Share this page
tsinannan daya yima wannan abun sai ya dandana kuɗan shi, har ni za'a yiwa iya shege a garin nan." Dije ta faɗa bakin ta na kumfar jaraba. "Ina.....Iya wallahi ba mutane bane, wannan Aljanu ne Aramma kumin maganin Aljanu inba haka ba zasu kashe ni wallahi kashe ni za suyi." Lirwanu ya faɗi yana sharbe majina. Aramma ya dube sa da kyau yace "yanzu dai zakayi mana bayanin meya same ka ko kuwa sokiburitson zakaci gaba dayi na kama gaba na." "Zanma bayani Aramma dan a samo min maganin Aljanu ma zan faɗa maka." "To yayi meya same ka, ba tare mukayi Sallar asuba ba?" Aramma ya faɗi yana duban Lirwanu. "Aramma muna fitowa daga masallaci titi na miƙe na tafi bahaya can bayan makaranta, saida na gama bayan gari na baro wajen ko taku biyar masu kyau banyi ba naji an ɗaure min ƙafafu da wani abu na kasa gaba na kasa baya, zan juya bayana da naji takun mutane sai aka saka min wani abu me ƙarfi aka manne bakina, da ido na, ina neman yadda zan cire abun ido da baki na aka zare min riga da karfin tsiya aka ɗaure hannayena ta baya wallahi na dauke yan mafiya ne kawai sai naji saukar duka tako ina su ke duka na babu bakin ihu da neman ceto saida suka yimin lilis sannan sama-sama naji ana faɗin ya daku ku barshi haka amma ku buge ƙafafun sa, wallahi da aka buga min wani abu a kafata wannan ta dama saida wajen yayi ƙara, da kansu suka mayar min da kaya na sannan suka kunce min ƙafafu da hannu, a wajen na zube ban sake gane abinda yake faruwa ba saida aka shigo dani gidan nan." "Innalillahi wa inna ilaihirraju'un!" Mutane wajen suka ɗibi ambaton Allah da masu Salati Husna dai tana tsaye a kusa da Ramma tana ganin ikon Allah, dan wallahi babu ƙarya ya daku duka ba kaɗan ba kuwa, saida Aramma yasa aka cire masa riga sanan akaga yadda jikin sa yayi wani irin burdin burnin bulala ga fuskar sa tasha maruka hakorin sa nagaba ya fita. Tsalaha abokin Lirwanu yace "Wallahi Aramma muna tafiya zamu bayan gari muka ganshi yashe a ƙasa baya numfashi har munji tsoro da farko dan bamu gane waye ba saida muka kawo shi makaranta muka zuba masa ruwa muka daye abinda aka rufe masa baki da ido da ƙyar sannan muka gane Lirwanu ne." Tsalaha ya faɗi yadda suka samu Lirwanu a jeji yashe, Dije ta fara zazzaga tsinuwa tana faɗin sai ta ɗauki mata ki. Aramma kuwa rasa tunanin daya kamata yayi ma yayi, gaba ɗaya kanshi ya kulle dan haka yace kowa ya tafi yabar wajen, ya dubi Lirwanu yace "kodai kayi rigima da wasu ne?" "Wallahi babu wanda muka yi rigima Aljanu ne kawai wannan dukan bana mutane bane." Lirwanu ya faɗa yana zufar wahala. Aramma yace shike nan kayi haƙuri za'a sama maka magani. ****** Da misalin sha biyu na rana ɗan aiken Mai gari yazo kiran Aramma ya same sa a kofar masallaci suka tafi wajen Mai gari tare, Aramma yana tunanin ko lafiya. A ƙofar Mai gari yaga wata mota ƙirar Honda Accord Baƙa da wani matashin saurayi da ba zai wuce shekara ashirin da uku zuwa da biyar ba tsaye a jikin motar, Aramma bai kawo komai a ransa ba ya shiga rumfar mai Gari da sallama. "Wa