Share this page
Momi ce ta fara cewa Dije "Sannu da Zuwa." Dije ta ɗago ƙananun idanunta fal masifa da bala'i ta kalle su goron data gama gogawa ta afa a baki sannan tace "nida gidan ɗana za'a yiwa sannu da zuwa? ko kuma Matar gidan Nana da gidan Mijin tane? Ai ku sannu da zuwa ta kama dangin naci da jaraba." Mai Kano ya dafe kai kunya ta rufe shi kamar ya nitse saboda abinda Dije tayi, tabbas Iyaye iyaye ne musamman uwa da Allah da Annabi suka ce abita, bashi da yadda zaiyi da Dije sai dai yayi addu'ar Allah ya raba su lafiya. Ran Tawakallatu a ɓace ta cewa sauran ƴan uwanta "dan Allah kumu je ciki." "Bansan kinji haushi ba sai naji saukar duka shegiya Fatakarkara." Dije ta faɗa tana furzar da goron bakin ta. Suna shiga ɗaki suka tarar da Safiya harta haɗa kayan da zasu buƙata ita da Husna. "Wallahi badan darajar tsufa da Abdullahi ba da sai naci mutuncin matar can." Aunty Momi ta faɗa ranta a mugun ɓace. "Barta da Allah Duniya ce kanta take wa." Cewar Aunty Sakina da jikin ta yayi sanyi da tijarar Dije, tabbas ɗazu labari Safiya ta basu yanzu kuwa da idan su suka gani. Abdullahi naso yaje ya bawa su Aunty Sakina hakuri amma tsoron abinda Dije zata ce ya hana shi dama tunda Safiya ta fita yake lallaɓa ta da ƙyar ya samu ta haƙura da zancen tafiyar da tace zata yi shima saida ya mata alkawarin zai saki Safiya sannan ta dawo ta zauna, tabbas ba tafiyar tata yake tsoro ba sai abinda duniya da ƴan gari zasu ce a kanshi, alkawarin sakin Safiya kuma yayi mata ne kawai amma badan yanajin zai cika ba saidan ya samu ta fasa tafiyar. Safiya ta fito hannunta riƙe da jakar goyo irin ta matafiya, Dije na ganin fitowar su ta miƙe tsaye tace "Mai Kano sake ta ta tafi gaba ɗaya bana son ta sake tako kafarta a gidan nan da sunan matar ka." "iya yanzu muka gama magana nace miki zan sake ta amma ba yanzu ba." ya faɗa hankalin shi a mugun tashe. "Saboda ita ta haife ka bani bako? Nonan Safiya kasha ba nawa ba ko?" "Subhanallahi" su Aunty Sakina da suka ji saukar zance wani iri suka faɗa. "Mai Kano inka bari Safiya ta fita daga gidan nan baka sake taba Allah ya isa Nono na daka sha, Allah ya isa zaman da kayi a cikina, Allah ya isa renon ka da nayi bazan taɓa yafe maka ba duniya da lahira." "Innalillahi wa inna ilaihirraju'un! innalillahi wa inna ilaihirraju'un!! Innalillahi wa inna ilaihirraju'un!!!" su Aunty Momi suka faɗa da ƙarfi wani irin tashin hankali da tsoro na shigar su lokaci ɗaya, Safiya data ɗaga kafarta zata sa a soron gidan da zai kaita waje ta dawo da ita baya ta tsaya a wajen ƙam kamar wacce aka dasa, ita kanta Nana tuwon data saka a bakinta dawo dashi tayi, Mai Kano kuwa wata irin muguwar zuface ta karyo masa lokaci ɗaya kuma mummunan Zazzaɓi yayi masa mugun kamu idanunshi har rufewa suke saboda tashin hankali. "Mai Kano saika zaɓi ɗaya ni ko Safiya da masifun cikin duniya?" Dije ta sake jifan shi da muna nan maganganun ta. Mai Kano da ƙyar ya samu ya miƙe jiri yana diban sa yayi taga....taga