Share this page
babu komai Mai Kano mutumin shine babu wata matsala. Kwanci tashi ba wuya a wajen Allah watan Mai Kano daya da sati uku da dawowa aka turo masa sakon Nana ta sauka lafiya an samu Mace, sosai yayi murna yaji daɗi dan yana dasan yara sosai, nan da nan ya fara shirin tafiya gida, anaya jibi suna ya tafi saɓanin waccen tafiyar da yayi a wannan karon ya yiwa mutumin shi Abdussamd sallama suka rabu yanata tsokanar sa wai matar shi tayi kira kawai ya fito ya fada masa gaskiyar zashi ganin ta. Bai ce masa komai ba ya girgiza kai yaja baron raken shi ya tafi yana masa dariya dan inda sabo ya saba da halin Abdussamad haka yake da zolaya, sosai Allah ya hada jinni su tun yana ɗari ɗari dashi har ya sake dan indai yana gida zaka samu yana wajen shi suna hira musamman ranar Lahadi da baya fita kasuwa tare suke wuni sai dai inya tafi buga ƙwallo ko wani uzuri. Anyi sunan Nana lafiya yarinya taci suna Ni’ima, bayan suna da kwana huɗu Mai Kano ya baro gida ya dawo birni, washegarin dawowar shi basu samu fitaba saboda wanda yake kawo musu rake bai kawo ba. Bayan sallar la’asar Mai Kano yayi wanka ya dau tsarabar da ya yiwa Baffa da naman sunan daya tahowa da Abdussamad ya yiwa su Sale sallama yace zashi Birget ya dawo, mashin mai kafa biyu ya hau ya kaishi har tsamiya, wajen Ubale mai tsire yaje suka gaisa. “Baba Abdullahi ka dawo ke nan? Ai kwana biyu mukaga shiru baka zuwa nake tambayar lafiya mutumin ka yace mana kaje ganin gida” Ubale ya fada, Mai Kano yace “eh gida naje.” “to madallah ya aka baro manyan?” Mai Kano yace “kowa lafiya Alhamdulillahi” Sukaci gaba da hira da Ubale amma hankalinshi yana kan kofar gidan Alhaji Kadiri yana ta ware ido yaga ta inda Abdussamad ko wani daga cikin jikokin gidan zai fito yace su kira masa Baffa, Ubale kamar yasan me yake tunani ya girgiza kai cikin jimamin abinda ya faru yace. “Baba Abdullahi baka tambayi mutumin kaba Abdussamad?” Bai ce wa Ubale komai ba ya ɗago yana kallon shi cikin neman ƙarin bayani, Ubale yaci gaba da cewa “ai washegarin tafiyarka tsautsayi ya faɗa masa ya faɗi a mashin yaji ciwo a ƙafa danma Allah ya kiyaye ciwon nasa babu yawa, tsagewar ƙashi ce ya samu sai ɗan gogewa da yayi a goshi, yana gida har yanzu bai taka ƙafar ba, jiya dana shiga dubashi jikin nashi da sauki kafar ce dai har yanzu baya iya taka ta amma ko ɗazu naga mai gyaran nashi ya kuma zuwa.” Mai Kano ya ɗanyi shiru cikin yanayin shi na rashin magana sai kuma cikin tausaya wa yace “subhanallahi amma na tausaya masa ciwo babu daɗi, Allah ya bashi lafiya.” Ubale yace “amin ya Allah bari na gama haɗa ƙulin nan saimu shiga ka duba shi” Cikin jin daɗin maganar ubale, Mai Kano yace “to.” Yana zaune Ubale ya gama haɗa ƙulin naman sa ya goge hannu yace “muje ko?” Yayi gaba Mai Kano ya bishi a baya. Wannan ne karon farko da Mai Kano ya fara shiga gidan Alhaji Ƙadiri. Da sallama suka shiga gidan Ubale ne a gaba yana binshi a baya, su Mama na tsakar gida Ubale ya gaisar dasu suka amsa, Mai Kano ma ya rusuna suka gaisa, Ubale yace wasu Momma “wannan shine Baba Abdullahi mun shigo ne ya duba jikin Abdussamad.” Maman Sama ta bude baki da mamaki tace “ikon Allah Baban Baffa zaka ce mutumin Abdussamad, sannu da zuwa Baba Abdullahi ai munashan labarin ka a wajen Baffa, kwana biyu baka nan kullum sai yayi rikimar neman ka .” Cikin kunya da girmamawa Mai Kano