ki bai dawo bako?" Yanzu ma kai ta ɗaga masa.
Hannun ta ya saki ta koma wajen Maman Sama da sauri kamar dama abinda take jira ke nan yayi musu sallama ya tafi.
Maman sama ta shigo ɗaki hannun ta riƙe dana Husna, Safiya ta ɗaga ido ta dube su tana ɗan murmushi tace "Husnah zomu raba tsarabar da Baba ya kawo miki tunda yau Yaya baya nan?" ta faɗa da yanayin san saka ta sakewa, dan tunda tazo gidan bata yi walwala kamar yadda ta saba ba, ga mamakin ta sai taga Husna ta miƙo mata ledar ta koma can karshen gadon Maman Sama ta kwanta tana kallon bango.
Wani abu mara daɗi ya daki zuciyar Safiya amma saita danne dan bata so ta zama emotional.
"Wallahi Abdullahi tausayi yake bani, gaskiya wannan Maman nashi in bata nemi gafar saba sai Allah ya kamata." Maman Sama ta faɗa tana zama a gefan Safiya.
"Ɗan tane Mama kome taga dama tayi masa tsakanin su ne ni kuma zaluncin data yimin ban mata komai ba bazan taɓa yafe wa ba." Rai a ɓace Safiya ta faɗi maganar tanajin ciwon Abinda ya faru yana taso mata.
Washegari Safiya tayi sallama da iyaye da ƴan uwanta suka wuce Lagos ita da Baba Habu, taso taga Baffa tayi magana dashi kanta tafi amma hakan bata samu ba dan hutun shi bai ƙare ba, kuma tana kunyar ta kira Musa tace ya dawo da shi, dole sai a waya suka yi magana tace masa zata je Lagos in hutun sa ya ƙare Yayan sa zai dawo da shi gidan Alhajin su kamar yadda Baba Habu ya faɗa masa, Baffa yaso ya tambaye ta me yasa zata Lagos amma sai bata bashi dama ba, ta haɗa sa da Husna yana ta mata hira ita kuma amsar ta bata wuce "eh ko a'a."
Kafin Baba Habu ya tafi saida ya kira Mai Kano yayi masa bayanin komai da suka yanke na matakin da suke son ɗauka akan matar shi, sosai Mai Kano ya fahimce sa ya kuma yi masa alkawarin in sha Allahu hakan ma ba zata sake faruwa ba wannan ɗin ma rashin sani ne.
Kullum Mai Kano saiya je duba Husna cikin kwana huɗun da tayi a gidan kakannin ta jikin ta yayi ƙyau inda ya farfashe duk ya kame ya fara ɓarewa da kansa, dan sosai take samun kulawa a wajen su Momma.
Tun washegarin tafiyar Nana kuma Mai Kano ya samu kira daga Aramma akan yaje yana neman sa lallai lallai yazo a cikin satin nan. Dama yasan za'ayi haka tunda yasan ko Nana bata je gidan su ba dole ni'ima can zata wajen Dije.
******Ranar Jumma'a da wuri ya shirya ya tafi garin su dan yana so ya samu sallar jumma'a acan, ƙarfe goma sha daya saura mota ta sauke shi a tashar garin su, yana sauka yaga Salisu ya taho wajen sa da sauri yana Murmushi yace "A'a yanzu kake tafe? Sannu da zuwa?" Salisu ya faɗa yana bashi hannu suka gaisa ko wannensu fuskarsa kwance da fara'a dan akwai sabo da shakuwa sosai a tsakanin su, bayan Mai Kano ya gaisa da sauran mutane, suka jero tare da Salisu suna tafe suna hira, mutanen tashar suna kallon Mai Kano suna yaba nutsuwa da rufun asirin da Allah yayi mana dan Mai Kano akwai saka sutura, yasan saka shadda da yadi, yau ɗin ma wata skyblue ɗin shadda ce a jikin sa ɗinkin tazarce sai maiƙo take yasa hula da takalmi masu kyau, saiya fito a baƙin Bahaushen sa ga tsayi ga cikar kamala irin ta tsayayyun magidan ta.
