.......Tun bayan jan Husna da Indo tayi yake zaune a wajen yana jiran dawowar ta amma sai yaji shiru wajen bishiyoyin da yaga sunyi yabi da kallo wajen ya ɗanyi duhu da yawa duk da akwai farin wata amma ba lallai ka iya ganin wanda ke zaune a kasan bishiyoyin daga nesa ba sai in kazo kusa dasu.
Yana dogara Sandar shi ya biyo ta wajen yana ɗan waiwayen ta inda suke, wani mashin ya gani a kafe a gaban ƙatuwar bishiyar maina harya wuce baiga kowa ba sai kuma yaji kamar magana ƙasa ƙasa, da baya ya dawo yana buɗe idon shi da kyau, can jikin bishiyar ya hango hefan hijabin Husna wani mutum mai kiba mara tsari yana tsaye a gaban ta baya iya ganin fuskar mutumin saboda ya bashi baya, amma yana iya jiyo maganar Husna tana cewa "ka barni ni gida zan tafi Babana ya hanani kula kowa."
Husna kuwa tana fama mutumin ya rabu da ita yaƙi saboda jaraba da rashin tsoron Allah sai kuma tayi shiru tana kallon ɗan Union da abunda yake ta roƙon ta taɓa masa zai bata kuɗi da yawa har wani rufe ido yake yana numfashin jaraba, tsautsayi ne ko ganganci ko kuruciya da rashin wayo yasa Husna ta yanke wa kanta shawarar kawai bari ta taɓa masa abun danya barta ta tafi gida tana miƙa hannun ta zata taɓa dai-dai lokacin kuma ya zagayo ta ɗaya gefan akan idanun shi ta miƙa hannun ta zata taɓa taji an jayowo ta baya da wani mugun ƙarfi.
Kanta tantance waye ya jawota da abunda ke faruwa taji an sauke mata wasu masifaffun marika guda biyu a ciki ƴan sakonnin da basu gaza biyu ba sai kuma ya turata bayan shi ya shaƙi wuyan Dan Union daya tsorata da ganin mahaukaci a gaban su.
Kan ɗan Union ya gama tantance waye har ya buga kanshi da jikin bishiyar a jejjere yake kifa masa marika ta hagu da dama Ɗan Union tsabar azabar marikan da rudewa sai ya kasa ihu, ga wajen babu mutane sosai, ga ihun waƙe da gadar ƴan mata ba lallai aji sautin marikan ba.
Husna kuwa saida ta faɗi a kasa kanta ya juya taga wasu taurarin azaba sun gifta ta gaban Idanun ta, takai wajen minti biyu kanta gama dawowa dai-dai.
"Innalillahi Yaya."
Ta faɗa tana miƙewa tsaye tayi wajen shi ganin ya shaƙe wuyan Ɗan Union a jikin bishiyar idanun sa sun yi wani iri kamar za su juye zaboda azabar shaƙa wandon shi ya zazzago ƙasa ga tsaraicin shi nan a fili.
"Yaya dan Allah ka sake shi karya mutu."
Wannan furucin na Husna shi yasa ya sake sa ya faɗo ƙasa tim bai sake sakon ɗaya a wajen ba yaja hannun Husna da mugun ƙarfi suka bar ɗan Union a wajen riƙe da maƙogwaro yana maida numfashi da ƙyar.
Da wani irin sauri yake jan ta tana masa magana bai tsaya ba, saida ya kawo ta har ƙofar shiga cikin gida sannan ya jefa ta ya juya zai bar wajen ta sake biyo shi tana masa magana ya juyo a wani irin fusacen da bata taɓa gani ba ya ɗaga Sandar hannun sa yayi kamar zai dake ta, ta koma baya da sauri ta shige cikin gida.
Har ya bar wajen babu wanda ya ganshi saboda ta baya ya biyo da ita, da wani irin sauri yake barin cikin garin gaba ɗaya.
