ganin Babanta daɗi ya ishe ta, sai haɗa kayan ta take dan ta dauka tare zasu koma.
Shi kuwa sai binta yake da kallo duk da tayi masa baƙi amma jikin ta babu rama, hankalin shi ya kwanta da yadda ya ganta tsarabar daya kawo mata ta ɗauka ta bawa Ramma ta aje mata da yake a gaban Aramma ne sai Dije bata ce komai ba.
Amma suna fita Sallah tabita har ɗaki ta amshe Sabulan da katon kilin ɗin daya siyowa Husna, sai gugguru da biskit ɗin daya bawa Husna ta bar mata shima saida ta ɗibi wasu.
Ran Zahara fes da abinda Dije tayiwa Ramma ita kuwa Gaje Ramma tayiwa masifar danme bata rage kayan ba ta bata duka.
Yau ma Mai Kano wayo yayi wa Husna ya tafi, ai kuwa tasha kuka harta gode Allah dan Aramma baya gidan haka Salisu yana kasuwa Ramma ce keta fama da ita harta haƙura.
Haka ce kuma taci gaba da faruwa duk lokacin da Mai Kano ya zo garin duk abinda ya kawowa Husna yana fita Dije zata karɓe, in aike ne kuwa dama hannunta yake shiga, baiwar Allah Ramma kuma bata dena kula da ita da zuciya ɗaya ba, dan sosai take bata tausayi danma yanzu ta sake tana shiga cikin yara suyi wasa.
Yanzu sabulun wankin ma Dije ta dena bawa Ramma randa ta tambaye ta kuwa sai ce mata tayi "ki siya mata a ladan tallar da take miki ai ba karɓar kuɗin ki take ba."
"To ita wankin da take mata biyan ta take iya?" Gaje ta faɗa, Dije tace "ta dena mana ai ba wani ya sata yi ba."
Tun daga lokacin in zasuyi wanki Husna sai taje wajen Salisu ta karɓo musu kuɗin omo.
Ranar farko data fara tambayar shi yayi mamaki dan yasan Babanta na aiko mata da sabulu amma kasancewar shi mutum mara bin diddigi sai bai ce mata komai ba yace "jeki wajen Sunday kice ya baki omon wanki injini."
Shike nan tun daga lokacin shima wannan nauyin ya koma kanshi.
Wata rana Husna taje karɓo Sabulu wajen Sunday taji yana waya da Yarabanci, saida ya gama yace "Achalugo." Da yake haka yake kiranta.
"Da Matarka kake waya?" Tambayar da Husna tayi masa ta saka shi kamewa a tsaye, yasan tanajin turanci har tana yi dan duk lokacin da tazo siyayya baya mata Hausa tunda ya gane tanajin turanci amma bai taɓa kawowa ranshi tana jin yarabanci ba, to a ina ta koya? Danya sake tabbatar wa kanshi tana ji ɗin sai yayi mata magana da yaren yace "kinji duk abinda nace ne?" Ai kuwa Husna ta bashi amsa da yaren.
Sunday saida ya kusa faduwa ƙasa saboda tsoron da Husna bata san na menene ba.
tace "dama kana yin aiki, amma kuma kullum kana nan, sannan waje dan...." bai bari ta ƙarasa maganar ba ciki gaggawa yace "eh Achalugo nida Matata ne, ehye inaso tabar aikin ta tazo nan saita bar ɗana a wajen Mamana."
Husna tayi murmushi tace "sai tazo ɗin." Ta karɓi aiken ta ta juya, Sunday ya ɗora hannu akai yana kiran "Chinekeeeee."
