Share this page
ba, gwamda ma ita yana ɗan raga mata saboda bata fiya shiga sabgar shiba bare ta hado su amma Zahara basa kwashe sati a gidan nan saiya zage ta saboda ita bata bashi kuɗin ta, duk jarabar shi saita gadama yake cin ficikar ta, ita kuwa tuni ya gurgunta ta ɗan jarin Alewar tata ma tuni labarin ta yabi iska dan ƴan uwanta harsun gaji da ɗora mata jari yana cinyewa. Yanzu a gidan nan Allah ne gatan ta Husna da ƴan uwanta ne gatan ta, wannan yasa Dije ta sata a gaba da gorin rashin haihuwa kuma Zahara ke sake zugata a fakaice. "Sannu Ma'u." Ramma ta faɗa, Husna ta aje kwanunkan a gaban ta, bata ce mata kala ba ta wuce ɗaki. Ramma da kanta ta wanke kayan abincin sannan ta biyo ta ɗakin ta same ta a kwance a ƙasa tayi rufda ciki tace "Kiyi haƙuri Ma'u, in sha Allah zanwa Yaya Gali magana in ya shiga Binni saiya siyo miki hijabin." Husna ta tashi zaune tana kallon Ramma tace "niban saki ba, ai bake kika ci kuɗin ba bare ki biya, ni kawai tunda nace ki dena bashi kuɗi na kinki denawa daga yau zan dinga aje abuna da kaina kuma bazan aje a gidan nan ba bare ya lalume ɗakin ya kwashe." Tana faɗin haka ta ciro cinikin yau ta bata ta fita ta ɗibi ruwa ta shiga banɗaki saida ta cire kayan ta sannan taga kwandon wankan nasu ma babu sabulu, dole haka ta sheka ruwan ta fito. Zanin atamfa ashirille (Yadi/ roba) ta ɗaura tasa riga bulawus ta ɗaura kallabi tasa hijabin ta tun na sallar bara, hijabin ya dage mata sosai dan da kaɗan ya wuce rigar jikin ta, bata yi kwalliya irin ta sauran ƴan matan garin ba ta fito tayi waje, tunda Ramma taga haka kuma ta fasa kai niƙan kunun yamma dan tasan yau ba zata fita ba ke nan. Husna na zaune a ƙasan kargon kofar gidan su har aka yi sallar la'asar rana ta fara ja, Aramma yazo shiga gida ya ganta zaune ita kaɗai yace "a'a Asma'ullahi yau babu Kunun yamma?" "Eh Aramma sai gobe." Ta bashi amsa, ya gyaɗa kai yace "to a huta Allah ya kaimu goben." Ya shige gida, Aramma be daɗe da shiga gidan ba sai ga Baba Lirwanu fuskar nan tashi a cunkushe, Husna ko dar bata jiba dan yanzu bata wani tsoron shi. "Ke ya akayi baki zuba ruwa a randar Zahara ba yau?" Ya dafa yana cogewa a gaban ta. "Ka tambayi matan gidan zasu faɗa maka ita na fara cikawa randa aika santa bata ganin ruwa ta bari." "Ke dan ubanki ni kike cewa na tambayi matan gidan dan kin raina ni? To muje ciki saikin sake ɗebo wani danta juye na ban ruwan shanu a randar ta." Yana yin maganar yayi gaba Husna bata yi mamaki ba dan tasan Zahara ta saba yin haka saita ƙarar da ruwan randar ta sannan tabi na Shanu ta juye in Aramma yazo musu banruwa yaga babu dole yasa Lirwanu ya ɗebo, shi kuma inta dawo gidan ya rufe ta da zagi randa ƴan muguntar shi ke kusa kuwa sai tasha mari. Husna na ganin ya shige gidan tayi tafiyar ta ƙwalam ɗin yamma tana faɗin "wallahi bazan ɗebo ba duka ne ka daɗe baka daka ba, mara imani kawai." Lirwanu ya ɗauka ta shigo ta ɗauki jarakunan saida yaji Aramma ya fara kiran shi ya zo ya samo ruwan