faruwa, suma sauran Drs ɗin inda Dr Sadiq ya kalla suka maida hankalinsu sai kuma duk suka sauke kawunan su.
Saida Dr Sadiq ya yiwa Sagir allura kamar yadda yace, ya sake dubasa ya tabbatar da komai na tafiya dai-dai sannan ya biyo bayan sauran Drs ɗin suka fito daga room ɗin.
After some minutes
Zaune MM yake a gaban Dr Sadiq dake ta yi masa bayanin halinda Sagir yake ciki amma yayi masa banza, yadda ya zauna tunda ya shigo office ɗin har yanzu a haka yake bai motsa ba, kai ka ɗauka badan sauraren Dr Sadiq ɗin ne yake zaune a wajen ba, sanin hali yasa Dr Sadiq bai wani damu ba saima ci gaba da cewa yayi.
"MM dan Allah ka nutsu, na faɗa maka ya tsallake matakin haɗari in sha Allahu zai samu lafiya."
Dr Sadiq ya sake faɗa cike da yakini, sai yanzu MM ya ɗan motsa baƙaken lips ɗin sa kaɗan yace "inason ganin sa."
"Oh kaifa wani lokacin matsalar ka tafi ta ƙasar nan girma, na faɗa maka bazaka iya ganinsa yanzu ba, dan har yanzu bawai ya dawo normal bane infact baya iya gane komai saboda yana cikin maye har yanzu."
Ta cikin gilashin idonsa ya sake kallon Dr Sadiq yasan tabbas ba zai masa karya ba, dan akwai yarda da aminci a tsakaninsu......
"Dan Allah Malam ɗauke idanunka a kaina."
Maganar Dr Sadiq daya yita cikin tsokana ta katse masa tunani.....sai kuma ya mike tsaye.
Tare suka fito daga office ɗin, Dr Sadiq yana biye dashi yana masa surutu, su Faisal suna hango su suka mike tsaye kana ganin su kasan hankulan su duka a tashe yake.
"Calm down guys everything will be fine okay."
MM yayi maganar yana duba ogogon hannunsa, karfe ɗaya harda rabi na dare, fuska ya ɗan yamutsa sai kuma ya juyo wajen Dr Sadiq ba tare da yace masa komai ba ya basa hannu, Dr Sadiq ya jinjina masa kai yana ɗan murmushi.... Faisal ya bawa Dr Sadiq hannu suka tafa irin na abokai.....
Saɓanin zuwan su asibitin yanzu a nutse suke tafiya a kan titin babban birnin na Abuja ko ina yayi shiru sai wucewar mototi cilli cilli, ga fitilu ta ko ina, garin yayi fayau da hasken lantarki kamar ba dare ba, Sunyi tafiyar wajen minti goma sha biyar kafin su iso central area kai tsaye suka ɗauke hanyar da zata kai su Lamiɗo City estate......a bakin gate ɗin katon estate ɗin daya amsa sunan sa gari guda saboda girma da tsarin sa, yace su ajiye shi, babu musu wanda ke jan motar ya tsaya, zaman P-cap ɗin kansa ya gyara hakan ya sake boye kamannin sa yana fitowa Faisal ya biyo shi, saida ya dagawa sauran yaran shi hannu sannan ya ɗan juyo yana kallon Faisal dake binsa kamar yayi masa magana sai kuma ya juya yana ƙwafa a ransa, Faisal kuwa yana ganin haka yayi dariya ƙasa ƙasa dan yasan kobai faɗa ba bai so ya biyo saba, kawai dan babu yadda zai yi dashi ne.
"Malam ka rage sauri mana kasan ina binka amma kake jefa wannan doguwar ƙafar taka da taku biyu in kayi mutum sai yayi gudu kafin ya iso ka."
