Share this page
ni yace "Barira wacece haka a kwance jiki duk yayi fushi?" "Husna ce fa baka gane taba ko?" "Wacce Husnan?" Malam idrisa ya jefawa Umma tambayar dan harga Allah shi bai gane wace ce a kwancen ba saboda kwanciyar rufda ciki da Husna tayi saboda bayan ta ya samu balance ɗin shan iska dan azabar da yake mata. "Husnan Mama Safiya cefa nan gidan Malam Abdullahi Mai Kano." Umma ta jawowa Baban Bishira godon bayanin da zai gane da wuri. "Subhanallah subhanallahi Subhanallahi!! Maiya sami jikin ta haka? Ɗazu fa da safe tare muka taho da ita lafiya na ganta." Baban Bishira ya yayi maganar hankalin sa a tashe. "Wallahi nima ɗazu bayan tafiyarsu Bishira makaranta ta shigo min nan sai kaga yadda ta shigo babu daɗi, anan muke tare da ita har su Bishira suka dawo daga makaranta bayan sunci abinci sun fita wasa kofar gida Faiza ta shigo na tambaye ta ita tace min an kirata a gidan su to bubu jimawa kuma sai gata ta sake shigo min a wannan halin da ka ganta." Malam Idrisa yanajin bayanin da matar sa ke koro masa yana gyaɗa kai da mamaki tare da kokon to yace "to meya sami jikin ta kaha?" "Ina zan sani Malma amma dai wannan daga gani duka ne." Umma ta bashi amsa tana share hawaye sai kuma taci gaba da cewa "Allah ya sani bayan tafiyar Safiya naso na rinƙa shiga ina duba yarinyar nan amma sai naji tsoron kar ace gulma ce take kaini tunda ba gaisuwar mutunci muke da matar uban ba shi yasa bana zuwa kuma dama kwana biyun nan kullum Bishira sai tace min bata ganin ta a makaranta." Malam idrisa daya gama jin duk bayanin matarsa saiya sake duban inda Husna ke kwance tana numfashin ciwo yace "Duka dai, Barira yanzu sai a daki mutum haka kamar wanda akaiwa bulalar haddi?" Umma tace "Hmmm!" kawai tana kallon shi, sai kuma yace "kinga yanzu duk abar wannan maganar Bishira tashi muje ki rakani a kira Norse ɗin can yama sunan ta?" "Aunty Nurse." Faiza ta bashi amsa, yace "Yawwa muje kimin sallam da ita tazo ta duba jikin nata dan naga sai rawar sanyi take in yaso daga baya koma meya same ta maji." Malam Idrisa yayi maganar yana yin gaba Bishira ta bisa a baya. ......Basu jima da fita ba suka dawo tare da Aunty Nurse Umma na ganin su ta tashi daga gaban Husna Aunty Nurse ta matso kusa da ita tana kallon shatin bulalan da suka kwanta a jikin ta da cibiyoyin ta a hankali take san ɗago da ita Husna ta kasa tashi saida Umma ta taimaka mata sannan ta iya zama tana rintse idanu saboda azaba sai kuma ta saki kukan azabar da bayanta ke mata, kukanta baya fita sosai saboda muryarta data dashe idanun ta kuwa sunyi wani irin ja. Ga mamakin Umma sai taga Aunty Nurse ta ɗauki jakarta zata juya da sauri Umma tace "Aunty Nurse ita ce mara lafiyar fa ya zaki tafi kuma?" A wulaƙance Aunty Nurse ta kalli Umma sai kuma ta juya wajen Baban su Bishira tace "dama wannan ta'asar akayi a gidan ka shi ne aka kirani nayi fixing matsalar gani Nurse ɗin mahaukata? to bazan duba taba ku kaita asibiti in suka saku nemo ƴan sanda kwayi musu bayanin yadda aka yi