Share this page
bila sabab (without a reason)." Baba ran shi a bace ya miƙawa Umma takardar yana cewa "ni dama wlh auren yarinyar nan be taba kwanta min a rai ba." Umma ta karɓi takardar ta karanta a gigice ta kalli Baba sai ta fashe da kuka, idon Baba ya kada sosai yayi jaah, wata jijiya ta daga a gefen kan shi da sauri ya fice daga ɗakin Umma idanunta sun kumbura sosai saboda kuka ta gyarawa Khadija kwanciya tinda Baba ya fita bai dawo ba har yanzu. Tana zaune Baba ya shigo ɗakin tare da su Ibrahim, Aliyu da Isma'ill suka gaishe da Umma da tambayar ta me jikin, ta ce "da sauƙi." Baba ya dube su yace "ku bamu waje zamu yi magana, ku jira ni a reception." Suna fita ya kalli Umma, "naje company neman Tahir aka ce min baya nan kuma naga motar shi tana nan, sai nayi tunanin ko ya fita da wata motar ne, na fito waje inda na yi parking, sai ga shi ya fito zai fita, kuma ya ganni mun haɗa ido dashi, toh kin ga abun nashi wulaƙanci ne kenan." Umma tace "ikon Allah ba a tara sani da Allah." "Baban su na Legas ma ya kirkira shi baya daga wa." Suna cikin maganar Khadijah ta yi wata zabura Umma ta yi kanta da sauri tana tofa mata addu'a "Habibi! Habibi!! Habibi!!!." Khadijah ta faɗa da ƙarfi, sai kuma ta ce "Zaliha! Zaliha!!." Umma na share hawayen tausayin ta tace "yi shiru ki yi addu'a Khadija, likita yace banda surutu." Kamar taji me Umma tace sai ta koma ta kwanta. Ran Baba babu daɗi yace "har yanzu ta na firgitar?" "tana yi, dan jiya ba mu yi bacci ba." Wayar Baba tayi ringing ya ɗaga, Baban cikin gida ne, ya sanar da Baba ya turo sarkin mota da malam Liman zasu zo a madadinshi, ya bisu suje wajen Waliyin Tahir Baba Isah, da shi zai zo da kan shi sai kuma ya tashi baya jin daɗi. Hakimi yace wa Baba "ace mishi lallai nina aiko ayi haƙuri komai ya wuce Khadijah ta koma ɗakin ta." Baba yace "to in sha Allah." Ya yiwa Babancikin gida Allah ya sauwaƙe, Baba yana ajiye wayar kiran Daddy ya shigo. Ya labartawa Daddy yadda suka yi da Babancikin gida, Daddy ya ce "okay yanzu zamuyi boarding zan baro US ina nan zuwa in sha Allah." Baba ya hau faɗan me yasa zai taho, Daddy yace "Muhammadu nine Waliyin Khadija, nina bada aurenta, an samu matsala a auren dole na zo." Baba ransa duk babu daɗi, yace "bari na sake kiran Babancikin gida, a bari sai goben inka iso sai a je a samu Alhaji Isan gaba ɗaya." Baba yana sauke wayar ransa a masifar ɓace, yace "wallahi Maryama badan likita ya tabbatar min Khadija nada ciki ba, wallahi da babu inda zamu roƙar su akan ya maida ita." Hankalin Baba Isah a tashe ya je Company ya samu Tahir ya balbale shi da faɗa ta inda ya shiga ba ta nan yake fita ba, "Tahir cikin girma da arziki aka bamu auren yarinyar nan, me tayi maka? ka fada min." Tahir ya buɗe baki da ƙyar yace "ni Baba ayi min afuwa amma na gama auren Khadija." "toh haka ake raba aure babu dalili? me ta yi maka? Dole akwai dalili ka faɗa min abunda zan faɗawa iyayen yarinyar nan, Waliyinta suna hanya, tun jiya Alhaji Ibrahim yace yana tafe, wlh Tahir baka kyauta min ba, koma dai menene ka yi haƙuri ka mayar da matarka." kamar ba zai yi magan ba yace "ni bata yi min komai ba kawai ina ganin hakan shi ne maslaha." Baba isa yayi kwafa "ka rubuta ka ajiye Tahir wlh haƙƙin yarinyar nan sai ya bibiye ka, ka bani kunya Tahir, ka bani mamaki, ka mayar da ni mutunmin banza a idanun iyayen yarinyar nan, mutane masu mutunci da dattako." Babu yadda Baba Isah be yi da Tahir yayi haƙuri ya janye sakin kafin iyayen Khadija su zo ya mayar da matarshi tunda saki biyu ne ba, amma Tahir ya ƙeƙashe kasa, yace "gaskiya Baba bazan iya maida ita ba ni matsayata kenan." Ran Baba Isah a mugun ɓace ya baro Company. 