Share this page
ya ishe ni, duk hukuncin da iyaye na suka zartar dai dai ne, dan lokacin dana kawo ra'ayi na sun goya min baya, dan haka yanzu duk abinda aka yanke min ba ni da jaah." "A'a my sis ko da can ma kina budurwa an baki zabi balle yanzu da kinsan meye aure, addini ya baki wannan damar, ke dai mu yi addu'a Allah ya zaɓa mana alkhairi." "Mamin Rijiya! Mamin Rijiya!! Mamin Rijiya!!! Suka juyo Muryar Umaimah tana doso ɗakin, tana tafe tana kira ta bude ƙofar ɗakin ta shigo Munnirah tace "ya aka yi Umaiman fanfo?" "Dada ta ce ko kun koshi ne an kawo abinci." suka yunƙura suka fito. Mazan suka shigo abin sha'awa su Daddy a Baban tray suka ce a basu tare suka ci abincin, shinkafa ce da masa, tuwon shinkafa, farfesun naman rago, farfesun kifi dana kayan ciki haka Dada tasa aka zube musu kowa yaci abinda yake so. Umma tare da Mami suke ci sai Hidaya da Amira, Umaimah da Uncle Ismah, Ibrahim shi kaɗai yake cin nasa haka Aliyu shima shi kaɗai. Umaimah ta ɗan saci kallon Uncle Aliyu tahau gulmar shi a ranta "oh su Ali badai jarabar san girma da baƙin raiba, shi komai na shi na daban, anya yana jin daɗin rayuwa kuwa? mutum kullum cikin kunci." Suna haɗa ido ta ɗauke kai. Dada ta kalli Umaimah da Ismael "maigida wannan ay sai ta cinye abincin ta bar ka, naga bata wasa." "Toh ga inda Siyama ta gado iko akan abinci, nidai ana mun gorin abinci da bani da lafiya na kasa ci hankula suka shi suka yi, amma yanzu inaci anamin gori." "wai wa ye Siyama? Dada ta tambaya. Daddy ya ce "Azumin ki ce Siyama." "kaji wata shiririta, Siyama kuma sai ka ce wata yarinya." Sallamar Baban sama ce ta katse da zancen, Umaimah ta tashi da gudu tayi kansa "oyoyo Baban sama." "ke yi a hankali, kar ki shafa mishi miya." Babu komai ta shafa duk cikin soyayya ne." "innaah wannan Amaryar tawa ce ni kaɗai." Baban ABU ya faɗa. "to shikenan ta zaɓi wanda ta fi so. Baba Dr ya faɗa. Umaimah ta tsaya tana kallon su "wai duk so na kuke yi." ta rufe fuska "to ni ya zan yi da ku? aka kwashe da dariya. Baban sama ya zaro yan 500 note "zo Amaryar wa kika fi so. "Baba Dr ya zaro ƴan 1000 note yana nuna mata "sweetheart kin gani, Abuja ma tare zamu tafi da ke." Umaimah ta ce "Allah" tayi shiru tana tunani. Baban ABU ya ce "na siya miki computer da kikace kina so kin tuna?" Umaimah ta kalle sa "Allah." Daddy yayi murmushi "ni India zan kai ki ki huta." Da sauri tace "zaka kai ni wajen Sharukhn? ana ta dariyar shiriritar Umaimah. Babangida fuskar nan a turnuke kamar be taɓa dariya ba mita kawai yake a ransa yadda suke biye mata, kira ne ya shigo wayar shi ya tashi ya fita. Dada ce ta katse rahar da ake yi da cewa "ya kamata muyi abunda ya tara mu, masu jika saiku ɗaga mana ƙafa." Baban sama ya ce Ismael ya je ya kira Babancikin gida (Hakimi), ya tashi ya fita, Sasi ta taho ta ɗane jikin Umaimah ta zauna ta ƙara zuba mata farfesun kifi tana ci tana saka wa magen a wani karamyin cointainer da ta taho mata dashi, ana ta ɗan hira sama sama kafin Babancikin gida ya ƙaraso, Umaimah da ke cin kifi ta kalli Magen ta, tace "Kai amma fa daa mage ta iya ruwa da kifaye sun shiga uku." Aka kwashe da dariya Daddy dariya har da ƙwarewa sai da