ya sunkuyar da kanshi ba tare da yace komai ba, Momma tace “sannu da zuwa Baba Abdullahi, Ubale ku shiga yana ciki, Baffa ɗazu yabi Baba Habu gidan shi da yasan zaka zo bazai bishi ba.” Suna ƙoƙarin shiga ɗakin da Abdussamad yake ciki saiga Yaya Ja’afar ya shigo gidan suka gaisa yayi musu jagora suka shiga tare, Abdussamad na zaune akan katifar da aka shimfida masa a kasa suka shigo suna haɗa ido da Mai Kano ya bude baki yana murmushi. “kai Baba Abdullahi harka gaji da ganin Masoyiya ka dawo?” Hararar shi yayi yana zama a gefan shi yace “kana ciwo ma bazaka daina neman magana ba, ko gaisawa bamuyi ba zaka fara surutu.” Abdussamad yayi dariya yace “Baba Abdullahi ba bakina ne yake ciwo ba.” Ubale na musu dariya yace “wai dama Mai Kano yana magana irin haka?” “wannan mai shirun da kake gani sai ya saida kai” Abdussamad ya faɗa yana kallon Yaya Ja’afar daya fito daga uwar ɗaki hannunshi riƙe da maganin sa. Mai Kano ya duba Abdussamad yana kallon kafar shi yayi masa sannu, Yaya Ja’afar ya sake duba magungunan yana tambayar sa kafar ya yamutsa fuska yace “wallahi Yaya kafar nan babu sauƙi kullum ciwo take min” Mai Kano ya kalli Abdussamd sai kuma ya sake kallan kafar sai ƙyalli take alamar ciwon ya tsumu, yana so yayi musu magana akan kafar amma baisan yadda zasu ɗauki maganar tashiba karya zama yayi musu shishshigi, yanajin Yaya Ja’afar na cewa “inaga zamu canja mai gyaran kawai komu koma asibiti” Zuciyar Mai Kano sai azalzalarshi take yayi magana sai yayi kamar zaiyi kuma sai yayi shiru, daga karshe dai ya kasa haƙuri cikin sanyin halinsa na halitta ya kalli Abdussamad yace “in zaka yarda zan iya duba maka kafar?” Yaya Ja’afar da Ubale suka kalle shi dan sunji mai yace, Abdussamad na masa murmushi yace “Baba Abdullahi dama ka iya gyara irin wannan?” “eh na iya a wajen Kakana na koya inka yarda saina dubama in sha Allah zaka warke.” Abdussamad nason yace ya duba masa amma yana son yaji mai Yaya Ja’afar zaice tunda yana wajen kuma duk yaji abinda suke tattaunawa. Yaya Ja'afar Kamar yasan me yake tunani ya kalleshi cikin harshen su na Yaroba yace “inka yarda dashi babu wata matsala ya duba maka.” Abdussamad na murmushi yace wa Mai Kano “to ka duba min.” Yaya ja’afar ya samu waje ya zauna akan wata single kujera yana kallon su, Mai Kano ya duba kafar Abdussamad saida ya gama duba kafar a nitse sannan yace “gaskiya ƙafar nan taka bata gyaru ba dole sai an sake sabon gyara gashi tayi tsami in za'a taɓa ta yanzu zakaji babu daɗi.” Yaya ja’afar dake sauraren duk abinda mai Kano ke faɗa sai yace “okay yanzu mene ne abun yi?” “eh dole sai an sake gyara ƙafar, zan iya gyara masa yanzu amma sai an samun wanda zasu riƙe shi da kyau saboda ciwon ya riga yayi fushi.” Yaya ja’afar ya kalli Mai Kano kamar yace masa zai iya riƙe sa shi kaɗai sai kuma ya miƙe yayi hanyar fita daga ɗakin yana faɗin "Ina zuwa." Yana fita Abdussamad yace “kai Baba Abdullahi nifa ba rago bane zaka ce wani sai an riƙe ni.” Mai Kano yayi masa murmushin zaka gayawa ƴan garin ku, sannan yace “zamu gani, Ubale ka zama shaida yace shi jarumi ne ko?.” Ubale yayi dariya yace “zan ma shaida Baba Abdullahi.” Suna haka Yaya ja’afar ya dawo shida Baba Habu daya shigo gidan yanzu, gaishe sa sukayi ya amsa, Mai Kano ya matso wajen kafar yace su riƙe shi da kyau, Abdussamad ya hararesa yana ganin abun kamar wasa saida Mai Kano