mata wannan dukan rashin imanin." Ran Aunty Nurse a mugun ɓace take maganar dama kuma ita irin matan nan ne da basu da tsoro ga faɗin gaskiya, Aunty Nurse babbar maca ce kusan duka rukunin unguwar ita ke duba su, har haihuwa tana karba a gidan ta, tana da kirki amma fa akwai faɗa dan irin matan sakkotawan nan ce bata da tsoro ƴar kai tsaye ce, kanta tsaye take faɗin gaskiya babu ruwan ta da girman ka ko yawan kuɗin da zaka bata, indai ka tsallake iyakar ka yanzu za'a jiku. Sai da Aunty Nurse tayi maganar kuma Umma ta gane inda zancen nata ya dosa da dalilin da yasa tace ba zata duba jikin Husna ba saidai suje asibiti, wato ta ɗauka ita ce tayi mata wannan dukan. "subhanallahi." Umma ta faɗi a ranta a fili kuma saita dubi Aunty Nurse da sauri tace "haba haba Aunty Nurse wallahi ba abinda kike tunani bane ya faru ba yata bace." Cikin zafin rai Aunty nurse ta sake cewa "Dama ke ina kika isa kiyiwa diyarki wanga duka ai wallah saidai a dakar miki, wato ƴar abokiyar zaman kice shi ne kika so ki karta, wai mata mii yasa baku da imani?" Umma tayi murmushi mai ciwo amma sai bata ji haushin maganganun Aunty Nurse ba dan tasan mata fiya da haka ma muna iya yi akan ɗan kishiya, mai makon Umma taji haushi sai ta shanye tace "Haba Aunty Nurse Musulma ce fani cikakkiya ma kuwa rashin imanin Barira bai kai tayi wannan ɗanyen aikin ba, haba haba Allah ya sawaƙe min dukan ƴar wani ma haka bare ƴar kishiya da inda kara da zaman mutumci a tsakani ai ƴata ce, wannan da kike gani ƴar makotan muce yadda kika ganta muma a haka muka ganta ta shigo mana tausayin rai da zaman arzikin da mukayi da uwarta kan tabar gidan ubanta shi yasa muka kiraki ki taimaka ki dubata kan ubanta ya dawo." Umma na dire maganar ta juya jikin Aunty Nurse yayi sanyi ta dubi Umma tace "Ayya baiwar Allah yi haƙuri ki fahimce ni a matsayina na uwa wallahi takaici naji da naga irin dukan da aka yiwa yarinya ƙarama haka." Umma dai bata sake magana ba har Aunty Nurse ta gama duba jikin Husna ta kira gidanta a waya ta faɗi duk abinda take buƙata su kawo mata. Ba'a jima ba saiga ɗanta ya kawo mata duk abinda ta buƙata, allurar zazzaɓi data samun relief tayi wa Husna sannan ta ɗaura mata ƙarin ruwa saboda jikin ta ya saki da yawa. Saida ta gama duba ta sannan tace "gata nan in ruwan ya ƙare ki cire mata ai zaki iya ko?" Umma ta ɗaga mata kai, wajen Baban Bishira ta juya ta bashi paper data rubuta magani akai tace "dan Allah a bata wannan maganin tasha na shafawar kuma a shafa mata yau inba haka ba ciwukan jikin ta za su bubbuɗe." Malam Idrisa ya karɓi takardar yayi mata godiya suka fita tare saida ya bata kuɗin aikin ta sannan ya wuce Dorawa ya koma shagon shi daga nan zai taho da maganin. ******Tunda Husna tabar ɗakin ƙawar Nana Zahira taci gaba da zuba mata mugwayen shawarwari akan Husna ita kuma Nana ta buɗe kunne tana ɗauka ɗaya bayan ɗaya suna shewa dan dama ƙawaye ne tun zamanin yarinta garin su ɗaya, ita Zahira tun Auran fari nan Kano aka kawo ta sai yanzu da Nana