Share this page
cece shi Sale ya shigo gidan hakan kuma shiya ɗauke hankalin ta akan maganar amma yasan ba mantawa tayi ba. Dama ɗazu a kasuwa Abdussamad yazo yace masa yaje gidan shi ance masa basa nan sun tashi. Shi wallahi gaba ɗaya ya manta bai faɗa musu ya tashi ba sai lokacin yake sanar da shi tashin sa daga gidan. Abdussamad yace "Allah yasa Albarka in sha Allah zan shigo duba Husnah." Ya faɗa yana miƙe wa suka yi sallama ya tafi. WASHEGARI ɗan Malam yazo yiwa Nana cefane tace wa Husna "ke ƴar hutu wacce ba yar wahala ba tashi ki bishi kiga inda yake siyo komai nagaji da cida ke a banza niba wata uwar kike tsinana min ba." Babu musu Husna ta saka hijabin ta tabi ɗan malam cefane. Ranar cefanan gidan tare suka yishi, shi ke nan kuma tun daga ranar Nana ta sallamin ɗan malam Husna ke zuwa cefane, gashi dan baƙar mugunta Nana bata tashi aken ta sai taga rana ta take. Haka zata aike ta tayi ta gallafiri a unguwa ga wajen aiken ba daya ba ba biyu ba. Kanta gama mata aiken duk tayi firgai firgai da ita. In taje ta tadda layi ta dade kuma inta dawo saita zage ta tsaf, duk wannan abun da ake kuma Ni'ima na zaune tana kallon su Nana bata isa ta sata abu ba saita gadama zatayi inta matsa mata kuma tace "Nifa Nana saina kwashe kayana na koma wajen Dije haka kawai bazaki hanani hutawa ba." Wannan yasa ko aikin cikin gidan Nana bata saka Ni'ima sai wanda taga dama zata taya ta. Husna ke tafe tana ta duba hanya, daga gidan su zuwa gidan Malam Malam taje ta dawo yafi a irga tana neman kuɗin da Ni'ima ta aike ta ta siyo mata riɗi a gidan Malam Malam, saida taje siyan riɗin ta rasa kuɗin ta sake biyo hanya kuma bata gani ba. Jikin ta asaɓule ta shigo gidan tana raɓe wa, Ni'ima ta zuba mata harara tace "Wato ke indai aka aike ki saikin shanya mutane kanki dawo ko?" Ni'ima ta faɗa a zafafe Husna ta sake komawa baya. Nana tace "Au yau da yake naki ne aiken ai kin magantu dani na aike ta ta daɗe haka nayi mata magana da tuni kince nina fiya masifa." Nana tayi maganar tana taɓe baki. "Wai aiken ne bazaki kawo min ba ko me kike nufi? Dama kin raina ni tunda kinga kanmu ɗaya ko Ma'u?" Husna dai tana tsaye a bakin kofa ita bata shigo ba ita bata fita ba. Saida Ni'ima ta shammace ta sannan ta danƙi rigar ta batayi wata wata ba ji kake "kauuuuu." Ta wanke ta da mari tace "Dan uwarki ina aiken dana miki?" "Ku....Ku....Kuɗin ne ya faɗi." ta faɗa tana fashewa da kuka dan sosai marin ya shige ta. "Kan bala'i ke kin isa ki yarmin da kuɗi, baki taɓa yarda kuɗin kowa ba sai nawa saboda kinga ina raga miki?" "Tass.....tass." Ni'ima ta sake wanke mata fuska da wasu marinkan guda biyu a jere sai kuma taci kwalar rigar ta kamar wata sa'ar ta. Nana dake kallon su daɗi ya cika zuciyar ta tace "da kyau dama ai lefin kine Ni'ima da kika bari ta rena ki." Ta ɗaga hannu zata sake marinta Abba ya shigo cikin gidan kanshi yayi wani irin aski tsakiyar kan anyi masa wani abu