ya shammace sa ya danƙi ƙafar sa sannan ya gane Allah da girma yake, dan wata azaba data ratsa cikin jijiyoyin jikin shi baisan sanda ya kurma wani uban ihu ba. “wayoooooooooo…….Allah na shiga uku.” Abdussamad ya kurma ihun da Maman Sama suka shigo ɗakin a sukwane, lokaci ɗaya zufar azaba da wahala ta jiƙa masa gaban riga, Abdussamad kukan ma saiya neme shi ya rasa ashe kuka ma Rahama ne in kaga ana yinshi matsala ce da sauƙi. Sake kama ƙafar Mai Kano yayi a karo na biyu ya juyata da sauri tayi kara kas kas…. Abdussamda ya yunƙura da zafin nama zai kawace daga hannun su Baba Habu Ubale ya saka hannu suka danne sa. “Wayyo Allah na ku sake ni dan girman Allah ku barmin kafa ta na warke ta daina ciwo, Abdullahi ka sake ni dan Allah ka daina taɓa wa zan mutu na shiga uku, Mamana kice ya daina taɓa min ƙafa, Momma wai bazaku ce su sake niba?.” Haka Abdussamad ke ihu yana zufa yana magiyar a sake shi ya warke, Hausa turanci da Yarabanci babu yaran da baiyi ba saboda azaba, su Momma harda hawayen tausayin shi, ana haka Alhaji Ƙadiri ya shigo gidan bai samu kowa a cikin gida ba sai ihun Abdussamad daya cika gidan da sauri yayi hanyar ɗakin shi yana shiga yaga abinda ke faruwa. Babu wanda ya kula da shigowar shi ɗakin saida Mai Kano ya gama gyara ƙafar tas yace a bashi man zafi da sauri Maman Sama ta fita ta kawo ya karɓa ya shafa masa su Baba Habu suka sake shi sai lokacin ya samu salamar yin kuka. Sai sannan kuma su Baba Habu suka kula da shigowar Alhajin su, sannu da zuwa suka yi masa tare da yi masa bayanin abinda ke faruwa, bayan ya gama jin bayanin su ya dubi Mai Kano yace “mungode ka faɗawa Abubakar nawa ne kuɗin gyaran zai baka.” Kan Mai Kano a ƙasa yace “ai ya biya Alhaji.” Yaya ja’far ya kalle shi dan tare suka shigo kuma baiga lokacin da Abdussamad ya bashi kuɗi ba. Abinka daba Hausawa ba basu gane yana nufin bazai karbi kuɗin ba saida Ubale yayi musu bayani sannan suka fahimci abinda yake nufi, Alhaji Ƙadiri yace lallai a bashi hakkin shi amma fir Mai Kano yaƙi karɓa dole suka rabu dashi sukayi masa godiya. Bayan kowa ya fita daga shi sai Ubale, yace “sannu jarumi Abdussamadu uban Mazaje.” “wallahi wannan gyaran naka harda mugunta, wanda yamin da farko banji ciwon da naji yau ba.” Saida mai Kano yayi dariya sannan yace “dan bai taɓa ciwon bane, amma karka damu nan da kwana biyu in sha Allahu zaka leƙa waje kaci gaba damin abinda ka saba.” Mai Kano ya ƙarasa maganar da barkwanci sai kuma ya bashi ledar daya shigo da ita yana faɗin. "ga tsarabar Baffa da naka, naji su Hajiya sunce baya nan.” Abdussamad ya karɓi ledar yana hararar shi ya zazzage ta riɗi ne kantu da gyaɗa mai gishiri sai ƙullin naman suna mai ɗan yawa. Mai Kano yace “naman suna naka ne sauran kuma na Baffa.” “naman suna, waya haihu na samu naman suna da yawa haka?” Abdussamad ya tambaye shi yana kunce naman ya faraci sai kuma ya mikawa Ubale yace “muci tsarabar Baba Abdullahi.” Ƙasa ƙasa kamar baya son kowa yaji ya cewa Abdussamad “Nana ce ta haihu.” “wacece Nana?” Abdussamad ya tambaya da sauri. “matar Abdullahi Mai Kano, an samu Ni’ima.” Ai sai Abdussamad ya tsaya dacin naman yana kallon shi kamar wanda yayi saɓo, yace “kai wai dama da gasken kana da mata? Nifa tsokanar ka nake” dariya Ubale yayi yace “ai ba abun mamaki bane Abdussamad.” Shidai Mai Kano bai sake magana ba sai murmushi da yake dajin