ta dawo kusa da ita Amintar tasu ta sake tashi. Bayan tafiyar Zahira Nana taci gaba da uzurirrikan ta hankalin ta kwance ko tunanin ta leƙa ɗaki taga wani hali Husna ke ciki batayi ba, sai walwalar ta take tana sake jinta a sake, ranta fes tanajin ƙarfin gwiwar sake samun damar kafa wani ɗan bar samun nasara akan Husna, ta koma mata yadda take so. "cikin ruwan sanyi zan sa ki raina kanki yadda ko ance ki motsa daga inda kike baza kiyi ba." Nana ta faɗa tana jin zuciyar ta wasai. Saida akayi sallar Magarba sannan Nana tayi maganar inda Husna ta tafi shima Ni'ima ce ta shiga ɗakin su taga bata ciki take faɗawa Nana. "Ma'u fa bata cikin ɗaki tunda na dawo kuma ban ganta a waje ba." Ni'ima ta faɗa tana fuskantar Nana da taci gaba da aikin ta, ko a jikin ta tace "duk ma inda taje ta dawo." Daga nan kuma taci gaba da sabgogin gaban ta har akayi sallar isha'i babu Husna babu dalilin ta, tunda Ni'ima ta faɗa mata ɗazu tare ta gansu da yaran makotan su ta tsarawa ranta irin makircin da zata faɗawa Mai Kano inya dawo. Yauma bai shigo gidan ba da wuri sai bayan sallar isha'i, yana tafe yana tunanin ya kamata gobe ya wuni a gida kamar yadda ya saba yanayi wasu lokutan, dama ya kwana biyu bai zauna a gidan ya wuni ba, raban shi da wunin gida tun kan a fara wannan hatsaniyar ta dawowar Nana gidan sa da tafiyar Safiya. Dan haka ya yanke wa ranshi gobe a gidan zai wuni, haka kuma kamar yadda ya saba duk lokacin da zai yi wunin gidan yana siyan ɗanyen nama da kayan miya masu yawa ya tafi dashi yauma saida ya tsaya ya siyi nama mai yawa da kayan miya sannan ya siyawa su Husna tsaraba, ya tsaya a wajen masu saida gugguru ya siyawa Husna dan yasan tana son shi sannan ya taho gida yana Murmushin yadda zasu kwashe da Husnan sa gobe da safe, yasan zuwa lokacin da zai shiga gidan tayi bacci dole sai gobe za su haɗu. "Sannu da zuwa." Nana ta faɗa tana dire masa ruwan data ɗebo a kofin silver, saida yasha ruwan mai sanyi data ɗebo a randar ƙasa sannan ya dube ta yace "Husnah har tayi bacci ko? Ga tsarabar ta nan na bawa Ni'ima tata." Mai Kano ya faɗa yana miƙawa Nana ledar kusa da shi. Nana tasa hannu ta ɗauki ledar tana duba abinda ke ciki a ranta tace "ai kuwa haramiyar ta wannan ba rabanta bace." A fili kuma sai ta numfasa ta kalle shi fuskar ta na nuna damuwa tace "hmmm! Baban Ma'u ai yau tunda ka fita nake fama da Ma'u ta tafi makaranta amma taƙi tafiya nayi lallashin amma fir taƙi tafiya wai ita sai an kaita wajen Mamanta da Yaya Baffa, daga karshe dai fakar idona tayi ta fice daga gidan nan saida na farga bata nan nasa Ni'ima ta duba min ita ashe wai tana wajen yaran makota suna wasa a waje can Ni'ima ta gano ta, tunda tazo taci abincin rana kuwa ta sake koma wa bata ƙara dawowa ba, dama yanzu nake cewa ko gidan matar nan ta kusa damu zan shiga naga in tana can na sako ta a gaba mu dawo gida." Tunda Nana ta fara rattaɓo masa bayanin Mai Kano ya dakata da abinda yake yi yana kallonta daki daki yake bin maganganun ta yana lissafa su a cikin