ba wannan ba, alfarmar data bawa ƴaƴan shi da matan shi da sauran mutanen gari da suka sanshi suka san tsatstsauran ra'ayin sa mugun Mamaki.
Akan sa Alhaji Ƙadiri ya aje aƙidar sa tsarin sa da tsatstauran ra'ayin sa naƙin bawa Bahaushe Auran ƴaƴan sa, shi Mai Kano Alhaji Ƙadiri ya rufe ido ya wanke yarshi mafi soyuwa a ransa ya bashi Auranta alokacin da shiba kowa bane face Yaron rumfar shi maici a ƙarƙashin sa, bai duba talaucin sa ba, bai kalli babunsa da ƙyauyen daya fito ba, bai kuma kalli bashi da komai ba, sai tsagwaron tsabar yarda da amincin dake tsakanin su kawai ya duba yayi masa wannan Alkhairi.
Sai dai kash ya kasa ya kuma gaza, yau yayi watsi da wannan aminci na Mai gidan shi Ubanshi a duk faɗin garin Kano kuma Surukin sa, ya karya alkawarin sa ya kuma lalata amincin sa alokacin da baya nan, yayi nesa da wannan Duniyar tamu gaba ɗaya, ƙasa ta daɗe da rufe masa ido, yaci Amanar shi ya sakar masa Safiya a wulaƙance.
Yaci amanar Mutumin daya amince masa ya fifita sa ya kuma ɗaga darajar sa akan duka Hausawan Duniya.
Abdullahi yayi nisa cikin tuna hannayen sa dafe da kansa idanunsa a buɗe suke yana kallon ƙasa amma wallahi sai jinsu yake kamar a rufe dan baya ganin komai baya iya hango komai sai fuskar Ubangidan sa dattijon arziki Alhaji Abdulkadiri Mai Shinkafa a shekarun baya alokacin da ya shigo cikin Birnin Kano neman kuɗi shi kaɗan shi bashi da komai, daga shi sai rigar jikin sa da tsohuwar ledar kinsuwai baƙa riƙe a hannun sa wacce Dije ta basa yasa wuƙa da laujen yankan rake sai riga da wandon sa kala ɗaya. Gani yake shekaru da lokutan na gifta masa kamar yanzu ne abunbuwan ke faruwa....
_*WRITING.....✍🏻*_
*_MUTUWAR AURE.....!_*
_(Ƙaddarar wasu ƴaƴan)_
*_Kanawa ne👌🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
_BOOK 1_
*_FREE PAGES_*
________________
*_WHATSAPP GROUP👇🏻_*
https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3?mode=gi_t
https://wa.me/+2348064789370
_________________
_EPISODE 6_
SHEKARU GOMA SHA HUƊU DA SUKA WUCE
Lokaci ne na hunturun sanyi, a yammacin daya haɗa hazo da ƙura a garin Kano, da misalin ƙarfe shida na yamma Mota kirar J5 ta tsaya dai-dai tashar Yankaba ta sauke Samari ƴanci rani data ɗebo da ga mabanbantan ƙyauyukan Jihar Jigawa, a ƙalla zasu kai su goma ko wannen su ka kalla fuskar sa wasai zaka ganta banda Mai Kano da kana ganin yanayin sa zaka gane bako ne shi a tafiyar.
Samarin ba yan gari ɗaya bane saidai duk sunsan junan su saboda ƙyauyu kan su maƙotan juna ne, suna yawan haɗuwa da juna a wajen ƴanmatanci ko shagalin bukukuwa irin na karkara, sannan duk wata tafiya irin wannan a zuga suke yinta, gaba ɗayan su ba zasu wuce shekaru a shirin zuwa a ashirin da biyar ba.
Matasa ne dake zuwa ci rani cikin garin Kano duk shekara, duk abinda kakar shi ce (lokacin sa) shi suke siyarwa kamar irin su yalo, ɗata, goba, karas, rake da sauran su, kamar dai yanzu daya kasan ce lokaci ne na sanyi Kakar rake, zaka samu ire-iren waɗannan matasa ako ina na lungu da saƙo a cikin birnin Kano suna yawo da rake a Baro suna siyarwa.
Ba wasu kaya ne dasu ba yawan cin su leda ce kawai a hannun su wacce suke sako huƙaƙe da kayan sawar su da bai wuce kala ɗaya zuwa biyu ba.