*****Sannu a hankali lokaci ya fara nisa kwanaki suka fara tafiya, yayin da Husna kullum take kwana da tashi cikin buri da fatan randa mahaifin ta zai zo ya ɗauke ta ta koma Kano, ata ɗaya bangaren kuma Nana ta dage iya ƙarfin ta dan ganin Husna bata dawo Kano ba, gaba ɗaya yanzu Nana bata da wani buri da fatan daya wuce taga Husna ta ƙare rayuwar ta cikin karkara, garin da babu makarantar Islamiyya ko ɗaya, sai makarantun allo wanda almajirai kan zuwa ci rani cikin garin jifa jifa, babu yarinyar dake zuwa makarantar allo da sunan koyan wani abu daya shafi addini, haka makarantar Boko ba ko wanne Yaro ne ke zuwa ba sai tsilli tsilli, a wannan gari Nana take fatan ƙare tata rayuwar, cikin ƙyauyen da tayi tsalle da murnar baro sa, cikin ƙyauyen data kira fitowa daga cikin sa da suna samun cigaba da tsallakawa bisa turba da wani matsayi na cigaba, wannan buri na Nana yasa taci damara ta kuma dage wajen ganin Husna bata dawo Kano ba bama gidan Baban ta kawai ba, a'a ita gaba ɗaya garin Kano ne bata so ta sake shigo shi, burin ta ta zauna ta ƙare rayuwar ta acan cikin wahala da kaiwa da kawowa irin na sauran matan ƙyauye, Nana bata tuno wata masifa a tare da ita data wuce mata zama da Husna ba, gani take ta zame mata masifa da tashin hankali a rayuwar gidan mijinta.
Zaman garin a wajen Husna yanzu ya fara zama wani abu na daban dan abubuwa da yawa sun fara canja salo da tsarin su.
Yanzu ankai matsayin da Husna bata kallon kowa a matsayin Baban ta sai Salisu dan shi ke mata komai, wannan yasa duk wata matsalar ta shi take kaiwa ciki ikon Allah kuma da ƙarfin zumunci irin nasa baya taɓa gajiya da buƙatun ta, sabulun wankin ta kuɗin kashewar ta tuni suka daɗe da komawa wuyan sa, har kawo wannan lokacin da Husna ke dosar cika watanni shida a Gidan'ari Babanta Salisu ke mata komai kamar yadda yake wa ƴaƴan shi.
Haka har gobe Babanta bai dena aiko mata da sakon kuɗin kashewa da sauran abubuwan buƙata ba, haka Dije bata dena karɓe wa ta hana uwar riƙon ta Ramma ba.
Husna na zaune a wajen Aramma suna tilawa Lirwanu ya shigo ɗakin ganin suna karatu saiya nemi waje ya zauna yana jiran su gama dan magana yake son sunyi da Aramma.
Yana zaune yana sauraren su sosai karatun Husna ya bashi mamaki, yana yawan ji ana faɗin ƙoƙari da yawan karatun ta a wajen yaran gidan da iyayen su amma ko kaɗan baiyi tunanin yarinyar ta kai haka ba.
Karatun tsakanin Husna da Aramma ya fara ne tun bata cike watanni biyu a garin ba, yadda abun ya faru shi ne wata rana ta shigo gaida Aramma da safe ta same shi yana taƙara ta zauna a kusa dashi tanaji harya gama sannan ta dube shi tace "Aramma kaima irin karatun Babana kake yi, niban iya irin wannan ƙira'ar ba, Yayana da Baba sun fada min cewa ita ake kira da warshu, Babana yace zai koya min amma sai nayi sauka, kuma kaga lokacin da Yaya da Mama suna nan ko?" Aramma ya ɗaga mata kai yana Murmushi taci gaba da cewa to a sannan na kusa cinye izu ashirin saura baifi shafi biyu ba, duka ƴan ajinmu fa na fisu ƙoƙari da ƙarfin haddda saboda ni a gida Yaya yake sake koya mini in baya nan kuma Mamana saita tuna min, amma kaga tunda Mama ta tafi shike nan na daina karatun."
Husna ta ƙarasa maganar hawaye na cika mata ido saboda Mamanta da yayan ta data tuna.
