Share this page
"babu komai fah my sis bacci na yi ban jima da tashi ba." Munnirah ta kafe ta da ido sannan tace "Dijengalele kenan Khadija tawa, idan da wanda zaki boyewa abu toh ban da ni, kasancewa ta Aminiyarki ta ƙuruciya kuma yanzu uwa nake a wajen ki tunda ina Auren Kanin Baba" Saida Khadijah tayi murmushi sannan tace "babu jaa na sani, tuni na sallama miki uwata maganin kuka na." Khadijah tana gama ɗurawa suka har haɗa kwalaben turaren masu yawa a cikin katon baho, Khadijah ta ce da Baba Rabi "mu kama mu shiga ciki, my sis please biyo mu da sauran" suka kama suka yi cikin gidan ****** Social studies teacher ce ta shigo class ɗin su Umaimah, ajin suka miƙe "good afternoon Mah" Umaima da Mr Alade ya saka crawling tun daga school premises har class ta gaji, bacci take kashirɓan, Sadiq ke ta buga mata desk ta tashi, har teacher ta lura ta ce "Sadiq wake her up" yayi ta buga desk ɗin har ta bude ido. Mis Helen tace "Fatima come here" Umaimah ta je gaban board mrs Helen ta kalle ta ta ce "what was our last topic? "we did Government" Umaimah ta faɗa. Mrs Helen tace "hmmm elaborate more" Confidentiality tace "forming of government such as Democracy, monarchy, and dictatorship, ta ƙara da cewa and we also did humanrights and responsibities within a society, exploring the concept of community national identity and citizenship" Umaimah cikin taccen turanci take bayanin, dake nursery sch ɗin da suka yi ta wata baturiya ce, sun samu background me kyau. "wow wow wow" Mis Helen ta faɗa tana tafawa Umaimah, Please class clap for her" dama ta san she would never dissapoint, ta bude hannayenta tace "please give me a hug Fatima" Umaimah tayi hugging miss Helen, kanta yayi girma sai blushing ta ke "go back to your seat and see me after the class" Umaimah tace "ok maah" ta koma ta zauna. Mrs Helen ta fara gabatar musu da lesson ɗin yau tace, "Our today's topic is culture and society, Repeat after me suka ɗauka "culture and society, again "culture and society." Suna fitowa break Umaimah tafi staff room wajan Miss Helen, tana shiga ta gaishe da sauran teachers ɗin ta nufi desk ɗin Miss Helen, Miss Helen ta bude jakar ta ta dakko 1000 Naira ta mikawa Umaima tace "is a small token from me ,keep it up I'm really impressed Fatima" Umaimah ta karɓa ta ce "thank you Maah" "You are welcome always Fatima, you can go." Ta fita tana murna baki har kunne dama teachers ɗin su suna son ta sosai saboda ƙoƙarin ta, ita take zuwa 1st position overall a js3 A&B second and third kuma a tsakanin Sadiq Mukhtar ne da Aminu Bello, suke kokawa a tsakanin su yau wannan yayi second, wani term din wani yayi third haka suke rotating a tsakanin su, Amma first position na Umaimah ne sun sallama mata, an bar mata kayanta. Suna komawa class period ɗin maths teacher ne yana class ɗin already, ya bada classwork yana marking row by row, Umaimah ta duba taga kowa hankalin shi na kan classwork ɗin da aka ba su. Saɗaf saɗaf ta lallaɓa ta ɗauke lesson note ɗin maths teacher, ta taho da sauri Sadiq ya matsa mata ta wuce, yace "me za kiyi da shi? Umaimah ta ce "na tsani maths wlh idan ya ga babu sai ya kyale mu ya koma inda ya fito, wanne irin abu ne wannan a ce maths da rana kuma double