar shi yayi ya barshi ke nan. "Allah ya yaye maka Fahad." Sa'ad ya faɗa yana girgiza kai, ya kira bolt, ya wuce gida. Sa'ad na hanya kiran Daddy ya shigo wayar shi, ya ɗaga wayar da sallama "Daddy barka da lokaci." "Barka dai Sa'ad ya preparations ɗin dawowa gida? "Alhamdulillah Daddy mun kammala komai dama Fahad nake jira ya gama project ɗin shi, shima kuma Alhamdulillah ya kammala, kuma mun je ya ga doctor har ya canja mishi medication." Daddy yace "Masha Allah that's development his improving, yanzu when are we expecting you?" "sai na tambayi Fahad tukun." "Okay yayi, you let me know idan kun yi fixing date ɗin, kaci gaba da hakuri da ɗan uwanka." Daddy ya faɗa. "in sha Allah Daddy." suka yi sallama. ******* Dawowarta kenan, ta fito daga wanka ta ji ringing ɗin wayarta, ta je ta ɗauka, Munnirah ce "Amrya ba kya laifi. " "wlh sis ki fita a ido na. Khadijah ta faɗa, "oh rashin kunya za ki yi min ina Umman ki? shikenan kin yi wa kan ki, dama Albishir zan miki kika gwale ni, Khadijah tayi dariya tace "yi hakuri my sis Allah ya sa u re pregnant?" Munnirah tace "a'a ba shi ba ne, kawo tukwuici na faɗa miki. "pls my sis kina ja min rai." "Dr ya biya mana Umara ni da ke, kafin ki Amarce." "Allahu Akbar." Khadijah ta yi kabbara, har ta yi waje ta dawo ta tuna towel ne a jikinta, "my sis da gaske? "zan miki wasa ne. Allah ya saka mishi da alkhairi, ya ba ku zuria dayyiba, ya bar ku tare." Munnirah ta amsa da "amin my sis, bari zan kira ki." ta katse wayar ta nemi doguwar riga ta saka, ta yi ƙasa wajen umma. ***** Daddy ne da Mami a zaune suna hira, Daddy yace "su Dattijo suna hanya next week Friday." Mami tace "in less than a week kenan, Allah ya kaimu. "ina yaran nan ne? na ji gidan shiru?" "Umaimah an kai ta surulere shagon Tailor ta madam Sara, da gaske tana da passion a ɗinki, su Hidaya kuma suna gidan Amal can suka yini, nace da pilot idan ya ɗauko Umaimah sai ya biya ya ɗauko su hidayan su taho gaba ɗaya." Daddy yayi dariya yace "uwata kenan Muhammad ya bani labarin sana'ar tuwon Madara take yi, yace an mi shi kyauta an kwace, wai dogaro da kai zata yi." Daddy ya faɗa yana dariya, Mami tace "nan ta fada min wai an yi mata cikas bata ko yi ɗinki ba, shine na ce ba za a yi haka ba, ga shi ta kusa sati da fara zuwa, madam Sara ta kira ni da kanta ta ce min Umaimah tana ganewa sosai." wayar Mami ta yi ringing ta ɗaga da sallama suka gaisa da Umma, Mami tana wa Umma dariya tace "lafiya ƙalau ba sa nan." Daddy ya ga ne Umma ce ,yace bani wayar Mami ta miƙa mishi suka gaisa da Umma, "wlh Maryama ki kiyaye ni, tun da yaran nan suka zo kin dame mu da waya, wlh idan kika matsa zan riƙe su gaba ɗaya na ga ta tsiya, kullum kika kira uwata ta yi ta kunci kenan." Umma tace "wlh Yaya ba ni nake neman su ba Hakimi ne zai yiwa Umaimah magana." "ba wani nan ke dai kulafucin uwata kike yi." Daddy ya faɗa, Umma tace "Ayi hakuri Yaya." "ah to ki ce Hakimin ni ya kira ni anjima zan haɗa su." "toh sai anjima Yaya. "Mu jima da yawa." ya katse wayar, Mami tace "ya za kayi haka Daddy? Rabu da ita bata da kawaici akan uwata kamar ba bafulatana ba. 