💫 UMAYMAH 💫 ✍️A&A PEN Follow our Whatsapp group via this link https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3 https://wa.me/+2348039352724 VOLUME ONE EPISODE 4️⃣6️⃣ Dr ya shigo ɗakin suka gaisa da Umma ya tambayi ta mai jiki, "da sauƙi Dr bacci ma takeyi." Umma ta yi masa complaining yawan Amai da Khadija take yi ga zazzaɓi sosai baya sauka. File ɗin Khadija ya buɗe yayi rubuce rubuce, Umma ta ƙara mishi bayanin firgita da rashin maganar da take yi, ga yawan tunani da take yi koyaushe, "okay idan an jima ta tashi nurse zata zo ta ɗauki jininta, akwai test ɗin da za a yi mata." Likita yayi wa Umma sallama ya fita. Dr yana fita babu ɗaɗewa Baba da Daddy suka Shigo, Umma ta gaishe da Daddy, yace "lfy ƙalau, su Mami suna gaishe ku dame jiki." Umma tace "ɗazu mun yi waya." Baba ya kalli Umma ya ce mata "yaya har yanzu tana firgitar ne?" umma idonta ya kawo ruwa "wlh haka muka kwana yau ma kamar jiya." Daddy ya girgiza Kai yace "Allah ya bata lafiya, zamuje wajen Waliyin yaron nan bayan masallaci, yaron ya bani mamaki ya wulakanta mu, ya ci mana mutunchi." Yadda Daddy yayi maganar kasan abun ba karamin bata mishi rai yayi ba, Baba be ce komai ba don shi wannan abun kamar a mafarki haka ya ke ganin shi, wai auren wata shida ne har an yi an gama, "Habibi." Muryar Khadija ta katse musu tunani. Tinda aka kawo ta asibiti haka take yi tana bacci tana ƙwala kiran Habibeey, Umma da sauri ta yi kanta Daddy yace "haka take yi daman?" Umma ta share hawaye ta hau tofa mata addu'a, Daddy ya sake cewa bari naga likitan." "yanzu ya bar nan, yace idan ta tashi za a ɗauki jininta." Umma ta faɗa. "Muhammad mu je wajen likitan." Daddy yayi maganar yana fita daga ɗakin, Baba da Daddy suka fita a tare. Sarkin mota da Malam Liman suna isowa suka ɗauki Daddy suka tafi gidan Baba Isah dake Ƴankaba, a waje suka yi parking, Daddy ya kira shi a waya yace ga su a waje sun iso. Baba Isah ya fito ya shiga dasu, suka gaisa a mutumce, gada ɗaya kunya ta lulluɓe Baba Isah. Cike dajin nauyi Baba Isah ya kalli Daddy yace "wato Alhaji Dan Allah ayi haƙuri wlh nauyi da kunya ne ya hana ni zuwa Asibiti na duba Khadija tuntuni, sai jiya dai muka daure muka je nida mai ɗakina, wlh ba a kyauta muku ba, kuma ni yaran nan ya saka ni a tsakiya na karɓar mishi aure a mutumce, amma wlh ya bani mamaki, saboda wlh ni zan faɗa maka yadda ya damu a ɗaura musu auren nan." Daddy ya katse shi da cewa "Alhaji ni yanzu abunda ya kawo ni maslaha muke nema, wannan yana wakiltar mahaifin mune." Daddy yayi maganar yana nuna Malam Liman, suka sake gaisawa da Baba Isah. "idan da hali munason ganin shi mijin nata, na tambaye shi idan akwai wani abunda take yi mishi bamu sani ba yayi haƙuri ta koma dakinta, yarinyar nan tana son shi yana son ta kar a bari sheɗan ya ɓata musu aure, ana yin tafi haka ma kuma a dawo a zauna." Baba Isah ya rasa inda zaisa kanshi gaba-daya Daddy ya saka shi a tsaka mai wuya, amma shi sun yi magana da Tahir yace ya gama aurenta, mutuncin mutanen nan ya wuce ya fito ya furta musu cewar Tahir ya ce ya haƙura da yarsu, amma bari ya kirawo