period, Ni idan rana ta take na fara jin yunwa ba ganewa nake ba." Sadiq yayi dariya ya taɓo Aminu dake gaban shi, Aminu ya juyo yace "ya aka yi ne? "Smart ta fanshe mu. Sadiq ya faɗa yana kunshe dariya, Aminu yace "me kake nufi? Umaima ta daga masa lesson note ɗin maths teacher, Aminu ya zare ido. Maths teacher ya na ƙoƙarin juyowa ta yi maza ta saka book ɗin a locker, ya na bi row by row har ya ƙaraso nata, ta fito da littafin ta yayi marking yana ta smilng ya san zata ci. Uncle Isma ne yake mata Assignment ɗin maths, da yake shi science student ne, ita kuma bata son maths ko kaɗan, amma kuma bata yarda da faɗuwa ba, dan haka take da baƙin naci, bata yarda ta hakura sai taga ta iya. ***** I hope we are communicating readers keep following u wouldn't regret it in sha Allah. ⚡ UMAYMAH ⚡ ✍️A&A PEN FOLLOW OUR WHATSAPP GROUP VIA THIS LINK https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3 https://wa.me/+2348039352724 VOLUME ONE EPISODE 0️⃣8️⃣ Maths teacher yana gama marking books ɗin students, littafin sa ya ce ɗauke ni inda ka ajiye ni, yace "kamar na shigo da littafi ko? ya tambayi class, ko ya ajiye littafi yana marking, aka hada baki "No sir, No sir" Aji ya ɗauka har da Umaimah. Yace "Okay class captain, go and check my table in the staff room please." Sadiq ya miƙe ya fita. Aminu ya juyo suka yi murmushi shida Umaimah, ba a ɗauki lokaci ba Sadiq ya dawo yace "is not there sir" Maths teacher yace "Okay class let me check myself" ya fita. Already an ci period ɗaya saura ɗaya, Umaimah tana dariya ta fito da 1000 Naira. Sadiq ya ce "waya baki kudi" Tace "social studies teacher" Aminu genius yace "Smart yau a gari kike kenan? a bamu salala." Sadiq yayi dariya yace "ashe Zaka bushe Smart da kudi, anya kin taɓa sadaƙa kuwa? Umaimah tuni ta tafi tunanin abin da zata yi da kuɗin ta, dan ba a basu kuɗi, a cafetria ɗin makaranta ake biyan kudi duk term, a nan su ke zuwa su karɓi duk suke so. Anisah ce tayi desk din su Umaimah, Anisah tana son Umaimah, Amma kullum a faɗa suke, jinin Umaimah yafi zuwa ɗaya dasu Wizard, kullum su Anisa maganar bollywood su ke yi, su Abhi&Pragya, ita kuma bata da interest sam a wannan sabgar, ko dan a gida ma suna tare da Uncle Isma ne, sai ya zama na ta fi gane mu'amalarta da mazan ajin akan matan. Hobby ɗin Umaimah girki ne ko dan me son Abinci ce oho! dan ma Umma tana hana ta, tace tana mata asarar gas. Anisah tace "Umaimah ara min note ɗin ki na social studies" A sheƙe Umaimah ta kalle ta tace "a nawa?" Anisah tace "daɗi na da ke wulaƙanci mutum nawa na wuce nazo wajen ki? Umaimah ta taɓe baki tace "toh koma in da kika fito" Sadiq ya kalli Anisa yana dariya ya ce "Kafa wadar Ajinmu" . Anisa ta sha kunu tace "bana so" Da gaske gajeriya ce. Umaimah ta dinga dariya har da riƙe ciki, tana buga desk dan shakiyanci, har sauran yan class ta ja hankalin su. Sadiƙa ta zo wajan su tace "me ake faɗa a bamu mu sha? Umaimah ta harareta tace "ke wlh munafuka ce" "ni, Umaima nice munafuka? Umaimah tace "eh ɗin an faɗa munafuka ko ba ita ba ce? Nan faɗa ya kaure a tsakanin su, Sadiq yaƙi rabasu ya kuma hana a raba su, dama haushin Sadiƙa yake ji ta fiya shiga abunda babu ruwan ta, ganin an kayar da Sadika, Anisah ta fara raba