Share this page
zaune ta ci gaba dayin kukan, Aramma yayi shiru yana sauraren ta, tausayin ta na tsarga masa zuciya. Dije kuwa haushin ta ya sake cika ta. "Yi hakuri bar kukan haka taso muyi magana kinji Asma'ullahi?" Aramma yayi maganar cikin sanyi rai yana ɗago ta ta zauna akan gadon da kyau. Da kanshi ya share mata hawaye tana haɗiyar zuciya ya fara mata magana cikin iya zance da kwantar da hankali. "Kiyi haƙuri Asma'ullahi, kiyi hakuri kinji? Komai da kike gani a duniyar nan yana da farko da kuma ƙarshe amma fa banda Allah da ikon shi, ke taki jarrabawar ce a haka, kuma in sha Allahu zaki ci ribarta a gaba. Ki kwantar da hankalin ki, Baban ki yaƙi yayi miki sallama ne dan baya son ganin kukan ki, amma zai rinƙa zuwa yana ganin ki akai akai, kuma kinga ai yace yana gama gina muku gida zai zo ya ɗauke ki ku tafi ko? Ko kinfi so ki bishi ku koma Abba ya sake dukan ki?" Aramma ya jerowa Husna maganganun duk da yasan wasu ba lallai ta gane me yake nufi ba amma yasan dole zata fahimci wasu. A tunanin Aramma ke nan, Husna tasan sunan ƙaddara da jarrabawa saidai bata san asalin ma'anar su a zahiri ba, sai yau, yanzu da Aramma ya kira halin da take ciki da ƙaddara sai ƙwaƙwalwa da tunanin ta ya hasaso mata kalmar a zahirin ta. Haka Aramma yayi ta lallaɓa ta da maganganu masu daɗi har tayi shiru. "Yawwa kullum in kinyi Sallah kina wa Baban ki addu'a ya samu ya gama yi muku aikin gidan ku da wuri, dan yazo ku tafi kinji Asma'ullahi?" "To." Ta amsa wa Aramma tana sake share idanun ta. Suna haka Salisu yayi sallama ya shigo, dawowarsa ke nan daga kasuwa dan yau Talata yaje cin Kasuwar talatar Kanya. Saida suka gaisa da Aramma da Dije sannan ya kula da Husna yace "A'a Asma'u yaushe suka zo?" Ya tambaya yana gyara zaman shi. Aramma ne ya bashi amsa da cewa "ɗazu Abdullahi ya kawo ta nan." Sai kuam ya kashe duk abinda ya faru ya fada masa da rigimar da take yanzu na tafiyar Baban ta.... _*WRITING.....✍🏻*_ *_MUTUWAR AURE.....!_* _(Ƙaddarar wasu ƴaƴan)_ *_Kanawa ne👌🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ _BOOK 1_ *_FREE PAGES_* ________________ *_WHATSAPP GROUP👇🏻_* https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3?mode=gi_t https://wa.me/+2348064789370 _________________ _EPISODE 16_ Salisu yayi shiru yana jinjina abinda ya faru, da yake shi mutum ne mai son yara ga kuma sanyi hali da tausayi saɓanin Lirwanu saiya miƙa wa Husna hannu yana murmushi yace "zo mu gaisa kinji." Tasowa tayi tazo wajen shi, ya shafa kanta yana kallon idanunta da launin su ya canja yace "Ki daina kuka kinji, nima ai Baban kine ko?" Ta ɗaga masa kai yaci gaba da faɗin. "Da kaina zan kaiki yana gama ginin gidan ku kinji ko." Yanzu ma kai ta sake daga masa.Ya tambaye ta taci tuwo tace a'a, kawai saiya miƙe riƙe da hannun ta suka fice daga ɗakin. Aramma ya bi bayan su da Murmushi, shi yasan ko a cikin ƴaƴan shi Salisu da Abdullahi daban suke, su mutane ne masu hakuri da sanin ya kamata ga jinkan