Share this page
ce zata aiko min da Atamfofi na siyar mata nima na ɗora nawa akai, nace mata babu damuwa gobe ma kayan za su zo, jirgin safe ne Jidda zai sauka da wuri zan je goben kar masu bada saƙon suyi ta jira na." "Amma wannan mata tana da kirki" cewar Asabe. magajiya ta tari numfashita da cewa "abunda Suwaiba ta yi min ba zan manta ba, duk da dai ba ɗaɗewa na yi ina morar farin cikin ba, amma na samu abun duniya, na samu jari har na samu zuwa nan, wani abun dai ba a tunawa." ****** Suwaiba tana sakin dariya tace "Shege ne maganin ɗan iska, yanzu komai yayi min dai dai. ta faɗa tana sheƙewa da dariyar mugunta. A zaune take akan kujera two sitter a cikin palourn da kallo ɗaya zaka yi masa ka san mamallakinsa mai rufin asiri ne, amma babu wayewar tsari da gyaran da zai bada sha'awa, wata divider ce tabkekiya ta cika bango guda, kayan karau na crystal ne wasu shudaye wasu ruwan makuba, wasu koraye abun gwanin tashin hankali, sai ƙaramar plasma tc da receiver, leather sit ne set din kujerun jajaye labule da centre carpet da centre table duka jajaye. Har yanzu dariyar take tana kallan matar dake zaune a kusa da ita, matar zata yi kamar shekara 33years, fara ce sosai kamar ba pull bahaushiya ba, farin nata har pink take yi, tana da faffaɗar fuska, hancin ta gajere a baje ya ke, lebbanta bakake ne kamar na masu shan sigari, tana da hujin hanci. Kana ganin ta kaga irin riƙaƙun ƴan duniyar nan da babu Allah a ransu. Ta kalleta cike da duniyan ci tace "Na gama da Magajiya na rufe babinta" "kamar yaya? Da Allah ba ni na sha kin bar ni a duhu. Suwaiba tace "ina kai ki Hajara ina ƙawata Magajiya dana tura SAUDIA? Hajara tace "na gane ta" "kinsan na mata halacci amma daga baya ta yi min rashin arziki da yake 'yar Akuya ce, ta nemi duniya da taimako na da taimakon Jaa zuga ta samu, ke kafin ma Jaa zuga har wajen mutumin ki malam na Zaure na kai ta har kuɗina na saka na taimaka mata, amma tana samun abunda take so tayi min halin Dan Adam, har ni Magajiya zata yiwa tsiya, mu da idan ana neman tsiyar wajen mu ake zuwa. Tai maganar tana jefa cingan ɗin data ɓare a bakinta ji kake ƙas ƙas ƙaƙaras.... Tana taunasa cikin Bariki da gwanance wa. Hajara ta bita da kallo bakin ta buɗe tace "ƙawata ina tsoran Allah ina tsoran ki, danfa ke guba ce mai azabtar da rai kafin ta kashe sa." Maganar Hajara ba ƙaramin daɗi da dariya ta bawa Suwaiba ba, kanta ya sake kumbura, ta sake sheƙewa da dariya cikin jin daɗin kalaman Hajara tana kaɗa ƙafa tace "na yi mata talala ne na warware ƙullin dan ubanta ta dawo ƙasa aci gaba da gashi, da ta bi ni a hankali zata daɗe tana jan zaren ta, nima da manufa ta akanta ba haka kawai na taimake taba." cikin ƙosawa Hajara tace "wai ni sai magana kike yi a ƙudundune ki faɗa min mana yadda zan gane abinda kike nufi." "Hmmm Hajara zance ne mai tsaho zan faɗa miki wani lokacin, ni na bata komai wlh irin su Magajiya ba ƴan goyo ba ne" "yanzu dai me kike son faɗa min" Hajara ta tambaya. "me kike ci na baka na zuba? ita kuma wannan tsohuwar maciya amanar Dije kayi na yi? kinsan kuɗina a wajenta wajen 4 million ta ƙi biya na. Hajara tace "na san zancen tsohon labari ne" "to da kanta ta zo wajena tace dan Allah na yi mata hanya ta tafi Saudiyya tunda ina harka da agent za ta biya ni kuɗina idan ta nutsu