da zaiwa shanu banruwa sannan ya gane bata shigo gidan ba. A zafafe ya fito, Zahara na masa maganar ya bata kuɗin magin miya ya sauke mata haushin da yake ji ta hanyar luƙa mata zagi. "Ai kuwa yau kome Aramma zaimim sai naci uban Ma'u a gidan nan." Lirwanu ya faɗa yana fita daga gidan zuciyar shi a sama. ......Tunda aka idar da sallar la'asar yake kallon inda take zama ta saida Kunun yamma amma sai be ganta ba har rana ta kusa faduwa babu ita babu dalilin ta. Shi kansa ba zai iya tantance yanayi ko halin da yake ciki saboda rashin ganin Husna ba amma tabbas yasan baiji daɗin rashin fitowar tata ba. Garba ne ya ganshi yana ta zagaye a tsakanin shagon Sunday da inda su Husna ke zaman saida kunun yamma, tsam ya miƙe yaje ya siyo masa ruwa kamar yadda yaga Husna nayi masa amma ga mamakin sa daya bashi ruwan sai yaga yaƙi karɓa, daga karshe ma wajen ya bari gaba ɗaya ya koma can kusa da majalisar Dan Hajja ya zauna yana jijjiga kai kamar yadda yake yawan yi indai yana zaune. Yana zama a wajen babu jimawa majalisar ɗan Hajja ta cika da abokan shi suka fara shewa da hira irinta Samari. "Kai ɗan Hajja yau bazaku yi mana kunun yamma bane? Ga mahaukacin ku nan yazo ya zauna ata bayan mu ina kallon shi yana zagaye inda taka ke zama." "Wai Ma'u kake nufi? Ai Gambo Ɗan Hajja ɓatawa kanshi lokaci kawai yake yi, duk matan garin nan ya maƙale wa Ma'u tana masa wulaƙanci, kullum fa sai yaje kiranta amma bata zuwa, wallahi bana jin ma ta taɓa yi masa magana." Wani daga cikin Samarin ya tari numfashin wanda yayi maganar farko. "Kaifa banza ne, yama zaka haɗa Ma'u da matan garin nan? Ai kana ganin Ma'u kaga matar manya, haba Malam kai kaga tudun bayan ta kuwa? in tana tafiya Uhmmmmm!" Ɗan Hajja yayi wani murmushin iskanci yana shafa kai yaci gaba da cewa "tunfa bata ji Maza ba ke nan malam? Wannan in namiji ya buɗe ta Hmmm." Ɗan Hajja ya ƙarasa maganar yana wani kaɗa kai cikin nishaɗi, sauran matasan wajen suka kashe da dariya. "Yanzu dai haka zakayi ta binta tana ma wulaƙanci ke nan? Wani a cikin su ya jefa masa tambayar. "Ina ai ina faɗa muku Kakarbaɗi (shekara mai zuwa) ya wannan na Aure ta, wancan gidan dana gama na Ma'un Dan Hajja ne, Malam zan sha shagali fa." Gambo yace "taɓ ai kuwa saika dage ka shawo kanta tunda bata kula Samari, ni Bahari ma da farko da naga suna shiri da ita na ɗauka santa yake sai daga baya na gane kawai mutumci suke." Ɗan Hajja yace "ai da farko nima na ɗauka haka ne harna fara yi masa shirin wulaƙanci sai kuma naga e.....ita ta wajen nawa ma babu wani abu a tsanin su. Ina so naje na gaida Kakar ta ma anjima kaɗan na ɗan bata wani abu, Kusan kafar ta na riƙe kuma tace min karna damu zasu bani ita, amma Ogan sama ya kira ni ɗazu yace akwai wanda zai zo muje mu duba masa hanya anjima, akwai kayan sa za su wuce cikin satin nan, kunga dole a soke zuwa gaida tsohuwa." Sauran ƴan majalisar suka zuba ihun murna suna kiran "sai ɗan Hajja sai Foma ɗin mu saika Auri Ma'u malam zamu sha