Share this page
babu labarin ta, nan fa hankali sa yayi asalin tashi ya kasa zaune ya kasa tsaye, daga tasha zuwa gidan su kuwa ba zai iya lissafa sau nawa yaje ya koma ba. Duk abinda yake faruwa dashi kuma Bahari na ankare ya zuba masa ido ne kawai yana kallon ikon Allah, mamakin Mahaukacin ya kashe Bahari har saida ya tambayi kansa a sarari yace "wai dama ana haka?" Duk da shi kansa Baharin rashin ganin Husna kwana ɗaya da wuni biyu ya sashi cikin tunanin san sanin halin da take ciki tunda yake a garin bai taɓa kwana ko wuni guda cur ba tare da yaga giftawar Husna ba, magana ta gaskiya shi kansa rashin ganin ta ya dame shi amma sai mamakin ganin zagayen da mahaukacin yayan ta ke yi tsakanin tasha da gidan su ya kashe sa a zaune, gaba ɗaya saiya rasa wani tunani ya kamata yayi. Indo na fitowa saida ƙosan yamma da sauri Bahari ya fara ƙwala mata kira tana zuwa inda yake ya tsare ta da tambaya. "wai Indo ina ƙawar ki Ma'u? kwana biyu shiru bana ganin ta kodai tayi tafiya ne?" Bahari yayi wa Indo tambayar yana duban ta cikin zaƙuwar sanjin abinda zata ce. "Lah Ma'u, wallahi bata da lafiya jiya da naje dubata tana ta amai bakaga yadda tayi ba, masassara (zazzaɓi) ce tayi mata mugun bugu." Cikin jimamin halin rashin lafiyar da Husna ke ciki Bahari yace "Subhanallahi kai Allah ya bata lafiya." Kamar yayi shiru ya danne tunanin dake ranshi sai kuma wata zuciyar ta hana sa tare da karfafa masa gwiwa, ya sake dubam Indo yace "dan Allah anjima ko zaki raka ni gidan su na duba ta." Indo ta ɗaga masa kai, ya koma wajen saida fetir ɗin sa ya zauna yana kada kafa wani tunani ya faɗo masa rai, tunanin yasa yadan buɗe ido da sauri sai kuma yayi wani cikakken murmushi haɗe da dariya ya ɗaga kai sama ya kalli sararin samaniya kamar me lissafa adadin gajimare yana kunshe dariyar sa, da wani irin nishadi ya sauke kansa yana shafa gemun sa a fili yace "da yace baya ji." Ya faɗa da nishadi kamar wani sakarai a karo na biyu ya saki murmushi yana dukan ɗaya tafin hannun sa ya koma ya zauna da kyau yana duban mutanen cikin tashar ɗaya bayan ɗaya har yanzu murmushi bai gushe daga saman fuskar shiba yadda kasan wanda aka yiwa albashir da farar haihuwa. _masu karatu nace ba, wai me kuke tunanin yasa Bahari irin wannan sambatu da farin ciki haka?🤔👇🏻_ *Yau da daddare mu haɗu a comment section 🤓😅* Bayan Sallar Magarba Indo ta raka Bahari duba Husna, sanda suka je Aramma na masallaci dan baya dawowa gida sai bayan sallar isha'i saiya shigo gidan gaba ɗaya, Dije najin anzo duba Ma'u tace koma waye ya shigo jikin ta na rawa dan ta ɗauka Dan Hajja ne ya zo dubiya saida Bahari ya shigo taga bashi bane. Ramma har kewayen su ta raka Bahari Indo na biye dasu, Husna na zaune akan taburmar da Ramma ta shimfiɗa musu ta jingina bayan ta da garu kanta babu ɗankwali ta juya kai gefe tana kallon waje guda kamar me tunani Bahari yayi Sallama Zahara na daga ƙofar ɗakin ta ta amsa tana sake kunna fitila dan daga waye da kyau. Husna