Share this page
mu yana wuyan iyayen ta, ga kuɗin haya da suke biya mana abunda ya kamata ace yan uwan Baffa ne suke yi mana." "Ah to faɗa mata dai sha sha sha kawai." Mama ta faɗa, "to wai roƙar su muka yi, ba niyyah suka yi ba." Zaliha ta faɗa ko a jikin ta, "haka kika ce toh Allah yasa cewa ya yi auranta zai yi mu ga tsiya sai ki mutu." Mama ta faɗa tana shigewa ɗaki. Zaliha a ranta tace kar dai ace Khadija boye mata tayi, idan da gaske cewa yayi yana sonta fa, ta yi shiru, can tace kai Khadija ba ta da wannan wayon, amma idan da gaske ne fah wata zuciyar ta kimtsa mata wannan tunanin, wani gumi taji ya tsartsafo mata, ta tashi cikin hanzari ta zari mayafi, ta nufi gidan su Khadijah. Tana zuwa ta yi kyakkyawan gani, tana buɗe ƙofar baranda taci karo da Khadija da Tahir zaune akan fararen kujeru, yayi ado cikin farar shadda da yake jumma'a ce, ga lemo da ruwa a kan tray a gaban shi, Khadija ta sunkuyar da kai ta na murmushi, shi kuma ya kafe ta da ido murmushi kwance akan fuskar shi. Zaliha ta kame a tsaye riƙe da handle ɗin kofa ta kasa gaba ta kasa baya, gaba ɗaya su basu san da tsayuwar ta a wajen ba. ko ba a faɗa mata ba wannan abun da idon ta ya gani ya gama bata amsa, ƙafafuwanta suka fara rawa, kira ne ya shigo wayar Tahir zai daga ya kula da Zaliha dake tsaye kamar mutum mutumi, ya ce "Zakiyya." Sannan Khadijah ta ɗago kai suka haɗa ido da Zaliha, idonta har ya sauya, yace mata "Bismillah." ya tashi ya bata waje, jikinta a sanyaye ta zauna da kyar ta gaishe shi, ta kafe Khadijah da ido, Khadija ta ce "ya su Mama? Kamar Zaliha ba zata amsa ba tace "lafiya." Tahir yace "dama ina son zuwa gidanku Zakiyya." muryarta a dashe kamar me mura ta ce "sunana Zaliha." "oh sorry haka ne Zalika zan zo har gida nayi miki godiya ta dalilin ki na haɗu da HAYATEE (my life), ta faɗa min ku biyu ne friends ɗinta ina Munnirah? kirawo ta mu gaisa." Zaliha kanta yayi wani irin sarawa, kirjinta yana sama da kasa, ta dai daure tace "babu komai bari ta Je tunda ta na da bako." yace "da wuri haka, ni da nake son ki faɗa min me Hayateey tafi so, tun ɗazu fama nake da ita taki magana, tana magana ma kuwa?" Zaliha ta yi yake ta ce "tana yi." Ta yi musu sallama. **** Ikon Allah ne ya kawo Zaliha gida ko Mama bata san da dawowarta ba ta shige ɗaki ta rikito da kayan cikin sip ɗinta ta hargito su tana wurgi da su gaba ɗaya ta rikice tana gunjin kuka kamar tabbabiya, "ni za a yiwa munafurci, ta yaya zai ce ita yake so? Ni ban cika mace ba ne? Komai Khadijah komai Khadijah na shiga uku." Kuka ta ke yi sosai hawaye da majina sun gauraye fuskar ta, da sauri Mama ta fito tun tana banɗaki take jiyo gunjin kukan Zaliha, ta zo hankalin ta a tashe, tace "ke yaya aka yi lafiya? Me ya faru?" "Khadijah" Zaliha ta faɗa, Mama ta dafe kirji tace "me ya sami Khadijan?" "Ashe da gaske ne." Mama tayi mata tsawa, "da gaske me? Kin sani a duhu." "Oganmu ita yake so, har ya zo suna zancen aure." Mama ta ja tsaki tayi waje kamar ta rufe ta da duka. Haka ta yini a kwance, wai Zakiyya ko sunanta ma be rike ba saboda wulakanci, tasan shegiyar Munnirah ita zata ce kar a faɗa mata. 