Share this page
wannan su yake san Umaimah ke kina ganin wannan soyayyar kin san dan sanda suke miki ne suke ƙaunar ta bawai dan Uban taba. ki ɗaure ki saka musu da kwantar da hankalin ki da sakin zuciyar ki kema kiyi rayuwar farin ciki kamar ko wacce mace mai ƴanci, astahfirullah banda bawa baya muce ƙaddarar sa wa zai kalle ki yace kin haifi Umaimah yanzu fa kike 30s ɗin ki kina da ƴar shekara 13, yanzu baga muba nema fa muke bamu samu ba, dan Allah kodan wannan ki kwantar da hankalin ki ko muma namu hankalin ya kwanta." Tabbas tasan duk abinda Munnirah ta faɗa mata gaskiya ne, Iyayen ta sunyi mata komai dan haka ta ƙudurce wa ranta daga yanzu zata fara yaƙi da zuciyar ta, zakuma tayi facing reality kodan farin cikin iyayen ta. Ta ɗan saki murmushi ta share hawayen fuskarta, saida ta kama hannun Munnirah cikin sanyin muryarta ta halitta tace "Uwata, ƴar uwata, ƙawata kuma Aminiyata, in sha Allahu daga yau zan yi iyaka ƙoƙarina na bawa kaina farin ciki da iyayena gaba ɗaya i promise you my sis zakiga canji." Munnirah ta sake riƙe hannun Khadijah a cikin nata cikin jin daɗin maganar Khadijah tace "Allah yasa my sis, haba har naji relief da ƙarfin gwiwar fara shirin biki." Khadijah ta harare ta, "sannu areni muje biki ni mijina baya faɗa, ai dai kya jira kiga mijin ko?" Munnirah na dariya tace "Allah tin daga jin sunan sa na nasan da ƙarfin sa yake tafe, wayyo kedai Allah ya mai da mu Kano lafiya." Khadijah ta girgiza kai, "my sis bazaki canja ba." Suka yi dariya a tare. "To gafaran kudai jama'a, nace na iya shigowa yanzu? Uzuri ne ya kawo ni, tin ɗazu nake tsaye ina jiran a bani izini na shigo kada ace laɓe nake yi.? Dada ta faɗa tana tsaye daga bakin ƙofar. ko yaushe ta shigo oho? "Saiki shigo ai koma meye ai kinji." Dada ta riƙe baki tace "inye Allah Hadiza daga zuwan Miji har kin yi baki? A lallai Ahmadu da ƙwarin ka kake tafe." Munnirah dai sai dariya take musu ganin yadda Khadijah ta wani cukwiykwiye fuska. Dada ta ɗau abinda ya kawo ta ta fice tabar musu ɗakin. Khadijah ba ƙara min ƙoƙari tayi ba wajan danne zuciyar ta da nuna babu komai ba, kuma taga am fanin hakan, dan suna shigowa Babban falon Hakimi ita da Munnirah, inda anan ne za'a ci abincin dare kamar yadda Dada ta tsara, taga idanun Baba da Umma akanta ko wannen su ƙoƙarin yake ya gano yanayin da take ciki. Tana ganin yadda Umma ta sauke ajiyar zuciya data ganta haka Baba saida yaɗan murmusa. A ranta ta sake godewa Munnirah dan ita ce tasa ta sake wanka tasa kwalli ta canja kaya. Daddy ke tambayar ina su Umaimah, Dada tace "barsu can su ƙarata gobe da safe Sarkin Mota yaje ya ɗakko su. Hakimi yace "Bintu kodai kishi kike yi ne?" "Inafa kishi mai gina, wannan in suka dawo yanzu ciwon kai za su saka." "da muka je duba Adda Balki ƙin biyo mu su kayi." Umma ta faɗa. Dada ta girgiza kai "Inafa zasu biyo ku sun samu waje suna baje kolin su san ransu." Bayan an gama cin abinci, Hakimi yaji duk abin da suka tattauna, yaji daɗin labarin daya samu na Mijin da Daddy ya yiwa Khadijah, ya sake yi musu nasifa tare da saka musu albarka. Kafin a tashi saida Dada ta sake dawo da maganar su Sa'ad akan lallai ne fa suna dawowa su kawo matan Aure. Daddy yace "in sha Allahu Dada za'a yi yadda kika ce." Washegari bayan Sallar Azahar suka baro Bichi cike da tsaraba, ƙarfe uku mai kyau a cikin garin Kano tayi musu. Baban ABU yayi wa su Baba Sallama ya wuce Zaria shida drivern shi, Baba Dr ma suka wuce gida. Ibrahim ya wuce gida dasu Umma, Baba da Aliyu kuma suka wuce dasu Daddy airport dan jirgin ƙarfe 4pm zasu bi. 