na ganin Bahari taja kallabinta ta rufa a saman kitson kanta daya fara tsufa. "Sannu Husnah, ashe baki da lafiya shi yasa muka ji shiru? Wallahi sai ɗazu Indo take faɗa min, kai sannu Allah ya baki lafiya." Bahari ya faɗa yana duban ta duk tayi wani fayau da ita ta faɗa lokaci ɗaya, wuyan ta da jelar kitson ta ya sakko kai ya sake tsayi wasu ƙasusuwa suka ɗan bayyana alamun tayi rama. Kai ta ɗagawa Bahari tana murmushi, Ramma ta amsa da "Amin an gode." Bai wani jima ba ya tashi zai tafi ya aje mata dubu biyu akan taburmar da take zaune yace "kya siyi wani abu Allah ya ƙara lafiya." "A'a kuma harda wahala? angode Allah ya bada lada." Ramma ta faɗa, Husna ta motsa bakin ta a hankali tace "nagde Bahari." Kai ya jinjina ba tare daya sake duban inda take ba ya fice daga wajen yana fita Lirwanu na shigowa yaɗan tsaya suka gaisa ya tambaye shi mai jiki bai kuma jira amsawar saba ya wuce sa shi kuma Lirwanu ya shiga cikin lungun nasa yana kallon bayan Bahari. Ramma ta ɗauki kuɗin tace "Alhamdulillah Ma'u gobe saina rakaki Doko kiga likita akwai kuɗi a hannuna saimu hada da wannan zai isa, kinga zazzaɓin nan da ya sauka yake sake hawa maganin da Aramma ya siya miki kuma in kika sha na dare ya ƙare." "Kema dai Ramma da fi'ilin tsiya kike banda haka duk zazzaɓin da yaran gidan nan ke yi naga dai magani suke sha har su warke, shi ne zakice wani zaki ɗauke ta kuje asibiti sai kace mai ciwon mutuwa." Zahara ta faɗa tana duban Lirwanu daya shigo, Husna kuwa ƙala bata ce ba ta koma ta kwanta. Lirwanu ya tambayi zancen me ake Zahara da dama dan yayi magana tayi zancen tsaram ta fara maida masa yadda maganar take, shi kuwa babu kunya babu tsoron Allah ya miƙawa Ramma hannu. "Bani kuɗin nan, dama akwai abin da zanyi da kuɗi neman su ma na shigo yanzu, tunda Allah ya kawo su cikin sauƙi kuma shi ke nan ta kwana gidan sauƙi bani su nan." Yayi maganar yana miƙawa Ramma hannu. "Haba Lirwanu Ma'u fa da zazzaɓin nan take kwana take wuni, wallahi koya sauka saiya dawo, amma in muk......." "Nace ki bani kuɗin ba tsari nace kimin ba ƴar Iya." Lirwanu ya katse Ramma a faɗace, zuciyar ta babu daɗi ta miƙa masa kuɗin yasa hannu ya karɓe ya jefa su aljihu ya fice daga gidan gaba ɗaya, Zahara kuwa zuciyar ta tayi fari fes dama burin ta ke nan ya karɓe kuɗin, kuma ya amshe. Bahari da Indo kuwa suna fitowa daga gidan su Husna suka ga Mahaukacin yayan ta tsaye a jikin bishiyar Kofar gidan yana kallon ƙofar fitowa kamar me jiran sallahu. "Turus." Bahari ya ɗan ja da baya ya tsaya saboda mamakin ganin sa a wajen sai kuma ya ɗan basar ya dubi Indo yana gyaɗa kai yace "taɓ Allah mai iko Indo dubi mahaukacin Ma'u a tsaye, wallahi da alama ita yake nema yo Mahaukaci mafa ke nan yasan me basa bare mai hankali?" Bahari ya dire zancen da sigar mamaki, Indo tace "kasan jiya ina zuwa duba Ma'u tana rawar sanyi amma saida ta tambaye ni shi, ita ko tsoron sa ma bata ji." Bahari ya ɗan matsa inda yake tsaye yace "to Ma'u dai