shi ya zo da kan shi yayi musu bayani. Maganar Daddy ce ta dawo da Baba Isah daga dogon tunanin daya tafi, "Alhaji bari na kira Tahir ɗin yazo." Malam Liman yace "babu laifi." Baba Isah ya kira Tahir, bayan sun gaisa yace yazo ya sameshi a gida yana son ganin shi yanzu, ya amsa da ga shi nan zuwa. Suna tare da Zaliha a lokacin yana sauke wayar tace "waya kira?" yace "Baba Isah ne ya kira yace na je na same shi a gida yanzu nan." "Kar ka je nasan akan maganar Khadija ne." Tahir ya girgiza Kai "dole na je kar ki manta fa shi ne waliyina a garin nan, bani da kowa sai shi, shi ne mai daura mana aure." "kuma haka ne toh muje ka siya min shawarma a Dhalal sai ka wuce.." ya amsa mata da "toh" suka kama hanya ya siya mata shawarma da ice cream ya ajiye ta a gida, sannan ya taho kiran Baba isah. Yana hanya Baba Isah ya ƙara kiran shi, yace "ina jiran ka fah." "ina hanya Baba na kusa ƙarasowa. Da sallama ya shigo faloon, da Daddy ya fara haɗa ido yayi maza ya sunkuyar da kai ƙasa ya zauna akan carpet ya gaishe su, suka amsa. Baba Isah yayi masa bayanin abinda ya kawo Daddy da Malam Liman. Daddy ya yi gyaran murya, ya kira Tahir, ya amsa kansa a ƙasa, "na ji abunda ya faru tsakanin ku da Khadija, dama na faɗa maka duk abunda ya faru ni za a nema, ni ne Babanta, ban ji daɗi ba da har aka zo wannan matakin nayin saki ba tare daka kawo min ƙara ba, idan wani abu ta yi maka ay sai ka kira ni, bawai ka yanke irin wannan danyan hukunci ba, yanzu dai Khadijah tana kwance a asibiti har yanzu ba ta cikin hayyacin ta." Tahir yaji saukar maganar har cikin ransa, kamar abun ya taɓa shi sai kuma wata zuciyar ta kutso mishi da tunanin Zaliha, nan da nan ta danne tausayin Khadija. Daddy yaci gaba da cewa, "ina neman Alfarma a wajenka ka yi haƙuri ka mayar da ita ɗakinta, wannan ni na roƙa ayi mata afuwa, duk ma abunda take yi maka ka fada min za mu jaa mata kunne in sha Allahu." Malam Liman ya gyara zama ya ɗora da cewa "Malam Ɗahiru da yawun Hakimi nake ƙara baka hakuri ka dawo da ita ɗakin ta." Falon yayi shiru kamar ba zai yi magana ba can kuma yace "Daddy babu abunda ta yi min, ayi haƙuri zaman ne ya zo ƙarshe tsakani na da ita, ina fatan Allah ya bata lafiya a gafarce ni." Yana faɗin haka ya tashi ya fita. Kunya da nauyi ya rufe Baba Isah, jikin sa a sanyaye, yace "Alhaji dan Allah ka yi haƙuri ba ni da kalmar dazan faɗa muku data wuce nace kuyi haƙuri." Daddy da ran shi ya riga ya gama ɓaci yace wa Baba Isah "babu komai Allah ya rufa asiri." ya miƙawa Baba Isah hannu suka yi Sallama, Daddy da Malam Liman ransu a ɓace suka wuce Bichi ba tare dasun nemi Baba ba. Suna isa Bichi suka samu Babancikin gida da baƙi sai da suka tafi sannan suka mayar wa Hakimi yadda suka yi da Tahir. Hakimi baice wa su Daddy komai ba ya ƙara tura Sarkin Mota ya je ya faɗawa Tahir yana son ganin shi ya zo Bichi ya same shi. Daddy suna tare da Hakimi Sarkin Mota ya dawo da saƙon Tahir ya "ranka ya daɗe Yaron nan yace indai zancen Khadija ne shi ya riga ya gama yanke hukunci." Lokacin goshin magariba ne, amma haka Hakimi ya sake cewa "bayan sallah ka sake koma wa ka faɗa mishi Alfarma na ke nema awajen shi ya zo ko ma menene za a sasanta." Daddy kamar ya ɗora hannu aka dan baƙin ciki, haka ya riƙa bawa Hakimi haƙuri ya rabu da Tahir, Babancikin gida yace "babu komai Ibrahim mu ke nema a wajen shi." Sarkin Mota bai dawo ba sai wajen