cibiri cibiri kamar kitso, wandon jikin shi kuwa irin crezy Jens ɗin nan ne da kaɗan ya wuce gwiwar sa singlet ce kawai a jikin sa baƙa kana ganin shi kaga irin yaran nan da basa jin magana cikin maganar sa ta marasa ji yace "Ke daga ina kike kin maƙale yarinya zaki more ta?" ya faɗa yana shigowa cikin gidan gaba ɗaya, Ni'ima ta bishi da kallon rashin sani, sai lokacin kuma Nana dake kwashe shanya ta ɗago kai ta ganshi, itama da ɗan Mamaki take duban sa dan bata sanshi ba. "To kai kuma daga ina zaka shigowa mutane gida babu sallama." Nana ta faɗa tana ƙare masa kallo. Baibi takan maganar Nana ba ya cewa Ni'ima "ke dalla sake ta, kibar nan." "A'a kai asuwa to? Kasan me tamin ne da zaka ce na sake ta? Haka kawai ka shigo gidan mutane kace zaka baza mata iko." Ni'ima ta faɗi maganar cike da fitsara. Abba yayi wata dariyar rashin mutumci yace "tab amma yarinyar nan yau kinci bulus kinyi sa'a yanzu na dawo bana son daga zuwana tsohon can yazo ya fara min faɗa amma bamda haka da kinci uwarki yau." Sai kuma ya haɗe rai yace "sake ta tayi gaba ko naci kazar ubanki." Abba ya luƙa mata ashar ɗin da Ni'ima da Nana basu taɓa jin irin taba, Husna kuwa saida ta tsorata da tsawar daya yiwa Ni'ima. "Ke sake ta karya buge ki daga ganin wannan ba ɗan arziki bane." Nana ta faɗa tana janyo Ni'ima baya. Abba yabi su da kallo yace "ke tsohuwar banza zanzo kanki." Sai kuma ya juya wajen da Husna ke tsaye tana share hawaye yace "dalla kema bar nan." Ga mamakin sa sai yaga itama tayi cikin gidan yabi bayan ta da kallo. Kamar ya shiga cikin gidan sai kuma ya juya ya fice, dan yaga alamar Baban sa yan haya yasa a gidan su. Da daddare su Mai Kano suna zaune suna cin tuwo Sale ya dubi Mai Kano yace "wai kasan Abba ya dawo kuwa?" "Alhamdulillah ya baro wajen Nasurun ke nan?" Mai Kano ya faɗa. Sale yayi murmushin da kana gani kasan bai kai zuciya ba yace "wazai iya zama da Abba ai sai iyayen shi suma danya zame musu dole ne, kasan Allah kaga nina haifi Abba ko? To wallahi dazan samu inda zan kaishi ya zauna da kaisa zanyi nima kona huta da tashin hankalin da yake sani." "Kayya nace ka daina faɗin haka a kansa amma baka ɗauka kaifa ubane ya kamata kana sanin mai zaka rinƙa faɗi akan sa." Mai Kano ya kwabi Sale. "Kayya a rashin ji wanne irin ne Abba bayayi? To inka cire sata wallahi ko wanne iskanci daka sani Abba yasan yadda ake yin sa, ni ƙarin damuwa ta ma yaƙi neman kuɗin arziki sai korar jakai, yaƙi karatu da ƙyar fa ya kammala aji ukun Sakandire, ." Mai Kano yayi shiru yana tunanin abinda Nana ta faɗa masa ɗazu "oh shiya shigo gidan ke nan, tabbas shi ne Nana bata sanshi ba shi yasa tace wani." Ya ayya maganar a ranshi sai kuma yaja numfashi, ya fara dannar Sale dan tabbas Abba jarrabawa ne a gare sa. Washegari Mai Kano yayi wa Nana bayanin waye Abba sai dai bai faɗa mata halayen saba. "Shi dai yanzu wannan mai zubin marasa mafadan kana nufin ɗan Sale ne na