Share this page
yi masa Allurar ta tsira masa Allurar ta saman kayan shi. Har tasa allurar ta cire bai motsa daga yadda yake zaune ba sai Idanun sa daya sake rufewa, Bahari ya fara jinjiga masa hannun a hankali dan kar allurar ta kume masa, Husna kuwa sai sannu take jera masa. Bahari ne dai ya sake riƙe kafar shi ya ɗora ta akan cinyarsa Chioma ta fara ɗinke masa yankan, Husna na ganin an fara ɗinkin ta rufe idanun ta da sauri saboda tsoratan da tayi bata san sanda ta riƙe ɗaya hannun sa ba. Kukan tausayin shi take mara sauti sai hawaye kawai ke bin fuskar ta, cikin kankanin lokaci Chioma ta gama ɗinki ta maida komai cikin jakar ta zuge zip ɗin. "Malama Ma'u Saiki sakar masa hannu an gama ɗinki mai ɗan uwa." Bahari ya faɗa yana miƙewa tsaye yana karkade jikin sa, kamar ya san me Husna take shirin yi kuma sai ya cewa Chioma. "Nawa ne kuɗin aikin ki?" Chioma ta gane me yake nufi dan haka sai tace "Three thousand Naira." Bahari yasa hannu a aljihu ya fito da kuɗi ya irga ya bata ta kudin ta, Chioma ta karɓa tana masa godiya ta tafi. "Nagode Bahari in sha Allahu zan kawo ma kuɗin ka kaji." Husna ta faɗa tana duban shi, sai yayi murmushi sannan yace mata "Ma'u ai bake kaɗai kike neman ladan ba nima sadaka nayi masa karki damu." Ta buɗe baki tana kallon shi ya sake tabbatar mata da kyauta ya biya masa. "Mun gode sosai Bahari." Husna tayi ta jera masa godiya kamar zata ari baki, Bahari wajen ya bari yana mata murmushi. Sai ta juyo zata yi masa magana taga ya tashi tsaye "sannu Yaya." Ta sake faɗa, shi kuwa bai kalli inda take ba ya fara dogara Sandar shi yana barin wajen. A hankali yake tafiya da gefan kafar sa Husna na tsaye tana kallon shi yana bin gefan titi yana tafiya har saida ta dena ganin shi da kyau sannan ta koma wajen kayan ta. Taje ta samu Indo harta siyar mata da sauran doyar tayi mata godiya ta ɗauki kwanunkan ta jikin ta a sanyaye ta tafi gida. Wunin ranar a haka ta ƙarasa shi tana tunanin koya yake yanzu, har dare jikin ta a sanyaye, rashin zuwan shi Dandali kuma saiya sake saka jikin Husna yin sanyi. Da safe Husna ta fita duba shi a tasha bata ganshi ba har yamma babu shi banu dalilin sa, nan fa hankalin ta ya fara tashi yanayin damuwa ya shige ta, komai yinsa kawai take babu kwarin jiki har dare yayi ta tafi dandali da wuri tana addu'ar Allah yasa yau yazo, amma sai addu'ar ta bata karɓu ba dan yauma dai irin jiya ne wato bai zo Dandalin ba, nan fa ta rasa inda zata saka ranta. Kwanan shi biyu Husna bata ganshi ba sai ana ukun da daddare tana zaune a Dandali ta haɗa kai da gwiwa tare da zabga abun tagumi ta faɗa duniya tunanin inda yayanta ya shiga tsawan kwanakin nan, abun duniya duk ya ishe ta, tana cikin tunanin kamar daga sama taji an zunguri kafar ta, a ɗan tsorace ta motsa sai kuma ta ganshi tsaye a kanta yana duban ta sosai yau ma idanun sa a waje, da sauri ta mike tsaye tana faɗin "Yaya inaka shiga? Ya ciwon kafar ka? Ya