Kafin su ƙaraso gida tuni labarin zuwan shi ya iske mutanen gidan su, da yake gidan su na kusa da tasha dan dangar gidan su na jikin katon Masallacin jumma'ar dake bakin titin garin Kofar gidan ce saika zagaya ta cikin gari sannan zaka shiga, amma ta tashar ma kana iya shiga gidan ta kewaye saidai Aramma bai fiya bari abi ta wajen ba inba ruwa za'a shigar ba.
Da sallama ya shiga gidan nasu Salisu na binsa a baya yaran ƙannen shi tuni suka zagaye shi suna murna da faɗin.
"Ga Baba na Kano ga Baba na Kano."
Matan gidan ma bakin su yaƙi rufuwa dan kowa yasan yau gidan za'a ci na rana mai ƙyau kamar yadda yake dabi'ar sa duk lokacin da yazo Garin girki yake sawa ayi mai ƙyau kowa yaci ya koshi har gidan Yayan Aramma dake kusa da nasu sai an kai dan dangar karace ce kawai ta raba tsakanin su kuma da yake akwai kafa sai gidan ya zama kamar guda ɗaya, matan gidan da matan su Salisu tare suke zaman hira a ƙasan ƙatuwar bishiyar mainar take tsakiyar gidan, yanzu kuwa da gidan ya sake cika da mata da jikoki saiya zamana anan suke surfe, masu casa ma anan sukeyi har koda (casar kuɗi ko ladan hatsi) sunayi.
Ni'ima na cikin ƴan yi masa sannu da zuwa, baiyi mamakin ganin taba dan dama yasan tana nan sai dai yayi matuƙar mamaki ganin Nana dake zaune tana busar dawa.
Yuuuuuuuu yara suka rakashi ɗakin Dije inda ya iske Aramma zaune yana cin kwaɗon yakuwa.
"Aramma ashe kana ciki? Na dauka kana masallaci." Mai Kano ya faɗa yana zama a kusa da shi.
"Ina ciki Abdullahi Bawan Allah ban kai ga fita ba, yanzu kake tafe? Sannu da zuwa, bismillah ga mutumin ka."
Aramma yayi magana fara'a kwance kan kamilalliyar fuskar sa ya tura masa akwashin kwaɗon ramar.
"Ai kuwa dama na kwana biyu bamu haɗu ba." Mai Kano yayi zancen yana jan akwashin ya fara cin kwaɗon, Dije ta karɓi tsarabar Burodi da biskit ɗin da ya kawo ta raba ta bawa kowa nashi, yara kowa ya karɓa nasa saiya fita da gudu yana murna haka ta rinƙa basu ɗaya bayan ɗaya na iyayen su kuma ta fita ta miƙa musu.
Ɗaya bayan ɗaya matan su Salisu suka rinƙa zuwa kofar ɗakin Dije suna gaida Mai Kano kamar yadda suke yi duk sanda yazo garin ko wacce zata zo ƙofar ɗakin Dije ta tsugunna tace "Yaya sannu da zuwa."
Shi kuma ya amsa sannan su tafi, Amaryar Lirwanu ce karshen zuwa ta gaisheshi.
Saida kowa ya watse ya rage daga Salisu, Aramma sai Dije a ɗakin sannan Mai Kano ya durƙusa suka gaisa da iyayensa anan yake jin Lirwanu baya nan sunje Kabawa ɗaurin aure, Aramma yace "Amma kayi fitowar wuri koda yake babu nisa ai bai wuce tafiyar awa ɗaya ba inka samu mota mai kyau ma baya kawai haka, to sannu da zuwa, ya kasuwa da Iyalin naka ina wajen Asma'ullahi Husnah ƴar Baba?" Aramma ya tambayi mai Kano yana Murmushi.
Iya wannan tambayar ta Aramma saida tasa gumi ya karyo masa amma sai yayi ta maza ya dake yace "Alhamdulillahi."