kamar zai faɗi cikin ikon Allah ya dafe bishiyar Dirimi da sauri ya tsaya kan ƙafafun sa, da taimakon Allah ya kawo kanshi inda Safiya ke tsaye idanunta sun bushe, tsawan minti biyu ya kasa magana jin kanshi yake kamar ana juya shi saida ya ambaci Allah sannan ya ɗauke idan sa akan ta a rarrabe kamar mai matsalar harshe ( Stammering ) yace "ki....k...ki gafarce ni." Sai kuma yayi shiru zufa na yanko masa kamar an zuba masa ruwa, saida yasa hannu ya yarfe gumin sannan ya sake kallon Safiya dake binsa da kallo kamar manyan idanun ta zasu faɗo ƙasa yace "Na...n.....na....sakeki saki ɗaya." Yana rufe bakin shi Safiya ƙafafun ta suka sare ta kusa faduwa ƙasa ƙyauran ƙofar soro ta riƙe tana murmushin ƙarfin hali ta cewa Mai Kano "Inada ciki wata biyu." Ita kanta bata zaci zaiji abinda ta faɗa ba bare ƴan uwanta dake bayan su, a zabure ya ɗago ya kalli cikin idon ta yana zare ido yace "ci....ci.....ciki dai na haihuwa Safiyya?" Kai ta gyaɗa masa, wasu hawaye masu zafi suka zubowa Mai Kano tabbas Allah Allah be ciki a irin wannan lokacin, tsawan shekaru suna fata da addu'ar ta sake haihuwa Allah bai basu ba sai yanzu da suke cikin jarabawa, "Alhamdulillah." ya faɗa yana burin fitar wannan ciki ya sassauta zuciyar Dije ta bari ya ci gaba da zama da matarsa. Su kansu su Aunty Momi jin Safiya nada ciki duk halin baƙin cikin da suke ciki saida suka gode wa Allah dan abune data riga ta cire ran sake haihuwa, su kansu ganin shekaru sun fara ja sun ɗauka ta gama ke nan, ashe tunanin su kuskure ne ba'a taya Allah yanke hukunci buwayi gagara misali. "Wake da ciki Mai Kano?" Dije ta tambaya a tsiyace, kana jin yadda tayi tambayar kasan babu alkhairi a cikin ta. Mai Kano jikin shi na rawa bakin sa a washe yace "wallahi Safiyya ce Iya kinga ikon Allah ko?" "Eh ni kuwa naga ikon Allah, wato ni za'a yiwa bariki da duniyan ci to wallahi kar nake kallon ku, ke Safiya ko cikin ne ma dake saikin bar gidan nan yau bare ban yarda akwai shi bama, tsabar munafunci da bariki shekara goma sha ɗaya tunda kika haifi Ma'u baki sake wani cikin ba sai yau da kikaji saki? To inma cikin gare ki jeki dashi gidan ubanki Ƙadiri anbar muku, kinga wannan." ta nuna Nana dake zaune tana kallon kowa ɗaya bayan ɗaya. "Mai haihuwa ce shi kansa ya sani badan Allah ya karɓe masa ba da yanzu Maza uku manoma gare shi, dukan su kuma yayun Ni'ima ne dan haka jeki keda cikin bana buƙatar ku a zuri'a ta." Ran Aunty Sakina yayi mugun ɓaci dacin fuskar Dije dan haka tana rufe baki tace "ke tsohuwar banza ki iya bakin ki karki jawa kanki abinda yafi ƙarfin ki, ke banda ƙaddara kowa yaga Safiya yasan ba sa'ar Auran ɗan ki bace tafi ƙarfin shi, ki tambayi ɗan ki inke baki sani ba ya baki labari." Dije tace "banyi mamaki ba dankin zagi tsufa na ina zaki san darajar furfura tunda a gidan ku babu tsofaffin arziki, Auran ɗana ne daga yau kun gama shi sai ku ƙara gaba." "Ke dai wallahi anyi tsohuwar Banza kalli halin da kika saka ɗan ki dan jaraba." Aunty