Faisal yayi maganar yana bin bayan MM da ɗan sauri ganin harya yi masa nisa....suna isowa bakin gate ɗin shiga estate ɗin sojojin wajen suka suruna suna gaida MM da suka gane sa tun kafin ya iso inda suke, kansa ya daga musu alamar amsa wa kai tsaye suka barshi ya shige cikin estate ɗin Faisal kuwa duk da sunsan tare suke da shi saida suka tabbatar babu komai na cutarwa a jikinsa sannan suka bari ya shiga...
Suna wucewa wani a cikin sojojin dake tsaran gate ɗin yace "Emanuel gayan nan kullum sake kashe ni yake da salon sa."
"Ai Oga MM ya wuce lissafin ka Osi, gay ɗin nan yana ji da kuruciya yana lokacin sa, lifestyle ɗin sa kamar ba yaron mayan ba, yana rayuwa kamar basu aje ko sisi ba, nan kuwa sune Abuja.
"ga bashi da wulakanci"
Wani a cikin su ya faɗa.
"Sai ɗaure fuska ko?" Emanuel ya faɗa yana dariyar sukaci gaba da hira akan MM da yake burgesu.
~~~~sunyi tafiyar wajen minti ashirin sannan suka iso kofar gidan su MM da zaka iya kiransa da Mahadi ka ture saboda tsabar girman da tsarin sa, duk jerin gidajen cikin estate ɗin ababan kallo ne amma kidan Engineer Mahmoud Mas'od Al-alfeey ya fita daban da sauran gidajen komai nasa na daban ne da sauran, tsaruwar gidan kuwa abun ba'a magana.
Sojan dake duty a bakin gate ɗin ne ya buɗe musu ƙaramar kofar gate ɗin da sauri yana sarawa MM cikin girmamawa, suna shige wa ya maida Kofar ya rufe, Masha Allah gaskiya gidan ya amsa sunansa tako ina, gidan ya haɗu tsarin ginin irin na turawan Andalus ( Spain) ne farfajiyar gidan ta wadatu da fitilu da shuke shuke masu jan hankali, saidai ko kaɗan babu wata haniyar kwale kwale a farfajiyar gidan.
MM ya doshi hanyar da zata kaisa asalin cikin gidan Faisal na biye dashi a baya yana ɗora hannunsa akan kofar falon ta bude kanta.
Ammi dake zaune a falon ta zuba uban tagumi tanajin buɗe kofar ta dago kanta tana ganinsa ta mike da sauri tana sauke ajiyar zuciya, kasa jira tayi ya iso inda take ta taresa da sauri, boyayyiyar ajiyar zuciya MM ya sauke dama yayi tunanin haka tunda yaga tarin missed calls din ta da bai san takira ba sai daga baya ya gani saboda wayarsa na silence.....yadda yaji bugun zuciyar Ammi sanda ta rungume shi abun saida ya basa tsoro.
"Ya Allah, Ammi ina lafiya fa."
Ya faɗa a hankali yana kama hannun ta, saida suka zauna saman kujera, sannan Faisal dake bayan MM yana kallon su yana murmushi Ammi ta kula da shi tace "A'a dama kuna tare ke nan? Faisal bazaka dena biyewa Lamiɗo kana biyo sa kana barmin yarinya ita kaɗai a gida ba ko?"
Ammi ta faɗa tana hararar Faisal dake ta sakin murmushi, sai kuma ya ɗan sosa kai ya rusuna yana mata sannu da gida.
"Ayi hakuri Ammi yanayin aikin namu ne sai kuna mana addu'a."
Ammi ta hadiye wani abu mara daɗi tana kallon MM dake rike da hannun ta har yanzu, tanaso tayi masa magana amma ganin Faisal yasa dole tayi shiru tace "babu komai Yaron kirki kuje ku kwanta ƙarfe biyu harta wuce nasan tunda ka biyo sa anan zaka kwana, zamu yi magana da safe, Allah yayi muku albarka."
Ammi ta faɗa tana mikewa tsaye sai kuma ta danyi baya kamar zata faɗi da sauri MM ya riƙe ta, Faisal na jera mata sannu.