Aramma yaɗan kalli yanayin sa daya canja lokaci ɗaya sannan bai amsa masa tambayar kamar yadda yake amsawa ba a duk lokacin da yayi masa irin ta ba, amma sai Aramma ya basar yace "An kusa kiran sallar wanka ni zan fara shirin tafiya masallaci, bayan mun sakko daga jumma'a mayi magana."
Dije a ranta tayi Hamdala da jin daɗin abinda Aramma yace sai bayan sallar jumma'a za'a zauna, dan dama tsoron ta Allah tsoron ta yayi mata shigar sauri ba tare data sake samun damar kwakwkwafe Mai Kano kanya dawo ba.
Har Aramma ya yunƙura zai tashi sai kuma ya koma ya zauna kamar yasan mai Dije take saƙawa a ranta ya dubi Mai Kano yace "nasan kayi wankan jumma'a ko?"
"Eh nayi Aramma."
"To Alhamdulillah tashi mu tafi masallacin tare yau ka kira mana Sallar wanka, kai kuma Salisu inka shirya ka taho."
Dije taji wani dum kamar ta hana Mai Kano binsa dan tasan indai ya bishi to ta rasa damar yin wata magana dashi a kebe kansu zauna babu yadda ta iya dole haka ta bisu da ido Aramma yasa Mai Kano a gaba suka fice daga gidan.
A bangaren Nana kuwa tunda Mai Kano ya shigo gidan ta kasa nutsuwa har sai da Zahara uwargidan Lirwanu ta kula da yanayin ta tace "kema dai uwar Ni'ima meye wani abun tashin hankali daga zuwan Yaya na Kano? tunda kinsan kina da gaskiya ni banga abun damuwa ba, kuma kinsan halin Aramma baya goyon bayan rashin adalci." Sai kuma ta ɗanyi kasa da murya tace "dama dai Iya ce sai kiji shakka dan ita basan gaskiya take ba in abu bai mata ba yanzu zata rufe ido."
Gaje matar Salisu dake zaune tana jinsu tayi dariyar renin wayo tace "yo waya sani ko bata da gaskiyar, kema dai Zahara da shiga shirgin daba naki ba."
Maganar Gaje ta ɓatawa Nana rai cikin jin haushi ta ta ɗago kai ta harare ta dan dama basa shiri ko kaɗan da ita, Nana akwai ji dakai da nuna isa da nina iya komai, ita kuma Gaje jin kai da rashin ɗaukar raini da wulaƙanci, wannan saɓanin halin nasu yasa tasu basa jituwa.
Ramma Amaryar Lirwanu kuwa tana zaune tana jinsu ta tafasa bata ce musu ba dama ita lamarin irin wannan zai yi wahala kaji bakin ta.
_BAYAN SALLAR JUMMA'A_
Kasancewar Aramma shi ne babban malamin garin saida ya tsaya yayi ƴan gaishe gaishen sa da ƴan gari da baƙin Fulanin dake shigowa cikin gari Sallar jumma'a sannan suka taho gida tare da Mai Kano dake biye da shi a baya.
"Dije kiramin Nana." Aramma ya faɗa yana zama a ƙasan inuwar rumbun shi dake can kusa da Kewaye wajan ya ɗanyi nesa da cikin gidan saidai komai ake yi a tsakar gidan kana kallo, kamar yadda ya buƙata anan Dije ta shimfiɗa masa taburmar Kaba babba, wajen akwai iska mai daɗi shi yasa lokuta da dama Aramma kesan zama a nan.
"Zo zauna nan kusa dani Abdullahi." Aramma ya faɗa yana nuna wa mai Kano kusa dashi.
Ran Dije babu daɗi tayi kiran Nana dan tasan yau Aramma saiya ɓata mata rai a wannan zaman da za'a yi in batayi da gaske ba.
