Share this page
daɗi, bakin Alhaji Ƙadiri yaƙi rufuwa saboda murna sai faɗi yake "Akwai albarka a hannun ka Abdullahi." Abdussamad kuwa yafi kowa farin ciki yaji daɗi kamar ya goya Mai Kano. ******Tun bayan dawowar Mai Kano gidan Alhaji Ƙadiri shakuwa ta sake shiga tsakanin shi da Baffa wani lokacin ma shi yake rakasa makaranta kanya tafi kasuwa. Kullum inya tashi a kasuwa kuma saiya tsaya ya sayi alewa minti wacce yake rabawa yara sadaka, amma fa tsarabar Baffa daban take data kowa. Mallam Bahaushe yace wai mai ɗa wawa nan da nan mutumci ya shiga tsakanin sa da Safiya Autar su Abdussamad, harga Allah da farko bai san ita ce Maman Baffa ba dan bata fiya zama a gidan ba, sosai Safiya ke ganin mutumci da girmansa ko bai ganta ba indai ta ganshi saita ce "Baba Abdullayi ina kwana?" A bakin Abdussamad ya samun labarin ita ce ta haifi Baffa amma sun rabu da mahaifinsa tun yana jariri, tayi Aure da wani babban mutum mai suna Alhaji Manu Kwabo ɗan asalin ƙabilar Margi ne, Auran soyayya suka yi, Alhaji Manu Kwabo ɗan kasuwa ne sosai a Kantin Kwari yana cikin Manyan ƴan kasuwar Kwari, sun haɗu da Safiya ranar ɗaurin auren Abdulganiyyu yazo wajen ɗaurin aure ya ganta. Yana da mata wacce suka yi Aure tun bashi da komai har yayi arziki saidai tsawan shekaru basu taɓa samun haihuwa ba, dangi sunyi sunyi dashi ya ƙara Aure yaki sai dai ya kama ƴaƴan ƴan uwa ya riƙe har yayi musu Aure. Alhaji Manu Kwabo mutum ne mai kirki da zumunci. Farkon auren sa da Safiya ba'a samu wata matsala a gidan sa ba sosai ake zaman lafiya tsakanin Safiya da uwargidan sa Hajiya Turai, dama kuma Safiya bata taso taga ana faɗan kishi a gidan suba wannan ya sake taimakawa wajen zaman su lafiya da Turai, sosai Safiya take bin Hajiya Turai, haka bata da matsala da yaran da Alhaji Manu yake riƙo saboda akwaita da kama kai ga kyauta, bayan Auran ta da Alhaji Manu Alhaji Ƙadiri ya bata jari mai tsoka kamar yadda yaba sauran ƴan uwanta mata. Da shawarar Alhaji Manu ta fara kasuwancin saida atamfofi da laces kuma sosai take samun alkhairi saboda tallafawar shi da kuma yaran sa da suke shiri sosai da ita, ana kawo kayan da za'a samu alkairi suke faɗa mata, wani abun ma suke ce mata "Mama Safiya ki gwada siyan wannan zaki samu alheri." Wannan yasa sosai take jin daɗin zama da su. An fara samun matsalar zaman Safiya da Hajiya Turai ne lokacin da ciki ya bullo a jikin ta, nan fa Hajiya Turai tace ina wuta ta jefa ta, kishi take da baƙin ciki da fitar cikin Safiya sosai. Wutar kishinta ta sake ruruwa ganin susucewar da Alhaji Manu da dangin sa suka yi akan cikin Safiya. Ansha fama da tashin hankalin Hajiya Turai amma da yake Safiya bamai fitana bace kuma Alhaji Manu Kwabo tsayayyen mutam ne a gidan sa saiya taka mata burki, cikin Safiya ya shiga wata takwas Hajiya Turai taga dai da gaske fa tana zaune shekara da shekaru da Alhaji bata haihu ba wata data zo daga sama zata haihu dashi ta barta da kale, wannan mugun tunani ya sake rikita mata lissafi, nan fa ta shiga neman mafitar yadda zataga bayan Safiya da abinda ke cikin ta. Wata ranar juma'a Safiya ta fito tattaki cikin gida kamar yadda ta saba Hajiya Turai ta shammace ta ta kamata da kokwawa Safiya tayi iyaka ƙoƙarin ta danta kwaci kanta amma ta kasa, babu imani Hajiya Turai tahau ruwan cikin ta tana duka har saida Safiya ta suma jini ya fara zuba sannan ta kyale ta, Safiya