su, da ƙyar ta banbare Sadiƙa daga jikin Umaimah ta ja ta suka koma seat din su. Umaimah tace "Ashe girman biredi ce" class aka hau dariya, sai gaa maths teacher ya dawo yace "I think we shall call it a day" ya fita. Aka kada tashi suka fir fito. Umaima ta nufi staffroom da lesson note din maths teacher, ana ta tsokanar ta, ta nufi maths teacher ta miƙa mishi lesson note ɗin. Tace "you left it on my desk, I saw it after you left sir." "really? maths teacher ya ce "I hope u are telling the truth? "is the truth sir. ta faɗa confidently and innocently, ya karɓa yace "thank you Miss Tahir." Ta fito gate Amira ta nufo ta da sauri tace "ina kika tafi? yi sauri muje kar yanzu ma ya barki, suka rankaya tare wajen motar Uncle Aliyu da ya zo ɗaukan su. Suna zuwa yace "Dalla ku shiga kar ku bata min lokaci ina da abin yi" Hayatu Umaimah ta faɗa a ranta. "and you" ya kalli Umaimah, ki zo ki same ni after magrib" ta gyaɗa Kai ba tare da tayi magana ba, yace "baki da baki" ta amsa da "Toh." ***** Aliyu a waje ya sauke su ya juya wajen aikin sa. Da gudu Umaimah ta shiga gidan ganin motar Munnirah a parking space, tasan tana gidan, akwai haduwar jini sosai a tsakanin su. Amira tana wa kika bar wa jakar, amma bata kula taba tayi gaba. Umma na zaune a falo tana kallon sunnah tv Umaimah ta faɗo cikin falon da gudu, Umma tace "kaai subhanallahi ni Maryama wlh kin bani tsoro" Umaimah tace "kai Siyama meye abun tsoro anan? "toh mutum ya shigo a guje ba sallama" "Umma Ina Mamin Rijiya? Umma tace "tana Rijiya" Umaimah ta ɓata fuska tace "kai dan Allah Siyama. "toh kya ce min wani Mamin Rijiya, ki ƙarasa mana ki ce Rijiyar Zaki ke kowa sai kin bata mishi suna. Umma ta faɗa. Amira tayi sallama ta shigo ta jefar da jakar Umaimah tace "ga shi nan. Umaimah tayi murmushi tace "thank you my lovely Amira" Umma sannu da gida. Amira ta faɗa.Umma na amsa wa ta haye sama, tabar Umaima anan. Umma tace "kin tsare ni da ido, baki san ɗakin Amminki ba ne ko sai an miki jagora? Siyam da jan rai kike. Umaimah tayi maganar tana haurawa sama da gudu. Tun daga bakin ƙofa Umaimah take cewa "Oyoyo Oyoyo, Mamin Rijiya" Munnirah tayi dariya tace "Oyoyo Umaiman fanfo" Munnirah tana kan gado, Khadija tana ta packaging order, ta buɗe hannayen ta ta rungume Umaimah ta, tace "Toh ya schl? kin gan ki kuwa? me Umma ta ke baki? Umaimah tace "me nake bawa kaina dai, Siyama ay cikinta kawai ta sani, dama dai Baba kika ce. Khadija tace "ki je ki cire uniform, kar ki zauna surutu. Umaimah ta taɓe baki tace "kaai Ammi yaushe ra bo na da Mamin Rijiya? Munnirah tayi murmushi tace "je ki cire uniform ɗin ki, yau a nan zan kwana." Umaimah ta zaro ido tace "dan Allah? "in sha Allah" Umaimah ta cikata ta fita. Munnirah ta kalli Khadijah ta ce "ikon Allah kin ga Umaimah tafiyar ta ma irin ta Tahir ce. Khadijah ta yi sauri ta miƙe tace "bari na wanke jiki na, sai ƙaurin turare na ke yi" ta kawar da zancen ta nufi toilet. Munnirah ta girgiza kai a ranta tace yau na shirya miki, yau maganar makiyin naki zan miki wato Aure. Khadijah ta tsani wani abu daya danganci zancen aure. ko ace ana son ta, yawanci ma an ɗauka matar aure ce, Akwai wani collegue ɗin Munnirah, watarana Munnirah tazo gidan kamar yadda ta saba