Bayan Nana tazo ta tsuguna ta gefan Dije Aramma yayi gyaran murya yana fuskantar Mai Kano yace "kwanaki huɗu da suka wuce iyalin ka suka zo nan cikin yanayi mara daɗi, Nana ta faɗa min duk abinda kayi mata, taso barin Ni'ima anan ta tafi gidan su ni kuma sai na hanata saboda ba sakinta tace kayi ba, ni kuma duk wanda ya sanni yasan tsari da tarbiyyar gidana kama daga kan surukai na har zuwa yaran ƴan uwa dana ke aurarwa duk kunsan ba'ayin yaji a gidana, in kaga yarinya tazo kota fita a gidana to kodai tazo ziyara ne ko kuma an sake ta, amma indai matsala ce irin ta gidan Aure kunsan bana bari azo ko a tafi kun sani da kaina nake takawa naje naji ko menene matsalar inna gyarawa ne na gyara inba na gyara wa bane mu nemi mafita a wajen Allah, daga surukai na har ƴaƴana kunsan haka nake, shin Abdullahi kaima kasan haka ko baka sani ba?" Aramma ya tambaya, Mai Kano kanshi a ƙasa yace "a gafarceni Aramma haka ne."
"Madallah, wannan dalili ne yasa na hana Nana tafiya gidan su, dan haka ke Nana yanzu ki sake maimaita abinda kika faɗa min randa kika zo garin nan a gaban Mijin ki yaji da kunnan sa, sannan shima yamin bayanin abunda ya faru dan ba'a Shari'a mutum ɗaya kamar yadda babu adalci a yanke hukunci dajin maganar ɓangare ɗaya ba tare da kaji ɗaya bangaren ba."
"Innalillahi wa inna ilaihirraju'un." Nana ta faɗa a ranta, dan gaskiya ba haka taso ba taso Aramma ya yanke hukunci kawai amma ta kwana da sanin waye Aramma tabbas shi mutum ne da baya shiri da rashin gaskiya.
"Uhm muna jinki Nana?" Aramma ya sake fadi yana duban ta.
Kamar yadda ta faɗa masa randa tazo yanzu ma haka ta kwashe labarin cin mutumci da zagin iyayen ta da Mai Kano ya rinƙa yi akan tayiwa Husna gyara tare da korota da yayi duka akan Husna.
Mai Kano bin bakin Nana kawai yake da kallo yadda take tsaro zancen kamar gaske, "wato dan ta yi wa Husnah gyara, lallai mata an bar muku sarautar munafunci." Ya ayyana hakan a ransa.
Aramma yace "To Bawan Allah kaji abinda Matarka tace, kai meya faru ya ya aka yi kayiwa iyalin ka irin wannan cin zarafi?" Aramma ya jefa masa tambayar.
Saida Mai Kano ya gyara zama ya fuskanci dattijon mahaifinsa da kyau sannan ya fara zayyane masa duk abinda ya faru tsakanin Husna da Nana ɗaya bayan ɗaya bai rage masa komai ba.
Aramma yana sauraran bayanan Mai Kano yana gyaɗa kai har ya dasa aya a zancen sa sannan ya ɗaga kai ya dube shi.
Tambayar data biyo bayan duban da Aramma ya yiwa masa kuwa ita ce "ina ita Safiyar sanda Nana tayiwa Asmaullahi duka irin wannan?"
"Dama nasan za'a zo nan wajen da bana so." Dije ta faɗa a ranta sai kuma tayi caraf kan Mai Kano yayi magana ta riga shi da cewa "Aramma maiya kawo maganar Safiya kuma? Kawai kayi musu sasanci sannan kaja masa kunne akan Ma'u da baya kaunar yaga anyi mata magana wannan ai saita lalace, haba ace yaro yayi kuskure aƙi gyara masa dan kar ranshi ya ɓaci."
"Saboda ni Aramman takarda ne Hadiza kawai shike nan saina yanke hukunci bansan makamar zance ba? To ba zai yiwu ba, kai Abdullahi nace ina Safiya take lokacin da Nana ta daki Asma'ullahi?" Aramma ya sake jefa wa Mai Kano tambayar a karo na biyu.