Husna kuwa a mugun tsorace ta shige gida tana mai da numfashi, Ramma na mata magana bata tsaya ba tayi ɗakin da take kwana ta shige ta kwanta ta dukun kune jikinta, take kuma ciwon kan daya fara zame mata jiki ya rufe ta, sosai take jin ciwon kan har cikin Idanunta ta.
Dan Union kuwa yana samu ya dawo dai-dai ya ja wandon shi ya ɗaure bai tsaya neman abokin tafiyar saba ya buga mashin ɗin sa da mugun gudu yabar garin a mugun tsorace dan shi kaɗai yasan abunda ya gani....!
_*WRITING.....✍🏻*_
*_MUTUWAR AURE.....!_*
_(Ƙaddarar wasu ƴaƴan)_
*_Kanawa ne👌🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
_BOOK 1_
*_FREE PAGES_*
________________
*_WHATSAPP GROUP👇🏻_*
https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3?mode=gi_t
https://wa.me/+2348064789370
_________________
_EPISODE 24_
Tun a daren Lirwanu yaso ya karɓi ɗan kunne da awarwaron Husna sai kuma ya barwa safe, wajen ƙarfe shida na safe Aramma yana Masallaci dan baya dawowa da wuri sai rana ta fito yayi walaha, Lirwanu ya shigo gidan ya cewa Ramma ta kira masa Husna.
Tana kwance cikin zazzaɓin data kwana dashi Ramma ta shigo tana tashin ta taji jikin ta zafi zau.
"Subhanallahi Ma'u dama baki da lafiya ne?" Ramma ta faɗa tana zama akan gadon karan da take kai a kwance.
Tsabar ciwon kan dake cin Husna kasa magana tayi Ramma ta fito daga ɗakin tana neman Yaro ya siyo mata magani da koko, Lirwanu da yaji shiru ya kasa haƙuri ya biyo bayan ta suka haɗu a cikin gida yace "Ina Ma'un take?"
"Wallahi tana ciki bata da lafiya."
"Kan uban can ni zata yiwa bariki.....wato saboda tasan zan neme ta shine zata yi ƙaryar ciwo to ko mutuwa take yau sai ta kawo su."
Lirwanu ya tari numfashin Ramma cikin hargowa, sai kuma "wuwuuuuuf." Ya daka tsalle ya fizgo tsimagiyar maina ya zuge ta yayi hanyar ɗakin da Husna ke kwance, Ramma na ganin haka ta bisa a baya tana fadin.
"Dan Allah Lirwanu karka taɓa ta wallahi bata da lafiya, wai mema tayi maka ne?"
"Kut*****mar kaza kazan ki tamin."
Lirwanu ya luƙawa Ramma zagi yana shigewa cikin ɗakin baiyi wata wata ba ya miƙa wa Husna hannu cikin bala'i yace "ke tashi bani abun hannun ki da ɗan kunnen ki ko naci ubanki yanzun nan."
Husna taja numfashi da ƙyar ta ɗago kanta ta dube sa da jajayen Idanun ta da suke mata mugun ciwo, tace "ba...s....sa wa...j....jena." ta faɗa muryar ta na rawar zazzaɓi, Ramma ta zagayo tace "me kika masa ne?"
Lirwanu kuwa wani baƙin ciki da ɓacin raine ya sake turniƙe shi yace "Mu zaki yiwa mugunta da munafunci Ma'u?"
Bai bari ta sake magana ba ya rufe ta da duka, Husna tayi ihun azaba dan sosai bulalar ta shiga jikin ta ga kuma zafin ciwo daya sake rura wutar abun, Ramma ta shiga tsakanin su Lirwanu da idanun sa suka rufe da san abun duniya da hango yawan kuɗin da zata ja ya rasa kawai saiya haɗa ita da Rammar ya rinƙa duka suna ihun tare, Husna ta fado daga gadon dan tuni ya ture Ramma gefe ya rinƙa dukan ta babu mai ce to Zahara da taji ihun Ramma da zage zagen Lirwanu tayo ɗakin da gudu tana ganin abinda ke faruwa ta tsaya daga waje dan tasan halin Lirwanu baiki ya haɗa da ita ba.