bata da lafiya saika juya kabar nan wajen, kazo ka tsaya musu a ƙofar gida." "Bahari wai kaima maganar kake masa irin na Ma'u sai kace wani me hankali?" Maganar Indo ta katse Bahari, ya juyo yaga ta riƙe baki cikin mamaki saida Bahari yayi Murmushi sannan yace "yo tunda yasan ya nemi me bashi abinci ai kuwa yaci ya gane zance na." Shi dai har suka yi maganar su suka wuce sa bai ɗago ya dubi kowa a cikin suba, Saida suka jima da tafiya sannan ya juya yabar wajen. Bai daɗe da tafiya ba kuma Dan Hajja da Gambo suka shiga gidan riƙe da ƙatuwar leda cike da lemo da ayaba. Dije najin Sallamar Dan Hajja ta fito dan dama tasan tunda ta aika a faɗa masa Ma'u babu lafiya dole zai zo ya dubiya shi yasa ma ɗazu da taji anzo dubiyarta ta ɗauka shi ne. "Maraba da jikan arziki lalle marhaban ku ƙaraso nan tana wajen su bari a kirata." Dije ta faɗa tana basu hanya suka shige lungun ta. "Ina wuni Dije?" Su Dan Hajja suka fara gaida ita, ta amsa musu bakin ta buɗe, sai kuma ta miƙe tana gyara ɗaurin zani tace "Bari a kira maka ita saiku gaisa." Ta fice kiran Husna su kuma suka Zauna zaman jiran dawowa ta. "Muguwa bazaki tashi muje ba ƴar baƙin ciki, yaron kirki mai rufun asiri yana sonki kinawa kanki da mutane bakin ciki, duk garin nan daga manya har Samari irin sa faɗa min mai rufun asirin shi, ko wacce yarinya so take ya taya ta amma ke yace yana sonki shi ne zakiyi wa mutane iya shege, kin tashi ko saina hau kanki da daren nan." Dije keta fama da Husna tana zuba mata masifar ta tashi suje wajen su Dan Hajja su duba ta amma fir taƙi tashi, Ramma tasa baki ma duk tayi banza ta rabu dasu. Zahara ce ta dubi Dije tace "kema fa Iya kinsan taurin kan Ma'u in bata so yin abuba bata yinsa, to me zai hana kawai kice suzo nan ɗin saisu suba ta." "Kaji ƴar Albarka ni ai banyi wannan tunanin ba, shegiya ƴar baƙin ciki zata yimin buƙulun abinda zan samu bari naje nazo dasu." Dije ta faɗa tana juyawa dingis dingis ta fita daga lungun. Bata jima da fita ba sai gasu sun dawo da su ɗan Hajja tana gaba suna binta a baya, a gefan taburmar da Husna ke kwance suka zauna, Gambo ne ya fara mata sannu tayi masa banza kamar wacce ke bacci, haushi ya sake ƙume Dije dan tasan ba bacci take ba. "Sannu Ma'u, Allah ya baki lafiya." Ɗan Hajja ya faɗa yana kallon ta shi ɗin ma banza tayi masa sai Ramma ce ta amsa da "Amin an gode." Dije kuwa cewa tayi "kunsan jikin nata ne babu daɗi inaga bacci tayi dan ɗazu ma da nazo kiran ta kasa tashi tayi, kai ai Ma'u najin jiki, wannan zazzaɓi ba ƙaramin kamu yayi mata ba." Ramma ta saki baki tana kallon Dije na yanko ƙarya Zahara kuwa murmushi tayi dan tasan wannan abun da Dije ke yi da biyu aljihun ta take gyarawa, dan haka ita ma ta taya ta da cewa. "Wallahi kuwa Iya Ma'u na jin jiki Allah dai ya tashi kafaɗun ta." Zahara ta faɗa da tata manufar kunshe a ƙasan rai. Ɗan Hajja ya dubi Dije yana karkace wa ya ciro ƴan ɗari biyar biyar sababbi saida ya irga guda goma sannan ya ajiye wa Dije a