za a saka mata, Khadija tayi shiru tana tunin wani abu ta sake kallon ƴar da dake kwance a cinyarta cikin kayan baby pink masu kyau, a hankali kamar bata son faɗar sunan tace "Fatima Umaimah."
Baba najin sunan da ce tana son a sawa babyn yace "ni dama tuni nayi mata huɗuba da Fatiman." umma ta ce "ko za a sanar da Babanta haihuwar?" Baba ya bankawa Umma wata harara kamar zai rufe ta da duka ya hauta da faɗa saida yayi wa Umma kaca kaca yadda kasan ita ce Tahir ɗin da kanshi.
Haihiwar Umaimah ta zo wa Baba da buɗi mai yawa, haihuwarta da sati biyu suka koma gidansu na Sultan road.
Shaƙuwa sosai ta shiga tsakanin Isma'il da Umaimah, sosai ya ke ɗaukan ta, da ya ji kukan ta ko cikin dare ne saiya fito, shi ne dan renon ta inka ganta a hannun wani tom sai dai in yana makaranta, idan yaje makaranta kuwa haka zai zo da sweet da yawa duka na Umaimah ne.
Saida Umma taga abun nashi yayi yawa tayi mishi jan ido akan indai ba zai na bawa Amira ba toh Umaimah ma ba za a bata ba, badan yaso ba yake bawa Amira itama, amma ƙuru ƙuru yake nuna masu banbanci.
A haka Khadija taci gaba da renon Umaimah har ta yaye ta, a lokacin ne kuma Baba yaso ta koma makaranta amma ina duk yadda taso tayi karatu abun yaƙi yiwuwa dole sai haƙura akayi.
A hankali rayuwa nata tafiya lokaci nata turawa su Umaimah harsun fara zama ƴan mata an shiga ƙaramar secondary.
A gidan Alhaji Muhammad Ali Bichi kuwa an daɗe da bunne maganar Tahir da duk wani abinda ya shafe shi.
Cikin ikon Allah aka yi Auren Munnirah da Baba Dr, burin da su ka ci su biyu na sama cikakkun lawyers Munnirah ce ta cika wannan burin, Iyayen Munnirah sun daɗe da komawa Abuja da zama.
Da taimakon Allah, da jajircewar iyaye da taimakon Munnirah Khadija ta dawo dai-dai, filin da Baban ABU ya bata da aurenta shi Baba ya siyar aka haɗa da gold ɗin ta aka siya mata mota, ta shiga makarantar interior decoration, Daddy ya bata shago a Zoo Road ta fara sana'a tinda karatun yaƙi yiwuwa.
To kunji wannan shine labarin Khadijah da abunda ya faru da ita.
******
💫 UMAYMAH 💫
✍️A&A PEN
Follow our Whatsapp group via this link https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3
https://wa.me/+2348039352724
VOLUME ONE
EPISODE4️⃣8️⃣
LAGOS
Cikin kwanakin daya ragewa su Umaimah su koma Kano ba ƙara min Sabo Umaimah da Sa'ad suka yi ba, ta samu makwafin Uncle Ismanta a gidan Daddy, sosai Sa'ad yake biyewa shirmen ta, yanzu kafin kaji ta kira kowa a gidan kaji tace Uncle Sa'ad. Sun sha yawo sunga garin Lagos da kyau sosai Sa'ad yake fita dasu susha yawo anyi ciye ciye.
Tin daga ranar da Umaimah suka haɗu da Fahad a dining basu sake haɗu wa ba. Sai dai sometimes takan hango shi a farfajiyar gidan a zaune akan kujerar roba. Hutun su ya ƙare ranar Monday zasu koma makaranta su Umaimah ƴan mata za'a shiga SS1 sai ɗoki da fi'ili ake, yau jumma'a ta kama gobe su Umaimah zasu koma Kano tare dasu Daddy. Aunty Surayya bata koma ba ita ma sai goben zatabi jirgin safe su Daddy kuma jirgin yamma zasu bi. Umaimah sai ɗokin komawa gida take, Uncle Isma yasha tsaraba, komai ta ɗakko sai tace "yawwa Uncle Isma yana son wannan ma. "Sa'ad yasha dariyar shirmen Umaimah har ya gode Allah.