Ramma na kuka tana roƙon shi ya daina dukan Husna amma bai saurare taba dukan ta yake yana tambayar ta inda takai ɗan kunne da awarwaron ta, Dije ma tazo ɗakin bakin ta na kumafa tana zagin Husna da kiranta muguwa dangin kafurai.
"Wallahi ka nina mata jiki saita faɗi inda ta kaisu shegiyar yarinya mai baƙin hali irin na kafurar uwar ta, ke yanzu har kinsan kiyi mana mugunta da baƙin ciki, to wallahi yau ko zaki mutu saikin faɗi inda kika kai su kika ɓoye." Dije ta faɗa ranta na suya da tsanar Husna.
Tun daga waje Aramma yake jin hayaniya har ya shigo cikin gidan, magiyar Ramma da bakaken maganganun Dije yajiyo daga ɗakin da Ma'u ke kwana yayi hanyar ɗakin da sauri.
"Innalillahi wa inna ilaihirraju'un, kai Lirwanu kana da hankali kuwa? kashe ta zakayi? Kulla wallahi inka sake taɓa yarinyar nan saina yima abinda bakayi zato ba." Aramma ya dakawa Lirwanu tsawa yana kallon yadda yake haki tsimagiyar hannun sa duk ta guggutsire.
Aramma ya kalli Lirwanu ranshi a mugun ɓace yace "ka kyauta Lirwanu ka kyauta Lirwanu abinda kayi yayi maka dai-dai yanzu yar ɗan uwan ka kayiwa wannan dukan kamar ɓarauniya?"
Baba Lirwanu bece komai ba ya fita daga ɗakin yana jin abinda yayi shine dai-dai sannan yana cin alwashi a ransa da wallahi Husna ko zata mutu saita fito da warwaro da ɗan kunnen.
"Zanga karshen taurin kanki Ma'u." Yayi jifa da sauran bulalar hannun sa ya fice daga gidan.
Dije ma ficewa tayi daga ɗakin Aramma da ransa yayi mugum ɓaci ya ɗago Husna da numfashin ta ke wani irin gudu kamar zata suma dan ta daku ba kaɗan ba.
"Wallahi kome yarinyar nan ta ma Lirwanu kayi mata irin wannan dukan sai nayi mugun saɓa maka, mutumin banza mutumin wofi."
Aramma ya faɗa yana sa Ramma da Zahara su kamo ta su fito da ita dan ba zata iya tashi da kanta ba.
Aramma kuwa sai ya hau bambamin faɗa yana faɗin "wallahi dole Abdullahi yazo ya ɗauki ƴar shi, bazan zama tsohon banza ba a garin nan, ace inaji ina gani Lirwanu ya illata yarinyar nan ba, ba zai yiwu ba." Cikin ɓacin rai Aramma yake maganar.
Duk nuna halin ko in kula irin na Zahara yau saida ta tausaya wa Husna.
"Yanzu tsakani da Allah banda baka isa kayi magana ba Lirwanu yasan Ma'u bata da lafiya yayi mata wannan dukan?" Zahara ta faɗa tana riƙe baki, Ramma ta kasa magana sai hawaye take share wa ganin yadda jikin Husna ya sake rurewa da zazzaɓi.
Cikin gidan ta koma ta aika asiyo mata koko da magani, Zahara ma waje ta fita.
Husna na kwance tana jin wani irin ciwo a cikin kanta da idanun ta.
Ramma na can tana neman Yaron da zai siyo mata magani a shagon Sunday, babu wanda ya kula ta lallaɓa tana bin jikin danga dan bata iya tsayawa da kyau saboda zazzaɓi ta fita daga gidan tana layi kanta babu dankwali ƙafafun ta banu takalmi daga ita sai zani da riga bulawus ɗin data tattare saboda dukan da tasha, jikin ta kuwa yayi butu butu da ƙasa.