"Sake ni Lamiɗo babu wani abu dake damuna gajiya ce kawai ke dauka na ga bacci inaji."
Ammi tayi maganar cikin karfin hali..... maimakon MM yayi yadda tace ɗin saiya cewa Faisal.
"Ka shiga ciki bari na raka Ammi."
Yayi maganar yana yin gaba da Ammi daya rungume ta bari ɗaya, saida suka haye saman bene sannan Faisal ya shige hanyar da zata kai sa ɓangaren MM yana tafe yana sake jinjina irin wannan soyayya dake tsakanin MM da Ammi, wani lokaci ganin kulawa da soyayyar dake tsakanin uwa da ɗan kan sashi tuna tasa mahaifiyar da ƙasa ta dade da rufe mata ido tun yana da shekara 7 a duniya, ƙwallar data cika masa ido ya share a fili ya furta "Allah ya kai Rahma kabarin ki Dadde."
*****
Yadda suke zaune a bakin gadon Ammi yana riƙe da hannayen ta inka gansu zaka rantse da Allah ba ɗa da uwa bane, sam Ammi bata yi kama da wacce ta haife saba inka cire rashin kama da basayi dashi tako ina, haka dole ne ka cire yanayin jikin Ammi dake nuna kuruciya, babu yadda za'ayi ka dauka ta shekara 48 a duniya, saboda ƙaramin jikin ta irin na Fulanin Manbila, danma tana da tsayi, har yanzu kyawu da zubinta na fulben Gembu yana nan babu abinda ya canja a tsarin jikin ta, san ado da kwanciyar hankali ya sake fito da hutu da rashin tsufan ta...... sun sha zuwa waje da MM mutane suce kanin tane, hatta kwayenta na nesa basu yarda ita ce ta haife sa ba, wasu kuma kance ɗan uwan mijinta ne, dan komai nasa irin na Babansa ne......a irin wannan lokutan sai dai Ammi tayi murmushi kawai tabar mutane da tunanin su, dan ita kanta wani lokacin inta kalli ginan nen ɗan nata sai taji alfaharin kasan cewar ta mahaifiyar sa......gashin kanta da cilli cillin furfura ya fara cikawa ne kaɗai ke bayyana girmanta.
Cikin sanyin murya MM yake lallashin Ammi da nuna mata ta kwantar da hankalin ta shi babu abinda ya same sa.
Kwalla cike da idonta take faɗin.
"Lamiɗo kullum nake ma addu'a amma kasan bana son wannan aikin naka, kullum inka fita bani da kwanciyar hankali sai naga ka dawo gida lafiya, dan Allah ka rufa min asiri ka karbi kasuwancin mahaifinka ka kyale wannan aikin da kake yi, duka duka nawa ake biyan ka da zaka dage akan sa, ga saida rai ga rashin kwanciyar hankali, aiki babu rana babu dare, duk nisan dare sai kun fita, wani lokacin fa Lamiɗo aikin nan bakwa tashi yinsa sai cikin dare, haba Lamiɗo nifa kai kaɗai gareni sai yar Uwarka da wata rana gidan wasu zamu kaita, nida Daddyn ka muna bukatar ka dan Allah indai kanason farin cikin Ammin ka kabar aikin nan haka wanda kayi musu a baya ma ya isa."
Yadda Ammi ke maganar tana share hawaye saida yasa kansa ya sara, yasan ko sau daya Ammi bata taɓa san aikin saba, tasha faɗa masa "Lamiɗo Allah ya karbi addu'a ta ya rabaka da ko wanne irin kayan maye rayuwar ka ta canja daga lalacewa zuwa kan hanya amma wannan aikin daka zaba wa kanka zai hana mutane shafe tsohon tarihin kokai wanene a baya."
Duk sanda Ammi ta faɗa masa haka saidai yayi mata murmushi yace "ki min addu'a ki manta da mutane, in kika biye musu bazakiyi rayuwa cikin salama ba".