na cikin wannan halin Allah ya kawo Musa babban Yaron da Alhaji ke riƙo, Alhaji manu ya aiko sa kawo cefane yazo ya tadda wannan tashin hankali. Da taimakon mutanen unguwa ya kai Safiya asibiti saida Likitoci suka karɓe ta sannan ya samu damar kiran Alhaji Manu ya sanar dashi abunda ke faruwa. Hankalin shi a mugun tashe yazo cikin asibitin Murtala, lokacin haihuwar ta baiyi ba amma dole likitoci suka bada shawarar ayi mata aiki a cire abunda ke cikin ta inba haka ba za'a iya rasa ta ko ɗan cikin ta. Alhaji Manu ya kira wannan labari da mummunan zance take yasa hannu aka shige da Safiya theater room. Labarin halinda Safiya ke ciki ya iske dangin ta babu ɓata lokaci suka cika asibitin har Alhaji Ƙadiri saida ya zo. Cikin ikon Allah aka yiwa Safiya aiki successfully aka ciro mata ɗa namiji lafiyayya kato kamar ubansa, Alhaji Manu yasha murna bakin sa yaƙi rufuwa, Norses ɗin da suka yi aikin sun sha kyauta, take ya sawa yaron sunan mahaifinsa Muhammadu Inuwa (Baffa) sai lokacin Musa ya faɗa musu ainahin abinda ya faru da halin da yaje ya tadda Safiya. Babu wanda ya sani su Aunty Mansura suka tafi gidan Alhaji Manu suka yiwa Hajiya Turai dukan tsiya da ƙyar makota suka kwance ta a hannun su. Sunsha faɗan abinda suka yiwa Turai a wajen Alhaji Ƙadiri yayin da Alhaji Manu yace sunyi masa dai-dai dama tunanin hukuncin da zai mata yake yi akan abinda tayi dan haka sun saukaka masa, ita ma taji ajikin ta, duk da haka sai da Alhaji Ƙadiri yayi musu faɗa sosai. Iftilaƙin rabuwar Safiya da Mijin ta uban ɗanta Alhaji Manu Kwabo ya faru ne randa ta cika kwana huɗu da haihuwa Alhaji Manu yazo asibitin da sassafe Maman Sama tanawa Baffa wanka ya shigo ɗakin ko gaisuwa basu yi ba ya bata takardar sakin Safiya ya kuma ce Baffa ba ɗansa bane Safiya ta nemi uban ɗanta. Wannan mummunan labari yayi mutukar tayar da hankalin Alhaji Ƙadiri, abun da ya faru sosai ya taɓa Safiya. Ƴan uwan Alhaji Manu Kwabo har gida suka zo suka bawa Alhaji Ƙadiri hakuri tare da tabbatar masa da aikin asiri ne amma su sun tabbatar da Baffa ɗansa ne. Tabbas a lokacin Alhaji Ƙadiri yaso yayi ƙarar Alhaji Manu amma sai yan uwan shi suka hana tare da Alkawarin zasu tsaya da Baffa har zuwa lokacin da Alhaji Manu zai dawo cikin hayyacin sa. Wannan shi ne abinda ya raba Safiya da mijinta na farko Alhaji Manu Kwabo. ****Rayuwa taci gaba da juyawa abubuwa da yawa suka yi ta canjawa, Mai Kano na kula da matar sa da iyayen shi sosai komai nashi nasu ne. A Wani zuwa ganin gida da Mai Kano yayi rigima ta ɓarke tsakanin sa da Nana tayi rantsuwa sai dai Mai Kano ya tafi da ita Birni inba haka ba sai ya sake ta, abun ya bawa Mai Kano mamaki dan zuwan shi na karshe lafiya lafiya suka rabu. Bai kula taba yaci gaba da sabgogin sa babu wanda yasan mai yake faruwa a tsakanin su sai randa ya shirya zai dawo Kano Nana tace sam bata san zance ba, shi kuma ya ƙyale ta ya fito amma sai ta biyo sa har wajen Dije tana masa diban albarka ta inda ta shiga bata nan take fita ba, har maƙota suka fara shiga zancen anata bawa Nana haƙuri amma taƙi haƙura da Dije tayi mata magana sai cewa tayi. "Dan Allah kiyi shiru ai da sanin ki Mai Kano yake zaman dadiro a birni amma kuka yi shiru kuka kyale sa to wallahi ban lamunta ya sake tafiya ya barni ba saidai ya tafi dani, indai yana da gaskiya, in kuma yaƙi to sai dai ya sakeni dan bazanci gaba da zama da Mai