Share this page
bata? badai madarar gida kika bawa mage ba? "Toh Siyama bata fi ta 100 ba na bata." Umma tace "ta 100 da kika siya da kuɗin ki ba." Umaimah ta turo baki baga. "Umma bari na je, na taho da keke yana ƙasa a ɗakin Hakimi inaso na ɗan rage aiki kafin gobe." Khadija ta faɗa tana miƙe wa, "toh sannu Allah ya yi jagora." ai Umaimah na jin zancen keke ta miƙe tini ta ri ga Khadijah fita daga ɗakin. Tana fitowa daga ɗakin Umma har tayi hanyar steps zata sauka ƙasa sai kuma ta juya ta tafi ɗakin su. Umaimah na shiga ɗakin su taji motsin ruwa a toilet Amira ce a ciki, kawai sai tayi tsalle ta haye kan gadon su, Amira na fitowa daga toilet ɗin Umaimah ta kalle ta tana daga kwancen tace "Amira wanne kaya za mu ɗauka?" Amira ta jawo trolley ta buɗe ta ɗakko wani material da aka dinka musu tare brown colour, jikin shi kamar tissue an yi musu gown, Amira ta ce "wannan zan saka ranar Sunday, gobe kuma zan saka wannan atampar, chiganvy ce mai gold dinkin skirt da riga turquiose blue dinkin ya dace da atampar. Umaimah najin haka ta fara zare ido, ita kam idan ba mantawa ta yi ba kayan duka suna wanki. Kullum fadan su da Umma bata san kayan zaman gida ba, bata san na fita unguwa ba, kowanne cakuɗasu ta ke yi san ranta. "Dan Allah mu canja wasu. Umaimah ta faɗa, "saboda me?" Amira ta tambaya. "wlh nawa duka suna wanki." Amira tace "gaskiya ni su nayi niyyar sawa." "ke Amirar nan fa yar rainin hankali ce, dan ma kin samu ina lallaɓa ki. shikenan na gode." Fuuu ta juya ta fita daga ɗakin. Baba da Umma suna zaune suka ganta kamar an jefo ta "na faɗa miki ki din ga yin sallama kafin ki shigo, Umaimah kullum nuna miki hanya ake yi kina ƙara shiga dawa." Umma tayi maganar tana hararar ta. "yaya aka yi ne?" Baba ya tambaye ta. Ta taɓe baki " ba Amira bace kayan da zamu tafi Bichi wanda ta zaɓa mana ni nawa suna wanki, kuma nace ta canja ta ki." Umma tace "maganin ƙazami kenan." Daga faɗin haka da Umma tayi Umaimah ta dage ta rinƙa kuka bil haƙƙi ta cika musu kunne, dama kaɗan take jira. Baba yana ta yi shiru bari a kira Amiran, amma tayi funfurus ta ƙi kula shi, Umma kuwa da ita ta jawo kukan ta yi tafiyar ta kitchen ta haɗowa Baba tea ta barsu anan. Malam Musa ne yayi sallama a ƙofar shigowa falon, Baba yace ya shigo. "ah ah Uwar masu gida me ya faru? Malam Musa ya tambayi Umaimah da taƙi yin shiru, Baba ya ce "kyale wannan, An yi service ɗin motar?" "eh Alhaji anyi." Malam musa ya miƙa wa Baba key ɗin motar. "toh sai da safe Alhaji, wajen ƙarfe nawa zan shigo?" "wajen 11am" Baba ya faɗa, Tinda Baba da Malam Musa suka fara magana Umaima ta yi shiru tana sauraro su kamar ba ita ce mai kukan ba, suna gama magana ta cigaba da kukan ta. Malam Musa yana fita Ibrahim ya shigo, ya gaishe da Baba ya samu waje ya zauna. Baba yace "yawwa Ibrahim duba min ka gani ko Babangida yana nan akwa aikin da na ke so yayi min yanzu." Baba ya faɗa kamar da gaske. Ibrahim yace "eh ya shigo tun ɗazu yana ɗaki bari na kira shi, ke menene kika cika wa mutane kunne da kuka? Ibrahim ya tambaye ta, Baba yace "ƙyale ta Amini, Maza jeka kiramin shi aiki zan saka shi, wanki zai yiwa Uwata, kayan da zata saka gobe zai wanke mata." ai Umaimah bata bari Baba ya dire maganar