ta samu kuɗi acan, nace mata babu damuwa kar ta ba da ko sisi zan yi mata komai, in ta dawo ta biya ni kuɗina, amma da sharadin zata ba ni takardar gidanta na nan Ɗorayi matsayin jingina ba zan ƙara linka kuɗi kamar wancan ba, tace ta yarda, tana ta murna, ta bani takardar na haɗa mata aiki (tafiya), na kawo saƙo nace idan babu damuwa ta bawa Magajiya da murnar ta da komai ta karɓe saƙo, na yi wa Magajiya saƙon da sai dai a lahira, banza na ɓata lokaci na a kanta, abinda ta ke harin ba ta san ita ma sharar fage nayi da itaba dan abun ya zo min da sauki. Hajara tace "hoooo mutuniyar amma fah kin yi tsiya. "Haba ƙawata nice fa, Wiwi ce yar gaske (weed) na yi basaja da yan atamfofi. "Ikon Allah inji Hajara. "toh ay Dijen ma kin saka ta a matsalar. Suwaiba tace "matsala?matsala fah kika ce Hajara? kafin na saka ta a matsala ita ta fara saka ni, data bani kuɗina ta girma da arziki da bamu zo nan ba, yanzu shi ne na kira ta, na ce ta shirya gobe ta je ta tari Dije a airport akwai saƙo, maciya amana guda biyu aikina a sauƙa ƙe za a yi min ram da su." Hajara ta jijjiga kai ta ce "kina wuta, uwar ɗakina kin san ta kan tsiya" Suwaiba tayi dariyar jin daɗi ta ce "Hajara kenan mantawa kika yi, na fi shekara 15 da fitowa bariki ai Bariki babu Amana, baka ci ba ma an ci Amanar ka bare kaci. Kinga bari na tura mata lambar Dijen kar na manta" tayi danne danne a wayarta ta ajiye "bari ma kawai na kira dillali ya yi wa gidan kudi na fan shi hakkina, ta yi daria tana miƙawa Hajara hannu suka tafah. ****** Da sallama ta shiga ɗakin hannunta rike da wani orange food flask "sannu Asabe" "Yawwa sannu Magajiya, amma kin dade, ko kin tarar da layi ne? Magajiya na sauke kulan hannunta tace "Wallahi da layi kin san wajen baya rabuwa da mutane Asabe matso mu ci." Shinkafa ce da hadin salad a gefe da Kaza sai laban da ruwa data karɓo musu. Suna cin abincin suna hira har duka gama aka kira Assalatu, suka miƙe suka dauro Alwala suka bubbuga Sallah (babu bin ka'idodin ta) daga gani dai neman kuɗin kawai aka iya ban da ibada, suna sallama Magajiya ta ce "ikon Allah azumin nan na bana shekara ta 8 kenan a Makka, amma kamar wadda aka yi wa baki, ya ci ace na siyi gidan kaina a Nigeria yanzu, nawa dana baro kuma ya lalace ina son gyarawa ko dan uwa ta da ta ke ciki" Magajiya tayi maganar tana kwance zani sai ga wani dan top irin na tsofaffi mai zip a gaba Kaja (ƙaramar jaka da ake zagaye kugu da ita a ɗaura) ta zazzage yan kunne ne da sarkoki da awarwaro na gold ne aciki. Asabe tace "Ay ke kina da kadara ma, wannan tsaf zasu siyi gida" "haka amma wasu ba su fi ni ɗaɗewa ba sun yi manyan gidaje da filaye, a shekarar nan takwas da nayi a Makka ai ya kamata ace na fi haka gaskiya" Magajiya ta faɗa tana tattare ɗankunnayen ta mayar da su cikin Ghana must go, ta ce da Asabe "mu je ki raka ni kawai idan muka dawo sai ki wuce gida. Asabe ta ce shikenan. Da hanzari su Magajiya suka shirya suka nufi motar da zata kaisu Jidda, suna sauka a Jidda sukayi airport. nesa da airport ɗin suka tsaya, matafiya har sun fara fitowa. Scanner ce ta ke scanning luggage ɗin matafiya har takalma ake cirewa ana sakawa a wata roba ta yi scanning idan akwai contraband ko da razor ce sai ya yi kara. Tana ajiye akwaitinta ta ɗauki ƙara sosai tini jami'an tsaro suka