"To mufa anan zamu rabu nida Mai Kano nan Sauna zamu shiga, kawai sai mun sake haɗuwa, Mai Kano zomu haura Magarba ta gaba to, su Hadi sai mun haɗu."
Wani baƙin matashi da ba zai wuce sa'an Mai Kano ba ya faɗawa sauran abokan tafiyar su.
"Eh Ɗanladi kufa ƴan gidan Talatu ne, muma da Ƙafa zamu tsallaka ai ba nisa nan cikin kasuwar Yankaba ne."
Wani daga cikin matasan ya faɗa. Sallama suka yi Mai Kano da Ɗanladi suka shiga kwanar Sauna, suna tafe Ɗanladi yana sake yiwa Mai Kano bayanin garin Kano da yadda suke neman kuɗi.
Wannan shine zuwan Mai Kano na farko tunda yake kuma bai taɓa wuce Gezawa ba, tun kan suyi Aure yaso ya fara zuwa neman kuɗi cikin birni kamar yadda sauran abokan shi suke zuwa duk rani amma sai Mahaifin sa Aramma Abdussalamu ya hanasa, kasancewar sa mutum mai tsananin biyayya sai bai taɓa yiwa Aramma musu ba, sai yanzu bayan tsawan lokaci sannan ya amince masa shima ya fito neman na kansa kamar sauran samarin gari.
Lokacin da Aramma ya kira shi yace ya amnice masa ya shirya yabi ƴan ci rani cikin binni abun ba ƙaramin daɗi yayi masa ba dan abune da ya daɗe yana ƙulafaci dason zuwa..
Gidan Hajja Talatu mai Baro ƙaton gida ne mai haɗe da babban gareji inda take zube tarin Barukan ta da Kurorin ruwa, Hajja Talatu Baro Baro ƴar kasuwa ce sosai kusan babu abinda bata siyarwa amma amfi sanin ta da Talatu Baro Baro saboda ita ce sana'ar da tayi shura akai, mutane kuma da ita suka santa sosai, saboda tarin matasa ƴanci rani dake taruwa a gidan ta, layin gidan ta kusan duka gidajen tane data zuba ƴan haya sai kuma ƙaton gidan ta mai tarin dakuna da take zuba matasa masu zuwa ci rani, daga ko wanne ƙyauye kuka zo zata baku hayar Baro ko kura amma fa da sharaɗin sai ƴan garin ku suna da yawa, kuma dole a gidan ta zaku zauna, duk kwanan duniya zaka biya ta Naira Ashirin ta wancan lokacin, balance ɗin Baro ko kura wannan duk sati take karɓa.
Gidan ta akwai banɗakunan wanka har guda huɗu amma fa babu na bayan gari dan haka yawancin Samarin bakin lanba suke haurawa da daddare suyi bayan gari (Kashi).
Hajja Talatu Baro Baro tana da kirki amma akwai ta da faɗa musamman in zaka mata wasa da balance yanzu za aji kanku.
Ana ƙwala kiran sallar Magarba su Mai Kano suka iso ƙofar gidan Talatu Baro Baro tun daga nesa kuma ya hango Abokan shi yan Garin su Sale da Sadi suna wanke Barukan su da lama basu jima da dawowa ba.
Suna isowa suka kashe (tafawa ) suna dariya, Sale yace "Shegen sama Mai Kano kace Aramma ya yarde maka yau? Kai amma naji daɗi."
"Wallahi kaidai bari sale jiya ya kirani yace na biyo ku Allah yasa su Ɗanladi zasu taho yau na biyo su." Mai Kano ya faɗa yana dariyar jin daɗi.
"Gaskiya labarin nan yayi daɗi, Ɗanladi sannun ku da zuwa"
Sadi ya faɗa, suka sake kashewa (tafawa) Ɗanladi ya shige cikin gida ya bar Mai Kano a wajen su Sadi, saida suka gama wanke Baron su suka yi Sallah sannan suka tafi gabatar da Mai Kano a wajen Hajja Talatu.
Hajja Talatu taga Mai Kano ta amince zata bashi hayar Baro bayan su Sale sun nuna masa gari da yadda ake kasuwar, kamar yadda yake a tsarinta kuma bazai fara biyanta kuɗin kwana ba saiya fara fita.
Godiya suka yi mata suka dawo gidan su nan fa suka tadda kusan kowa ya dawo, gida ya cika da Samari sunata hayaniya da labarai.