💫 UMAYMAH 💫 ✍️A&A PEN FOLLOW OUR WHATSAPP GROUP VIA THIS LINK https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3 https://wa.me/+2348039352724 VOLUME ONE EPISODE 2️⃣2️⃣ Tahir da ƙyar ya iya gane gidan Baba Isah dake Ƴankaba Sabaru bayan makarantar Wamy, duk sai yaga wajan ya canja mashi da sabbin gine gine. A ƙofar gidan Baba Isah ya sauka yanata kokonton gidan ne kuwa, saboda an sake gyara gidan anyi masa gini na zamani fiya da yadda ya san shi a baya. Gate ɗin gidan yayi knocking wani mutum ya buɗe ƙofar ya leƙo suka gaisa a mutum ce yace "Baba dan Allah nan ne gidan Alhaji Isah?" Mutumin ya ɗan yi shiru yana kallon shi da mamakin jin yayi Hausa, sai kuma yace "eh nan ne." wata irin ajiyar zuciya Tahir ya sauke "dan Allah in yana ciki kace masa yana da baƙo daga Lebanon Tahir Fadoul." "ina zuwa." Mai gadin ya rufo ƙofar gate ɗin ya shige ciki, bai fi minti biyar ba da shiga ciki sai gashi sun fito da wani matashin Saurayi yana ganin Tahir ya gane sa suka gaisa sannan yayi masa jagora zuwa cikin gidan. Hajja Halima Matar Baba Isah ta shigo cikin falon da fara'ar ta "Tahir Barka da zuwa." Tahir ya gaisheta ta amsa tana tambayar sa ya Ummi da Yasir yace "Alhamdulillah. Ruwa tasa aka kawo masa da ɗan abun taɓa wa sannan tace "kazo Alhaji baya gida amma in sha Allahu yana kan hanyar dawowa." Sallar magrib aka kira suka fita Masallaci tare da Yaron Baba Isah Hashim. Ana idar da Sallah suka fito daga masallacin, Kusan a tare suka shigo gidan da Baba Isah. Baba Isah mutum mai tsananin kirki tsohon Managern Abbinsu ne, yana ganin Tahir suka rungume juna da murna. Baba Isah ya rasa in da zai saka Tahir saboda jin daɗin ganin shi. Saida suka gaisa sosai da Baba Isah, sannan Tahir yayi masa bayanin abinda ya kawo sa da kuma dalilin rashin zuwan sa akan lokaci, Baba Isah yayi shiru cikin jimami yace "subhanallahi subhanallahi, amma banji daɗi ba, Allah ya ƙara kiyaye wa sannu Tahir lallai kasha jinya." Tahir yace "Alhamdulillah Baba na samu lafiya." Baba Isah ya nisa "Alhamdulillah haka ake so, Allah ya ƙara kiyaye wa." "Aamin." Tahir ya gyara zama ya fuskanci Baba Isah, "Baba kasan duk abinda ya faru a baya, kamar yadda nama bayani yanzu nazo wajan ka ne dan Allah ka taimaka min ka gafarce ni da duka lefuka na, in kasan gidan su Khadijah suke ka sake rakani a karo na biyu kamar yadda ka rakani neman auran ta a shekarun baya." Baba Isah ya girgiza kai yace "Tahir kai ma ai ɗana ne kamar yadda Hashim yake ɗana, sannan komai yara suka yiwa iyayen su komai rashin daɗin sa haka suke haƙura su yafe musu, naso a shekarun baya ka tsaya ka saurare ni, saboda Tahir ni tin a lokacin na gane akwai wani abu a tare da kai saboda ban sanka mutum mara girmama na gaba da shi ba. Amma Mallam Bahaushe yace wai kaddara ta ruga fata, haka ko wanne bawa da jarabawar sa, ina tabbatar maka abin da ya faru ya wuce a wajena har abada, kuma in sha Allahu zan yi iyaka ƙoƙari na wajan ganin komai ya daidaita." (Duk wannan hirar Baba Isah da Tahir suna yinta ne cikin harshen larabci, dan Baba Isah ya iya larabci sosai tin