iyali da tausayi, saɓanin Lirwanu da saidai yace Allah ya shirye sa kawai. Dije kuwa baki ta taɓe dan bataga amfanin wani lallaɓa tan da suke ba a fili tace "banda ɓata yaro shi kuka ai aiki ne inta gaji saita dena." Aramma dai bai kulata ba ya fara cin tuwon shi. Salisu kai tsaye wajen Isuhu mai shayi ya kaita ya siya mata indomi da soyayyen ƙwai, tana riƙe da ledar suka dawo gida yana ta janta da hira, tadan sake dashi kuwa ba kamar ɗazu ba, yanzu ma wajen Dije suka koma ta zauna a kusa da Aramma yana tsokanar ta tana cin indomin. Ɗan kaɗan taci tace ta koshi yace ta wanke hannun ta tazo ta kwanta. "Ni bazan kwana a nan ba." Husna ta faɗa tana kallon Aramma, Dije tace "nima bana neman ki. Salisu kuwa dariya yayi yace "to zomuje wajena saiki kwana wajen su Indo dama ai kawar kice ko?." Ai kuwa shi tabi ya kaita har ɗakin su Indo yace wa Indo "ga kawar ki nan ku kwanta tare wajen ai zai ishe ku ko?" Tace "eh." Yana fita Indo ta matsa mata tace "ki kwanta anan Sa'a bata iya kwanciya ba kan gari ya waye saita yiwa mutum duka da kafafunta." Inda ta nuna matan taje ta kwanta indo nayi mata hira tayi mata banza ta juya baya tana tunanin shike nan shi ma Babanta ta dena ganin shi kamar yadda ta daina ganin Mamanta da Yaya. Tun tana jin motsin Indo harta dena ji alamun tayi bacci, ita kuwa baccin ta nema ta rasa, zuciyar ta tayi mata nauyi tunani ya addabe ta, inta tuno wancan saita tuna wancan daga kashe tashi tayi ta zauna tana bin ɗakin da hasken Shekarau ya gaza ya haske cikin shi da kallo. Babu wanda take son gani yanzu sai Mamanta, to amma me yasa Baba yaƙi kaita wajen ta ko wajen Yayanta ya kawo ta ƘYAUYE? Yanzu anan ma haka zata zauna kamar yadda ta zauna da Nana? Babu zuwa makaranta babu Yayan ta babu Mamanta shima Baban ya kawo ta ya tafi ya barta. Tana zaune tana tunani ta kifa kanta a tsakanin cinyoyin ta tana kukan da babu sauti bata san tsawan lokacin data ɗauka a haka tana kukan ba har bacci ya ɗauke ta a yadda take. Da sassafe hayaniyar yara da matan gidan ce ta tashe ta daga bacci, ɗakin ta kalla taga sai ita kaɗai ɗankwalinta ta nemo ta ɗaura ta fito, babu kowa a lungun duk suna cikin gida, tana fitowa da Ramma ta haɗa ido tana dafa tuwo. Ita ta bata buta tayi Alwala tayi Sallah a ɗakin ta sannan ta fito ta fara binsu ɗaya bayan ɗaya tana gaishe su, ai saita zama abin kallo a idon yaran gidan dan abu ne da ba'a saba ganin yara masu shekarun ta nayi ba. Wajen Dije taje ta samu Aramma a ciki, yana ganin ta ya fara mata murmushi, shima ta durƙusa tace "ina kwana." "Lafiya lau Asma'ullahi kin tashi lafiya?" Ya tambaye ta da kulawa ta ɗaga masa kai, Dije ma ta gaishe ta ta amsa. Tana wajen Aramma Lirwanu ya shigo Salisu na biye da shi a baya. "Baba ina kwana." Ta gaida Salisu ya amsa bakin shi a washe yana tambayar ta "ya kwanan bakunta?" "Alhamdulillah." Ta faɗi kamar wata babba, ta juya wajen Lirwanu tace "Baba Lirwanu ina kwana." Shima ya amsa. Indo ce ta shigo da ƙosan