Husna tafiya take badan tasan inda take saka ƙafafun taba dan bata iya ganin gaban ta da kyau, babban burin ta kawai shi ne ta fice tabar gidan, kai tabar garin ma gaba ɗaya, bata burin ta sake dawowa cikin gidan su ko a mafarki.
A kusa da bakin titi dai-dai bayan gidan kallo kallo ta faɗi ta kasa tashi Garba ya zo wucewa ya ganta kwance a kan hanya numfashin ta na fita da sauri da gudu yayi kanta yana kiran.
"Ke wace a nan kwance?" Ya faɗa yana zagayawa barin fuskarta.
"Innalillahi Ma'u ke Ma'u daga ina kike?" Ya faɗa yana jinjiga ta sai tayi luuu ta sume a wajen, Garba yayi wuru wuru ya rasa yadda zai yi da ita ƙwaƙwalwar sa ta toshe ya kasa tunanin kirki, yana haka Bahari ya zo wucewa ya gansu a wannan hali a sukwane ya daga Husna babu ko dar ya ɗauke ta Garba yarufa masa baya da gudu gudu Bahari yake tafiya da ita a hannun sa kamar bai dau komai ba, titin ya tsallaka da ita sai kuma cikin tashin hankali ya cewa Garba "tare mana mota mu miƙata asibiti tafa sume."
Garba bai yi tunani na biyu ba ya fara tare musu mota, mota na tsayawa Bahari ya shige bayan ta yana faɗin "Doko zaka kaimu dan Allah yi sauri, Garba faɗawa ƴan gidan su tana asibitin Doko."
Bahari na rufe bakin sa kuma mai motar yaja ta da mugun gudu suka cilla saman titi.
Garba kawai sai ya saki baki yana kallon motar data daɗe da ɓace wa ganin sa.
Sanda Garba ya gama yiwa Aramma bayanin abinda ya faru ya miƙe tsaye babu shiri yace "muje Dokon Garba ai zama bai kama mu ba."
Ramma kuwa da taji zancen Husna ta suma a bakin titi ɗan cainan hannun ta da aka kawo kokon da zata kai mata bata san sanda ya ƙwace a hannun ta ya zube ba tace "Yaushe Ma'u ta fita bamu sani ba? A ɗaki fa na barta.
Zahara ma tace "gaskiya dai nima a lungun mu na barta.
Dije kuwa budar bakin ta sai cewa tayi "in batayi haka ba ai bazata tona mana asiri a gari ba ta jawa mutane zagi."
Aramma bai bi takan zancen suba ya gyara zaman rawanin sa suka fita daga gidan Garba na biye da shi a baya.
"banda matsiyacin san jawa mutane magana ɗan wannan dukan ne har za'a ce ta suma a titi an tafi da ita asibiti, matsiyacin taurin kanta ne yaja mata wahala, da batayi taurin kai ba ai da yanzu tana nan ƙalau." Ramma ta kalli Dije irin kallon "kina da imani kuwa."
Sai kuma ta ɗauke kwanon Kokon daya zube ta wanke shi a ruwan dabobi ta shige lungun su danta shirya tabi bayan su Husna.
"Magana ta gaskiya fa Iya dukan da Lirwanu yayi wa Ma'u yayi yawa, sannan kuma yasan bata da lafiya amma ya dake ta, gaskiya dai ba'a kyauta ba." Karo na farko da Zahara ta faɗi gaskiya, Dije kuwa a tsiyace ta dube ta daga sama har ƙasa tace "Sannu mai fuska dubu yaushe kika fara sanin gaskiyar harda zaki faɗe ta, ke Zahara wallahi ki fita daga idona bana son gulma da munafuncin da kika saba."
"Oho dai....."
Zahara tayi wajen dumamen tuwon data ɗora tana mita.
_Doko Hospital_
Bahari na kaita Nurses suka shiga da ita ciki nan da nan suka fara bata taimakon gaggawa, tasha allurori saida likitan ya tabbatar da dai-dai tuwar numfashin ta sannan yasa mata ruwa ya fito Bahari na biye dashi a baya har suka shiga office ɗin sa.