cikin sa Baban Ma'u?" Nana ta maimaita zancen tana kama baki. "Eh ɗan sane shine babba sai ƙannen shi biyu mata suna hannun yayar Sale, saiki kama kanki, yawwa maganar da kika min shekaran jiya nace a'a." Ya danyi shiru yana juya zancen dan harga Allah ba'a son ranshi zaibar Ni'ima zuwa makota tayin kwana ba, amma babu yadda ya iya hakan ya kamata yayi yasan Sale bazai ce su bawa Abba ɗaki ba saidai shi a matsayin sa na wanda yasan daidai dole hakan za'ayi. "Wai maganar taya Amarya kwana kake nufi?" "Eh ita, kince ita da yar Malam Malam ne zasu rinƙa taya ta kwanan ko?" Ya faɗi yana duban ta. Nana tace "Eh haka tace, yarinyar nada kirki dan tunda aka kawo ta garin nan tana yawan shigowa mu gaisa, Mijin nata ne wai inya tafi sai yayi wata uku huɗu bai dawo ba kuma ita ba yar nan bace daga Jalungo aka kawo ta." "Ni duk ban tambaye ki wannan ba, ke kinsan badan dawowar yaron nan ba da babu inda Ni'ima zata wani tayin kwana makota to dole ce tasa, na yarda taje su kwana gari na wayewa kuma ta dawo gidan nan, in sha Allahu zuwa karshen watan nan za'a fara ɗora min gini, kuma ki kula da itafa banda gantali iya kwana zatayi ta dawo in lokacin kwanciya yayi ta tafi da safe ta dawo gida." "To shike nan." Nana ta amsa tana tunanin yadda zai yi da Husna, kamar ta tambaye shi sai kuma tayi shiru tana addu'ar Allah yasa ya maida ita can dangin uwarta ita ma ta huta da baƙin cikin da suke ƙunsa mata. Saida ya kira Ni'ima da kansa ya sake ja mata kunne sosai sannan ya shiga ɗakin su ya fara fito da kayan su. Kayan sawar Husna ne kawai a cikin ɗakin sai katifar su dan kayan Ni'ima suna ɗakin Nana. Abun ya bawa Nana mamaki ganin Mai Kano na kafa bululluka a ƙarshen ɗakin dake tsakanin su wanda ragunan Sale suke kwana. Saida ya gama jera bulon sannan ya ɗakko ƙyauran daya fara siya na gidansa yana ajiyewa ya ɗora akan bulon wajen sai yayi kamar gado, Nana bata sake tsinkewa da lamarin Mai Kano ba sai da taga ya ɗakko katifar Husna ya ɗora akai, ya sake sharo ɗakin tas dama ya wanke shi kan ya fara aikin, kayan sawar Husna yasa a saman katifar yabar gefe ɗaya inda zai ishi mutum kwanciya. Saida ya gama aikin yana wanke hannu sannan Nana ta ce "wai wa kayiwa makwanci haka?" Bai dube taba yace "Husna ce zata rinƙa kwana a ciki kafin muga abinda Allah zai yi, in sha Allah ginin nan ba zai cini wata biyu ba, inna samu nayi mana ko ɗaki biyu ne kawai saimu koma na ƙarasa sauran muna ciki." Nana tayi sororo tana kallon shi kamar ta sake cewa wani abu sai kuma tayi gum da bakin ta. "Meye nawa a ciki yarka ce can ta matse muku." Ta faɗi a ranta, sai kuma ta tafi kai masa ruwan wanka. Kanya fita saida ya kama hannun Husna ya nuna mata komai tare dayi mata bayanin da zata gane a nutse. Ta ɗaga kai ta kalli Baban nata bayan ya gama yi mata bayanin a nan zata dawo da kwana tace "Baba kuma da ragunan Baba Sale zan dinga kwana?" Saida ya tsuguna a gaban ta dai-dai tsayin