zagaye ta, nanfa ta fara zare ido kai tsaye aka jaa ta zuwa wani ɗaki (investigation room) ana ta Larabcin da ba ganewa take ba, nan fa hankalin Dije ya sake tashi, abinka da ƙasar da aka ci gaba nan da nan aka nemi mai jin Hausa ya yi mata translating abinda yake faruwa, ma'aikacin na su mai jin Hausa shi yayi mata bayanin abunda ake tuhumar ta dashi, hankalin Dije a tashe ta fara kuka tana ba nata bane, aka ce ta bude box ɗin, hannun ta na rawa ta buɗe sai ga Weed (Wiwi) kaya guda a tsakiyar kayanta, Dije sai gumi take tana kuka, aka ce ta kira mai kayan. hannun ta na rawa ta kasa rike wayar sai karɓa ma'aikacin su ya yi , yayi dialing number Magajiya da Dije ta nuna masa, Magajiya na ɗaga kiran yayi mata bayanin saƙon ta ya iso daga Nigeria zata iya zuwa ta karɓa yanzu. Jahilci mugun ciwo jikin Magajiya na rawar zata samu kuɗi babu wani godon tunani tace ai gata ma har tazo tana waje tana jiran fitowar Dijen. Nan da nan aka tura ma'aikata suka shigo da ita, tana ta raba idanuwa jikin Magajiya sai yanzu yayi sanyi, aka tasota a gaba har inda Dije take, abun ba ƙaramin tsoro ya bata ba. "Hayya Hajja ku yi mana bayanin kayan waye wannan" da sauri Dije ta nuna Magajiya, Magajiya har zufa ta lullube fuskarta tana numfashi da ƙyar ta hadiyi miyau tace "Wallahi ban san an saka ba ni atamfofi aka ce min zan karɓa" Jami'in ya kalli Dije ya ce "ke meyasa da aka baki sakon baki buɗe ba" da sauri ta tari numfashin sa da cewa "wlh yallabai cewa aka yi atamfa ce" Jami'in tsaron ya kafe su da Ido yace "toh wanda ya baki atamfa shi ya shirya muku haka" yana gama faɗar haka ya fara bada umarnin yadda za'ayi dasu. kasan cewar hukumar ƙasar Saudia ba irin ta Nigeria bace take aka fara ɗaukan hotunan su cameras ta ko ina, mutumin ya tausaya musu, saboda shi kansa yasan daga ganin wannan matan basu isa suyi wannan kasuwancin kasadar ba, kai basu ma da wayewar da zasu yi wannan harkar, dan kana ganin su psychologically kaga gajiyayyu (mabuƙata), saidai shi kansa yasan bashi da yadda zai yi ya taimaka musu saboda duk wanda yasan ƙasar SAUDIA yasan bata ɗaukar wasa akan duk wanda ya shigo mata da kaya irin wannan. Babu wani ɓata lokaci aka yi cike ciken takardu yana tambayar sunayen su yana rubutawa "ke mai saƙo ya sunanki? tana gunjin kuka ta ce "Hadiza Samimu." "ke fah" Magajiya kamar ta shiɗe dan kuka da ƙyar ta ce "Zaliha Sale" Readers hope I am communicating na saka ku a duhu ko???? a cigaba da bi a sannu komai zai warware. 💫 UMAYMAH 💫 ✍️A&A PEN Follow our Whatsapp group via this link https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3 https://wa.me/+2348039352724 VOLUME ONE EPISODE 0️⃣3️⃣ Matashin bakinsa ɗauke da sallama ya shigo cikin falon "Ummi! Fuskarsa ƙunshe da farin cikin yake ƙwala kiran Ummi!! Ummi!!!" ya ji shiru bata amsa ba, sai ya haura sama da sauri yana haɗa steps biyu-biyu. knocking ƙofar ɗakin yake da sallama duka a tare. Wata Kyakkyawar dattiguwa ce ta buɗe ƙofar ɗakin tana murmushi, tace "Na'am Ibni (my son)" Fuskarsa cike da farin ciki, yace "khumn madha ya Ummey(guess what)? Bata bashi amsa ba ta ja hannun shi suka shiga cikin ɗakin ta zaunar da shi a bakin gadon ta. Masha Allah ɗaki ne na Alfarma gado ne ɗan Turkiyya ya sha manyan bedsheets, dressing mirror ɗinta cike maƙil da