ba ta tari lumfashin shi da cewa "ah ah Baba zan canja wasu kayan, na fasa saka irin na Amiran. tuni ta haɗiye kukan, dama iya shege ne. Baba yana ɓoye dariyar sa ya ce "a yi haka kuwa uwata? a dai kira shi ya wanke mikin." "wlh Baba na hakura, Allah ba sai ya zo ba." "kin tabbata?" Baba ya sake tambayar ta. "na tabbata." "toh shikenan Ibrahim dawo ka zauna tinda ta hakura." daya ke Ibrahim sarkin zolaya ne sai cewa yayi "Baba ai da an kira shin tsab zai wanke mata." Da sauri Umaimah tace Uncle "ko dai so ka ke ya wanke min jiki da bulala ba, ni dai nace na yafe. "Ahto daa kika ce ba kya ji." Ibrahim ya faɗa yana murmushi. Ana haka Siyama ta fito daga kitchen mage ta na binta a baya. Umaimah na ganin Magen ta hau kiran "Sasi Sasi zo nan." Umaimah ta kirata. Umma ta kalli magen tace "Au har an raɗa mata suna? ta gyaɗa kai "Sasi sunanta." "toh ina goron sunan? "Abinda dama Mangoro na taho da shi zan rabawa yara muyi nishaɗi, kuma ayi partyn sunan Sasi Babangida ya yi min asara." Ibrahim na mata kallon tuhuma ya ce "me kika ce?" Sarai ta san abinda ta yi, amma sai cewa tayi "menene? "ni kike tambaya menene? bari ya shigo, Babangida ko?. Umaimah ta wani kwantar da murya "Haba Uncle Ibrahim Aminin Baba bafa haka na faɗa ba." Baba daya kurɓi shayi ya kusa ƙwarewa saboda jin daɗin bakin Umaimah, ta wani kwantar da murya kamar ba itaba. Umma tayi kwafa tace "hmm Allah ya nuna min randa zakiyi hankali." Uncle Ibrahim kuwa kawai kansa ya girgiza a ransa yace lallai ƴan matancin wannan ƴa tasu akwai kallo. "shikenan Allah ya kaimu wata jumaar sai ayi raɗin sunan." Baba ya faɗa. Yawanci ranar jumma'a Baba bayan masallaci babu inda yake zuwa yana gida, kusan akan idon shi yaran su ke taruwa su yi iface ifacen su a garden, wani lokacin ma yakan saka kujera yana kallon su har su yi su gama, kafin kowa ya watse, da farko gida gida Umaimah take zuwa ɗauko yaran kafin daga baya Iyayen yaran kesa wa a rako su, yaran sunsan Umaimah sun saba da ita sosai. Allah ya ɗorawa Umaimah jarabar son yara, da farko Umma ta so ta hanata amma Baba ya ce a kyale ta, yaran duk na kusa da gida ne be gaa wani abinda ba dai dai ba, tinda gashi iyayen yaran ke rakosu sometimes, sauda dama kuma yana wajen suke hidimar su, har abinci ya sa'a ake karawa duk jumaa saboda su. Umaimah sama ta koma ta ɗakko kayan ta exactly irin wanda Amira tace shi zata saka, Umma da Baba suna falon tazo ta wuce ta shiga ɗakin Uncle Isma. ***** 💫 UMAYMAH 💫 ✍️A&A PEN FOLLOW OUR WHATSAPP GROUP VIA THIS LINK https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3 https://wa.me/+2348039352724 VOLUME ONE EPISODE 1️⃣8️⃣ Uncle Isma don Allah taimaka min zaka yi please." Umaimah ta faɗa tana shigo wa ɗakin da kaya a hannun ta, yana zaune a kan study table yana assignment yace "me zan miki? "Dan Allah taya ni wanki za ka yi." "wanki da daren nan, me yasa baki saka a wanki ba tinda kinsan kina son sawa?" "Wlh Amira ce ta dage da su zamu Bichi, ni kuma nawa sun yi datti." ta tsaya kan shi da kayan a hannunta, "pls Uncle Isma ka ji." "Umaimah pls rufe min kofa sauro." ta koma ta rufe ta dawo "pls Uncle Isma." Yace "daɗi na da ke wutar ciki idan kina son abu yanzu yanzu." ya faɗa yana harararta. Umaimah