siyarwa, Salisu ya siyawa Husna kamar yadda ya siyawa yaran shi, Aramma ma ya ƙara mata tace ya ishe ta. Salisu ya bawa Indo Naira Hamsin yace "inkin maida tallar tunda ta ƙare ki biya gidan madiga ki siyo muku koko." Ta karɓi kuɗin, Husna ta biyo bayan ta suka fito tare, sauran kosan ta ta kaiwa Ramma tace "gashi na koshi." "To kikai ɗaki ki ajiye anjima sai kici." Ramma ta faɗi, Husna ta girgiza mata kai tace "Ni bana cin kosai mai sanyi." Maganar ta ta bawa Ramma dariya dan kana ganin yadda tayi da fuska kasan da gaske bata so ɗin, karɓa tayi tace "to shike nan." Ɗakin ramma taje ta ɗakko maganin ta ta fito ruwa ta ɗiba a ranta tasha duka maganin dan jiya bata sha na dare ba. Data maida maganin saita kwanta a tsakar ɗakin Ramma. Can cikin gida anata hayaniya Indo ta siyo kokon Babanta yace ta nemo Husna susha. "Inagafa tana ɗakin Ramma dan naga shigar ta wajen su." Gaje ta faɗa wa Indo. Tayi ɗakin ta same ta a kwance. "Lallai Ma'u kowa na cikin gida ke kika taho nan? Kizo muje musha kokon nasiyo mana." Saida suka zauna shan kokon Indo uwar yan shiririta ta tuna bata siyo siga ba da gudu ta tashi ta cewa Husna. "Ina zuwa." Husna na zaune tana jiranta ta dawo da sugar zata zuba musu a ciki tace "ni bana sha kunu da sugar." Abin saiya zame wa Indo abun mamaki, Gaje ta shigo ɗaukan abu ta same su, Indo tace "taɓ Gaje wai kinji Ma'u bata shan Koko ta sugar." Gaje tace "saiki diba mata nata ke kuwa uwar ƴan zaƙi kisa a naki, yawwa ku dibawa Sa'a nata karku shanye." Tana gama faɗin haka tayi waje. Bayan sun gama shan Kokon basu fita a wajen ba saida Gaje ta kira Indo. Wajen ƙarfe goma na safe Salisu ya fito zai tafi Kasuwa, kamar yadda yake bawa yaran shi kuɗin abinci duk randa baza'a yi girkin rana ba haka ya bawa Husna nata kuɗin. Da rana ma Indo ta ɗakko tallar awarar siyarwa anata siya yara kowa kuɗin shi yake ci dan kusan duka ƴan matasan gidan suna talla su samu biyar da goma, wanda basu isa nema ba kuma Iyayen su mata ke siya musu. Husna na zaune bata siya ba Ramma ta siya mata tace "bana son awara." Zahara tace "kema Ramma sai shegen shishshigi naga Yaya Salisu ya bata kuɗin abinci, tuwon safe ma haka kika yi ta binta dashi tana yanga, ke baki san Ma'u bane haka take da gwasale mutum ni shi yasa koda uwarta suka zo bana matsawa kaina shiga sabgar ta." Gaje ta dubi Zahara "ba gwasale wa bace halin tane a haka tunda ko waye ya batan ma in bai mata ba bata karɓa, ke Ramma amana Aramma ya baki riƙe hannu bibbiyu duk da baki mori uwarta kamar yadda wasu suka mora ba amma ke kiyi dan Allah sai Allah ya biya ki." Gaje tayi maganar da biyu. Zahara ta shaƙa iya shaƙa dan tasan da ita take tunda tasan tafi kowa shishshige wa Safiya in tazo garin, kamar ta tanka mata sai kuma ta fasa tayi shiru, dan tasan halin Gaje ƴar kai tsaye ce bata shiga sabgar daba tata ba amma kuma akwai faɗin gaskiya ko tama daɗi kota kashe ka. Da yamma yara sun fara fita ƙwalam Husna tabi Indo data ɗauki tallar