Sosai Mai Kano yaji daɗi dan ko kaɗan Aramma baya barin shi ya matsa daga kusa dashi, yau sai ya ji dadin ganin shi cikin Abokan sa da sauran mutanen gari yau jinsa yake a sake.
Washegari
Sadi ne ya fara fita da Mai Kano ya fara nuna masa yadda gari yake da yadda suke saida rake. Suna tafe suna hira suna tallan rake, ta cikin Haye suka fara sune har Mariri basu dawo ba sai bayan sallar Magarba, sosai Mai Kano yaji daɗin fitar duk da akwai gajiyar rashin sabo tare dashi.
Washegari kuma Sale ne ya fita dashi suka danna cikin Dakata sune har Birget, dama haka tallar tasu take babu inda basa zuwa da ƙafafun su suna tafe suna saida rake daga inda ya ƙare ko dare yayi saika juyo gida.
Mai Kano ya kai wajen sati guda su Sale ke fita dashi su nuna masa gari, saida ya gane kan kasuwar da garin sannan ya fara daukar nasa Raken.
Randa ya fara fita ta dakata ya fara yabi ta Tudun Murtala har Birget yana tallar Raken shi.
Cikin sati biyu ya goge ya zama ɗan gari gashi Allah yayi masa baiwar kasuwa yana fita kafin karfe huɗu ya saida Raken shi ya juyo gida Magarba a gida take masa kusan yana riga kowa dawowa.
Yawancin tallar shi kuma yafi yin wajen Tudun Murtala zuwa Birget Tsamiya, ya wanci ma a Tsamiya yake tsayawa da yake wajen akwai majalisar Samari da magidan ta ga tukubar mai tsire sosai yake ciniki a gun.
Sannu a hankali ya saba da ƴan wajen suka gane shi, duk randa bai ƙaraso ba Raken shi ya ƙare washegari in yaje sai sun tambaye sa jiya bai zoba, Musanman Matasan wajen sosai suke yinsa saboda nutsuwar shi da sanin ya kamatan sa, duk sanda yaci kasuwar Raken shi kanya tafi saiya share wajen tas, daga baya ma tsintsiyar kwakwa ya siya ya aje akan rumfar Ubale Mai tsire, kullum in ya gama cin kasuwa saiya dakko ya share inda ya ɓata da bawon rake, inya gama ya maida ita ya ajiye, wannan yasa sosai yan wajen ke yinsa.
Mai Kano na samun alkhairi a sana'ar shi a satin sa na uku da zuwa Kano sau biyu yana aiken kuɗi gida da Sabulun wanka da omon wanki.....
Saida Mai Kano yayi wata biyu cur a kano sannan ya shirya tafiya ganin gida babu wanda ya faɗawa zai zo kawai sai ganin shi sukayi, lokacin da ya shiga gidan su Nana bata nan taje karbo casar hatsi a Musissika sai shigowa tayi ta ganshi zaune a ƙasan bishiyar maina suna hira da Dije, ta sashi a gaba kamar yadda ta saba shi kuma kanshi a ƙasa yana bata labarin garin Kano.
Sallamar Nana tasa ya ɗaga kai ya kalleta tana tahowa inda suke a hankali cikinta ya sake tsufa, tunka ta iso ya mike ya tayata sauke masakin (ƙwarya) kanta, wani sanyin daɗi ya ziyarci zuciyar Nana ta kalli Mai Kano taga ya sake yin fes dashi, ita sai taga ya ƙara yin girma da tsayi.
“sannu da zuwa, Mai Kano saukar yaushe?”
Bai bata amsa ba saida ya turawa Dije Masakin hatsin gabanta sannan yace “Iya tace min kina fita na shigo, na same ku lafiya?”
“mun gode Allah”
Nana ta fada tana zama akan tirmin dake kusa da ita, sai lokacin kuma Dije tace mata “sannu Nana sun cire nasu ko? dan waccan casar da suka mana basu cire ba sai ladan kuɗi Salisu ya basu wai sun manta basu cire ladan su ba, Uwar Safi taji shiru ta biyo baya Allah yasa Salisu na nan ya basu Ladan kudi”
“eh, nina cire musu na yau.”
Nana ta fada tana kallon Mai Kano daya ke tsince sauran tsilli tsillin kaikayin geron da be gama fita ba.