💫 UMAYMAH 💫 ✍️A&A PEN Follow our Whatsapp group via this link https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3 https://wa.me/+2348039352724 VOLUME ONE EPISODE 3️⃣0️⃣ Umma ta ajiye wayar, da gaske kewar Umaimah ta ke yi, su Babangida ba ma zauna ba ne, idan sun dawo ma suna chalet ɗin su, Hakimi kuma yanzu ba ya son zama a gida saboda ba abokan fira. Khadijah kwanan nan ita ma kullum a gajiye ta ke dawowa suna gaisawa take haye wa sama, ga shi Baba baya nan, gaba ɗaya gidan sai take jinshi wani iri babu daɗi, yanzu ma kawai dai tace Hakimi ne yake neman ta, amma Hakimi baya nan daga ita sai Baba Rabi suke kaiwa da kawowa a gidan, kawai ta so ta ji muryar Umaimah ne shi yasa tace Hakimi ke neman ta, Umma na cikin tunanin Isma'il ya shigo falon da Sallama, ta kalle shi, "Hakimi ka ko yi yawo ko? yaushe rabo na da kai ? Tun safe." Yaɗan sosa kai "sannu da gida umma, na je gidan su Abbas ne." "eh naga alama duk ranar da Babangida ya ritsa ka akan yawon nan ba za ka ji daɗi ba." "Umma to zaman gida sai mata. "haka kace" Uncle Isma yayi dariya, yace "toh Umma Allah gidan babu daɗi yanzu, yaushe za su dawo ne?" "Ka tambayi Babangida sarkin gida shi zai faɗa maka, amma hutun ya kusa ƙarewa dole su dawo." "ina son yi wa Umaimah magana. "ka kira Daddy ku zai haɗa ku. Umma ta faɗa Isma'ill yace "toh Umma ara min wayar ki? don shi ma Baba ya ce sai ya gama secondary zai riƙe waya, yawanci ko assessment ne dashi sai dai yayi a wayar Umma kota Yaya Khadija. Suna cikin haka, Khadija ta sauko da sauri ta nufi Umma fuskar ta cike da fara'a, tace "Umma Baba Dr ya biya mana Umara ni da Munnirah." Umma tayi murmushi "Masha Allah, kai Alhamdulillah, amma ya kyauta Allah ya saka mishi da alkhairi, kin kira shi kin yi godiya? "A'a Umma yanzu zan kira shi. " Khadijah ta faɗa tana danna wa Baba Dr kira. Umma tace "yawwa kira shi maxa mu yi godiya. **** Lagos Surayya wai ke kaɗai kika zo kika bar yara a gida? Mami ke tambayar babbar ƴar ta Surayya. "Mami ni kaɗai na zo ai Baban su yana tare da su ga Mariya ma tana kula da su sosai. Mami ta ce " kin yi sa'ar mai aiki." "Mami ay Mariya ƴar uwa na ɗauke ta, yarda na yi nisa da gida, tun da Dada ta nemo min ita a Bichi, sai nake jin ta kamar yar uwa ta." Suna cikin hirar Umaima ta shigo ta tafi wajen Mami, "Aunty Surayya ina kwana? "A'a yan matan Mami Ina yan uwanki." "Aunty Surayya suna bacci, Mami ki bani kaya zan ɗinka miki." Mami ta kalle da mamaki "har kin iya? "Wlh na yi mugun iyawa Mami, don ma matar akwai saka aike har shara na ke mata, amma ba komai tunda koya nake gaba ni ce da riba, Mami ta girgiza kai Umaimah na burgeta sosai gata dai yarinya goyon Kaka, amma tana da hankali da hangen nesa, inka cire wauta da ƙuruciyar ta. Mami ta ce "shi yaa sa kike burge ni Umaimah. Surayya ta ce "ni zan fara baki kayana ki ɗinka min, a fara da ni." Cikin jin daɗi Umaimah ta ce "Dan Allah Aunty? Surayya tayi murmushi "ƙwarai ku wa, zo mu je ki raka ni siyayya naga alama Amal da ke gari zata ɓata min lokaci, yakamata abubuwan da zamu yi amfani da su ace an siyo yanzu, shirya mu je." Umaimah ta amsa da "toh." Gaba ɗaya suna kitchen sun kacame da aikin tarar su Fahad, mai aikin Mami, Surayya da Amal sai chef guda ɗaya da aka yi hiring ɗin shi kawai dan yayi musu International dishes, yayi baking cake, su kuma suka yi snacks, daya ke jirgin yamma ne suna da time ɗin gama komai on time. Amal tace wa Surayya "Yaya Surry Allah yasa dai wannan abun da mu ke yi ma Fahad ya ci, kin san shi picky eater ne, idan bega dama ba duk wannan abun ba burge shi zai yi ba." "Dattijo rigima kenan, wannnan matar shi sai tayi damarar gaske, ni yanzu idan aka ritsa