Momi ta faɗa a ƙufule. Nan fa rigima ta kaure tsakanin su Tawakallatu da Dije, Mai Kano ya rasa inda zai saka ranshi kowa inya masa magana baya sauraren shi, abinka da yare yaren ma Yarabawa da energy ɗin su suke faɗan itama Nana ta shigar wa Dije nanfa gidan ya sake kacamewa har Umman Bishira (maƙociyar su) tajiyo hayaniya ta zagayo, da ƙyar aka samu rigimar ta mutu Umman Bishira taja Safiya da ƴan uwanta, Mai Kano kuma ya cewa Nana. "Kina sake yin magana a bakin Auran ki." Tanajin haka tayi muƙus, Dije ya fara roƙo tayi shiru, bakin ta sai kumfa yake da masifa ta kalli su Safiya da Umman Bishira tasa a gaba zasu fice daga gidan tace "Kuma wallahi ku dawo da Ma'u gidan Ubanta yadda kika zo ke kadai ke kaɗai zaki koma, inba haka ba har abada babu ita babu Mai Kano ta nemi wani uban bashi ba, yadda nace ko bayan ƙasa ta rufe min ido in Mai Kano ya dawo dake gidan shi ƙasan igiyar auren sa Allah ya isa ban yafe masa haihuwar shi da nayi ba to haka wallahi in baku dawo da Ma'u gidan nan ba babu shi babu ita har abada har bayan raina na raba tsakanin su, ta nemi wani uban bashi ba." "Tirƙashi." Umman Bishira ta faɗa, su Aunty Sakina zasu sake magana Umman Bishira ta hana ta tura su waje suka fita daga gidan, suna fitowa ƙofar gida kuma Safiya ta yanke jiki ta faɗi a sume jini nabin gefen ƙafafun ta.... Asibitin Gwagwarwa Tunda Likitoci suka shiga da Safiya ciki su Aunty Sakina ke addu'ar Allah yasa ba wata matsala bace ta same ta dan kusan minti 20 ke nan da shigar su amma har yanzu babu likitan daya bito, kana kallon su kasan hankulan su a tashe yake Umman Bishira ce ma mai ƙarfin halin dannar su, Aunty Momi ta Hango Yaya Ja'afar ya shigo cikin dogon falon sanye da uniform ɗin shi na police yana ta wai waye da alama akwai abinda yake nema, batayi mamakin ganin saba saboda aikin su maybe wani suka kawo, hannu ta daga masa tana faɗin. "Yaya Ja'afar." Yana gano su yayo wajen da sauri, kan yayi magana Tawakallatu tace "Ah wani kuka kawo asibiti Yaya?" "Ka jimin maganar banza, ina Safiyar take? Yanzu Kemi ta kira ni tace kuna Asibiti da Safiya ina take?" Aunty Sakina da saurin kuka saita hau share hawaye, gaba ɗaya suka yi shiru suna kallon sa aka rasa mai bashi amsa a cikin su. "Wannan wanne irin iskanci ne ina tambayar ku kun tsare ni da ido." Ja'afar ya faɗa da alamun ɓacin rai a muryar sa. Umman Bishira ce tayi ƙarfin halin ce masa "Tana ciki tunda suka shiga da ita basu fito ba." Tana rufe baki saiga Likita na tahowa wajen su yace "suwaye suka kawo Safiya?" Da sauri suka miƙe tsaye Ja'afar yace "gani." Likita ya miƙa masa hannu suka gaisa da alamun sanayya tsakanin su yace "Yallaɓai kai ne? Okay muje na ganka." Likitan yayi gaba Yaya Ja'afar ya bishi a baya suka jera, office ɗin sa ya buɗe suka shiga, saida ya cire Safar hannun sa ya zauna a kujerar shi sannan ya kalli Yaya Ja'afar da har yanzu yana tsaye yace "Ah Yallaɓai zauna mana." Kujerar gaban shi yaja ya zauna yana fuskantar Likita. Takarda