zaman dadiro a gidan Yarabawa ba." Tirƙashi Nana ta kawo inda Mai Kano ya kasa haƙuri ya ɗago kai ya kalle ta ranshi a mugun ɓace yace "to baki isa ba in zaki zauna ki zauna in kuma bazaki zauna ba kiyi gaba." Wannan magana ta sake tunzura Nana ta ɗora hannu aka ta fasa ihu tana zage zage gashi Aramma baya nan sunje wajen jana'iza a Baragon. Ko takan Nana Mai Kano bai sake biba ya dau jakar goyan shi zai fita Nana tasha gaban sa tace bai isa ya tafi ya barta ba. Shedan da ɓacin rai suka sa a nan take yayi mata saki ɗaya ba tare daya sake kallon kowa a ba ya kada kanshi ya fice daga gidan. Wannan ke nan. **** Shekaru sun fara nisa Kasuwa babu abinda zasu cewa Allah sai godiya, duk damuna Mai Kano yake tura kuɗin da za'ayi noma gida. Yanzu baya yawan zuwa ganin gida kamar da. Kusan cin sa da Alhaji Ƙadiri da ƴan gidan sai abinda ya karu, yanzu ya zama ɗan gida, shida Safiya kuwa sosai suke shiri yanzu shine yake karɓo mata kayan ta in yazo daga Lagos tana kiran sa komai yake yi zai bari ya tafi ya karɓo mata. Haka Baffa komai ya ce Baba ne ya siyamin Kaza Baba ne yaban Kaza. Anata zuwa neman Auran Safiya tako wanne bangare amma taƙi yarda ta bawa kowa fuska, sam bata kula kowa abun harya fara zama rigima tsakanin ta da Yayun ta Maza dan zuwan ƙarshe da Baba Habu yayi yace in bata fidda Miji ba har ya sake dawowa duk wanda yaga dama shi zai bata. Safiya da Mai Kano sun daɗe suna son juna amma kowa sai ya shanye abinda ke cikin zuciyarsa saboda sanin tsari da tsaurin ra'ayin Alhaji Ƙadiri akan Auran Bahaushe. Masu iya magana suka ce wai in rabo ya ranste....! Wata ranar Laraba da Mai Kano da iyalan gidan Alhaji Ƙadiri baza su taɓa mantawa da ita ba. Kamar wasa Alhaji Kadiri ya kira Mai Kano Falon shi yace ya bashi auran Safiya. "Alhaji Auran Safiya nidin?" Murmushi irin na manya Alhaji Ƙadiri yayi sai kuma ya sake fuskantar Mai Kano da mamakin sa yaƙi ɓoyuwa yace "Ni nasan kana son Safiya ita ma kuma nasan tana sonka Abdullahi sanin wane ne ni da tsarina yasa bazata taɓa nuna wa ba, Abdullahi na yarda da kai da tarbiyyar ka inada labarin dalilin da yasa kuka rabu da matar ka Abdussamad ya faɗa min komai. Amana guda ɗaya ce kuma na yarda kanada ita na amince maka na baka amanar yata Safiya in dai iyayen ka sun amince maka zan Aura maka ita." Harga Allah Mai Kano harya yiwa Alhaji godiya ya baro falon shi jin zancen yake kamar a mafarki, shi dai Mai Kano shi Alhaji Ƙadiri zai bawa Auran ƴar sa bayan yana da sahihin tarihin tsaurin ra'ayin sa da kafiyar sa akan bada Aure ga Hausawa. Tabbas labarin ya girgiza ahlin Alhaji Ƙadiri sosai kuma suka ji maganar kamar daga sama, Abdussamd kusan yafi kowa murna dajin wannan zance. Lokacin da Mai Kano yaje gida da maganar Auran ƴar mai gidansa bai samu matsala da Aramma ba amma Dije taso bashi matsala saida Aramma da Salisu suka yi mata bayani sosai sannan ta yarda amma duk da haka gani take kawai Mai Kano arniya zai Aura tunda Beyerabiya ce.... _*WRITING.....✍🏻*_ *_MUTUWAR AURE.....!