alewar Ramma. Ƙwalam ɗin babu nisa da gidan su dan kana gano gida daga wajen, yara da ƴan mata an taru kowa da abin da yake siyar wa masu ɗan malili, Shashshaka, hallaka kwabo abubuwan yara dai da yawa, Husna na zaune kusa da Indo tana kallon yadda take ta cinikin alewa, wanda basu santa ba suyi ta tambayar Indo "bakuwa kukayi? Ita kuma sai tace musu "ƴar Baban mu ce na Kano." Saida yamma tayi sosai sannan suka taso zasu tafi gida Indo tace "Ma'u zoki rakani shagon Sunday na siyo omon wanki gobe zamu makaranta wanki." Husna tabi bayan ta suka zagaya ta gefan gidan su suka tafi tasha. Suna tafe Samarin garin na kallon Husna wanda suka santa suyi mata magana ta ɗaga musu kai, wanda basu santa ba kuma su tambayi Indo wacce. Sunday na gani Indo ya fara tsokanar ta dan mutuniyar shice sosai suke shiri. "Ke budurwar ƙyauye ba turanci, me za'a baki?" Yadda yake Hausar kamar jakin Kano zaka ɗauka Bahaushe ne dan sosai yaji hausa bakin shi ko alamar tangardar Hausa irinta yare babu. Indo ta murguɗa masa baki tace "ni omo zaka bani, kuma kaima ai wani ya fika iya turancin." Yana mata dariya yace "Allah in kika yimin 123 zuwa ɗari zan baki omon nan kyauta." "Kaidin a jarabar san kuɗin ka yasin ko na iya bazaka bayar ba." Indo ta faɗa tana hararar shi. Husna dai tana gefe a tsaye tana kallon su saida ya miƙo mata omon sannan ya kula da ita, yace "mutuniyar ƙawa kikayi yar gayu?" "Eh yar Baban mu na Kano." "Haba shi yasa ta fiki kyau." "Kaji dashi." Indo taja hannun Husna suka tafi, a hanya Indo ke bawa ta Labarin Sunday. "Kinga duk garin nan a wajena yake siyan Awara, inna ɗakko talla shi nake fara kawai ya siya da yawa wata rana ma duka yake siye wa, amma mugun san kuɗi ne dashi kinsan ance Yarabawa Mayun kuɗi ne." Husna ta kalli Indo kamar bazata kula taba sai kuma tace "kowa ma mayen kuɗi ne." Indo ta saki baki tana kallon yadda ta ɓata rai tayi gaba, kaiwa dan tace Yarabawa nada san kuɗi to ai ba ƙarya tayi ba, sai kuma tabi bayan ta da gudu tana faɗin. "Hmmmm! Ke fa dan baki san halin shi bane, san kuɗin Sunday na daban ne, hmmm, in faɗa miki akan Naira biyar saiya ki siyar miki da kayan shi, baya wasa da yara fa, nima dan Baban mu na mana siyayya a wajen shine shi yasa yake tsokana ta." Husna dai bata sake cewa Indo komai ba dan ta bata haushi da tace Yarabawa nada mugun san kuɗi, har suka je gida Indo keta zuba surutu, Ramma ta karɓi Alewa suka lissafa cinikin da aka yi da wacce ta rage ta bawa Indo ladan tallar ta. _Washegari_ Husna tabi Indo inda zuke zuwa wanki can bayan gari Famfon makaranta, wajen na can nesa da cikin gari ya ɗanyi jeji da gari duk da kana iya hango gidaje daga makarantar, Famfon makaranta anan ƴan mata da kamar yakan su Indo ke zuga suje yin wanki. Famfo ne na ƴan makaranta da governoty ta yi musu, ba'a fiya zuwa ɗiban ruwa ba daga cikin gari saboda wajen yayi nisa saidai in Famfon tasha ne ya lalace kan a gyara shi mutane ke zuwa ɗiban ruwa. Husna na zaune