Baba ya miƙa mishi ruwa, Dada ta ce "wlh jikar azumi sai dai ta fita, idan ba haka ba shiririta za a yi, ba dariya ce ta kawo mu ba." Umaimah ta sha kunu ta kalli Umma "Siyama wai sunan wa aka saka min? Baban ABU ya ce "sunan Dada ne. "shi ne bata taraiyar ta?" Dada ta haɗa rai "Azumi jikar ki tana da makarai ku nema mata magani." Baba Dr yace "ba wani makarai Dada ƙuruciya ce kawai." "Toh ubana sarkin tsari." sallamar Ismael ce ta katse zancen. "Babancikin gida ya ce yana da baƙi idan ya sallame su zai shigo." Daddy ya cewa Ismael koma ka kira su Ibrahim su zo mu fara. ya ce "toh" ya fita . Kowa ya Shigo, Umaimah ta rarrafo ta radawa Daddy magana a kunne ya ce "toh shikenan zamu yi maganar, ke dasu Amira kuje sarkin mota ya kai ku gidan Baban sama." Baban sama a Bichi ya ke zaune da iyalansa. Shi ne ne babban ɗan wajen Dada, police ne shi mai matsayin DCP a nan Kano Sulaiman Isma'il Bichi, sai mai bi mishi Baban ABU Abubakar Isma'il Bichi, shi a ABU Zaria ya ke lecturing har ya kai matsayin VC yayi tenure ɗin shi ya sauka, yanzu yana nan a department of economics, mai bi mishi Baban Legas Ibrahim Isma'il Bichi yana aiki a foreign affairs, Maryam (Umma) ke binshi sai auta Yusuf Isma'il Bichi (Baba Dr), Dr ne a National hospital Abuja, ita Umma (Azumi) auren zumunci aka yi mata da Muhammad Ali Bichi (Baba) Mahaifin shi ƙani ne a wajen Hakimi, a hannun shi ya auri mahaifiyar Muhammad (Baba) a lokacin ita ce aka kawo da Dada a matsayin yar zaman ɗaki, su biyu ne a wajen iyayen su Bintu (Dada) da Mairo, a wajen haihuwa Mairo ta rasu bayan ta haifi ɗan ta namiji, Dada itace taci gaba da riƙon Muhammad, yana da shekara biyu a duniya mahaifinshi ya rasu, Dada tana tsananin son Muhammad, shi kaɗai take gani a matsayin yar uwarta Mairo mafi soyuwa a wajenta. Babangida ya ci sunan kakan shi ne Aliyu, a duniya Baba bashi da wasu iyaye da ya buɗe ido ya gani sai Dada da Hakimi, Muhammad kuma sunan Baban su Hakimi ne shiya sa Dada ta ke ce mishi Magaji tunda ita sunan surukin tane ba zata faɗi sunan ba.. Bayan fitar su Umaimah Baban sama ya gyara zama yace "sallu alannabiyul karin, salallahu alaihi wa sallam, aka yi addu'a yayi wa yan uwa barka da zuwa. "toh kamar yarda kuka sani Dada ta buƙaci na tura muku saƙo kamar yadda na faɗa muku, ta kuma kira da kanta ta ƙara jaddawa muku saboda mahimmanci haduwar, Dada bismillah." Dada ta yi gyaran murya ta fara addu'ar Allah yaa yi musu albarka, ya raya musu zuri'a, ya jiƙan wanda suka rasu har muryarta na rawa, sai da ta share kwalla ta ɗan nisa sannan ta ce "a gaskiya kwanan nan damuwa ta yi min yawa akan zaman Hadiza haka babu Aure shekara 30 tana zaune a gaban ku, in ba dan zamani ba daa yanzu an saka ta a waƙa." Khadijah ta sunkuyar da kai, Munnirah ta riƙe hannunta tana so ta kalle ta amma ta ƙi. "Ibrahima." "Na'am Dada." Daddy ya amsa. "kai ka ɗaure mata kugu tun auren baƙon hauren nan Ɗahiru, bayan aure ya mutu yan shekaru na dawo da maganar nan aka ce min bata da lafiya, na ƙara maganar aka ce na barta ta nutsu kana so hankalinta ya kwanta. ta yi shiru ta ja fasali sannan taci gaba da cewa "duk wanda ya kalli Hadiza yanzu ya san a nutse