💫 UMAYMAH 💫 ✍️A&A PEN Follow our Whatsapp group via this linkhttps://whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3 https://wa.me/+2348039352724 VOLUME ONE EPISODE 3️⃣8️⃣ Su Khadija sun shiga ss3, karatu yayi zafi, sosai suka mayar da hankali a kan karatu, Tahir ya siyawa khadija waya saboda su rinka gaisawa tunda ba kullum su ke haɗuwa ba, da kyar Baba ya bari ta karɓa sai da Umma ta sa ka baki, kullum bayan isha'i suke waya da shi, zuwa 9 Umma ta ke karbe wayar sai gobe kuma saboda kar hankalinta ya rabu biyu. Alakar su da Zaliha ta canja sosai a lokacin dan sai Zaliha ta share su gaba ɗaya har Munnirah, sai da Umma ta aika Ibrahim ya kirawo mata Zaliha akan rashin zuwan ta, Khadijah bata kawo wa ranta Zaliha son Tahir ta ke ba. Zaliha ta zo kiran Umma, ta tambaye ta me ya haɗa su da Khadijah, daya ke mai wayo ce sai cewa tayi, ta tambayi Khadijah tsakanin su da Oganta, tace mata babu komai tsakanin su wai tayin aiki kawai yayi mata ta boye mata gaskiya. Umma ta bawa Khadijah rashin gaskiya, tace su ne kawayen ta yaya za ta yi haka, sosai Umma tayi wa Khadijah faɗa, da gaske Khadijah ta ɗauka shi ne dalilin share tan da Zaliha tayi, ta bata hakuri, rashin wayo irin na Khadija sai cewa tayi, "Munnirah ce tace nayi shiru sai komai ya tabbata." Zaliha a ranta tace haba ita ta san a rina, wannan Munnirar munafuka ce, haka suka cigaba da kwancen su kamar komai ya wuce, amma a ƙasan ran Zaliha be wuce ba, sai dai tana ƙoƙarin dannewa idan suna tare da Khadijah. Kwanci tashi babu wuya a wajen Allah cikin Aminci da huwacewar ubangiji suka fara rubuta waec da neco, Baba ya siya musu form din jamb su uku, kowanne centre ɗin ta daban, ranar da za'ayi jamb Baba ya kai su, Khadija a Rumfa college centre, Zaliha a Kano capital, sai Munnirah a legal, Zaliha aka fara saukewa, sai Khadijah da Munnirah kusan hanyar su ɗaya. Cikin taimakon Allah suka gama jarabawarsu, Ranar da suka yi last paper din su washegari uwargidan Baba isah da yan uwanta suka kawo lefen Khadija aka saka ranar biki sati biyu masu zuwa. Duk wani kayan ciye ciye na tarbar baki Hajiyar su Munnirah ce ta ɗauki nauyin shi ita da Baban Munnirah, Mami ta zo daga Legas, matan yayyen Umma duka sun zo banda matar Baban ABU da Baba Dr. Da Bichi za a kai Lefen sai Hakimi yace a karɓa a nan kar a wahalar da mutane , Daddy shi ne uban Amrya, dan haka Baba kawai sai ganin alert yayi mai nauyi na kayan gadon Khadijah, Daddy yace hakkin shi ne yayi mata kayan ɗaki tinda shi ne ubanta. An kawo lefe set ɗaya, kaya ne na gani na faɗa masu tsadar gaske, kana ganin kayan kasan zababbu ne kaya ne na Alfarma, komai yaji abun masha Allah sai fatan Allah ya kade fitina, aka yi raha irin ta dangin miji dana mata, uwargidan Baba Isah ta buɗe jaka ta fito da sarkar gold, Aunty Balki matar Baban sama ta karkace ta saki guda, ta ce "yata tayi goshi." Aka yi wasa da dariya Munnirah da su Ibrahim ne masu kai snacks da lemo mota na baki ,ita Amarya tana gidan su Munnirah ita kaɗai, tayi mamaki da bata ga Zaliha ba ta ɗauka zata zo dan tin jiya ta faɗa mata, haka Mamanta tazo tana tambayar Umma ko akwai abunda zata taya su na aikin tarar baƙi. Umma ta ce babu aiki. Ita kaɗai ta na ta tunani ta ji an ɗaka mata duka, Munnirah ce ta bakin ta ya ƙi rufuwa tace "taso mu je sun tafi mu kalli kaya." Khadijah ta ce ba zata ba "ke wlh da gaske nake sun tafi sai na gida kawai." Khadijah ta ki kula ta, Munnirah sai hakura ta yi ta kyale ta. Munnirah ta ce "Maman Zaliha ta zo, bayan baƙin sun tafi baiwar Allah wai baƙi ta yi