Ganin yanayin ta daya canja sai Aramma yaji babu daɗi ya kuma yi saurin janye hankalin ta da cewa "shike nan yanzu kinaso na koya miki irin nawa?" Da sauri ta ɗaga masa kai, yace "to kinga ni na iya irin naki amma na daɗe banyi ba, ki fara karanto min shi naji inzan iyasa sai muyi tare ko? Ai kinsan yadda ake musaffa ko?" Aramma yayi mata maganar da yanayin barkonci, Husna ta ɗaga kai cikin jin daɗi dan sosai suke yi da Yayan ta, zamanta ta gyara harda lankwasa ƙafa ta fara karanto masa daga ƙasa, yana zaune yana sauraren ta bai mata gyaran ko ɗaya ba har takai sabbi, wannan karatu na Husna ya yayi wa Aramma daɗi dan abune dabai taɓa zato ba, bai taɓa tsammani yarinyar nada basira irin haka ba, ai bai sake shan mamakin Husna ba saida yace suyi musaffa shafi bayan shafi suke yi yana ajewa zata ɗora daga inda ya tsaya.
Salisu yazo ya tadda sunayin karatun daɗi ya ishe shi a ranar kuwa saida ya shagwaɓa Husna dan fita yayi ya siyo mata abu mai daɗi ya kawo mata sannan yace yau girkin ranar da za'ayi a gidan sai abin da ta zaɓa za'a dafa saboda ita.
Wannan karfafa gwiwa da yabawar da Babanta Salisu yayi mata ba ƙaramin daɗin tayi mata ba, ranar wuni tayi bakin ta a buɗe sai fara'a take, tun daga lokacin kuma Aramma ya matsawa Mai Kano yazo ya ɗauke ta ta koma gida taci gaba da karatun ta karya lalace, a lokacin yace masa to kuma har cikin zunciyar shi yana nufin zuwa ya ɗauke tan amma abu kamar wasa sai zuwa ya ɗauke Husna ya gagare shi har yanzu kuma da Husna ke dosar rabin shekara a garin zancen ɗaya ne kullum "zan zo na ɗauke ta in sha Allahu, abu nake son ƙarasa wa, Aramma a ƙaramin lokaci."
Duk lokacin da Aramma ya yiwa Mai Kano magana akan yazo ya ɗauki Husna amsar ke nan.
Saida suka gama karatun Husna ta fita sannan Lirwanu ya dubi Aramma sukayi maganar data kawo shi, bayan sun gama Aramma yace "kai kiramin Abdullahi naji yaushe zai zo, yau Asma'ullahi ta cike izifi talatin cif, wannan karon wallahi Abdullahi ko baya so saiya tafi da Asma'ullahi, yarinya duk ta fara zama budurwar ƙyauye, haba bana son shiririta ya daga kawo yarinya kace inka gama gini zaka ɗauke ta kuma saika barta ko yaushe aka yi magana shike nan kai kana da uzuri, kiramin shi naji randa zai zo garin." Aramma yayi maganar yana mai tabbatar wa kanshi a wannan karon Mai Kano in bai ɗauki Husna ta daɗin rai ba tabbas zai yi masa dole ya tafi da ita ko baya so.
Lirwanu ya danna wayar shi ya kira Mai Kano.
"Gashi Aramma ya ɗaga." Ya faɗa yana miƙa masa wayar, yace
"Yawwa." Ya karɓi wayar ya kara a kunne.
Mai Kano najin Aramma ne suka gaisa ya tambaye shi yan gida yace "kowa lafiya, ni nace Lirwanu ya kiramin kai naji randa zaka zo, dan wannan karon babu uzurin ka dazan karɓa akan Asma'ullahi, indai ina raye to ƙafarka kafar ta."
"Ayimin haƙuri Aramma in sha Allahu wannan jumma'ar dama zanzo, dan jiya Babban wan Safiya ya sanar dani ta haihu an samu Alhajin su." Yayi maganar yana Murmushin da kanaji kasan yana cikin farin ciki.