take, wacce nutsuwa kuma ake ne ma mata? daga haka kawai sai ji na yi wai an buɗe mata shago, haba jama'a lalacewar tawa bata kai nan ba, ni dai gaskiya abun na damu na nagaji da yawo da ake min da hankali shi yasa nace ku zo kawai ayi wacce za a yi." "Ayi wacce za a yi sai ka ce faɗa." Baba Dr ya faɗa yana ƙunshe dariya, Baba Dr mutum ne mai barkon ci, yana yawan zolayar Dada ya kan ce shi be san kakar shi ba, saboda haka ita ce uwa kuma kakar shi. *Hi nace hellooooooo ya kukaji Umaimah da Kakanninta? Wai da mage ta iya ruwa, This girl is funny ooo she makes me laugh incontrollable!* 💫 UMAYMAH 💫 ✍️A&A PEN FOLLOW OUR WHATSAPP GROUP VIA THIS LINK https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3 https://wa.me/+234803935272 VOLUME ONE EPISODE 2️⃣0️⃣ Toh Alhamdulillah in sha Allah Dada in dai a kan Khadijah ne komai ya zo ƙarshe. Daddy ya faɗa, "Ikon Allah wani sabon shagon zaka sake buɗe mata ni Bintu Gwani Isihu?" Yadda Dada tayi maganar saida tasa suka murmusa, Daddy yace "nina isa." Ba Khadijah ba har Baba jikin shi yayi sanyi da Dada take maganar, sai da ya ji a matsayin shi na uba yakamata ya magantu akan zaman Khadijah haka babu aure, amma daga shi har Umma sun kasa yin abunda ya dace ne saboda tausayin Khadija, da gaske shekaru gaba suke ba baya ba. "Muna jinka Ibrahimu." Daddy ya gyara zama yana fuskantar Dada yace "Ko Muhammad ba mu yi zancen nan da shi ba har ga Allah, nasan kiran nan yana da nasaba da Khadijah saboda haka na bari kawai idan mun haɗu duka ayi maganar baki da baki. in sha Allahu dai wannan karon na yiwa Khadijah Miji da kaina, wanda nake fata dasa ran ya zame mata ƙarshen matsalolin ta." Khadijah ta ƙara runtse Ido gabanta na faɗuwa Munnirah ma ta ji maganar ta dake ta, ta ƙara riƙe hannun Khadijah. "shi ma baƙon hauren ne?" Dada ta katse Daddy. shi kuwa Baba hamdala ya ke a ranshi yana yiwa Allah godiya yasan Daddy ba zai taɓa yi mata zaɓen tumin dare ba, Umma da Mami ba a gane yanayin fuskar su. Su Baban sama suka ce shikenan komai ya zo ƙarshe in sha Allah, Baban sama yace "ay dan dai yarana mata ne da wani zancen ake yi ba wannan ba." Duk yaran su babu wanda yayi aure a kananan shekaru irin na Khadija, Umaimah ce jikar farko a Familyn gaba ɗaya, shi Baban sama yaran shi duka mata ne su uku Fatima ce babba Hindu mai bi mata sai auta Anisah, dukan su sai da suka yi degree aka aurar da su, Baban ABU shi bature ne yaran shi biyu duka maza ne Fa'iz da Farouk, Baban Lagos yaransa biyar Surayya ita ce babba ta na aure a Pothacourt, sai Amal tana zaune a Lagos da mijinta, Sa'ad da Fahad ƴan biyu sai Hidaya Auta. "Ba baƙo bane hasali ma zan iya cewa kani yake a waje na saboda girmama ni da yake baya ko iya kiran sunana, Daddy ya kalli Baba yace Muhammad ina lokacin da Dada ta yi rashin lafiya na zo dubata kaje ɗauko ni a airport, idan baka manta ba ay tare da baƙo na ke? "an yi haka tabbas." "to lokacin idan baka manta ba ya ce za a zo ɗaukan shi nace babu damuwa ya bari sai mu ajiye shi." Baba yace "kwarai an yi haka." "muna tare a motar Khadijah tayi kiran Muhammadu da yake da motar ta ya taho ɗauko ni, Allah dai ya ƙaddara za a yi hakan, amma ay da