gaban ta yana faɗin "gashi a kaita asibiti ai batayi ta zama da ciwo ba, mu zamu tafi sai goben in kun shirya zuwa asibitin Gambo sai ya zo ya kaiku taga likita." Dan Hajja ya faɗa yana miƙewa tsaye Gambo ya ajiye ledar hannun shi yana faɗin "Allah ya bata lafiya." "Kaga yaron arziki kuma harda kuɗi bayan wannan wahalar da ake tayi damu? An gode an doge Allah yaji kan Malma Mudi (Babansa), ai da yake Aramma ma ya siya mata magani kasan masassara ce da naci." Dije ta faɗa tana raka su, suna tafe tana zuba wa Dan Hajja addu'a, saida suka fice daga gidan sannan ta dawo wajen su Ramma. Ma'u ke dai akwai muguwa ƴar baƙin ciki, da har zaki jamin asara na rasa wannan kuɗin badan shawarar Zahara ba." Dije ta faɗa tana zubawa Husna harara sai kuma ta dubi Zahara tace "Zahara dubi abun arziki yaushe raban na kama farare irin wannan ai tun Salisu na raye." Sai kuma "fesssss..." Ta bace majina tana tsane hawaye tace "Allah yaji kanka Salisu." Da sauri Zahara ta amsa da "Amin Amin Iya." Ɗari biyar Dije ta cire a cikin kuɗin da ɗan Hajja ya bata ta mika wa Zahara. "Ungo wannan kema kisa albarka." Zahara tayi caraf ta amshe tana zuba godiya da banbaɗancin kwaɗayi. "Ke kuma da yar baƙin cikin naki sai kuci kanku sisi na baza ku gani ba wallahi, tunda ai iskancin da Ma'u ke yi mini wani ke kike zigata." Dije ta faɗa tana kallon Ramma data zuba musu Ido tana kallon ikon Allah, Husna kuwa ko inda Dije da kuɗin suke bata duba. Ledar da Dan Hajja ya kawo Dije ta buɗe ta cire lemo da ayaba guda biyu biyu ta bawa Ramma Zahara kuma ta bata lemo ɗaya ayaba ɗaya, ta kulle sauran ta tafi dasu. Tana fita daga lungun Zahara tace "kai gaskiya Iya badai san kaiba, yanzu duk yawan lemo da ayabar nan da aka kawo ta rasa nawa zata bamu sai ɗai ɗai." Ramma da Husna suka yi banza da ita kamar basu ji abinda tace ba... _*WRITING.....✍🏻*_ *_MUTUWAR AURE.....!_* _(Ƙaddarar wasu ƴaƴan)_ *_Kanawa ne👌🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ _BOOK 1_ *_FREE PAGES_* ________________ *_WHATSAPP GROUP👇🏻_* https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3?mode=gi_t https://wa.me/+2348064789370 _________________ _EPISODE 22_ Yauma haka ya gama zagayen shi a Dandali babu Husna babu dalilin ta, har kowa ya watse yana tsaye yana kallo. Washegari da safe wajen ƙarfe goma saiga Indo da matar Sunday a gidan, da gwarin Hausar ta suka gaisa da matan gidan sannan Indo ta cewa Ramma. "Naje siyan magi Sunday ke tambaya ta Ma'u kwana biyu nace bata da lafiya shi ne yace Matar shi tazo ta duba ta." Duka matan inuwar sai suka ƙara bin Matar da kallo dan basu taɓa ganin taba suna dai ji a bakin yara suna cewa Sunday ya kawo matar sa amma basu taɓa ganin taba sai yau. Ramma tace "Allah Sarki muje to tana ciki yanzu na baro ta zata shiga wanka." Tayi maganar tana miƙewa Indo da matar Sunday suka bita a baya. Suna tafiya matan inuwar suka kafa gulmar ta daga masu cewa farin ta yayi yawa sai masu cewa tayi ja da yawa. A bakin