"Allahu Akbar, Allah ya raya Abdulkadir Allah yayi masa Albarka, lallai Asma'ullahi tayi ƙani kai Masha Allah, ai kuwa yanzu zan faɗa mata dan bata jima da fita ba gama tilawar mu ke nan nace a kiramin kai, Abdullahi bana son Asma'ullahi ta rasa ilimi inaji ajikina in sha Allahu zatayi albarka, ƙwaƙwalwar ta nada kyau sosai gashi harta fara wuce iyayen ta yawan Kur'ani." Aramma ya faɗi maganar yana taɓa kafadar Lirwanu.
Mai Kano yayi murmushi yace "In sha Allahu Aramma ina nan tafe jibin."
"To Allah ya nuna mana da imani a gaida Ni'imatu."
Aramma na sauke wayar Lirwanu yace "ah dama Safiyar da ciki ta fita ke nan?"
Murmushi mai ciwo Aramma yayi sai kuma cikin girma yace "gashi kuwa kaji, nida kai duk yanzu muka san haka, shi karatun rayuwa ai bai bar kowa ba, in kabi Allah ya karanta maka da sauƙi inka bijire masa wayon ka da duniya saisu biya maka nasu."
Lirwanu yayi shiru yana sauraren Aramma bai jima ba kuma yayi masa sallama ya fita, yana fita daga lungun Salisu na shigowa.
Aramma ya faɗa masa haihuwar Safiyya da yadda sukayi da Mai Kano akan Husna.
"Aramma ai ko bai zo ba wannan jumma'ar in sha Allahu saina kaita da kaina." Salisu ya faɗa da tabbacin hakan a maganar shi.
Indo ce ta biyo bayan Baban ta, tace "Baba na manta baka bamu kuɗin sabulu ba yau zamu wanki, kuma dan Allah karka manta yau ka taho mana da gorubar da muka baka sautu nida Ma'u."
"In sha Allahu yau dai bazan manta wannan sakon goruba ba, sabulu kuma kuje wajen Sunday ku karɓa Asma'u tace min itama yau binku wankin zatayi ko?"
Indo ta ɗaga kai yace "to banda wasan banza ana gama wankin ku dawo gida."
Harta juya ta sake dawowa tace "Baba kacewa ɗan Idi yau ya kawo ruwa da wuri jiya fa sai nida Ma'u ne muka ɗebo na sanwa, yawwa kuma baka bamu kuɗin abinci ba."
"Baki abun magana Indo A'isha." Aramma ya faɗa da tsokana tayi masa fari da ido, yace "Maza nemo min ƙawar taki Asma'ullahi nayi mata albashir."
Indo tace "to."
Salisu yace "yau babu kuɗin abincin rana nasa ayi dambu ɗan tsame tunda muna da ƙaura (jaddawa), ruwa kuma zai kawo akan lokaci jiya ma yace Famfon tsangaya ne ya lalace shi yasa akayi layi a na cikin gari amma sun gyara." Sai kuma ya ɗakko Naira Hamsin ya bata, yace "gashi keda Asma'u in an kawo abun siyar wa saiku siya da rana." Indo ta karɓa tana dariyar jin daɗi ta juya.
Aramma yayi ta binshi da addu'a, Dije ta shigo ita ma Aramma ya faɗa musu haihuwar Safiyya da abinda aka samu budar bakin Dije sai cewa tayi "to in ta yaye sa saita dawo da shi gidan ubanshi karya tashi bare."