zaman sa da Fadoul Al-arabey saboda yawan huɗɗa da yake yi da larabawa) Tahir ba ƙaramin jin daɗin maganar Baba Isah yayi ba cikin ƙarfin gwiwa ya yiwa Baba Isah godiya, sannan yace " Baba ko kana da labarin inda suka koma yanzu?" "Wallahi Tahir bani da labari, dan nima lefin kane ya shafeni tin daga wancan lokacin duk wani zumunci dake tsakanina da iyayen Khadijah ya yanke, da nakan ɗan kira su lokaci bayan lokaci mu gaisa to daga baya kuma saina daina samun su ma gaba ɗaya a waya. Sai kuma shekarun baya dana haɗu da shi Alhaji Muhammad ɗin a masallacin Da'awa ranar jumma'a, ban gansa bama shi ne yamin magana muka gaisa. tin daga wancan lokacin kuma bamu sake haɗuwa ba." Baba Isah nakai ƙarshen maganar sa Tahir ya sunkuyar dakai sai hawaye, wannan wacce irin jarrabawa ce mai ciwo haka. Baba Isah ya tausayawa Tahir kwarai da gaske, kana ganin sa kasan ba ƙaramin tashin hankali yake ciki ba. Baba Isah ya rinƙa yiwa Tahir nasiha da kalamai na kwantar da hankalin saida yaga Tahir yaɗan nutsu sannan yasa ya kira masa Ummi dan yazu bashi da number ta. Bayan sun gaisa yayi mata bayanin halin da ake ciki tare dayi mata alkhawarin in sha Allahu zai taimaka wa Tahir har ya samu gidan su Khadijah. "kayi hakuri Tahir ka kwantar da hankalin ka in sha Allahu inna dawo daga Umara zanje har can Bichi wajan kakannin Khadijan. Badan tafiyar tawa gobe ce bama da naje kafin zuwan Hajiya Faɗima (Ummi)." Zuciyar Tahir duk babu daɗi yace "babu komai Baba kaje Umaran nima zan koma gida na taho da Ummin kafin lokacin ka dawo." A haka suka bar maganar, Baba Isah saida ya raka Tahir har masaukin sa. Tahir yayi masa godiya sosai da fatan dawowa lafiya. ****** AMERICA Yau cikin makarantar duk babu students sosai sai tsilli tsilli kasan cewar lokaci ne na damuna ba'a dade da ɗauke ruwan sama ba, garin saiya sake ɗaukar sanyi fiya da kima, gently yake haurowa cikin department ɗinsu jikin sa sanye da wata classic plane white T-shirt da baƙin wandon jens, boot ɗin ƙafar sa white color sai Black p-cap daya ɗora akan tarin sumar kansa, yaɗan janyo p-cap ɗin gaba ta rufe fuskarsa, kayan ba ƙaramin kyau suka yi masa ba sai ya fito kamar irin Black American nan, Fahad ke nan badai iya ɗaukar wanka ba komai yasa kyau yake yi masa, sauda dama in suka siyi kaya Sa'ad kance "hi guy let me choose this one, i know you don't have problem with color dan kai komai kasa kyau yake maka." Duk lokacin da Ad yace masa haka he just smiled. Yadda yake takun kaɗai abin burgewa ne, a gaban office ɗin Prof Shazen ya tsaya kamar bayaso yayi knocking ƙofar. "Yes come in" aka amsa daga ciki. Calmly ya tura ƙofar office ɗin ya shiga, wani Farin Bature ne a zaune a cikin office ɗin akalla zai kai shekara 50 yana ganin shi ya saki murmushi "Mr Bichi welcome." "Thank you Sir." Fahad ya faɗa. Prof Shazen haka kawai yake son Fahad, ba ƙaramin burgesa Fahad yakeyi ba ya sha cewa bai san akwai mutane irin sa a Nigeria ba, sometimes yakan ce Mr Bichi you are different. Shine supervisor ɗin shi. Yanzu ma abinda ya fito da shi kira ya samu daga Prof Shazen akan yazo ya same sa a office ya gama duba project ɗin sa, Prof Shazen ya basa izinin zama, sannan ya fara yi masa bayani akan project ɗin. Yakai wajan 30minutes a office ɗin Prof Shazen kafin suka fito tare, suna fitowa daga department ɗin