ta sannan yace "kiyi hakuri kinji babu abinda zasu miki kuma kinga ai ina kusa ko? komai kikaji ki kirani zanzo kinji, in kika yi Sallah kiyi tamin addu'a na samu kuɗi na gina mana namu gidan da wuri kinji ko?" Husna baiwar Allah babu musu ta ɗaga masa kai. Sale baisan mai yake faruwa ba saida ya dawo yaga abinda Mai Kano yayi ai kuwa nan yace sam bazata yiwu ba. "Haba Abdullahi ya zaka min haka? Shiba namiji bane yaje can cikin abokan shi ya kwana." Sale ya faɗa. Mai Kano ya tari numfashin sa da cewa "Muda muke addu'ar Allah ya shirya mana shi sai kuma mu sake tura shi ciki su? Kaga karka damu duka kwana nawa ne? Asiri ma ai ya rufu tunda da wajen kwanciyar." "A'a wallahi, a ina asiri ya rufe kasa yarinya kwana da dabbobi, to kuwa sai dai na fito dasu waje in rabone a samu." "Wallahi bazaka fito dasu ba inka fito dasu kuma to ka nuna min iyaka ta Sale." Mai Kano ya fadi maganar cikin tabbatar wa. Wannan abu baiwa Sale daɗi ba amma babu yadda ya iya da Mai Kano dan yayi kicin-kicin da fuska. A ranar farko da Husna fara kwana da raguna a ɗakin suna ganin mutum a ɗakin su suka rinƙa kuka, ita ma kusan kwana tayi tana kukan da babu wanda ya sani, kuka tare irin kukan nan da ake kira da kukan rashin madafa, kukan maraicin uwa, kukan da babu mai baka haƙuri ka daina, duk da ƙananun shekarunta amma wani irin ciwo take ji aranta, nan da nan ciwon kai mai zafin da har cikin Idanunta take jinshi ya rufe ta bata samu bacci ba sai can cikin dare bacci yayi awon gaba da ita Idanun ta sharkaf da hawaye.... Da safe shiya shigo ya tashe ta, lokacin da ta buɗe idanun ta akan Babanta ta ɗora su, ya tsare fuskar ta da ido yana bin bushashun hawayen da suka kwanta akan kumatun ta da kallo a ranshi yaji babu daɗi amma saiya dake yace. "Husnah kuka kikayi? Meya saki kuka?" Ya tambaye ta. Budar bakin ta sai cewa tayi "Baba dan Allah ka kaini wajen Yayana tunda kace Mama bata nan." Husna ta yi maganar da yanayi na roƙon da mai Kano har sai da yaji wani abu mara daɗi a ransa. "In sha Allah zan kaiki amma ba yauba kinji?" Kasan cewar ta yarinyar da aka rena cikin sanyin hali rashin gaddama kulawa da soyayya saita ɗaga masa kai ba tare da ta sake cewa komai ba. "To tashi kiyi Sallah." Ya faɗa yana kama hanyar barin ɗakin, yana so ya gyara inda dabbobin suka ɓata kanya fita tunda dama kwana kawai suke yi a ciki, yasa kafarshi zai fita a ɗakin tace "Baba yaushe zaka samu a makaranta?" "In sha Allah ranar Lahadi ina gida zan kaiku Islamiyya keda yar Iya, Boko kuma yanzu ana hutu sai an koma zan saku." "To." Ta faɗi tana tashi ta fito waje. Tana fitowa tsakar gidan da idanun Nana ta fara cin karo, ta watso mata uwar harara. Kanta ta ɗauke ta wuce banɗaki, zata shiga Abba na fitowa yana gyara ɗaurin wando baya ta koma ta tsaya ya wuce yana binta da kallo. Kanta gama alwala Baban ta harya gama sharo ɗakin inda ragunan suka ɓata Kuma ya wanke sa tas kamar basu kwana