ya janyo ya fara rubutu na ƴan seconds ni kafin ya yace "Yallaɓai ya kuke da Patient ɗina?" "Ƙanwa tace?" "Subhanallahi!" Likita ya faɗa yana kallon Yaya Ja'afar, sannan yaci gaba da cewa "kasan cewar jinin data zubar yayi yawa da farko muna bukatar jinin da zamu ƙara mata leda biyu karya wuce nan da 1 to 2 hours Please." "Okay in sha Allah Dr amma actually meke damun ta?" Yaya Ja'afar ya tambaya. Dr yaci gaba da rubutu sai kuma yace "Yeah, bayanin da zanma yanzu ke nan Yallaɓai, Safiya nada ƙaramin ciki gaskiya bana jin ya wuce 2 month amma inta tashi za muyi mata scanning dan mu tabbatar da kwanakin cikin, sannan jininta yayi mugun hawa irin wanda ba'a so, dole sai an kiyaye shigar ta damu da ɓacin rai inba haka ba komai na iya faruwa da ita ko cikin jikin ta, dan binciken mu ya tabbatar mana wani abu na firgici ne yasa ta shiga wannan halin, and gaskiya badan anyi gaggawar kawo ta asibiti akan lokaci ba da zaiyi wahala mu iya controlling cikin." Yaya Ja'afar yayi kasaƙe yana kallon Dr dan harga Allah jin maganar yake wani iri Safiya da hawan jini shi bai taɓa jiba, dama tana da shi ne ko yanzu ta samu? Likita ne ya katse masa tunani da cewa "Yallaɓai ga wannan dan Allah a siyo su kanta farka, akwai alluran da tana tashi muke so ayi mata, yawwa kuma jinin ayi ƙoƙari kanta tashi a samu." Ya kalli agogon hannun sa yana miƙewa. "akwai Patient ɗin dazan gani yanzu, nan da 2 hours allurar baccin da aka yi mata zata sake ta Please Yallaɓai don't take it long coz patient ɗina tana buƙatar su urgently." "Okay Dr." Yaya Ja'afar ya faɗa yana miƙewa suka fito tare. Wajen su Aunty Sakina yaje a gurguje yayi musu bayanin abinda ke faruwa, jikin su ya sake yin sanyi. "Karku damu in sha Allah zata samu lafiya, bari na kira su Abdussamad ko suna kusa suzo a duba nasu, Baba Habu baya gari tun shekaran jiya dama shike iya bawa kowa jini tunda nashi O+ ne, um bari naje ku kula da ita sai na dawo." ya faɗa yana juyawa hannun sa riƙe da wayar shi, su Aunty Momi muryar su a saɓule suka ce "Allah yasa a dace." Harya fara tafiya ya sake juyowa ya kira Tawakallatu tazo da sauri, yace "kada wanda yaje gida acikin ku fa kunsan matsalar Momma, in kuna bukatar wani Abu kuje gidan wani acikin mu kunji ko?" Tawakallatu ta daga masa kai ya juya ya fice daga cikin Asibitin.... _*WRITING.....✍🏻*_ *_MUTUWAR AURE.....!_* _(Ƙaddarar wasu ƴaƴan)_ *_Kanawa ne👌🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ _BOOK 1_ *_FREE PAGES_* ________________ *_WHATSAPP GROUP👇🏻_* https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3?mode=gi_t https://wa.me/+2348064789370 _________________ _EPISODE 11_ Kwanan Safiya biyu a asibiti tana jinya aka sallame ta, duk wannan kwanakin kuma su Momma basu san halin da ake ciki ba basu da labari saboda Yaya Ja'afar ya hana kowa ya faɗa sannan Baba Habu ya kira ya sake jan kunnen su. Ranar da za'a Sallami ta ƙarfe tara a Asibitin tayiwa Baba Habu da yake jirgin safe ya biyo ya iso da