motoci a gidan ya ɗauki motar Khadijah ya fita, ita kuma ta saka kayan mutane da za a zo karɓa a ciki har sun iso karɓa, Muhammad yace wa baƙona yayi hakuri kafin ya kaisa bari ya koma gida ya bada saƙo, anan yake faɗa min yana sauri yazo ɗauka ta ya ɗakko mukullin motar Khadijah saida ya fito ya kula maimakon ya koma ya canja kawai saiya fito da motar tinda ba jimawa zaiyi ba, baƙona yace babu damuwa, dan ni dama sai na huta a gidan shi kafin da yamma mu zo Bichi tare dashi, mun iso Khadijah tana tare da masu karɓar kaya a bakin gate tana jiran ƙarasowar mu, tazo muka gaisa ta karɓi kayan muka juya muka ajiye shi a galadanci, Na san shi mutumin kirki ne, tun daga ranar ya dameni yana son Khadijah, matar shi rasuwa tayi yana da yara biyu, tunda ta rasu be sake marmarin ƙara aure ba, tare muke aiki da shi, ko ni na sha mishi faɗa akan ya kamata yayi aure, yana ta yi min maganar Khadija ni na ce ya dakata tukunna ba don komai ba kuwa nima bincike nake yi akan sa, kuma Alhamdulillah duk inda ake neman tushen da za a haɗa auratayya dasu sun kai, sai dai mu ce Alhamdulillah, yanzu ma ya matsa min nace inada magabata ya jirani na fara kawo maganar gaban su, dan shi cewa yayi zai aiko da Iyayen shi ni na dakatar sa shi nace ya kamata su fara fuskantar juna tukunna." "Alhamdulillah burina zai cika dan so nake tayi azumi a ɗakinta." Dada ta faɗa, Daddy ya nisa ya ce "ban tari numfashin ki ba Dada, amma kamar yadda na faɗa muku a wajen aikin mu yake wannan karon an tura ni india zan yi shekara biyu acan, shima kuma ya na ɗaya daga cikin wanda aka tura mu tare zamu tafi, tafiyar tamu nan da wata 3 ne, ina ganin yanzu abunda ya fi shi ne su fahimci juna kafin lokacin, tunda dukan su ba yara ba ne da za a tsaya bata lokaci." Baban ABU yace "ya sunan surukin namu sai jaa mana rai ka ke yi." Daddy yayi murmushi "sunan shi Ahmad Bashir Lamiɗo, Dan nan cikin garin Kano ne, mahaifin shi tsohon chief judge ne, Daddy ya kalli Munnirah "wata ƙila zaki ji sunan shi Barrister, dan ba lallai kin tarar da shi ba." Munnirah ta gyada Kai "kwarai Daddy lokacin da aka ɗauke mu aiki a shekarar yayi retire." "Madallah ɗan nan unguwar Galadanchi ne, yaran shi suna tare da kakannin su. Yanzu dai Khadijah zai kira ki ku daidaita kan ku, idan be miki ba kuma sai muyi fatan Allah ya kawo wani mai albarka, idan kuma Alllah yasa kun daidaita nan da wata uku sai a ɗaura Auren shikenan ni da yata muna tare." Daddy yayi maganar yana murmushi." Baba Dr ya miƙa mishi hannu "toh ina maka murna Allah ya sa alkhairi yasa a yi damu." Baban ABU yace "toh masha Allah sai ka turo shi waje na yazo nima na yi mishi screening." Baban sama yace "amma kai da duk da wannan maganar haka mai mahimmanci ka yi mana shiru? "bin komai na yi a sannu, shi lamarin aure ba a yi mishi gaggawa." Yaya ka yi shiru baka ce komai ba? Baba Dr yayi maganar yana kallon Baba, Baba yayi murmushi " to me zan ce likita? duk ga ku iyayenta ay bani da abun cewa sai fatan Allah yasa albarka." Khadijah jin su kawai take yi kamar mai bacci kamar ido biyu, ita ba za ta ce ga yanayin da take ciki ba. "toh Alhamdulillah Maryama kowa ya tofa albarkacin bakin sa, amma