shagali." Duk wannan kirarin suna masa ne dan sunji ya ambaci aikin Oga sama dan sunsan indai yayi aikin ogan sama suma suna wata yawa, dan kowa saiya samu wani abu. Ogan sama mai gidan Dan Hajja ne, a sanin su yana shigo da buhhunan Madara da sauran kayan masarufi ta marauniyar hanya, ta Niger yake shigo da kayan shi ya biyo dasu ta ƙyauyu kan Jigawa saboda gudun custom da sauran jami'in tsaro, ogan sama yana da yaran dake duba masa hanya a kusan ko wanne ƙauyuka na Jigawa har kayan shi su tsallake iyaka, kuma sosai yake biyan su da manyan kuɗaɗe naban mamaki, duk sanda ya shigo da kaya suka wuce lafiya suna samun alheri, Dan Hajja na cikin yaran shi da suke masa aikin duba hanya, a garin kuma babu wanda yasan yana wannan aikin sai abokan shi na kusa irin su Gambo.... _*WRITING.....✍🏻*_ *_MUTUWAR AURE.....!_* _(Ƙaddarar wasu ƴaƴan)_ *_Kanawa ne👌🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ _BOOK 1_ *_FREE PAGES_* ________________ *_WHATSAPP GROUP👇🏻_* https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3?mode=gi_t https://wa.me/+2348064789370 _________________ _EPISODE 19_ Suna zaune suna hira har baƙon ɗan Hajja yazo sukai waya ya ce gashi a tasha ɗan hajja ya daga masa hannu ya ƙaraso inda suke, shima saurayi ne matashi ba zai wuce sa'an ɗan Hajja ba akan mashin ɗin sa Bajat yazo a gaban su Gambo Ɗan Hajja ya fara masa magana akan aikin da zasu yi shi kuwa bakon ganin su Gambo a wajen sai ya basar, ganin Dan Hajja nata magana a gaban abokan shi yasa abokin tafiyar tasa yace "mu ɗan yi magana a sirri mana." Ya faɗa yana yin gaba ya tsaya a jikin bishiyar da yake zaune tun ɗazu. "Kai baka da hankali ne kake maganar a gaban mutane? In wani a cikin su ya zagaye ya faɗawa jami'an tsaro fa? da alama Oga baima kashe ɗin aikin mu sirri bane ko?" Ɗan Hajja yayi murmushi yace "karka damu Abokina waɗannan da kake ganin su kaf na hannun dama ta ne, ko kuɗi ka basu bazasu faɗawa kowa wannan aikin nawa ba." Kallon baka da hankali bakon yayi masa yace "Gaskiya baka da tunani kai kasan halin mutane kuwa akan kuɗi? to kai banda rashin wayo ma ya zaka bude wa mutane hanyar neman ka, ai sai suma baƙin ciki." "Nace karka damu bani da matsala dasu dukan su a ƙasa na suke ci, amma babu matsala zan dena faɗa musu shine nan?" Matashin ya bi Dan Hajja da kallon kai wawa ne, suna juyawa zasu tafi saurayin nan yaga mahaukaci zaune a gefan su yana gangadi ɗan jim yayi yana kallon shi sai kuma ya dubi Dan Hajja yace "wannan fa?" Dan Hajja ya kalli mahaukacin saida ya yiwa wancan dariya sannan yace "wai kai meye duk ka wani tsorata ne? Bafa a shiga dawa dan ƙarya ina faɗa maka aboki na a shirye nake, wannan kuma kamar yadda ka gani mahaukaci ne ko magana bayayi ko mutum ka kashe a gaban shi saidai ya kalle ka ya wuce shike nan kaci banza ba zai wata magana ba, kaga zo muje dan Allah muna bata lokaci." Ɗan Hajja ya faɗa bai tsaya jin mai zaice ba yayi gaba, shima kan mashin ɗin sa ya haye suka yi cikin gari da