Wai ba za ki cire uniform ɗin ba Umaimah? Umma keta mita tunda ta dawo daga Islamiyya take kwance a ƙasan carpet taƙi tashi. Umma data matsa mata sai cewa tayi ita ta gaji ne. Sasi ce ta zo ta kwanta a kusa da ita, tana ta shafa ta Isma'il yayi sallama ya shigo.
"sannu da gida Umma."
"yauwa Hakimi yau baka dawo tare da su ba."
"eh Umma malam ne ya rike mu."
Umaimah tana daga kwance tace "Uncle Ismah akwai labari."
"nima da labarin nazo." Uncle Isma ya yaɗa yana miƙe wa ya shiga dakin sh.
"akwai gulma dai, labari a fada a gaban kowa mana."
"kai Siyama kowan ne zance akwai abokin yin shi. Tana gama faɗar haka tabi bayan sa. Knocking ƙofa tayi ya buɗe mata ta shiga
"ashe Business yayi, uncle isma, mun yi samuwa fah a Bichi Baba nake jira ya dawo na karɓi kuɗin da su Daddy su ka ba mu, daa nace na bawa Baba ya ƙara yayi cefane, yanzu kuma jari zan ƙara na gullisuwar nan akwai alkhairi, ta karɓe ni wlh kafin short break fah ta ƙare." Ismael ya girgiza kai "uhhhm kedai kamar Inyamura kike wajan san kuɗi, kin fara bani tsoro fah, kuma wannan ne labarin? "shi ne" ta faɗa tana gyaɗa kai. "kai fah meye labari?
"shi zan faɗa miki yanzu. meya haɗa ki da Ustaz ya kawo ƙararki?" Umaimah tayi caraf tace "lallai ma sharrin shi ya girmama."
"Au haka zaki ce?"
Isma'il ya san Umaimah ciki da bai, ko tayi wa kowaa rainin hankalin ta shi da wuri ya ke gane ta.
"maimaita abunda kika ce?" sai tayi murmushi ta sunkuyar da kai. "wlh ki kiyayi Ustaz yace zai zo har gida ya faɗa." Ta zaro ido "gida kuma? Dan Allah ka bashi haƙuri, ni wlh sharrin shaiɗan ne."
"a to idan ya zo sai ki faɗa mishi, dan yace yaya Aliyu zai zo ya faɗawa ni babu ruwa na.
Umaimah ta ɗora hannu aka "na shiga uku ni Fatima dan Allah?" Idanta har ya fara tara ruwa. Uncle Isma yace "ba ke mara jin magana ba."
Umaimah na tsoron Allah tana tsoron hukuncin uncle Aliyu, sai da ya gaa jikinta yayi sanyi sannan yace mata ya dai ce a jaa miki kunne ne, sannan hankalinta ya kwanta.
Khadijah har ta kwanta wayarta tayi vibrating, sunan Daddy tagani yana yawo akan screen ɗin wayar, ta miƙa hannu ta ɗauka ta tashi zaune, ta amsa kiran da sallama "barka da dare Daddy." daga ɗaya bangaren Daddy ya amsa da "Barka kadai, baki kwanta ba ko? "eh Daddy yanzu dai na ke shirin kwanciya."
"good, na bawa Ahmad digits ɗinki expect his call at any moment from tomorrow zai kira ki, and zai zo yace acikin week ɗin nan, daughter feel free ki sanar damu idan kin ji wani abu na rashin gamsuwa, we will never force you kin ji?" Khadija ta gyaɗa kai kamar yana ganinta. "are you there daughter."
"eh Daddy"
"Toh madallah I want the best for you and Ahmad is a nice person I pray he treats you right in sha Allah, bari na bar ki ki kwanta. "toh Daddy sai da safe." ta ajiye wayar tana runtse ido, ikon Allah yau ita ce, ita Khadijah ake wa maganar aure da wani ba Tahir ba, abunda bata taɓa kawo wa ranta ba, ko a mafarki bata taɓa yin tunani irin wannan ba. ta juya ɗaya ɓarin wayar ta tayi haske text ne ya shigo taga unknown number.
"Assalamu alaikum, I just collect your number from your Uncle, is ready late I don't want to bother you at this time, here is my number pls save it, Goodnyt.
Ahmad B Lamiɗo.