Fahad na kwance a ɗakin sa Sa'ad ya shigo. Fahad ya ɗaga kai ya kalle shi, "wash Allah na gaji wallahi." Sa'ad ya faɗa yana zama akan kujar dake kallon Fahad. "Kaifa ɗan renin Sense ne ina magana bazaka kula ni ba kamar baka ganni ba."
"I'm not a parrot." Fahad ya faɗa ƙasa ƙasa. Sa'ad ya buɗe baki zai yi magana sai kuma ya kwashe da dariya "zaka ga parrot guy gobe war haka kana Kano jibi kuma kana Bichi, can't wait naga yadda zaku kwashe da Dada."
Fahad najin haka ya miƙe zaune shi wallahi gaba ɗaya ma ya manta da gobe Daddy yace zasu tafi Kano, "oh!" Ya dafe kanshi, "Aure." Ya furta kalamr Auran kamar baya son faɗa. Sa'ad ya baro inda yake yazo kusa da shi ya zauna kafaɗun su na gugar juna, "kasan me? Just open your heart bro I'm sure zakaga matarka, all these girls dake binka kamar zasu mutu ka basu dama mana, you know tinda Dada tayi maganar nan Aure babu fashi, so is better for you to do the right things for yourself."
Fahad ya juya kansa ya kalli Sa'ad, sai kuma yayi smiling ya girgiza kai.
Sa'ad na baro ɗakin Fahad ƙasa ya sakko ya tadda mutanen gidan gaba ɗaya a folo, "a'a yaushe kika shigo Maman boy?" Sa'ad ya faɗa yana kallon Aunty Amal da bata jima da zuwa ba, "naɗan jima fa da shigowa ina Dattijo?" Sa'ad yana zama a kusa da Yaya Surayya yace "Allah yasa yajiki da wannan sunan babu shakka haka zaki koma gidan ki baku gaisa ba." Mami ta girgiza kai "wai ina mai gidan ya shiga ne kince dashi kika zo kuma ban ganshi ba?"
"Yana wajan Umaimah." Aunty Amal ta faɗa. Suna cikin haka Umaimah ta fito daga kitchen hannunta riƙe da plate, Mami na ganin ta ta buɗe baki "Umaimah me nake gani haka, wannan ƙaton saurayin kika goya shekara 4 fa, Maza maza sauke shi yayi miki nauyi, wannan ai sai ya buɗa miki jiki." Umaimah na dariya tace "Allah Mami bashi da nauyi." "Eh naji sauke shi dai."
Wajan Sa'ad tazo ta miƙa mishi plate ɗin indomien "Uncle Sa'ad riƙe min na sauke shi." Sa'ad ya karɓi plate ɗin ya kallon indomien yadda tasha kifi da kayan ganye yadda kasan ba indomie ba, ga wani ƙamshi dake tashi dole yasa mutum haɗiyar yawu. Sunkuya wa tayi Boy ya sakko dama bada zani aka yi goyon ba. Yana sakkowa yayi wajan Maman shi dan ƙiwa gare sa baya bari kowa ya ɗauke sa musamman mata gwanda ma Maza bai fiya yi musu ƙiwa ba, amma wani ikon Allah baiwa Umaimah ƙiwar ba suna shigowa ta miƙa masa hannu yaje wajan ta.
Sa'ad ya kalli Umaimah data gyara zama a kusa da shi zata fara cin indomien ta, yace "daughter waya dafa miki wannan delicious ɗin?" Ta buɗe baki da mamaki "Uncle ni nayi fa." Sa'ad ya sake kallon ta sai kuma ya kalli indomien kamar ba zai yadda ba sai kuma yace "really?"
"Yes Uncle, ka tambayi Mami da Aunty ma zakaji, jiya ma nina dafa mana jellop ɗin taliya, ruwa kaiwa Deborah ta zuba min." Umaimah ta faɗa with so much proud of herself.