alaikumussalam maraba da Aramman gari, bismillah." Mai gari ya faɗa yana nunawa Aramma wajan zama. Saida suka gaisa cikin mutuntawa Sannan Mai gari yace a kira masa baƙuwar da tazo a cikin gida. Suna zaune ta shigo da gwarin Hausar ta da kana ji kasan a sama ta koya suka sake gaisawa da Mai gari, Mai gari ya dubi Aramman yace "wannan baƙuwar kace, ɗazu tazo aka rako ta nan tace min ita da ɗanta ne suka zo zaka ganshi nan waje da mota, wajen ka tazo amma bazata je gidan kaba saboda abinda ya kawo ta magana ce daya kamata ayi ta a gabana to shi ne yasa na aika a kiraka." Aramman ya dubi matar yace "baiwar Allah sannu da zuwa daga ina haka dan ban gane kiba." Saida ta rusuna ta gaishe da Aramma ciki girmamawa kamar yadda yare suke yi sannan ta gyara zama ta fuskanci Aramman tace "Ni sunana Mansura Abdulkadir Mai Shinkafa, daga Kano nake ni yayar Safiya ce tsohuwar matar Abdullahi" "Allahu Akbar kabiran, wallahi ban gane kiba saida kika faɗi haka sannan naga kuna yanayi da safiya, sannu da zuwa Mansura ya kika baro manyan? Ina Alhaji ƙarami (kanini Husna)" Aramma ya faɗa yana duban Aunty Mansura. "Kowa yana nan lafiya Alhamdulillahi." "To Masha Allahu." Aramma yayi shiru yana sauraren ta, Aunty Mansura ta sake tara hankalin ta waje ɗaya tace "Aramma nazo ne domin ka bani Husna na tafi da ita, saboda mu inganta rayuwar ta, munyi ta zuwa duba lafiyar ta a gidan Baban ta amma saiya sanar damu tana nan, tun muna saka ran zai dawo da ita Kano sai kuma muka ji shirun yana sake yawa wannan dalilin yasa ni na wanke Kafa nazo wajen ka ka bani ita da adalcin ka na tafi da ita, in ma bakwason zaman ta damu kamar yadda Maman Abdullahi ta kafa sharaɗi a wancan lokacin da tasa Abdullahi ya saki Safiya to mun yarda zan maida ita gidan Baban ta taci gaba da zama acan, amma shi zaman nan ɗin ne ga yarinyar da bata taso anan ba kamar Husna sai nake ganin gaskiya akwai shiga hakki." Aunty Mansura ta jero maganganun cikin salama da kwantar da kai. Mai gari ya gyaɗa kai ya ce "tabbas tabbas akwai shiga hakki kam, yarinya mai basira irin wannan." Aramma yayi shiru yana juya zancen Aunty Mansura filla filla yake musu bashin baƙi, wato dai Dije ce tasa Abdullahi ya saki Safiya ta ƙarfin tsiya kamar yadda yayi tunani a wancan lokacin, sannan ita ce ta hana su riƙe Asma'ullahi. Lallai rashin adalcin nata ya kai, tabbas duk maganganun ta haka suke kuma tazo akan gaba, tabbas daya faɗa wa Abdullahi halin da Asma'ullahi take ciki da babu shakka zai ce shiya aiko ta, amma danya sake tabbatar wa sai yace mata. "Gashi kuma shi Abdullahin bai faɗa mana zakizo ɗaukan taba." "Eh kamar yadda na faɗa maka da farko Aramma Abdullahi baisan nazo ba, wannan zuwan kaina ne." Aunty Mansura ta sake faɗa tana karantar yanayin Aramma. "To babu lefi kin kyauta Mansura Allah ya baki ladan zumunci yaji kan mahaifin ku mutumin kirki sannan kin zo akan gaɓa, dan cikin satin nan nake zuba idon Abdullahi ya zo ya ɗauke ta ko nakai masa ita da kaina, amma tunda Allah ya kawo ki shike nan faɗuwa tazo daidai