ta kwana, da safe zata fita aiki karfen Nasara babu tabbas motar ta taki tashi, sai tare suka fito da Khadijah ta ajiye ta a wajen aiki, a nan suka haɗu da abokin aikin ta Barister Farouk Bello Makama, shi kenan ya dami Munnirah yana san Khadija, Munnirah bata boye mishi ba, tace ba lallai ta saurare ka ba bata san maganar Son nan, amma ya matsa. Data yiwa Khadija maganar sun kai ruwa rana Sosai, Khadija ta dena ɗaukan kiran Munnirah, sai ta yi mata missed calls rututu taƙi ɗauka, kuma baza ta bi kiran ba, sai da Munnirah ta gaji ta zo har gida tace "Khadijah indai akan Farouk Makama ne na daina yi miki maganar shi, bashi ya haɗa muba, tare ya gan mu." Sai kuma Khadija ta ji kunya ko ba komai Munnirah ba kashin yarwa bace, tarihin rayuwar ta ba zai cika ba sai da Munnirah, shi kenan a ka bar zancen sa ya wuce. Yanzu ma wani Abokin Dr ne (Mijinta) tunda ya haɗu da Khadijah wata ranar weekends, fitar kusan ta dole ce, haka kawai Munnirah ta zo gidan zata tafi Umaimah ta hau rigimar sai ta bi ta. dake Friday ce Baba yace a tafi da ita, Ranar Saturday da safe Umma tace wa Khadijah taje ta dakko ta za a yi musu kitso ita da Amira, tana sauri har sun zo harabar gidan Umaimah tace fitsari zata yi ta koma. Baba likita aka budewa gate ya shigo da wani mutum a gaban mota, Khadijah ta durƙusa ta gaishe su, Dr yace "a'a Khadija har kinzo tafiya da Amarya ta, ba za a bar min ita ba ta ƙara kwana biyu ba? ki bar ta zan kawo ta da kaina" Tun a lokacin Khadija ta tsargu da kallon da mutumin ya ke mata. Khadijah tace "dama Umma ce tace a zo a ɗauke ta. Baba Dr yace "kyale ta zan kira Umman ta ku." Khadijah ta wuce ta tafi, tun daga ranar mutumin yake damun Dr shifa ya ga mata a gidan sa, shima likita ne a asibitin Malam Aminu Kano ya ke aiki, Usman Usman Bebeji sunan shi, dan yau takanas zuwan na Munnirah na shi ne. 💫 UMAYMAH 💫 ✍️A&A PEN Follow our Whatsapp group via this link https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3 https://wa.me/+2348039352724 VOLUME ONE EPISODE 0️⃣9️⃣ Siyama tuwo kika dafa fisabilillahi wanne irin tuwo da tsakar rana. Umaimah tayi maganar kamar zata rusa kuka. Sallamar Baba ce ta katse taɓarar da ta ke yi da gudu taje ta rungume shi tana murna tace "Baba na ya dawo" Baba ya jaa hannunta suka zauna yace "uwa ta oyoyo." "sannu da zuwa Baban Khadija" Umma ta faɗa tana risnawa, Baba yace "mun same ku lafiya? Umma ta amsa wa Baba da "lafiya ƙalau, bari na kawo maka ruwa" ta karɓi trolley da brief case ɗin Baba a hannun malam musa daya rako shi ƙofar falo. "Barka da rana hajiya" Malam musa ya gaida Umma yana rusunawa. Umma tace "yawwa Barkan mu dai Malam musa ya hanya? Yace "Alhamdulillah" ta ƙarbi kayan ta shiga dasu ciki, sannan ta haɗo ruwa da lemo ta kawowa Baba tace "ko zaka fara watsa ruwa? yayi murmushi "to Matar bari na watsa ruwa ko? ya faɗa yana kallon Umaima data yi shame shame a jikin shi, dama haka take so, idan Baba yana nan taɓara sai wadda ta manta. "Baba yau fah sati ɗaya ban ganka ba, in naji kuna waya da Siyama nace ta bani sai tace wai shirme zan maka" Umaimah ta faɗa a shagwaɓe. Baba yace "Au haka ta ke cewa? ni kuwa ce min take kin yi bacci"Umma tace "haka zaka yi min, wannan fah bata da saiti sai ta