warke? cikin murnar ganin sa take maganar tana ƙare masa kallo, "Har yanzu wajen yana ma zafi?" ta jero masa tambayoyin dake cinta. Yau shiya Zauna a gaban ta yana fuskantar ta saidai kamar yadda ta sani baice mata komai ba sai binta daya rinƙa yi da kallo. "Yaya kafan ya dena maka ciwo?" Ta sake jefa masa tambayar kamar zata saka masa kuka. Bai ce mata komai ba sai taga ya miƙe Kafafun shi daya nade, wacce yaji ciwon ya miƙe Husna ta kalli wajen sai taga ciwon ya warke sai ɗan abida baza'a rasa ba, tana sakar masa murmushi tace "Yaya naji daɗi ciwon ka ya kusa wake wa." Idanunsa ya ja ya rufe ya mai da duban shi ƙasa, ita kuma ta fara zuba masa surutu da bashi labarin neman shi data rinƙa yi tsawon kwanakin nan. Tana masa surutun yana jinta wani abun kuma inta faɗa saiya ɗago kai ya kalle ta. _Bayan sati uku_ Rayuwa tayi wa Husna babu yabo babu fallasa musamman yanzun da bata zuwa ɗiban ruwa dan an daɗe da gama aikin ruwan garin ga famfuna nan tako ina a layi kan gari lungu da saƙo, ruwa ya wadaci ko ina, ga ruwan mai kyau da daɗi. Gidan su Husna yana ɗaya daga cikin gidajen da akaja musu ruwa har cikin gida. Rana nayi ruwan zai fara zuba ba zai ɗauke ba har Magarba. Wannan sauƙi ne babba a wajen Husna da ire-iren ta, randa ruwan ya fara zuwa kuwa murnar ta kin ɓoyuwa tayi, tana zuwa dandali ta saka Yayanta a gaba tana bashi Labarin ruwan da aka kai musu gida da irin daɗin da taji. Yadda yake mata dai har yanzu haka ne babu wani canji komai tace masa babu amsa sai dai ya jita kawai. Yau Litinin beguwa ke ci Husna dawowar ta ke nan ta shigo gidan hannunta riƙe da farantin tallar ta, yauma ranta a ɓace yake dan tunda ta fara yiwa Baba Lirwanu talla duk ranar kasuwa da ɓacin rai take dawowa gida. Ramma tayi mata sannu ta amsa tana wucewa ciki, saida tayi wanka ta canja zanin jikin ta da doguwar riga baƙa, ta sallar bara ce da Baban ta ya kawo mata farin hijabin ta mara girma ta saka mai kawai ta shafa tasa kwalli ta fito. A ƙasan inuwa ta sake samun matan gidan tana zama Iro ya fito daga lungun Dije yace "Ma'u kije inji Dije." "To me kuma ya faru?" Husna ta faɗa a ranta dan tasan Dije bata kiran Alkhairi. Da sallama ta shiga wajen ta samu Dije tare da wata bakuwa, bakuwar ta amsa mata sallamar tana binta da kallon ƙurulla daga sama har ƙasa kamar wacce aka bawa aikin tantance halittar da Allah yayi mata. Husna ta dubi matar a fuzge a shekaru dai ba zata gaza 50 ba, irin Hajjojin nan ne na Saudiyya tasha doguwar riga ruwan makuba anyi mata ado da yellow zare, ta saka ƙaramin hijabi sai kuma ta rufa mayafin rigar akan hijabin, fuskarta duk zane bakin ta yayi baƙi baƙi, tun daga bakin lungun shigowa wajen Dije kuwa zakaji wani kamshin tulare mai ɗan karfi na tashi a jikin ta, saida matar ta gama ƙarewa Husna kallo sannan tace. "A'a Hadiza kardai ki cemin wannan ce ma'un ɗan Hajja?" Matar ta faɗa tana sake ƙurawa Husna ido. Saida Dije tayi dariyar