Share this page
faɗa tana sake jijjuya jikin Husna tana ƙare mata kallo. Abdulganiyyu ya bi jikin ƴar ƙanwar tashi da kallo kuma takwarar Momman su ya dubi Safiya yace "mene ne wannan a jikin ta meya same ta haka?" "Duka ne Yaya Abdulganiyyu, dukan ta suka yi." Safiya ta fada tana rusa kuka sai kuma ta sake cewa "tun jiya na cewa Maman sama zanje naga Husna yau kanmu tafi amma na faɗa mata bazani gidan Abdullahi ba saidai naje gidan Umman Bishira nasa yara su kirata, ina shiga gidan su Bishira na ganta a haka, dan Allah kuga yadda na same ta a gidan maƙota." Ran Abdulganiyyu ya ɓaci sosai amma sai bai ce musu komai ba ya ɗauki hijabin Husna ya maida mata ya ja hannun ta suka fita daga falon, Safiya na ganin haka ta ɗora hannu aka ta zunduma uban ihun kuka dan ita a tunanin ta fita da Abdulganiyyu yayi da Husna gidan su zai mai da ita. A bakin gate suka haɗu da Abdulgaffar daya ji shirun tayi yawa ya biyo baya, yace "A'a ina zaku haka?" "Policetation." Abdulganiyyu ya faɗa yana yin gaba riƙe da hannun Husna, sai Abdulgaffar ya zama lost. "policetation kuma?" Ya tambayi kanshi sai kuma ya biyo bayan Abdulganiyyu da sauri yana masa magana amma tuni harya ɗora Husna a mashin yaja sun tafi, dai dai lokacin kuma motar Baba Habu ta iso Kofar gidan, yana fitowa ya tadda Abdulgaffar a tsaye da baki a buɗe. "Ya aka yi ne?" Baba Habu ya tambaye shi. "Wallahi Abdulganiyyu ne yanzu ya tafi da Husnah policetation, ina tambayar shi lafiya bai bani amsa ba ya wuce." Ai Baba Habu beyi jinkiri ba ya koma cikin motar sa ya cewa Abdulgaffar "zo mubi bayan shi, kasan halin sa in ranshi ya ɓaci bai iya yanke hukunci ba." .......Direct Bamfai Abdulganiyyu ya tafi da Husna, bai samu tsaiko wajen samun ganin DPO ba dan kananun ƴan sandan dake aiki a wajen sun san shi. "Na rasa meke damun wasu matan indai akace yaro ɗan kishiya ne sam basu da imani akan shi." Dpo ya faɗa bayan ya gama sauraren duka bayanan da Abdulganiyyu yayi masa, ya sake kallon jikin Husna yana girgiza kai cikin takaici yace "Tun yaushe ne ta dake ki?" Cikin lallashi DPO yake tambayar ta tana bashi amsa rabe a jikin Kawun ta. "Jiya ne." Ta faɗa a karye. Yace "Kiyi hakuri kinji? In sha Allah bazata sake dukan kiba." DPO ya sake faɗa cikin yanayin san kwantar Husna hankali sai kuma ya maida indansa kan Abdulganiyyu yace "Anyway zamuyi duk abinda ya dace in sha Allah." Sai kuma ya jawo takardar gaban shi ya fara rubutu, ya ɗago zai miƙawa Abdulganiyyu takardar suka haɗa ido da Acp Ja'afar Mai shinkafa daya shigo office ɗin kai tsaye babu knocking bare jiran a bashi izinin shiga, Abdulganiyyu daya bawa Ƙofar shigowa baya bai san da shigowar Yaya Ja'afar ba saida yaga DPO ya miƙe ya sara yana faɗin. "Morning Sir." "Morning Rano." Yaya Ja'afar ya faɗa yana zagayowa da sauri DPO Sunusi Rano ya matsa ya bashi waje ya zauna a inda ya tashi Yaya Ja'afar yana fuskantar ɗan uwanshi daya ɗauke kai kamar bai sanshi ba yace "Rano" "Yes Sir." "Please excuse us." "Okay Sir." DPO Rano ya amsa tare da girmama wa ya juya ya fita daga office ɗin ya rufo musu ƙofa yana tambayar kanshi ko Acp Ja'afar Mai Shinkafa yasan mai ƙarar ne, saida ya fito waje yaji wani ɗan sanda na faɗin ai kanin Oga Ja'afar ne. Bayan fitar Rano yaya Ja'afar ya kalli ɗan uwanshi da Husna yace "meya faru ka baro gida da ita babu wanda ka nema? kuma daka zo nan me yasa baka kirani