da zama, yanzu bari nasa a kirata." Aramma ya faɗa zai tashi mai gari yace "a'a Aramma ai ba sai kaje da kanka ba duk ga yara nan bari nasa su kirata." Mai gari ya faɗa yana miƙewa ya shiga cikin gidan shi saida ya tura a kirawo Husna a gidan su sannan ya dawo rumfar sa ya zauna. Husna tana zaune tana taya Ramma tsintar wake yaro ya shigo yace taje inji Aramma yana wajen mai gari. Tsaram Husna ta zare hannunta ta shiga ɗaki ta dakko gyalan doguwar rigar dake jikin ta ta fito, ƴar uwar rigar da aka basu ce a asibiti a jikin ta, rigar ruwan goro ce mai dubu ta saukar mata har ƙasa gata da faɗi mayafinta bashi da wani girma sosai Husna ta yafa gyalan a kanta fuskar ta sanye da eyesglass ɗin ta ta tafi gidam mai gari, inda akace Aramma na kiran ta. A kofar gidan ta wuce Abdulyassar dan Aunty Mansura sam bata gane shi ba kamar yadda shima bai gane taba. A bakin rumfar Mai gari tayi sallama daga ciki mai gari yace "shigo Ma'u." Aunty Mansura najin an ambaci sunan ta ta zuba wa ƙofar shigowar ido. Husna ta shigo cikin sanyin hali da nitsuwar ta ta halitta, Aunty Mansura ta bita da kallo daga sama har ƙasa. "Husnan Safiya ce ta girma haka? Allahu wahid, tayi tsayi saidai ta rame sosai fuskarta tayi fiyau, kayan jikin ta ta kalla da mamaki tabbas tasan rigar da kuɗin ta dan design ɗin na cikin irin kayan da suka kawo na karshen nan. Abdullahi nada zuciyar yiwa iyali ba wani abu bane dan ya siyawa Husna wannan rigar ba." Aunty Mansura ta ayyana a zuciyar ta. Saida Aramma ya nuna wa Husna Aunty Mansura dake zaune sannan ta kula da ita, da sauri ta ɗaga kai tana kallon ta tace "Mami....Mami yaushe kika zo nan? Mami tare zamu tafi ko?" Husna ta faɗa tana yin kan Aunty Mansura da sauri ta faɗa jikin ta ta ƙanƙame ta kamar ance mata zata gudu ta barta sai kuma ta fashe da kuka. "Mami dan Allah ki tafi dani kinji? Mami ki kaini wajen Yaya ni bana son zaman nan Mami dan Allah karki tafi ki barni." Husna ta jero maganganun tana rusa kuka, sosai hankalin Aramma ya tashi zuciyar shi tayi masa babu daɗi. "Allah sarki Husna ashe danne ta akayi shi yasa take zaune anan dan bata da yadda zata yi amma dubi daga ganin wacce zata iya tafiya da ita yadda take kuka tana haɗa ta da Allah karta tafi ta barta." Aramma yayi zancen a rasa a fili kuwa sai yace "In sha Allahu tare zaku tafi Asma'ullahi yau kin gama zaman nan sai dai kizo mana da ziyara." Husna ta saki Aunty Mansura dake share hawayen tausayin ƴar ƙanwar tata tace "Aramma da kaske." Ya daga mata kai yana Murmushi alamun tabbatar wa. Ai Husna saita dena kukan ta saki Murmushi ga wahaye ga dariyar jin daɗi, Aunty Mansura ta cire mata gilashin idan ta ta share mata fuskarta da hawaye ya jika tana kallon ta, sai kuma ta goge mata gilashin ta ɗaga shi sama tana ƙare masa kallo da sauri ta dubi Husna idanun ta a waje cikin tsoro tace "Husnah matsalar ido gare ki?" Husna ta ɗaga mata kai Aunty Mansura kawai saita koma da baya ta zauna daɓas a ƙasa tana sauke numfashi riƙe da gilashin tace "lahaula wala ƙuwwata illa