jin daɗi sannan tace "ita ce fa Hajja, ya kika ganta?" "Marra wannan tayi har fiya da zato na, la la la gaskiya za'a yi mace anan Masha Allah. Gaskiya dole ɗan Hajja yace min shifa sai Ma'u, ashe haka Asma'un tashi takai, ah lallai takai a jirata, gaskiya muna kamu wannan babu wasa kanna koma Makka kawai za'a gama magana Hadiza." Dije bakin ta yaƙi rufuwa Hajja ta cewa Husna "zo nan mu gaisa mana suruka ta, kai Masha Allah." Husna ta ɗan tsaya kamar ba zata jeba sai kuma taɗan matsa kusa da ita fuskar ta a cunkushe dan sai yanzu ta gane Maman Dan Hajja ce. Hajja ta sake kallan kunnen Husna da warwaron hannun ta da tunda ta shigo idanun ta ke kansu kamar tayi shiru sai kuma tace "Ah ƴata wa ya baki wannan abu mai daraja haka? Lallai surukar tawa ƴar gata ce." Hajja ta faɗa tana taɓa ɗan kunnen dake kunnan Husna da warwaron hannun ta dan ta sake tabbatar da abinda Idanun ta suke gane maba ba kuskuren idanun ta bane sai tace "Yata muga wannan ɗan kunnen naki?" Hajja ta sake fada tana kallon Husna. "Mamana tace karna bari kowa ya cire min." Husna ta bata amsa tana matsa wa daga kusa da matar dan tularen ta harya fara hawa mata kai. "Eh tana da gaskiya ai ba ƙaramin ƙoƙari tayi ba data baki su kike yawo dasu a gari ba, irin wannan kadarar ai ɓoye su ake, lallai Maman ki na sonki. Dije data kasa gane kan zancen Hajja saita dube ta cikin neman ƙarin bayani tace "shi ɗan kunnen har wani abu ne? kin ganta nan tunda uban ya kawo ta nan ya aje shi ne a kunnen ta sallah biki ko suna bata taɓa cire wa ba, haka wannan abun hannun nata na jaraba da bata bari a taɓa shekara uku ke nan yanzu." "Ai bazata bari a taɓa ba Hadiza ita kanta da tasan me take yawo dashi a hannu ai da tuni ta daɗe ta cire wa ta adana abunta saboda gudun asara." Husna ta dubi Hajja sai kuma ta ɗauke kai. "Kai Hajja ɗan kunne ne fa kawai da warwaro sai kace wani kayan gabas." Saida Hajja tayi dariyar jin maganar Dije sannan tace "to wannan da kike gani a kunnen ta da hannun ta dukan su gold ne mai daraja ma kuwa, dan yanzu wannan kuɗin da za'a karɓa dasu ba ƙananan kuɗi bane, tsaf kuɗin su zai siya mata kayan ɗaki da ɗan maraƙi (Sa)." Dije ta zare idanu tana matsowa kusa da Hajja tace "ke Tsahare karki zolaye ni." Hajja tayi dariya a fili a ranata kuwa sai tace "haba nidai nasan baku san mene wannan ba, ai kuwa ta faɗi gasassa karɓa zanyi na baku wani abu na riƙe su, wannan inna kai Makka ai saina linka kuɗin shi." A fili kuma sai tace "wallahi rantsuwar ɗan musulmi Hadiza in kuna son siyarwa ma ni akwai wanda zan haɗa ku dashi ku karɓi yan kudaden ku, yarinya kema a siya miki wani abu mai amfani da kuɗin har a samu canji." Ai jikin Dije saiya fara rawa taji kuɗi faɗi take "kai Hajja zuwan ki yafi zuwan Sule Lamiɗo (Governor Jigawa) ai kuwa bari Lirwanu ya shigo muyi magana a nutse zaki jimu gobe duk yadda muka yi dashi." Husna dai tana tsaye tana jinsu ana haka sai ga Sallamar