“Yawwa ai hakan yafi, kinga yunƙura ki dakko min alasaini (Murfin ƙaramar langa, yana ɗaukar matsayin kwata) a saman ragaya na auna muku na tuwon yau sai ki leƙa wajen Salisu kiwa Gaje magana ta fito ku surfa da wuri kafin Aramma ya shigo an bushe yayiwa shanu banruwa da dusar.”
Mai Kano ya kalli Dije kamar yayi magana sai kuma yayi shiru dan ba komai yake son saka musu baki ba yanzu sai tace ya fiya tsirfa shi yasa Nana ta lalace, amma banda haka yaushe za’a ce da wannan katon cikin na Nana amma har yanzu tana surfe, duk da hakan ba komai bane a cikin karkarar tasu, mace har randa zata haihu tana iya yin casa tayi surfe kuma ta haihu lafiya, tunda abune da suka tashi akai tun iyaye da kakan ni.
Yana ta cire sauran ƙaiƙayin Geron Nana ta kawo Alasaini da kanshi ya karɓa ya gwada mata Dije na masa hirar Salisu daya tafi cin kasuwar Doko Nana tasa hannu zata dauki Geron Mai Kano yace “jeki tambayo Naja nan cikin gidan su Amadu kiji in zatayi surfau ki kai mata ta surfa amma kice bazata bushe dusa ba sai a bata kudin surfan.”
Mugun daɗin daya ziyarci zuciyar Nana saida ya kasa ɓoyuwa akan fuskarta, ita kanta tasan yanzu zata huta da ayyukan gidan nan tunda Mai Kano ya dawo dama kuma shi mutum ne mai tausayi da kulawa da yanayin mutum, danma wasu lokutan idon Dije ke sawa yabar wasu abubuwan saboda kartayi magana, amma a farkon auran su in zaiyi wanki har da nata yake haɗawa ya wanke.
Da yake a kewayen su ya keyi Dije bata taɓa kulaba, randa ta ganshi yana mata wanki kuwa yasha faɗa ba kaɗan ba har saida Aramma ya shiga cikin zancen sannan ta sarara masa, duk da haka bai daina taya ta gaba ɗaya ba in yaga aiki yayi mata yawa saiya yi musu wanki da daddare babu wanda ya sani kafin safe kayan sun bushe.
Wannan kyautata wa da tausayi na Mai Kano yasa Nana ke mugun sanshi, wannan ita ce haihuwa ta uku da zatayi amma yaran basa zama tana yayesu suke komawa (mutuwa) amma duk haihuwar nan Mai Kano indai akace cikinta ya tsufa dai-dai da sharar wajen su baya bari tayi, haka duk wani aikin wahala sai yasan yadda yayi ya taya ta cikin hikima yadda Dije baza ta ce ya lalace a ƙarƙashin mace ba, bata san zuwa Musissika karɓo casa ba saida ya tafi birni neman kudi haka bata san zuwa yiwa awaki ciwaya ba saida ya tafi.
Haƙika Mai Kano mutum ne mai tausayi da sanin ya kamata, ya banbanta sosai da saurna Mazan kyauyen, a hallaya kuwa ya banbanta da Dije tako wacce fuska, shi maihaifinshi yayo ka ma daga zubin halitta da halayya, dabi’un sa kaf irin na Aramma ne, haka dan uwanshi Salisu komai nasa irin na Aramma ne, Lirwanu ne kawai yayi halin Dije amma shima da Aramma yake kama dukan su dogaye ne sosai kamar mahaifinsu, zubin fuska dogon hanci da asalin bakar fatar Aramma ta asalin Bahaushe duka irinta sukayo, kananun idanu ne kawai suka dakko na DIJE sai autar su MARIYA ita ta dakko kamanin Dije amma itama tsayin mahaifin su tayo doguwa ce sosai.
Dije harta bude baki zata yiwa Abdullahi magana akan me zaice akai surfau dan asarar kuɗi, kamar yasan me take shirin cewa ya bi bayan Nana data miƙe da Masakin geron saɓe a kafaɗarta da cewa.
“dan Allah maza miƙa mata kizo ki wanke min kayan nan.”
Nana tace "to." ba tare data waiwayo ba tayi gaba tana murmushi har haƙoran ta na bayyana dan har ranta tasan saboda gudun maganar Dije yace haka bawai dan wanki zai bata da gaske ba.