billah, mun shiga ukku ni Mansura." "Subhanallah! Kulla karki sake faɗin haka Mansura jarrabawar Husna ke nan in sha Allahu zata warke." Aramma ya faɗa da yanayin nuna wa Aunty Mansura ba komai bane hakan. Mai gari ma ya jajan ta mata Husna kuwa na zaune a kusa da ita ta maƙale mata, suka sake tattauna wa da Aramma sosai akan Husna ta kira Abdulyassar ya gaida Aramma ta nuna masa Husna yayi mamakin ganin ta. Da yarabanci yake cewa Aunty Mansura "Amma ta girma." Sai yaga Husna tayi murmushi ta gaisheshi da Yarabanci, abun ya bawa Aunty Mansura mamaki har saida ta kasa haƙuri ta tambaye ta bata manta yare ba. Husna tace "eh akwai wani mai shago ana Ibone amma yana jin Yerabanci shi yake min yare." sosai Aunty Mansura taji daɗi. Aramma ya tashi yace wa Aunty Mansura bari ya yi wa uwar riƙon ta magana sai tazo tunda ita tace ba zata koma gidan suba. Aunty Mansura tayi murmushin jin kunyar tsohon amma kuma tayi alkawarin bazata gidan su Abdullahi ba dan ko kaɗan bata son ganin Dije, kar taje ta faɗa mata wata maganar ta biye mata su kunta hali shi yasa ma ta zaɓi zuwa gidan Mai gari. Aramma ya tafi ya faɗawa Ramma zuwan Aunty Mansura. Sanda Aramma ya fadi zuwan Aunty Mansura da tafiyar da zatayi da Husna balli saiya nemi tashi dan Dije ɗora hannu tayi aka tace bata yarda ba shi kuma Aramma yace babu wanda ya isa ya hana a tafi da Husna. Lirwanu ma yana fama da kanshi amma saida yabi bayan Dije, Aramma yace wa Ramma. "haɗa ya nata ya nata ki tafi gidan Mai gari, yau zanga wanda ya isa ya hana su tafiya a garin nan." Ramma ta shige ɗaki haɗa kayan Ma'u har cikin ranta murna take taya Husna sai dai akace wai sabo shi ake wa kuka gaba ɗaya saita rude ta rasa abinda zatayi a ɗakin saida Aramma ya turo Zahara tayi mata magana sannan ta haɗo ɗan kayan Ma'u da basu fi kala shida ba daga sabin har tsofin ta zuba a kongwaramar akwatin ta ta tafi gidam Mai gari. Nan fa zance ya tashi a gidan, da masu yiwa Husna murna da masu cewa hakan bai dace ba, da munafukai masu fuska biyu irin su Zahara. Dije kuwa baƙin cikin rusa mata tsari da Aramma yayi ne ya ƙume ta ya sata kuka gaba ɗaya ya lalata mata komai. Taso ta maida Ma'u tari a wajen Hajja da Ɗan Hajja amma yanzu an lalata mata komai. Inta tuna abubuwan da zasu kuɓce mata dalilin tafiyar Husna bata sanin sanda take fasa sabon kuka, kaf dangin Safiya kuwa babu wanda bata tsinewa albarka ba sai wanda ta manta... _*WRITING.....✍🏻*_ *_MUTUWAR AURE.....!_* _(Ƙaddarar wasu ƴaƴan)_ *_Kanawa ne👌🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ _BOOK 1_ *_LAST FREE PAGES_* ________________ *_WHATSAPP GROUP👇🏻_* https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3?mode=gi_t https://wa.me/+2348064789370 _________________ _EPISODE 27_ Aunty Mansura tayi zugum ɗaya bayan ɗaya take kallon kayan da Ramma ta kawo mata da sunan kayan sawar Husna, kayan Husnah dai tasu ƴar gidan Safiya Autar gidan su. "Allahu Qadir." Ta faɗa a bayyane kawai sai ta kama hannun akwatin ta rufe tana duban Ramma tace "sannu baiwar Allah, mungde