iskancin da Abdussamad ke masa wai a shekarun sa har yayi girman da zaiwa mace ciki. Sai bayan sallar magarba Mai Kano yayi sallama da Abdussamad ya tafi su Momma nata masa godiya. Washegari da yazo kanya fara saida raken shi saida ya zabawa Abdussamad rake masu kyau ya fere ya daddatsa ya zuba a leda ya tsallaka gidan Alhaji Ƙadiri, a soro yayi sallama daga ciki yaji ance ya shigo. Maman sama ce kaɗai a cikin gida tana ganin shi ta saki fuska, Mai Kano ya durƙusa yace “Hajiya barka da rana?” “yawwa sannu da zuwa Baba Abdullahi, ya kasuwa?” Maman sama ta fada, yace “alhamdulillahi.” “Allah bada sa’a, ka shiga yana ciki, ai ƙafa tayi ɗauki Abdulgaffar yace mana jiya sosai suka yi bacci bai kwana da ciwon ƙafar ba, mungode Allah yama albarka.” Mai Kano kanshi a ƙasa ya amsa da “amin Hajiya.” Yana shiga ya samu Abdussamad a zaune yana kallo, yana ganin shi ya saki murmushi ya nuna masa kusa dashi yace “ah Baba Abdullahi zoka zauna anan.” Mai Kano ya zauna yana fuskantar shi yace “ya jikin ka” “Alhamdulillah kafa jiya nayi bacci sosai.” Raken daya kawo masa ya bashi ya karɓa yana murna yayi masa godiya, Mai Kano ya ɗan jima a wajen Abdussamad suna hira saida ya sake duba kafar yaga babu wata matsala sannan yayi masa sallama ya koma wajen sana’ar shi. Kwanan Abdussamad biyu kafarshi tayi sauki sosai aran da ya cika kwana uku ya fara taka kafar da taimakon Mai Kano dan kullum in yazo saiya shiga ya duba shi. Take kafar Abdussamad ya ƙara siyawa Mai Kano girma da kima sosai a idan iyalan Alhaji Ƙadiri kai harda shi kanshi Alhaji Ƙadirin ma sosai yaji daɗi har saida yasa aka kira masa Mai Kano ya sake yi masa godiya ya kuma ce matan shi daga ranar kada a sake bari Abdullahi ya siyi abinci ya bada umarnin kullum akai masa abinci, haka yayi wa Abdussamad dadi. kullum sai an zuba abinci ankai masa, satin Baffa ɗaya a gidan Baba Habu ya dawo, yaji dadin ganin Baba Abdullahi ya dawo, shima yaji daɗin ganin yaron. Sannu a hankali rayuwa take tafiya gashi yanzu har lokacin rake ya fara nisa ba’a samun shi sosai sai kaɗan kaɗan. Wata ranar Lahadi Mai Kano ya gama saida raken shi da wuri sai bai tafi ba ya zauna suna hira da Ubale, yau tunda yazo kuma baiga Abdussamad ba duk da yasan baya fita kasuwa ran Lahadi, har ya mike zai tafi saiga Abdussamad ya fito daga gida, suka gaisa kamar yadda suka saba Mai Kano yace “yau lafiya kuwa baka fito ba? nina dauka ka tafi ball.” Abdussamad ya sauke ajiyar zuciya yace “kai dai bari wallahi lissafi ne ya sakoni a gaba kasan karshen shekara yayi yanzu muke lissafi a fidda kuɗin kaya da riba, to abun ne yaƙi daɗi musamman rumfar Alhajin mu komai ya fi rikicewa, gaba ɗaya mun kasa gane kan lissafin shi, kwata kwata babu ci gaba ga dukkan alamu.” “ayya Allah ya warware muku.” Mai Kano ya fada, Abdussamad yace “Amin.” Saida ya ɗan sake tsayawa sukayi hira da Abdussamd sannan sukayi sallama ya tafi. Abu kamar wasa al’amura suka rincabewa su Abdussamad lissafi yaƙi fita yadda ya kamata komai ya tsaya Alhaji ya salami duka yaran rumfar shi danya gane akwai masuyi masa zagon kasa. Kamar da wasa Abdussamad ke faɗawa Mai Kano halin da suke ciki yace ya nuna masa yadda lissafin yake kozai iya taimakawa, Abdussamad ya dube shi da mamaki dan shi baya masa kallon wanda yayi karatu bare yasan yadda ake fidda lissafin kasuwa, amma da yake shi ba mutum bane mai