Turaruka, carpet milk colour, labulayen ma milk ne mai kauri an kunna Ac, sautin karatun qur'ani na tashi a hankali a tashar Saudi live ɗakin sai kamshi yake yi. Cikin ɗoki ya ƙara riƙe hannunta. Ummi ta shafa kanshi, tace "madha (what hapeen)? murmushi ya faɗaɗa akan fuskarsa yace "innahu bi khayr wa - sallim (he is free from danger)". Farin ciki kwance akan fuskarta tace "Alhamdulillah!Alhamdulillah!!Alhamdulillah!!!" Sai kuma ta cika hannun shi ta kalli gabas ta yi sujood shukr, yana daga zaune yana dariyar farin ciki. Yau tsawan shekara 8years kenan ɗan uwan shi daya gaji mahaifin su wajan jan ragamar Kamfanonin daya kafa a Nigeria, rana tsaka ya dawo LEBANON a burkice. Washegari ya fita Sallah tsautsayi ya faɗa mishi yayi accident ta sanadin wasu Matasan Samari suna tseren mota, dai-dai lokacin ya fito daga gida za shi masallaci suka kwashe shi motar ta taka shi sosai, sai da yayi sama ya faɗo da ka. A take jini ya yi ta zuba a wajen, duk wani mahaluki da yake wajen hankalin shi ya tashi, da taimakon mutane aka kai shi asibiti. Samarin da suka buge shi suna ta kuka, dan ba a yi tunanin ma yana da rai ba sai da likita ya tabbatar be mutu ba, amma za su shiga dashi theare gaggawa, kafin aka buƙaci yan uwan shi. wayar shi wani magidanci ya ɗako ya miƙawa Dr. mutumin yana cikin mutanen da suka fara zuwa kansa kusan shine mutum na farko daya fara zuwa kansa lokacin da accident ɗin ya faru kafin sauran mutane suzo su taimaka a kawo sa asibitin, to a lokacin ne ya cire wayarsa daya gani a aljihun sa. Direct aka fara kokarin kiran ƴan uwansa, Allah ya so wayar babu pin aka duba last call ɗin shi an yi saving da Akhi (brother). Yasir yana wajen aiki aka kira shi aka sanar da shi wannan tashin hankali daya same su, babu shiri ya bar abinda yakeyi ya taho asibitin da akace masa nan aka kai ɗan uwan shi. Nanfa ya ji halin da ɗan uwan shi ya ke ciki, har yayi dialing wayar Ummi saiya fasa, dan bayanin da likitan yayi mishi ya firgita shi sosai, likitan ya ce ya bugu sosai a kai, yana tsoron kar yayi rayuwa shi ba mahaukaci ba, shi ba mai hankali ba. Dole idan ya ji sauki sai an yi mishi aiki an bude kan shi an yi mishi aiki. Bayan bugawa da yayi kugun shi ma ya bugu sosai, ƙafar shi ma sai an yi mishi aiki, sannan ya samu karaya a cinyar sa, dan haka zasu fara yin akin raunukan da yaji yanzu, in yaso daga baya inya samu sauƙi saisu duba lafiyar Kwakwalwar tashi. Hankali Yasir sa a tashe ya baro office ɗin likita, a ƙofar ɗakin da aka kwantar da ɗan uwan shi ya tsaya yana ƙare masa kallo, ba a bar shi ya shiga ba sai ta window ya ga halin da dan uwansa ya ke ciki. Har Ummi ta ɗaga kiran ya katse Yasir bai sani ba, saboda tsabar tashin hankalin da yake ciki, Ummi ta yi ta kiran shi Black be ɗauka ba. Baya san tayar da Ummi hankalin da suke ciki, daga ƙarshe kawai saiya saka wayar a flight mode. Likitoci sun buƙaci jinin da za'a ƙara masa Yasir yace a ɗebi nasa tinda jinin su iri ɗaya ne, yana zaune a reception ya rasa abunda ya ke mishi dadi. Sai yanzu ya sallami mutanen da su ka kawo dan uwan shi asibitin tare dayi musu godiya, Samarin da suka yi sanadin accident ɗin ya ce kawai suje sun yafe, abun ya bawa mutane mamaki "sun yafe fa yace “Saurayin daya ke jan motar ya maimaita maganar jikin shi a sanyaye, don shi