ba?" Sam Abdulganiyyu bai so suka haɗu da Yaya Ja'afar ba shi yasa bai neme shiba tun farko daya shigo saboda baya son sumai katsalandan yafi so sai ya gama komai sannan kowa ma yaji dan baya son a kawo masa wani tsari na daban. "kowaye ya faɗa masa yana nan ma oho?" "Tambayar ka nake baka ce komai ba?" Kanya bashi amsa wayar Yaya Ja'afar tayi ringing, yana ganin mai kiran ya ɗaga. "Hello, eh na ganshi muna tare." "Okay gamu nan zuwa." Baba Habu ya faɗa daga can bangaren. Ran Abdulganiyyu a ƙuntace yayi wa Yaya Ja'afar bayanin abinda ya faru kamar yadda Husna ta faɗa musu, sai kuma ya cire mata hijabi ya nuna masa jikin ta, shi kanshi yaya Ja'afar ganin dukan da aka mata ba karamin ɓata masa rai yayi ba... Dan haka baice komai ba ya jawo wata paper yayi rubutu akai. Baba Habu yayi shiru yana jijjuya abinda ya faru bayan sun gama yi masa bayanin komai shima ya ga jikin Husna, a gaskiya a wannan karon ranshi yayi mugun ɓaci kuma ko bai faɗa ba yan uwan shi sun ga alama saboda furucin shi daya biyo bayan gama sauraren komai daya faru shine. "yanzu wani mataki zamu ɗauka a hukumance Ja'afar?" "Eh na riga na shigar da ƙorafi, so yanzu zan tura a kawo min Mai Kanon, ina so naji wanda ya bawa matar shi daman dukan mutum haka.." yaya Ja'afar ya faɗa ranshi a mugun ɓace. Murmushi Baba Habu yayi dan yasan za'ayi rigima akan abinda zaice musu yanzu amma kuma dole hakan za'ayi dan ya fuskanci yadda suka hau dokin zuciyar nan inya biye musu batacciya za'ayi wacce zata iya kaisu ga nadama nan gaba, dan haka ya fuskance su yace "Babu wanda zaka tura su ɗakko Abdullahi, turawa a taho dashi wannan cin mutunci ne babba, kuma duk yadda abubuwa suka kai ga lalacewa dole shi ne uban Husnah bamu isa mu canja wannan ba, sannan kar fushi yasa ku manta waye shi a wajen maihaifin mu, haka koba komai shi surukin gidan mune, mu kuma tarbiyyar gidan mu bama sharri bama cin mutunci kamar yadda bama bari aci mana mutumci, dan haka ni zan kira shi da kaina nasan zai zo, in har da sanin shi matar sa ta yiwa Husnah wannan dukan ina mai tabbatar muku da kaina zanyi karar shi har sai naga abinda ya turewa buzu naɗi, in kuma babu sanin shi ma'ana bai sani ba to zamu duba masalahar da tafi dacewa da yanayin" Baba Habu ya faɗa ba tare daya jira cewar suba ya dannawa Mai Kano kira. Tsayawar Mai Kano ke nan a Birget ƙofar gidan surukin nashi yaji wayar sa na ringing, wallahi saida gaban shi ya faɗi sanda yaga me kiran, amma saiya dake ya daga wayar da sallama, yayi shiru yana sauraren abinda Baba Habu ke faɗa masa. "innalillahi wa inna ilaihirraju'un" ya faɗa bayan ya gama jin abinda Baba Habu ya faɗa. "In same shi a Banfai kuma?" Ya sake maimaita maganar a fili yana sauke wayar daga kunnen sa. Bashi da zaɓi dole ya hau Mashin ɗin sa ya tafi Bamfai ɗin yana tafe yana sake-sake a ranshi, amma ko wanne tunani ya ƙulla sai ya kunce dan har ya isa gate ɗin shiga ciki Bamfai tunanin shi bai hasaso masa dalili da abinda zai sa Baba Habu yace ya same shi acan ba. Tun daga bakin gate ɗin shiga ƴan sanda suka tare shi da tambayoyin ina zashi, wa yazo nema? Meya kawo sa? Amsar ma saiya rasa wacce zai basu. Yaya Ja'afar yasan za'ayi haka shi yasa ya turo Abdulgaffar da wani ɗan sanda su shigo da shi. Yana tsaye an hana shi shiga su Abdulgaffar suka iso gate ɗin suka yi wa ƴan sandan wajen magana suka barshi ya wuce. Sanda Mai Kano