a gefe tana kallon ikon Allah, ko wacce ta zube kayan ta gurbi gurbi, suna wanki suna zuba hira da zancen Samari ana shewa, duk wacce ta gama nata saita shanya a gonakin kusa da wajen akan kargo da sabara, kan kice meye wannan kayan sun bushe to waje ne fili fetal ga isaka ga rana, insun gama wankin kuma sai a kafa dabar ƴar carafke ana jiran wanda basu gama ba ko wanda kayan su bai gama bushewa ba su ƙarasa. Sai kowa ya gama nasa wankin ya linke kayansa sannan sai a kamo hanyar gida ana tafe ana cin kai. Rakiyar wankin tayiwa Husna daɗi dan sosai yan matan suka yi ta janta da hira, har shanya ta taya Indo da kwashe kaya ta riƙo mata roba ɗaya suka taho gida. ******Sannu a hankali rayuwa ta fara canjawa Husna, Ramma na iyaka kokarin ta wajen kulawa da ita, haka Salisu komai ya siyawa yaran shi koya basu saiya bata, Aramma kuwa indai yana gida to tana wajen shi a zaune, ƙarfi da yaji canjin rayuwa yasa Husna ta zama miskilar dole, tsakanin ta da Dije kuwa sai harara da baƙar magana. A ɗakin su Indo take kwana randa Ramma bata da girki kuma ta gudu ɗakin ta ta kwanta, yanzu sosai ta sake da Indo dan ita ce dai-dai ita a gidan, duk inda Indo zata a cikin gari tare suke tafiya. Zaman ƙyauye yayi wa Husna sauƙi saboda babu zama da yunwa duk da har yanzu wani abincin nasu bata saba dashi ba haka tuwon dare har yau bata iya cin miyar saidai tayi dangwale, musamman in Zahara ce tayi tuwo taɓ ai su kansu ƴan gidan da haƙuri suke cinta dan miyar bata hankali ko kaɗan, haka yanzu babu zagi da hantarar Nana. Duk ƙanƙantar shekaru da rashin wayon Husna kuma saita fara gane halin Zahara na fuska biyu da munafunci, ga san gwaninta da shishshigin tsiya, haka kayan ta baya tabuwa a gidan inka taɓa mata kuwa yanzu zata hauka da maganganu da gorin babu wanda ya siya mata, tun randa ta taɓa robar wankan ta tayi mata gori da cewa taje ta ɗauki na uwar riƙon ta shi ke nan Husna ta daina taɓa kayan ta. Haka Lirwanu ma tunda ta gane yanada faɗa shike nan bata zuwa inda yake, Dije kuwa dama inka ganta kusa da inda take zaune to sai in Aramma na nan, inka cire kewa, canjin rayuwa da tunanin Iyaye da yayanta zamu iya cewa babu abinda ke damun Husna yanzu... Wata rana Husna na zaune Ramma keta fama da Iro yazo ya siyo mata magi a shagon Sunday amma yaƙi zuwa, Husna ta taso daga inda take zaune tace "kawo na siyo miki." Ramma ta dube ta tace "kinsan shagon ne?" Kanta bata amsa Zahara tace "kema dai da bata sani ba tace ki bata ta siyo miki? naga dai tare suke fita da Indo yau wajen satin ta guda ai yaci ta fara gane gari." Ramma ta bawa Husna kuɗin ta tafi siyan magi, tazo wucewa ta komafar masallaci taga Aramma da abokan shi har ƙasa ta tsuguna suka gaisa yace "ina zaki ke kaɗai ina Indon?" "Magi zan siyowa Ramma, Indo bata nan." "To maza jeki siyo mata." Aramma ya faɗi Husna ta wuce. A ƙofar shagon Sunday ta tsaya tace "a bani Magi." Yana daga ciki yana waya beji anyi magana ba, ita kuma Husna jin yana waya