gado suka samu Husna harta fito daga wankan tasa kaya tana shafa mai. "Ga bakuwa nan Ma'u tazo duba ki." Ramma ta faɗa tana nuna mata matar Sunday dake bin ta da kallo, duk sai taga ta rame idanun ta sun sake fitowa waje bakin ta ya bushe sosai kamar mai jin ƙishirwa. Husna na murmushi suka gaisa da matar Sunday cikin harshen Ingilishi dan bata wani iya Hausa ba, sai suka zama abun kallo a wajen Ramma da Indo. "My friend kinajin jiki fa amma inkin yarda zan iya duba lafiyar ki, dan ni Likita ce a garin mu." Husna tace "da gaske?" Chioma ta ɗaga mata kai tana murmushi, Husna ta dubi Ramma tayi mata bayanin abinda suke faɗa. "To in kina ganin babu matsala ta duba kin mana, Allah yasa dai kuɗin wajen mu ya isa." Husna tayi shiru tana tunani, ita kanta tana so a duba ta saboda ciwon kan dake damun ta ga zazzaɓin da yana sauka saiya sake dawowa. "to amma in kuɗin wajen su bai kai bafa?" Wata zuciyar tace "saita fara faɗa muku kuɗin kanta baki magani." Da wannan shawarar ta zuciyar ta ta yarda ta dubi Matar Sunday tace "ki dubani sai muji nawa ne kuɗin." Murmushi Chioma tayi wa Husna har saida fararen haƙoran ta suka bayyana sannan tace "bari muga menene matsalar ki sannan sai muyi maganar kuɗi daga baya." Take ta fara duba ta kamar wanda ta zo da shirin ta ta zura hannu a aljihu ta fito da wani farin abu mai nombobi ajiki, a jikin rigar Husna tasa abun ta saitin ƙirjin ta saida yayi wasu mintina sanna ta cire ta duba jikin abun, ta kama hannun Husna ta duba ta buɗe idanun tama ta duba sosai. "Zan je na dakko magani saina dawo." Ta faɗa tana tashi tsaye, Husna ta gyaɗa mata kai suka fice ita da Indo. Husna Tayiwa Ramma bayanin abinda tace. "To bari naje mu ƙarasa kwashe surfan can kanta dawo." Ramma ta fita daga ɗakin. Sha biyu saura matar Sunday ta dawo, wannan karon ita kaɗai ta dawo hannun ta riƙe da farar leda me ɗan girma. Abinka da yare yanzu ma saida ta sake gaida matan inuwar sannan Ramma ta raka ta ɗakin ta wajen Husna. Zazzabi harya sake rufe ta, tana rawar sanyi suka shigo ɗakin. "Heeee sorry my friend?" Matar Sunday ta faɗa tana fiffito da kayan ledar tarkacen Allurai ne magunguna da ledar ruwa guda biyu. Ramma ta zauna a bakin gado tana kallon yadda matar ke neman jijiyar da zata ɗaura wa Husna ruwa. Cikin kankanin lokaci tasa mata ruwan da Allurai tayi mata wasu a jiki, tana saka mata ruwan tana mata sannu, cikin mintunan da basu wuce biyar ba bacci mai nauyi ya ɗauke Husna saboda alluran data saka mata a ruwan harda na bacci. Magungunan data kawo ta bawa Ramma da gwarin Hausar ta tace "zan zauna in ruwan shi ya ƙare zana saka mishi wani." Ramma ta karɓi maganin tana mata godiya tace bari taje waje tana zuwa. Ramma na dawowa inuwar ta tadda Dije dawowar ta ke nan daga fitar da tayi tace "me kuke kullawa ne a ciki? Yanzu nake jin labarin Matar Sunday na cikin ɗakin ki." Ramma ta dubi su Zahara a ranta ta jinjina wa munafuncin su sai kuma yace "Eh tazo duba jikin Ma'u ne sai