raini ba saiya dakko komai na lissafin ya nuna wa Mai Kano ya ƙara yi masa bayanin inda matsalar take. Cikin ikon Allah Mai Kano ya taya shi ya fidda lissafin komai cikin sauƙi. Abdussamd da aka ɗorawa nauyin fidda lissafin ya fidda komai cikin kwana biyu da taimakon Mai Kano ya fidda kuɗin kasuwa abinda ya rage a rumfa da adadin asarar da akayi a shekarar. Abun ya bawa Abdussamad mamaki ya kasa haƙuri saida ya tambayi Mai Kano. “Abdullahi wai dama kayi karatu?” Mai Kano ya kalle shi kamar bazaiyi magana ba sai kuma yace “a’a banyi dogon karatu kamar kai ba iyaka ta Secondary.” Sosai Abdussamd yayi mamakin abinda Mai Kano yace. Abdullahi nada baiwar iya lissafi da sanin makamar shi tun yana yaro har zuwa lokacin da ya fara makarantar primary ƙoƙarin shi ya sake fitowa, suna Amaguwa Secondary school hazakar shi ta ƙara fitowa ta basirar gane lissafi (Maths) da Allah yayi masa baya buƙatar calcutor in zaiyi lissafi komai rikicewar lissafi kana faɗa masa zai faɗa ma amsar shi daidai, sosai abun ke bawa malaman su mamaki dan abune da basu saba gani ba, haka yasa suka kira basirar shi da baiwa daga Allah, nan da nan sunan shi ya yi fice a cikin makarantar har lissafin yan gaba dashi ake kawo masa kuma cikin ikon Allah sai ya warware. Lokacin da suka zo fita daga Secondary yana cikin dalibai guda uku da governortyn JIGAWA ta dauki nauyin karatun su zuwa kasar waje a wancan lokaci, saidai lokacin da labarin ya jewa Aramma saiya hana yace sam bai amince ba babu inda Mai Kano zashi, Secondary ɗin ma ya barshi yayi ne dan yaga yana so kuma kusane da gida amma bazai taɓa barinshi ya tafi kasar turawa ba... _*WRITING.....✍🏻*_ *_MUTUWAR AURE.....!_* _(Ƙaddarar wasu ƴaƴan)_ *_Kanawa ne👌🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ _BOOK 1_ *_FREE PAGES_* ________________ *_WHATSAPP GROUP👇🏻_* https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3?mode=gi_t https://wa.me/+2348064789370 _________________ _EPISODE 8_ Wannan abu daya faru tsakanin Mai Kano da Abdussamad shiya janyo hankalin shi ya samu yan uwansa yayi musu bayanin abinda ya faru sukayi ta mamaki. Baba Habu ne ya kawo shawarar mai zai hana su samu Alhaji da maganar inya yarda kawai sai ya ɗauke shi aiki a rumfar sa tunda dama ya salami yaran shi. Sosai jin haka daga bakin Baba Habu ya yiwa Abdussamad dadi dama yanada plan din in aka kwana biyu suka gama lissafin tasu rumfar ya yiwa Yaya Ja’afar maganar su daukeshi aiki a wajen su yasan zai taimaka musu sosai. Bayan gabatar wa da Alhaji Ƙadiri lissafin karshen shekara Baba Habu yayi masa bayanin Mai Kano da abinda suka yanke, Alhaji Ƙadiri yayi shiru yana tunani kamar yace musu a’a saboda shi yanzu lamarin yaran kasuwa ya fara bashi tsoro kowa ka dakko so yake ya karyaka ya kafa kanshi, amma dole yana bukatar mataimaki. “kun yarda da Amanar shi?” Alhaji Ƙadiri ya tambayi yaran shi yana kallon su. “eh yana da kirki da Amana.” Abdussamad ya fada da sauri, murmushi Alhaji Ƙadiri yayi yana kallon sa yace “nima na yarda yana da kirki Abdussamad amma ita riƙe amanar nizan baku labari in ya fara aiki dani.” Sosai jin amsarshi ta yiwa Abdussamad daɗi, aransa yake jin Mai Kano ba zai bashi kunya ba in sha Allahu. Abdussamad ya samu Mai Kano yayi masa bayanin komai, Mai Kano yayi shiru yana tunani har Abdussamad yaji tsoron ko ba zai amince ba, a hankali ya dafa kafadar