saita tsaya nufin ta inya gama saiya bata, saida ya ɗago zai ɗauki abu yayi ido biyu da ita a tsaye. Wayar ya katse yana kallon ta yace "mai za'a baki?" "Magi ta faɗa tana miƙa masa kuɗin ya karɓa, sai kuma yayi mata murmushi ya ɗakko magin cikin asalin harshen sa na ibo yace "Achalugo (Beautiful)" Ga mamakin shi sai yaga Husna tayi murmushi, ai kuwa saiya tsaya yana kallon ta, yana bata magin tace "thank you." Sunday ya buɗe baki yana mamakin jin tayi masa magana dan duk zuwan da suke yi da Indo bata taɓa cewa ƙala ba, oho ita tuni tayi gaba. Shike nan tun daga ranar duk sanda Husna tazo siyan abu shagon shi saiya tsare ta da zance ita dai bata kula shi, dan dama bata da saurin sabo musamman da Maza. Sannu a hankali mutanen gari suka fara gane ta, haka yanzu ita ke yiwa Ramma aike in bata san waje ba Indo ta raka ta suje tare, kwanunkan Ramma ma yanzu Husna ke wanke mata, kuma sosai hakan ke kular da Zahara dan ita manyan yarana ta duk Maza ne macen ta ɗaya kuma ƙarama ce. Wata ranar Laraba suna zaune a inuwar gidan yaro ya shigo da leda yace "wai gashi inji Sunday saƙon Ma'u ne daga Baban ta." Kafin kowa yayi magana Dije tayi wuf ta karɓe ledar. Sabulan wanki ne dana wanka sai man shafawa da kuɗi dubu biyu. Babu kunya ba tsoron Allah Dije ta ɗakko sabulun wanki guda biyu ta miƙa wa Ramma. "Gashi na Ma'u ne, mai kuma ta shafa naku in babu tazo wajena ta shafa, shima Mai Kano wannan uban kaya haka sai kace wata babbar mace." Gaje da bata bari tace "to uwar Mari ba ubanta bane? Kuma ai kya bata kuɗin kashewar tunda kowa yana gani a gidan nan Ramma da kuɗin ta take siyawa Ma'u abun siyarwa in an kawo." "Bazan bayar ba saiki zo ki kwata mata mara kunya kawai, wallahi bari Salisun yazo inshi ya daure miki wani waje ma a gidan nan kike min rashin kunya sai naji." Gaje ta taɓe baki dan tasan babu abinda zai faru anyi haka tafi dubu fes take kallon ta ita ma ta sani. Ramma ke faɗawa Husna Babanta ya aiko mata da sako amma Dije ta karɓe, sai kuma ta nuna mata sabulun data bata. "Kinga daman kayan ki sunyi dattin gobe saiki taya ni mu wanke ko?" ta ɗaga mata kai sai kuma tace "ki kawo Alewar nakai miki ƙwalam." Ramma ta ɗanyi jim tana tunanin kar ace ta ɗora mata talla tunda bata taɓa yi ba. "Kinga ki fara faɗa wa Aramma inya yarda saina baki ko?" Husna tace"to." Ai kuwa da daddare ta faɗawa Aramma yace "zaki iya kuwa Asma'ullahi?" Tace "Eh naga yadda Indo take yi." "To Allah ya bada sa'a." Aramma ya fada. Kamar da wasa Husna ta fara fita da Alewar Ramma, ranar farko data fara fita da ita nan da nan sai gata ta dawo gida kamar wacce tayi bari, harta ƙare, ta lissafa kuɗi ko biyar bata ɓata ba, dalan tallar ta ta bata kamar yadda take bawa Indo da sauran yaran dake fitar mata talla amma sai Husna taƙi kamar tace "ki ajiye a wajen ki." Wata rana lokacin Husna na cika sati biyu da zuwa suna zaune tana taya Ramma wanki Mariya tazo gida. Suna zaune a kofar Dije suna zance tana kallon Husna