Koda yaushe Daddy ke basa ƙarfin gwiwa, yana mutuwar san aikin sa kamar yadda ya tsani ganin kukan Mahaifiyarsa, yasan dole zaiyi mata yadda take so amma ba yanzu ba, a hankali ya furta
"Ammina zan bari, nayi miki alkhairi na kusa aje aikin nan gaba ɗaya amma kimin alfarma na karasa wannan aikin dana fara da kaina, burina shi ne na kama mutumin nan da kaina, zan yi nasara a kansa amma in kika yimin addu'a kuma kika samin albarka, dan Allah Ammi kimin wannan alfarmar."
Yana maganar yana ɗauke ƙwallar data cikawa Ammi ido da babban ɗan yatsan sa, saida ya share mata fuskar tas sannan ya sake kallon ta ta cikin gilashin idonsa, yaga tayi kicin kicin da fuska alamar ba haka taso ji daga gare saba, wani sassaukan murmushi da yayi mugun yiwa fuskarsa kyau ya sakar mata sai kuma ya ce "Ammi ki saki fuskar mana kafin Mijinki ya dawo gobe yace na sake masa mata ba haka ya tafi ya barmin ke ba."
Yayi mata maganar cikin rahar da saika manta ya iyata kafin kaga ya sake wata.
"Dama haka zakace mana Lamiɗo tunda ka tsarani koda yaushe haka kake faɗa min akan aikin ka Kum......."
Har yanzu fuskar MM da sauran murmushi ya katse Ammi da faɗin "ni anya rashin sa'ar nan tawa ma ba rashin albarkarki bace Ammi."
Sai kuma yanayin sa ya canja tuno yadda yayi missing target ɗin daya ɗauki tsawan watanni yana shirya masa amma cikin abinda baifi 30 minutes ba komai ya juya masa baya, tunda suka rasa nasarar kama kayan ransa yake a mugun bace, ga abunda ya samu Yaron sa da kaf cikin yaransa babu wanda yake ji dashi ya kuma yarda da shi kamar sa, wani abu mai ciwo daya tsaya masa a maƙoshi tun ɗazu ya hadiye.....Ammi data tsare shi da ido ta fuskanci sauyawar sa lokaci ɗaya cikin san basa ƙarfin gwuiwa tace "Subhanallah! Da albarka ta kake komai na rayuwar ka Lamiɗo koda banason aikin ka ban taba kin yi maka addu'ar samun nasara ba, karka damu in sha Allahu zaka cika burin ka."
Ta karasa maganar tana jan dogon hancinsa, sai kuma tayi masa murmushi tace "jeka kwanta karfe uku saura."
Saida Ammi ta kwanta yaja mata bargo ya rufa mata sannan ya sunkuyo ya sunbaci goshin ta, cikin Fullanci yace "Allah ya tashe ki lafiya." Ya juya ya kashe mata wutar dakin, Ammi tabi bayan tilon ɗan nata da murmushi, tana jera masa addu'a a cikin ranta har ya fice daga dakin.
A hankali yake sakkowa daga saman yana karewa falon ƙasa kallo komai a tsare yake kamar yadda ya saba gani tun yana Yaro, kofar da zata kaisa bangaren sa ya shige, da Sallama ya tura Kofar sai kuma ya ɗan tsaya cikin mamakin ganin Faisal da ya canja kaya da wata ruwan kasar Jallabiyar shi zaune a bakin gadon sa yana danna tab da alama wanka yayi.
"Kaima dai kasan bazanyi bacci ba dole sai munyi maganar abin da ya faru saboda musan abinyi gashi gobe kace 8am akwai meeting a office, social media har sun ɗauka kowa da abinda yake cewa different story, zance mafi munu kuma shine mutane sunata zagin Hukumar yaƙi da miyagun kwayoyi (NDLEA) musamman term ɗin da suka yi aikin"
Faisal ya faɗa yana kallon MM dake tsaye, mai makon ya bashi amsa kawai saiya wuce toilet ba tare da ko takamin kafarsa ya cire ba, ya kai wajen 15 minutes a banɗakin sannan ya filo sanye da riga da wando na bacci farare tas masu tsayi, har yanzu Faisal yana inda ya barsa.