Lirwanu dawowar shi ke nan daga kasuwa ya shigo lungun Dije. Nan fa Hajja ta sake zuzuta musu abinda za'a samu in aka saida ɗan kunnen Husna da awarwaron ta. Ai Lirwanu sai yafi Dije rudewa babu abinda yake hasasowa sai ruwan kuɗin da Hajja ta kira musu, a zabure ya dubi Husna yace "Ke zo nan a cire su tun yanzu kar a samu matsala kan goben, Hajja ki tambayi me saiyan kawai." Lirwanu yayi maganar yana kallon Husna data tashi zata bar wajen. "Dan ubanki ba magana nake miki ba kike tafiya kamar baki jini ba." Ya faɗa a zafafe yana yowa kanta ta kwasa da gudu ta fice daga lungu Dije, ya yunƙura zai rufa mata baya Dije tace "kai dawo nan ka rabu da ita karka bita, ai a gidan zata kwana da daddare sai ka karɓo mana inta kwanta, shegiyar yarinya ƙarama sai mugunta." Lirwanu ya fasa bin bayan Husna Hajja kuma taci gaba da zuga Dije cikin dabara da iya bariki. Husna na barin lungun Dije kuwa ta fice daga gidan ta tafi gidan su Indo tana tafe tana tuna huɗubar da Mamanta tayi mata akan ɗan kunnen. "Husnah karki bari wannan ma a cire miki kinji Mamana? Duk wanda yace kizo ya gani karki je, kuma koda wasa karki sake naga kin cire sa inba haka ba babu ruwana dake, haka zan bar miki kunnen ki yayi ta kuraje babu ɗan kunne tunda kinga duk wanda aka saka miki kunnen ki baya so, kina jina ko?" Maman ta ta faɗa mata tana sake maimaita mata kashe din. Awarwaron hannun ta kuwa randa ta fara ganin sa a wajen Mamanta har kuka tayi akan saita bata tasa amma sai ta hanata tace "haba Husnan Babanta kiyi hakuri yanzu yayi miki yawa saikin sake girma saina baki kisa daman ai naki ne, kinji." Da haka tayi mata wayo ta ɓoye shi daga ranar kuma bata sake ganin saba sai randa Mariya ta buɗe zif ɗin ƙasan akwatin ta. "Yanzu ya zan yi dasu kar Dije da Baba Lirwanu su kwace min?" Husna ta yiwa kanta tamabayar a fili. Wata zuciyar tace "ki bawa Indo ta ɓoye miki a ɗakin Ladi." Sai kuma ta girgiza kai tana jin hakan ma bai yi mata ba. "To ya zatayi dasu?" _nima A'isha ina daga gefe nace fans kuna ganin a ina Husna zata ɓoye su tsira?_ _*WRITING.....✍🏻*_ *_MUTUWAR AURE.....!_* _(Ƙaddarar wasu ƴaƴan)_ *_Kanawa ne👌🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ _BOOK 1_ *_FREE PAGES_* ________________ *_WHATSAPP GROUP👇🏻_* https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3?mode=gi_t https://wa.me/+2348064789370 _________________ _EPISODE 24_ Tun da Husna ta fita daga gidan bata dawo ba suna tare da Indo a gidan su har aka yi sallar isha'i suka ci tuwon dare suka tafi Dandali daga can kuma har zuwa lokacin bata gama yankewa kanta matsaya akan ta bawa indo ajiya ba ko a'a. Suna zuwa Dandalin saurayin Indo ya zo ta tafi zance wannan yasa Husna taɗan tsaya cikin ƴan matan kafin daga baya ta bar tsakiyar Dandalin ta tafi inda suke zama. A zaune ta samu yayan ta yana duban gaban shi, yana ganin ta ya janye ƙafafun sa dake sanye cikin baƙin takalmin soson da ta siya masa tun