suka riƙe ta har da kuɗin gudummawar ta 10k, Umma ta ƙi karɓa har da kukan ta wai Umma ta raina, sai da Mami ta saka baki, Zaliha dai da halin Mamanta tayi da ta ji daɗi, na tambayi ina Zaliha, da mamaki tace min wai tun safe ta ce mata ta taho nan, nace mata to ba ta zo ba." ita dai Khadija sauraren Munnirah kawai ta ke yi ba tare da tace mata komai ba. Wayarta tayi ringing, deke an bar mata waya yanzu a hannun ta tunda sun kammala exams, "Habibi" sunan ya bayyana akan screen ɗin wayar, Munnirah ta leƙa, "Ango ne yake kira." Zaliha ce kwance a ɗaki abun duniya yayi mata yawa, Mama bata nan sai ita kaɗai a gidan, tunani take shi kenan kullum su ne a karkashin su Khadija, ita abin haushin ma wai har yanzu sai dai ya ce mata Zakiyya ko sunanta ya kasa riƙe wa mwsss ta ja tsaki, amma Munnirah kamar shi ya raɗa mata sunan, zuciyar ta sai ƙara ingiza ta take yi, tana cikin wannan halin taji anyi sallama ta ɗaga kai ta amsa, Suwaiba ce ƙawarta, amma ta ɗan girme mata, ta miƙe tana mata sannu da zuwa. ita ke mata kitson attachment, suka gaisa tace "ƙawata ya na ganki wani iri." Zaliha tace "wlh ina cikin matsala ne." "mu je soro muyi kitson a can ya fi iska." Zaliha kamar ta ce bata da lafiya ba zata iya kitso ba sai kuma ta daure dan sosai Suwaiba ta ke biyan ta kuɗin kitso. Suwaiba irin yaran nan ne masu ƴanci, don watarana ba a gida take kwana ba, ta taɓa aure ta fito, har kofar gidan su ake zuwa a ɗauke ta a mota (Allah ya shirya mana zuria). Sun fara kitso wayar Suwaiba tayi ƙara ta daga, tace "shegiya Hajara na kusa shiga daga ciki, ta ɗanyi shiru tana saurarar me ake faɗa mata sai kuma ta yi dariya, "an faɗa miki ina ramin kaina ne? sai dai mutum yayi ni kuma in dai yayi min sai na shiga ko ta tsiya ko ta arziki, kinsan auran dana fitoma mijin Rashida ne ƙawata na aure, toh dama bariki akwai Amana ne, shike nan goben kizo ina nan tun safe zuwa dai 6 zan fita. shike nan sai kin zo ɗin." ta katse wayar. Kamar don Zaliha aka yo wayar nan sai cewa tayi "ƙawata wlh nima ƙawata ce ta haɗu da miji ta dalilina saura sati biyu bikin ta bakiji raina ba, Suwaiba ta juyo ta kalli Zaliha, "kuma kina son shi? Idon Zaliha ya ciko da hawaye tace "hmmmm! Nan ta kwashe labarin komai ta bawa Suwaiba, har da cewa an munafunce ta, Suwaiba ta luka wata Uwar ashar, "ƙawata share hawayen ki wannan zuwan dana yi Allah ne ya kawo miki ni, baƙin cikin ki ya ƙare gobe goben nan ki zo ki same ni a gida da wuri za mu fita, duk inda Azahar ta yi mun dawo, ita din banza ya kika ce sunan shi?" Suwaiba ta tambaya. Zaliha tace "ban daɗe da fara aiki a kamfanin suba, ni dan baƙin ciki ma ko sunan shi ban tambaye ta ba, ita kuma sunan ta Khadijah." "to kiyi ƙoƙarin samun sunan shi, ba wanda zaki tambaya mana kiji?" Zaliha ta yi ɗan tunani tace "Akwai Alkasim zan tambaye shi. Ji take kamar an saka ta a Aljanna, kamar ma ance buƙatar ta ta biya, ta mayar da hankali suka gama kitson, Suwaiba zata bata kuɗi ta ce ta bar shi, ta rakota har kofar gida, Suwaiba ta ƙara jaddada mata ta zo da wuri fa. Washegari Zaliha ta yi wa Mama ƙaryar ta tafi gidan su Khadijah, tana fita ta nufi gidan su Suwaiba, tana zuwa suka kama hanyar gidan Malam, a unguwar kurna ne can ciki duk sammakon da suka yi saida suka tarar da layi, suka samu waje suka zauna har layi yazo kan su suka shiga. Wani mutum