"Danka addabeni ka biyo ni ke nan?"
MM yayi maganar yana zama akan dorowar gefan gadon sa.
Saida Faisal ya ajiye wayar hannun sa a gefe sannan ya maida hankalinsa gaba ɗaya kan MM.
"Wannan kuma matsalar ka, amma wai ya aka yi maganar fita kama kayan nan ta fita ne abun fa akwai ɗaure kai?"
A nitse MM ya tashi ya zubo shayi a wani ƙaramin mog ya tsaya a jikin ɗan madaidaicin table ɗin dake tsare a gefan dakin cike da karkacen books da na'uroro sai ɗan ƙaramin board irin me stick ɗin nan anyi wasu irin zane da maka akai da wasu nambobi barkatai, wajen a tsare yake kamar wani ɗan ƙaramin dakin binkice, yawanci anan yake yin wasu personal ayyukan sa, saida ya kurbi shayin sa yaji yakai masa inda yake so sannan calmly ya furta.
"cin amana ne."
"Ban gane cin amana ba, baka cemin duka yaranka ne akan aikin ba, nasan baka da matsala da team dinka, ni Wallahi gaba ɗaya kaina ya kulle."
"Kana buƙata ne?"
MM ya dagawa Faisal mog ɗin hannun shi yana nuna masa ƙaramin tea flask ɗin gaban shi.
"Wa? Badai ni ba, wa zai sha shayin ka ana zaune lafiya, kaidai da kaga zaka iya sai kayi tasha."
"Kana san surutu."
Sai kuma ya yiwa shayin zuka biyu ya shanye sa gaba ɗaya, yace "Faisal ba aiki yarana suka fita ba, neman tabbacin jita jitar dana samu na aika su bincika wa, and bana zargin su, amma tabbas akwai abinda ba daidai ba, wannan damar ma na rasata Faisal, kusan shekara biyu ke nan mutumin nan yanayin nasara a kaina, amma Wallahi wannan lokacin sai naga karshen sa ko uban waye ya ɗaure masa ƙugu a ƙasar nan saina kaisu ƙasa."
"Calm down, MM mubi komai a sannu kasan dai yadda ƙasar nan take, kasan kuma abinda yaso ya faru dakai wancan lokacin daka kamasa kuru-kuru aka so dorama laifin da zaka mutu a ɗaure badan taimakon Allah ba da yanzu fa ba wannan maganar ake ba, dan haka kabi komai a sannu wannan zafin zuciyar zaisa yaci gaba da yin nasara a kanka, abinda nake son sani shi ne ya aikayi har mota uku suka fita bayan kace ba aiki ka tura su ba?"
"Mota biyu na tsara zata fita da mutum huɗu ɗaya tasa ido ɗayar kuma ta bisu a baya cikin badda kama, Chike ya faɗa min suna fita daga office Sagir yana shigowa shi ne yabisu a baya ba tare da sanin suba saida suka yi nisa suka kula da shi, nafi tunanin ganin motar sane ya ankarar da masu lefin saboda shi da motar office ya bisu saɓanin su da suka fita da private."
"Sagir Sagir...." Faisal ya maimaita sunan har sau biyu sai kuma ya zubawa MM ido yana cewa "shine yaron nan da ya tare ma harbin watannin baya ko?"
Faisal ya faɗa yana shiga cikin dogon nazari.
MM yace "Yeah."
Faisal ya ɗora da faɗin "Amma yaron nan kamar ba alakar uban gida da yaron sa kaɗai bace tsakanin ku ba?"
"Mene?"
MM ya faɗa yana maida hankalin sa kan Faisal.