ke ba ki ce komai ba? "Dada duk ga iyayenta nan ni me zance kuma? Allah yasa albarka." Mami ma tayi addu'a da fatan Alkhairi, dan ko ita bata san da maganar ba sai yanzu. Dada tace "wannan ta kau sai ka faɗa mishi ya zo ya nemi izini a wurin iyayenta, a kawo shi nan nima na ga angon nawa kafin lokacin biki." Baban sama ya kira Khadijah ta dago kai idon nan ya kaɗa yayi ja. "ko kina da abin cewa? Addini ya baki dama." ta girgiza kai "duk hukuncin da kuka yanke daidai ne Baba" ta faɗa muryar ta a sanyaye nan suka hau saka mata albarka. "Toh masha Allahu sai magana ta biyu, su Dattijo yakamata su ma su ajiye iyali, idan ban manta lissafi ba shekara biyu suka bawa khadija, karatun haka ya isa yaushe rabo na da Dattijo har na manta, gwara ma ɗan uwanshi zai kira ka a gaisa." Baba ya ce "ayi mishi afuwa, saboda matsalar shi ne." Dada ta tari numfashin Baba da cewa "ba wata matsala Magaji, a ina tsabta ta zama matsala? sai ku yaran zamani masu janye janye. Yauwa likita kai da Abubakar (Baba ABU) ku matan ku sun fita daga cikin mu ko? duk zuwan da za ku yi sai dai ku zo ku kaɗai ko? Zainab tuni nasan ta fi ƙarfin ka. ta kalli Baba Dr "dama bakin su daya da maimunatu, toh ba macen da zata watsa min zuri'a, itama Bilkisu (Matar Baban sama) abinda yasa baku ganta ba ta haɗu da tsautayi ne a ƙafa, bayan La'asar ku shiga ku duba ta wanda be yi zumunci a duniya ba zai yi a Lahira." Suka bawa Dada hakuri tare dayi mata alkhawarin za'a gyara . "ku dai riƙe zumunci Allah yayi muku albarkarsa, Magaji rufe mana taron da addua." ***** Tahir da kyar ya bude idanun shi ya jawo intercom ya danna kira receptionist ta ɗaga ya bukaci a zo room ɗin shi, ya faɗa mu su he is down with fever "ok sir will be there in a moment." ya yi hanging up. Ba a ɗauki time ba akayi knocking "yes" ya bada umarnin shigowa, aka murɗa ƙofar aka shigo, ma'aikacin hotel ɗin ne ya shigo da wani mutum a bayan shi daga gani likita ne saboda shigar sa, ya matso daidai gadon "ma'aikacin ya ce "sir the Dr is here to examine you." Da ƙyar ya yaye bargon jikin sa, Dr ya taɓa jikin shi yayi mishi sannu,, "your temprature is high, dole a yi allura, ka ci abinci? Sai a sannnan ya tuna be ko ci abinci ba ya kwanta, ya daga kai 8:30 na safe kenan haka ya kwana a mummunan yanayin nan, ya girgiza kai. "dole ka ci wani abu yanzu kafin ayi maka allura. I wil be back in 30mins time." ya gyaɗa masa kai. su ka fita tare da ma'aikacin. Toilet ya shiga yayi wanka ya fito ya sallaci Asuba data kunce mishi, yana idarwa aka kawo mishi breakfast haka ya daure ya ci sama sama chips ne da egg sai tea, aka yi knocking Dr ne ya dawo ya hada allura yayi mishi, jikin shi ba kwari ya sa mishi ruwa, yace he will be around idan ruwan ya ƙare zai zo ya cire mishi. Tahir daga lokacin be farka ba sai 2:10, duk yadda aka yi an sa allurar bacci a cikin ruwan, ya tashi yaga an cire masa ruwan. Alhamdulillah he is feeling much better ya sauka yayi sallah a masallaci ya dawo hotel room yayi order abinci ya ci ba don daɗi ba sai don ya samu kwarin jiki dana gwuiwar sanin matakin da zai ɗauka na gaba. 