kwakwalwar shi, lokacin da Nana ta dire zancen ta kuwa gaba ɗaya kallon mara lissafi da hankali Mai Kano yake mata dan inba haka ba shi bai ga abinda zai sa tun rana bakaga yaro ba kuma kaci gaba da zaman jiran shi ya dawo ba har zuwa wannan lokacin. Toshi ya tsaya ya bata amsa ma koya takan zancen nata ai gani yake sake ɓatawa kanshi lokaci ne, dan haka ya tsallake ta kawai ya wuce ya fice daga gidan ya barta da baki buɗe tana bin bayan shi da kallo. Nana taji haushin ƙin tankawar da Mai Kano baiyi mata ba dan a tsarin ta ba haka taso tattaunawar tasu ta kasance ba, taso ya tanka mata ita kuma ta samu hanyar da zata sake cusa masa wani mugun tunanin mara kyau akan Husna. Mai Kano na fita gidan makocin shi Malam Idrisa ya nufa a bakin ƙofar gidan yayi Sallama tare da Kwankwasa kofar gidan, yayi haka wajen sau biyu kafin Malam Idrisa ya fito, a mutumce suka gaisa sama sama abun harya ɗan bawa Mai Kano mamaki amma sanin yau da gobe sai Allah kawai saiya share ya fuskanci makocin nashi yace "wallahi yanzu na dawo gida mai ɗakina ke dafa min Husnah na tare da su Bishira tun rana bata dawo gida ba." "Uhmmmmm!" Malam Idrisa ya faɗa yana kallon shi wallahi ji yake kamar ya rufe Mai Kano da duka dan takaici. "Dan Allah ayi mata magana tazo mu tafi gida, Husnah ba dai rigima ba." Mai Kano ya faɗa yana ɗan sakin murmushi. Sama da ƙasa malam Idrisa ya dube shi sai kuma yace masa "lallai fa rigima, to Allah ya kyauta Malam Abdullahi, sai dai da yake kasan su yara amana ce Allah ya bamu dole sai ana saka musu ido saboda gudun shiga fushin Ubangiji, yanzu dai kayi hakuri ka koma gida dan Husna tayi bacci sai dai zuwa gobe da safe in Allah yasa muna raye saita dawo gida." Mai Kano yabi Malam Idrisa da ido kamar yace a taso ta dan haka kawai yake jin zuciyar shi taƙi nitsuwa amma sai kuma yayi wani tunani yace "haka ne, shike nan Allah ya nuna mana goben." "Amin ya Allah." Baban Bishira na faɗin haka ya juya yabar Mai Kano tsaye a wajen, mai Kano kuwa da mamakin yadda makoncin nasa yau yake masa magana ya bi bayan shi da kallo, shi dai yasan tsawan zaman su da Malam Idrisa ba haka suke gaisawa ba kamar ana faɗa,sosai ake ganin mutuncin juna, haka Mai Kano yabar Kofar gidan Malam Idrisa jikin shi a saɓule. Ranar kwana yayi yana jijjuya maganganun Malam Idrisa, kamar fa magana yake faɗa masa a fakaice "to meya janyo haka?" Ya yiwa kanshi tambayar da babu amsa sai kuma yace wa kanshi "koma mene ne goben zakaji tunda wunin gida zakayi." Baban Bishira ya koma cikin gida ya tadda Umma na kwashe kwanukan daya gama cin abinci, a bakin gado ya zaune yana labarin yadda sukayi da Baban Husna. "Allah ya kyauta." Umma ta faɗa tana yin waje, dan wallahi tuna maganar ma ɓata mata rai take. _WASHEGARI_ Husna ta tashi babu zazzaɓi sai ɗan banzan ciwon jiki dake damun ta, jikin ta kuwa jinshi take kamar ba nata ba gaba ɗaya jinshi take a daddaure musamman bayan ta, haka fuskarta tayi wani iri, manyan idanun nan nata sun sake fitowa waje sai dai