*****
"Baba dogaro da kai, shi zan yi." Umaimah ta faɗa tana kallon Isma'il, irinka saka min baki ɗin nan. Uncle Isma ya ɗauke kai kamar bai gane ba. Umma ta ce "to kuɗin da aka dinga yi min yangar Baba za a bawa ya yi cefane shine za'a karɓe, yau dai na ganku a rana da Baban naki."
Siyama ba mai shiga tsakani na da Baba sai Allah. Baba yayi dariya yace "uwata nace a faɗa min me za a yi na dogaro da kan kin yi shiru, haka ake sana'a babu plan? babu market strategy, babu komai." Da sauri Umaimah ta tari numfashin Baba da cewa
"Baba mun fara tin tini fa ku ne dai ba ku sani ba, yanzu ma expanding nake so na yi, zafa ka yi alfahari da ni Baba, da sana'ar nan saina kai ka Makka." Baba ya ɗaga hannu sama kamar mai addua "Allah Amin ni Muhammadu waya ganni a jirgi uwata ta biya min Makkah."
"in sha Allahu kuwa" Umaimah ta faɗa da yaƙini.
Baba yace "Toh manager ba ka ce komai ba? , Isma'il yayi dariya "Baba ni nawa assisting
Kawai nake ita take abun ta."
"to meye ake ƙumbiya ƙumbiya a faɗa mana abinda ake siyarwa? Abin kusa da baka ne Baba, na ɗan kwaɗayi kuma wlh akwai alkhairi ko uncle Ismah? Yanzu ma ribar mu ta kai nawa?" Umaimah ta tambayi Isma'ill, yace "zata kai 60k."
Baba yace "A'a lallai ki ce Hajjin bana dani za a sauke farali." daɗi ya cika Umaimah tana murmushi bata san lokacin data cewa Baba ba "wlh gullisuwar nan akwai alkhairi."
"gullisuwa" Umma ta maimaita "gaskiya ne ashe shi yasa nan da nan Madara ta ƙare."
"wlh bama yi da ta gida." Umaimah ta tari numfashin Umma "sau biyu kawai muka taɓa ɗiba data yi mana ruwa muka ɗaure, ko Uncle isma? ya ce "haka ne ni ke siyowa a singa in ina dawowa daga makaranta."
"Ah lallai duk wannan ciniki babu labari, toh yanzu dai ku tsaya za a ƙara jari, amma bana son sana'ar ta ɗauke muku hankali a karatu, ke kin kusa shiga ss1, kai kuma Hakimi yanzu waec zaka rubuta, komai da muhallin shi, dan haka yanzu abar sana'ar nan sai kowa ya gama exams ɗin shi.
Uncle Isma yace "in sha Allahu ba zan baka kunya ba."
Toh kira auta itama gaa kuɗin ta ban taɓa muku ba, yan gatan Daddyn su, wannan ai kun fi ni kuɗi."
Umaimah ta tashi ta yi sama Sasi ta bi bayanta kamar tare aka aike su har da gudunta. Jim kaɗan suka sauko tare da Amira har tayi shirin bacci.
"Auta ko har kin kwanta? "A'a Umma assignment ma nake yi.' "Allah ya taimaka." Baba yace "kuɗin ki ne da Daddyn ku ya baku uwata tace sana a zata yi da nata, ko akwai abunda kike so?" Amira ta girgiza Kai "a'a Baba ka ajiye a wajen ka. Baba yace "ya kamata Babangida ya buɗe muku account saidai shekarun ne da saura, shi kenan je ki zan bawa Siyama ta ajiye miki, itama mai sanar sai ta dinga saka ribarta a account ɗin Managern ta."
Umaimah ta ce "la la la" tana kaɗa yatsa "ai mu ne banki, ko Uncle ismah da kan mu muke ajiye wa, ni dai haƙƙina ya zauna a wajena."
Umma tace "Allah dai ya rufa miki asiri Umaimah, wannan jarabar son kuɗin ina zaki kai ta? toh Siyama kuɗi abin so ne, idan sun miki yawa bani na dinga adana miki." Umma ta harare ta, tayi dariya "to Siyama naga ba kya son kuɗi. kar nazo na biyawa Baba Umrah ki ji haushi, gara dai ki nuna goyan baya, dan za a tuna baya, idan baki ba ni support ba kina kallo Baba zai yi tafiyar shi ya bar ki a Kanon Dabo."