Jin abinda tace yasa Aramma ya balbale ta da faɗa "ke wai Hadiza mai yasa kullum kina sake girma kina kuma shiga dawa ne? Kullum bakin ki ba zai faɗi abu mai daɗi bako? Kin kashe Aure kin raba uwa da ƴaƴan ta, dubi yadda Asma'ullahi ta zama kina neman lalata rayuwar yarinya, yanzu daga cewa Safiya ta haihu kizo kina wata maganar banza data wofi, to bazata dawo da shi ɗin ba nace bazata dawo da shi ɗin ba, ai ba ke kika yi mata dakon cikin da naƙudar haihuwar shiba, me ɗa. Kullum ke magana akan addini kabilanci da wani banzan tunanin ki, yanzu faɗa min duk cikin jikokin naki da suka girma a gaban ki wa yakai Asma'ullahi ƙoƙari, duk ta fisu nitsuwa da tarbiyya wacce duk mumsan uwartan da kika tsana ita ta bata ba ɗan naki ba tunda ita ke zama da ita su wuni a gida ba shiba."
Aramma nata faɗa ta inda ya shiga ba tanan yake fita ba dan dama yana da cikin ta, ko ba'a faɗa mishi ba yasan ita ta saka Mai Kano ya saki Safiya ido kawai yasa mata ya barta da duniyar.
"Daga magana kuma saika hauni da faɗa, to ta riƙe ai ɗa namiji ne komai daran daɗe wa zai nemi gidan uban shi." Aramma ya kalli Dije da takaicin ta, Salisu yana zaune yana jinsu, ranshi duk babu daɗi, yasan Aramma yana hakuri da Dije sauda dama baya biye mata ne yayi ta magana akan abinda take amma wasu lokutan dole take kaishi bango.
"Salisu yau babu zuwa kasuwa ne?" Aramma ya tambaye shi da yanayin son kauda ɓacin ran da Dije ta guma masa.
"Eh nama shirya sallama nazo muyi zan tafi, yau Larabar gurgunya zani."
"Eh ai yau take ci, Allah ya tsare ya bada sa'a." Aramma ya faɗa, Dije ma ta bishi da addu'a, saida ya ajiye musu kuɗin kashewa kamar yadda ya saba sannan ya tafi.
Bai jima da fita ba kuma sai gashi ya dawo, Aramma yace "A'a mantuwa kayi ne?"
Salisu yace "A'a Aramma motar ce bata cika ba da yake ta safen ta tafi, shi ne na sake shigowa." Yana maganar wayar shi ta fara waƙar
_A 2011, madara mai kama da nono ɗa mai kamar uba Ahmad Abacha zamu zaɓa governer a Kano a cpc jam'iyyar mu a 2011._
Ringing tone ɗin shi ke nan tunda wakar ta fito yasa ta a ringing tone ɗin shi.
Aramma yace "Salisu wannan alamar kiran naka ƙarar tayi yawa mutum ko bacci yake a gidan nan aka kiraka saiya tashi." Salisu baice komai ba yayi murmushi yana ɗaga kiran yace
"To gani nan fitowa." Ya kashe wayar yana duban iyayen nashi yace "mota ta cika zamu tafi sai Allah yayi mana dawowa."
"To Allah ya bada sa'a Allah ya kiyaye hanya." Yarya juya zai fita daga ɗakin ya sake dawowa yace "bakwa bukatar wani abu ko Aramma?"
Dije tayi murmushin jin daɗi, Aramma yace "babu komai Salisu jeka abunka suna jiranka Allah yayi maka Albarka." Ya juya ya fice daga gidan.
Husna sosai tayi murnar jin Mamanta ta haihu, sai kuma jikin ta yayi sanyi har Aramma ya kula da sauyawar yanayin ta yace "Asma'ullahi keda zakiyi murna kuma saiki ɓata fuska."
"Aramma naji daɗi nima nayi kani." Ta faɗa Idanunta suna tara ruwa, Aramma ya jawo hannun ta kusa da shi yace "to mene ne na ɓata fuskar kuma?"
Saida ta goge hawayen daya zubo mata wanda zubowar tasu ya sake bawa Aramma mamaki sannan cikin karaya da sanyin murya tace "Aramma dan Allah ka hana Babana ya ɗakko ƙanina daga wajen Mamana kace ya taimaka ya barshi a wajen Mama, karya ɗakko shi kamar ni shima zai kawo shi nan kuma kaga ai ba zai rinƙa ganin Mama ba, ba zai je makaranta ba."