yayi ido biyu da jikin ƴar shi Husna mutuwar zaune yayi Baba Habu da su Yaya Ja'afar suka zuba masa ido suna son karantar reaction ɗin sa, Husna kuwa yin duniya akayi da ita taje wajen Baban ta amma taƙi zuwa, Lokacin da ya shigo ma tana ganin shi ta fashe da kuka ta sake ƙanƙame Abdulganiyyu. "Husnah waya dake ki haka? A ina aka yi miki wannan dukan rashin imanin?" Mai Kano ya faɗa yana zuba mata idanunsa da suka canja kala. Husna ba amsa sai kuka, hankalin Mai Kano yayi mugun tashi, Yaya Ja'afar ya kalle shi duba irin na jami'in tsaron da yasan aikin shi yace "Matar kace ta dake ta baka sani bane?" Mai Kano yaji saukar maganar ta Yaya Ja'afar a cikin kunnuwan sa kamar saukar aradu. "Nana ta daki Husnah irin wannan dukan? To ta ya ya? da yaushe? Me ta yi mata? " Saboda tsabar ruɗanin da Mai Kano ya shiga su da suke jiran amsoshin duka wadannan tambayoyin daga bakin shi amma su yake jerowa tambayoyin da amsar ta suke jira daga gare sa. Duk sun karanci Mai Kano, sun kuma gane baisan da dukan ba, to amma ta ya ya? Bayan Husna tace jiya akayi mata dukan ba yau ba. "Bai ganta ba tun jinya ke nan?" "Dan Allah kawai a haɗa information ɗin abinda ya faru a shigar da kara Court koma waye yayi dukan da yadda akayi dukan da dalilin da yasa yayi dukan, duka ayi mana bayanin su a gaban Alkali." Baba Habu yayi murmushi na wanda ya fi Abdulganiyyu sanin duniya da fahimtar ta, sai da Baba Habu ya gyara zama yana fuskantar Mai Kano da daya kasa zama da kyau saboda ruɗani yace "Abdullahi zamu ƙarasa wannan case ɗin a gida, Ja'afar a rufe case ɗin nan, Abdulganiyyu kama Husnah mu koma gida." Wani mugun baƙin ciki Abdulganiyyu yaji ya zo ya tokare masa a wuya, dama yasan tunda Baba Habu yazo ya shiga maganar saiya hana ayi abinda ya dace, bai kula kowa ba ya fice daga office ɗin fuuuuuu a zafafe ya doko musu ƙofa ji kake "bummmm." Baba Habu ya bishi da kallo yana girgiza kai, Yaya Ja'afar bai dubi kowa ba ya rufe case ɗin Abdulgaffar ne ya kama hannun Husna suka fito daga office ɗin. Mai Kano da ƙyar ya iya miƙe wa ya biyo bayan su yana jin kanshi na sara wa da ciwo saboda tunani, basu sake ce masa komai ba shima bai sake cewa kowa komai ba ya hau kan mashin ɗin sa ya kama hanyar gida, yana tafe a titi yana saƙa yadda zasu yi da Nana, yana tunanin me ya kamata yayi mata ne dan ya huce wannan cin mutunci da tayi masa... _*WRITING.....✍🏻*_ *_MUTUWAR AURE.....!_* _(Ƙaddarar wasu ƴaƴan)_ *_Kanawa ne👌🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ _BOOK 1_ *_FREE PAGES_* ________________ *_WHATSAPP GROUP👇🏻_* https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3?mode=gi_t https://wa.me/+2348064789370 _________________ _EPISODE 5_ Safiya da tayi kuka harta gode Allah tanayin ido biyu da Baba Habu yana shigowa cikin Falon riƙe da hannun Husna bata san sanda ta saki Murmushin jin daɗi ba, su kansu su Momma saida suka sauke ajiyar zuciya, dan gaba ɗaya sun ɗauka fita da ita da Abdulganiyyu yayi maida ita gidan su yayi. Safiya nata bin Husna da kallo Maman Sama ta kamo ta ta cire mata hijabin ta barta haka jikin ya rinƙa shan iska, Kitchen ta shiga ta zubo abinci da shayi mai kauri da kanta ta zauna ta rinƙa bata abaki tausayin Husna na sake huda mata zuciya. "Ai duk mun ɗauka gidan su kuka maida ita?" Momma ta faɗa tana kallon zaratan magidantan ƴaƴan nata. "A'a ai ba zai yiwu mu mai da ita gidan