kuma tasa mata ƙarin ruwa." Ramma ta faɗa tana zama danta ƙarasa busar hatsin da take, Dije tace "ban gane ruwa ba? Saka ruwa kamar a asibiti." Sai kuma tayi hanyar ɗakin Ramma dan ganewa idan ta dahir. Chioma na zaune tana jire Husna Dije ta bankada labulan ɗakin, ta kalli farar matar zaune tana danna waya Husna kuma na bacci ɗaure da ƙarin ruwa. "Sannu Mama." Chioma ta gaishe da Dije. "Sannu ƴar nan, dama likita ce ke?" Chioma ta bita da Ido dan bata gane abinda take faɗa ba. "Hausa babu Mama." Chioma ta faɗa wa Dije haka a gwarance. "Ikon Allah ke kuma Hausar ma bakya ji ke nan?" Dije ta faɗa tana sakin labunlan ta juya. Saboda tsabar sheda da sunan dubiya saida kowa ya zo dakin Ramma a cikin matan inuwar ya leƙa ɗakin Ramma yaga abunda ake yi. Chioma tana zaune ruwan ya ƙare ta sake sa mata ɗayan, sai wajen ƙarfe biyu Chioma ta baro gidan bayan ta cire wa Husna ƙarin ruwan, da kwatance ta nuna wa Ramma in Husna ta tashi daga bacci tazo. Ramma nason tayi mata maganar kuɗi amma Chioma babu Hausa ita kuma ba turanci, kawai saita bari in Husna ta tashi taje taji nawa ne kuɗin ta. Ramma ta gane abinda take nufi saita ɗaga mata kai tayi mata godiya. Husna bata tashi daga baccin ba sai bayan sallar la'asar, lokacin da ta tashi taji jikin ta yayi mata daɗi babu wani ciwo da take ji yanzu sai rashin kwarin jiki, dan fayau take jinta kamar iska. Saida tayi wanka tasa kaya sannan Ramma ta faɗa mata yadda suka yi da Chioma. A hankali Husna ta fito daga gidan su ta kama hanyar tasha dan zuwa shagon Sunday taji nawa ne kuɗin maganin da Chioma tayi mata, tana tafe tana addu'ar Allah yasa kuɗin wajen su ya isa su biya kuɗin maganin nata. Chioma kaɗai Husna ta samu a cikin shago suka gaisa Chioma nata mata murmushi da jero mata sannu, Husna ta mayar mata da martanin murmushin ta sannan tace "thank you Mrs Sunday, nawa ne kuɗin ki? Baki dafa mana ba ɗazu." Chioma tayi murmushi tana kallon Husna sai kuma ta dafa kafaɗun ta tace "kin manta randa muka fara haɗuwa nace miki mu ƙawaye ne?" Husna ta ɗaga idanun ta da suka sake girma saboda faɗawar da suka yi ta dubi Chioma cikin san ƙarin bayani akan abinda tace. Chioma ta gane abinda take nufi sai ta sake sakar mata murmushi tace "Inason cewa komai kikaga nayi miki nayi miki shi ne kyauta saboda ƙawancen mu." Husna ta buɗe baki da mamaki tana duban Chioma dan kowa a garin nan yasan Sunday mayan kuɗi ne baya kyauta bare sakada amma shi ne yanzu matar shi zatayi mata magani kyauta. "Karki damu da gaske nake yi kyauta nayi miki, ina miki fatan sake samun lafiya." Chioma ta sake faɗa. Husna ta gyaɗa kai tana murmushi zuciyar ta cike da mamakin ta a sanyaye tace "nagde sosai Mrs Sunday, Allah ya biyaki." "Karki damu." Chioma ta faɗa, saida Chioma ta yiwa mata bayanin yadda zata sha maganin ta sannan ta baro shagon cikin juyayi da dunbin mamakin abinda Chioma tayi mata. A hanyar Husna ta komawa gida tayi ta wai waye a cikin tashar ko zata ga yayan ta, amma