mugun gudu suka ɗauki hanyar da zata kaisu Kabawa suka danna cikin jeji suna gudu kamar zasu tashi sama. Bayan tafiyar su ɗan hajja ya daɗe a wajen a zaune har saida aka fara kiran sallar Magarba sannan ya tashi ya mike titi dama tunda ya zo garin Magarba nayi yake miƙe titi ya tafi shike nan kuma sai gobe wannan yasa mutane ke ɗauka a makaranta yake kwana. *****Husna bata koma gida ba sai bayan sallar isha'i, tana shiga gidan Ramma tazo inda take da sauri tace "yau karki shiga wajen mu Lirwanu na fakon ki kema Ma'u waya kaiki kin ɗebo ruwan bayan kisan halin shi." Ramma na rufe baki ya fito daga wajen shi, Husna tayi kamar bata ganshi ba tayi lungu Dije data jiyo maganar Aramma. "Kin fara zama Munafuka ko Ramma?" Lirwanu ya faɗa yana bin bayan Ma'u da sauri, bata ƙarasa shiga lungun ba yayi tsalle ya ciro tsimagiyar maina yayi kanta zai daketa ta taka da gudu ya rufa mata baya suka fara zagaye cikin gidan, yana binta zai daka tana zillewa yana dura mata ashar, Aramma ya fito kanshi ko rawani babu yana kiran. "Kai Lirwanu baka da hankali ne? Meta maka da daran nan? Ba magana nake maka ba? Bazaka dena binta ba?" Lirwanu bai saurari Aramma ba Husna tayi wuf ta fice ta kafar gidan su Naja yabi bayan ta da gudu, ta fito waje tacan kofar gidan ya biyo ta dai-dai duhuwar Mainar ƙofar gidan yaji an taɗe masa ƙafa yayi gaba zai faɗi aka riƙo shi ta baya, kanya dawo daga firgicin muguwar faduwar da yaso yi yaji an kifa masa marika masu azabar zafi ta hagu da dama, dummm......yaji kunnen sa da kansa sun ɗauke, kanya dawo dai-dai aka shaƙe masa wuya a cikin duhun ya buɗe baki zai yi ihu aka kiɓa masa naushi a baki saida yasha maruka masu ƙyau sannan akayi jifa dashi kansa ya bugu da jikin bishiya baki a kunbure babu damar ihu, yana jin an sake shi ya kwasa da gudu ya koma cikin gida dafe da bakin shi. Matan gidan na tsaye cirko cirko Aramma ya fita neman su ta Kofar gida Lirwanu ya shigo da gudu ta gidan su Naja ɗakin Dije ya shige ya turo ƙofar ya rufe jikin shi na rawa. Dije da matan shi suka rufa masa baya. "Kai Lirwanu buɗe ƙofar mana, lafiya kuwa? Ina ita Ma'un?" Dije ke faɗa tana buga kofar Lirwanu yaƙi budewa. Fir Lirwanu yaƙi buɗe kofa saida Aramma ya zo yayi masa magana sannan ya buɗe yana haki. "Lafiyar ka kuwa Lirwanu ina Asma'ullahin?" Aramma yayi masa tambayar yana duban shi hannu dafe da baki, Saida Aramma ya sake masa magana sannan da ƙyar yace "wallahi Aramma nayi gamo dan Allah kamin addu'a gamo nayi da sheɗanu dubi yadda suka fasa min baki suka shaƙemin wuya Aramma nasha marin da ban taɓa jin irin sa a duniya ba." Yadda Lirwanu ke jero maganar yasa Zahara komawa da baya tana kumshe dariya a ranta tace "wallahi kome yasa Lirwanu wannan tsoratar zan so na ganshi." Sai kuma tace "alhakin zagin iyayena da kayi ne ɗazu Allah ya saka min." Duk hasken wutar Shekarau ya gaza ɗin daya haske ɗakin Dije saida Aramma ya sake kunna tochligh ɗin sa ya haske fuskar Lirwanu da tayi fushi lokaci ɗaya, ga