sosai Allah ya biyaki, tunda muka shigo Husnah ke faɗa min kece Maman ta sai Aramma, mungde miki amma dan Allah wannan kayan ki tafi dasu kawai nasan baza a rasa wanda zaki bawa ba, babu matsala in munje gida sai a nema mata wasu." Ramma tayi murmushi tace "to Maman Ma'u nice da godiya, amma zanye kewar Ma'u." Ta faɗa idan ta na cika da ƙwalla, matan Mai Gari suka hau bata haƙuri tunda sunsa ita bata da yara sai Ma'un. Aunty Mansura ma haƙuri da godiya take ta mata, suna ta maida zance Husna ta fita da gudu babu wanda ya kula ta tafi tasha neman Mahaukacin yayanta, saida ta zagaye tashar tana neman sa amma bata ganshi ba, wajen Bahari ma taje baya nan, ta wuce Chioma a ƙofar shago tana mata magana amma hankalin ta yayi gaba bataji taba. Ta daɗe a tsaye a tashar tana tunanin wanda zata bawa saƙo ya faɗa wa yayan ta Mami tazo tafiya da ita amma kowa ta kalla sai taji ta kasa faɗa masa komai, jikin ta a mugun sanyaye ta kamo hanyar barin tashar a hanya suka haɗu da headmaster ya tsuke ciki riga da wando yasa gilashi yana kallon mutane ɗai ɗai, Husna ta wuce shi tana masa kallon banza ta saki tsaki. Dama tun daga randa taga yana ƙoƙarin dukan yayan ta ta tsane shi haka bata sake siyar masa da komai nata ba. Ko yace ta bashi akan idon sa zata ce bazan siyar maka ba, tun yana binta ta siyar masa da kayan siyarwar ta har ya haƙura ya daina tayawa. A ƙofar gidan Mai gari ta samu Abdulyassar, Aramma da Aunty Mansura Aramma ne ya fara gano ta yace "yawwa gata nan ma, Asma'ullahi ina kika tafi? Kin barsu suna jiran ki." Husna ta sunkuyar dakai tana murmushin jin daɗi. Ramma ta fito, Mai gari ma ya fito Aunty Mansura ta ciro kuɗi masu yawa tabawa Mai gari ya karɓa yana ta zuba mata godiya, haka Ramma saida tayi mata alheri, yaran da suka zagaye Motar kuwa dubi daya ta basu tace suje su siyi alewa nan da nan suka watse suna murna. Aramma ya dubi Husna da bakin ta yaƙi rufuwa yace "to Asma'ullahi Allah ya kiyaye hanya ki gaida Mamanki da yayanki kinji, ki gaishe min da Alhaji ƙarami, Allah ya raya ki yayi miki albarka." "Amin Amin Aramma mun gode sosai Allah ya ƙara girma da lafiya." Aunty Mansura ta faɗa tana kama hannu Husna Ramma na danne kukan ta ita ma tace "Allah ya kiyaye hanya Ma'u sai wata ran." Ta faɗa tana barin wajen da sauri dan kuka ne ya ƙwace mata. Husna kuwa taji babu daɗi sai dai murna ta hanata yin kuka dan Allah Allah take su tafi gani take kamar za'a ce an fasa tafiya da ita. Harta juya zata shige mota sai kuma ta dawo da baya ta tsaya a gaban Aramma tana kallon sa tace "Aramma dan Allah sako zan baka ka faɗawa Yayana." Aramma ya tsaya yana kallon ta dan bai gane wanne yayan nata ba, ganin bai gane wa take nufi ba sai Husna tayi murmushi tace "Aramma Yayana fa wanda bashi da lafiya." "Oho wai bawan Allah nan?" Husna ta ɗaga masa kai tace "naje tasha kozan ganshi na faɗa masa zan tafi amma baya nan, dan Allah Aramma ka faɗa masa na tafi sai wata rana." Husna ta ƙarasa maganar hawaye na cika mata ido, maganganun ta kuma suka bawa Aramma mamaki