har ya kira Baban shi ya ya zo, Uban Saurayin ya ɗebo kudi masu yawa ya bawa Yasir. Yasir ya girgiza kai ya ce su yiwa ɗan uwan shi addua ita ya fi buƙata yanzu. "in sha Allah zai tashi." Suka faɗa a tare. Sannan suka yi mishi sallama suka tafi. Ya daɗe a zaune a wajen ya kasa tashi, Dr ne ya ƙaraso inda yake zaunen yace ya taso su je a ɗibi jinin tinda blood group din su ɗaya ne. A take aka dibi jinin shi leda 2, likita ya ce ya ɗan huta ya kawo mishi abinchi ya girgiza Kai, alamar baya buƙatar sa. Likitan ya kalle shi da kulawa yace "Sadiqi Anta bihajah illayh (my friend you need it)" Da kyar ya lallaɓa Yasir ya ci abincin, likitan mai faram faram yana ta kwantar mishi da hankali, yawa Yasir ya kwantar da hankalin shi, suna ganin cases da yawa har wanda suka fi wannan, dan haka ya kwantar da hankali shi in sha Allah ɗan uwan shi zai warke. Yasir ya dai kalli Dr ne kawai. Likitan ya gane kallon da Yasir yake masa, sai yayi murmushi ya dafa kafaɗar sa, yace "Asdiqni kull shay, sayakun bi khayr in sha Allah (believe me everything will be okay)." Yasir ya amsa da "in sha Allah." "In sha Allah" Dr ya ƙara maimaitawa yana masa murmushi giving him hope. "Ma ismuk? (what is your name) Yasir ya tambayi Dr. Likitan yace "ismy Huzaifa bhin Abdallah, wa Anta (and you)? "Ismiy Yasir bhin Fadoul Al-arabey "Al-arabey" Likitan ya sake maimaita sunan cikin mamaki sai kuma yace "Ma alaƙatuka bil marda? (what is your relationship with the patient )" Idan Yasir ya cika da hawaye yace "innahu Akhi, ibni Ummi (he's my biological brother)". Yasir ya miƙa mishi hannu yana cewa "shukran laka ya doctor" (thank you doctor). Suka fito tare da Dr, Yasir ya wuce gida don ko ya zauna ba barin shi shiga za a yi ba, sannan yana buƙatar ya sanar da Ummi halinda suke ciki. Readers hope ku na ganewa? duka shimfida ce ba mu shiga gundarin labarin ba, kudai ku biyo mu a hankali yanzu za'a fara. 💫 UMAYMAH 💫 ✍️A&A PEN Follow our Whatsapp group via this link https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3 https://wa.me/+2348039352724 VOLUME ONE EPISODE 0️⃣4️⃣ KANO STATE No 40 Sultan road Tafkeken gida ne da kallo ɗaya zaka yi mishi kasan cewa mamallakin gidan mai sukuni ne (mai wadata), gate ɗin gidan milk colour ne da katuwar haraba da tasha interlock, daga hannun dama ɗakin maigadi ne da garage ɗin motoci wasu a rufe da Tampol guda uku a buɗe, kana shiga main entrance ɗin sliding door tana kallo ka, Ƙaton palour ne da wani palourn a jikin shi, Daga hannun dama idan ka Mike sirrin passage ne sai wani palourn, ka yi gaba kuma kitchen ne da store sai ƙofar baya ta shiga kitchen, duka palour 3 ne a ƙasa sai bedroom guda ɗaya da toilet ɗin shi aciki, sai bedrooms 4 a sama kowanne da toilet a ciki tare da ƙofar baranda, ko wanne ɗaki zaka iya buɗewa ka sha iska, gidan Alhaji Muhammad Ali Bichi kenan. Wasu ƴan ƙwailayen matasan ƴan mata ne suka Shigo cikin falon da gudu ko sallama babu, suka hau kokawa da uniform din islamiyya a jikin su. "A'a bismillahi, daga dawowar ku zaku fara raba hali" muryar wata Dattijuwa da zata kai a ƙalla shekara 50 ce ta katse su, Umma ke nan wankan tarwaɗa ce tana da matsakaicin tsaho, kyakkyawar gaske da alama lokacin kuruciya ba ƙaramar kyau aka zuba ba. Umma na ƙarasowa inda suke tace

Chapter 2 of 29