Hakika furuci da kalaman Husna sun gasa zuciyar Aramma sun kuma narka ta, har saida yayi ta maza sannan ya iya hana raunin shi na tausaya shi bayyana, a zuciyarsa kuwa ya sake cin buri da ɗaura damarar raba Husna da ƙyauyen bawai dan wani abu ba a'a haka kawai yake jin an cuce ta an kuma tauye mata rayuwa, dan bata saba irin tasu rayuwar ba ba kuma aciki ta taso ba, Aramma a ƙasan zuciyar shi yace "addini ma yana meman ci gaba bare ɗan Adam lallai nayi alƙawarin rabaki da zaman garin nan Asma'ullahi." A fili kuwa sai murmushi ya lulluɓe kamilalliyar fuskar shi mai cike da daraja yace "in sha Allahu ba zai karbo shiba, har saiya zama saurayi ya zo da ƙafafun shi ya gaishe sa ya koma wajen Mamanki." Jin wannan kalamai na Aramma ya faranta zuciyar Husna tayi dariya har saida haƙoran ta suka bayyana, Aramma ya bita da kallo.
"Lallai wahala babu daɗi."
Bayan an gama cin tuwon safe su Husna suka tafi wanki Famfon makaranta, Husna sai murna take itama yau zata wankin ta ba rakiya ba.
Ramma ta bata robar wankan ta da botiki, suna fitowa suka tsaya a Dandali inda ake tsayawa, anan ake taruwa sai kowa ya fito sai a tafi gaba ɗaya.
Kawayen Indo suka fara tsokanar Husna wai yau itama zatayi wanki.
Bayan sun gama wanki suka kafa ƴar tsaraf ke, in zakayi wanka kuma saika ɗaura zani ka tsugunna a gaban famfo wata tana bugoma ruwa kana wanka inka gama itama tayi haka ka bugo mata.
Wajen ƙarfe biyu na rana kayan kowa ya gama bushewa suka linke sannan suka taho gida, masu ɗebo ruwa a ɗaya botikan su suka ɗebo wanda basa ɗebo wa kuma irin su indo suka ɗauki kayan su suka kamo hanyar gida.
Suna gaf da shiga cikin gari Indo ta hango Iro yana tahowa da gudu tace "Ma'u dubi yadda Iro ke gudu in kika bibiya kashi ne ya koro shi, shi ba zai tashi zuwa jeji ba sai yaji kashi zai zubo ai wata rana sai yayi a wando."
Husna tayi dariyar maganar ta, daidai lokacin kuma ya fara yowa kusa dasu yana ƙwalawa Indo kira. "Indo......Indo......Indo...!" Yana kiran sunan yana haki ga hawaye.
"Indo kizo gida Baba ya mutu yanzu aka zo aka faɗa." Ai da Indon da Husna duk sai suka rude dan kowa tunanin shi Baban shine ya mutu tunda duk haka suke kiran iyayen nasu....
_*WRITING.....✍🏻*_
*_MUTUWAR AURE.....!_*
_(Ƙaddarar wasu ƴaƴan)_
*_Kanawa ne👌🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
_BOOK 1_
*_FREE PAGES_*
________________
*_WHATSAPP GROUP👇🏻_*
https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3?mode=gi_t
https://wa.me/+2348064789370
_________________
_EPISODE 17_
"Wanne Baban?" Indo da Husna suka faɗa a tare cikin ƙarfin hali.
Sauran abokan tafiyar tasu kowa yayi cirko cirko.
Iro da kuka ya tiƙe da kyar yace "Baban mu mana."
"Baban mu?" Indo maimaita sai kuma tayi jifa da kayan kanta ta kwasa da gudu tayi cikin gari Iro ya rufa mata baya.