su haka kawai ba." Baba Habu ya faɗi yana kallon Abdulgaffar yace "kiramin ɗan uwanka a waje, uban ƴan zuciya wato ba'a masa yadda yake soba shi ne yaƙi shigowa gidan ya tsaya daga waje." Baba Habu ya bawa su Maman Sama labarin abinda ya faru Abdulganiyyu Bamfai yaje shigar da ƙara, da yadda suka yi da Mai Kano. "Bai san anyi mata duka irin wannan ba tun jiya, anya kuwa Baba Habu baza'a sake shawara ba kawai mu riƙe Husnah a hannun muba? Dan ni wallahi naji tsoro da lamarin Matar Abdullahi." Maman Sama na rufe baki, Momma ta ɗora da cewa "gaskiya dai ya kamata a sake duba wannan magana." Baba Habu najin iyayen nashi yana Murmushi, yasan me suke gudu kuma baiga lefin suba shi kanshi ya jinjina wa rashin imanin Matar. Mai makon ya basu amsa saiya juya kan Abdulganiyyu daya shigo ya samu waje ya zauna yana sake cushe fuska yace "Abdulganiyyu ka rinƙa danne zuciyar ka in kana cikin fushi, hanaka shigar da ƙarar da nayi ba yana nufin baza'a ɗauki mataki akan matar Abdullahi ba, amma ina so ka sani duk tsiya da lalacewar Abdullahi shine dai uban Husna, sannan ko munƙi ko munso dole shi surukin gidan mune, yin Shari'a da matarsa kuma kamar yin Shari'a dashi ne akan ƴar cikin sa, wallahi Abdulganiyyu kaji na rantse maka da Allah ko? yau da ace Abdullahi yasan anyi wa Husnah wannan dukan yayi shiru bai ɗauki wani mataki ba to wallahi da babu abinda zai hana mushiga Court dashi da matar sa, to amma Bawan Allah nan ku da kanku shaida ne, bai sani ba duk kunga halin daya shiga lokacin da yaga Husnah, amma inama uzuri Abdulganiyyu har yanzu kai kana da kuruciya sannan baka san halin makircin mata ba." Baba Habu ya ɗanyi shiru yana karantar reaction ɗin su, sannan yaci gaba da cewa "Hakan da nayi kuma ba wai yana nufin baza mu ɗauki mataki bane, A'a? Zamu ɗauki matakin Shari'a akan Matar Abdullahi yadda nan gaba ko kuɗi aka bata akace da ɗora hannun ta akan Husnah wallahi baza tayi ba, amma fa ni nawa tsarin ba irin naka bane babu kotin da zamu shiga da ita." Duk sai suka yi shiru suna sauran abinda zaice, sun sanshi farin sani, shi Mutum ne mai yawan kara ga haƙuri da ɗauke kai, wani abun in akayi ya ɗauke kai har sai ya baka haushi da mamaki amma fa fushin sa babu daɗi, maganar shi kuwa tasa wani ciwo daya tsaya a ƙirjin Safiya taji yana narkewa a hankali yana faɗawa cikin ta, shi kansa Abdulganiyyu da ranshi ya kai makurar ɓaci saida ya ɗago ya zubawa Yayan nasu ido. "Nasa Ja'afar ya samo mana Lauyan da zai fitar mana da agreement paper da sahalewar Court wanda za ayi wa Husnah tsakani da Matar Babanta, sannan Abdullahi zai kawo Matar shi muma zamu kai Husnah zata saka hannu ƙarƙashin yarjejeniyar babu ita babu sake ɗora hannu akan Husna da sunan duka, koda kuwa da wasa ne, duk randa ta sake haka kuma kotu zata kamata tare da ɗaukan mummunan mataki akan ta. Sannan bayan komawar Husna gidan su duk sati ɗaya ko biyu Abdulganiyyu, Abdulgaffar ko Abdussamad ɗayan su zai rinka zuwa yana duba ta, dalilina nayin haka kuma shine dan Matar Abdullahi taji a ranta cewa da gaske fa ake mata ba da wasa ba, sannan na zaɓi Mazan su rinƙa zuwa duba Husnah ne saboda inna tura su Mansura su rinƙa zuwa suna duba ta wata rana za'a yi batacciya dasu. Kowa a falon sai yayi shiru yana juya hukuncin da Baba Habu ya yanke, in akwai abinda bai yi wa wasun su daɗi ba shi ne cewa da yayi Husna zata sake komawa gidan