ni na fadi wani abu daya fi so wlh ba zan iya ba, amma Sa'ad sosai na sani." Surayya ta fada, Amal ta ce "kamar me? "Toh na san turaren shi Dior sauvage ne, in dai ba ya canja ba, na san yana san wrestling, club ɗin shi Arsenal ne and yana san polo, kuma na san irin matar daya ke son aura. Amal ta tari numfashin Surayya da cewa "my chocolate zaki ce." suka kwashe da dariya. "ay Sa'ad is free spirit, amma Dattijo Allah na tuba ko Mami bata san inda ya sa gaba ba." "hmmm Amal kira mai decoration ɗin kar lokaci ya ƙure." Jirgin British Airways da ya taso daga US, ya sauke zaratan matasan Samarin ƴaƴan Ambassador Ibrahim Isma'il Bichi a filin tashi da saukan Jirage na Murtala Muhd da ke a birnin Lagos, passengers suka fara fitowa, Sa'ad ne ya fara biyu matattakalar Jirgin hannun shi rike da trolley black colour yana sanye da brown T-shirt da baƙin wando ya dora wata doguwar riga akai, ta wuce gwuiwa, da ipad a hannu shi, Fahad na biye dashi a baya yasa white T-shirt da blue jeans ƙafar sa sanye da wani haɗaɗɗe Black Boot, ya ɗora black p-cap akan sumar kan shi da kana ganin ta kasan taci kuɗi, saboda yadda take ɗaukar ido, ya rufe fuskar shi da baƙin glass, yana jan trolley kamar baya son tafiyar haka yake sakko wa, Sa'ad yayi gaba sai kuma ya juyo ya jira shi, Sa'ad ya ci re sim ɗin shi na US ya saka na gida Nigeria ya kira Mami, "Assalamu alaikum Mami mun sauka." "Alhamdulillah welcome home my dear, bari na turo maka da number Pilot, ko kana da ita. "a'a Mami." Sa'ad ya faɗa, "okay bari na turo maka." ta kashe wayar. text ya shigo wayar sa yana duba wa yaga Mami harta turo masa number, ya kira Pilot ya faɗa musa inda yayi parking. Decoration din yayi kyau sosai daga entrance an saka welcome home Fahad & Sa'ad, falon an yi mi shi arrangement mai kyau, an yi wani abu kamar ƙofa da balloons, aka saka table daga ciki aka ɗora cake, setting ɗin kamar na biki, an saka pillows aka jera plates da spoons da fork kowanne seat drinks da abinci kala kala a tsakiya, palourn sai kamshin turaren wuta ya ke yi, an saka diffusers na turare daban daban. "sun ƙaraso Daddy." Mami ta faɗa bakin ta yaƙi rubuwa dan murna, Daddy yayi dariya yace "Darsha kin kasa zaune kin kasa tsaye, oh matar nan da son ƴaƴanta ta ke." Mami tayi dariya "shekara nawa? Daddy na yi kewar su." Su Amal sai yi wa Mami daria suke. "ina su Hidaya ki kirawo su, su fito suna can ana ta fente Fenten fuska." Yaya Surayya ta faɗa. Da Sallama Sa'ad ya shigo cikin Falon, da sauri ya nufi Daddy ya rungume shi "I'm back home Daddy." Daddy ya daki kafadar shi, "Sa'ad ka zama ƙato." Aka yi ta dariya, ya tafi wajen Mami, tace "oh sai yanzu ka ganni? har nayi fushi." ya rungumebta yana dariya aka hau murna, Fahad yana tsaye yana kallon su, gently yazo yayi hugging Daddy Muryar shi very calm yace "I hope all is well with you?" Daddy yayi murmushi yace "we are all fine Dattijo. ya je wajen Mami ya rungume ta, su Surayya suka saki Sa'ad suka zo zasu rungume shi ya dakatar da su, su ka yi dariya suna girgiza kai, sanin hali ya sa basu wani damu ba dan dama shi haka yake. Nan aka zauna ana ta hirar yaushe gamo, banda Fahad da yayi shiru kamar baya wajan, Sa'ad ya kalli Hidaya yace "a'a Auta kin zama ƙatuwa fah." ta yi dariya "Yaya ss1 fah zan shiga." yace " that is nice, ya kalli Amira be gane ta ba, Mami tace "Amira ce ƙanwarka." sai da kwakwalwarshi ta yi caji