yana tsauri, Muryar Baba ta katse Umma.
"me uwata tayi ne aka saka ta ɗaukan buhu? Aliyu yace "Baba fita ta yi ba izini ta taho da mage, ta roƙo mangoro. magen kamar ta ji ana maganar ta ta fara meow meow.
"Ikon Allah duk ita kaɗai." Baba ya faɗa. "wanne irin buhu kuma ni Maryama? Baba yace "ah ah ba buhun da kike tunani ba ƙarami ne wannan." Umma tace "duk da haka, ay sai kirjinta ya bude, me ye a buhun? Babangida yace "mangoro ne."
Baba ya katse su da cewa "toh a yi haƙuri da uwata yarinya ce sai a na nusasshe da ita cikin hikima, shi yaro sai da rarrashi ake nuna mishi kuskure ba da tursasawa ba, wani hukuncin na maza ne a dai dinga hak'uri, yau dana je makarantar su im impressed sosai da performance ɗinta, har Auta ma dukkan su suna kokari, kaga shaida duk shiriritar nan zata daina kuruciyace kawai, Babangida Baban kowa." Baba ya fada yana murmushi dan yayi cheering din shi ganin yarda ya haɗa rai.
Still Baba na masa murmushi yace "Tashi ka je Allah ya yi maka albarka." Uncle Aliyu ya musu sallama ya fita. yana fita ya kira Baba Idi da hanzarin shi ya zo yace "gani Alhaji ƙarami."
"Ɗauki Mangoron nan ka rabawa almajirai. ya yi hanyar chalet ɗin su.
Baba ya kalli Umma da ta bata rai yace "to sa ki ran ki, na taɓa ganin don an yiwa kishiya hukunci ki din ga fushi." Baba yayi maganar yana murmushi. Umma ta ce "wlh na ɗauka wani aiki ya saka su dana tambayi Auta tace suna tare da Hakimi, nan yaran nan suka zo naga ta shigo tana ta kokawar kama mage ashe ritsa su yayi." Baba yace "abinda zan faɗa miki idan Babba yayi hukunci a gaban yara ki daina nuna mishi yayi ba daidai ba, sai raini ya shiga tsakanin su."
"haka ne, za
a gyara in sha Allahu." Baba yace "yawwa Siyama ta ko kefa." Umma tayi dariya tace "Au kaima."
*****
Khadijah ce ta fito daga ɗin ta cikin shigar ta ta kamala as usual tace "Hamisu ina su Dauda?" Wanda ta kira da Hamisun yace " Hajiya ya tafi karɓo saƙon jiya a tasha, Isiyaku kuma ya je service din keke." Khadija ta amsa da "ok zan fita, gobe ba zan samu shigowa ba zan ɗan yi tafiya, ina ganin sai ranar monday, Dan Allah ku mayar da hankali, ayyukan mutane a kula dasu dan Allah, yanzu ɗauko min wancan keken da ba a cika aiki da shi ba ka samun shi a mota." ta miƙa mishi mukullin mota, "nima dole zan rage wasu ayyukan a gida, bari na harhaɗo kayan da za a zo karba, dan Allah ku kula bana son asamu wata matsala." Hamisu ya amsa da "in sha Allahu Hajiya za'a kula."
Nasara Bedsheets ne a jakar su, irin masu pillows da American cotton duka suna ɗinkawa a DIJAH COLLECTION, su na ɗinka Bedsheets ne da curtains na gida dana offices irin kyan da ayyukan nasu ya ke da shi yasa mutane ke tururuwar basu aiki, da a gida ta fara kaɗan kaɗan kafin Baban Lagos ya buɗe mata shago anan zoo road, da yake interior decoration ta karanta saita zaɓi inda take so ka ƙware akai, Khadijah ɗinkin curtains da Bedsheets ta take yi, sai daga baya kuma mutane saboda jin daɗin services ɗin ta suka fara tambayar basa ɗinkin Amare, saboda yawan tambayar ta da mutane keyi yasa ta yanke shawarar ta gwada.