_* _(Ƙaddarar wasu ƴaƴan)_ *_Kanawa ne👌🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ _BOOK 1_ *_FREE PAGES_* ________________ *_WHATSAPP GROUP👇🏻_* https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3?mode=gi_t https://wa.me/+2348064789370 _________________ _EPISODE 9_ Babu daɗe wa akayi Auran Safiya da Mai Kano, a lokacin yaso ya kama musu haya sai Aminin sa Sale yace ya zo su zauna tare a gidan sa, da farko Mai Kano yaƙi amincewa da wannan shawara sai da Sale yayi ta roƙon shi sannan ya yarda zai zauna a gidan sa, kuma cikin ikon Allah zaman Safiya da matar Sale ba'a samu matsala ba, zama suke lafiya babu wata fitina dan dukan su basu da faɗa. Bayan Auran ne Alhaji Ƙadiri ya sallami Mai Kano ya bashi ƙaramar rumfar shi kyauta yace ya bar masa ita duniya da lahira ya saka nasa jarin aciki yaci gashin kansa shima, Wannan abun Alkhairi da Alhaji Ƙadiri yayi wa Mai Kano Aramma har gida yazo yayi masa godiya. Mai Kano ya ƙara dagewa da neman na kanshi zaman sa da Safiya kuwa babu abinda zaice sai san barka. Mai Kano irin mazan nan ne da ake kira da Mijin marainiya akwai sa da tausayin iyali, Safiya kuma akwai haƙuri da sanin ya kamata kwata-kwata abun hannunta bai rufe mata ido ba. Zaman Aure suke na rufa wa juna asiri, abubuwa da yawa Mai Kano sai dai ya dawo ya tarar Safiya tayi su da kuɗin ta, da yake mace ce mai san ado da kwalliya kamar yadda ta taso a gidan su bata saka ƙananan suturu haka a gidan Mai Kano ma babu abinda ya canja, saka gold kuwa dama wannan kamar ajinin ƴan gidan su yake, suna san saka gold ɗan kunne sarka da abun hannu. Wannan hali da dabi'u na Safiya ya ƙara wa zaman Auran su daɗi da fahimtar juna, tuni Baffa ya dawo wajen ta da zama kasuwancin ta yana tafiya sosai dan yanzu har shago gare ta a kasuwar Birget, sosai Mai Kano yake supporting ɗin ta tako wani ɓangare babu baƙin ciki babu ƙyashi tsakanin sa da Allah yake yi mata komai. Bayan Auran su ba dadewa suka je garin su Mai Kano, Safiya taga ƴan uwan shi ƴan uwansa sun ganta, Dije ta rinƙa bi waje waje tana nunata kamar kuɗi, Safiya takai musu abun Alkhairi har gidan Mariya taje suka gaisa, kwanan su biyu suka dawo, kansu dawo Safiya taso Dije ta basu Ni'ima su taho da ita amma fir taƙi Aramma yace su tafi su barta wata rana da ƙafarta zata zo musu haka kuwa aka yi suka koma suka bar Ni'ima. Auran su nada Shekara biyu Safiya ta haifi yarta Mace, ta roƙi Mai Kano ya bari tasa Asma'u sunan Momma babu ja ya aminci ranar suna yarinya taci suna Asma'u Husna, Momma ta aiko da dan kunne da sarkar gold na takwarar da akayi mata dashi aka huda mata kunne. Baffa yaji daɗin haihuwar Husna kusan yafi kowa murna da haihuwar duk abokan shi saida suka san yayi ƙanwa, in makaranta yaje tsarabar shi ta Husna ce, sosai take ganin gata tako wanne bangare dan Mai Kano bai taɓa riƙe ɗan kansa ba sai a kanta. Rayuwa haka tayi ta tafiya shekaru suka fara ja har an sa Husna a makaranta, tun daga kan ta kuma Safiya bata sake haihuwa ba tun tana damuwa harta barwa Allah, duk bayan hutu suke zuwa garin su Mai Kano su kwana biyu ko uku su dawo. Tunda Safiya ta fuskanci iyayen Mai Kano basu da ƙarfi duk zuwa saita tafi musu da abubuwan buƙata, kayan sawarta dana ƴan uwanta in zasu bayar duka su take haɗa wa ta kaiwa Mariya Autar su Mai Kano da matan Salisu da Lirwanu, haka Ni'ima bata rabo dayi mata ɗinki kayan yaran Aunty Femi in zasu bayar duka Ni'ima take kaiwa, kuma sosai kayan suke mata kyau tasha adon ta dasu, da yake kayane masu daraja kuma ba wani shan jiki suke ba ake cire wa. Dije da Aramma kuwa bata rabo dayi musu saban ɗinki duk zuwan da zasuyi, haka in zasu tafi sai ta soya Jar Miya mai yawa da nama ko kifi ta kaiwa Dije, banda sauran abubuwan buƙata. Hatta kayan