Sa'ad ya kalli Mami tayi dariya tace "wannan yar taka expert ce fa." Aunty Surayya ta dora da cewa "ai da Umma zata bani Umaimah dana more ƴa." "Saɓo kike yi Surayya, wannan ita ce zuciyar Umman Khadija." Aunty Amal na dariya tace "naga alama."
Umaimah da Sa'ad tare suka ci indomien yana ci yana santi, "anya daughter baza mu buɗe gidan abinci ba kuwa, gaskiya ban taɓa cin indomien mai daɗin wannan ba." Umaimah sai wani blushing take.
Mami ke tambayar inda su Amira suka shige Aunty Surayya tace suna ɗakin Hidaya.
"na rasa abinda suke shuka wa yaran nan basu da aiki sai shiga ɗaki su kulle" Mami ta faɗa tana miƙe wa ta yi kitchen ta duba masu girkin rana dan sha biyu harta wuce. "Hmmm wai Yaya kinsan me suke yi a ɗakin Hidaya?" Umaimah ta faɗa tana kallon Yaya Surayya. "A'a daughter saikin faɗa." "To in faɗa miki makeup suke koya online har practical suke yiwa kansu."
Aunty Amal tace "banyi mamaki ba Hidaya da jarabar san kwalliya yadda kasan aljana haka take, ashe itama Amiran haka take, ai sai suyi tayi." Yaya Surayya tayi dariya "a'a barsu suyi abinsu ƴamma tanci saida kwalliya."
Wajan ƙarfe biyar Amal ta shirya zata tafi gida, a farfajiyar gidan suka hangi Fahad a tsaye a jikin mota yana amsa waya, Surayya ta zunguri Amal "ga ƙanin ki can fa."
Amal ta buɗe baki "wa? Taɓ wannan ai nabar masa girman, bakiga yadda ya sake zama wani garjeje ba, yayi biyun Sa'ad fa."
Wajan shi suka ƙarasa, Boy yana ganin shi ya saki hannun Maman shi yayi wajan shi da gudu, wani cool murmushi Fahad ya saki, ya ɗaga Boy sama, Yaron ya fashe da dariyar murna.
Dawowar su wajan sau uku Fahad yaje gidan Amal kuma badan ita yake zuwa ba, kawai yana zuwa ne saboda Boy, haka zaije gidan ta harya fito tsakanin shi da ita baya wuce afternoon or evening, dan Fahad yace ma good afternoon in complete ma gani yake words ɗin sun yi masa tsayi, gashi daman ba wani shiri suke da Amal ba dan ita Allah ya zuba mata surutu ga neman maganar jaraba shi kuma baya shiri dame hayaniya.
Yadda Fahad ya riƙe Boy fuskar sa cike da murmushi zaka gane ba ƙaramin daɗin ganinsa yaji ba, yaja hancin Boy "yaushe kazo." Cikin gwarancin magana Boy yace "da Mahmah cazo."
"Malam Sama'ila ina yini inka gama da ɗan naka." Muryar Yaya Surayya ta katse su. Juyowa yayi ya kalle su, "evening." Ya faɗa a gajarce, Aunty Amal tayi murmushi a ranta tace "Allah ka nuna mana randa Fahad zai sake yayi hira damu kamar sauran ƴan uwa, dan Allah ji wata gaisuwa wai evening, wannan inda ciwo ma harda hali yasin."
Fahad daga gaisuwar bai sake bi takan suba ya maida hankalin shi kan Boy.
💫 UMAYMAH 💫
✍️A&A PEN
Follow our Whatsapp group via this link https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3
https://wa.me/+2348039352724
VOLUME ONE
EPISODE 4️⃣9️⃣
Suna tsaye motar Aisha ta shigo gidan Amal da Surayya sukabi motar da kallo dan ba ɗaya daga cikin motocin gidan bace. Saida ta gyara parking da kyau sannan ta fito sanye take da abaya army green direct wajan su Aunty Surayya ta kasaro suka gaisa kamar sun san juna abinka da wayayyu.
Fahad yaji lokacin da Aisha ta iso wajen amma ko kallon inda suke baiyi ba.