tare da jefa shi cikin kokonto, Husna bata tsaya jin me Aramma zaice ba ta juya ta shige cikin motar a baya ta zauna tana ɗagawa Aramma hannu Abdulyassar ya rufe ƙofar Aunty Mansura ta shiga gaba yaja motar suka tafi, Husna ta juyo baya tana dagawa Aramma hannu yana tsaye yana kallon su yana Murmushi har suka karya kwana. *****Alokacin da motar su Husna ke daidaita zaman ta akan titi dan barin garin a dai-dai lokacin kuma mahaukacin yayanta na zaune a ƙasan bishiya can gaban rumfar Bahari bai daɗe da zuwa wajen ba, yana zama kuma ko minti biyar baiyi a wajen ba, mai mota ya sauke Bahari da jarkokin fetir ɗin sa daya siyo daga Doko, haka ta bayan shi motar su Husna tazo ta wuce, akace wai rashin sani wanda yafi dare duhu, yadda baƙin gilashin motar ke sawa na waje baya iya gane na ciki haka Husna dake barin garin su Mahaifin ta bata ganshi ba har suka yi nesa da garin. A fili murna da wani irin farin cikin barin garin ne kwance akan fuskarta, ata can ƙasan zuciyar ta kuma wani irin kunci da rashin jin daɗi take ji duk lokacin da ta tuno da ta tafi ta bar shi a ciki garin da suke masa kallon mahaukaci sai taji kamar ta koma, sanda kuma ta dena hango garin su ta cikin gilashin idanun ta sai taji jikin ta ya saki wata irin kewa da damuwa na rufe gabobin jikin ta a hankali ta koma ta zauna tana sauke ajiyar zuciya. ........Yana zaune a kasan bishiyar Dan Hajja ya zo ya wuce shi da sauri kamar zai tashi sama waya manne a kunnen sa yayi wajen Bahari dake zubawa headmaster mai a mota yana faɗin. "Eh ina nan zaku ganni ta ƙarshen tasha ɗan gaba dame saida fetir bumburu tu." "Eh yawwa daga shi saini shagona ne babban shago duk tashar, zaku ganshi ginin kwangiri, yawwa sai kunzo." Ya sauke wayar yana kashe ta yace "Bahari yimin full tank a mashin ɗina, yanzu Gambo zai kawo maka." Bahari ya gyaɗa masa kai yaci gaba da zuba fetir ɗin. Dan Hajja kuma ya juya yana sake daga wata wayar yana zaune yazo ya sake wuce sa kaɗan sai kuma ya tsaya yana danna wayar shi Gambo ya iso inda yake tsaye yace "Yawwa ka kaiwa Bahari mashin ɗin yamin full tank, abokan aikina ne zasu zo oga ne zai bada sako a kawo min kasan yana gaf da sauka saura ƴan kwanaki, to sai ɗazu ya sanar mana zamu ɗan haɗu da wani yaron shi akwai sakon da zai bamu kan ya diro, na kira íla ma yace min tare zasu taho." Gambo ya buga ihu yana faɗin "Yau muna da kuɗi Malam kut**** du*** eeee.....yau zamu baje ta." "Hhhhh." Ɗan Hajja yayi dariyar nishaɗi. "Ai zuwan Oga alkhairi ne tun kafin yazo sai yasa an jiƙa mana maƙoshi da Naira." Ɗan Hajja ya faɗa suka tafa da Gambo yayi shagon shi, shi kuma Gambo ya tafi wajen Bahari. Ba'a dade da fitowa daga sallar azahar ba wata mota ƴar ƙurƙura ta tsaya a tsakiyar tasha, mutane huɗu dake bayan motar suka fara diddirgowa ƙasa kafin mutum biyun gaba su fito, gaba ɗayan su sun yi futu-futu da ƙura ƙafafun su sunyi fururu haka kawunan duka ƙafafun wandunan su a dage suke, rigunan jikin su kuwa duk sun koɗe da alama sunji jiki, slifas ne a kafafunsu harda wanda nasu ya