shi yace “kayi tunani kanka yanke hukunci amma ina tabbatar maka aiki ne mai kyau zakaji daɗin zama da Alhajin mu indai ka kiyaye abinda baya so." Murmushi Mai Kano yayi yana duban yanayin Abdussamad yace “karka damu zanyi magana da iyayena insun amince sai nama magana.” Bayan kwana biyu Mai Kano yaje gida ya samu iyayen shi da maganar Aramma yayi shiru yana tunani dan gaskiya shi bai tura sa Kano neman kuɗi dan ya zauna gaba ɗaya ba, ya turashi ne yaje yayi rani kamar sauran samarin gari in damuna ta faɗi ya dawo gida yayi noma. To amma Mai Kano mutum ne mai biyayya yasha yanke masa hanzari ya haƙura yasan duk ƴaƴan shi babu wanda zaiwa abinda yake wa Mai Kano ya zauna lafiya. Numfashi ya sauke yana kokarin fahimtar yanayin dan nashi yace “kace mutumin Beyerabe ne kuma musulmi ko?” Kan Mai Kano a ƙasa yace “eh musulmai ne?” Kafin Aramma ya sake magana Dije tace “wai barin shi zakayi yaje wajen Yarabawa yayi musu aiki? Wanne musulunci ne a wajen yaren mutum? Musulinci ko suna yanzu haka ma basa sallah.” Aramma da takaicin maganar Dije ya ƙume kawai saiya fuskanci Mai Kano yace “tashi kaje Allah yama albarka saika yiwa iyalinka bayani ta sani.” Sosai maganar Aramma ta bawa Mai Kano mamaki danko kadan bai ɗauka zai aminnce masa ba. Aramma yabi bayan Mai Kano daya fita da kallo yana jin daɗi dabai hana shiba dan yana kula da yanayin sa yana son aikin kawai biyayyace tasa yake jiran umarnin su. Wajen Dije data cika tayi fam Aramma ya maida hankalinshi ransa a ɓace yace “wayace miki duk yaren da ba Hausawa ba basa sallah? Su asalin Hausawan ba Maguzawa bane? To in baki sani ba ma na faɗa miki ako wacce ƙabila akwai Musulmi akwai wanda ba Musulmi ba. Bayan dawowar Mai Kano Abdussamad yaji daɗin amincewar sa, babu ɓata lokaci ya gabatar da shi a wajen Alhaji Ƙadiri ya karɓe sa hannu bibbiyu sannan yayi masa bayanin komai yace washegari zai fara zuwa Rumfa, abin ƙarin jin daɗin kuma sai yace ya zo su rinƙa kwana da Abdussamad tunda bashi da wajen zama. Mai Kano yaji daɗin wannan karamcin da Alhaji Ƙadiri yayi masa, Washegari Abdussamad ne ya rakashi har Rumfa sai da yaɗan zauna sannan yayi masa Sallama ya tafi dan su a Kasuwar Kantin Kwari suke nasu kasuwancin. Rayuwa ta fara canjawa Mai Kano sannu a hankali ya fara zama da Alhaji Ƙadiri cikin ikon Allah kuma suna zaune lafiya, dan Mai Kano mutum ne mai sanin ya kamata ga ɗauke kai da rashin san abin wani. Shima kuma Alhaji Ƙadiri sosai yake jin daɗin zama dashi, duk ƙarshen wata yake zuwa ganin gida yayi kwana biyu ko huɗu ya dawo. Nan da nan Mai Kano ya fara canjawa dan zaici mai kyau ya sha mai kyau ya kwanta a mai kyau ga kuma kwanciyar hankali, gashi babu lefi Alhaji Ƙadiri yasan hakkin na ƙasa dashi, sosai yake biyan sa hakkin shi babu ƙyashi da mugunta. Amintar su da Abdussamad sai ta ƙara karfi dan yanzu kusan komai tare suke yi dan ma Mai Kano yana da kama kai duk yadda Abdussamad yaso ya sake masa komai nasa shi yana yiwa kansa iyaka baya yarda ya wuce matsayin sa. Cikin shekara ɗaya Allah ya sake sawa kasuwancin Alhaji Ƙadiri albarka wannan shekarar da Mai Kano ya kawo masa lissafin kuɗin Rumfa riba da adadin sauran kayan da suka rage sosai yayi mamakin ganin abinda aka samu, rabon da a samu riba irin wannan a rumfar sa tun sanda suke zama da Baba Habu. Wannan ya sake yi wa Allhaji Ƙadiri da yaran sa

Chapter 7 of 31