isha'i ya dawo da saƙon Tahir ya ce shifa ya gama magana. Lokacin da Dada ta samu labarin wannan wulaƙancin da Tahir yayi musu a bakin Daddy, harda kukan ta saboda ɓacin rai, Daddy yasha faɗa kuwa ba kaɗan ba dan duk alhakin abinda ya faru Daddy ta ɗorawa, faɗa Dada take kamar zata ari baki, da labari ya iske Baban ABU kuwa cewa yayi dan Allah Hakimi ya amince masa ya kai ƙarar Tahir, har su zai nuna wa shi dan yau ne wallahi tsaf zai ɗaure sa. Baban sama ya goyawa Baban ABU baya, amma Hakimi yace sam baza ayi haka dasu ba, su barshi yaje yayi wa kansa. ***** Likita tare da nurse suka Shigo ɗakin da aka kwantar da Khadija, Umma tana zaune suka gaisa ya tambaye ta me jiki tace "Alhamdulillah." Likita yayi wa Umma bayanin cewa "Hajiya wannan rashin lafiya na patient ɗin nan yanzu mun ɗan yi stabilissing condition dinta, tana fama da depression ne, sannan jininta ya hau amma ba sosai ba." Tinda ya fara bayanin Umma take salati, ya miƙa wa Umma takardar tests ɗin, Umma ta fashe da kuka, ita dama ta yi tunanin haka, "Hajiya kiyi haƙuri." muryar likita ta katse ta, "ayi haƙuri Hajiya zamu yi discharging ɗin ku daga nan zan tura ku AKTH psychiatric department anan zata ci gaba da ganin Dr zata fi samun kulawar data ke buƙata acan. Dr ya yi rubuce rubuce a file ɗin hannun shi, ya fita. Tinda Dr ya fita Umma take kuka har kukan ta ya tashi Khadijah daga bacci, gata dai kallon Umma ta ke yi amma hankalinta baya kan Umma. An kawo khadija AKTH amma ba kwantar da ita aka yi ba, tana ganin psychiatric doctor ne a maida ita gida, duk sati Baba da Umma suke kawo ta, yau ma Baba ne a gaban likitan bayan an gama duba Khadija yake ƙara yi mishi bayani, "condition ɗinta zai yi dai-dai, tana cikin trauma ne (firgici) na wani abu da ya faru da ita, kar a tuna mata da bacin rai, a rinka kwantar mata da hankali, A dena barinta ita kaɗai." Dr ya ƙara rubuta mata wasu drugs, Baba ya karɓa ya siyo, ya dawo ya nuna wa Dr yace "yayi." Sannan yayi masa godiya suka yi sallama da likita, a hanya Baba da ran shi ya gama ɓaci ya ce "Allah ya saka mana tsakanin mu da yaron nan." Umma tace "tunda aka kwaso kayanta da daddare idan na shiga dakinta kallon hotonan bikin su take yi tana kuka." Baba ya juya baya ya kalli Khadija ya ga bacci ta ke yi mai nauyi, haka take yi duk lokacin da aka yi mata alluran ta, tana shiga mota sai bacci mai nauyi ya ɗauke ta har su isa gida tana bacci. Baba ya cewa Umma "ki tattara duka wani hoto daya danganci yaron nan ki bani, wayarta ma ki bani ita, duka abinda ya shafe shi ba na son shi a gidana." Su na zuwa gida Umma ta haɗa hotuna da CDs ɗin bikin Khadijah ta bawa Baba, kai hatta lefen ta Baba yace a saka a store Dada za a kaiwa Bichi ta rabawa mabuƙata. Haka Umma ta haɗa komai daya shafi Auren Tahir da Khadija ta bawa Baba da Aliyu suka ƙona. Abu ɗaya ne ba za a iya gogewa ba shi ne cikin Khadijah, cikin ma Baba cewa yayi sai dai a zubar da shi ba ya bukatar haɗa jini da Tahir, Daddy ya hana shi yaƙi, har sai da Babancikin gida ya shiga maganar ya kira Baba yayi mishi faɗa sosai, "idan rai ya ɓaci hankali baya gushewa Magaji kar ayi wa Allah shisshigi a lamarin shi." Shike nan Baba ya haƙura aka bar zancen zubar da cikin Khadija. 