Faisal ya girgiza kai cikin tabbatar wa yace "Yes, kayi tunani mana, wannan yaron duk cikin yaranka yafi kowa nace maka, sannan akwai wani abu da na dade ina gani a cikin idon yaron fiya da sauran yaranka, yes nasan duk yaranka na sonka da girmama wa saboda alkhairinka gare su, amma na Sagir gaskiya is different and so da girmamawar da nake ganin Yaron nayi maka kamar akwai wani abu dake boye a zuciyar sa, abunda ya faru sanda aka kawo ma hari watannin baya ya sake sawa na tsinke da lamarin sa, ya tare harbin da aka yi ma, cikin jini muka kaisa asibiti amma bakinsa banda kai babu abinda yake kira, sannan me yasa a bayan fage yake kiranka Hamma, naso muyi maganar nan tun lokacin da abun ya faru amma sai ka nuna min wannan tunani ne kawai, MM ina tsoron ayi amfani da kyautatawar ka a shirya maka wani makircin."
"Hey.....officer nan fa ba office ɗin SS bane, bance kamin aikin ka anan ba, ka bari inna gayyato ka sai kamin duka wannan lissafin."
MM ya fadi maganar ko a jikin sa kai saika rantse da Allah abinda Faisal ya faɗa bai dame saba, a ƙasan zuciyar shi kuwa tsaf ya dade da gane abinda Faisal ɗin yake san haska masa akan yaron nasa, shi kanshi ya dade yana yiwa kansa tambayar me ya taɓa yiwa yaron na alkhairin da yake masa irin wannan mugun son, amma zai binciki Yaron da kansa.
"MM bafa komai bane ake share wa ya kamata kayi tunani akan magana ta, inba haka ba Mutumin nan da kake rena wa zai ci gaba dayin nasara a kanka ta inda baka yi zato ba"
"Nasara kuma ta nawa Faisal, ko ka manta tarihi ne? Ni da Kaca fa alaƙar me siye dame siyarwa ce, in sha Allahu ni zan zama silar ajalinsa, Sadiq ya faɗa min akwai abinda aka shaƙawa Sagir da ya sashi a halin da yake ciki."
Ya danyi shiru yana tuna abubuwa masu ciwo da suka faru a kansa shekarun baya da wanda Kaca ya faɗa masa satin daya wuce.
_"Ƙwaya na samu labarin idonaka nakan kayana, inama albashir wannan karon bazakayi nasara ba kayana za su wuce lafiya zan kuma saida su cikin kwanciyar hankali babu yadda zakayi dani, akwai mutuniyar zata shigo da zafinta, irin kayan gabas ne nasan kana santa nasa a kawo maka ne? Hhhhhhhh"_
Sanda ya karanta sakon baki kawai ya tabe danya sawa ransa saiya bawa Kaca mamaki, indai yana kan aikinsa ya daina yin nasara.
Muryar MM a cin kunshe yace "Faisal in abinda nake tunani Kaca yasa aka yiwa Sagir dole saiya fita daga ƙasar nan yaga manyan likitoci inba haka ba zai rasa tunanin sa koma ya rasa hankalin sa gaba ɗaya."
MM yayi maganar ransa a mugun tafashe sai kuma ya mikawa Faisal wayarsa.
_Nagode daka bani damar yin gwajin sabon zubi akan yaron ka._
Faisal ya karanta sakon a fili sai kuma ya kalli MM da sauri idanunsa cike da tsoro ya buɗe baki zai yi magana MM ya rigasa da cewa.
"Abinda yace ɗin shi ya aikata dan Sadiq ya faɗa min an shaƙawa Sagir wani abu da suka kasa gane ko menene kuma ba ƙwaya bace hodar iblis bace."
Duk yadda sanyi AC ya huda dakin saida Faisal ya share wata guntuwar zufa data jika masa goshi.
"Kai wannan mutumin yanada hankali da imani kuwa?"
"Mai su zai yi abinda yake aikatawa ne?"
"A'a."