tace "toh idan baka yi min ba wa zai yimin ubana na kaina." "bana son daɗin bakin nan naki." "Allah Uncle Isma kasan kai na hannun dama na ne, ina yinka over." "Toh kin tsaya a kaina, kya bari dai na gama assignment ɗin ko. Data zauna kan kujera sai kuma ta miƙe kamar an mintsine ta, ta tafi wajen keke tana taɓawa. Isma'il ya kalle ta "wlh yanzu Yaya ta tashi akan shi duk abunda kika ɓata zan faɗa mata ke ce." ta haye keken. "dan karambani ba fah ɗinki kika iya ba." "Da koyo akan iya Uncle Ismah, nifa dogaro da kai zan yi." ya rufe littafin ya ce mata ba ni kayan, ya karɓa ya nufi bandaki, har ta taso zata bi shi yace "malama zauna ina zuwa." ta koma kan Keke tana ta takawa yana ta ƙara kamar mai ɗinkin gaske. Uncle Isma bai jima a toilet ɗin ba sai gashi ya fito da bucket a hannu. Umaimah tace "Allah dai ya biya ka. muje na raka ka shanyar." suka fito daga ɗakin. ***** Bichi Gida ne babban gaske yanayin tsarin gidan sarauta ne mai sassa sassa daban-daban, akwai wajen masu aiki, shara, wanke wanke, da masu daafa abinci, tsarin gidan yana da babbar farfajiya mai girman gaske irin ta gidan masu mulki, sai ɓangaren Hakimi part ne babba tare da fadar sa inda ya ke saukar baƙi da zaman fada, anan yake jin koken mutane da ƙorafe ƙorafen su, matsalar gonaki ne, matsalar makiyaya, Rabon gado, rikicin filaye da sauransu, duka ana kawo matsalar gaban Hakimi ayi sulhu idan abin ya gagara ya turasu kotu. Dada ita kaɗai ce matar Hakimi tun Auren Saurayi da budurwa, ɓangaren ta na can cikin gidan ɗauke da babbar Rumfa (falo) sai ɗakuna guda 3 na bacci kowanne da toilet, a takaice fasalin gidan na gargajiya ne amma ta ciki gini ne na zamani, Dada Mace ce farar bafulatana, fara ce tas doguwa mai yalwar gashi, Hakimi kyakkyawan ne dogo baƙi mai ginan nan jiki. Duka ƴaƴan Dada kalar fatar Hakimi sukayo, kai hatta jikokin su yawancin su baƙaƙe ne chocolate color kyawawa Masha Allah, inka cire Sa'ad da yayo farin Dada da yanayin zubin jikin fulani. Sai kuma Baba shima fari ne tas wanda yake ɗa ne ga kanwar Dada Mairo wacce Umma taci sunanta. Tin bayan rasuwar Mairo riƙon sa ya dawo hannun Dada kamar yadda ta riƙe ƙanwarta tin bayan rasuwar Iyayen su har tayi mata Aure, haka Dada ta riƙe Baba tin bayan rasuwar ƙanwar ta, a hannun ta ya tashi tare da sauran ƴaƴan ta, wanda be sani ba zai ɗauka shima ɗan tane, dan Mairo na haihuwar sa ta rasu Dada tayi kukan mutuwar Mairo dan ita kaɗai ce ta rage mata a dangi na kusa. Baba da Baban Lagos tare suka taso dan sa'ani ne tsirar su ƴan watan nine Baban Lagos ya girmi Baba da shi. Tin farko Dada taso ta shayar da Baba sai Hakimi ya hana yace mata "a'a Bintu karki fara gudun gaba bamusan mai Allah zai yi a tsakanin ƴaƴan mu ba muna raye ko bayan mutuwar mu, ita matsalar shayar wa girma gare ta dan haka kiyi hakuri Bintu zaki iya riƙe kayan ki Allah zai raya miki Magaji ko baki bashi nono ba in sha Allahu." Wannan maganar ta Hakimi ita ce ta saka dole Dada ta haƙura aka rinƙa bawa Baba madarar Shanu da sauran dabaru irin na mutan da. Baba ɗa ne guda harda ƙari,.na daban ne a zuciyar Dada da Hakimi ba ƙaramin so suke yiwa Baba ba. Akwai ɓangare guda da aka ware cikin gidan sabida yaran su idan sun zo gari, duk