Ibrahim ne yayi wa wani abokin shi Kamal ɗan Fage magana da yake gidan su duk teloli ne kuma kwararru ne sosai suna ɗinkin Manyan mutane da yan siyasa (Fage unguwa ce da ta yi fice sosai a harkar dinki a Kano) akwai masu ɗinkin maza akwai masu yin na mata, kamal yace wanda zai yi wannan aikin sai Hamisu dan har celebrities yake yiwa dinki yasan ɗin ki sosai. Dan haka kai tsaye Ibrahim ya haɗa Khadijah da Hamisu, a hankali suka fara bridal outfit kamar da wasa Allah ya sakawa abun albarka.
*****
💫 UMAYMAH 💫
✍️A&A PEN
FOLLOW OUR WHATSAPP GROUP VIA THIS LINK https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3
https://wa.me/+2348039352724
VOLUME ONE
EPISODE 1️⃣6️⃣
Yana cikin jerun passagers ɗin da jirgin Max air ya sauke a filin tashi da saukar jirage na Mallam Aminu Kano (International airport), a hankali yake saukowa daga matattakalar jirgin ya fito ya tsaya inda ake ɗaukar luggage, na'ura tana gangaro da boxes na matafiya har na shi ya zo ya ɗauka ya nufi hanyar fita.
Masha Allah yau garin ranar a bude take kasan cewar lokaci ne na rani.
Alhamdulillah yau dai gashi a Nigeria a cikin garin Kano, ya sauka da fata da kuma burin samuwar cikar farin cikin sa, ya so su zo tare da Ummi sai dai Allah bai kaddara hakan ba, sakamakon Jadda (Kakar sa) mahaifiyar Ummi da bata da lafiya.
Tunda ya saka ranar zuwa Nigeria kusan kullum cikin saƙa da warwara ya ke, shin ko Khadijah zata yafe mishi? bashi da ƙwarin gwiwar tunkarar ta, da gaske yanajin kunyarta data Iyayen ta, amma yaya zai yi in bai nemi afuwar Khadijah ba yasan abune mai wahala ya sake yin farin cikin a rayuwar sa, to dama ita ce farin cikin sa kuma Rayuwar sa.
Ya so ya kuma yi fatan ace Aminin sa likitan sa Dr Huzaifa yana Beirut da babu shakka zai riƙo hannun sa ya kaisa har gaban Iyayen Khadijah ya kuma tayasa roƙon gafarar su, akwai shaƙuwa sosai a tsakanin sa da Dr Huzaifa da kai tsaye ma zai iya cewa Dr Huzaifa kamar ɗan uwan sa yake ba likitan saba, Dr Huzaifa yasan komai akan Khadijah from A to Z.
Yasan da yana nan zai tayasa neman afuwar ta da duka ƙarfin sa, amma yau gashi a garin Kano shi kaɗai babu Akhey (Yasir) babu Ummi kuma babu Dr Huzaifa.
Allah yasa su yafe masa su karɓi uzurin shi, yana tafe yana ta zancen zuci har ya fito harabar airport, ya tsayar da taxi, mai taxi ya fara mishi turanci, ya mayar mishi da Hausa, duk da Hausar tasa babu daɗi, amma ana iya gane wa, "wapa zaka kai ni inason nayi canjin kuɗi, daga can saika kai ni masauki."
Driver yasa akwatin shi a boot suka wuce wapa yayi canji daga nan yace ya kai shi Ni'ima guest place, Thair ya zaɓi ya sauka a Ni'ima ne saboda daga nan zuwa gidansu Khadijah babu nisa titi ne kawai a tsakanin su.
Sannu a hankali suna tafiya yana ƙarewa garin kallo tsawan shekarun da yayi rabonsa da garin na Kano ya gaa canje canje sosai, bridge ne, flyovers, ga sabbin wurare na cin abinchi da hotels an buɗe, lallai inka ɗauki wasu lokuta ba kaje waje ba baƙo ka ke zama.
Basu tsaya ko ina ba sai Ni'ima, gaban shi ya yanke ya faɗi, ya saka a ran shi hakan yana da nasaba da shigowar sa unguwar masoyiyar shi, ji yake kamar yayi tsuntsuwa ya tafi gidan su Khadijah ba sai ya huta ba, amma dai bari ya ajiye kayanshi ya rama sallar da ke kan shi tukunna, ya sallami driver ya shiga reception.