Dije Allah Allah take Mai Kano ya ɗago kai su haɗa ido dan ta hana shi faɗa wa Aramma ya saki Safiya amma sai Allah bai bashi ikon ɗagowa ba, a hankali kuma yace wa Aramma "Safiya tana gidan su."
"Tana gidan su? Ban gane tana gidan suba? Itama mutumcin nata kaci ka kore ta ko ya ya aka yi?"
Aramma ya jero masa tambayoyin ranshi na fara ɓaci dan dama tun tafiyar da Dije tayi gidan sa ta daɗe da sunan yiwa Nana rakiya yaso yayi zargin wani abu, amma sai yayi shiru a matsayin sa na babba karya zamana yana saka musu ido akan komai tsakanin su da mahaifiyar su.
"Mun rabu ne."
"Kun rabu? Ma'ana dai ka sake ta Abdullahi?" Aramma ya maimaita abinda Mai Kano ya faɗa.
"Eh."
Mai Kano ya amsa muryar sa a saɓule.
Aramma bai sake cewa komai ba saida yayi shiru naɗan wani lokaci sannan ya ɗago ya kalli Dije da tayi kicin-kicin da fuska ya gyaɗa kai yana jin ciwon baƙin labarin da yake ji yanzu amma danya sake tabbatar da zargin sa akan Dije sai yace "tun yaushe ka sake ta?"
"An kusa sati biyu."
"Da kyau."
Aramma ya faɗi a ransa a fili kuma saiya dube sa duba irin na tuhuma yace
"Me yasa ka sake ta? Dama ka maida Nana ne danka sake ta?"
Gumi ya lulluɓe Mai Kano a zaune, ya rasa abinda zaice masa dan bai manta jan kunne da gargadin Dije ba, Aramma na kula da shi da yanayin daya shiga sai yayi murmushi irin nasu na manya yace "to babu lefi, yanzu ita Asmaullahi kace tana gidan su Safiyar ko?"
"Eh."
Sai kuma Aramma ya maida hankalin sa kan Nana yace "Nana tabbas abinda kikayi ba dai-dai bane, ina kika bar imanin ki? Zalunci babu kyau ko akan ɗan da ka haifa ne bare ɗan wani, ɗan da ba naka ba, bazanyi magana mai yawa ba haka ba zan tsanan ta bincike ba, duk abunda zance miki kuma yanzu babu gurbin sa saboda iyayen Asma'ullahi sun riga sun shiga maganar kuma abunda suke shirin yi ni sunyi mini dai-dai, sun kuma ɗauki mataki na dai-dai da Zamanin ki, dan haka in Mijin ki zai koma zaki bishi ku tafi tare ki koma ɗakin ki kici gaba da haƙuri haka ibada take sai bawa ya ɗaure kanya samu aljanna, sannan in kun koma zai kaiki har wajen yan Sanda kuyi duk abinda ya dace dan kafa hujja da yarjejeniya kamar yadda iyayen ta suka buƙata, Nana hakan da suka yi yayi min dai-dai ɗari bisa ɗari. Ko a addinin musulunci babu lefi in wani ya cuceka kace bazaka yafe ba saika rama dai-dai da abinda yama, dan haka kema sai kije in sun so su yafe miki dukan ƴar su da kikayi in kuma basu so ba saiki karɓi hukunci dai-dai da abunda kika aika ta musu, sannan kiji tsoron Allah Nana duniya ba'a sabo da ita"
Yana gamawa da Nana sai kuma ya juya kan Mai Kano ya rufe shi da faɗa akan zagin daya yiwa Nana sai da yayi masa tas tare dajan kunne da ƙaƙƙarfan gargadi akan karya sake jin irin haka ta faru a tsakanin su sannan ya cewa Nana "tashi kije ku haɗa kayan ku."
Nana tayi godiya ta miƙe tana tafiya da ƙyar dan gaba ɗaya a tsoroce take musamman dataji maganar za'a kaita wajen ƴan sanda saida cikin ta ya karta.
Saida Nana tabar wajen gaba ɗaya kamar daga sama Aramma yace wa Mai Kano "Uwarka ce tasa ka saki Matar ka ko?"