maimakon farin su na halitta yanzu sunyi ja, su Bishira na tafiya makaranta Umma ta tashe ta da kanta ta zuba mata ruwa a buta mai ɗan ɗumi tace taje tayi Alwala. A hankali Husna ke tafiya daga ita sai ɗan pant Umma na binta da kallon tausayi saida taga ta fara alwalar sannan ta shige ɗaki danta nemo mata rigar da zata iya sawa. Bata daɗe da fara alwalar ba taji an turo ƙofar gidan taci gaba da alwalar ta ba tare data juya ba, ruwan data ɗebo zata wanke fuska ya sulale daga hannun ta ya zube a ƙasa a dai-dai lokacin da taji muryar Mamanta tana sallama. "Assalamu alay........" Sallamar Safiya ta maƙale a maƙoshinta dai-dai lokacin da tayi ido biyu da bayan Husna tsugunne ta bawa kofar shigowa gidan baya. Bata sake samun ƙarfin halin yi wata magana ba saida ta ƙaraso inda Husna ke tsugunne ta dagota danta sake tabbatar wa kanta Husnan ta ce dai ba wata ba, jikin ta take ƙarewa kallo cikin tsoro kamar wacce bata taɓa ganin taba. Husna kuwa tunda taji muryar Mamanta kukan daya tsaya mata tun jiya ya sake dawowa sabo, sai dai kukan nata baya fita sosai saboda dashewar da muryar ta tayi. Umma taji kamar anyi Sallama amma jin shiru ba'a shigo ba sai bata fito ba taci gaba da dubawa Husna rigar da zata iya sawa acikin kayan Bishira wacce ba zata yi wa jikin ta susa ba dan tun jiya pant ne a jikin ta har yanzu. Umma taci gaba da burkita cikin kayan Bishira sai kuma taji kamar tashin magana ƙasa ƙasa jin haka yasa Umma tabar sif ɗin a buɗe ta fito kamar daga sama tayi ido biyu da Safiya dake juya Husna tana tambayar ta meya sameta amma Husna ta kasa bata amsa sai kuka. Rai da zuciyar Safiya a mugun ɓace ta fizgi hannun Husna tayi hanyar waje da ita, ganin haka Umma ta fara kiran sunan ta. "Maman Husna tsaya dan Allah karki fita da ita a haka? Tsaya tsaya dan Allah." Mama taji maganar Umma amma saita ki tsayawa taci gaba da tinkarar kofar fita daga gidan ganin bafa tsayawa zatayi ba Umma tasa gudu tacim mata hijabin ta ta riko tana janta ta dawo baya. "Safiya dawo ciki dan Allah, dan Allah dawo ciki nasan ranki ne ya ɓaci amma yi haƙuri dawo ciki na samowa Husna kaya karku fita a haka." "Umman Bishira bazan iya ba kiyi hakuri amma wallahi bazan zauna ba." "To naji amma duk ma inda zaku je tsaya na dakko mata kaya." Badan tana ganin kima da mutumcin Umma ba da wallahi bazata tsaya ba. Suna haka Malam Idrisa ya shigo gidan Umma tace "yawwa Malam dan Allah hanata fita da ita a haka bari na kawo mata kayan da zata saka." Umma ta juya ciki da sauri. Safiya duk halin tashin hankali da baƙin cikin da take ciki saida ta cewa Baban Bishira "ina kwana?" Murmushi yayi ganin duk ta rude mai maimakon ya amsa gaisuwar ta saiya dube ta da Husna cikin tausayin su yace "kiyi hakuri Maman Husna jarrabawa ce ko wanne bawa da irin tashi." Wallahi bata so tayi kuka ba amma yadda Malam Idrisa yayi mata magana saida zuciyar ta ta karye har bata san lokacin da hawayen da take ta danne wa suka zubo mata ba, hannu tasa tana share hawayen wasu suna zubowa. Da