bayan yankewar da yayi, da taje cin kasuwa ta siyo masa saban takalmin sosai baƙi cikin ikon Allah kuma sai bata samu matsala da shiba sanda ta bashi takalmin dan tana basa ya karɓa sosai kuma hakan yayi mata daɗi, tun daga ranar duk inda zaka ganshi zaka ganshi sanye da takalmin. A gaban shi Husna ta zauna kamar yadda ta saba tana sakin murmushi tace "Yaya yau ka riga ni zuwa?" Kamar ko yaushe bata samu amsa ko nuna wata alamar fahimtar abinda tace daga gare shi ba. Hannu tasa ta tallafe kumatun ta tana kallon shi tana juya shawarar da zuciyar ta ta bata tun ɗazu akan ta bashi ajiyar ɗan kunnen ta da awarwaron ta. "To amma inna bashi ya yarmin fa? Tunda bashi da lafiya." ta ayyana hakan a ranta. "Husna in baki bashi bama duk inda kika kai sai Dije da Lirwanu sun bi sun karɓo in kuma kika ɓoye da kanki dole zasu sa ki fito da shi." Wani sashe daga can ƙasan zuciyar ta ya tuna mata. "Ki bashi kawai ya aje miki in Baban ki yazo saiki karɓo ki basa ya kaiwa Maman ki." Tunani da hankalin ta ya sake tabbatar mata da tayi hakan kawai "Kuma gwanda ma ki bashi ajiyar kinga a wajen sa babu wanda zai yi tunanin kin bashi bare Baba Lirwanu ko Dije suje su karɓe miki." Husna tayi nisa sosai a cikin tunanin, shi kuma tun yana kallon ta ta kasan idanun shi harya ɗago kai ya zuba mata ido kai tsaye yana ƙare mata kallo amma bata sani ba saboda nisan da tayi cikin tunani, gashi dai Idanun ta akan shi suke amma bashi ɗin take kallo ba. Da Sandar shi ya ɗan bugi ƙafafun ta yadda baza taji ciwo ba. Firgigit ta dawo daga duniyar tunanin data shiga sai kuma tace "Yaya dan Allah na baka ajiya zaka ɓoye min?" Tayi masa tambayar tana tsare shi da manyan idanun ta akan fuskar shi dake cike da suma. A fuzge ya kalle ta sai kuma ya dauke kanshi gefe ƙwaƙwalwar shi ke san gane abinda take nufi, sai kuma yaji ta sake cewa. "Yaya dan Allah ka ajiye min a wajen ka kaga in na ɓoye da kaina Dije da Baba Lirwanu zasu ɗauke min, in kuma nace zan bawa Indo ta taya ni ɓoye wa a nan ma sai Dije ko Baba Lirwanu sunje sun karɓa, dama bazan bawa Ramma ajiya ba dan ita kona aje a ɗakin ta Baba Lirwanu yana tambayar ta zata bashi, hmmm ita mafa tsoron shi take ji." Husna ta jero masa maganganun cikin rashin wayo da sakalcin da wahalar rayuwa ke sawa ta manta data iya yin ta, sai a irin wannan lokutan in suna tare da shi take jinta kamar a gaban Mamanta sannan take tunawa da wannan yanayin nata na kuruciya da bata sanin sanda take sauke masa su in suna zaune. Yanzu kallon ta yake kai tsaye amma bai motsa daga yadda yake ba. "Yaya zaka aje m.....?" Kanta ƙarasa maganar taga ya miƙa mata hannun shi a buɗe alamar ta bashi koma meye, ganin ya miƙo mata hannu saita saki Murmushin jin daɗi. Ga mamakin sa sai yaga ta fara ƙoƙarin cire ɗan kunnen ta amma sai yaƙi fita ta daɗin rai saboda matse shi da Mama tayi sosai, tanayi tana yarfe hannun ta daya ƙage harta samu ta cire ƴan kunnayen ta