wuri, ya samu Aunty Sakina da Aunty Momi a asibitin dama kuma basa rabo da Asibitin, Yaya Kemi ce kaɗai suka hana ta zuwa saboda tana jego sai yau da Baba Habu yazo yace ta taho da Husna ta same su a gida. Likita ya shigo ya sallame ta, Safiya ta warware babu lefi sai dai ta rame sosai fuskar ta ta faɗa sai idanu. Suna fitowa Abdulgaffar na tsayawa da mota da mamaki yake kallon Baba Habu dan baisan ya dawo ba, sama sama suka gaisa yace "ɗauke su ku wuce gida zan biyo ku a baya." Sun sami Yaya Kemi harta zo, cike da mamaki Maman Sama ke kallon Safiya data yi zuru zuru, sai kuma ta maida hankalin ta kan su Aunty Momi tace "Lafiya na ganku haka? Meya samu Safiya duk naga ta rame?" Maganar Maman Sama ce ta fito da Momma daga ɗaki tana haɗa ido da Safiya gaban ta ya faɗi, kafin wani ya sake magana a cikin su Tawakallatu da Aunty Momi suka shigo Abdulgaffar na biye dasu a baya riƙe da hannun Husna. "A'a yana ganku a tsaye kuma?" Abdulgaffar ya faɗa, sai sannan Husna taga Mamanta tayi wajen ta tace "Mama ina Yaya? Mommy ta soya mana fara da yawa kuma taban na ɓoyewa Yaya nashi harda Baba ma." Husna ke maganar cikin jin daɗin ganin Mamanta ba tare data kula da yanayin da take ciki ba, dama kwana biyun nan da tayi a gidan Yaya Kemi ba ƙaramar rigima tayi ba ita sai an kaita wajen Mamanta da Yayanta dare nayi kuma zata fara neman Babanta yadda kasan wata yar goye haka Husna take, yanzu shekarun ta na haihuwa zasu kai goma sha ɗaya amma har yanzu bata da sabo ga maƙon uwa, duk yaran su na zuwa hutu gidan ƴan uwa amma banda ita, tafi yarda ko ina ne suje tare da Mamanta ko Yayanta su dawo gida tare. Hannun ta Safiya ta kama tana sakin murmushi tace "Husnan Yaya tace wa Mommy ta gode ko?" Bakin Husna a washe tace "eh Mama na cewa Mommy na gode kuma Yaya ma nace mata ya gode." Shigowar Baba Habu da Yaya Ja'afar ce ta katse hirar Husna da Maman ta, ya rusuna ya gaida su Momma da kulawa suka amsa suna yi masa sannu da zuwa, ƙannen shi ma suka gaishe shi tare dayi masa sannu da zuwa. Kowa ya hallara a babban Falon gidan matan su da mazan su kowa yana nan. Husna na zaune kusa da Momma Yaya Ja'afar ne ya fara magana da cewa "Alhamdulillah yau an sallamo Safiya daga asibiti ta samu sauƙi muna addu'ar Allah ya ƙara mata lafiya da hakuri." Gaba ɗaya suka amsa da "Amin." Yaci gaba da cewa "mun samu labarin abinda ya faru da ita kamar yadda Sakina Tawakallatu Momi da Kemi suka faɗa min na yiwa Baba Habu bayanin komai da shawarar su muka binne zancen har zuwa yau da aka Sallame ta ta dawo gida." Aunty Momi ce ta sake bada labarin duk abinda ya faru a gidan Safiya har cin mutuncin da Dije tayi musu da yadda tasa Mai Kano ya sake ta da ƙarfi, da suman da tayi suka kawo ta asibiti da taimakon Mijin maƙociyar ta (Umman Bishira). Aunty Momi na rufe baki Maman sama ta fashe da kukan tausayin ta, Momma kuwa mace mai tawakkali da haƙuri Safiya dake share hawaye ta juya ta kalla sai kuma ta ɗan saki Murmushi mai ciwo ta fuskanci