ne baƙaƙirin dashi babu kyan gani ya jibga kaya a jikin shi fuskar shi sai maiko ta ke, yana zaune a kan buzu ga ƙato carbi mai dubu a gefen shi da wasu shirgin litattafai a gefe, ga wata fata a rataye kamar ta Akuya, anzaye ɗakin da wasu irin abubuwa kamar duma. Zaliha sai bin ɗakin take da kallo, wani irin kamshin turaruka masu hawa kai sun gauraye ɗakin. Ya kalle su yace "Maraba da malama Suwaiba yau ke ce a tafe." Tace "ni ce Malam ƙawata na kawo." ta faɗa tana nuna masa Zaliha, ya kalli Zaliha, "ina aka baro Amarya? gasu can suna siyan kayan ɗaki ina kika shiga?" Zaliha ta wani gwalalo ido cike da mamaki, yayi dariya yace "kar ki damu tun shigowarku an sanar da mu." "yawwa Malam na Zaure" Suwaiba tayi maganar tana sake gyara zama, ta fara yi masa bayani, ya jawo wani kulli ya buɗe kasa ce a ciki ya fara wani za ne dashi ya san me ya ke zanawa, yayi kamar minti sha biyar yana abu ɗaya sannan ya ɗago ya kalle su, "gaskia sai dai ku yi haƙuri auren nan sai an yi shi, dan yana cikin zanen kaddararsu, sai dai idan ta tare mu ma zamu yi amfani da damar mu mujuya ta ta fita daga gidan ke ki shiga, cikin zaƙuwa Zaliha tace "Allah yasa." yace "wannan ba wani abu ba ne mai wuya, ki kwantar da hankalin ki kar ki nuna damuwa duk abunda ake yi na biki ki shiga a yi da ke, bayan ta yi sati daya da tarewa ki dawo mu fara ɗora aiki." "Toh babu abunda zaka bata tayi amfani da shi?" Suwaiba ta tambaya, yace "babu komai ta dawo bayan Amarya ta tare da sati ɗaya. Suwaiba ta kirgo kuɗi ta bashi, "toh sai na sake ɓullowa." ya ce "ya al'amuran naki." "komai yana tafiya yadda nake so." Suwaiba ta faɗa, suka yi masa sallama. Ranar farin ciki a wajen Zaliha kamar an ce mata an ɗaura aurenta da Tahir. Mami, Aunty Balki Matar (Baban sama) da Hajiyar Munnirah ne suka tafi Hayfa furniture's anan aka siyawa Khadija Royal bed, suka dawo mahogany aka siya mata wani set ɗin gado da kujeru set ɗaya, sun so siyan set biyu na kujeru toh falo daya ne, Dan har sun je sun ga gida 2 rooms ne ,sai falo daya,kitchen, da store, kowane room da toilet a ciki, compound ɗin gidan baifi yaci motoci 2 ba, suka zo kamfanin LG suka siya mata electronics. Sai da Mami ta kara kwana uku ta koma Legas sannan biki saura sati biyu, ana biki saura kwana uku zata ƙara dawowa, Kayan gara kuwa Babancikin gida ne ya dauki nauyin sa, Baban ABU kuma kyautar wani filin shi yayiwa Khadija, haka Baban sama ya turawa Baba kuɗi masu yawa, Baba Dr shi ya ɗauki nauyin events ɗin da Khadijah zata yi, sun tsara za su yi luncheon ranar Alhamis, jumma'a za a ɗaura aure a Bichi. Ranar Asabar za a dawo a yi yini da walima a tourist camp da yamma a kai Amarya. 💫 UMAYMAH 💫 ✍️A&A PEN FOLLOW OUR WHATSAPP GROUP VIA THIS LINKhttps://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3 https://wa.me/+2348039352724 VOLUME ONE EPISODE 3️⃣9️⃣ An sha shagalin bikin Khadijah, dangi sun taru ba kaɗan ba, kasancewar she's the first daughter da suka fara aurar wa a family, dangi sun yi kara anyi hidima. Wannan aure ya sake fito da gatan Khadija. Baba Isah shiya tsayawa Tahir akayi komai na biki, ana ya gobe ɗaurin Aure Yasir ya iso Nigeria. Yasir har gaban su Daddy yaje suka gaisa ya sake jaddada musu saƙon Ummi da amincewar su akan Auren. Zaliha ta saki jikin ta kamar babu komai a rants, akasha hidimar biki da ita, danma