Share this page
ta kasance, an cika motar da ihun suturu, sunyi nisa da Garki suna gaf da shiga Doko Naira ya ware kiɗa yasa waƙar Sadi sidi sharifai ta (Baba kai mana mairos musa a ɗakin Aure na) motar ta sake rudewa da sowa, ana bin waƙar ana buga faranti. A tsakiyar tasha Naira ya taka burki cikin gwanin ta yayi ribas ji kake "ƙuuuuu....." saida ya juya motar a filin tashar sannan ya tsaya aka fara fitowa. Husna da Indo suna cikin wanda suka fara fitowa, kuɗin mota kowa ya haɗa wa Naira, Indo da Husna suka taho a tare shagon Sunday Husna ta tsaya siyan ruwa taga wata farar mata a cikin shagon, da ɗan Mamaki suke duban matar. "Mai za'a baka?" Matar ta faɗa da gwarin Hausar ta, kansu Husna suyi magana Sunday ya fito daga cikin uwar ɗakin shagon yana wa Husna murmushi haƙoran shi a waje yace "Achalugo welcome." ta dube shi ta dubi matar, Indo tace "Sunday a ina ka samo Mace fara da ja kamar tsada?" Sunday yayi dariya yace "Matata ce Achalugo kin tuna nace miki zata zo?" Husna ta ɗaga masa kai tana kallon matar dake binsu da ido kamar maisan haddace kamannin su. "Welcome to our village Mrs Sunday." Husna ta faɗa tana miƙa wa Sunday kuɗin hannun ta. "Ka bani pure-water guda huɗu masu sanyi Allah yasa kasa ƙanƙara yau." Matar da Sunday yace tashi ce tayi murmushi tana kallon Husna tace "heeee thank God wooo i have new friend in this village, you really deserve this name Achalugo because you're so beautiful." Husna tayi mata murmushi tana karɓar ruwan tace "thank you." Tana faɗin haka tayi gaba Indo data saki baki ta biyo ta tana tambayar me suka ce. Bayani tayi mata ruwa ɗaya ta bawa Indo ta wuce gida itama ta doshi hanyar gida. Tazo wuce rumfar su Dan Hajja ta ganshi a tsaye dogare da Sandar shi yana kallon ta tace "Lah Yayan Husna" Ta faɗa da murnar ganin sa. Ruwan data siyo ta miƙa masa guda biyu, yaƙi karɓa ta zare ido tana kallon shi saiya dauke kai daga kanta ya mai da ganin shi kan titi. "Yaya baza kasha ruwan ba? Ko Sunday ya baka ne? Kaga yau Jumma'a ina zuwa cin Kasuwa Garki shi yasa baka ga nayi abincin siyarwa ba." Husna ta jero masa bayanin cikin sanyin murya kamar wanda ya tambaye ta inda taje. Kanshi ya juyo ya sake duban ta sai yaga duk ta bata fuska kamar zata saka kuka, ruwan ta sake miƙa masa yasa hannu ya karɓa, yau ma bai warta ba. Yana karɓar ruwan tayi murmushin jin daɗi. "Ma'u da mutumin ta." taji muryar Bahari ta bayan ta juyawa tayi ta ganshi kusa da su. "Kaifa ɗan saka ido ne Bahari labe ka fara yi mana?" "Wa zanwa laben ma'u? ko wannan mahaukacin?" "Karka sake kiran shi da mahaukaci shiba mahaukaci bane karka sake na faɗa maka." ta tari numfashin Bahari tana jin haushin sunan mahaukacin daya kira sa dashi. "Allah ya baki haƙuri Ma'u irin wannan tada jijiyar wuya haka, to in ban kirasa da haka ba dame zan kirasa? Duk garin nan dai babu wanda yasan sunan shi tunda baya magana." "Sunan shi Yayan Husna daga yau ka kira shi da haka." Husna tayi maganar tana yin gaba ta bar Bahari a tsaye riƙe da baki. Shi kuwa idanunshi ya rufe kamar mai bacci sai kuma ya juya ya raka ta da ido. A kofar gida ta haɗu da Iro yace "Ma'u yau kuna tafiya kasuwa Baba na Kano ya zo yana ciki." "Dan Allah da gaske?" ta faɗa tana shigewa cikin gidan da gudu. Ramma na mata sannu da kasuwa bata amsa ba ta shige wajen Dije, Mai Kano da Aramma suna zaune suna hira Dije na gefan su tana dama fura Husna ta