Baba Habu tace "ita kuma Safiya ƙaddarar ta da jarrabawar ta ke nan a Rayuwa Abubakar? Ta dawo gidan nan da Baffa kwanan sa huɗu da haihuwa, tayi reno babu ubansa babu taimakon sa, yanzu kuma Auran da muke mata murna da tunanin Allah ya dubi wahalarta ta baya ya bata Miji mai santa da kulawa da lamarin ta shima ya mutu, Auran Safiya ya sake mutuwa? Auran da Alhaji ya daura da kansa, saida ya mutu bayan ransa, lokacin da baya Duniya ƙasa ta rufe masa ido sannan Auran ya mutu?" Momma taja numfashi tana share hawayen daya zubo mata. "Me Safiya tayiwa Maman Abdullahi? Haka kawai ta zaɓi ta kashe musu Aure saboda ta isa? kodan ita ce ta haife sa? bayan saki kuma harda guzurin hawan jini? a shekarun Safiya ace har ta kamu da hawan jini." Baba Habu yace "kuyi haƙuri Momma haka Allah ya ƙaddara mata, Allah ya bata wuyan ɗauka, Safiya kiyi haƙuri ki barwa Allah komai karki tashi hankalin ki." Yayi shiru yana kallon Husna dake sharewa Mamanta hawaye tana ɓata fuska, tausayin yarinyar yaji ya kama shi, a shekarun ta ace iyayen ta sun rabu gata mace dole akwai tashin hankali da tausaya wa, jin zuciyar sa na neman karyewa sai ya ɗauke kansa daga kan Safiya da Husna ya fuskanci Iyayen su da ƴan uwanshi ya fara magana cikin ilimi da yarda da ƙaddara yace "Ni naji daɗi da Alhajin mu baya raye wannan abun ya faru dan na tabbata da yana raye Abdullahi ya saki Safiya wallahi baƙin cikin haka na iya sashi cikin wani mummunan hali, Allah shiya halicci Safiya kuma shiya tsara mata rayuwa dan haka ina so musa a ranmu komai ya faru da ita ƙaddara ce daga cikin littafin ƙaddarar ta." Falon ya sake yin shiru kowa na sauraren shi, yace "Zan ɗauki Safiya na tafi da ita Lagos can gidana tayi renan cikin ta acan harta haihu, bayan ta haihu sai muga abinda Allah zai yi, duk abinda Safiya ta haifa kuma zamu riƙe sa kamar yadda uwar Abdullahi tace amma nasa ayi mana duk abinda ya dace na shaidar Safiya na ɗauke da cikin Abdullahi dan baza mu amince a batawa zuri'ar mu suna ba." Baba Habu yayi shiru yana tauna abinda zai faɗa yanzu dan yasan ba zai yiwa kowa daɗi ba musamman Safiya da ƴan uwanta Mata saidai yin hakan shine rufun asirin su dana Husna gaba ɗaya. "zan ɗauki Husna na maida ita gidan Mahaifinta da hannu na kamar yadda Kakar ta ta buƙata, baza mu riƙe taɓa badan bama santa ba saidan Mace ce ita, a al'adar Bahaushe kuma ya mace mutumcin ta gidan Ubanta, sannan suna da tsaurin ra'ayi akan yaran da suka rasa riƙon iyayen su Maza dan haka zamu maida musu ita Allah ya raya ta." Tunda Baba Habu ya fara maganar maida Husna gidan Babanta Safiya ta ɗora hannu aka tasa kuka sai kuma ta rungumota ta riƙe ƙam, yana rufe bakin shi Yaya Kemi ta ɗora da cewa "gaskiya Baba Habu maganar maida Husnah gidan su ba mafita bace saboda mutanen nan sun nuna basa sonta, kuma yarinya ce babu abinda ta iya yiwa kanta, tsakani da Allah wannan shawarar batayi ba." Tana dasa Aya a zancen ta Aunty Mansura tace "ai maganar maida itama a barta