Munnirah nayi mata cikas, sannan yawancin dangin Khadija Munnirah suka sani. Saiya zama na indai maganar ƙawa ake kowa Munnirah yake kira. Amma duk da haka Zaliha ta danne zuciyar ta ta nuna babu komai. Yanzu jin ta take freely tinda tana da mafitar ta a hannu, sai take jin zuciyar ta sakayau. Alhamdulillah an gama taron biki lafiya an kai Khadija gidan mijinta Tahir dake Ƴankaba Hadejia-road. gida ne flat ɗan madaidaici, gaba ɗaya gidan bazai wuce one Plotty ba, ginin gidan gwanin sha'awa komai yayi daidai. Yadda iyayen ta suka tsara mata gidan dole ya burge ka. Tinda aka kai Khadija gidan Tahir Zaliha bata jeba, kullum take lissafa sauran kwanakin da suka rage mata su koma wajan Malam na Zaure, jin kwanakin take sunyi mata nauyi, gani take kamar an ƙara tsawan dare da yini. Kullum inta tina Khadija na gidan mijinta sai taji wani irin tashin hankali da baƙin ciki ya tokare mata zuciya. Cikin ikon Allah anaya gobe zasu koma wajan Malam Zaliha ta tashi babu lafiya sosai take jin jiki. Faɗin baƙin cikin da Zaliha ta shiga da wannan ciwon ma ɓata baki ne, tana cikin halin ciwo ta kasa hakuri ta kira Suwaiba tayi mata bayanin halinda take ciki. A daren ranar saiga Suwaiba tazo dubiya da kayan dubiyar ta niƙi niƙi. Zaliha ta yinƙura ta tashi da ƙyar, tace" Kai amma nagode ƙawata, harda wannan hidima haka." Suwaiba tabi Zaliha da kallo tana sakin wani ɗan iskan murmushi, tace" Ah ah ashe kema Shegiyar ce ina kallon ki haka, nina ɗauka kin haƙura dana jiki shiru. Zaliha tayi sauri ta rufe wa Suwaiba baki, tace" Rufa min asiri, kinsan yadda nake ji kuwa, hmmmm bazaki gane ba, ni yanzu tashin hankalina lokacin da Malam ya bamu harya wuce bamu koma ba, wallahi kullum da baƙin cikin Khadija nake kwana." Suwaiba ta kwashe da dariya harda rangaɗa guɗa, tace" Kinga baki da case da Malam mutumi na ne fa, yanzu dai tinda naga ciwon naki harda rashin kuɗi da shan magani shirya muje na kaiki Chemist, nan da kwana biyu zaki jiki normal, in yaso sai mu koma wajan na zauren." Zaliha ta kalli Suwaiba kamar zatayi magana sai kuma ta fasa, tace" Ai da wajan nasa muka fara zuwa, ƙawata na matsu ayita ta ƙare, Khadija zataci ubanta sai tayi dana sanin sani na saina ƙunsa mata baƙin ciki, harni zata munafurta. Hmmmm! Kinsan shegiyar tinda tayi Auran nan yau kwana goma ke nan ko nema na bata sake yiba. Suwaiba tayi shewa, "Ta neme ki kiyi mata me? Tana can ta cin amarcin ta, kedai shirya muje karki ɓata min lokaci akwai wajan wanda zani kar yajini shiru. Zaliha ta miƙe da ƙyar ta watsa ruwa, tana shiryawa Suwaiba tace" Wai ina Maman ku, tinda na shigo naji gidan shiru?" "hmmmm! Taje gidan su Khadijah wajan Umman su, muje na gama." Direct Chemist Suwaiba takai Zaliha akayi mata duk abinda ya dace ta biya kuɗin sannan suka yi sallama akan sai jibi zata zo suje wajan Malam. Kamar yadda Suwaiba tace kwana biyu a tsakani sai gata, suka ranka ya wajan na Zaure, basu samu layi ba, kai tsaye suka shiga wajan sa, yana ganin su ya kwashe da dariya ya nuna Zaliha da hannu, "Tsinanniya kin dawo ke nan? Bai jira tayi magana ba yaci gaba da cewa" Yanzu aikin ki zai yi kyau, amma kafin nan saikin kawo min mahaɗin aikin." Jikin Zaliha na rawa tace" Allah ya taimake ka duk abinda kace zan kawo, indai burina zai cika ya Aureni." Na Zaure ya ɓata rai kamar ba shi ne mai dariya