da cewa su Baba sun yi gini a Bichi da gidajen su, amma sun fi sauka a gidan Hakimi in dai ba dadewa za su yi a garin ba basa sauka a gidajensu. Babban ɗan Dada ne kawai yake zama a Bichi, amma duka sauran yaran ta suna other state da iyalansu. Dada na zaune a kilisar ta Uwar murhu ta shigo ta risina tayi gaisuwa, Dada ta amsa mata sannan ta bata umarnin abunda za a ɗora, dan tasan duk inda suke suna dab da ƙarasowa. "Hajiya Bintu ƴar Fillo kenan kin kasa zaune kin kasa tsaye, duk ɗokin ganin yaran naki ne yasa yau ba a bani dumame ba. Hakimi dake shigowa rumfar Dada ya faɗa fuskarsa wa dace da murmushi. "Allah ya taimaki Mai gidan Bintu ni ba wani ɗoki da nake." ta faɗa tana miƙe wa, food warmers masu kyau ta ɗakko akan kilishi ta ajiye ta koma ta ɗauko ruwa da kunun zaki ta ajiye a gaban sa. "maigida wannan yaran shi da yake a kusa har yanzu be shigo ba." Hakimi ya wanke hannu ya kalle ta "zai zo ne kila wani uzurin ya rike shi, ni dai alfarmar da zan roƙawa Hadiza lokacin da ki ke son yankewa na ta fito da miji ya yi kaɗan, yaushe ta fuskanci mijin har suka saba?" Dada ta numfasa "za su fuskanta ne a hankali, na gaji da yawo da hankalin da Ibrahima yake min, wancan auren nata shi yayi uwa yayi makarɓiya ya hana kowa magana gashi be haifar da ɗa mai ido ba. Kai wannan turke Allah ya yaye mata shi, ita ba muni ba, ba rashin ilimi ba, ba rashin nasaba ba, shekara nawa rabon ta da aure, tin wancan gantalallen auren nata da baƙon haure, nifa dama ƙarfina aka fi, amma Ɗahiru bai kwanta min ba, shekera 30 mace na zaune gaban Iyayen ta, ba miji ta rasa ba taƙi Aure, ni ban taɓa ganin inda aka yi haka ba, lokacin da aka aura maka ni ban fi shekarar jikar Maryama ba, amma yanzu ina maganar uwarta Hadiza ace nayi hakuri lokaci yayi kaɗan, tsakani da Allah wanne lokacin kuma bayan na shekarun data kwashe a zaune." Dada mace ce mai tsage gaskiya, da riƙon addini da al ada sabida faɗin gaskiyar ta ake ganin ta kamar tana da faɗa, tana da zafi sosai dan bata ganin ba daidai ba ta ƙyale. Tana da son mutane da kyauta bata da kyashi hannun ta a buɗe yake, ga zumunci akwaita da tausayi, shiyasa kullum gidan Hakimi zaka samesa da mutane. Hakimi cikin dattaku yayi murmushi yace "Babu komai lokaci ne zata yi auren in sha Allahu." ta amsa da "Allah ya sa, idan son samu ne ma ace tayi azumi a gidan ta." Hakimi yace "nan da wata hudu fa kenan? Allah ya amince." "Ai ibrahima shi yake ɗaure musu kugu ace mace tana yawon shago ban taba ji ba, Auren dai shi ne mutuncin mace, su Dattijion ma sa'anin su daga masu yara 4 sai masu biyar, ga Mamuda nan yaran da aka goya su tare yaransa huɗu ga cikin na biyar." Hakimi yayi dariya yace "Bintu ya zaki haɗa rayuwar bariki da ta ƙauye, wani lokacin sai ki rikice ki yi ta faɗa ni kaina saina kasa gane kanki Bintu." Dada ta ja fasali "ay shikenan, kamar ma ba zaka goya min baya ba, naga alamar bakin ku ɗaya da yaran ka." "Wane ni Sama'ila Allah ya taimaki Uwar garke na, duk yadda kikace haka za'a yi." Dada ta wani karangai dakai "yawwa yanzu naji zance Mai gida." **** A'a uwata kenan yau hijabi aka saka? Baba ya ke yi wa Umaimah Magana ganin yadda ta fito cikin yijabi abinda bayi take ba, Umma dai kallonta kawai