shigo da sallama. Aramma yace "to gata nan ma Asma'ullahi an dawo?" Saida ta zauna a kusa da Baban ta tana murmushi sannan tace "na dawo Aramma, ina wuni? Baba sannu da zuwa?" "Yawwa sannu Husnah, ya kasuwar an dawo lafiya?" Mai Kano ya tambaya yana bin ta da kallo, koda yaushe inya ganta a cikin wannan yanayin na yawon talla dabin kasuwanin kauyuka yana jin wani abu mara daɗi a ƙasan ranshi, duk lokacin da yazo garin yana jin kawai ya ɗauke ta su tafi amma sai wani abu mai nauyi da baisan ko meye ba ya taso ya danne wannan yunkurin nashi. Tana zaune a gefan shi tana masa surutu da tambayar Yaya Ni'ima, sai labarin kasuwa take bashi yana jinta yana ƙare mata kallo da murmushi kwance akan fuskar shi. Duk halin bauta da takurar da Husna ke ciki Mai Kano yana da labari, wani abun har kiran shi ake a waya daga garin a ce "kazo ka ɗauki ƴar ka kafin Lirwanu ya kashe ta da bauta." Wasu lokutan kuma da shaguban magana ake faɗa masa halin da take ciki. "To me yasa ya kasa daukar matakin ɗauke ta ya raba ta da garin?" Ya yiwa kanshi tambayar daya kasa samo amsar ta. Husna ta katse masa tunani da cewa "Baba nayi sabon Yaya amma bashi da lafiya baya magana abun tausayi." Shida Aramma suka bita da kallo. "Wanne yaya kuma Husnah? A ina yake?" Baban ta ya tambaye ta cikin neman ƙarin bayani, tace "Ni ban san inda yake kwana ba amma kullum zaka ganshi a tasha a zaune baya faɗa baya duka baya kula kowa." Sai yanzu Aramma ya gane wanda take faɗi dan haka ya riga Mai Kano magana da cewa "ah wai wannan bawan Allah mai tabin hankali wanda kike bawa sadakar abinci?" Husna ta cune fuska tace "Aramma bafa mahaukaci bane kawai bashi da lafiya ne, kuma zan dinga masa addu'a zai warke." "In sha Allahu." Aramma ya amsa ta yana Murmushin wauta da rashin wayon irin na Husna, gata dai wasu lokutan kamar mai wayo amma in tayi wani abun sak ƴaƴan fari ko auta. Mai Kano yaɗan tsora ta dajin mahaukaci ne take magana a kanshi dan haka ya yace "ke meya haɗa ki da mahaukaci kuma harda kiran shi yayanki? Ki rinƙa kula kina baya baya dashi kar yaje yayi miki wani abu." Dije tace "barta dai da iyayin jaraba sai taje ya mata illa wata ran garin san gwaninta." "A'a Hadiza babu abinda zai mata in sha Allahu, in kikaga Mutumin kirki a masifa to jarrabawa ce." Sai kuma Aramma ya dubi Mai Kano yace "ai ciwon nashi ma da alama mai sauƙi ne dan na taɓa ganin sa yana Sallah sau biyu, da farko abun nashi yaso ya bani mamaki dan Sallah naga yanayi a nitse babu baragada na tsaya ina kallon shi daya idar kuma sai naga ya tashi ya kalli yamma ya sake tada wata sallar, dana sake ganin shi ma yana idar wa ya juya kudu ya sake wata sallar Allah dai ya bashi lafiya ko daga ina ya fito oho?." Aramma yayi maganar da tausaya wa, Mai Kano ya girgiza kai yana juya maganar Aramma yace "lallai ciwon nasa da sauƙi tunda har yasan yayi Sallah, Allah ya bashi lafiya." Husna na jinsu tana murmushi, ta daɗe a wajen Babanta suna hira har aka fara kiran sallar Magarba suka fito tare tana binshi a baya yayi Alwala suka fito waje ta rako shi dan ya faɗa mata suna fitowa daga masallaci zai tafi. "Baba Mama bata zo nema na ba ko? Shima yaya bai zo ba?" Husna tayi masa tambayar da bata manta yin ta duk sanda yazo. Kai ta karyar cikin karayar murya tace "babu komai ma nasan fa sun manta dani yanzu, ƙanina ma ban sanshi ba, Baba dan Allah shi karka dakko sa kaji?" Husna ta