kwanciyar yatsu miyar nan a ko wanne kunci hagu da dama bakin sa kuwa tuni ya haye yayi suntun ta gefe kuma ya fashe, haka wuyan rigar shi inda aka shaƙe sa ya cukwikwuye. "Subhanallah kaida waye haka Lirwanu? ina ita Asma'ullahin?" "Aramma bansan inda tayi ba ina binta a baya muna fita ƙofar gidan su Amadu naji......shuuuuu...anyi sama dani an min ɗaukar Amarya kan a sauke ni ƙasa saida akamin marika huɗu a jere, wallahi saida idona ya makance saboda azaba, zan yi ihu naji kummmm....an shaƙe wuyana an dagani sama an sakarmin naushi a baki sannan akayi jifa dani na faɗo kasa tim." Ramma ta koma baya tana rufe baki saboda dariyar data taso mata dan yadda Lirwanu ke fasalta yadda akayi dashi dole yasa ka dara, shi kansa Aramma saida ya murmusa sai kuma yace "babu wani sheɗanu ko dai faɗa ya haɗa ka da mutanen ka can, ni bari na duba inda Asma'ullahi tayi kada tsoro yasa tayi wani wajen." Aramma yayi maganar yana ficewa daga gidan. Dije ta dubi Lirwanu tace "kaima me yasa ka bita har waje? Baka bari saita kwanta ka ritsata kayi mata duka, shegiyar yarinya zata ja a illataka a banza, yanzu haka bayin Allah nan (aljanu) ka taka suna zaune, bari na baka hayaƙi kayi, ke Zahara ku bani garwashi." Dije ta faɗa tana sake duba fuskar Lirwanu. ...... Husna kuwa tana gudu ta juya taga baya binta kawai sai tayi tafiyar ta Dandali dan har an hura wutar kara yan mata sun fara gaɗa. Indo ta fara nema saida ta kutsa kai cikin ƴan gadar sannan ta ganta a cikin su tana rawa, bata tsaya a wajen ba ta fita, tana zuwa inda suke zama da Indo mamaki ya kashe ta dan shi ta gani a zaune yana babbuga Sandar shi a ƙasa, Husna bata ji tsoron ganin sa ko tunanin meya kawo sa wajen ba ta cire takalmin ta ta zauna a gaban shi tana murmushi kamar mai magana dame lafiyyan tunani tace "kaima daman kana zuwa Dandali?" Tafa san ba zai amsa ba amma sai taci gaba da cewa "ai dai nasan kana jina ko bakayi magana ba" Ta faɗa tana kallon shi kamar me jiran ya bata tabbacin haka. Sai yanzu ya ɗaga kanshi ya dubi fuskarta, ita kuma ta kalli fuskarshi data cika da gashi tace "nifa bana son naji ana cema mahaukaci nasan fa kai ba mahaukaci bane." Sandar da yake dokawa a ƙasa ya ɗan tsaya da bugawa yayi kamar yana sauraren ta, ita kuma hakan da taga yayi saita sake zagewa tace "Ai nasan baka da lafiya ne, kuma Mamana tace duk wanda bashi da lafiya addu'a ake masa ya warke, kaima kana so na rinƙa yi ma addu'a?" Yanzu ma shiru babu amsa haka kuma bai saka Husna yin shiru ba taci gaba dayi masa surutu. "Kaga ni inada Yaya sunan shi Baffa yana can Kano, shida Mamana suka tafi shike nan ban sake ganin suba." Sai kuma tayi shiru kamar me tunani muryarta a hankali tace "dan Allah na rinƙa kiranka Yaya kana so? Tunda kaga yanzu bani da Yaya shike nan saika zama sabon Yayana ka yarda?" Shiru babu amsa, tace "Shike nan ma nasan ka amince daga yau ka zama Yayana duk wanda ya sake cema mahaukaci zance masa sunan ka Yayan Husna." Husna ta faɗa tana