A'isha ta kallesa taga bashi da niyar nuna yasan da ita a wajen, a ranta taji wani iri amma yata iya da aiki zuciya. Amal ta katseta mata tunani da cewa "ki shiga Mamin na ciki."
Aysha ta sunkuyar da kanta ƙasa kunya ta kamata a ranta tace "ni Aysha maiya kawo ni wajen shi nema bayan yace min kar nazo." Sai yanzu taga wautar ta da ƙuruciyar ta, gashi tazo ya dizga ta ya nuna kamar bai san taba.
Yaya Surayya ta dafa ta "hi wa kike nema ne?" Aysha kunya kamar ta nitse tace "uhm....uhm... Actually i came to see Isma'il uhmmmmm i mean Mr Bichi.? Ta ƙarasa maganar tana nuna Fahad.
Amal da yaya Surayya bushewa suka yi a tsaye saboda tsabar mamaki, Amal ta kasa hakuri tace "if i understand you very well, you mean you come to see Isma'il right?" Aisha ta ɗaga kai tana kallo Fahad da har yanzu bai nuna yasan mai yake faruwa ba.
Amal ta kalli Yaya Surayya, yaya Surayya ta kalli Amal suka gyaɗa kai a tare. Kamar haɗin baki suka ce "wonder shall never end."
Amal ta kalli Yaya Surayya tace "oh kinga nayi mantuwa a ciki muje na ɗauka, suka juya cikin gidan suka bar Aysha da Fahad anan.
Suna tura ƙofar falon Sa'ad na shirin fitowa suka turashi ciki, ya tsaya yana kallon su "how far? Sister baki tafi ba."
"Hey Mal manta da tambayar na tafi ko ban tafi ba, wace a waje tazo wajen Fahad please?" Amal ta faɗa tana nuna Ƙofar waje. Kafin Sa'ad yayi magana Yaya Surayya tace "wai da gaske yau mace ce tazo neman Fahad har gida?"
Amal ta sake ɗorawa da cewa "taɓ to wai how? Taya ya ma? rascal ashe yana magana rashin M ne kawai yasa yake mana yanga, taɓ Yaya kinga yadda take kallon shi kuwa."
Sa'ad ya dafe kai "okay, okay yanzu zaku bari nayi magana ko na barku da expectations ɗin ku?"
"See you jo, Fahad fa akace mace ta zo nema ba dole muyi mamaki ba." Amal ta faɗa. Yaya Surayya tace "okay yanzu dai tell us please who is she?"
Wani tunani Sa'ad yayi kawai sai cewa yayi girlfriend ɗin shi ce."
Surayya da Amal suka zare ido a tare "yes haka nace is his girlfriend."
"Amma sai naci ƙaniyar Dattijo duk randa na kuma yi masa magana ya gyaɗa min kai." Yaya Surayya ta faɗa tana zama akan kujera.
"Wato he knows how to talk with his woman. But his sisters akan su ciwan shi ke tashi, lallai Fahad dan renin wayo ne." Sa'ad ya harari Amal da tayi maganar "see you kamar baki san condition ɗin shiba, dama jin gulma ne ya dawo dake, to da wasa nake friend ɗin shi ce, tin da muka dawo take roƙon shi zata zo yana avoiding ɗin ta."
Yaya Surayya tayi dariya tace "lallai wannan friend ɗin muna bukatar ta, dan Allah jeka shigo mana da ita yau dai Mami taga budurwar ɗan ta Sama'ila, oh! Sorry like you said friend ɗin shi."
Sa'ad bai sake bi takan suba ya fita.
Yana fitowa ya hangosu har yanzu Aisha na tsaye, idanta ya cika da ƙwalla, har yanzu Fahad baiyi mata magana ba, "Please Fahad kayi hakuri idan zuwa na ne ya ɓata maka rai, i just want to see you ne shi yasa na kasa holding kaina, but I'm so sorry please." Tayi maganar kamar zata fashe da kuka. "Am i not telling you karki zo?"
"You are but........" "Excuse me please." Fahad ya katseta yana juyawa zai wuce suka yi karo da Sa'ad dake tsaye a bayan su, sam basu yi noticing zuwan shi wajen ba.