a ciki ba. Bayan tayi Sallah ta gaida Nana kamar yadda ta saba amma ko kallan inda take bata yi ba, haka ta tashi ta koma ɗaki, saida taji Baban ta ya fito zai tafi sannan ta fito tayi masa a dawo lafiya. Mai Kano a ƙofar gida suka haɗu da Sale anan yake sanar da shi yau zai yi tafiya ƙyauye duba noman da ake masa. "Kaga naso mu tafi da waccan Yaron amma yaƙi, hmmm Allah dai ya shirye shi, zan yi kamar sati ɗaya." Mai Kano yace "Abba sai addu'a komai zai wuce, anya nima ba noman nan zan fara ba kuwa? Kafa yi mana wayo." Sale yayi dariya yace "ai kai ka daɗe da zama Bakano saidai a noma ka siya kaci." "Au haka ne? Zan baka mamaki kuwa, kawai saidai kaji nace ma zo ka rakani girbi." "Hhhhh ai kuwa daka kyauta noma ai da daɗi." Sale ya faɗa suna tafawa. Bayan an gama karin safe Husna ta haɗa kwanukan wanke wanke zata wanke, saida tazo ɗiban ruwa Nana tace "ke rufe min ruwan nan na gaji da wannan lalacin naki maza ɗauki botiki ki ɗebo na wanke wanken a famfon masallacin mai unguwa." Husna tayi sororo tana kallon Nana, Ni'ima dake kusa da ita a zaune tana cin nata tuwon sai ta dubi Nana tana taɓe baki tace "kema dai Nana da jawa kai magana kike, banda haka tsakani da Allah a ina Ma'u zata iya buga tuka-tuka? Kuma ma naga nan shekaran jiya da aka yi wahalar ruwa naje dibo na wanka Baba ya ganni kina jin faɗan da yayi tamin yace karna sake zuwa ɗiban ruwa, shi ne kuma yanzu zaki turata?" "Na tura tan, nace na tura tan uwata, ke babu dama ayi magana sai kin samu abin faɗa, sallamammiyar yarinya yadda kika san bani na haife kiba duk wani halin ubanki kin kwashe, to saita ɗebo ɗin in yaso in uban naku ya dawo saiki faɗa masa nasa uwarki Ma'u ɗiban ruwa." Nana tayi maganar da masifa kamar zata rufe Ni'ima da duka. "A'a ni meye nawa a ciki kuma Nana? Daga faɗar gaskiya." "Ba'a son gaskiya taki." Sai kuma ta juya wajen Husna dake tsaye tana kallon su tace "ke kuma kin ɗau botikin kin tafi ɗebo min ruwan ko saina taso kanki? Munafuka kika tsaya kina kallon mutane." Jiki a sanyaye ta dau botikin ta tafi ɗiban ruwan. Nana kuma taci gaba da zazzagawa Ni'ima faɗa "ke babu dama nayi magana saiki sani a gaba kina min tsari kuma saboda rashin sanin daraja ta a gaban wannan munafukar yarinyar kike yi salon ta raina ni, kema kinyi min bare ita? Aikin banza aikin wofi." Nana keta zuba ruwan masifa Ni'ima kuwa ko a jikin ta taci gaba da uzurin gaban ta kamar bata san da ita Nana ke faɗan ba. .......layi ake a famfun sosai wanda yafi ƙarfin ka ya ture ka ya diba, duk wanda Husna ta riga su zuwa tana kallo suke ɗiba su tafi, tana tsaye a gefe riƙe da botikin ta a hannu. Babu wanda ya damu da tsayuwar ta a wajen bare yace layin ta yazo bari ta ɗiba, to famfo ne da kowa ƙarfin shi ke ɗiba masa ruwa. Tana nan tana zaman jiran gawon shanu Abba da Jaku nan su suka zo shan ruwa, cikin ƴan sakwanni suka tarwatsa mutanen kan famfon suka fara bawa Jakunan su ruwa, har