"Wanne irin ni kuma Aramma? Magana ta gaskiya fa wannan ba magana bace haka kawai dan dai kana son ɗora min lefi saika ce nina sashi ya sake ta." Dije ta tari numfashin Aramma da sauri.
"Hum kinsan nasan halinki nasan abinda zaki iya yi akan san zuciyar ki da wanda bazakiyi ba ko? tunda kika taso da maganar komen Nana gidan Abdullahi da zaman da kikaje kikayi a gidan shi da sunan rakiya nasan bazaki shuka abin arziki ba, amma babu komai tunda kince bake kika sashi ya sake taba, Allah na kallon ku, kuma Hadiza Allah da kike gani baya baci baya barin zalunci, bazan tsanan ta bincike ba amma wallahi tsakanin keda Abdullahi duk wanda ya cuci Safiya da yarta Allah saiya saka mata ina raye ko bayan na mutu. Kuma ina so na faɗa miki ki sani Hadiza ke....ke wannan halittar baki isa ki hana abinda Allah ya ƙaddara ba wallahi kinyi kaɗan, sannan in sha Allahu abinda kika shuka in baki tuba ba saikin kwashe shi da tafin hannun ki, gaki ga Nana nan ta dawo gidan Abdullahi, ni ba baki nayi miki ba amma Allah ya baku sa'a, duk wanda bai gode wa ni'imar Ubangiji ba saiya godewa azabar ta." Aramma ya dire maganar ranshi a mugun ɓace, Dije kuma saita fara matsar hawaye wai yayi mata sharri, bai sake bi takan taba ya cewa Mai Kano.
"Kai kuma abinda ka biyewa uwarka kukayi yayi maka dai-dai, sannan nasha faɗa maka ba'a yiwa kowa biyayya wajen sabawa Allah, uwarku tun muna da jajayen sahun mu take bani matsala nake hakuri da ita, ku kanku kun sani bata da daɗin zama haƙuri kawai nake da ita amma tunda ka biye mata kuka jiƙawa kwaɓar ku ruwa babu tushe shike nan kuje Allah ya baku sa'a."
Jikin Mai Kano yayi mugun sanyi da maganganun Aramma, yasan gaskiya ce zalla ya faɗa masa to amma ya zai yi da Dije a lokacin tayi masa ɗaurin da ba zai iya kuncewa ba shi yasa yayi sakin.
"Astahfirullah! Astahfirullah!! Astahfirullah!!!"
Ya maimaita sau uku yana jin babu daɗi.
"Oho Safiya ce dai ta tafi kuma in sha Allahu ta tafi ke nan, ba wa'azi ba in kaso ka sauke Kur'ani, duk rashin daɗin zama dani kuma nida kai mutu ka raba." Dije tayi maganar a ranta tana barin wajen tayi cikin gida ranta a ɓace.
Bayan tafiyar Dije Mai Kano ya rinƙa bawa Aramma haƙuri tare dayi masa bayanin abinda ya faru suke da ba komai ya faɗa masa ba, Aramma yaji kan zancen sai abunda dije tayi yayi masa ciwo, sai kuma tausayin ɗan nasa ya kama shi da irin uwar da Allah ya basu.
Sosai ya kwantar masa da hankali ya kuma yi masa nasiha tare da addu'ar alkhairi, anan Salisu ya zo ya same su shima yaji babu daɗi dajin abinda ya faru, ya tausaya wa ɗan uwanshi, ya sake karfafa masa kuwa da cewa.
"Kayi haƙuri Yaya Mai Kano Iya bata da daɗi mu kanmu da muke zaune tare wallahi haƙuri kawai muke da ita, Allah dai ya raba mu lafiya."
Nan suka haɗu sunata hira har lokacin Sallar la'asar yayi suka yi alwala suka fice masallaci.....
Shigowar dare sukayi saboda basu baro ƙyauye da wuri ba, Nana ta samu gidan babu datti ko ƙura irin wacce mace kan samu in ta kwana biyu bata gidan ta saboda Mai Kano kullum saiya share gidan kanya fita haka inya dawo da yamma, kan ya kwanta kuma saiya gyara ɗaki da inda zai kwanta.