su Abdussamad in zasu bayar haɗa wa take ta kaiwa Lirwanu da Salisu, Safiya sam bata da rowa ga haƙuri da sanin ya kamata. Wannan halin kyauta na Safiya ya sake siya mata so da Ƙauna a wajen dangin Mai Kano. Aramma tsakanin shi da ita sai addu'a, Dije ma babu lefi tana godiya saidai ita a nata bangaren gani take duk wannan abubuwan da Safiya ke yi musu da kuɗin Mai Kano take yinsa dan haka ba wani burgeta abun yake ba, In Safiya tazo garin kuwa ta rinƙa binta da kallo sama da ƙasa tana gyaɗa kai. Sunada shekara Shida da Aure aka ɗaga filin kusa da su za'a siyar Sale ya faɗawa Mai Kano in yana so ya siya, dan wajen yayi kyau da sauƙi, Mai Kano ya samu Safiya da shawarar yana son ya sayi wajen amma kuɗin hannun shi baza su kai ba yana ganin kawai zai saida mashin ɗin sa sai ya cika kuɗin ya siya. Nan fa Safiya tayi fir tace ba zai saida mashin ɗin sa ba, yana fita ta ɗauki sarkar bikin ta da Alhaji Manu taje bakin asibiti ta siyar yana dawowa ta bashi kudin duka tace "gashi nan ka cika ka siya saimu fara tara na gini." Mai Kano yayi mata faɗan saida sarkar ta kamar zai ari baki, amma Safiya sai ta ce "kayana fa namu ne Baban Husna kaje ka biya Allah ya bamu na gini." Mai Kano yaji daɗin abunda tayi masa a ranshi ya ci alwashin biyan ta sarkar ta da wacce ta fita. Wata rana!!! Safiya nawa Husna wanka tana mata tsarki ta faɗa mata in suna wasa a ƙofar gidan Mallam Malam almajiran sa suna musu irin wannan. Sosai hankalin Safiya ya tashi da dabara ta tambayi Husna da waye da waye suke saka musu hannu a wando, ta faɗa mata suda ƴar gidan Malam Malam in suna wasan ɓuya da almajiran suke saka musu hannu a wando, yaro ba wayo tsaf ta faɗa wa Mamanta wa'yanda suke musu haka. Abinka da yare Safiya bata tsaya fadawa Mai Kano ba washegari tayi dumamen safe tasa a kira mata almajiran nan da Hausa ta lissafa mata su, suna zuwa ta juye musu abinci tasa musu a ɗakin Baffa murna da ishe su saida ta bari hankalin su yayi kan abincin sannan ta rufe ɗakin ta ɗauki wayar rediyo data adana ta tun jiya ta rufe almajiran nan da duka Umman Abba (Matar Sale) tayi bugu da roƙon duniya Safiya ta buɗe ƙofa taƙi budewa almajiran suna kuka da ihu amma Safiya bata kyale suba saida tayi musu dukan tsiya sannan ta buɗe ƙofa suka fita suna kuka. Bayan fitar su babu daɗewa saiga Malam Malam ya shigo gidan neman ba'asin dukan almajiran sa da Safiya tayi, nan fa tayi masa banza yin Duniya akayi da ita taƙi yin magana. Dama haka take akwai ta da haƙuri da ɗauke kai amma fa in tayi fushi abun baya kyau tana da kafiya. Mai Kano yana dawowa tun daga waje Malam Malam ya tare shi yana masifar ba zai yarda ba sai yayi ƙarar Matar sa. Hankalin mai Kano a tashe ya shigo gida ya tambayi Safiya meya faru hankalin ta kwance tace "yarinya na zasu ɓata min hannu suke saka bama a wando." Mai Kano ya dafe kai yace "amma da kin min baya ni na samu malamin su, da baki ɗauki hukunci irin wannan ba." Ai fa anan Mai Kano yaga asalin fitinar Safiya dan burkice masa tayi saida Sale ya shiga cikin maganar sannan ta mutu, nan kuma tace ta gama zaman Hotoro. Wannan shi ne dalilin barin Mai Kano Hotoro suka koma Rimin kebe. Ni'ima na yawan zuwa tayi musu kwana biyu, sosai Ni'ima da Husna suka saba ƴan uwan Safiya babu wanda baisan Ni'ima ba. .......Suna da shekara huɗu da komawa rimin kebe har lokacin Safiya bata sake haihuwa ba. Watanni biyu