"Ayi haka." in ji Baba yana dariya, "bana baƙin ciki, Allah ya kai shi lafiya." Umma ta faɗa tana miƙawa. "nagaji da labarin ƙanzon kurege nan na bar ku lafiya."
Baba yace "A'a fah Siyama kar na saɓa jaka zan tafi kice ga zance ga magana." Baba ya faɗa yana kallon Umma, "shikenan Hakimi gobe Babangida zai ba ku kudin, zani Abuja gobe da sassafe zan tafi, sati ɗaya zan yi insha Allah, Allah ya sa wa nema albarka."
"Amin Baba zan yi missing ɗin ka." Umaimah ta faɗa tana rungume shi.
******
Monday ce yau su Umaimah na class first period din su Art ne, Sadiq ya shigo yace "Art teacher wouldn't be around today."
"Ye ye ye." Umaimah ta faɗa da ƙarfi Sadiq yace "Smart Mama tana gaishe ki, kullum sai ta ce na gaishe ki kamar karatu. "Allah sarki Mama in sha Allahu zan bullo."
"me ake tattaunawa babu ni? Aminu ya faɗa, yauwa akwai fah haja Umaimah ta faɗa tana buɗe jaka ta fito da gullisuwa, Alawar Madara da albishir, "ga fa abin daɗi, yan class. Sadiq ya faɗa da ƙarfi, kafin ki ce kwabo masu 100,200 har da 500 within wannan period ɗin har ta ƙare.
"kai Alhamdulillah na shiga kasuwa a sa'a. Sadiq ya ƙirga mata kuɗin ta cas ya bata, komai ya ƙare.
Umaimah ta miƙe tace bari naga me mu ke da shi next, next period ya shiga, ajin ya rude masu hira na yi, masu bacci na yi, serious students kuma sun yi engaging kan su, Umaimah ta duba Time table Hausa ce next period.
Ta kalli ƴan aji tace "ku bani hankulan ku. ta faɗa da ƙarfi, duka ajin aka tsaya ana sauraron ta. Malamin Hausa yana ɗan dingisa ƙafa, kuma yana yawan amfani da kalmar AGURGUJE idan yana magana, kawai sai ta fara kwaikwayon shi, ta tafi wajen black board tana ɗin gisa ƙafa ta dawo gaban class.
"toh agurguje yau zamu fara sabon darasin mu Tarihin kasar Hausa kamar yadda kuka sani, agurguje Baya Jidda yazo daga Habasha, agurguje zamu fara da taƙaitaccen bayani. haba aji aka ɗauki ihu ana ta dariya da iface iface, Umaimah kuwa ta dage sai kwaikwayon Hausa teacher ta ke yi, can ajin class yayi tsit, irin shirun nan da ake cewa mutuwa ta ratsa, bata sani ba ashe Hausa teacher ne ya zo ya daɗe yana kallon ta, wizard da Aminu sai inkiya su ke yi mata da Ido, amma malamar sai bayani ta ke yi, jin shiru ajin ba a daria ya sa ta juya suka haɗa ido da Hausa teacher. Yau ƙarya ta ƙare ya kama ta red-handed.
"Biyo ni." ya faɗa yayi waje hankali a tashe ta bishi kamar kwai ya fashe mata aciki, ta ga yayi office din principal "innalillahi wa inna illahirrajiun kawai Umaimah take maimaitawa."
Readers dis gel knows how to do tsokana woo.
💫 UMAYMAH 💫
✍️A&A PEN
FOLLOW OUR WHATSAPP GROUP VIA THIS LINKhttps://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3
https://wa.me/+2348039352724
VOLUME ONE
EPISODE 2️⃣5️⃣
Umaimah tafiya take a harhaɗe har suka Shigo office ɗin principal, Mrs Abdu magashi ta kalli Hausa teacher ta ce "yaya aka yi ne malam misbahu? ta kalli Umaimah "Fatima what is the problem? Umaimah ta durƙusa tana gaishe da Principal "fine miss Fatima, how are you? ita dai Umaimah ta yi shiru tana jiran Hausa teacher yayi bayani.
Hausa teacher yace "Hajiya yau na ɗan makara kamar da 15 minutes, ina wani aiki ban samu na shiga js3A da wuri ba, ina zuwa na tarar da Fatima tana kwaikwayon tafiya ta da magana ta ana ta dariya a ajin."