A nutse Likitan ya fara yiwa Bahari bayani "Maralafiyar daka kawo ta fita daga cikin haɗari sai dai tana fama da Chronic Typhoid da kuma matsanancin ciwon kan da har yanzu bamu gano menene matsalar data haddasa mata shiba, amma in sha Allahu inta farka zamu sake duba ta in bamu fahimci komai ba gaskiya sai dai mu turaku Dutse kuje kuga Babban likita."
Bahari ya gyaɗa wa Likitan kai yana duba agogon hannun sa yace "okay yanzu zata kai kamar nan da awa nawa kanta tashi?"
"Yeah, tana iya kawai 2 hours haka."
Bahari ya miƙe yanawa likitan godiya ya karɓi paper biyan kuɗin Dr ya kwatanta masa inda zashi ya biya.
Yana baro wajen biyan kuɗin su Aramma na shigowa cikin asibitin.
"Sannu Yaro Allah yama albarka kaji, ina ita Asma'ullahin." Aramma kewa Bahari godiya tare da tambayar sa Husna
"La babu komai Aramma, tana ciki tana bacci yanzu Likita ya baro wajen ta." Sai kuma ya dubi Garba yace "sannu da ƙoƙari Garba mun gode."
Aramma yayi murmushi yace "a'a Muhammadu Bahari ai kai za'a yiwa godiya daka kawo ta akan lokaci muje na ganta in zasu bari." Bahari yayi gaba suka rufa masa baya.
Ita kaɗai ce kwance a ɗakin an ɗaura mata ƙarin ruwa bakin ta ya bushe sosai gaban goshin ta ga wasu jijiyoyi nan a kwakwkwance sun fito sosai har saman fatun Idanun ta alamar tana fama da ciwon kai mai tsanani.
"Sannu Asma'ullahi Allah ya baki lafiya, Garba dan Allah kiramin Abdullahi ai kana da number sa ko?" Aramma ya faɗa yana duban Garba.
"Eh akwai bari na kira sa" Ya zaro wayar shi daga aljihu ya fara neman number Mai Kano.
"yawwa ya daga gashi."
Bahari na ganin haka ya fita waje yana taɓa Bluetooth ɗin kunnen sa.
"Wa alaikumussalam Abdullahi kana jina ko?" Aramma ya faɗa yana riƙe wayar da kyau.
"Aramma ashe kaine bari na kira." Saiya kashe wayar ya sake kira, Aramma ya ɗaga.
"Aramma ina kwana?" Mai Kano ya gaida shi, Aramma ya katse gaisuwar iya nan da cewa.
"Lafiya muke Alhamdulillahi, inka samu lokaci cikin satin nan kazo ina son ganin ka."
"Aramma lafiya ko?"
"Eh lafiya ƙalau Alhamdulillah."
"To in sha Allahu zan zo dama jiya masu neman Auran Ni'ima sun zo mun tsai da lokacin bikin nata cikin sabon wata mai kamawa, dama inaso nazo muyi maganar."
Mai Kano ya faɗa yana wani tunanin a ransa. Aramma yace "To Masha Allahu, Allah ya kawo ka lafiya a gaida mutanen gidan." Aramma ya kashe wayar.
"Gashi Garba Nagode Allah yama albarka."
Ya miƙa masa wayar.
Bahari na tsaye a waje yana amsa kira hankalin sa yayi nisa sosai akan wayar da alama zance yake mai muhimmanci.
A bakin asibitin mai mota ya sauke Ramma, tana gano Bahari ta taho wajen sa, bai ganta ba saida tayi masa magana sannan ya juyo.
Yana ganin ta yace "zan kira daga baya."
"Okay."
Ya kashe wayar, ya rusuna yana gaida Ramma cikin girmamawar data bata mamaki sai kuma ta amsa tana tambayar shi jikin Husna ya rakata har ciki.
Bayan awannin biyu Husna ta farka jikin ta da sauƙi dan babu zazzaɓin yanzu sai azababen ciwon kan da ya saka idanun ta suka koma ja kamar an zuba mata wani abu acikin su.