sake faɗa tana riƙe masa hannu, duk lokacin da tayi masa magana irin wannan sai yaji zuciyar shi tayi rawa "anya baka zalunci yarinyar nan ba Abdullahi?" Ya faɗa a zuciyarsa a fili kuma sai yayi murmushi yace "na faɗa miki basu manta dake ba har yanzu Mamanki tana Lagos, Yayanki kuma yana wajen Yayan shi Musa, in sha Allah wata rana zaki gansu duka har kanin ki, Husna me ƙani." Ya faɗa da yanayin san sata ta sake dan baya son kukan da take masa duk sanda zai tafi. Kuɗi ya ciro ya bata ta karɓa tana masa godiya, ya shafa kanta yace "na bawa Sunday tsarabar Popcorn da biskit ɗin ki harda sabulun wanki." Da sauri tace "Baba ka siyo mana man shafawr?" "Eh na siya an jima sai kije ki karɓo ko?" Ya faɗa yana duban ta cikin tausayin ƴar tashi, wai ace duk abinda zai siya mata saidai ya bata a munafurce saboda Dije karta kwace, tun wata rana data faɗa masa inya bata abu Dije karɓe wa take ya koma bawa Sunday ko Bahari su a jiye mata daga baya sai taje ta karɓa babu wanda ya sani. Wallahi iya wannan inya tuna yana jin ranshi babu daɗi. Jin har an shiga Sallah Husna ta saki hannun shi ya tafi tana ɗaga masa hannu har ya ɗan yi mata nisa ta daina ganin shi da kyau sai dishi dishin sa. Sai bayan sallar isha'i har an saka wutar Dandali sannan ta tafi karɓo sakon ta a wajen Sunday dama kuma bata zuwa karɓa da wuri sai daren saboda dauke hankalin Zahara a kanta, dan Zahara akwai mugun sa ido ga ƙyashin jaraba koya taga abu saita faɗa wa Dije saboda munafunci da neman gindin zama, wannan yasa duk lokacin da zata karbo sakon Babanta take taka tsantsan. Tana zuwa Sunday ya ɗakko leda babba ya bata dama kuma yasan da zuwan ta tunda Baban ta ya faɗa masa, ta karɓi saƙon zata tafi Chioma ta fito (Matar Sunday) tana ganin Husna tayi murmushi tana mata magana ta ɗan tsaya suka yi hira sama sama sannan ta tafi. A ɗaki ta tadda Ramma tana linke kayan ta data wanke ɗazu da rana, sai da ta zauna sannan tace "Sannu Ramma yau wanki kikayi? Dakin bari ma gobe zamu wanki saina wanke." "A'a gwanda dana wanke miki Ma'u kema saiki huta ai kina ma ƙoƙari." Ramma ke nan mace mai kawaici haƙuri da sanin ya kamata, Allah ne gatan Husna Ramma ce gatan ta badan Ramma ba ita kanta tasan wahala da azabar da zata sha a gidan nan sai tafi haka. "Wani hutu kuma Ramma? Ai kawai tunda kin wanke gobe tumatirin Baba kwade zan ɗauka nakai Tsaba ko Salifawa tunda in ban fitan bama Baba Lirwanu saiya nemo wani abun ya manna min tunda shi baya burin yaga na huta." Husna ta faɗa tana fito da kayan ledar, Sabulan wanki ne manya manya guda shida sai na wanka sinƙi guda da robar man shafawa babba, wata baƙar leda data gani a ciki ta kunce taga Popcorn ɗinta da biskit harda chaculate manya guda shida, sosai taji daɗin tsarabar musamman Popcorn ɗin da chaculate ɗin yaushe rabanta da chaculate ai harta manta. Popcorn ɗin ta dibawa Ramma da yawa ta bata chaculate ɗin ce tace "kinsan bana shiri da zaƙi bani biskit ɗin dai guda ɗaya, wannan Sabulan ai zasu kwanar mana biyu naga kin siyo wasu ma ɗazu." Ramma ta faɗa tana haɗe kayan waje ɗaya ta ɓoye, Husna ta ɗauki tsarabar wanda za taci a Dandali da wacce zata bawa Indo duk da tasan indai Baban ta ya zo harsu ake raba abinda ya kawo amma duk da haka saita ƙara bata a nata. .......A Dandali ta samu Indo ta bata tsarabar ta karɓa tana murna tace "Nagode Ma'u." Suna zaune suna hira yaro yazo kiran Indo saurayin