sannan ya ce "Amira Autar Umman Kano right?." Mami tace "Ashe ka gane ta." "wow,wow,wow gaskiya yaran nan sun girma, me ku ke ci haka? Amira ta yi dariya, Daddy yace "wai ina uwata ne? "tana hanya ta kusa dawowa." Mami ta faɗa, shi dai Fahad kamar baya wajen suna ta hira, Daddy ne ma yake sako shi, jefi jefi ya ke amsawa da eh ko a'a ɗin daya saba. A ranshi kuwa wannan hirar ta su ta ishe shi, a takure yake. Ya miƙe "let me freshen up." Mami ta ce "Sa'ad ku je ku huta, ku zo sisters ɗin ku tun safe ba su huta ba suna ta aikin tarar ku." "eh wlh na gani decorations ɗin yayi kyau, thank you sisters. Sa'ad ya faɗa yana miƙe wa shima." Bayan sun huta aka haɗu a dining, Surayya ce ta fara serving Daddy da Mami, ta cewa Sa'ad "me za ka ci? Ya kalli dining ɗin "ay komai za ki zuba min, na yi missing abincin gida." tayi dariya, Amal ta ce "Sa'ad ba dai ci ba." kowa ya zauna a position ɗin shi, Daddy ya cewa Mami "kira pilot har yanzu basu iso ba, uwata bata dawo ba, ga mutanen ta sai wanda ta zaɓa." Mami tayi dariya "jiya ay ina jin su da Deborah, tana cewa Deborah u no sabi cook." Daddy yayi dariya, Mami tace "wai fa saboda ta yi eba." Amal ta ce "da gaskiyar ta nima ba na son Eba." "ƙarshe dai sai indomie ta dafa." Hidaya ta ce "wai Umaimah akwai cin abinci." Daddy yayi murmushi "tubarakallah gashi ita ce karama ta fi ku kyan gani, ina Dattijo ne? Hidaya je ki kirawo shi. Hidaya ta miƙe, tayi kamar 10 minutes ta dawo "yace yana zuwa." Tana rufe baki ya shigo da sallama, aka amsa mi shi "let me serve you." Surayya na ƙoƙarin yin serving ɗin shi ya ce ta bari, ta dawo ta zauna, ya jawo plate ya juya shi yana kallon plate ɗin sai kuma ya juya yayi kitchen bai jima ba ya fito hannusa da ruwa, plate ɗin yaje ya sake wanke wa, babu wanda yayi magana yazo ya zuba abunda ya yake so, kamar na yaro ƙarami, ya tafi can gefe ya zauna, yadda in mutum yanzu ya shigo ba lalle ya kula da mutum a wajen ba. Babu wanda yace masa komai dan duk sunsa halin shi. Umaima ta shigo falon da sallama ta taho da sauri, tace "Amma dai an ci da rabo na." Daddy yace "tun ɗazu na ke jajenki." Sa'ad ya kalle ta, yana dariya yana tunanin wacece wannan, Mami tace "ƴar wajen Khadijah ce." Sa'ad ya buɗe baki cike da mamakin girman ta. Tana shigowa ta cika falon da surutu, "zo ki zauna." Sa'ad ya matsa mata, ta ɗauki plate, "kai wannan plate ɗin ya min kaɗan." Daddy ya ce "idan kika ci sai ki ƙara." "kaaai Umaimah" Hidaya ta riƙe baki ganin yarda ta ciko plate, "ci abinda kike so uwata, ina ruwan ki ne Hidaya? Daddy ya faɗa. Umaimah ka wai kaiwa ta ke yi. Sa'ad dai kallonta ya ke yi yana gulmarta a ran shi, amma ta burge shi babu ruwanta. Sai da ta kammala ta cewa Mami "Mami gaskiya Daddy ya kamata ya ƙara yi miki sabon lefe." "saboda me? Daddy ya tambaya. "Toh Daddy wannan abinci kamar a villah, wlh yayi daɗi. Sai lokacin Fahad ya ɗago kai ya kalle ta, sanye take da wando palazo pink color sai rigar wandon white color mai dogon hannu ta sauka har gwiwar ta, kanta babu ɗan kwali saita ɗora veil baby pink akanta, kana iya ganin gaban sumar kanta yadda ta kwanta tayi luf exactly irin na yaran Larabawa, fuskar ta babu makeup ko kaɗan amma tayi kyau sosai. tun shigowar ta ta cika wajen da surutu very noisy girl, ya mayar da kan shi ya cigaba da cin abincin shi. Mami ta ce "Allah ya yi miki Albarka Umaimah, toh ka dai ji ranka ya daɗe kishiya