tsinke suka daure da leda kana ganin su kaga ma'aikata da alama daga wajen aiki suke suka tsaya anan. A rumfar shagon Sunday suka zazzauna Chioma ce kaɗai a cikin shagon, ruwa me sanyi suka siya pure-water suka sha da lemo, sun ɗan jima a zaune a wajen kafin suka tashi Mutum ɗaya a cikin su ya tuka motar sauran kuma suka biyo shi a ƙafa a famfon masallaci suka tsaya suna wanke jikin su wanda yaja motar kuma ya tsaya a wajen Bahari ya fito yana kallon gaban shi yace "malam zoka ƙaramin mai rabin galon a motar nan." Ya ciro kuɗi yana tambayar shi nawa ne, Buhari ya faɗa masa kuɗin ya miƙa masa sannan yace yana zuwa kanya gama saka masa man, sai kuma y juya wajen abokan tafiyarsa yace "Kai in kun gama ku same ni shagon can na gaba naga kamar yana awu, bari na duba ko zan samu Ƙaura a wajen sa." Ya faɗa yana ɗaga wa abokan tafiyarsa hannu yayi gaba yabar motar a wajen Bahari. Shagon Dan Hajja ya wuce yana ɗan dube dube, a waje ya tsaya Dan Hajja ya fito suna magana sauran mutum biyar ɗin suka taho wajen suna tafe suna hira. Dukan su babu wanda ya zauna wanda ya iso wajen na karshe ne ya dubi Dan Hajja yana ƙarewa wajen kallo yace "ɗan hanya ne." Dan Hajja ya kalle shi da sauri sai kuma yayi murmushi yace "ba hanya." Sauran suka kwashe da dariyar gane su da yayi, wani mai ɗan jiki a cikin su da sai yanzu yayi magana yace "zaka karɓi saƙon ka yanzu lallai kana kwashe wa abokin hanya." Yana faɗin haka wanda ya fara zuwa wajen da farko ya ciro wani emblop mai ruwan ƙasa ya miƙa masa, ya karɓa ya bawa Dan Hajja sai kuma yaɗan bugi kafaɗun sa ƙasa ƙasa yace "kana ƙoƙari, ka huta da wannan sai mun haɗu gani na biyu." Sai kuma yaɗan yi masa alama da hannu yace "ka kula." Ya juya zai bar wajen ke nan ya ga mahaukaci zaune a ƙasan bishiyar da suke tsaye ya riƙe Sandar hannun sa ya cakata a kasa ƙafarsa ɗaya a miƙe daya a tanƙwashe da sauri ya juya ya kalli ɗan Hajja yace "wannan kuma daga ina?" Ɗan Hajja yayi murmushi yace "ai mahaukaci ne yaɗan kwana biyu da zuwa nan." "Kai amma baka da hankali ko? Ban faɗa muku duk wanda yazo gari inya wuce 24 hours ku faɗa min ba?" Kafin Dan Hajja ya sake magana wanda yayi maganar har yayi gaba da sauri da nufin yabar wajen yana isowa inda Mahaukacin ke zaune kawai sai gani yayi ya miƙa hannun ya tare masa hanya, sauran abokan tafiyar da suke kamar yan rakiya a wajen mutumin daya tarewa hanyar da dantsen hannun sa sai suka taso masa suna fadin. "Kai matsa mana a hanya mu wuce a ina ma kuka samu mahaukaci irin wannan?." Wanda aka tarewa hanyar kuwa saida yaji wani mugun abu ya daki zuciyar sa dan babu abinda ya faɗo masa rai a lokacin sai kashe din da bokansa yayi masa, akan zuwa garin wannan nema yasa yayi badda kama yazo kuma a lokacin da bashi ya faɗawa yaran saba, amma tsabar rashin bada kai sai ya dubi Dan Hajja yace "kai zoka korar mana shi mu wuce." Yanzu da asalin muryar sa yayi wa ɗan Hajja da mamakin mahaukacin ya cikawa zuciya magana, jin muryar mutumin ta asali kuma ɗan Hajja baisan sanda rudewa

Chapter 30 of 31