💫 UMAYMAH 💫 ✍️A&A PEN Follow our Whatsapp group via this link https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3 https://wa.me/+2348039352724 VOLUME ONE EPISODE 4️⃣7️⃣ Ana gobe Daddy zai koma US suna zaune suna hira da Baba ya cewa Baba "ga shi wannan takardar fili ne na siya mana ni da kai anan Sultan Road suke, in nayi retire nan zan dawo da zama, na dade ina mana tanadin su, sai yanzu Allah ya yarda." Filaye ne Daddy ya siya musu guda biyu a jere, Baba yama kasa magana ganin abun yake kamar a mafarki, Daddy yayi murmushi yace "na ga nan ɗin ya yi muku kaɗan, gasu Babangida sun fara zama samari." Baba ya rasa me zai cewa Daddy, ya karɓi takardar filin yana juyawa a hannun shi, tunda aka fara wannan rikicin na auren Khadijah sai yau ya ji wani abu na farin ciki, Baba na hawayen farin ciki ya rungume Daddy. "haba Muhammad kar ka damu Allah ya yi mana jagora ya sa mu amfana." Daddy ya faɗa yana bubbuga bayan Baba. Baba da ƙyar ya iya bude baki ya cewa Daddy "ba ni da abunda zan faɗa maka Yaya Ibrahim sai Allah ya saka da alkhairi ya sa a fi haka ya dubi bayanka." Daddy ya harari Baba, "kai amma Muhammadu Allah ya shirya ka, yau nina zama Yaya kuma na tashi daga ɗan uwa" Baba bebi takan maganar Daddy ba ya kira Umma ya nuna mata takardar filin, nan suka hau murna. Daddy yace "idan an yi Sallar La'asar sai muje mu gani ko." Sunje sunga filayen a Sultan Road manya ne sosai guda biyu a jere. Daddy ya koma US, amma kullum saiya kira yaji ya jikin Khadijah haka ba'a cinye wata sai Baba yaga saƙon shi. Tin Baba na magana har ya hakura yabi Daddy da addu'a. Munnirah suna yawan gaisawa da Umma a waya, Umma na yawan kiransu taji ya jikin Hajiya, Hajiya jikin ta da sauƙi an yi aikin lafiya cikin nasara. Duk lokacin da Munnirah ta kira Umma tana yawan tambayar ta Khadija dan bata samun ta a waya, duk lokacin da Munnirah ta matsawa Umma da tambayar Khadijah takan ce "ki kwantar da hankalinki Munnirah ai kun kusa dawowa zakizo ki sameta lafiya in sha Allah." Koda yaushe a haka Umma take kaucewa maganar har suka saka ranar dawowa. Key ɗin gidan su Munnirah na hannun Umma, anaya gobe zasu dawo Umma ta buɗe gidan ta gyara musu tas, tayi musu abinci. Bayan sun dawo sun huta Baba ya shiga yayiwa Alhaji barka da arziki, Alhamdulillah Hajiya jiki yayi kyau, sai rashin kwarin jiki. Anan Baba yake faɗawa Baffa gwamnati zata siyar mu su da gidajen da su ke ciki owners occupier, zata siyar musu da sassauci, wasu su gyara su shiga wasu su siyar, Baba ya faɗawa Baffa Daddy ya siya musu fili a Sultan Road, Baffa sosai ya taya Baba murna, Baffa yace "kaga nima ina ta processing komawa under Federal govt. Lokacin da Munnirah tayi ido biyu da Khadija ba ƙaramin tashin hankali ta shiga ba dakyar Umma ta bata hakuri, inta kalli Khadija taga yadda ta koma kawai sai taji wani kuka ya taso mata. Tunda Munnirah ta dawo kulawa da Khadija ya dawo hannun ta, kasan cewar Umma ta yi nauyi, lokacin ta kusa haihuwa. Tinda abun nan ya faru Khadija bata taɓa cewa kowa komai akai ba saida Munnirah ta dawo sannan Khadija ta faɗa mata duk abunda ya faru, ran Munnirah ba ƙaramin ɓaci yayi ba taci burin sai taci uban Zaliha. Munnirah ta sha zuwa gidan su Zaliha neman ta amma sai Mamanta ta ce bata nan, Umma ta gano Munnirah na zuwa gidan su Zaliha neman ta akan abunda tayiwa Khadija, ta hana ta zuwa, tace "ayya Munnirah ƙyale ta barta da Allah, zata tsince abinda tayi in sha Allahu." Munnirah badan ranta yaso ba ta haƙura da zuwa neman Zaliha. **** Cikin Khadijah sam baya girma, idan