da Ramma. Can bayan sun gama wankin Dije tayi kiran Ramma. "Ki ɗakko kayan Ma'u Mariya ta zaɓe sababbin ta tafi dasu ta ajiye mata a wajen ta kar duk ta turmushe su ta rasa na ado." Dije ta faɗawa Ramma. Ramma sai taji zancen wani iri dan taga Ma'u a wajen ta take kuma tunda tazo ita ke kula da kayan ta, sannan kayan nan ba'a wulaƙance suke ba bare ace, to meye kuma na a karɓi wasu wai za'a ajiye mata. Jikin ta a sanyaye ta juya ɗakin ta, Mariya ta rakata da harara. Tana fito da akwatin kayan Husna ta shigo daga siyan Magin da taje. "Ina za'a kai kayana kuma?" Ta tambaye ta, kanta bata amsa Mariya ta ƙwala mata kira tana faɗin. "Ke tunda kika zo bakije kin gaishe niba." Mariya ta faɗa tana garewa rigar jikin ta kallo, sai kuma tace "haka kike saka kaya babu lissafi wannan ai duk saiki sake su a rasa na kwalliya." Husna dai bata tanka mata ba har Ramma ta kawo kayan Dije tace "ina sauran?" Ta koma ta ɗakko Husna na tsaye tana kallon ikon Allah. Ramma ta juya Gaje ta tsare da ta tambayar Meya faru tace "wai sababbin kayan Ma'u Mariya zata ɗebe ta aje mata kar a watsa." "Kan ubancan wannan ma ai maganar banza ce ke kuma da yake lusara ce sai ki ɗakko mata?" "To ya zanyi musu uwar Indo kinfa san halin Dije inban ɗakko ba yanzu saita zage Iyayena." Ramma tayi maganar tana komawa ta zauna, sauran matan suka fara tofa tasu akan lamarin. Husna na tsaye tana kallon Mariya ta rinƙa zaɓe kayan ta masu kyau da daraja tana zubawa a gefan ta, saida ta zaɓe wajen kala shida sannan ta jawo jakar sama anan ma saida ta debe hijabai sababbi kuda uku da mayafi biyu. Akwatin tazo zata rufe hankalin ta yakai kan zif ɗin gefe da yayi tudu alamar ansa abu a ciki, tana zugewa saiga sarkar ji'el da ɗan kunnen ta masu kyau da wasu abun hannu manya guda biyu da aka nadesu daban, idanun Husna ya sauka akan abun hannun da tayi tabin kan Mamanta ta bata tasa tace yayi mata yawa saita sake girma ashe yana nan. Mariya bata kula ba Husna ta kwashe abun hannun tana murna, Dije tace "me zakiyi dasu bata ta haɗa ta aje miki." Husna ta girgiza kai tace "A'a." "Ban gane a'a ba? Ana miki magana kina musu? yaushe kika fara yiwa na gaba dake gadda ma?" Mariya ta faɗa tana miƙa hannu zata karɓi awarwaron daya ɗauki hankalin ta saboda ɗaukar idon da yake, tunda ta ganshi ta ji tana son shi danma bazai shiga hannun taba ai da ita zata saka, Husna ta matsa baya ta hana Mari awarwaron. Mariya ta zare mata ido tana mata tsawa, amma fir taƙi bata ta taso zata kwata ta ruga da gudu, zata bita Dije tace "kinga barta ki kwashe wannan kayan kan Aramma ya shigo ya gani kin sanshi da tsari yanzu saiya hanaki ɗauka, duk wannan uban kayan yaushe za'a bar mata tasa su a gaba ita kaɗai, kema kya samu na bawa su Sajida yo dubi laces da zannuwa wannan tsaf zakaci Sallah dasu." Mariya ta haɗe kan kayan data ɗiba tasa a bakko, Dije ta kira Ramma tazo ta kwashe sauran. Satin Husna uku a garin Mai Kano yazo, sosai taji daɗin

Chapter 17 of 31