ta yazo ta tashi ta tafi zance Husna kuma taci gaba da zama a wajen tana cin tsarabar ta. Indo bata jima da barin wajen ba Husna ta ɗago kai ta ganshi a tsaye yana kallon ta. "Ko yaushe ya iso wajen?" Ta tambayi kanta tana miƙe wa tsaye tace "Yaya yaushe kazo nan?" Abinda bata sani ba shi ne ya daɗe a bayan wajen a tsaye tun lokacin da suka zo wajen ita da indo yake kallon su bai fito daga inda ya ɓoye bane sai yanzu da yaga Indo ta tashi. "Ka zauna yau na baka labarin Babana daya zo." Husna ta faɗa tana nuna masa kan ican data tashi ita ko tsoron shima bata ji. Zama yayi a inda ta nuna masa yana kallon ƙasa murmushi kwance a fuskar Husna ta miƙa masa chaculate guda biyu data ɗakko ledar Popcorn ɗin ma saita miƙa masa...tace "Gashi kaima kaci tsarabar da Babana ya siyo min ce." Rufaffun idanunshi da ba'a iya ganin cikin su ya ɗago ya zuba mata naɗan sakon ni sai kuma ya zare chaculate ɗin guda ɗaya daga hannun ta ya sake sunkuyar da kanshi. "Yaya ka karɓa duka inada wasu a gida naba Ramma ta ɓoye min, babu wanda yasan ya siyamin fa, hmmm kasan me yasa?" ta faɗa taka tallafe kumatun ta, bai ce mata komai ba dama kuma bata jira amsawar tashi ba taci gaba da cewa "In fa Dije tasan ya kawo min karɓe wa zatayi ta hana ni shi yasa nace ya daina kawo min gida tunda tana ƙwace wa saidai ya bawa Sunday ko Bahari su aje min, sai naje na karɓa a ɓoye babu wanda ya sani sai Ramma dan Zahara munafuka ce inta gani saita faɗawa Dije." Husna ta hau zuba masa surutun da bata da tabbacin yana ganewa ita kanta bata san me yasa take fada masa komai daya shafe ta ba dan surutu irin wannan musamman da Maza ba halin ta bane, hasali ma zata iya cewa tunda ta rabu da Yayanta da Mama ta rasa abokin hira, kai ko Indo bata faɗa wa magana irin wannan iyakar su hirar duniya, amma haka kawai take jin sake wa da walwalar zuciya dashi, duk lokacin da ta ganshi ji take kamar yayanta ne zaune a gaban ta ita ko kaɗan baya bata tsoro haka bata jin ƙyamar ganin shi. Kanshi ya ɗago ya zuba mata Ido tana ta bashi labari ɗan bakin ta da labbanta masu tudu sai juyawa suke. Haka ta nace masa da roƙon ya karɓi Popcorn ɗin da sauran chaculate ɗin harda hawayen ta saida ya karba sannan ta kyale sa, taji daɗi daya karɓa amma sai taga ya saka a aljihun jallabiyar jikin shi. Sun daɗe a wajen tana masa surutu har dare ya fara yi duk da ga ƴan mata nan tako ina wasu na zance, babu wanda ya kula da wanda suke zaune dan wajen da suke ya ɗanyi gefen Dandali kaɗan ba lallai ka gane waye a wajen ba. Suna zaune Husna taga ya miƙe tsaye riƙe ta Sandar shi, kai ta ɗaga ta kalle sa sai kuma ta miƙe tana karkade hannun ta tasa takalmi tana kallon shi. A gaban ta ya tsaya taga yaƙi tafiya ta waiwaya taga babu wanda yake kallo saita maida hankalinta kanshi sai taga ya koma ta gefan damar ta ya tsaya kamar ya kare ta kamar kuma ya saka ta a gaba Husna ta kasa gane me yake nufi. "Tafiya zakayi?" Ta tambaye shi sai taga ya ɗauke kanshi yana kallon hanyar gidan su, kamar wacce tasani ko aka faɗa wa manufar sa sai ta sake duban shi tana cewa. "Ni zan tafi gida?" A fuzge ya dube ta sai kuma taga ya daga Sandar hannun shi ya sata a gaba irin muje ɗin nan, bata kawo komai a ranta ba tajuya ta fara tafiya sai taga ya tsaya yana kallon ta, dawowa tayi da baya taga yabi ta hanyar da zata kaika gidan su amma ta can barin da bata bi dan yafi nisa da rashin idon mutane. Husna