ɗora masa akan tafin hannunsa dake buɗe, zaman ɗan kwalinta ta gyara sannan ta ciro awarwaron hannun ta guda biyu masu kauri ta sake zubawa a tafin hannun shi tana sakin murmushi tace "Yaya ka ɓoye min su kaji, Mamana ce ta samin ɗan kunnen tace karna bari kowa ya cire min, su kuma awarwaron nawa ne ta ɓoye min tace saina sake girma sai ta bani, da Baba ya kawo ni nan randa Mariya ta ɗebe min kayana na gansu a cikin akwatina shi ne na ɓoye sai yanzu nake sawa, shi ne fa ɗazu wannan Maman Ɗan Hajjan tazo gidan mu take faɗa wa Dije wai in an siyar dasu za'a samu kuɗi har ɗan maraƙi ma za'a iya siya da kuɗin, shine Baba Lirwanu zai karɓe min ni kuma na gudu gidan su Indo tun da yamma, ai dai zaka ɓoye min ko?" Husna ta faɗa fuskar ta na canjawa. Tsam yayi yana ƙare mata kallo irin kallon da tun randa ta siya masa takalmi bai sake yi mata irin shiba, duban ta yake da duka ƙwayar Idanun sa. Maganar tace ta katse masa tunanin da ƙwaƙwalwar shi tayi nisa cikin yin sa. "Yaya zaka ɓoye min ko?" Shi kanshi bai san sanda ya rufe tafin hannunsa data zuba ɗan kunnen da awarwaron aciki ba, tana kallon shi ya zuba su acikin aljihun jallabiyar jikin shi. Hakan yasa Husna sakin dariya mara sauti... Suna haka sai ga Indo tazo wajen daga baya ta tsaya tana duban Husna tace "Ma'u zo kiji." Husna ta kalli inda Indo ta tsaya ɗan nesa dasu kaɗan, ita ta rasa me yasa Indo take tsoron yayan ta bayan bai taɓa yiwa kowa komai ba, haka kullum cikin yi mata mitar ta daina kula shi take karyayi mata illa wata rana. "Ma'u wallahi baki da wayo kiyi ta shigewa Mahaukaci har kina kiran shi da yayan ki." Ire-iren maganganun Indo ke nan a duk lokacin da tazo ta same su tare. Husna ta miƙe tsaye tana kade jikin ta sai kuma ta dube shi tace "Yaya ina zuwa." Tana zuwa Indo taja hannun ta suka yi wajen bishiyoyin dake gaban Dandali kaɗan Husna na tambayar ta ina zasu? bata ba ta amsa ba saida ta kaita har wajen mai kiran tana. Husna ta kalli mutumin da dake kiranta tsaye a jikin mashin ɗayan kuma da bata gane waye ba yana tsaye a gefan shi. "Dama na cema yanzu zan nemo maka ita." Indo ta faɗa tana dariya, mutumin da yaɗan manyan ta kaɗan yayi dariya yana mata jinjina yace "gaskiya ne kin cika alkawarin ki saura nawa." Ya faɗa yana zura hannu a cikin aljihun sa ya ciro ɗari biyar sabuwa ya miƙawa Indo, ita kuwa tasa hannu ta karɓa tana godiya. "Haba ai kin fi haka yau tunda kika kawo min ƙawar ki." Ya faɗa yana duban Husna data ɗauke kai gefe yace "Gimbiya ta Ma'u sannu da zuwa, kawai sai kika ganmu a garin ku ko? Ai Indo yau ta biya ni data faɗa min garin ku, tun ɗazu muka shigo munata neman ki bamu ganki ba saida nagan ta ta nemo min ke." Mutumin ya jero zancen ko haɗiyar yawu babu yana magana yana bin ta da kallo kamar maye bakin shi yaƙi rufuwa. Husna ta kalli mutumin ta watsar kamar bata sanshi ba sai kuma ta dubi Indo da suke magana da ɗaya mutumin suna dariya. A ranta take