da suka wuce ne kuma Allah yayi wa Alhaji Ƙadiri rasuwa bayan doguwar jinya daya sha, wannan mutuwa ta daki ƴaƴan sa da jikokin sa kai harda al'ummar unguwa, ansha jimami da rashin daɗin zuciya, bayan sadakar arba'in suka raba gado, gidan su na Birget Baba Habu ne ya siya yasa aka sake maida shi ginin zamani sannan yace su Momma suci gaba da zama a gidan tsawon rayuwar su, wannan karamci da Baba Habu yayi saiya sake haɗe kansu waje ɗaya. Wata rana da Safiya ta kira da baƙar rana a tarihin rayuwar ta, suna zaune a soro ita da yaran ta sai sukaji dirar mota a ƙofar gida, Baffa ne ya leƙa da Dije ya fara cin karo yace "Lah Mama Iya ce tazo." Safiya najin haka ta miƙe Dije ta shigo Wasu mata na biye da ita a baya, Safiya tace "kumu shiga ciki sannun ku da zuwa." Matan suka amsa da fara'a Dije kuwa fuska a ɗinke tace "Yawwa." Safiya bata Kawo komai aran taba suka shiga cikin gida, ɗakin kusa da ita ta buɗe musu dan yafi girma kuma a gyare yake suka shishshiga tasa Baffa ya karɓo musu ruwan sanyi a wajen Umman Bishira ta zauna suka gaisa tace "bari a ɗora muku abinci." Sukace "a'a yanzu zasu wuce." Wata dattijuwa a cikin matan ta gyara zama tace "to yarinya ga Nana nan Allah ya sake yi mata dawowa gidan Mai Kano tunda zama bai ƙare ba, dan Allah kuyi haƙuri ku zauna lafiya." Da rashin fahimtar inda zancen matar ya dosa Safiya ta kalle su da matar da aka nuna a matsayin Nana sai kuma tace "Mama ban gane inda zancen ya nufa ba?" Da mamaki sauran matan suke kallon juna, to kamar ya ya bata gane ba? Kafin su sake magana Dije tace "ai ba zata gane ba dan ni na hana Mai Kano ya faɗa mata Nana zata dawo gidan shi, ni nace masa zan faɗa mata da kaina bayan Nana ta tare a gidan sa dan bana son ya faɗa mata Nana zata dawo a ɓata abun da biye biye." Dije tayi maganar a gadaran ce, sauran matan da suka rako Nana duk sai suka saki baki dan basu yi tunanin jin haka ba. Safiya kuwa sai ta bi Dije da ido dan harga Allah duk da taji mai suka ce tunani da ƙwaƙwalwar ta basu taɓa kawo mata Mai Kano zai yi Aure bata sani ba. Miƙewa tayi ta fice tana ƙoƙarin gane abinda ke shirin faruwa, tana fitowa daga ɗakin tayi turus tana kallon mutanen dake shigowa da katifa da sauran tarkacen mu na mata. Ɗakin ta ta shige ta bawa Husna kayan islamiyya tasa, tace "Maza kira Yaya kuzo ku tafi lokaci yayi." Da sauri ta fice kiran Baffa ita kuma ta ɗauki waya ta kira Mai Kano amma har kiran ya katse bai daga ba, haka tayi masa kiran duniya baya ɗauka, abun ya bata mamaki dan abune da bai taɓa faruwa ba, wayar ta ajiye ta fito ta ɗora girkin dare Dije ta fito suda sauran matan nan ta buɗe musu ɗakin gefe suka shiga ciki suka zauna, ɗakin da suka fito kuma aka fara shiga da kayan Nana. Gaban Safiya sai faduwa yake wani tashin hankali take ji yana taso mata amma haka ta danne cikin awa ɗaya ta gama jallof ɗin taliya ta zuba ta kai musu har ɗaki, matan jikin su duk a sanyaye suka karɓa suna godiya. Karfe shida na yamma saiga Mai Kano da Sale Abokin shi kusan a tare suka shigo dasu Husna, kamar yadda Mai Kano ya saba yau ma saiya ɗaga Husna ya dora ta a saman wuyan shi suna dariya suka shigo gidan, lokacin har sun gama gyara ɗakin Nana, ɗakin baƙin suka shiga aka gaisa Safiya najin su daga ɗakinta ana masa alasanya alkairi sai lokacin taji wani gumi na zubo mata. "Da gaske dai Aure Abdullahi yayi?" Ta faɗa

Chapter 8 of 31