yayi wa Prof Shazen sallama ya wuce. Yana gaf da fita daga ciki department ɗin yaji ana ƙwala mishi kira, kamar bai ji ba yaci gaba da tafiyar shi, da sauri harda ɗan gudun ta ta cimsata suka jera suna tafiya a tare. "hi good afternoon." Yatsunsa guda biyu ya ɗaga mata alamar "hi" maimakon A'isha taji haushi sai tayi murmush "Please Isma'il i want talk to you, i have been calling you but you didn't pickup." A ransa yake mitar halinta bai san mai yarinyar nan take nema dashi ba, he told her Ad ya samu Mata tayi hakuri, dama abinda ya haɗa su ke nan, ya ɗauka bayan yayi mata bayani zata barsa ya huta, amma taƙi kullum cikin kiransa take dayi masa messages, he don't even know what does she want. Baya son takura ko kaɗan harga Allah ya fara jin haushin ta yanzu. Cikin yana yinsa na rashin fara'a yace "uhmm." A'isha har cikin ranata taji babu daɗi, ganin ko kallo bata ishe saba to amma ya zata yi da zuciyar ta tin randa ta fara ganin Fahad ta tabbatar wa kanta tayi falling. Ganin sa kawai farin ciki yake sata ko da ba zai yi mata magana ba. "Nagama karatu na tin last week, jibi zan koma gida Nigeria gaba ɗaya, Please Isma'il will you help me with your address?" Jin abinda tace yasa ya tsaya ya zuba mata idanunshi, as usual sanye take da shigar ta ta a baya, ɗauke kansa yayi daga kanta muryarsa very low kamar wanda aka yiwa dole yayi magana yace "Congratulations Miss Aisha." Tana murmushi tace "thank you dear, please will you give it to me?" Ko mai zata yi da wani address ɗin shi, oh! Sai yanzu ya tuna randa tace masa a Lagos iyayen ta suke, karatu ne ya kawo ta nan yanzu take kokarin haɗa first degree ɗin ta akan computer science. Baya son takura yasan in bai bata ba definitely haka zata dame sa da kira day and night. "i will send it to you." Yana gama faɗa mata haka yayi gaba ya barta anan. "Yes." A'isha ta faɗa cike da murna tana bin bayansa da kallo, ko kaɗan bata ɗauka zai ce zai bata ba. 💫 UMAIMAH 💫 ✍️A&A PEN FOLLOW OUR WHATSAPP GROUP VIA THIS LINK https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3 https://wa.me/+2348039352724 VOLUME ONE EPISODE 2️⃣3️⃣ Yau jumma'a ta kama kwanan Tahir biyar da zuwa Kano ke nan, tin baro warsa gidan Baba Isah yake cikin tsimayen zuwan ranar ta jumma'a da yake ganin kwanakin ta sunyi masa tsayi, gani yake kamar ranar baza ta zoba. Ƙarfe 12:30pm a Masallacin Da'awa tayi masa, ya iso masallacin cike da addu'ar Allah yasa yaga Baba ko wani daya danganci Khadijah. Ƙarfe ɗaya aka tada Sallah, bayan an idar da Sallah Tahir ya fito waje ya tsaye, da duka ida nunshi yake ƙarewa kowa kallo, amma har mutane duka watse ya rage baifi yan tsurari suka rage ba, baiga Baba ko wani daya danganci Khadijah ba. Tahir saida ya jira yayi Sallar la'asar a masallacin sannan ya koma hotel ɗin shi jikin shi a sanyaye. ***** Ana gama karɓar Hadda aka kira sallar la'asar farfajiyar makarantar suka fito inda anan ake shinfiɗa taburmi matan su yi Sallah mazan kuma su shige cikin masallaci. Ana idar da Sallah Sumayya ta zunguri Amira "gafa mutumin ki Fatima Muhammad." Amira ta ɓata rai tace "mugu dai ai Allah yana ganin sa abinda yamin." Umaimah dake kusa dasu tayi caraf "wai maiya faru ne?" Sumayya na dariya tace "kinsan halin Ustaz da ƙaƙalen masifa saida ya bari ta gama basa haddda yace saita sake batayi daidai