kawai sune matsiya ta mu ko sun kai irinta ɗari zamu iya riƙe su." Su Aunty Sakina ma kowa ya fara tofa tashi albarkacin bakin nan fa Falon ya kacame da hayaniya maganar dai ɗaya ce basu goyi bayan a maida Husna gidan Baban taba. Yaya Ja'afar ranshi a ɓace ya kalle su dama kuma shi akwai sa da zuciya ga faɗa murya a sama yace "to baku isa ba wallahi ko Baba Habu bai maida itaba ni saina kaita, in yaso in an kaita su kasheta su faɗa mana jana'izar ta zamu je mu taya su binne gawar ta." Abdussamad duk haƙurin sa yau jin abunda Uwar Abdullahi tayi musu ransa yayi mugun ɓaci dan haka shima yace "kawai a maida ita baza mu riƙe musu ƴa a gidan arna ba tunda nasu musuluncin daban yake dana kowa, akai ta su koya mata kalar nasu." Kowa a Falon saida yayi mamaki dajin furucin Abdussamad dan kowa yasan shi mutum ne mai haƙuri kusan halin su ɗaya da Safiya sai ayi abu ɗari bai ce komai ba amma yau kowa yasan an kaishi ƙarshe tunda har yayi magana haka. Abdulgaffar da Abdulganiyyu kuwa cewa su kayi "Baba Habu kai ka kula su ma kawai ka ɗauke ta mukai musu ita duk ma yadda zasu yi da ita suyi." Rigima ke neman tashi a cikin Falon dan Safiya ta riƙe Husna suna kuka abin gwanin ban tausayi, su Yaya Kemi kuma sun dage ba za'a maida ita ba yayin da Mazan suka ce basu isa ba maida ita ya zama dole, da ƙyar Baba Habu ya samu kowa yayi shiru. "Maman Sama da Momma baku ce komai ba?" Baba Habu ya faɗa yana duban su Momma da suka yi zuru suna kallon abinda ke faruwa. Maman Sama ce ta fara magana da cewa "Abubakar na fahimce ka amma yanzu dole sai an maida Husnah? mai zai hana a bari ta sake girma saita koma." Ajiyar zuciya Baba Habu ya sauke yana kallon Maman Sama dama yasan baza su gane abin da yake nufi ba amma dole dai haka zasu haƙura, maganar Momma ce ta bawa kowa mamaki da tace "Abubakar ka mai da ita nina amince maka, nasan Hausawa nasan me suke nufi da maganar da Kakarta ta faɗa, sannan nayi imanin a yau da Alhaji na raye zai goyi bayan a maida ita dan haka Safiya kiyi haƙuri ki yiwa takwarata addu'a Allah ya raya ta." Managar Momma ta sake tada hankalin Safiya su Aunty Sakina kuwa kuka suka saka yadda kasan wanda akace musu Husna ta mutu. Maman Sama bata so a maida Husna ƙarshe ma fushi tayi ta kama hannun Safiya ta miƙe rike da Husna ta jata suka fita daga falon, Abdulgaffar zai bisu Yaya Ja'afar ya girgiza masa kai ya koma ya zauna, su Aunty Mansura ma tashi suka yi suna masifa, Yaya Kemi ce kawai ta zauna suka ƙarasa maganar da abin da ya kamata suyi. Suna uwar ɗakin Maman Sama a zaune, Husna na kwance akan ciniyar Mamanta su Aunty Mansura sun zagaye Safiya dake ta share hawaye har yanzu, Yaya Kemi ta shigo ɗakin Baba Habu na biye da ita a baya. "Wai Abubakar me kake nufi ne daka sake biyo mu nan?" Maman Sama ta faɗa ranta a ɓace, baice mata komai ba dan yasan halin ta da rigima daƙin karɓar abinda bai mata ba, wajen Safiya ya wuce ya zauna a gaban ta, idanunta a jeme ta ɗago ta kalli

Chapter 10 of 31