ma ta yaba." Amal ta ce "Umaimah mu ne fa muka yi girkin ba Mami ba." Mami ta harari Amal aka yi dariya. Umaimah tace "Allah idan aka yi miki lefe tsab zan miki ɗinki." Daddy ya ce "don ki yi ɗinki zan sa ke lefen gaskiya." Sai kuma tace "Au na manta ta miƙe ta bar wajan, bata daɗe ba ta dawo da leda a hannunta ta miƙawa Surayya, Surayya ta buɗe ledar bubu ce an saka mata manyan buttons daga sama har kasa, rigar ta material ce orange colour yayi kyau sosai. "wow" cewar Surayya "bari ma na canja." ta tashi, bata fi 5 minutes ba ta dawo, kayan sun yi mata kyau sosai, "ah masha Allah." Daddy ya faɗa, "uwata ta zama Tailor." Sa'ad ya kalle ta, "ki na dinkin maza? Tayi dariya "koyo fah na ke yi, ta kara kallon shi "kai ne dama brothern Hidaya? Ya aka yi na manta ka? Sa'ad Yayi dariya "Saboda ina makaranta ne, kuma mun daɗe ba ma nan, I guess lokacin da muka tafi kina ƙarama sosai." Umaimah ta ce "gaskiya ka fi su kyau, kai fari ne su baƙaƙe." aka kwashe da dariya, Amal ta ce "Dan fari ne shine ya fimu kyau? ba wani kyau daya fimu, kalle ni fah Umaimah." Fahad ya ƙara kallon ta for the second time yayi tsaki. "toh ko dai da shi za a yi ne, shikenan tuwo na mai na. Daddy ya faɗa, Umaimah ta ce "me za a yi dashi." "Aure mana." "Aure" ta faɗa tana rufe fuska, toh ay ni yarinya ce, ba don haka ba dana aure ka Uncle Sa'ad." Sa'ad dariya har da ƙwarewa sai da ya sha ruwa,.kowa yana ta dariya, sai yanzu hankalin ta ya kai kan zoɓo, tace "kut ashe an yi zoɓo." Ta tashi ta ɗebo zoɓon ƙafarta ta bugi kujerar dining tayi gaba kamar data faɗi ta saki zoɓon da glass cup ɗin hannun ta basu faɗa a ko'ina ba sai kan white shirt din Fahad, ya tashi a fusace ya ɗaga hannu zai mare ta "you are very stupid." "don't you dare slap her." muryar Daddy ta katse shi, jikin shi har tsuma ya ke yi kamar mazari saboda ɓacin rai, ita kuma ta runtse ido tana jiran taji saukar mari, Fahad ya ɗauki phones ɗin shi ya bar falon da sauri. 💫 UMAYMAH 💫 ✍A&A PEN FOLLOW OUR WHATSAPP GROUP VIA THIS LINKhttps://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3 https://wa.me/+2348039352724 VOLUME ONE EPISODE 3️⃣1️⃣ Da sauri ya shiga ɗaki, kana ganin fuskarshi kasan yana cikin ɓacin rai, wayoyin shi ya ajiye ya shiga toilet, ya daɗe aciki toilet ɗin kafin ya fito ɗaure da towel ya zauna a kan kujera ya dafe kan shi, kamar an mintsine shi ya ƙara komawa toilet, ya fito ya zauna ya ƙara tashi ya koma, yayi haka ya kai sau uku, ran shi kawai a ɓace ya ke, "damn it, damn it, dammn oh God." ya yarfe hannu, that small clown oh God ya dafe kan shi, she ruined my day, this is bullshit." haushin da ya ji Daddy ya hana ya mare ta "who is she Rubbish! Rubbish!!Rubbish!!!." mtsw yayi tsaki ya buɗe balcony ya shiga ya samu kujera ya zauna ya rufe idon shi kamar mai bacci. ***** Sallamar malam Idi ce ta katse musu hira, suka amsa, yace Barkan ku da gida. "barka kadai malam Idi." Ibrahim ya faɗa. Dama Ummina (Khadijah) ce ta yi baƙo yace na sana'ar da iso warsa." "toh toh bari a faɗa mata." Umma ta faɗa tana miƙe wa, tace "Hakimi je ka shigo da shi babban falo." ya amsa da toh. Umma ta hau sama ɗakin khadija. Tana shiga ta tarar da ita tana kwance tana bacci, Umma ta tashe ta "a'a ko baki san da Zuwan shi ba ne? Umma ta tambaye ta. Ta tashi zaune tana murza ido, Umma tace "haba Yayarsu kamar me baccin dare, wai bai faɗa miki zai zo ba

Chapter 16 of 29