"good afternoon sir?" receptionist ta faɗa, ya amsa mata da barka da rana, ta buɗe baki da mamaki ashe yana jin hausa yayi murmushi. Yayi booking daƙi aka bashi key wata daga cikin ma'aikata ta tashi tayi directing ɗin shi zuwa ɗakin.
"thankyou sir." tace bayan yayi mata kyautar kuɗi ya buɗe ɗakin ya shiga, komai na room ɗin yayi mishi komai is intact, ya ajiye boxes din shi don akwai gajiya sosai a tare da shi, Toilet ya shiga ya watsa ruwa ya ɗauro Alwala, ya fara sauke sallolin da ake binshi, kafin ya san next move ɗin shi.
*****
Lagos
"Mami kwana nawa zamu yi a Bichin?"
"haba Hidaya har tambaya kike yi?" Hidaya Autan Mami ce ta kwana murnar zuwa Bichi don zata haɗu da mutanen ta su Amira da Umaimah ayi tsiya ayi daɗi, kusan age mates ne dukkan su sai dai Hidaya ta bawa Amira 6month Umaimah kuma tsakanin su 9 months.
"in ba don Dada tayi kiran gaggawa ba ay yanzu ba lokacin zuwa Bichi ba ne, ku na school." Hidaya ta gyada kai alamar haka ne. "gobe zamu tafi jirgin safe zamubi mu dawo jibi jirgin yamma."
Hidaya tace "to Mami Allah ya nuna mana, bari Daddy ya zo na karɓi kuɗin tsaraba." Mami tace "kina son yin latti ke nan? kinsan dai ba kya fita da daddare."
"pls Mami to ki bani ATM ɗinkin naje idan Daddy ya dawo sai ya baki kuɗin ki.? "Hidaya yaushe aka taɓa baki ATM ki fita shooping? You're still a child bana son wannan san girman, ki rubuta duk abinda kike so Deborah ta siyo miki ok." Hidaya tace "Yes Mami, thankyou."
****
Munnirah ta kalli mijinta Baba Dr cike da so tace "Mon Amour (mylove ). yana daga kwance a kan kujera ya ɗaga mata gira "yes cheri (darling). "ya kake ta kwanciya ne tun ɗazu?
"I'm exhausted, wallahi na gaji sosai I drove from Abuja to Kano."
"Oh me yasa baka nemi flight ba? "saboda bacin rai jiragen mu na gida sai a hankali, kina ganin last time sai 2 na dare na shigo miki, so this time around kawai na biyo hanya ga shi na zo da wuri sai dai gajiya kawai."
"haka ne, amma kar ka damu I will massage you." Munnirah ta faɗa tana dage mishi gira. ya lumshe ido yace "I trust you." ya buɗe mata hannu daga kwancen da yake "come here ma cheri." Ta taho ta isa wajen shi ya gyara ta kwanta a jikin shi.
"Mon Amour "yes my love."
"Na yiwa khadija maganar friend ɗin ka." Sai kuma ta yi shiru "uhhm go on, so how does it goes any hope? Kinsan ya matsa min." Baba Dr ya faɗa yana kallon ta, "toh na lallaɓa ta dai tace na bata time, bana son na takura ta." Baba likita yace "toh Allah yasa a dace, zan so ta zama matar Dr Usman, na san shi tun muna secondary school tare muka yi BUK Masters ne yayi a UDUS Sokoto, ni kuma na yi a unimaid Maiduguri, Usman ba shi da matsala ko kaɗan I wish she will give him a chance."
Munnirah tace "haka ne, I reason with her Tahir betrayed her that's why." Baba Dr Bai bari ta ƙarasa maganar ba ya katse ta da cew "pls kar ki yi min maganar shi, ki duba fah Babancikin gida da kan shi ya aika mishi yayi hakuri tunda ba saki uku bane ya maida ita amma ya ƙi be daraja Iyayenmu ba, Yaya Muhammadu da kan shi ma ya roƙi wannnan alfarmar still be saurare saba, Munnirah idan na tuna wannan wulakancin da Tahir yayi mana abun baya min dadi."
"wallahi Dr ni duk wannan ban sani ba sai daga baya nake samun labari kasan lokacin ina tare da Mama a Egypt, sai bayan na dawo naji wannan labari mara daɗi."