Jin abinda Mai Kano ya faɗa yasa Dije hadiye abinda tayi niyyar faɗi.
Nana na kai surfan ta dawo ta tarar baya wajen.
Dije ta raba tsarabar daya kawo ta bata tasu, ta karɓa ta wuce ɓangaren su a kwance ta tadda Mai Kano.
Sannu ya sake yi mata ta amsa, saida ta aje tsarabar sannan ta kalleshi tace “ina kayan da za'a wanke maka?”
Yana daga kwancen yaɗan juyo ya kalleta sai kuma ƙasa ƙasa yace “babu wani wanki, zanyi da kaina inna tashi kwanta ki hutawa rankai kan lokacin ɗora sanwar dare yayi.”
Cikin jin daɗin maganar sa Nana ta samu waje ta kwata zuciyar ta fari tas yaushe raban ta da baccin rana in batayi karya ba ai tun tafiyar sa Birni.
******Satin Mai Kano ɗaya a gida ya dawo Kano yabar Nana da kewar shi. Washe garin dawowar sa ya ɗauki rake kamar yadda ya saba yana tafe yana siyarwa har ya kai Birget Tsamiya dai-dai inda yake aje baron shi kusa da Ubale mai tsire ya tsaya muta nan wajen suka fara tambayar sa kwana biyu bai zoba lafiya? Cikin yanayin shi na nutsuwa yace musu.
“wallahi gida naje sai jiya na dawo.”
Abdussamad yana dariya yake tsokanar shi "kodai mai ɗakin ka kaje gani, dan Abdullahi baka rasa Aure.”
Shi dai Mai Kano baiyi magana ba sai murmushi da yayi, dan yasan halin Abdussamad da tsokana inya kula shi to kowa sai yaji su.
Abdussamad mutumin shine sosai suke shiri baza su wuce sa’anin juna ba.
Abdussamd shine da na huɗu ga Alhaji Abdulkadiri Mai Shinkafa gidan su na kallon tukubar Ubale mai tsire titine kawai ya raba tsakanin su.
ALHAJI ABDULKADIRI MAI SHINKAFA
Beyerabe ne kuma shahararran ɗan Kasuwar da yayi suna sosai a cikin sabuwar kasuwa (Kasuwar Birget) duk daga inda ka taho indai ka shigo Birget kace gidan ƘADIRI MAI SHINKAFA ko yaro ka tambaya zai kaika.
Alhaji Ƙadiri nada wadata sosai yana cikin masu kuɗin Birget ƙaton benan gidan sa ginin azara kaɗai inka kalla kasan Allah ya rufa masa asiri, bene ne na azara irin ginin da da sai wane da wane.
Ɗan kasuwane sosai dake da rumfuna acikin kasuwar Birget kusan duk wani nau’in kayan abinci babu wanda baya siyarwa sai dai anfi sanin sa da Mai Shinkafa saboda ita ce kasuwancin sa na farko ɗaya farayi tun yana matashin saurayi matan shi biyu Asma’u (Momma ) itace uwargidan shi kuma uwar manyan ƴaƴan shi, saida ta haifi yara uku sannan ya kara Auren matar shi ta biyu Fatima Maman sama, dukan su Yarabawa ne.
Momma Asma’u yaranta shida biyar maza ɗaya mace, Abubakar shine babba (Baba Habu) Ja'afar ke binsa sai Abdulgaffar, Abdussamd, Abdulganiyyu sai autar su Safiya saida ta cire rai da sake samun haihuwar gaba ɗaya sannan Allah ya bata wani cikin tazarar shekaru tara ce a tsakanin Safiya da Abdulganiyyu.
Maman sama yaran ta biyar dukan su mata Zainab (yaya Femi) itace babba mai binta Mansura, Tawakkaltu, Asma’u (Momi) sai Sakina, dukan su a dakin Momma suka taso Maman sama tana yaye su Momma take karɓa taci gaba da rike wa har Auran su haka yaran Momma kusan komai nasu Maman sama suke tinkara kafin kaji sunce Momma sau ɗaya sunce Mama babu adadi komai nasu itace, in baka sani ba zaka ɗauka Mama keda yara Maza Momma keda mata sosai ake zaman lafiya a gidan Alhaji ƘADIRI babu rigima da sauran hayaniya irinta kishiyoyi, hatta yaran basa iya banbance mai girki a cikin su sai insun ganki a tiraka to sunsan kece da miji.