kullace ni." Baba yayi dariya yace "A'a toh ba a yi hakan ba. UMMA ta miƙe ta hau sama ta haɗawa Baba ruwan wanka Umaimah tace "Baba minti 10 na baka toh" Baba na dariya yace "godiya nake, an yi min iznin na je kenan? "na yi maka Babana. Baba yace "ina mutanen gidan su ke tinda na shigo banji motsin kowa ba? bai rufe bakin shi ba Ismael ya shigo da murnar shi ya gaishe da Baba. Baba yace "Hakimi sai yanzu kake dawowa? Umaimah ta yi carab tace "extra lesson su ke yi sun kusa fara waec da neco." "toh madallah" Baba ya hau sama. Umaimah tace "yawwa Uncle Isma cire uniform din ka, kazo mu yi shawara. "shawara, tame? Umaimah ta wani langwaɓar dakai tace "kai dai ka shirya kazo" Yayi cikin ɗakin shi ita kuma ta zauna jiran shi, harya fito, sanye da blue jeans da white shirt a jikin shi Umaimah na ganinsa tace "Uncle Isma ka yi kyau, wlh duk wacce zaka aura sai ta bani kuɗi masu yawa saboda Baba na mai tsada ne". Isma'il yace "Allah mutuniyar? "Allah uncle Isma" Ismael yace "to dai ya a ke ciki" ya katse ta. Tace "Dama kudi na samu, nace wacce sanaar zan yi saboda dogaro da kai? Ammi birge ni take innaga tana ƙirga yan dubu dubu." "wa ya baki kudin?kuma har dubu nawa ne? Isma'il ya tambaye ta. Tace "Social studies teacher ce ta bani 1000, Ismael ya maimaita "1000" cab ni kan ban ga abinda za a yi da 1k ba gaskiya. Suna cikin haka Amira ta sauko dake Alhamis ce babu islamiyya, tace "Umaima Baba ya dawo ne? Umaimah tace "me kika gani? "Na ji kamshin turaren shi ne" Amira ta faɗa. Ismael ya kalli Amira ta kasan ido, ta gani ita ma kallon da ya ke mata irin na ɓace daga nan ne, ta wuce kitchen, can ta leƙo tace wa Umaimah "za ki ci abincin na zuba mana tare, ko kinci?" Sai Amira ta yi maganar ma ta tuno da zancen tuwo, ta shafa ciki, tace "gaskiya ba zan ci ba, Uncle Isma ko na dafa mana indomie? yace "yauwa dafa mana ki same ni a ɗakina sai mu ƙarasa maganar" ya miƙe ita kuma ta shiga kitchen. Amira na zaune a kitchen akan island tana cin Abinchi, Umaimah ta shigo ta wuce store ta debo indomie, Amira tace "kaai duk wannan za ku ci, ina za ku kai ta? Umaimah tace "inda ake kai ta" Amira ta girgiza Kai tace "Baba yana kokari, ciyar da ke ba karamin aiki ba ne" Umaimah tace "yau naga ikon Allah, ke wani ne ya hana ki kici, a bar ni na sarara" ta ɗauko tukunya ta zuba ruwa ta dora a wuta. In kaga yadda Umaimah take aikin dole ta baka mamaki, dan yinsa take cikin ƙwarewa da natsuwa kamar ba Umaimah ba. Kodan abinda take sone wato Kirki Zaune suke a ɗakin Uncle Isma bayan sun gama cin indomien data dafa musu. Ismael yace "Why not ki fara gullisuwa? "yes ka kawo shawara, idan abun ya bunƙasa har alawar madara, ko na baka wata ka tafi mun da ita sch din ku" ya harare ta, tayi dariya tace "idan na samu, ka samu. Yace "toh kuma haka ne, amma zaki fini ciniki kinsan mata sun fi Maza kwadayi" Umaimah tace "kuma haka ne, toh yau da daddare sai mu yi idan an kwanta, kasan neman na kai sai da sirri." Ismael yayi dariya yace "No wahala." ***** Daddare gaba-daya an hadu za a yi dinner, Umaima ta ɗakko wani tray, taga kowa hankalin shi na kanta ta tsargu da kallon da ake mata, kawai saita tafi wajen Baba, tace "Baba nayi serving dinka? yace "Toh uwata a zuba min" Jellop