"mu bar zancen nan sweetheart let's face future wancan past ne banason tunawa." Baba Dr ya faɗa,
"toh in sha Allahu komai zai wuce. "Allah yasa dai wannan kiran na Dada ba akan Khadijah ba ne, Su Sa'ad ɗin
Yaya Ibrahim ma nasan za a yi maganar na su auren.
"oh Allah ina tausayin Khadija." Munnirah ta faɗa.
"khair in sha Allah." "in sha Allah Amour". Munnirah ta ƙara maimaitawa.
Ya shafa mararta yace "Allah yasa dai na yi ajiya yau."
Uhhm ta nisah, shekara kusan 4 ke nan da aure su da Dr amma bata taɓa missing period ba, ba ita ce matar shi ta farko ba yana da mata da suke zama tare a Abuja sun yi kusan 15years da Aure itama bata haihu ba. Kasan cewar sa gynaecologist kuma ƙwararen likitan da ake ji da shi yayi iyaka ƙoƙarin sa da taimakon abokan aikinsa akan matsalar su ta samun haihuwa, After series of tests an tabbatar da lafiyarsu ƙalau at anytime zasu iya samun rabo, amma har yanzu shinu, gashi shekaru nata turawa.
Sauda dama Dr yakan ce ta kwantar da hankalin ta, but shi kan shi abun na damun shi baya son nuna karaya ne, yafi tausayin Munnirah dan ita Zainab bata damu ba harkar kasuwancin ta ta saka a gaba, ah ah yau kayanta za su iso, ta samu riba kaza da kaza shi ne damuwarta, shi kan shi mijin bata kula da shi ba sai azababben kishi.
Muryar ta da sanyi tace "Allah ya bamu masu albarka Mon Amour." ya amsa da Amin.
*****
AMERICA
Tun ɗazu wayar Fahad ke ta haske alamar kira na shigo wa, baya son disturbance shi yasa kusan koda yaushe wayarsa zaka sameta a silent, ya ɗauko wayar "Aysha" sunan ya fito akan screen din wayar. Kansa ya dafe "this girl is a pest, this girl is a pest." yayi ta maimaita wa, shi baya son damuwa yayi regretting amsa Sallamar ta da yayi.
A'isha is the only girl ɗin da suke gaisawa da Fahad a kaf faɗin school ɗin su, tsaki yayi ya ajiye wayar. Ya tuna randa suka fara haɗuwa da ita a cikin garden, a School ne ya sami wani garden da in dai yana makaranta yana yawan zuwa can ya zauna, yana samun nutsuwa sosai a wajen is peaceful babu mutane ba hayaniya ga shuke shuke, that is pleasing to your view, a very serene atmosphere.
Yana zaune a cikin garden ɗin ta shigo at first da ta yi mishi sallama ya ɗago suka haɗa ido for the first time abunda ya jaah hankalin shi da ita shi ne duk wani personality da Ad (Sa'ad) yake so a mace ta haɗa, what drew his attention kenan da ita, har bai san ya amsa mata Sallamar ba.
Kullum zancen Ad yana son mace chocolate colour har cewa ya ke bourvita colour doguwa mai tsaho da kiba. baya manta wa yadda in Ad yana description ɗin his future wife har wani lumshe ido yake. shi Fahad a shiririta ya ke ɗaukan maganar shi, that's why sometimes in Sa'ad yana maganar he barely smile.
Ganin A'isha tayi occupying duk characteristics ɗin da Ad ɗin sa yake so a mace saiya amsa mata Sallamar yana ɗauke idanunsa a kanta.
Ta samu waje ɗan nesa dashi kaɗan ta zauna, be kara 5min a wajan ba ya tashi, dan yadda ta zauna kusa da inda yake sai ya fara jinshi uncomfortable.
Shi ke nan tin gada nan ta samu wajen zuwa, wani lokaci in ta mishi magana idan yaga dama ya amsa, idan bai ga dama ba yayi mata banza, sai daga baya ya fahimci tana da nutsuwa bata da hayaniya ba kamar sauran ƴan matan Jami'ar ba, a hankali suka fara gaisawa har ta ji course din da yake karanta, suka dan saba sama sama dan ita ce ke yi masa magana, sai tayi masa magana takai sentence guda, amma amsar sa bata wuce yes, no, okay, tin tana ɗaukar tsabar jan ajini ne da wulaƙanci yasa yake yi mata haka harta gane halin sane rashin san yin magana, dan akwai randa tazo wajen taƙi tayi masa magana irin bari ta gani zai kulata, amma har ya gama zaman sa ya tashi ko kallan inda take baiyi ba, haka tana kula da shi ko a waya aka kirasa amsar dai bata wuce yes, no, okay.