Babanta, amma basu da wani zaɓi dole sai dai su bita da addu'a. Safiya kuwa duk da bata so akace Husna zata sake komawa gidan Babanta da zama ba amma sai ta ji abunda Baba Habu yace yayi mata daɗi, sosai taji sauƙin tsoro da fargabar data hanata sukuni da kwanciyar hankali tsawan kwanakin data rabu da gidan mijinta. Baba Habu ya miƙe yana duban agogon hannun sa, su Momma suka saka masa albarka shida sauran ƙannen sa, wanda tun bayan rasuwar mahaifin su Alhaji Ƙadiri suka sake zame musu gata musamman ma shi daya ɗauki nauyin uba ya ɗora a kansa. Kan Baba Habu ya fita daga gidan saida ya sake faɗawa Safiya lallai ta gama shirin ta da wuri dan gobe jirgin Safe zasu bi zuwa Lagos, gaskiya ta so ya tafi ya barta ta taho daga baya, bayan an gama case ɗin Husna da Nana amma sai Baba Habu yaƙi amincewa yace zaman nata me zai yi, Husna zata ci gaba da zama dasu Momma har zuwa lokacin da zasu gama yin abinda ya dace. Dole badan Safiya taso ba haka ta amsa wa Baba Habu da "to." ******Mai Kano ya iso ƙofar gidan sa kamar zai tashi sama mashin ɗin ma bai masa packing ɗin kirki ba ya afka cikin gidan kamar wanda aka koro. A tsakar diga ya wuce Nana da Ni'ima "fuuuuuu." ya shige ɗaki Ni'ima na masa sannu da zuwa bai amsa ba. "Ikon Allah lafiya kuwa?" Nana ta faɗa tana miƙewa tabi bayan sa. A tsakar ɗaki ta same shi yana kaiwa da kawowa, tana shigowa suka haɗa ido yayi kanta da masifa kamar zai rufeta da duka yake faɗin. "Ke ashe dama baki da mutumci ban sani ba? Ashe muguwa ce ke annamimiya mara imani wacce bata yarda da Allah ba?" Numfashin sa na sama da ƙasa saboda ɓacin rai yake nuna ta da ɗan yatsa kamar zai kai mata duka. "A'a wai Baban Ma'u menayi maka ne kazo kana min ɗiban albarka da rana tsaka?" Nana ta faɗa tana komawa baya dan wallahi ta tsorata da yanayin sa data ganshi dan tunda take aure da Mai Kano zata iya rantse wa da Allah bata taɓa ganin fushi da masifar da take hanga a cikin idanunsa ba yau. "Abun kazan na ubanki kika yimin, nace abu ta kaza da Kazar uwarki kika yimin, ƴar iska mara mutunci, munafuka muguwa makira annamimiya, ke mara imani ce, ke azzaluma ce, ke maha'inciya ce, wacce bata san Allah, ba bata san ma'aikin Allah ba, bata yarda da ƙaddara da ikon Allah ba, to wallahi baki isa ba danni ba mutumin banza bane, niba lalataccen namiji bane, ke kinsan nafi ƙarfin kimin iskan ci da rashin mutumci, dan haka maza maza ki haɗa yanaki yanaki ki barmin gidana yanzun nan ba sai an jima ba, gidana ba gidan kisan kai bane, ba gidan ƴan dambe marasa imani bane." "Innalillahi wa inna ilaihirraju'un, Mai Kano kana cikin hankalin ka kuwa? Kasan me kake faɗa min kuwa? Iyayena fa kake zagi." Nana ta faɗa tana rushewa da kuka hankalin ta na mugun tashi. Mai Kano jikin sa har rawa yake saboda ɓacin ransa daya taso masa yace "shaye shaye nake, ko baki jiba nace haukacewa nayi, ke banda ina gudun nayi abinda bai kamata ba wallahi yau da saina miki irin dukan azabar da kika ganawa Husnah." Nana najin ya ambaci sunan Husna saita tsaya cak tana kallon shi kukan da take yi ma sai ya tsaya saboda mamaki tace "au yanzu dama Mai Kano duk wannan cin mutuncin da zagin ƙare dangin da kake yimin akan na daki Ma'u ne?" Itafa har ranta bata ɗauki irin dukan data yiwa Husna a bakin komai ba, bata ma ɗauke shi a wani abu da har zai zo yana mata irin wannan masifar akai ba. Ran Mai Kano ya daɗa ɓaci