Faisal ya faɗa cikin sarewa da lamarin, MM kuwa idanunsa da suka jirkice ya rufe kwakwalwar sa na tuno masa abinda ya faru a shekaru shida da suka wuce, wanda faruwar su ya zama silar shigar sa aikin NDLEA da baya cikin tsarin sa bare ya taɓa yin tunanin zai zama ɗaya daga cikin ma'aikatan su.
"Ina tunanin zanyi wani abu a wannan karon Faisal, bazan iya ci gaba da bari rayuwar matasa tana lalacewa ba kamar yadda tawa taso ta lalace ba a baya, duk yadda zan faɗa maka illar wannan mutumin a cikin al'umma Wallahi ya wuce haka, Kaca ya wuce tunanin ka, ba iya Ƙwaya da hodar iblis yake siyarwa ba, yana da wasu mugwayen kasuwanci a bayan saida Ƙwaya, amma zan bashi mamaki zan karanta masa karatun da mutane ke fada na (mugu shi yasan makamancin mugu)."
Jin furucin MM yasa Faisal ya zare ido yana faɗin "me kake nufi? Me kuma zaka yi, abinda dokar aikin ka ta baka dama akai shi ne ka kama duk wasu masu siyarwa ko safara da shan muyagun kwayoyi ka miƙasu ga SS ko DSS suyi bincike akan su insun tabbatar da lefinsu su mika su kotu tayi musu hukunci wannan shi ne aikin ka a takaice, banaso ka sake yunkurin shiga cikin aikin da ba naka ba bare mutanen nan su sake samun damar yi maka wani sharrin."
Faisal yana sake maimaita masa abinda ya sani ne danya kiyaye, amma shi hankalin sa ya dade dayin nisa da abinda Faisal ɗin yake faɗa, idanunshi da suka cirkice ya zubawa Faisal......babu abinda tunanin sa ke hasko masa sai fuskar Matashin yaron da silar taimakon sa ta canja lissafin rayuwar sa gaba ɗaya......ya tashi daga mutum mara manufa zuwa cikakken mutum kamar kowa..... wannan silar ce kuma ta zama sanadin..... tashin sa daga mashayi zuwa mahaukaci a indon dangin mahaifiyar sa....silar da tasa yan uwa suka guji Ammin sa suka hana ƴaƴan su zuwa gidan ta.....wannan sila ita ce taja aka zagi Ammin sa akan idanunshi....tayi kuka da baƙin cikin da bai taba ganin akan fuskar taba...... A Cikin zuciyar sa dake ci da wutar bakin ciki ya furta.
"Tabbas Kaca in ban kawo karshen harƙallar kaba niba ɗan mahaifiyata bane....."
Hmmmm🤔
Da akwai fa kura da alama to amma muje zuwa.
_*WRITING.....✍🏻*_
*_MUTUWAR AURE.....!_*
_(Ƙaddarar wasu ƴaƴan)_
*_Kanawa ne👌🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
_BOOK 1_
*_FREE PAGES_*
________________
*_WHATSAPP GROUP👇🏻_*
https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3?mode=gi_t
https://wa.me/+2348064789370
_________________
_EPISODE 3_
Baban Bishira na ɗaga wayar Umma tace "Malam dan Allah kazo gida yanzu."
"Subhanallah yana jiki haka Barira lafiya dai ko?" Malam idrisa cikin tashin hankali dajin muryar matar sa kamar tana kuka yayi tambayar.
"Lafiya dan Allah kazo kawai."
Umma ta sake faɗa kan ya kuma cewa wani abu harta kashe wayar.
Suna nan a zaune sun zagaye Husna suna kallon ta Malam Idrisa ya shigo gidan a sukwane, hango kafatanin iyalan na sa zaune a waje ɗaya ya sauke ajiyar zuciya dan hankalin shi ba ƙaramin tashi yayi da wannan kiran ba.
"Baban Bishira ƙaraso nan kaga ikon Allah." Umma ta faɗa tana tashi daga gaban Husna.
Lokacin da Malam Idrisa yayi ido biyu da Husna saiya juyo ya dubi matar shi cikin neman ƙarin baya
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 3 Chapter of 31