faɗin za su haɗu da Indo sai tayi mata rashin mutunci, dama wannan mayan mutumin ne ya zo shi ne jikin ta ke rawa saboda kwaɗayi. Ɗan Union kamar yadda Husna tasa masa sunan ya daɗe yana cewa yana sonta amma bata taɓa sauraren shi ba, mutumin ɗan Union ne a Kasuwar Litinin beguwa a ƙasan Mainar da suke zuwa cin abincin rana yake, wajen akwai masu saida abinci kala kala..... tunda suka fara zuwa wajen yake bin Husna taƙi kula shi dan ya fiya kallon jaraba gashi da suturu, duk sanda suka je sai dai su karaci maganar su shida Indo ya siya mata abinci ya bata kuɗi, Husna kuwa koya siya mata bata ci haka bata karɓar kuɗin sa, ɗazu a kasuwa tana kallon shi da Indo suna zance ashe garin su ta kwanta ta masa. "Haba gimbiya ta baza a yimin magana ba?" Ya faɗa, Husna ta kalli Indo da suka bar wajen ita da ɗayan mutumin ta juya zata tafi yasha gaban ta yana faɗin. "Haba Asma'u ai kya tsaya mu gaisa mana uhm? Kinsan fa ina sonki, kinga tsaya muyi magana duk abinda kike so shi za ayi haba mana ke sai kace ba wayayyiya ba." Yayi maganar yana wani kallon ta ƙasa ƙasa. Husna kuwa ganin ya hana ta wucewa saita koma jikin bishiyar ta tsaya ta ɗauke kanta gefe. "Yawwa ko ke fa, yanzu dai ya gida?" Ya faɗa yana matsowa kusa da ita. "Nifa bana zance ka matsamin na tafi gida." ta faɗa muryar ta na ɗan rawar rashin sabo. Kallon ta yayi da kyau yaga rashin wayo ƙarara a tare da ita sai yayi murmushi a ranshi yake faɗin "af ashe ma bata da wayo baza tayi wahalar jan hankali ba." A fili kuma sai yayi murmushi yace "Ayya ashe baki taɓa zance ba, ai kuwa zance babu wata matsala ki saki jikin ki yanzu saina koya miki yadda ake yi ko?" "A'a nidai bana so ban taɓa yiba gida zan tafi." "A'a ai ba'ayi haka ba Ma'u, nima yanzu zan sallame ki ki tafi gidan amma sai munyi zancen kaɗan sai ki tafi ko?" Ya faɗa yana sake matsawa kusa da ita. Husna na son ja da baya dan sun yi kusa da yawa sai kuma bishiya ta tokare ta. "Caraf taji ya riƙo hannun ta yana murza wa yana wani mici mici da ido kamar munafuki yace "kinga wani abu zan nuna miki ki taɓa min shi da hannun ki saina sallame ki ki tafi kinga har kuɗi zan baki da yawa jaka goma zan baki in kika yimin da kyau kinji Ma'u mai kyau." Husna gaba ɗaya saita tsorata da yanayin shi kamar wata shashasha kuma saita ɗaga masa kai dan ita burin ta kawai ya bata hanya ta tafi. Shi kuma gaulan ganin tayi haka sai yayi murmushin samun nasara a ranshi yana faɗin "kai ashe ma sakara ce mara wayo na tsaya ina bin kanki, ai da nasan haka kike ba wayo da tun a kasuwa na shafe ki." Ya zayyano zancen a ranshi a fili kuma sai yaci gaba da hillatar Husna har ya fito da jikin shi bata sani ba. "Kinsan wannan abun." Ya faɗa yana turo mata shi gaban ta Husna ta girgiza kai tana kallon abun cikin rashin wayo da tsoro tace "wallahi ni ka matsamin na tafi gida. "To kin gan shi yana motsi ko? To har Ruwan sama yake yi kuma taɓa ma kiji."

Chapter 26 of 31