suka gama ban ruwan babu wanda ya zo wajen da sunan zai ɗebi ruwa, dan sun san halin su basu da kirki yanzu in ka musu wasa zasu fasa maka bokiti kuma sun fasa banza, sanin wannan halin nasu yasa kowa ke matsawa ya basu waje saisun gama sun tafi sai kowa yaci gaba da ɗiban ruwan sa, har sun gama zasu juya Abba yaga Husna tsaye da bokiti a hannu. "Ke zo nan." Abba ya kirata da gwarjin muryar shi ta masara ji. Husna bata zoba dan ko kaɗan bata ɗauka da ita yake ba, saida ya sake kiranta sannan ta zo inda yake, yace "Waya turo ki nan?" "Nana ce." "Nana." Ya sake maimaita sunan sai kuma ya karɓi botikin ta ya jefa wa wani acikin su yace "kai Maɗi zuba mata ruwa tabar wajen nan." Yana faɗin haka ya ɗane kan jakin sa yayi gaba. Wanda Abba yasa ya zuba mata ruwan saida ya cika mata botikin ya ɗora mata sannan ya kada nashi Jakunan yabi bayan su Abba. Duk da babu nisa tsakanin gidan da Famfon amma da ƙyar ta kawo ruwan gida saboda bokitin yafi ƙarfin ta. "Ni'ima kama mata ta sauke ruwan nan dan wallahi in kika fasa min botiki ubanki saiya biyani." "Kema uban wa ya saki cikowa." Ni'ima ta fada tana sauke wa Husna ruwan tana hararar ta. Washegari ma haka ce ta faru, sannu a hankali zuwa ɗiban ruwan wanke wanke ya shiga cikin jerin ayyukan da Husna keyi a gidan. yauma kamar kullum ta ɗebo ruwa tana tafiya ta wuce ta gaban su Abba a zaune a dabar su suna busa wiwi tazo ta wuce su, Maɗi ya bita da kallo sai kuma ya juya yana duban Abba dake murza wiwi yace "wai yarinyar nan dama a gidan ku take?" Abba ya dubi Husna data ɗanyi nesa dasu sai kuma yace "eh ƴar gidan Baba Abdullahi ce." "Shege Abba naga kana kula ta kodai kana ciki ne?" Wani a cikin su ya faɗi haka yana dariya. Abba ya harare sa sai kuma yace "kai fa banza ne mezan samu anan inna bita, kawai dai." Sai kuma yayi shiru. "Maɗi yayi dariyar ƴan iska yace "wallahi ban yarda da kai ba Abba munfa san baka abu dan Allah, amma kuma tayi ƙarama fa dan naga ko eah abun nan bata fara ba babu abin da zaka samu." Saida Abba ya zuki wiwin shi ya busa hayakin ta sama ta bade masa fuska sannan yace "zasu fito in sukaji wannan." Ya ware yatsun shi guda biyar sauran abokan iskancin sa suka kwashe da dariya. Maɗi na dariyar mugunta yace "shege Abba kasan takan tsiya gashi kuma yarinya ta tara mazaunai duk da ƙarancin shekarun ta." "Ina faɗa ma wannan in taji Maza za'a yi mace fa." Haka suka rinƙa maganganun banzan su akan Husna da duk wacce ta zo wucewa ta gaban su. *****Yawan kukan da Husna keyi in taje kwanciya bacci yasa ta kamu da ciwon ido mai zafi, amma duk da haka Nana bata ɗaga mata Kafa, Baban ta ya kaita Cemist aka bata magani nasha dana digawa, kullum in zata kwanta da kanshi yake sa mata, yanzu harta fara sabawa da kwana tare da ragunan. Har maganin ya ƙare aka kuma siyo mata wani idon bai warke ba saboda yawon aiki da take yi da shi a rana, ido kuma baya son wahala duk lokacin da tayi aken