Aysha na ganin shi tayi sauri ta haɗiye kukan daya taso mata, tayi murmushin dabai kai zuci ba "good evening Sa'ad."
Fahad ya zagaye shi ya shige cikin gida. Sa'ad yabi bayan shi da kallo sai kuma ya dawo da hankalin shi kan Aysha, "kiyi hakuri haka yake, so karki wani damu he likes you kawai yanayin shine haka." Aysha tayi yaƙe tace "i understand, let me go home, thank you Sa'ad."
Ya dakatar da ita, badan Aysha taso ba Sa'ad yasa ta suka shiga cikin gida, dan gaskiya taji ciwon abinda Fahad yayi mata yau, amma duk da wannan wulaƙancin da yayi mata wani sabon sanshi taji yana shiga zuciyar ta.
Fahad na shigo wa Boy yayi wajen Maman shi shi kuma ya wuce sama ransa a ɓace, yana shiga ɗaki yaja tsaki yafi a irga, "i hete matan da basu da class." haka yayi ta maimaita wa (Repeatedly).
Sa'ad ne a gaba sai Aysha a bayan shi suna shigowa cikin falon Mami na Sakkowa daga sama, da fara'a su Amal suka karɓi Aysha, suka sake gaisawa.
Aysha ta zamo daga kujera ta gaida Mami. Mami da fara'ar ta amsa tana tambayar su Yaya Surayya "bakuwa mukayi ne?"
Amal tayi tsagal ta ce "baƙuwar Fahad ce fa Mami." Yaya Surayya ta harari Amal "Allah kedai bazaki girma ba Amal, am Mami wannan abokiyar karatun su Sa'ad ce, shine tazo mu gaisa." Yaya Surayya tayi maganar tana kallon Aysha data sunkuyar dakai.
Cikin jin kunya Aisha ta sake gaida Mami.
Aysha bata bar gidan ba saida Amal ta karɓi number ta, Sa'ad ya rakata ta tafi.
Yana dawowa suka ɗora da zancen ta Mami dai ta gane Aysha baƙuwar Fahad ɗin ce da gaske kamar yadda Amal ta faɗa, ita kanta tasha mamaki wai Fahad ke kula mace, kuma har tazo gida wajen sa, lallai wannan jaridar mai tsada ce. Sa'ad dai komai suka ce bayan Fahad yake bi, "anya kuwa Sa'ad ka taɓa ƙin bin bayan Fahad?" Amal ta faɗa tana kallon shi, "dama abinda ya hanaki tafiya ke nan ai gulma, sai kiyi tayi." Ya tashi ya haye sama a ranshi yace "nima bari naje na ɗan kunna shi."
Washegari
Daddy da iyalanshi suka baro Lagos, Ibrahim da Uncle Isma ne suka zo ɗaukar su a airport, Umaimah na ganin Uncle Isma ta rungume shi suka hau murnar ganin juna.
Tarba mai kyau suka samu a wajen Umma, Baba da Daddy suka Rungume juna, Umaimah ta maƙale wa Umma, sai kuma ta sake ta tace "Umma ina Sasi na." Umma bakin ta har kunne tace "tana nan zaki ganta."
Su Daddy basu jima da shigowa ba Khadija ta dawo daga shago. Taji daɗin ganin su, Daddy sai saka mata albarka yake yi dan Ahmad Lamiɗo ya faɗa mishi yadda suka yi da ita, bayan zuwan sa na farko ya sake zuwa har sau biyu kan ya koma Lagos wajen aiki.
Maganar Auren su har tayi nisa dan iyayen sa tuni sukaje Bichi wajen Hakimi, an tsaida nan da 3 months za'ayi auren in yaso sai su wuce India tare kamar yadda Angon ya buƙata, yanzu babu lefi tana ɗan sakewa dashi, haka kawai Allah ya ɗora mata wani irin tausayin shi. Kusan duk lokacin da suka yi waya takan ce "hope kana shan maganin ka?" Wanda wannan tambayar tata ba ƙaramin kashe Ahmad take ba, shi kaɗai zaka ga yana murmushi, wanda hakan yaja abokan aikinsa suka saka masa suna murmushi garaɓasa.