Ɗan abinda baza'a rasa ba kawai Nana ta sake gyara wa ta kunce musu dambun da suka taho dashi suka ci suka kwanta.
Mai Kano kuwa tunda suka taho sabgar gaban sa kawai yake Nana ko kallo bata ishesa ba komai zaice saidai yayi wa Ni'ima magana saboda haushin ta yake ji har yanzu.
Washegari bayan sun karya wajen ƙarfe goma sha ɗaya na safe ya ɗauki Nana a bayan mashin suka tafi Bamfai dan shi kansa ya fiso a tsorata masa ita sosai kan Husna ta dawo gidan inba haka ba komai na iya faruwa nan gaba, saboda yasan halin ta farin sani bajin magana take ba.
Bai samu matsalar shiga ba dan sun yi magana da Yaya Ja'afar kanya taho.
Tunda suka fito Nana a tsorace take ai batayi asalin tsorata ba saida suka shiga cikin Bamfai taga taron ƴan sanda tako ina, ga yara ƙanana da manya masu lefi wasu an kawo su hannu sanye cikin handcup, wasu yan uwan su sun zo neman beli suna kukan neman taimako, wasu kuma sun zo ganin nasu babu dama.
Gaba ɗaya jikin Nana saiya kama rawa cikin ta ya kulle, to sashen masu manyan lefika na Bamfai suka shiga kuma wajen ne da ko Namiji ya shiga in yaga yadda wajen yake dole zuciyar sa tayi rawa hankalin shi ya tashi bare mace, macen ma irin Nana da bata da wayewar rayuwa bata taɓa experiencing abu makarancin wannan ba, matar da bata taɓa zuwa ko gaban mai anguwar garin su ba yau ita ce a cikin tsakiyar Bamfai tsamo tsamo ai dole taji tsoro.
A ranta kuwa ta tsinewa Zahira da shawarwarin ta yafi cikin carbi, duk halin firgicin data shiga Mai Kano yana kula da yanayin ta yana mata dariya a ƙasan ransa, wallahi yau fes yake jin zuciyar sa dama da gangan ya roƙi Yaya Ja'afar a tsorata ta da kyau yadda kashe din zai shiga kunnen ta da ƙwaƙwalwar ta ya zauna sosai ba tare daya sake nina mata shiba, in ba haka ba kuwa nan gaba sai baƙin halinta yasa ta tayi kisan kai taja masa masifa.
Yaya Ja'afar na haɗa su da Abokin aikin shi Asp Zawaciki wanda Case ɗin yake hannun shi ya fito yabar musu office ɗin dan baya so yayi Case ɗin da kansa haka baya so ayi a gaban sa.
Nana da Mai Kano suna zaune a gaban Asp Zawaciki ya ɗago fuskarshi babu rahama da sauƙi ko kaɗan yace "ke ce kika yiwa yar kishiyar ki dukan mutuwa ko?"
Nana da ta riga ta kama tsorata ta daga kai da sauri.
"Magana zaki buɗe baki kiyimin ba body language ba." Ya faɗa a tsawace, jikin Nana ya sake ɗaukan rawa kar.....kar...kar...sai kuma ta fashe da kuka.
"Yallaɓai nice a gafarceni wallahi sharrin shaidan ne da zuciya."
"Zakiga sharrin shaiɗan randa kika sake koda dungurin tane." Zawaciki ya faɗa yana danna kira a wayar sa, yace "Eh shigo dasu sannan ka karɓo File ɗin Case ɗin Asma'u Abdullahi Mai Kano a wajen Mai Shinkafa." Yana gama bada umarnin ya kashe wayar yana kallon Nana dake kuka har yanzu yace "will you keep quiet my friend?"
Nana ta sake rudewa dan bata san mai yace ba, Mai Kano ya dube ta yace "Kiyi musu shiru basa
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 12 Chapter of 31