ba. Ta sake maimaita wa yace wannan ba Alkur'ani take karanta wa ba. Yayi mata bulala yace batayi hadda ba, kuma ya mai da ita baya." "Kutimelecy shifa wannan Ustaz ɗin ɗan rainin wayo ne tun da suka yi sauka aka basa aji yake mana lukutin wulaƙanci, ranar nan ma haka yayi min gashi da kallon jaraba." "Kai Umaimah kefa baki da M." Salma ta faɗa. Amira tace "sai ƙaryar Ustazanci kunga Sallar ma sai yanzu zai yita. Wasu samari ne su uku suka shigo cikin makarantar da sauri da alama suma Sallah zasu yi. Anan gaban su Umaimah kaɗan suka haɗa sahu Ustaz da samarin nan sai wasu ƴan babban aji mutum biyu. Uncle Isma ne yazo wucewa yaga su Umaimah basu shiga ajiba sun haɗa kai a waje ɗaya ƴan ajin su harsun fara komawa. "Mai kuke yi baku koma aji ba?" Amira zata yi magana Umaimah tayi caraf tace "banyi Sallah ba ni suke jira." Suka kalle ta da mamaki dan sudai sun san tare suka bi jam'i da ita. Uncle Isma ya girgiza kai "saiki tashi kiyi ai dan yanzun nan Malam Aali zai fito, inya same ku anan kuma kunsan sauran." Uncle Isma na wucewa Sumayya tace "nidai ku tashi mu koma aji kunga duk an watse an bar mu, kuma kunsan halin Malam Aali yana zuwa babu tambaya saiya dake mu ko ya samu wanke bayan gida." Duk suka miƙe tsaye Umaimah ta kalli su Ustaz da suka yi Sujuda ta zare ido tana kallon su Amira da ƙarfi tace "Na shiga uku wallahi wandon wani ya yage acikin masu Sallar nan." Su Sumayya suka ce "me? Umaimah ta riƙe baki tana zare ido ta sake cewa "Wallahi wandon wani ne ya yage acikin su Ustaz, taɓ Allah sarki." Wasu ƴan mata da suka tashi zasu koma aji suma suka ce "kai." Abinka da ƴan makaranta dasan ganin ƙoƙof gaba ɗaya suka zubawa su Ustaz Ido da suka kasa dagowa daga Sujudar, can kuma kamar haɗin baki ɗaya bayan ɗaya suka rinƙa zuro hannu suna shafa wandon su, duk wanda ya shafa yaji ba nasa bane ya yage saiya zame ya zauna, wannan in yaji ba nasa bane saiya kalli na kusa dashi irin kodai naka ne. Su Umaimah da sauran ƴan matan nan suka kwashe da dariya harda riƙe cikin, suna cikin haka Malam Aali ya fito daga cikin masallaci suna hangoshi suka kwasa da gudu suka yi aji, suna gab da shiga cikin ajin Umaimah tace "wallahi ƙarya fa nake, kuma Allah duk wanda ya tonamin asiri a cikin ku hmmm!" Amira ta zare ido tace "ƙarya kuma? Ni dai babu ruwa na." Umaimah ta zuba mata harara "banza matsoraciya. Allah kina tona min asiri zamu haɗa baki muce kece, koya kukace Summy." Su Salma suka ce haka ne Fatima Tahir, dama su ƴan abi yarima ne asha kiɗa. Wani a cikin samarin da suka shigo sallar ne ya kasa hakuri ya kalle su gaba ɗaya yace "nidai ba wando na bane ya yage, amma dan Allah na waye ya yage? Fisabilillahi duk wanda nasa ne ya yage yadau alhakina dan wallahi da ƙyar na zame na zauna." Na kusa da shi yace "Nima ba nawa bane ya yage gaskiya saidai ko a cikin ɗaliban nan." Haka kowa ya rinƙa ba nasa bane ya yage banda Ustaz da yayi shiru ya sunkuyar dakai idanunshi suka yi ja. Ganin haka duk sai suka ɗauka ko nasa ne ya yage. Kusan a tare suka ce "ayya sorry Ustaz." Wani baƙin ciki ya sake ƙume shi dan wallahi yayi imanin wannan rashin mutumcin na Fatima Tahir ne dan ya gane muryar ta. Har Samarin suka sake wata sallar suka fita suna maida yadda akayi Ustaz bai tashi ba, yanajin wani a cikin su yana dariya yana cewa "kai amma fa yarinyar