ɗin cous cous ne da Cole slow, sai farfesun kayan ciki, ta fara zubawa, Baba yace "kadan" ta saka mishi Cole slow ɗin, ta zuba peppersoup ɗin da yawa, yace "rage, yayi yawa koh tare zamu ci? Umma tace "ta ɗauka kowa ma irin ta ne." Ibrahim yace "nima zuba min. Umaimah tace "tsaya tukun na Uncle, da ma Baba nake son fara zubawa. Ta ɗakko tray ta lafta abinci, ta zuba farfesun a katon bowl, tana gama zubawa ta cewa Ismael "mu je uncle isma" ba musu ya mike kamar Raƙumi da Akala suka bar wajen. Baba yayi dariya yace "wannan soyayya ta uba da 'ya Allah ka dauwamar da ita har Aljanna." aka amsa da Amin, Babangida yace "Baba Daddyn Lagos ya kira ni da safe yace idan na same ka na ce lallai ka kira shi, Umma ma ta ce nima ya kira ni jiya wlh mantawa nayi ban fada maka ba." Baba yace "Naga missed calls ɗin shi zan kira shi, kogi ne ba su da service mai kyau, Khadija yaya shago? Tace "Alhamdulillah Baba" " Munnirah ya wajen su Alhajin ku, mun kwana biyu bamu gaisa ba? "yana lafiya Baba" Munnirah ta amsa. Baba yace "Toh madallah." Khadijah da Munnirah Suka miƙe a tare suka yi wa su Umma sai da safe. Baba yace "Babangida ya wajen aiki? "Alhamdulillah Baba." "Babu wata matsala ko, regional manager din naku mun hadu da shi yana ta yaba maka, dan Allah a cigaba da rike Amana." Aliyu yace "in sha Allah Baba" Ibrahim ya housemanship? Ibrahim yace "mun kusa gama wa in Sha Allah." Baba ya gyaɗa kai yace "kace an kusa shiga Labour Market, Allah yayi jagora." Haka Baba yake idan ya dawo daga tafiya sai ya tambayi kowa masu aiki da masu karatu. Baba yace "Auta ana ta karatu ko? Amira tace"eh Baba" Masha Allahu, Allah yayi muku albarkarsa. Amira kira mun Uwata da Hakimi na tambaye shi dazu naji ya kusa zama graduate" Umma tace lallai kam. "Gani Baba" Umaimah ta faɗa. Baba yace "ya makaranta ana dai karatu ko? Tace "sosai ma Baba, bari ma ka gani, ta karɓo 1000 a wajen Isma'il ta nunawa Baba" Aliyu yayi siririn tsaki yace "ji shirme ana tambayar ta karatu, ta kawo kudi." Umaimah tace "Tambaya na amsa aka bani kyauta" Amira ta kalle ta don bata faɗa mata ba, Baba ya kalli Amira da she looks comfused yace "yaya dai Auta? Umaimah tace ay Amira js3 b ta ke ni a A, shi yasa bata sani ba." Aliyu yace da Amira "gobe ki Je ki tambayar min teacher. Umaimah tace "taje mana tinda wlh da gaske ne" Aliyu ya harare ta, ta yi shiru. "A'a fah Babangida uwata mai kokari ce, kar ka damu gobe da kaina zan kai su sai na tambaya." "Dan Allah Baba"? Umaimah ta fada, da zumudi ta rungume baba, tace "ina kaunar Baba, Allah shi ne shaida. Dariya kawai Baba yayi dan duk wanda yake gidan nan yasan Umaimah da Baba haka suke **** Sun gama duk wata al'adar su, bayan sallar isha, sun yi wanka Khadija ta ɗakko wata riga mai laushi doguwa da kaɗan ta wuce cinyarta ta saka ta feshe jikin ta da turare ta taje gashin ta ta daure da ribbon, tayi kyau fatar nan tata sai sheki take yi. Munnirah ta kalleta tana shafa cream tace "my sis u look cute." "har na kai ki" Khadija ta faɗa. "oh haka zaki ce? Dan ita compliment din Munnirah ba haka kawai ya ke zuwa ba sai ta faɗi wani abu. Munnirah tace "kyau wankan nan akwai mai biya" nan da nan fuskar Khadijah ta canja kamar an fada mata

Chapter 5 of 29