Husna kuwa waje ta samu ta zauna tana kuka, sauran kawayen Indo jikin su yayi mugun sanyi masu saurin kuka tuni suka fara.
Husna kuka take bil hakki saboda hankalin ta yayi mugun tashi, masu ƙarfin halin cikin sune suka kamo ta wasu kuma suka ɗebo musu kayan su.
Lokacin da suka iso Kofar gidan su, sun tadda Maza danƙam abinka da mutum na mutane tuni garin ya amsa da labarin mutuwar Salisu ko ina ka gifta zancen ake.
Har cikin gidan suka raka Husna da kayan su. Gidan ya ɗinke da mata ko ina ka duba mata ne anata ihu da koke koke, can kofar su Ramma Husna ta hango Gaje da katon cikin ta a gaba haihuwa yau ko gobe mata sun zagaye ta tana rusa kuka suna bata hakuri, abin gwanin ban tausayi.
Waje Husna ta samu ta zauna a ƙasan bishiya tana kuka, Maza harsun fara shigowa ana shirin ɗora tukunyar wanka kan su ƙaraso da gawar.
Dije kuwa tana ƙofar ɗakin ta tsofaffi kamar ta sun sata agaba tana kuka tana surutu yadda kasan wacce ta samu matsala cewa take.
"Wayyo Allah wayyo ni Dije gata na ya ƙare shike nan na fito rana, Salisu yaron kirki ɗa mai albarka, baya bari muyi kukan rashi, Salisu bai bari mun rasa komai ba, ko ɗazu da safe saida ya bamu kuɗin kashewa harya fita ya sake dawowa ya tambaye mu koda wani abu nace babu ashe tafiyar ke nan, Salisu ashe tafiyar ke nan." Sai kuma ta hurma ihu su Madiga na bata haƙuri.
"Shike nan yanzu asirina zai tonu, mutane zasu mana dariya, Salisu ya tafi, ka tafi Salisu ka barni, ina zaune anan ina auna hatsin tuwo kawai sai ganin Lirwanu nayi ya shigo yana kuka jikin shi yana rawa yake faɗa min an bugo masa waya motar su Salisu tayi haɗari duk sun mutu."
Dije tana kuka tana bada labarin bakin ta yaƙi shiru.
Ƴaƴan shi kuwa sun haɗa kai a waje ɗaya suna nasu kukan dole inka kalle su su baka tausayi.
Gawar Salisu da Mai Kano tare suka iso, saida ya zo garin ma ya gane wanda ya mutu dan da Lirwanu ya kira shi cewa kawai yake "Yaya Mai Kano ya mutu shike nan wallahi ya tafi ya barmu."
Haka ya rinƙa faɗa ya kasa faɗa masa ainahin wanda ya mutum, wannan yasa hankalin sa a mugun tashe ya taho ko gida bai tuntuba ba.
Sanda ya iso Kofar gidan su yayi daidai da ana fitowa da gawar Salisu daga mota, ta cikin taron Mazan yabi ya iso inda motar take, hanya mutane suka rinƙa bashi yana wucewa suna binshi da sannu.
Dashi aka riƙo gawar ɗan uwanshi da besan shi ne ba kwance babu rai saida yaji mutane na fadin "Allahu Akbar bawan Allah mutumin kirki Salisu Allah ya gafarta maka Manzon rahama ya karɓi baƙuncin ka."
Lokacin da kalaman nan suka sauka a kunnen Mai Kano Ƙarfin zuciya da jarumta ce kawai ta kai ƙafafun shi cikin gida, su huɗu suka kamo gawar har zuwa tsakiyar ɗakin shi, shigowa da gawar cikin gida ta sake ruda mutane kukan jama'a ya sake ƙarfi. Gaje kuwa suna giftata da gawar ta sume.
Baba Adamu wanda suke ƴaƴan Maza shiya tsawatar yace a daina masa kuka haka
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 18 Chapter of 31