hanzari Umma ta dawo hannun ta riƙe da sabon hijabin Bishira ta kama hannun Husna tasa mata ya saukar mata har ƙasa kuwa dan dama yayi wa Bishira yawa ita kuma Husna ta fita tsayi. Umma na gama sawa Husna hijabin Safiya bata ƙara ko sakon ɗaya a gidan ba ta fice, su Umma suka bi bayan ta da kallo. Dai-dai lokacin da Safiya ke fita daga gidan Malam Idrisa riƙe da hannun Husna hakan yayi dai-dai da lokacin da Mai Kano ya miƙe ya cewa Ni'ima. "zo muje ki kira min ƙanwar ki." Yayi gaba Ni'ima ta bishi a baya Nana kuma ta rakasu da harara hankalin ta kwance dan ita bata ɗauki dukan data yiwa Husna a bakin komai ba. Tunda Mai Kano ya tashi yake kallon hanya yaga ta inda Husna zata shigo gidan amma yaji shiru har takwas ta wuce babu ita babu labarin ta, ganin bata shigo ba har yanzu haƙurin shi ya ƙare kawai ya yanke hukuncin zuwa ya taho da ita da kanshi. Safiya bata kai ga fita daga layin ba Ni'ima ta shiga gidan su Bishira kiran Husna yana tsaye a ƙofar gidan yana jiransu su fito, da mamaki yake kallon Ni'ima data fito daga gidan ita kaɗai yace "A'a ƴar Iya ina Husnan?" "Baba wai yanzu Mama ta zo suka tafi da ita." Mai Kano yaɗan ya mutsa fuska yana kallon Ni'ima dan bai gane kan zancen ba. "Mama kuma yaushe tazo?" Ni'ima bata da amsar tambayar sa dan haka saita bishi da ido, yace "Kinga shiga in Baban Bishira na ciki kice ina sallama dashi. "To" Ni'ima ta juya ta koma cikin gidan. Tare suka fito da Malam Idrisa, Baba yace "jeki gida gani nan zuwa." Ta juya ta tafi shi kuma ya dubi Malam Idrisa a gajar ce suka gaisa yace "Husna ce naji shiru bata dawo gida ba shi ne nace ƴar Iya ta kirata sai kuma tazo min da zancen daban gane kansa ba?" Mai Kano yayi maganar yana haɗa duka hankalin shi akan Malam Idrisa. "Eh, nima na dawo karin safe naga Maman ta tazo basu daɗe da tafiya bama ita ƴar uwar ta shigo neman ta." A hagunce Mai Kano ya ke kallon shi ganin yadda yake faɗa masa maganar hankali kwance, kamar ya tambaye shi koda wani abu daya faru ne sai kuma yayi wani tunani ya basa hannu tare dayi masa godayi ya juya ya koma gida yana rarraba tunanin shi. Koda ya shiga gidan bai cewa Nana komai ba ya fara shirin tafiya Birget, haka kawai yake jin akwai wani abu a ƙasa inba haka ba yasan Safiya ba zata zo ta tafi da Husna haka kawai babu sanin kowa a cikin su ba "gaskiya akwai wani abu." Ya tabbatar wa kanshi. "Baban Ma'u ya naga kana shirya wa kuma? Ba kace yau bazaka fita ba?" Nana ta faɗa sanda ta shigo ɗakin taga yana saka kaya. "Eh Birget zani." Iyaka abinda yace mata kenan ya zagaye ta ya fice riƙe da mukullin mashin ɗin sa... _*WRITING.....✍🏻*_ *_MUTUWAR AURE.....!