rana ta tawo gida haka idon zai cakwale ya sake yin ja. Babu wanda ya damu koya kula da halin da take ciki, Baban tane kawai ya damu da lafiyar ta shi kuma sai Magarba yake dawowa gidan wannan yasa bai san mai yake faruwa ba. Yau Nana ta sata shara, tana sharar tana share ido tsabar ƙura ko ganin gaban ta batayi sosai. "Kina min ba daidai ba saikin sake gwanda ma ki maida hankali kiyi mai kyau." Nana ta faɗi haka lokacin da ta fito taga yadda take sharar sama sama, dan da gaske bata iya share gida mai rairayi ba. Kanta gama sharar tayi jargaf da gumi ga ruwa nabin idan ta, da dabara ta ɗebi ruwa a buta ta fara wanke idonta amma ina yau jin ciwon idon take har cikin kanta. Tana tsugunne a bakin makwarara Nana ta fito ta dube ta, sai kuma ta kalli cikin gidan kwata kwata bai sharu ba saboda rashin iyawa da batayi ba ga idan ta da bata ganin inda take sharewar da kyau saida dabara. "Lallai ma wannan ita ce sharar dana saki? To ai saiki tashi ki maimaita." "Ba zata maimaita ba." Abba da shigowar shi gidan ke nan ya faɗa yana cogewa a ƙofar gidan yana kallon Nana a ɗage. "To uban mutane kai asu wa da har zaka sawa mutane baki?" Nana na rufe bakin ta Abba yace "ni a wanda na isa, ke kallon kifa kawai nake dama kin kular dani jiya nayi shanya kin haɗa mini kaya, to wallahi in kika sake shiga sabga ta sai nayi maganin ki, bani da kyau fa, bar ganin ina ɗaga miki kafa." Abba yayi maganar yana wani ciccijewa. Nana tace "An tattare ɗin ai ba kaika ɗaura min igiyar ba da zaka zo ka baza Kayan dattin ka akai kaki kwashe wa." "Ke ni kike faɗawa haka?" Abba yayo cikin gidan yana ɗan layin da kana gani kasan a buge yake. "Daga ciki Ni'ima tace "wallahi Nana in kika kula wannan komai yayi miki yawa banza babu abinda za'a masa, hmmm bashi da mutumci dan baki sani bane." "Hhhhh faɗa mata dai yarinya, ita bata fita ke kuma mun haɗe dake a waje dole ki fita sanin karatun." Abba ya faɗa yana dariya. Nana tayi cikin ɗakin ta da sauri tana zagin shi. "Debabbe wanda bashi da albarka, yo iyayen kama baka bari ba bare ni, ɗan isaka." Husna dai tuni ta zare jikin ta ta shige ɗaki da ƙyar ta iya diga maganin ciwon idonta ta kwanta, kuma sai Allah ya taimake ta har bacci ya ɗauke ta Nana bata neme taba kodan Abba na gidan yana zuba rashin mutumcin ne oho! Ita dai gaba ta kaita koba komai ta samu ta huta yau. Bayan kwana biyu idan ta ya ɗanyi sauki saidai har yanzu da sauran ciwon. Kamar kullum yauma saida Baban ta ya tabbatar ta kwanta yasa kuba ya rufe ɗakin ta waje sannan ya koma ɗaki ya kwanta. Wajen ƙarfe biyu na dare Husna taji kamar ana taɓata ta sake juyawa ɗaya barin tana ɗan kunkuni irin na mai bacci. Abba da yayi likimo a gefan katifar da take kwance ya zare hannun shi daga kan mazaunan ta da yake shafawa, saida yaga ta koma baccin sosai sannan ya sake maida hannun sa jikin ta yana matsa mata ɗuwawo yana wani lumshe idon iskanci. Hannun

Chapter 14 of 31