murmushi yayin da shi kuma ya tsaya kallon ta da rufaffun idanunsa. "Ma'u.....ke Ma'u..." Taji muryar Indo tana ƙwala mata kira, ta juya sai taga tana tahowa inda suke Indo bata kula da waye a zaune ba saida ta ƙaraso. "Ke Ma'u dama keda mahaukacin nan ne kika zauna a gaban shi ko tsoron sa bakya ji? Allah kefa wani lokacin baki da wayo sai kinje wata ran ya miki duka, ki taso muje Aramma ne yake ta neman ki tun ɗazu." Indo ta faɗa tana tsayawa daga bayan Husna dan ita tsakanin ta da Allah tsoron shi take ji fuskarshi mai gashi kuwa tafi komai bata tsoro. "Dalla Malama ba mahaukaci sunan shi ba daga yau sunan sa Yayan Husna." Ta juyo zata yi masa magana taga yana kallon ta. "ko yaushe ya ɗago oho?" Tana masa murmushi tace "kaga Aramma yana kirana dama fa Baba Lirwanu ne zai dake ni na gudu bai kama niba." Sai kuma ta mike tsaye tace "Na tafi Yaya saida safe." tayi maganar tana juyawa Indo ta biyo ta a baya tana mata masifar danme zata je ta zauna kusa da mahaukaci. "Wallahi ma'u ki kiyayi kanki Hmmm! Haka kawai kije ki zauna kina masa zance sai kace wani me hankali to wallahi sai kinje wata ran ya yi miki illa, kina ganin shi kullum yana yawo da sanda kamar Bafulatani." Aramma ya gano Indo da Husna suna tahowa tare ya sauke ajiyar zuciya, dan harga Allah yaji tsoron kar tayi wani wajen saboda gudun duka. "Indo a ina kika gano ta?" Husna ta riga Indo magana da cewa "inda muke zama naje na zauna." "To sannu A'ishatu da kika samo min ita na gode miki." Indo tayi murmushi, Aramma ya cewa Husna suje gida Indo ma ta biyo su suka taho gaba ɗaya. Lirwanu yasha hayaƙin korar aljanu sai tilliƙa tari yake, Ramma tace "ko a ɗora ma ruwan zafi kayi dundumi sai kasa rof wajen bugun zai saki." Dije ta gwasale ta da cewa "Wani dundumi kuma abun iska ne fa kafin safe zai baje ai sunji hayaƙi." Zahara kuwa daga Sannu bata sake cewa komai ba ta kama bakin ta ta tsuke. Hankalin Husna kwance suka shigo cikin gidan tasan ta tsira tunda Aramma yana kusa wannan yasa har suka gama hirar su ita da Aramma bata da fargaba, sai can dare Aramma yasa Indo a gaba ya raka ta har gida, yau Husna bataje ɗakin Ramma ba dan acan take kwana in Lirwanu na ɗakin Zahara, ɗakin su da Indo nada da yanzu ita kadai take kwana aciki ta shige ta kwanta, yau ko fitilar ma bata nema ba a duhun ta laluma ta karkade gadon karar ta tayi kwanciyar ta. Washegari Lirwanu ya tashi baki ya sake haye wa danfa ya daku a wajen, fuskar shi duk ta kukkunbura, daga karshe dai dole shawarar Ramma ta jiya aka ɗauka Dije da kanta tayi masa dundumin ya shafa rof a wajen, tanayi masa gashin tana tsinewa Husna dan tace ita ce taja Aljanu suka buge shi, Aramma kuwa daga sannu bai sake bi takan suba ya fice. Koda suka haɗu da safe lirwanu be yiwa Husna magana ba saboda ta kansa yake. Yau take Jumma'a kuma yaune kasuwar Garki ke ci, kamar yadda Husna ta saba zuwa cin kasuwar duk jumma'a tayi tallar Barkono, yauma ana gama cin tuwon safe tayi wanka tasa doguwar rigar