💫 UMAYMAH 💫 ✍️A&A PEN FOLLOW OUR WHATSAPP GROUP VIA THIS LINK https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3 https://wa.me/+2348039352724 VOLUME ONE EPISODE2️⃣1️⃣ A ranar Tahir wuni yayi a kwance yana jinyar jikin sa, zafin ciwon nasa fargaba ce da tunanin daya yi masa yawa, yana cikin wannan halin kiran Akhey Yasir ya shigo wayarsa ya miƙa hannu ya ɗauka muryarsa a shaƙe ya amsa Sallamar Yasir. Hankalin Yasir a tashe yake tambayar sa yana lafiya kuwa. A karye Tahir yayi wa Akhey Yasir bayanin halin da yake ciki, da abinda ya tarar zuwan shi Quarters ɗin su Khadijah. Cikin rashin jin daɗi Yasir yayi shiru yana tunanin shi kuma Tahir ƙaddarar shi ke nan, yama rasa abin da zai faɗa wa Tahir wanda zai kwantar masa da hankali, dama ya kirasa ne yaji ya ake ciki tsakanin shi da Iyayen Khadijah, sai kuma ya faɗa masa jikin Jadda da sauƙi sosai Alhamdulillah, amma hawan jinin Ummi yaɗan tashi jiya saidai jikin nata da soƙi. Jin wannan halin da Tahir yake ciki dole yasa Yasir ya fasa faɗa masa Ummi jikinta yaɗan motsa, maimakon haka kawai sai yayi masa bayanin jikin Jadda da sauƙi. Cikin lallashi ya cewa Tahir "to mai zai hana kaje ka samu Aminin Abbin mu Baba Isah ko za'a dace shi yasan inda su Khadijah suka koma, tinda dama shi ne yayi maka komai na neman auran ka a baya." Ai Tahir najin haka ya miƙe shi completely ya manta da Baba Isah saboda tsabar tashin hankali da ruɗa nin daya shiga. Suna yin sallama da Yasir ya shiga wanka, yana fitowa ya shirya a gurguje, ya kira Bolt ya faɗa musu location ɗin da zasu kai shi, in minutes mai motar ya kira yace mishi zai ƙaraso nan da 15minis. Reception ya fito ya zauna yana jiran zuwan mai Bolt ɗin, Ummi ya kira suka gaisa ya sake tambayar ta jikin Jadda tace da sauƙi. Yayi mata bayanin halin da yake ciki na rasa gidan su Khadijah da yayi, amma yanzu zashi gidan Baba Isah. Cikin tausayi irin na uwa Ummi tace "zaka sameta in sha Allah." "In sha Allah Ummi." Mai motar na zuwa ya yiwa Ummi sallama suka tafi gidan Baba Isah dake Ƴankaba Sabaru. ~~~~~* Dan Allah Khadijah ki daina kukan nan haka kiyi hakuri, in sha Allahu inaji a jikina wannan zaɓin na Daddy zai zame miki alkhairi." Munnirah keta faman lallashin Khadijah tin da aka tashi daga wajan meeting ɗin suka ƙule a ɗakin Dada. Khadijah ta share hawayen ta, "babu komai Munnirah yau komai ya same ni nina jawa kaina kuma Tahir yaja mini amma Allah yana gani idan........da sauri Munnirah tasa hannu ta rufe mata baki ta hanata ƙarasa abinda zata ce. "Karki yi haka Khadijah karki yiwa Allah butulci mana, sau nawa na baki hakuri, sau nawa kuma Iyayen da ƴan uwa suka baki hakuri? Ke kanki kin san an soki an kuma tausaya miki, Auran Tahir ƙaddarar kice kuma Khadijah ko kinso ko kinƙi dole keda Tahir kun zama ɗaya dan shine uban Umaimah na halal, dan haka dan Allah ki rinƙa kai zuciyar ki nesa a kansa ba komai ya kamata ya zo bakin ki kifada akan saba." "Wacce ƴa? Ƴarda bai san da ita a duniya ba." "Duk da haka dai shi ne uban ta. Kiyi hakuri ni ban sanki da zafin zuciya ba duk da nasan ba'a kyauta miki ba, amma ya kamata yanzu ace kin manta komai kin barwa Allah ikon sa kodan Iyayen ki da kullum burinsu su faran ta miki, Khadija kalli yadda ko

Chapter 11 of 29