Su Aramma kuwa suna waje suna jiran jin abinda likita zaice dan Bahari yayi masa bayanin yadda suka yi dashi kafin su zo.
Ramma ce a wajen ta sanda ta farka tace "Sannu Ma'u?" Husna Ta kasa amsawa sai kanta data dafe da hannu ɗaya saboda ciwon da yake.
Ramma ta kira Likita ya zo ya sake duba ta yayi wajen minti goma akan ta yana mata tambayoyi tana bashi amsa da ƙyar sannan ya fito daga ɗakin.
Bahari yana ganin shi ya taso Aramma ya biyo sa. "Yawwa kamar yadda na faɗa maka ɗazu gaskiya wannan ciwon kan nata yayi wurse dan haka zamu rubuta muku transfer zuwa Babban Asibitin Dutse."
Likitan yayi musu bayani yana faɗin Bahari ya biyo sa ya karɓi takardar transfer ɗin.
Ya bisa ya karɓo yana dawowa Aramma yace "inaga dole dai sai Abdullahi ya sani, dama ɗazu ban faɗa masa ba dan ban yi zaton abun zai kai haka ba."
"Dan Allah Aramma karka kira Baba dan kar a daga masa hankali, in sha Allahu babu abinda zai gagara, komai zamu iya biya da ikon Allah, akwai mai motar ma dana yiwa magana tunda Likita yamin maganar Dutse na faɗa masa yace inya fito sai muyi waya, in anyi mana transfer ɗin saiya tafi damu da yake ma'aikaci ne acan." Bahari ya tari numfashin Aramma da wannan magana.
"Anya kuwa ayi haka Muhammadu wahalar ai sai tama yawa, yaushe za'a ɗora maka nauyin da ba naka ba? Gaskiya a dai faɗa wa Babanta." Aramma ya faɗa yana jinjina lamarin.
"Na haɗa ka da Allah Aramma kamin wannan alfarmar nima Husna ai ƙanwata ce komai zan iya mata." Maganar Bahari taso bawa Aramma mamaki sai kuma yayi tunanin kodan suna shiri da ita ne.
Garba ma yasa baki akan Aramma ya barshi tunda shi yace zai iya.
Aramma baya so Yaron yaji babu daɗi shi yasa yayi shiru amma gaskiya dole zai sanar da Abdullahi koda bayan sunje Dutsen ne.
_Dutse general hospital_
Saida suka sauke Garba a gida Bahari yace dan Allah ya kular masa da fetir ɗin sa Ramma kuma ta shiga gida ta dakko wa Husna kaya kala ɗaya da hijabi sannan suka wuce Dutse.
Bahari da Aramma ne a zaune suna jiran ganin Likita Husna ta jingina kanta a jikin Ramma dake zaune kusa da ita.
"Wacece Asma'u Abdullahi Mai Kano?" Wani matashi sanye da rigar Likitoci ya faɗa, Bahari ya miƙe da sauri ya isa wajen me kiran.
"Gamu nan."
"Okay Likita yace ku shiga." Ya faɗa yana juyawa ciki.
Da taimakon Ramma Husna ke tafiya a hankali kana ganin ta kasan tana jin jiki, Bahari ya zauna yace "Aramma ku shiga ni zan jira ku anan."
"A'a tashi kuje kune yara zakafi ni gane bayanin likita duk yadda kukayi kamin bayani in kun fito."
Bahari bai sake magana ba ya miƙe yayi gaba yana Murmushi su Ramma suka bisa a baya, dama da biyu yayi maganar Aramma yaje dan baya so tun farko ya nuna shi ke son zuwa ganin likitan shi yasa ya basa dama sai gashi kuma kamar yadda yayi zato yayi nasara dan dama yayi tunanin Aramman ba zai bisu ba.
Ita da Ramma ne zaune a gaban likita Bahari kuma yana tsaye daga gefen su.
"Wacece Patient ɗin?"