Yadda iyayen kansu ke haɗe haka ma yaransu maza da matan kansu ke mugun haɗe babu maganar dan wancen ɗakin da wannan ɗakin dukan su abu ɗaya ne kamar yadda sukaga iyayen su.
Alhaji Abdulkadiri Mai Shinkafa mutum ne mai kirki ga kyauta da sadaka, yana da san mutane kowa nashine amma fa yana da faɗa inka taɓoshi bashi da sauki mafaɗaci ne sosai, ko jikokin sa baya yiwa wasa sam bai yarda da wani abu wai shi wasan kaka da jika ba.
Mutum ne mai riƙo da Yaren shi bai yarda ayi wani yare a gidan saba sai Yarabanci da turanci musamman in yana gida turancin ma baka isa kayi yaji ba. Wannan tsarin nasa yasa yaranshi suka tashi da yaren su sosai yadda ko magana sukayi kanaji sai kasan yare ne, Hausa kuwa a waje da makaranta suka koyeta.
Yaran shi maza da mata duka sunyi karatun boko har zuwa matakin degree matan kuma iyakar su diploma yake musu aure ya baki jari ki rinƙa juyawa a tsarinsa bai yarda da zaman banza ba, ko kaɗan bai yarda ka zauna sai an baka ba, a’a ka tashi ka nemi naka.
Baba Habu da Ja’afar ne ma'aikatan governorty amma duka sauran yan kasuwa ne mazan su da matan su, suma kuma suna ɗan taɓa harkar kasuwancin sai dai ba sosai ba.
Alhaji kadiri mutum ne mai tsananin ra’ayi da ƙabilanci musamman akan ƙabilar mallam Bahaushe. Ya yarda yayi ko wacce alaƙa da Bahaushen mutum amma babu auratayya duk tsakanin ku dashi akan wannan yanzu zaku raba hanya.
Sam bai yarda da Bahaushe akan aure ba.
Kallon su yake wanda basu san darajar mata ba haka basu ɗauki sakin aure a bakin komai ba, wannan yasa yake da tsanani, a tsarinshi da tunanin sa babu shi babu haɗa iri da Hausawa har abada, ko wanne yare ne kai zai iya baka Auran ƴar sa amma shida Bahaushe a’a babu wannan maganar a tsakanin su, mutanan unguwa da abokan huldar shi na kasuwanci duk sunsan wannan aƙida da tsaurin ra’ayin na Alhaji Abdulkadiri dan haka indai kasan kai Bahaushe ne ma baka taya ƴaƴan shi dan bazai taɓa baka ba, manyan mutane Hausawa sunsha neman auran ƴaƴan shi wa kawunansu ko ƴaƴan su amma fir sai ya hana su, anyi haka dashi basau ɗaya ba basau biyu ba.
Yaran shi ma duk sun sani shi yasa basa kula mazan Hausawa...
_*WRITING.....✍🏻*_
*_MUTUWAR AURE.....!_*
_(Ƙaddarar wasu ƴaƴan)_
*_Kanawa ne👌🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
_BOOK 1_
*_FREE PAGES_*
________________
*_WHATSAPP GROUP👇🏻_*
https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3?mode=gi_t
https://wa.me/+2348064789370
_________________
_EPISODE 7_
~~~*Sannu a hankali sabo ya shiga tsakanin Mai Kano da jikokin Alhaji Kadiri musamman Baffa karamin jikan shi, kullum in yazo saiya fere rake ya yayyanka yayiwa yara sadaka, wannan ya sake ja masa farin jini sosai wajen yaran unguwa da iyayen su musamman jikokin Alhaji Kadiri nan da nan yara suka saka masa Baba Abdullahi sosai sunan ya shiga bakin manya da yara.
Lokaci daya shaƙuwa ta shiga tsakanin Mai Kano da Baffa, yaron shekarun sa bazasu wuce hudu zuwa biyar ba, yanzu kullum a wajen shi yake wuni yana zuwa yake gudowa daga gida ya zo yajen sa ya zauna, tare suke zama akan bencin da yake zama, komai ya siya tare da Baffa suke ci haka kawai shima Allah ya ɗora masa san yaron, sosai Baffa ya shiga ransa.
Da farko Momma taso ta hana Baffa zuwa wajen Mai Kano sai Abdussamad yace a barshi
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 6 Chapter of 31