atamfa Ashashagarai anyi mata ɗinki rafa ta buɗe ta kasa, Ramma ce tayi musu anko da aka yi biki a gidan su, kallabi ta daura mai zanen baƙi da fari, duk da arhar suturar sosai ɗinkin ya zauna a jikin ta, mai kawai ta shafa ta fito dama kuma bata kwalliyar ƙyali irin ta sauran ƴan matan garin wannan kuma shiya sake bambanta ta dasu, kuɗin mota ta karɓa a wajen Ramma ta dau katon farantin silver tayi waje mayafinta ta ɗaure a ƙugun ta kamar wacce tayi shirin dambe. A ƙofar masallaci taga Aramma dasu Baba kwade, ta gaishesu, abokin sa Baba Alhaji ya fara mata kirari cikin tsokana yake faɗin. "Karya uwar faɗa Jikar Dije, Allah ya tsare yar gidan Abdullahi Jikar Aramma Abdussalamu ikon Allah, Allah ya kai miki Asma'ullahi." Aramma yayi dariya, Husna tace "Baba Alhaji wata rana zan maida kai Makka dan nasan yanzu ka manta yadda ɗakin Allah yake Saboda ance akan Jaki kaje taka Hajjin, kai kuma Baba Kwade zan taimaka na biya maka ummara ladan kirari." Sai kuma ta juya wajen Aramma dake ta murmushi tace "Aramma na tafi Kasuwa." "Allah ya tsare ya bada sa'a Jikar Dije nima yau na ɗana ko?" Aramma ya faɗi yana mata dariya, tayi gaba da ɗan gudu tana ɗaga musu hannu. A motar Naira Husna ta tadda Indo da sauran abokan tafiyar su, suna cikin motar Bahari ya zo wajen ya tsaya ta window inda Husna ke zaune yace "mutuniyar yau babu magana inata ɗaga miki hannu kika share ni?" Husna ta dube shi tace "ni ban ganka ba sarkin ƙorafi, wai dan Allah Bahari bazaka aske wannan uban gemun naka da saje daka tara a fuska kamar ɗan izala ba? Kanka cike da gashi sai kace mace, dan Allah ka rage ko za'a rinƙa ganin fuskar ka da imani are okkyau." Saida ya harare ta sannan yace "Malam wai ke ina ruwan ki da gemu na ne? Kinfa dame ni da yawa, Matata ke sonshi tace haka take son gani na shi yasa na ajesu, yawwa in kuma kyau yake miki ki faɗa naji kawai?" Husna ta zabga masa harara da manyan fararen Idanunta, yayi dariya dan yasan shike nan kuma ya rufe mata baki. "Yawwa nifa sautu nazo baki kika tsare ni da tsokana." Ya faɗa yana ciro kuɗi daga aljihu, Husna tace "ai wallahi bazan karɓa ba tunda kamin wulaƙanci, ko me kake so kahau Mota kaje ka siyo da kanka." Bahari ya buɗe baki yace "yanzu daga faɗar gaskiya saiya zama wulaƙanci Husnah?" "Kaji yaudara harda wani kirana Husnah." Indo dake kusa da Husna tana jin diramar tasu tana kwasar dariya tace "kawo sautun naka nina siyo ma?" "Bana son naki." Sai kuma ya juya yace "yawwa gani nan" da sauri ya tafi wajen fetir ɗin shi da aka zo siya. *****Yau ma Kasuwa tayi kyau Husna ta saida buhun barkono biyu harda rabi, ta haɗa ladan tallar ta da yawa, ta siyi sabon silifas dan nata ya fara mutuwa, Gurasa ta siyawa Ramma da tasan tana so, saita siya musu sabulu da omo. Karfe huɗu mai kyau sun gama haɗuwa a mahadar su, a motar Naira suka dawo dama shike kaisu ya dawo dasu, wanda suka sissiyo abun ci anata ciye ciye a Mota wasu kuma suna ta hira da maida yadda kasuwa

Chapter 21 of 31