Likitan mai yawan fara'a ya tambaya yana duban su, likitan ba wani babba bane dan ba zai wuce shekara talatin zuwa talatin da biyu ba.
"Gata nan." Ramma ta nuna masa Husna data dafe kanta idanun ta a rufe.
"Ai naga alama."
Likitan ya dubi Bahari yace "duk naga bayanan ta a transfer ɗin da kuka kawo, shi matsalar ciwon kan nata ina tunanin wani abu amma dai akwai likitan da zata gani kuna da sa'a yana nan bai koma ba dan daga Aminu Kano yake zuwa nan sau biyu a sati, so zan turaku wajen shi." Likita ya faɗa yana yin rubutu akan takardar transfer ɗin sannan ya miƙa wa Bahari yace "Wannan zaku bashi in kunje, zansa a raka ku."
Bahari ya karɓi takardar yayi masa godiya suka fito daga office ɗin Ramma na riƙe da hannun Husna.
Bahari yayi wa Aramma bayanin yadda sukayi da Likita yace "to Allah yasa muji alkhairi, zan jira ku sai kuje ko sannu da ƙoƙari Muhammadu Allah yama albarka."
"Amin ya Allah." Bahari ya amsa yana Murmushi.
Wanda zai raka su wajen likitan yazo suka tafi, can cikin asibitin ne wani apartment ɗin daban da wanda suka bari, suna zuwa wanda ya rako su ya shigar da File ɗin su, wanda ke ciki na fitowa suka shiga.
Office ɗin likitan babba ne sosai dan yafi wanda suka baro kyau da kayan ƙawa, Ramma ƙin zama tayi ta bawa Bahari ɗaya kujerar ya zauna, likitan bai ɗago ba saida ya danyi rubuce rubuce sannan ya ɗago kanshi ya dubi Bahari ta cikin farin eyeglasses ɗin dake saman idanunsa yace "Asma'u Abdullahi Mai Kano right?" Bahari ya ɗaga masa kai.
"Husna meke damun ki?"
Likita yayi mata tambayar yana mai da hankalinsa kanta.
"Kaina ke ciwo sosai da cikin ido na ma." Amsar tambayar tashi ta fito daga bakin Husna raunane.
Ya sake ƙura mata ido da kyau yaga yadda take dafe da kanta Idanun ta a rufe yace "Asma'u kalle ni muga Idanun."
Husna ta ɗago kanta danta dubi likita hawayen azaba suka zubo mata dan ko kaɗan bata son motsa kan bare harta ɗaga Idanunta.
Dr. Ya dubi fuskarta da saman idanun ta sosai cikin ƙwarewa da sanin makamar aikin sa ya fara observing wani abu dan ya sake tabbatar da zargin sa saiya dubi can ƙarshen office ɗin sa inda akayi wani ɗan madaidaicin shealt ɗin litattafai mai kyau yace "Asma'u me kika gani a can wajen?" Ya faɗa yana nuna mata bayan ta da hannun sa, tambayar tashi ta bawa Bahari da Ramma mamaki amma sai suka zuba musu ido cikin son gane abinda likitan ke nufi dayi mata wannan tambayar.
A hankali ta juya kanta ta ɗaga idanun ta ta kalli inda likita ya nuna mata, takai second talatin tana kallon wajen sannan ta ɗauke kanta.
"Me kika gani a wajen." Likitan ya sake jefa mata tambayar yana zuba mata ido.
"Banga komai ba?" Husna ta faɗa tana karya kai gefe.
Kamar ya bakiga komai ba? Kina nufin babu abinda kika gani?"
"A'a."
"To ya ya ne Asma'u?"
"Naga wajen da duhu duhun wani abu mai ɗan tsayi haka...."
"Amma sai baki gane mene a wajen ba right?" Ya ƙarasa mata maganar, kai ta ɗaga masa alamar tabbatar da abinda yace.
"Nayi tunanin haka." Sai kuma ya kalli Bahari daya saki baki cikin mugun mamaki da ɗan wani abu da
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 27 Chapter of 31