Shi Fahad ya ɗan bata fuska ne saboda yana son haɗa ta da Ad broda din shi, har ta karɓi digits ɗin shi be rufe ta ba, yace mata ita spec din brodan shi ne yana son ya haɗa su, tayi dariya suka bar zancen a haka.
Ya tuna randa ya yiwa Ad maganar Aysha, Sa'ad sai cewa yayi "Guy you are late, na bar maka ita ni na sami mata Fareeda the love of my life."
Fahad yasan yarinyar dan yana yawan ji suna waya da ita amma ko kaɗan bai taɓa kawo wa ransa Ad soyayya suke da ita ba.
Aysha ta damu Fahad ya haɗa ta da brodan shi da yace, Fahad ba boye boye ya faɗa mata he has found someone.
Kiranta ya ƙara shigowa wayar shi almost 6 missed calls ke nan yayi tsaki ya ɗaga call ɗin.
Pls react and comment. Har yanzu muna introduction ne zuciyar labarin na gaba be patient and follow us.
💫UMAYMAH 💫
✍️A&A PEN
Follow our Whatsapp group via this link https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3
https://wa.me/+2348039352724
VOLUME ONE
EPISODE 1️⃣7️⃣
Tahir ya bude ido, ashe bacci kwashe shi yayi ya kalli agogo, "Subhanallah" ya miƙe ya shiga toilet ya ɗauro alwala ya nufi masallacin hotel ɗin ya sallaci magrib, yana idar da Sallar ya ɗauki qur'ani ya fara tilawa har lokacin isha'i yayi, bayan sun idar da sallah kamar ya koma ya ci abinci sai kuma ya haƙura, Allah Allah yake yi kawai ya je gidan su Khadijah.
Yana fitowa daga hotel ɗin ya tsallaka titi yayi rukunin gidajen Sulaiman crescrent, tinda ya fara shiga cikin Quarters ɗin abinda ya lura shi ne, an yi gine gine na zamani mafi yawancin gidajen kamar ma'aikatu, yana tafe yana zancen zuci har ya iso block ɗin su Khadijah to his surprise sai ganin block ɗin nasu yayi kamar lounge ne "ah ah to ya haka?" Ya yiwa kansa tambayar.
Amma yasan duk ɗaɗewar da ya yi ba zai gagara gane block ɗin su ba. to ko dai gidan ya bace mishi ne? bari ya koma baya ya gani, nan ya sake komawa baya har yazo dai dai secondary school ɗin su Khadijah Da'awa, makarantar tana nan, ya ƙara yin gaba wasu block din sun zama shaguna, heroine collection ya karanta, Dis and Dat by mansura. "A'a ya haka?" a take ya ji kamar jiri zai ɗauke shi saboda tashin hankali.
Ya duba ɗaya gefen shi masu dafa indomie ne kamar wajen kamar join har kifi a ke gasawa. Ya daɗe a wajen yana tunani saida ya daidaita nutsuwar shi, sannan ya ƙarasa wajan masu suyar da sallama suka amsa mishi.
"Dan Allah tambaya na ke, akwai block ɗin dana ke nema block 12 anan Sulaiman crescrent, amma sai naga kamar lounge aka mayar da shi?"
"Ayya ai gwamnati ta yi owners occupyer ɗin wajan, duk wanda ya daɗe a gidan gwamnati ta siyar mi shi a kan farashi mai rahusa, toh da yawa wasun su sun siyarwa da yan kasuwa sun tafi wata unguwar sun siyar ko sun gina na su, kasan dama ma'aikatan gwabnati ne a cikin gidajen, ina ganin suma sun tashi kenan." mutumin nakai ƙarshen zancen shi, Tahir yace "inna lillahi wa inna illahirrajiun, yayi ta maimaitawa, ya zama kamar mutum mutumi, mutumin yana ta yi mishi magana ma amma ba fuskantar sa ya ke ba, ya riƙe kan shi ya kasa gaba ya kasa baya.