harta wuce rumfar Bahari da taga wajen a rufe ta wuce ta ɗan Hajja bata ganshi ba, tana tafe tana tunanin ko ina yake kwana biyu nan tayi kewar sa, sai kuma tayi murmushi tana sake duban yanayin garin da yamma tayi sosai, tana jin dokin dare yayi taje dandalin. A ranta tace "Allah yasa yau kazo Yaya." Sanda Husna ta faɗawa Ramma yadda suka yi da Chioma sai Ramma ta cika da mamaki tayi ta jera mata godiya dan sosai taji daɗin abinda tayi musu dan dama ba wani kuɗin kirki bane a hannun su. Ana yin sallar isha'i Husna cikin sauri da doki ta cewa Ramma ta tafi dandali, Ramma ta dube ta sanda take saka Hijabin ta tace "amma Ma'u dakin bari kin sake warware wa, daga jin sauƙin ki yau kuma saiki tafi dandali." Husna tayi murmushi tace "Ramma nafa samu sauƙi, zan iya zuwa." Tayi maganar tana fita daga ɗakin da sauri dan Allah Allah take ta isa Dandalin. Indo na tsakiyar ƴan mata ana shirin fara yekuwar saka Asure ta hango Husna na tahowa, fitowa tayi daga tsakiyar ƴan matan tayi wajen ta tana ƙwala mata kira. "Aha Ma'u jiki yayi kyau, dama fa yanzu nake jira mu gama saka ranar Asure sai naje na dubaki ashe ma kinji sauƙi." Husna ta dubi Indo fuskar ta a sake tace "naji sauƙi." Indo ta kama hannun ta tana janta tace "zo muje kinga har za'a fara yekuwar, kinsan yau zamu saka ranar bikin Asure." Husna taɗan yamutsa fuska tana cire hannun ta daga na Indo tace "wai har lokacin saka Asuren yayi? Lallai bana da wuri za'a yishi." "Eh yayi kinsan hatsi ya riga ya zo gida tuni shi yasa, zo muje karsu fara babu mu, kinga sai ki hau dokin ki dama Ummai ce ta hau naki tunda bakya nan kuma dole saida mu za'a saka tunda mune ƴan Auran baɗi." Indo tayi maganar tana jan Husna dan su isa wajen, Husna kuwa saita coge tana faɗin. "Jeki kawai ni bazan jeba inkun saka naji." Indo ta juya ta kalli Husna kamar zata yi magana sai kuma tayi cikin Dankalin da gudu soboda jin har sun fara shewar saka Asuren bata nan." Husna kuwa saita juya ta tafi inda suke zama zuciyar ta cike da fatan Yayan ta yazo, abinda bata sani ba shine daga fitowar ta daga gida har zuwa tsayawar ta da Indo duka akan idanun shi ya faru. Tana isa inda suke zaman ta cika da farin ciki da wani irin jin daɗin ganin shi a zaune akan ican da suke zama riƙe da sandar shi da baya rabo da ita yana bubbaga ta a ƙasa kanshi na sunkuye, daɗi ya cika zuciyar Husna ta washe masa baki tana kallon sa tace "Lah Yaya yau kazo." Ta faɗa da murna, ya ɗago kanshi kamar mai jiran isowar ta wajen ya kalle ta ta cikin rufaffun Idanun sa, Husna kuwa saita cire takalman ta ta saka a gaban shi ta zauna akai tallafe da kumatun ta tana ƙarewa fuskar shi data cika da gashi kallo cikin jin daɗin ganin sa tace "Yayaaaaa." Ta kira shi a sakalce. Idanun sa ya buɗe gaba ɗaya ya zuba su akan Husna ta cikin hasken farin watan daya ratso ta inda suke zaune yake ƙare mata kallo, duk sai yaga ta rame masa fuskar ta tayi kuyat, hakan saiya ƙarawa Idanun ta girma da

Chapter 24 of 31