ka kalle ta ba za ka ce tana da ciki ba. Umma ta haihu lafiya aka sakawa yarinyar suna Fatima sunan Dada suna kiranta da Amira. Sosai Munnirah ke kula da Khadija ita ke bata abinci haka kula da shan maganin ta Munnirah ce dan har lokacin tana shan anti depressant saboda ba a son ta samu matsala a wajen haihiwa. Ranar wata Asabar munnirah na tare da Khadija a falo ta goya Amira, Umma tana daki ta na rama bacci dan Amira bata barinta tayi baccin dare, kawayen su Khadija na Da'awa suka yi Sallama Munnirah ta amsa musu da fara'a suka Shigo. Ƴan mata ne guda uku dukan su ƴan ajin sune bayan sun gaisa Munnirah ta kawo musu ruwa da lemo, "Hafsat Dakata tace "oh Khadija sai kuma mukaji abun da ya faru babu daɗi." Munnirah ta ɓata rai tace "wani abu ne ya faru? Hafsah ta kalle su da mamaki tace "taɓ wai kardai kuce baku san ƙawarku Zaliha ta auri Mijin Khadija satin da ya wuce ba, har mun je bikin ma ta ce mana sun rabu da Khadija." Wata a cikin su tace "hmmm ai wallah Zaliha ƴar Akuya ce wlh." Munnirah saura kaɗan goyon Amira ya kunce ta dafe da sauri, ta kalle su kamar zata rufe su da duka tace "mun sani to sai me? Dan Allah idan shi ya kawo ku ku ƙara gaba mungode ku tashi ku tafi." haka Munnira ta rufe ido ta kore su. Tun daga ranar kuma aka rasa gane kan Khadija ciwon ta ya dawo Sabo, ihunta da take ya dawo, sosai treatment ɗin ta ya dawo baya don abun yakai bata iya yin Bacci sai an bata magan. Dada najin halin da Khadija ta kuma shiga ta baro Bichi tazo gidan Baba, abun ya yiwa Umma yawa ga jego ga ciwon Khadija, dan ma Munnirah anan take kwana kuma tana taimakawa Sosai tare su ke kula da Khadijah. Ganin irin ƙoƙarin da Munnirah ta ke yi akan Khadija Dada tayi wa Autanta Yusuf Isma'il Bichi (Baba Dr ) sha'awar auren ta, ta dai bar abun a ranta bata furta ba, Amma sam Baba Dr be yi sa'ar mata ba, kwanaki da ta je Abuja akan ciwon ƙafarta ta sake ganin abinda ake faɗa mata akan zaman su, Mace bata zama ko kaɗan kullum sai dai ta yi kwalliya ta yi ficewarta, kullum hankalin ta yana kan kasuwancin ta, sai Mai aiki ce zata bata abinci, shima mai gidan tana gani sai dai inya dawo ya shiga kitchen da kan shi ya soya ƙwai ya haɗa da tea, kullum aikin ke nan, abun dai babu arziki Dada taƙi zaman Abuja ta dawo Bichi tace likita ba shi da mata, ganin Munnirah yanzu saita yaba da nutsuwa da hankalin ta, gashi iyayenta mutanen kirki, ko hidimar da take yi da Khadijah da Umma abin a jinjina mata ne. Kwanci tashi babu wuya a wajen Allah cikin Khadija ya isa haihuwa, tsaf suka shirya suna jiran lokaci.. Ranar wata Alhamis Khadijah ta fara labour cikin dare aka kaita asibiti, cikin ikon Allah suna zuwa Asibitin ta haifi kyakkyawar yarta mace ,Baba ya karɓe jaririya ya ƙankanme, Umma tana masa dariya tace "ka ƙanƙame ta nima ka bani kishiyar tawa na gani mana." Baba ya sake kallon jaririuar yana jinjina girman Allah, sai hawayen farinciki yake share wa, shi da ya ce a zubar da cikin amma kallo ɗaya yayi wa yarinyar ya ji wani iri Santa ya shige shi lokaci ɗaya, kamar abun tsafi baijin ko Khadijah da take yar fari yaji irin wannan son akanta, haka dama Mallam Bahaushe yace wai (Abun cikin ƙwai ya fi ƙwan daɗi). Dadaa ta aiko wa da Umma Baba Rabi ta rinƙa taya ta aiki Saboda saka ruwan wankan jego da hidindumun gida. Bayan sun dawo gida mai jego tayi fes Umma ta tambayi khadija wanne suna

Chapter 24 of 29