Umaimah ta yi ƙasa da kanta, ya cigaba da maganar "idan nace zan ɗauki mataki da kaina sai nayi mata illah, shiyasa na kawo ta wajenki." ko a muryar shi zaka gane abin ya bata mishi rai.
Principal ta kalli Umaimah, she is brilliant but she is stubborn, an sha kawo mata ƙararta, amma this time around dole ta bata suspension for atleast 2 weeks as a punishment.
TA kalli Malamin Hausa "ku jira ni a class ɗin mallam ga ni nan zuwa, Fatima follow him." Umaimah jiki a sanyaye ta bi Hausa teacher suka koma class, za a gaishe shi ya daga musu hannu, su ma haushin su ya ke ji, ba a dauki lokaci ba saiga Principal ta shigo, suka miƙe Good afternoon maah, ta ɗaga musu hannu, "afternoon seat down. ta cewa class ɗin.
"I'm suspending your classmate for 2weeks, this is unacceptable for a student to imitate her teacher this is very bad of you, miss Fatima I'm not happy with you and I'm ashamed of your behaviour, Nobody should try this henceforth thats why I gave her the suspension letter right in front of you, its should be an eye opener for all of you, i repeat Nobody should try this again, I'm i clear?"
"yes maah."
Wani gumi ne yake tsiyaya ta skirt ɗin Umaimah jikinta yayi sanyi, Principal ta miƙa mata suspension letter tace "and you must write an apology letter to your teacher, enjoy the rest of your day." ta fita.
Hausa teacher ya kalli Umaimah yace "ɗauki jakar ki ki fita."
Taje ta harhaɗa books ɗinta ta zuba a jaka ta fita daga class ɗin
Tana fita ta samu gindin bishiya ta zauna, tana jiran lokacin tashi yayi.
Ita yanzu ya zata yi, gashi Baba baya gari, tasan ta kaɗe har buzunta, tasan Uncle Aliyu sai yayi mata dukan sakwara in yaji abinda ta aikata, duk ba wannan ba ma, Revision su ke yi, exams za su fara next week, tana zaune a ƙasan bishiyar tanata saƙawa da warware wa. Can wata zuciyar tace mata to Daddy zaki kira ne? Kai ta girgiza, tasan ko ta kira Daddy Uncle Aliyu dai zai saka, kuma abinda bata so ke nan.
Siyama kuma ba a sirri da ita, kowa sai ta faɗa mishi, Uncle Isma kawai zata faɗawa su nemo bakin zaren, tana ta saƙe saƙe har aka tashi tana nan, tana ganin mator Uncle Aliyu ta miƙe da sauri ta shige cikin students, dan kar a gane tana waje, ta nufi motar ta buɗe ta shiga, tayi masa sannu da zuwa, ita dai bata ji amsa war shi ba. Saiji tayi yace "yau ya aka yi kika fito da wuri?" kafin ta bashi amsa Amira ta shigo da sallama.
"sannu da zuwa yaya." ta faɗa, ya tada motar suka tafi.
*****
Khadija tun fitowar ta daga gida take Jin wayarta na rigging, bata tsaya duba mai kiran ba kawai ta mai da hankalinta kan tukin, dan bata so ta makara, sai ta bari idan ta isa shago ta kira koma waye. Tana yin parking ta fito ta shiga shagon, suka gaisa da su Hamisu, Isiyaku yace "matar nan ta zo."
"wacce mata?
"wacce ta zo jiya, mai sarin bedsheets."
"ok nagane ta, ya kuka yi?
"tace zata dawo bayan Azahar.
"toh ba komai Allah ya kaimu lokacin." Key ta ɗakko a jakarta ta buɗe office ɗinta, tana shiga ta ɗanyi shara da goge goge sama sama, dan office ɗin babu wani datti, saida taga komai yayi mata daidai, tana zama aka yi knocking ƙofa, "yes" ta bada izinin shigowa, wata budurwa ce ta shigo da ƙatuwar bagco a hannunta, Khadijah ta bata izinin zama, sannan suka gaisa, budurwar tace " ɗinkin bridal outfit na kawo."
"ok" Khadijah ta ce ta buɗe kayan, duka kayan masu tsada ne, daga gani an kashe kuɗi.
"Wannan shi ne na dinner, wannan gown za a dinka min na bridal shower ne, wannan kuma I want something flashy na cocktail ne." Khadijah ta samu paper tayi rubutu, tayi sticking da pin sannan tace "in yi miki karambani? budurwar ta yi dariya "babu damuwa ina jinki."