take, dan idan Umaimah tayi wani abun da bata saba ba to yana da manufah, yarinyar da idan ba islamiyya zata ba bata saka komai haka take yawonta indai ba abaya ba ce ta saka. "Amira shiga gaba". Baba ya faɗa, Baba da Umma suka zauna a baya suka saka Umaimah a tsakiya, ɗayar motar kuma Babangida ke tuki, Ibrahim a gaba, Khadijah da Hakimi a baya. Khadijah jikin ta a sanyaye tun jiya ta san wannan gangamin na Dada a kanta ne. Basu daɗe da fara tafiya ba Umaimah ta yaye hijabin ta. Ashe mage ta ɗauko, Umma takaici kamar ta rufe ta da duka, Baba yace "uwata tafiya da mage, me yasa baki bar ta a gida ba? "toh Baba naga ba kowa." Umma tace "idan kika bar wa Baba Rabi zata kula da ita ai, itama magen munafuka ta yi shiru wlh dana gani ba inda zamu da mage." "sai da nace kar ta taho da ita tace babu ruwa na." Amira ta faɗa. Malam Musa yace "ana ji da magen nan." yayi dariya. "sunan ta Sasi." malam musa yace "saci." Amira ta ce "Sasi." "ay to, Allah ya raya ta. Malam Musa nayin parking Umaimah ta buɗe motar ta fita da gudu tayi cikin gida. "sallama alaykum." Umaimah ke kwaɗa sallama tin daga kofar shiga shingen Dada, Hakimi ya kalli Dada "muryar wa na ke ji kamar Umaimah?" Dada najin haka ta mike ta fita. " Sassanunku da zuwa Baba Habi mai aikin Dada tahau musu maraba. "mai sunan Dada sannu da zuwa." Umaimah ta ce "ina kwana. "ina yini dai." tayi dariya da sauri tayi hanyar falon Dada, "ke lafiya? Dada da suka haɗu a ƙofar falon ta ta faɗa. ta yi ciki da gudu, tana matse matse "Dada fitsari nake ji." ga mage a hannu. "je ki maza kar ki yi min a wando." Umaimah ta shige ciki da gudu. Da Sallama su Baba da Umma suka ƙaraso tare da Amira da buhun gurasar Dada a hannunta, Dada baki a washe tahau musu sannu da zuwa, suka zazzauna, Hakimi na yiwa wa Amira wasa yace "matso nan ki zauna kusa da ni, yau ga tawa Amaryar." "Barka da rana, mun same ku lafiya." Baba ya tsugunna yana gaishe da Hakimi da Dada, murmushin Dada ya faɗaɗa tana son duka yaranta amma soyayyar Magaji daban take (Baban Khadijah), ko dan ɗan yar uwata ne tilo data rasu ta bar mata, a gaban kowa indai Magaji na waje manta fulatanci ta ke yi. "Magaji ya naga ka rame? Ince dai lafiya." Dada ta faɗa. Umma ta kalli Dada tace "Ni ban gani ba." "ah ah Azumi ya rame, Magaji me ya ke damun ka?" Iyaye kenan su duk girman ka a gaban su kai yaro ne, kafin Baba yayi magana Umaimah ta fito daga toilet ɗin cikin falon riƙe da Magen ta a hannu tace "wlh Dada Siyama ɗan zubi ta ke yi wa Baba, ba ƙoshi ya ke ba, kawai ba yarda zai yi ne, nima iko take min." "haba ko da na ji." Umma ta kalli Umaimah da mage a hannu ta ce "wa ya sa da bakin ki? Kuma da mage kika shiga banɗaki?" Hakimi yayi dariya yace "kaga jikar Maryama zo ki faɗa min ɗan zubin da ake yi wa Magaji, nima na yarda dan ba shakka gashi nan Azumi sai hanƙara kiba kike yi ɗana kuma a rame." Baba ya ce "wlh shirmen Umaimah ne." Dada ta kalli Umaimah da Magen ta a hannu "Azumi ku nema wa yarinyar nan maganin makarai, daga gani ba lafiya ba." Sallamar su Babangida ce ta katse hirar saiga su Baban Legas kamar a tare suke, an hargitse ana ta gaishe gaishe, Umaimah ta ajiye Sasi ta tafi ta ɗane Baban Lagos ya ɗaga ta sama yana dariya. Hidaya