da tayi maganar nan bata ji, tashin hankali wa yaga wadon Musty ya yage." Sauran suka kwashe da dariya. Afusace Ustaz ya tafi office ɗin Malam Aali. yana shiga ransa a ɓace ya yiwa malam Aali bayanin abunda ya faru. Malam Aali yace "subhanallahi! Subhanallahi!! Ita Fatiman? Maza kirawo ta tinda ka gane ta, ita zata fito da sauran." Suna tilawa aka aiko ana kiran Fatima Tahir Al-arabey. Tana jin haka ta kalli su Salma, Amira ta zare ido cikin tsoro. Umaimah ko a jikinta ta miƙe ta fita. Da sallama ta shiga office ɗin Malam Aali yadda kasan salihar gaske, tana ganin Ustaz tasha jinin jikinta amma da yake Umaimah ƙwararriya ce saita maze. Malam Aali ransa a ɓace yace "maza kirawo sauran wanda kuka yi rashin ɗa'ar tare, karki ɓata min lokaci maza kirawo su." Umaimah ta kalli Mal Aali hankalin ta kwance tace "Malam ban gane ba suwa zan kira wo maka ba?" Ustaz ji yake kamar ya tashi ya rufe ta da duka dan baƙin ciki. Malam Aali ya daka mata tsawa "zaki wuce ki kira su ko saina ɓata miki rai." "Malam to nace suwa zan kira baka faɗa min ba." Tayi maganar tana shirin fashewa da kuka. Malam Aali ya tsaya kawai yana kallon ta, yasan Ustaz ba zai yi mata ƙarya ba, amma shine take san rena masa hankali. Malam Aali ya kalli Ustaz yace "kirawo min ƙawayen ta." Su Amira na shigowa cikin office ɗin sukayi zuru zuru da ido bama ya Amira Sarki tsoro. Malam Aali yace Ustaz ya sake maimaita abinda ya faɗa masa. Ustaz ya sake yin bayani. Malam Aali ya kalle su "wace a cikin ku ta faɗi maganar?" Kafin suyi magana Umaimah tayi sauri tace "Allah subhanahu wata'ala yana cewa "Wamashahidnaa illa bimaa allimnaa wa maa kunna lilgaibi hafizeen. Haka a Hadith Abu Huraira Allah yace baya zalunci kuma baya son masu zalunci." Malam Aali yayi shiru yana ƙare wa Umaimah kallo. "Malam nidai a sani na babu wacce tayi wannan maganar a cikin mu, kuma shi zato zunubi ne, amma tinda yace nice, shikenan Ustaz kayi hakuri saboda Allah, Allah ya baka ladan haƙurin abinda kace nayi maka." Malam Aali ya zubawa Umaimah Ido ganin yadda ta kafa ta tsare ta hana sauaran magana, yadda take maganar cikin nutsuwa da kwanciyar hankali babu yadda za ayi ka gane ita ce tayi lefin da ake tuhumar ta dashi. Daga karshe dai dole malam Aali yasa suka sake bawa Ustaz hakuri ya sallame su suka koma aji. Ana tashi suka fito bakin gate suna jiran Uncle Isma ya fito su tafi gida saiga Ustaz ya fito zai tafi. Yana zuwa wucewa ta kusa dasu, Umaimah tace "Allah Subhanahu wata'ala yana cewa "Wa anlaisalil insani illa ma sa'a, wa anna sa'a yahu la saufa yuraa." (In direct translation kamar kace "Duk tsontson daya ja ruwa shi ruwa kan doka) Ustaz ya juyo ya kalle ta tayi sauri ta ɗauke kai kamar ba ita ce tayi maganar ba. 💫 UMAYMAH 💫 ✍️A&A PEN Follow our Whatsapp group via this link https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3 https://wa.me/+2348039352724 VOLUME ONE EPISODE 2️⃣4️⃣ Bayan wucewar su ba dadewa Isma'il ya fito har ya fara tafiya Ustaz ya tsayar da shi, yayi mishi ƙorafi akan abunda Umaimah ta yi, har kiran su da Malam Aali yayi da maganar data faɗa mishi yanzu a fakaice saida ya faɗa masa, yace a ja mata kunne in ta ƙara rashin ji irin wannan da kan shi zai zo har gidan su ya faɗa wa Baban su, Ismael ya ba shi haƙuri ya ce in sha Allahu zata gyara.

Chapter 12 of 29