na tsaye tana kallon shi cikin tafiyar shi ta sarsarfa yayi taku ɗaya biyu sai ya tsaya yana kallon ta bata ji tsoro ba ta bi bayan shi tana zuwa inda yake ya matsa ta wuce gaba ya rufa mata baya kamar Ubangida da mai gadin shi haka ya rinƙa binta a baya har saida suka zagayo bai ƙaraso ƙofar gidan suba ya tsaya daga nesa kaɗan amma kana iya hango mutum tayi masa murmushi tace "ai na gane nufinka Yaya kaima yau ka rakoni irin yadda nace ma Yayana namin ko?" ta faɗa tana sakin murmushin jin daɗi, sai kuma taga fuskarshi ta motsa kamar wanda yayi murmushi. Juyawa tayi ta tafi harta shige gida yana tsaye a wajen yana kallon ta, saida ya tabbatar ta shiga gida sannan ya juya ya tafi yana kada Sandar hannun sa. _Washegari_ Da wuri Husna ta gama ɗiban ruwa ta ɗauki tallar tumatir dan a Kafa zata Tsaba, tumatir ɗin kullin ashirin dana Hamsin saida tayi tsiri da katon farantin silver sannan ta kama hanyar Tsaba. Akan idon Dan Hajja ta wuce yana mata magana tayi masa banza dan ko wannan zuwan da Babanta yayi saida ya sake ja mata kunne akan kula Samari. Tana tafiya a hanya ita kaɗai sai iska da kadawar bishiyu duk da haka babu tsoron hanyar ko kaɗan a ranta danta saba bin irin wannan hanyar kuma har taje ta dawo babu abinda ke samun ta, ta gota rugar Harɗo kaɗan taji ƙarar tahowar mashin da gudu ta koma gefan hanya ta ratse dan mashin ɗin ya wuce. Daga nesa bata gane waye akan babur ɗin ba saida ya iso inda take sannan taga ashe Bahari ne. A gaban ta ya tsaya yana mata murmushi yace "yau kuma nan akayo Ma'u kan talla." Hararar shi tayi tace "kaci gaba da tsokana ta wallahi saina dena ma magana." "A'a me yayi zafi, kinga hau na rage miki hanya duk da kinmin rashin mutumci jiya." Ya faɗa yana karkata mata mashin ɗin. Husna ta hau suna tafe take tambayar shi me zai yi a Tsaba, yace "wallahi wake zanje nema." "Yaushe kuma ka fara awu?" Ta tambaye shi da mamaki dan kowa yasa banda fetir Bahari baya saida komai. "Wanne awu kuma? Banni a saida fetir ɗina, Matata nake so na siyawa kamar buhu biyu ta rinƙa siyarwa a gida, shi ne na fara neman shi a ƙyauyuka kanna tashi zuwa ganin gida na samu kinga kawai saina kai mata." Husna ta gyaɗa kai tace "kaha ne ai kuwa ka kyauta." Yayi murmushi, suna tafe yana zolayar ta har suka shigo cikin garin tsaba ya sauke ta yace "Allah bada sa'a in kin siyar kanna koma saimu tafi tare, in kuma na riga ki samu shike nan saikin dawo." ta amsa mishi tayi masa godiya yayi gaba. Cikin abinda bai rufe awa ɗaya ba Husna ta saida tumatirinta tas ta haɗe kuɗi ta irga su babu wanda ya ɓata. A bakin gari ta haɗu da Bahari kamar wanda ke zamn jiran ta, yana dariya yace "lallai Ma'u yau Dije ta yanke miki saƙa, irin wannan bati haka kizo a mashin ki koma a mashin babu ko sisin ki, kawai muje ki siyamin kwatar mai kuɗin kaiki da maidaki gida da zanyi." Husna ta haye mashin ɗin tana dariya tace "aniyar ka dai yau ta bika Bahari na more ka, duk abinka kuma sisi na bazaka gani ba." Yanzu ma suna tafe suna zance har suka kusa shigowa cikin gari tace "sauke ni anan na zauna sai yamma zan shiga gari wallahi yanzu ina komawa sai an jona min wani aikin wahalar." Bahari bai aje taba yace "kai wa zai baki aikin wahala kawai muje yau kiyi mana kunun yamma dama kwana biyu bakiyi ba." Tana masifar Bahari ya sauke ta a bakin gari yaƙi saida ya kawo ta har ƙofar gidan su sannan yaja mashin ɗin shi yayi