ta tafi ta rungume Amira ana ta murnar ganin juna. Mami tace "yau bari na kama kaina ta Amrya ake yi." Nan da nan ma'aikatan Dada sukai ta shigo da lemo da ruwa. Sunata raha aka kwaɗa kiran sallar Azahar Hakimi yace "aje ayi sallah a masallaci a dawo, suna fita suka haɗu da baban ABU zuwan shi kenan be ko shigo gidan ba, suka gaisa a tsaitsaye suka fara alwala. Dr da Munnirah motar su ta tsaya, suka jero Munnirah ta durƙusa tana gaishe da su Daddy, Dr ya kalli su Daddy yace "ga fa giwar ta wa nan sai yanzu muka iso." Daddy ya kai mishi duka a ƙeya aka kwashe da dariya, Munnirah kuwa kunya ta rufe ta haka ta lallaɓa ta shige ciki. Dr yayi ta wannan wasan da yayyen shi, ita fah Iyaye ta ɗauke su, ta faɗa a ranta. "Toh ku shiga kuyi sallah." inji Dada ta cewa su Mami. duk suka miƙe. "wannan yaron har yanzu be iso ba (danta na fari), ke Fatima zo ki kiramin shi." "wacce daga ciki?." Umaima ta tambaya. "jikar Maryama." Dada ta faɗa, sarai Umaimah ta san da ita Dada take, amma sai cewa tayi "wa kenan?" Hidaya da Amira suka sa dariya, sun san Umaimah ta tsani Dada ta ce mata jikar Maryama. "gani." "Yawwa ungo kira min wannnan yaron." "wanne yaro? Umaimah ta tambaya. "Je ki kawai kar ki sa min ciwon kai daga zuwan ki. zo nan Hafsatu." Hidaya ta je wajen Dada "ungo kamo min wannan yaron." 💫UMAYMAH 💫 ✍️A&A PEN FOLLOW OUR WHATSAPP GROUP VIA THIS LINK https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3 https://wa.me/+2348039352724 VOLUME ONE *Assalamu alaikum sisters muna barar addu'ar ku Allah yayi wa Aunty ɗin mu rasuwa shekaran jiya, muna roƙon Allah ya gafarta mata yayi mata rahama yasa aljanna ce makomar ta, iyayen mu da ƴan uwa musulmi gaba ɗaya.* EPISODE 1️⃣9️⃣ Maigida babu cefane. Dada ke yiwa Isma'il tsiya, bayan da aka idar da sallah ya shigo gida ya bar su Baba a waje. Ismael yayi dariya ya ce "Dada duk kaji da zabin dana ke aiko miki wa yake karba?" "Uhmm ba wani nan karyar kawai ba ko sisi." "Ah toh Dada ina suka maƙale, dole na bi ba'asi." "Ni fah hantsi ya dubi ludayi, don gaskia ni ban yi wani kari yadda ya kamata ba ga Sasi nan ma baiwar Allah ita ma yunwar take ji, Dada haka ake saukar baƙi?" Umaimah tayi maganar taba shafa ciki. "toh acici ba ki da magana sai ta abinci." Amira ta faɗa. "ni ce acici? Wlh bari Baba ya shigo." Dada tace "Abinci dai sai kin ture, sallah gaba ta ke da komai shi yasa aka fara yinta." "Dada amma dai a hadisin gidan nan ko? Dan nidai ba haka na karanta ba." su Umma suka fito daga ɗaki bayan sun idar da Sallah, aka ƙara gaggaisawa. Dada ta ce wa Mami "ina wajen su Sa'adu da Dattijo? "suna lafiya Dada sun kusa kammalawa ma su dawo gaba ɗaya." "Allah ya taimaka." ta miƙe ta fita bayan yan mintuna ta shigo tare da Habi aka fara jere abinci. "My sis gaba na faɗuwa ya ke yi." Khadija ta faɗa duk tayi wani iri kana ganin ta kasan a firgice take, Munnirah ta kalli Khadijah gani tayi jikin ta duk yayi sanyi, "babu komai ki kwantar da hankalin ki." "ya ya hankalina zai kwanta, bayan nasan gangamin nan ni aka yi wa shi." "khair in sha Allahu, Komai zai yi daidai my sis, wata rana sai labari, wata rana haka zamu zauna muna mayar da yanda aka yi." "Hmmm Munnirah zullimi kawai da fargaba

Chapter 10 of 29