"ina ganin wannan na cocktail ɗin yafi dacewa da dinner, idan kin yarda sai a canja."
Wow! sai da khadija ta faɗa kuma ta gaa hakan zaifi gaskiya, dan haka tace "kuma kin fi ni gaskiya."
Khadijah tayi murmushi tace "thank you, don't mention, ai aikin mu ne, yanzu yaushe ne bikin?
"in two weeks time" ta faɗa.
"kin bamu short notice, wasu 2-3 month suke bayarwa, kinsan wani lokacin sai mun nemi accessories ɗin da zasu yi matching da material ɗin, kuma muna taking time gaskia, saboda we want our customers to be happy, we deliver nothing but the best."
Ta jijjiga kai "na sani wlh, kayan ne ba su zo da wuri ba."
"its okay, we will try our best, yanzu dai bari na ɗauki measurements ɗin ki." Khadijah ta ɗauko tape a drawer, ta miƙe ta fara gwada ta, tana rubutawa a jotter, sannan tace "ki samu su Hamisu ki basu deposit, sai yayi attending ɗin ki nagode."
Tayi mata sallama ta fita, kamar jira ake ta gama kira ya shigo wayar ta, sai lokacin ta tuna ɗazu an kira ta. Ta buɗe handbag ɗinta ta ciro wayar, gabanta ya faɗi ganin number jiya da akayi mata message ce, that means shi ya ke kiran ta, ta ɗaure ta ɗaga kiran da sallama.
"wa alaikumussalam wa rahmatullah." aka amsa mata daga ɗaya ɓangaren. Ranki ya daɗe ɗazu na kira na ji shiru ba'a ɗauka ba, nace ko gimbiyar tawa bacci ta ke yi, na dai kasa haƙuri Yanzu na sake kira ko Allah zai sa a ɗaga, dan ɗan jiran nan dana yi sai naji kamar na jira for the whole day."
"Barka da safiya? Khadijah ta katse shi.
"oh sorry ba mu gaisa ba, barka ka dai, amma ni dai bacci na rabi da rabi ne.
Khadijah dai ta yi shiru tana sauraran shi. Dan ita ta manta yarda ake zance, ko lokacin Tahir kusan shi yake hirar, tayi maza ta kauda tunanin shi.
"are you there? ya tambaya, ta amsa da "eh"
"ai naji kin yi shiru ne, kamar yadda aka faɗa miki, sunana Ahmad Bashir Lamiɗo, ni ne ɗa na biyun ƙarshe a gidanmu, Babana tsohon chief judge ne a federal High Court, mahaifiya ta ita kaɗai ce a wajen mahaifin mu, ina da Yayye shida, wannan idan kin shigo zaki sansu, let me not go into details, na yi aure da wuri in my 20s. Ya ɗan yi shiru, sannan yaci gaba da magana, ina da yara biyu Maza duk suna jami'a, kar fa kiji nace jami'a ki ce tsoho ne ni, I got married very early kamar yadda na faɗa miki, suna karatu a nan maryam Abach American University, ina aiki tare da uncle ɗin ki a nan ministry of foreign affairs, tafiya ce a gaba mu nan da 3months, Khadijah ya kika gani?
Aka buɗe ƙofar office ɗin aka shigo, Munnirah ce ta shigo "wlh yunwa na ke ji" ta faɗa tana buɗe fridge, ta ɗauko maltina ta dawo ta zauna a kujerar da ke facing Khadija.
"waya shigo? ya tambaye ta, tace "my sister."
yace "Amira? ta buɗe baki, kamar yana ganinta yace "kina mamaki ne? I knew almost everything about you.
Munnirah ta hau daga mata gira tana murmushi, ta gane dawa take maganar..
Khadijah ta ce "no my best friend Munnirah. yayi dariya yace "ki ce our best friend dai, bata wayar mu gaisa." da sauri Khadijah ta miƙa wa Munnirah wayar kamar me jira, ta miƙe ta shiga Toilet.
"our best friend." Munnirah ta yi dariya suka gaisa.
yace "pls our friend, ina son friend ɗin ki, tunda na ganta I haven't be myself, it's love at first sight, I most say, tun rasuwar Maman yarana ban sake dating ba, infact na cire rai da ƙara aure ma."
Munnirah ta ce
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 13 Chapter of 29