Umaimah da Uncle Isma tini suka ƙule a ɗakin shi suna ta hirar yaushe gamo, Umaimah sai labarin Lagos take bawa Isma'il, labarin Uncle Sa'ad da Uncle kurma (Fahad) kamar yadda tasa mishi sunan, "Ina faɗa maka Uncle Isma ranar da Daddy ya bar shi ya mareni da basamuden hannun shi, Allah da sai dai kuji ance hello Muhammadu sai haƙuri fa Allah yayi wa Fatima Tahir Al-arabey rasuwa sanadin physically accident ɗin data samu a dining table." Isma'il mai zai yi inba tariya ba, "Umaimah bazaki kashe ni ba, tsakani da Allah a ina mari yake kisa, kawai daga ya bare ki sai ki mutu." Isma'il ya faɗa yana dariya. "Hmmm Uncle Isma bazaka gane ba, kaga girman hannun shi kuwa? Taɓ to Allah yayi goman na Uncle Aliyu." "Taɓ Allah ya yafe miki Umaimah."
"Allah ina faɗa maka."
💫 UMAYMAH 💫
✍️A&A PEN
Follow our Whatsapp group via this link https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3
https://wa.me/+2348039352724
VOLUME ONE
EPISODE 5️⃣0️⃣
Umaimah na fitowa daga ɗakin Uncle Isma tayi sama, Umma da Mami na zaune suna hira ta shigo ɗakin da sallama, Umma ta kalle ta "ina kika shige ne? Su Hidaya nata neman ki." Tana zama a kusa da Mami tace "ina wajan Uncle Isma, Yawwa Umma ina Baba? "Sun fita shida Daddyn ku." Umma ta bata amsa,
"Lah saƙo fa zan bashi, Siyama aramin wayar ki na kira shi na faɗa mishi."
"Koma menene ki bari ya dawo mana bana son wutar ciki." Umma ta faɗa, Umaimah ta zumɓura baki gaba "ai kawai Mami inaga binku zanyi mu koma Lagos, kinga abinda Siyama take yimin daga dawowa ta." Mami tayi dariya, ta shafa kanta "rabu da Siyama karɓi wayata ki kirasa, tinda bata lallaɓa ki saimu koma kawai." Umaimah ta karɓi wayar Mami ta fara saka number wayar Baba data haddace ta kamar fatiha, "Mami da wasa fa nake ba binku zan kuma yi ba gaskiya kawai faɗa nayi." Mami ta girgiza kai "nima nasan haka Mamana." Umma ta harare ta "au kin fasa bin nasu ke nan?" "Umma Allah kar kisa na cewa Daddy zan koma Lagos da zama." Umma tayi banza ta rabu da ita, dan tasan Umaimah bata san gatse ba yanzu saita faɗa masa.
Baba na ɗaga wayar tace "Baba nice." Daga ɗaya bangaren Baba yace "a'a uwata ina jinki lafiya?"
"Baba kasan me zaka tahomin dashi?" Umaimah ta faɗa tana murmushi kamar Baba yana ganin ta, "a'a Uwata saikin faɗa." "Yawwa ina kifin nan da kake siyo min mai ƙarau ƙarau?"
Baba yace "karfasa." "Yawwa dan Allah Babana rabin raina shi zaka siyomin, yawwa Baba kuma ka siyamin Bama da tomatoes ketchup."
"To an gama uwata duka zan siya miki in sha Allahu." Baba ya faɗa, "Babana Allah ya ƙara maka lafiya da kuɗi masu albarka." Baba yana dariya yace "Amin ya Allah Uwata."
Umaimah na kashe wayar ta bawa Mami wayar ta "thank you Mami" Umaimah ta faɗa, tayiwa Mami peck a kumatu ta fita daga ɗakin, Umma tace "au abun haka ne zamu haɗu ne."
Mami tayi dariya, "ikon Allah ke nan Maman Khadija yanzu wa zaice Khadija ce ta haifi wannan? Gaskiya wannan yaron ya yi wa kanshi."