dajin abinda tace, kallonta yake zuciya na cinshi, wallahi yadda yake jin kanshi inya biye mata saiya illata ta. "Haɗa kayan ki ki barmin gida na nace ko baki ji bane?" "Wallahi bab.........." "Idan kika sake magana baki fita daga gidan nan ba wallahil azeem a bakin igiyoyin Auran ki." Dif.......maganar da Nana ta ɗebo zata yi ta ɗauke daga bakin ta kamar an ɗauke wutar nepa, zufa ta yanko mata tsoro da fargaba suka shige ta. "Karfa wankin hula ya kaini dare ni Nana, in Mai Kano ya sake ni yanzu ai na shiga uku." Nana ta ayyana haka a ranta sai kuma tayi wuru-wuru a tsakar ɗakin ta rasa me zata ɗauka, Ni'ima na tsaye a ƙofar ɗaki tana jinsu tana rusa kuka dan duk abinda ke faruwa a cikin ɗakin akan kunnen ta ya faru. Mai Kano ya fito daga ɗakin Nana harya wuce Ni'ima ya dawo ya ciro kuɗi a aljihun sa da baisan nawa bane ya kama hannun ta yasa mata kuɗin amma sai ya kasa ce mata komai ya juya ya fita daga gidan. Yana zaune a kofar gida ya dafe kanshi da ke masa mugun ciwo Nana ta fito Ni'ima na biye da ita a baya suka wuce shi, da ƙyar ya iya ɗaga kansa dake masa ciwo kamar zai rabe gida biyu yabi bayan su da kallo yana jin takaici da baƙin cikin abinda Nana ta aikata masa. Yasan halin Nana bata da daɗi amma bai taɓa sanin bata da imani ba sai yau, kai ko a mafarki wani yace masa Nana zata iya yiwa ɗan mutum irin wannan dukan data yiwa yarsa wallahi ba zai taɓa yarda ba, ashe shawarar da ta rinƙa basa kwanakin baya da daɗin bakin tada rinƙa yi masa akan Husna duk na ƙarya ne da yaudara. Ƴan uwan Safiya sunyi masa halacci, ya saki yar uwar su da ƙaramin ciki bayan uwarsa ta gama ci mata mutumci, yanzu kuma ace matar shi na neman illata ƴar su amma duk da haka basu bari anci mutuncin sa anci na iyalan saba, to shi yanzu da wanne ido ma zai kalle su? Me ma zaice musu?. Alhaji Ƙadiri Mai Shinkafa ya shaideshi yayi masa halacci yayi masa gata ya mutumta shi amma dubi abinda ya saka masa dashi bayan baya nan, wannan wacce irin masifa ce haka? Wai dama shi mutuwar Auran haka yake zame wa mutum tashin hankali da masifa ko kuwa nasa ne yazo da haka? Kansan dake masa mugun ciwo ya dafe, sai kuma a hankali tunani da ƙwaƙwalwar sa suka fara tuna masa da baya, can wani tsohon tarihi. Safiya! Safiya!! Wani suna mai daraja, girma da ma'ana a cikin tarihin rayuwar sa, tabbas tahirin rayuwar sa bazai taɓa cika ba in aka cire sunan Safiya. Haƙika yaga karamci, sannan yaga halacci da sanin ya kamata a wajen ta, tabbas ɗan halak yana gadon halin kirki da mutumci daga wajen iyaye sa amma na Safiya bayan gadon harda ƙari da tukaici a nata halin. Wani sashe na zuciyar yace "Haƙika Mai Kano ka rushe yadda da amincin dake tsakanin ka da Alhaji Abdulkadir Mai Shinkafa." Mai Kano saiya rufe idanun sa da sauri yana sauraren bugun zuciyar sa. Haƙika har abada bazai daina tuna randa Alhaji Ƙadiri ya kira sa har cikin falon gidan shi ya zaunar dashi a gaba sa ya kuma mutumta shi ya girmama sa tare dayi masa abun da bai taɓa zata ba, bai kuma taɓa tsammani ba, tabbas Alhaji Ƙadiri yayi mishi Alfarmar da bai taɓa yiwa kowa ba, bai kuma taɓa amincewa kafatanin ƙabilar Hausawa akan taba, duk kuɗin ka duk ikon ka indai sunan ka Malam Bahaushe to a wajen Alhaji Ƙadiri baka isa ba, baka kai ba, kayi kaɗan haka kuma kayi tsararo yayi maka wannan alfarmar, sai dai ka nemi wani abun daban a wajen sa amma

Chapter 5 of 31