"toh ka kira su a waya su kwatanta maka inda suka koma." maganar mutumin ta dawo da shi hayyacin shin.
Muryarsa a dashe yace "nayi loosing contact ɗin ne."
"Ayyah" mutumin ya faɗa da alhini.
"Nagode" ya ce wa mutumin ya kama hanyar komawa hotel ɗin.
Da ƙyar ya ke jan kafa miyan bakin shi gaba ɗaya ya ƙafe, wani jiri ne yake ɗaukan shi, a take kan shi ya Sara, ya tabbatar da za a gwada BP ɗin shi a wannan lokacin za'a samu ya wuce 200, ikon Allah ne ya kawo shi hotel ɗin, dan wajen tsallake titi mota ta kusa buge shi mutumin ya fito zai mishi masifa yaga ga shi dai tsab dashi amma kamar ba a hayyacin shi ya ke ba sai ya haƙura ya jaa motar sa kawai ya tafi, haka ya rarrafa ya shiga ɗakin sa, yaja bargo ya lulluɓa, cikin ƙanƙanin lokaci zazzaɓi mai zafi ya rufe shi.
******
Siyama Ina mangoro na? Umma tace "wanne Mangoro kuma? Umaimah najin haka ta tirza ƙafa "wlh sai an biya ni." tayi rau rau da ido zata yi kuka. Umma tace "yau naji ikon Allah ni kika bawa Mangoron? Tukunna ma yanzu ke da daren nan zaki sha Mangoro? kya tsuge da gudawa kuwa."
"gidan su Sadiq fah na je na tsinko abuna, nidai kawai a biyani Mangoro na."
Allah ya yaye miki kwaɗayin nan Umaimah, tayi ɗai ɗai akan gadon Umma tace "wlh duk jiki na ciwo ya ke yi, ga azabar ɗan ki ga rashin Mangorona, wayyo miƙamiƙi na, wayyo sangalali na, wayyo ƙugu na." Umaimah ta dinga birgima a kan gadon Umma tana iya shege iri iri.
Umma na jera kaya a wardrobe iya ishen Umaimah ya ishe ta, dole ta juyo tana kallon ƙudirar Allah, ta buɗe murya sai birgima take yi akan gadon from edge to edge.
"wai ke lafiyar ki kuwa? Au ba za ki yi shiru ba shikenan sauko min daga gado. "Siyama dan Allah tausa za ki yi min. Umma ta juyo ta harare ta "ay da yake ni na aike ki, zullumin da kika sani ma Allah ya yafe miki. "Siyama zullimin me toh?" kafin Umma ta bata amsa Khadija ta shigo ɗakin da sallama.
Umaimah na ganinta ta miƙe "Ammina oyoyo." ta nufi khadija ta rungume ta. Khadijah na murmushi ta riƙe mata hannu ta nemi ƙasan carpet ta zauna "Umma sannu da gida."
"yauwa sannu Yayarsu kin dawo?" "Na dawo Umma, na gaji da yawa." Umma tace "ay haka ne daman Allah ya yi jagora."
"Amin Umma" khadija ta amsa. "kin shirya ko? gobe tafiya Bichi. Umma ta faɗa tana kallon Khadija.
"eh zan shirya Umma, bari na je na shirya kaya na." Umma tace "kala ɗaya zaki dauka jibi zamu juyo."
Umaimah tace "Dama a bar mu acan mu yi sati." ta haye kan cinyar Khadija. Khadijah ta kalle "makarantar fah? "kai wannan makaranta akwai cikas, ay mun kusa fara exams."
"sai ku je idan anyi hutu cewar Umma.
" A'a Lagos za mu da Amira." Umaima ta faɗa, sai faman nuƙurƙusa Khadija take yo. "Wai ke baki san kin girma bane? To ɗaga ni na gaji." Khadija tayi maganar tana ɗan ture ta gefe.
"Ahto gara kema yau ki ɗana uwar san jiki, ga raino can ta rakito min, ina magen taki? Umma ta tambaya tana kallon Umaimah da har yanzu bata sauka akan jikin Khadijah ba.
"tana hutawa a ƙasa, na bata madara ta sha ta ƙoshi."
"wacce madarar kika
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 9 Chapter of 29