Umma ta cije baki "ai wani lokacin inna tina Tahir ne uban Umaimah sai naji wani ɓacin rai ya kama ni."
"To ya za'ayi bawa baya wuce ƙaddar shi, kwanaki Daddy yake cemin yana so ya yiwa Baban Khadija magana akan ya kamata su nemi iyayen Tahir kodan su san da zaman Umaimah saboda halin rayuwa."
"Nima na daɗe ina tunanin haka amma zafin da Baban Khadija ya ɗauka yasa ban taɓa kwatanta faɗar maganar ba, kinsanshi in yayi fushi abun sai Allah." Umma ta faɗa cikin jimami.
Baba ya kawowa Umaimah duk abinda tace ya siya mata, ta karɓa da murna ta rungume shi " Baba thank you Allah ƙara maka sona." Baba yayi dariya, Daddy ya miƙa mata ledar ice cream, bakin ta kamar zai rabe biyu dan murna ta karɓa" Daddy Allah ya ƙara buɗi mai yawa."
"Amin Amaryar."
Washegari da safe aka haɗu akayi breakfast kowa yazo wajen banda Fahad, Daddy ya kalli Sa'ad, "ina Dattijo ne?" "Yana ɗaki Daddy kasan ba zai fito ba." Daddy zai sake magana Baba ya riga shi da cewa "in an gama Ibrahim ka karɓi abinci ka kai masa, Khadija in an gama cin abincin ki haɗa na Dattijo ki bawa Ibrahim."
"To Abba" Khadija ta amsa.
"Wai ina Amaryar tayi ne? Daddy ya tambaya yana kallon su Amira, "Daddy suna kitchen ita da Uncle Isma." Amira ta faɗa. "Okay Maza kirawo su su zo suci abinci." Hidaya tace "Daddy sunce bazasu ci ba, indomie Umaimah zata dafa musu, wai wani sabon style ɗin dafa indomien ta koya a wayar Mami." Mami ta kama baki "haba no wonder, ashe shi yasa naga an cika min waya da videos ɗin girki."
Yawwa Uncle Isma wannan zaka yanka mana. Umaimah ta faɗa tana miƙa wa Isma'il karas da bens. Gaba ɗaya sun har gitse kitchen ɗin, saida suka gama yayyanka duk abinda zasu yi indomien dashi sannan suka rufe komai a tsare yadda suna zuwa kawai zubawa zasuyi, Umaimah ta kalli Ismael tace "Uncle Isma babu bread ɗin da zamuyi Honey bread ɗin dashi yanzu ya zamuyi?" Islam ya kalli agogon kitchen ɗin ƙarfe 9am saura, "kinga bari na duba mana shagon baya in suna nan saina siya mana naga suna kawo bread masu kyau."
"Tom kafin ka dawo na share kitchen ɗin kana zuwa sai mu fara, dan Allah kayi sauri yinwa nake ji." Uncle Isma yana fita Umaimah ta fara share kitchen ɗin, tana kwashe sharan Uncle Isma ya dawo da bread ɗin. Girkin Umaimah ta ɗora sunayi suna hira, nan da nan kitchen ɗin yadau ƙamshi, Sa'ad ya leƙo kitchen ɗin yace
"daughter gaskiya zanci wannan delicious ɗin, ina jira in an gama a sammin nawa." Ya faɗa yana mata murmushi.
Cikin mintina ƙalilan suka gama Umaimah ta ɗakko plate ta zuba musu nasu sannan ta ɗakko wani ɗan ƙaramin plate ta zuba wa Sa'ad, bread ɗin ta ɗakko ta shirya shi akan wani plate ɗin daban, "gaskiya wannan bread ɗin ya burge ni, dubi yadda kika haɗa shi, Allah kamar baci za'ayi ba,nifa harna matsu naji inaci, dan Allah kiyi sauri kije kiyi wankan ina jiran ki a falon." Uncle Isma ya faɗa, suka fito daga kitchen ɗin Umaimah ta wuce sama da
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 25 Chapter of 29