ba, yace" Ke!!!!!!!! Karki sake kiramin Allah anan, kinsan da Allah kika zo nan?" Sai kuma ya wai waya wajan Suwaiba yace mata" Baki faɗa mata anan ba'a kiran kowa ba saini?" Suwaiba tayi far da ido tace" mutumi na a yafe mata sabon shiga ce bata san sabgar ba." Zaliha gaba ɗaya ta tsorata amma saboda kwaɗayin san cikar buri haka ta daure tace" Na tuba, amin afuwa." Na Zaure ya zubawa Zaliha ido yana wani lashe baki kamar maye, yace" Zaki kawo min gashin kanta da sawun Mijin nata, aikin ki zai yi kyau idan kika kawo komai kamar yadda muka buƙata." Bakin Zaliha kamar zai yage dan murna tace "an gama Malam wannan ai shi yafi komai sauƙi zan. Kawo su." Suwaiba ta gyaɗa kai "Mutumin mene ne ladan akin ka. Budar bakin na Zaure sai cewa yayi" In baƙuta ta biya zata bamu ladan aikin mu kamar yadda aka saba, ke ai kin sani." Cike da murna Zaliha suka baro wajan na Zaure tana ta yi wa Suwaiba godiya, Suwaiba tace" Karki damu ƙawata ana tare. **** A yau Khadija ta cika sati biyu a gidan Tahir, kuma a yau ne Zaliha ta shirya zuwa gidan ta. Wajan karfe Shaɗaya na rana Zaliha ta shirya ta cewa Mamanta ta tafi gidan Khadija. Allah Sarki Mama baiwar Allah nan da nan ta haɗowa Khadija kuka da daddawa har da kanwa taba Zaliha tace ta kaiwa Khadija, tace mata in sha Allahu ita ma zata zo ta ganta in ta sake kwana biyu. Zaliha cike da takaicin Mama ta karɓi kayan kaɗin ta fita daga gidan tana mitar halin Mama a ranta. Adaidaita sahu Zaliha tahau ya kaita har ƙofar gidan Khadija, ta jima a tsaye tana knocking gate ɗin kafin Khadija ta tazo ta buɗe, Khadija na ganin Zaliha ta rufe baki baiwar Allah cike da murna, tace" Lallai Zaliha sai yanzu zaki zomin ai har nayi fushi ma, shigo. Zaliha ta harareta kamar gaske "ni matsa min na shiga kona koma inda na fito tinda ba nemana kike ba." Khadijah na dariyar maganar ta suka shiga cikin Falon tare, Zaliha ta cire mayafin ta ta faɗa kan kujera tana sake ƙarewa falon kallo, a ranta tace eh lallai an kashe kuɗi anan. Khadijah ta wuce kitchen ta ɗakkowa Zaliha lemo mai sanyi da ɗan abun taɓa wa, ta ajiye mata a gaban ta tana cewa" Allah Zaliha banji daɗi ba da baki zo min ba, na tambayi Munnirah ina kike tace min ita ma bata sani ba, dan tin bayan biki baku sake haɗu wa ba." Zaliha ta ɓalle murfin lemo, saida ta kora sannan tace" hmmm! Ke dai kawai kin samu gidan miji kin manta dani." Zaliha tayi maganar tana rarraba ido "ko dai mai gidan yana ciki ne nake ta zuba." Khadijah tayi dariyar ta mai kyau tace "lah yanzu ya fita Company." Zaliha ta jinjina kai, yanzu ya fita a ranta, hmmm mutumin da baya lattin zuwa wajan aiki, lallai aure daɗi. Khadijah ta yunƙura tace" Zaliha bari nayi wanka nazo naji ina kika ɓoye min kwana biyun nan." Zaliha ta miƙa mata saƙon Mama, "Au kice wanka ma zaki shiga, nifa ince irin wannan yijabi haka da kika zindima." Khadijah bata, bata amsa ba sai murmushi da tayi ta karɓi saƙon Mama tana godiya ta wuce dashi kitchen sannan ta shige ɗakin ta. Tana shigewa ɗaki Zaliha ta buga wani uban tsaki, "Kin kusa yin gaba." Khadijah bata jima ba ta fito sanye da lace baƙi anyi masa ɗinki umbrella, kayan yayi mata kyau, saita fito a Amaryar ta shar da ita. Ta iso falon tana baza ƙamshi, Zaliha ta ɗago kai ta kalle ta ai sai ta buɗe baki ta miƙe tsaye tana ƙarewa Khadija kallo, wani mugun abu taji

Chapter 20 of 29