tasha. Husna na shiga gida Ramma tace "kai har kinyi me? yanzu fa kika tafi kodai baki je ba?" Saida ta aje farantin tana zama saman turamin da suka gama surfe tace "naje harna siyar da Bahari na haɗu ya rage min hanya." Caraf Zahara tace "ai kuwa da munsan zaki dawo yanzu da munbar surfan nan kin mana muma mu huta." Husna ta kalle ta a ɗage tana miƙewa tsaye tace "ai har abada na daina muku surfe wanda nayi muku a baya ma Allah ya bani lada." Tayi gaba tabar Zahara da baki a buɗe. Baba kwade taje ta kaiwa kuɗin shi ya bata ladan tallar ta yanata mata kirarin daya saba. Gida ta koma ta cewa Ramma tayi Kunun yamma sannan ta sake ficewa dan bazata zauna a gidan bama bare a sata wahala.... _*WRITING.....✍🏻*_ *_MUTUWAR AURE.....!_* _(Ƙaddarar wasu ƴaƴan)_ *_Kanawa ne👌🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ _BOOK 1_ *_FREE PAGES_* ________________ *_WHATSAPP GROUP👇🏻_* https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3?mode=gi_t https://wa.me/+2348064789370 _________________ _EPISODE 20_ ......zuwan ta tashar ke nan wani mutum daya sha zanzaro da belat akan baƙin Jens da farar riga yace ta bashi kunu, ko zama batayi ba ta zuba kunun ta tafi kai masa. Husna ta dawo daga kai masa Kunun ranta a ɓace tana tafe tana mitar fi'ilin mutumin data kaiwa kunun. Ranta fal jin haushin mutumin tace "Ko daga ina ya fito oho masa mtchew." Taja tsaki tana zama, Indo tace "ke dawa kike mita?" "Hmmm wancan ɗan renin wayon mana wai na kai masa kunu sai cemin yayi kin wanke robar ko? Dan bana son datti, jifa wulaƙanci ko waye Kazami? Ai wallahi daban zuba masa ba ya fadi haka da saidai ya siya a wajen wani." Indo tace "hmmm shine fa sabon headmaster ɗin da aka kawo, kinsan an canja wancan, ɗazu Ummai ke bani labarin sa wai ya sayi alalar ta jiya saida takai masa ya bata kuɗin yace ta tafi da ita baya so wai bata wanke cokali ba." "Kut amma wannan bashi da mutumci, ai kuwa yawa kanshi wazai yiwa ƙaryar tsafta da wani tanƙwal ɗin shi har ƙyalli yake." Indo saida ta dara da maganar Husna sannan tace "haba Ma'u ance fa har mota gare shi mai kyau ƴar wulwula (ƙaramar mota) baki sani bama bai jima da korar kurman mahaukacin ki ba kika zo wai kyankyamin yake bashi kinga yadda yayi kanshi kuwa kamar zai dake sa saida akayi masa magana sannan ya kyale shi." Ran Husna yayi mugun ɓaci ta dubi Indo fuskar ta a cunkushe "shi ɗin ne ya yiwa Yaya haka? Ai kuwa wallahi zaiga wulaƙanci, kuma malama ba sunan shi kurman mahaukaci ba in bazaki kira shi da yayan Husna ba karki sake yin maganar shi, yanzu haka ma kishin ruwa ce ta kawo sa nan, aikin banza kawai mugu zai wani kore shi." Husna tayi maganar tana hararar Indo. Shi kuwa yana barin wajen da headmaster ya kore shi ya tafi can wajen rumfar Bahari ya zauna a ƙasan bishiya, bai jima da zama ba sai ga Dan Hajja ya zo ta bayan shi yana waya. "Kai dan Allah? Ihu kace aikin Babba ne? to saina jika saika shigo ɗin." Dan Hajja ya sauke wayar bakin shi a buɗe, Gambo ne ya hango sa ya taho wajen yana faɗin. "Ya mutumin ta samu ne? Naga tun daga nesa kana washe baki." Dan Hajja ya bashi hannu suka kashe yana sakin dariya jin daɗi yace "kaidai bari yau zaka samu kuɗin ƙasar da kace za'a kawo maka, yanzu kuɗi suka sauka kayan Ogan sama sun wuce lafiya babu wata matsala." Gambo yayi ihun murna jin za'a biya masa kuɗin ƙasar da zai yi yabe, yace "kai amma naji

Chapter 22 of 31