_* _(Ƙaddarar wasu ƴaƴan)_ *_Kanawa ne👌🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ _BOOK 1_ *_FREE PAGES_* ________________ *_WHATSAPP GROUP👇🏻_* https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3?mode=gi_t https://wa.me/+2348064789370 _________________ _EPISODE 4_ Mota ta sauke Safiya da Husna a ƙofar gidan su bululim bululim taja hannun Husna suka shiga cikin gidan ko ganin gaban ta batayi, a kofar gida ta wuce Abdulganiyyu da Abdulgaffar suna mata magana amma ko ganin su batayi ba bare taji me suke cewa. "Wannan lafiyar ta kuwa?" Abdulganiyyu ya faɗa yana duban Abdulgaffar. "Eh kamar dai da wani abu, ni kamar ma Husnah na gani a hannun ta fa." "Husnah kuma ita da take gidan su?" Abdulganiyyu ya faɗa da ɗan kokonto, sai kuma ya miƙe yace "bari na duba naga ko lafiya, Allah dai yasa lafiya take wannan saurin kamar zata tashi sama." Yayi cikin gidan. Safiya na shiga babban Falon gidan su ta saki hannun Husna ta zauna a kasan kafet ta ɗora hannu aka ta fashe da kukan da saida Maman Sama ta fito daga Kitchen da gudu hannun ta riƙe da ludayin miya, Wallahi saboda rudewa da ganin kukan da Safiya ke yi ko Husna dake tsaye a gaban ta bata gani ba ta wuce. "Innalillahi Safiya lafiya? Ke Safiya lafiyar ki kuwa kike fasa kuka irin wannan? Meya faru?" Maganganun Maman Sama da kukan Safiya ne ya fito da Momma daga ɗaki, saɓanin Maman Sama ita ta kula da Husna dake tsaye a gefe tana kallon Mamanta tana kuka sai dai ita nata sautin kukan baya fita. "Subhanallah meya faru kuma? Husnah waya kawo ki?" Momma ta faɗa tana riƙo ta. Safiya bata saurari lallashin da Maman sama ke mata ba bare tambayar da Momma keyi sai kuka take bil hakki, dan kuka ne da ta riƙe shi tun sanda tayi ido biyu da jikin Husna take so tayi shi. Suna cikin haka Abdulganiyyu ya shigo falon, shima Safiyar ya fara tambaya da. "lafiya?" Amma ta kasa bashi amsa sai kuka take babu ƙaƙƙautawa, ranshi har ya fara ɓaci dama shi kuma yana da zafi ga saurin zuciya, sai ayi abu yafi a irga a gidan ƙala baza kaji yace ba, in kuka sashi a zancen ku in bai masa ba yanzu zaice ba hurumin sa bane, a hali da dabi'a ya fita daban da sauran yan gidan amma fa in ka taɓo shi ta kwaɓe muku abun babu daɗin ji da gani, wannan yasa matan ke shakkar shi sosai dan baya wasa, su kansu mazan gidan tsakanin su dashi sai lallashi. "Ke dalla Malama in baza kiyi mana bayanin meya same kiba kiyiwa mutane shiru, kin zo kinsa mu a gaba da kuka ana tambayar ki lafiya kuma kina dojin." Ya faɗa da tsawar data sake ruda Safiya, Maman Sama ta rungume ta tana hararar shi. Safiya tana jikin Maman sama tana kuka tace "Yaya zasu kashe ta wallahi kashe ta zasuyi basa sonta dan Allah ku karɓo mini ƴata nizan riƙe ta da kaina." "Wa za'a kashe ɗin?" Abdulganiyyu ya jefa mata tambayar yana kallon ta sama da ƙasa dan bai gane kan zancen ba. Maimakon ta basu amsa kawai saita tashi daga jikin Maman Sama ta kamo hannun Husna dake kusa da Momma ta janyo ta tsakiyar su, dukan su suka bita da kallo, a tsakiyar su ta tsaida Husna tasa hannu ta cire mata hijabin jikin ta. "Innalillahi wa inna ilaihirraju'un." Momma ta faɗa tana ɗauke kanta da barin kallon jikin Husna daya farfashe. Maman Sama sarkin saurin kuka saida ta fasa nata ihun sannan ta ƙwala kiran. "Husna! Husnah me nake gani haka a jikin ki? Meya samu jikin ki haka?" Maman Sama ta

Chapter 4 of 31